[Advertisements⬇️]

MISBAH BOOK 2 CHAPTER 8 BY SA'ADATU WAZIRI - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MISBAH BOOK 2 CHAPTER 8 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

amsa sallamarta. Tayi murmushi, a ranta ta ce, “Wannan
akwai son nunawa mutane isa”.
Gado ya nufa ya kwanta, ya juya mata baya. Ta matsa kusa da gadon. “Deeni abokina ba gaisuwa? Ko fishi kake
dani ne? Sorry”.
Ta kama kunne, “Na tafi na bar abokina, to ai ba laifina ba ne, in na zo baka kula ni, ba ka jin magana ta, ba ka taya ni aiki, shi yasa na daina zuwa. Ina zaune yau a gida sai (mind) dina

ya dinga fada min Decni abokina yana (missing) dina, kuma gashi na zo ka juya min baya”. Duk surutun nan da take bai ce mata kala
ba har ta gaji ta kyale shi, can ta canja salo. “Naji, labarin abokina ma’abocin son karance-karance ne, ko zaka iya fada min waye (favourite author) dinka?”
Har yanzu bai kulata ba, nan ta mike ta bar inda yake ta zauna kan kujerar da ke dakin, ta jawo jakar da ta zo da shi ta fara ciwo littatta fan da ke ciki tana dubawa, har yanzun ya juya mata baya. Waya ta dauko tayi kamar tana magana.
“Naga kun sa min sabbin littattafai har wanda bana karantawa, wa ya ce kusa min littafin MISBAH? Ni bana son karanta labarinsa, yabi ya ishe mu da labaran rikicin rayuwa, duk labaransa na bakin ciki shi kullum sai wahalar da mutane, kullum yana hada mutane da matsaloli. In soyayya ce ma yayi ta wahalar da su, mutum ba zai samu wanda yake so ba”. Tana maganar tana satar kallonsa.
Gani tayi ya juyo ya mai da hankalin sa kanta gaba daya, ganin ya mai da hankalinsa gareta tasa ta ajiye wayar ta juyo da sauri suka hada ido, ya yi saurin kau da kai. Tayi dariya ta mike ta matso kusa da shi

