[Advertisements⬇️]

MISBAH BOOK 2 CHAPTER 5 BY SA'ADATU WAZIRI - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MISBAH BOOK 2 CHAPTER 5 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

kituna yanzu nauyin asibiti da sauran al’umma da ke cikinsa na kanki, ki tuna mafarkin mu ne da burin mu wannan asibitin. Sai dai ki kula kar abinda ya faru dani ya faru da ke, mutum yana nan yana rayuwar sa bai damu da wani ba ashe makiya suna nan sun sa masa ido suna neman yadda za su cutar da shi.
Ki tuna nauyin asibiti da Muhammad na kanki, sannan in bani da rabon haduwa da Mama in ta zo kun hadu kice ta yafe min”. Bahijja dai kuka take kamar zata hallaka, ga tsoro da fargabar rasa mijinta, ga maganar sa mai kama da bankwana, ga azabar ciwon da ta ganshi a ciki,

“Dole ne in maka kuka my dear, dole kuma in yiwa kaina kuka. Mutanen nan sun cuce mu, sun rusa mana ‘yar karamar duniyar mu da muke farin ciki a cikinta”.
“Sun cuci kansu Bahijja, ki tuna kece me lallashim wasu da (couseling) dinsu in sun shiga hali makamancin wannan, yau rana tazo da za ki yiwa kanki wannan fatan.
Bahijja kada ki karaya kima fi yadda na sanki da, kiyi ta addu’a Allah na tare da ke, kada ki taba jin ke kadai ce a duniya. Ki tuna duniya taki ce da mutanen arzikin da suke cikinta, duk wani Musulmi dan uwanki ne.
Abu na karshe Bahijja, wannan bawan Allah da ya shiga rudanin rashin lafiya da karin ruda masa jiki da kwakwalwa da ya samu ta sanadina, ina fata za ki taimaka masa ya warke da iyakar iyawar ki. Ina fata za ki gyara kuskuren da nayi”. v
Tayi karfin halin share hawayen da ke
zuba mata tare da yi masa murmushi, ta ce.
“Inshaa Allah my dear zan taimaka masa dear zanyi har kaima ka samu lafiya mu taimaka masa tare, mu cigaba da kula da asibitin mu da

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Muhammad, duniyarmu za mu sake ginata tare da kai inshaa Allah”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Duk da yana cikin ciwo sai yayi mata murmushi alamar gamsuwa da maganarta. Nan ta kwantar da kai a gefen filonsa da ke jike da jini, tana rike da hannunsa, ita kadai tasan irin radadin da zuciyarta ke mata, tana masa addu’ar fatan samun sauki da lafiya.
Hawaye na gudu a idonta ba kakkautawa, tana tunanin duniyarta ta zo karshe a duk lokacin da ta rasa Doctor Mislihu.
“Ya Allah nasan Baka barin wani don wani, Ya Allah Ka bani karfin imani da karfin zuciyar daukan duk wani ikon Ka da Ka aiwatar akan mu”.
Da irin wadannan addu’o’in a zuciyarta bacci ya debe ta bata sani ba, sai farkawa tayi taji hayaniya akanta. Sauran likitocin asibitin ne suke bata hakuri mijinta kam ta Allah ta kasance akansa, ya bar duniyar.
Jin abin ta dinga yi ba zata, kamar a mafarki. Wani jiri taji yana dibanta tana salati tana kallonsa tamkar mai bacci.Wayyo duniya, duk wanda ya dauke ki da zafi tabbas yana cikin masu asara. Jiya tana tare da mijinta, abokin rayuwarta, gatanta a duk duniya, amma yau ba ya duniyar.
Hawaye na zuba ta ce, “Allah Ya jikanka Doctor, Allah Ya maka rahma, Ya yafe maka kurakuran ka, Yasa ayyukanka na alkhairi su bika”. Www.bankinhausanovels.com.ng
#Bahijja tayi kuka tayi kuka har taji ba dadi. Kafin a yiwa Doctor wanka da sutura ‘yan uwansa suka iso daga Kano, mahaifiyarsa da danginta tare da dangin mahaifinsa tare da