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


Www.bankinhausanovels.com.ng
hannunta rike da littafin.
“Kasan labaran marubucin nan kuwa?”
Ya dago idanunsa ya tsareta da su, “Kar ki sake”.
Ya fada yana kallonta har ta so ta rikice, akwai wani abu a muryar sa mai sa a saurare shi, kuma ayi yadda yake so. Zai iya (controlling) mutum da muryar sa kawai wanda za mu iya cewa baiwa ne da Allah Ya yiwa Deeni.
Tayi saurin cire idanunta cikin nasa, ta ce. “Kar in sake me?”
“Zagin (best authur) na MISBAH. Dazu
kin tambaye ni waye (best writer) na, to MISBAH ne”Ta dan yi murmushi ta ce, “Ai ba zaginsa
nayi ba, gaskiya na fadi”. “Ba gaskiya bane, me ka sani akan
rubutun MISBAH?”.Fada min, ina son sani”.
Haka nan yaji yana son biye mata, ya ce.”Ba zan fadi ba sai dai in kina so mu zama abokai kamar yadda kika nema ki dauko sabon littafin da kika ce ya yi sabo ki karanta min, saboda yanzu ina da ciwon kai ba zan iya karatu ba. Kinga kema in kin karanta za kiji wani darasi ne da irin (logic) hikimar da ke cikin rubutun sa”.
Tayi murmushi, “Me zai hana? Zan karanta maka, amma ba don mu zama abokai ba, saboda na riga na zama bokiyar ka tun tuni. Sharadin karanta maka labarin MISBAH shi ne, zaka dinga jin maganata, zaka dinga fada min damuwar ka, sannan zaka yarda in dinga duba lafiyar ka”.
“Lafiya ta?” Ya tambaya yana kallonta. “Ban fada maka abokiyar ka Bahijja likita
bace? Kuma na lura abokina baya cikin koshin lafiya, kamar ciwon kanka, in ka bani hadin kai cikin kankanin lokaci zamu yi maganin sa. Sannan kana fada min damuwar ka in baka shawara, kaga riba biyu, yi sauri ka amince, yi sauri ka yarda”.
Kallon ta yake yana mamakin ta, ita ko wace iri ce? Bata fushi, bata gajiya da magana,duk da baya kulata ba ta gajiya da duk halin da ya nuna mata, gashi har ta koya masa ya saba da ita da halayyarta.
Zura masa ido tayi tana kallon sa, “Ina sauraron amsar ka”.
Bai bata amsa ba sai jan filo da yayi ya hada su wuri guda yayi matashi da shi, ya dago kansa tare da dora kafa daya kan daya. Ya kalleta ya ce.Ina jinki”.
Ta yi murmushi, “Ina son (style) dinka da (attutude) dinka”. Tayi saurin ciro wani (card) da biro a Www.bankinhausanovels.com.ng jakarta.
“Sa min hannu mana (autograph) in zama mutum ta farko saboda nan gaba in ka fita kana yiwa ‘yan mata wannan halin za su haukace akan ka, kasan ‘yan mata na son namiji mai aji (classic tall, handsome) sannan ga (attitude), yana musu jin kai, yana shan kamshi, magana ma tsada take masa, yanzu sai su haukace akan ka. Kaga lokacin nan zan zo ince in suna son zuwa kusa da kai to su zo ta wajena, saboda ni abokiyar ka ce, ta hannun damar ka, har (Autograph) dinkaina da shi. A lokacin ni zan zaba maka irin matar da ta dace da (personality) dinka, wacce za ku dace, zata haifa maka (cute cute little angels)”. Tsayawa yayi yana kallonta kamar wata
t.v, yana mamakin ta. Cikin tsawa da daga murya ya ce, “Za ki karanta ko a’a? Na rasa wane irin tunani ne da ke”.
Ta harare shi, “Kai, kar fa kaga na ce ni abokiyar ka ce ka nemi raina ni, ni yayarka ce, na girme ka (at least respect my age) ka daina min tsawa”.
Juya mata baya yayi ya kyaleta, dariya ma ta bashi, ya hau murmushi shi daya.
Leka shi tayi ta ce, “Laa murmushi nake gani a fuskar ka? Amma shan ko kamshin nan ya fi maka kyau, gaskiya zaka daina murmushi kar ya bata maka kwatancen ka na (Mr. Attitude)”. Karamin filon dake gabansa ya dauka ya.wurgeta da shi, layi saurin cafkewa tana dariya taceTo tsokanar ya isa, lokacin karatu yayi”.Nan ta dauko wasu littatta fanta ta fara karanta masa.Ya juyo ya kalleta, “Sabon littafin MISBAH”.
Nan ta hau ‘yan kame-kame tana zare ido, “Ka bari wannan sai gobe, bari in fara maka da wani”.
“Ban so”. Ya fada kai tsaye “Sai kin fara wannan”.
“To naji (Mr. Attitude)”.
Nan ta dauko wani litta fin da tayi BALLE
ta karanta masa, don haka kawai ta juya masa
baya ta soma kirkiro masa sabon labari a lokacin, saboda duk littafin da zata karanta masa nata ya sani, kuma ba yadda za ayi ta karanta masa labaran wasu ta ce nata ne, don haka tayi dabarar kirkira ta hada masa labari a lokacin. A hankali yaji labarin na ratsa shi yana taba zuciyar shi, yaji yana sa shi nishadi, bai san
yaushe ya juyo ba ya sa mata ido duk da ta bashi baya, ya lumshe ido yana sauraronta. Bahijja na ta kokarin hada labarin kiran Sallah ya katse su, tayi godiya ga Allah ta juyo ta kalle shi.
“Lokacin sallah yayi”. Ya bude ido, “Kinyi alkawarin ci gaba?”
Ta girgiza kai, “Amma bayan ka dawo daga masallaci”. Mikewa yayi ya fita daga dakin ya nufi
masallaci, sabanin da da yake sallah a daki. Fitar sa ya bata damar gyara gadon da kade kurar da ke kan gadon, ta tattara dakin sannan ta fita ciki tayi dakin Mama don yin sallah.
Mama ta sa aka kai masa abincin sa daki, yayin da suka zauna da Bahijja suna hira wanda duk ya kare akan rashin lafiyar Deeni ne da irin canjin da aka samu sosai a tare da shi.
Deeni ya dinga kaiwa da kawowa cikin dakin yana jiran dawowar Bahijja a haka ta same shi. Www.bankinhausanovels.com.ng Ka ci abincin kuwa?”
“Sai kin karasa min”.
Ta nade hannu, “Sai ka ci abinci”. “Ba zan ci ba”.
“Nima ba zan karasa ba”.
Nan ta bude abincin ta zuba masa ta mikas masa, karba ya yi da karfi yana ci..Bi a hankali kar ka kware, baka san cewa akwai (manners) na cin abinci ba ma?” Ban sani ba Mamana, sai kin fada min”. Ta girgiza kai, “Za dai ka iya kirana
yayarka amma banda maman ka”.
Murmushi ya yi ya girgiza kai, ya kyaleta
har ya gama cin abincin ya mika mata. Tayi dariya, “Good boy, karbi magani kasha”,
Bai musa mata ba saboda burinsa ta cigaba masa da labarin da ya tsaya masa a rai, yayin da Bahijja ke tunanin ta ina zata fara karasa masa? Haka dai ta zauna tana hado labarin tana jan ransa har bacci mai karfi ya fisge shi alamar maganin da yasha ya fara aiki, ta kimtsa dakin ta tattara jakarta da (box) din maganinsa ta adana wuri guda, ta zo fita ta tsaya tana kallon sa.
“Ina taya ka murna da sabon canji da aka soma samu a rayuwar ka, na fahimci kai mutum ne mai kirkin gaske da saukin kai duk da zafin zuciyar ka”
Sau da dama Bahijja kan debewa kanta kewa ta hanyar hidimar Deeni da asibiti wanda ta lura suna taimakon juna ne ta samu abinda ke debe mata kewa, tana mance damuwarta da kuncin da take tsintar kanta na dan wani lokaci, yayin da in ta koma gida da dare ne komai ke zama mata sabo, soyayyar mijinta da danta ya dawo mata sabo. Www.bankinhausanovels.com.ng
A haka kullum Bahijja ke yi da Deeni, har (time table) na karatu ta sa musu, in suka yi karatu na addini kamar Alkur’ani da sauran takardu, sai ta yi ta kokarin hada masa labarin da take kirkira, daga nan sai shawarwari ya biyo baya. Cikin dabara da hikima da kwarewa irin nata ta dinga masa (brain therapy) tana bashi addu’o’i da magani na asibiti da (Islamic medicine) kamar su Habbatussauda da Zaitun da makamantan su, tana bashi shawararwari masu amfani da misalai kala-kala.
Haka nan cikin dabara ta dinga dangana labarin da take masa na kirkira da labarin rayuwar sa, a hankali ta dinga saita tunaninsa har ya soma manta damuwar sa da bacin ransa. Ya tsinci kansa da rungumar sabuwar rayuwar da ya tsinci kansa, wacce yake jin dadin ta. Kana ganinsa zaka ga alamar sauki a tare dashi, sai dai duk lokacin da yaga mahaifinsa ko yaji sunan s uwansa Shamsu yakan tsinci kansa cikin bakin çiki da damuwa
sKamar kullum yau da ta shigo samu ya yi kaca-kaca da jakar takardun da suke karatu yana uta bincike”Meye haka Deeni? Me kake nema?”Naji sauki ne nake neman littafin da kike karanta min na MISBAH in karanta, meye sunan
olabarin ma?”Ras! Taji gabanta ya fadi.Ya tsarela da ido, “Ina littafin?”  Tayi saurin kau da kai, “Ban sani ba, don
kawai kana neman littafi sai ka wargaza min kaya? To sai ka tattara” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ba zan tattara ba”. Ya bata amsa kai atsaye.Ba zan tattara ba, kuma sai kin bani littafin nan”, in naki fa?
In kinki yau bazaki fita a dakin nan ba
Hannu yasa ya danna password din kofar

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]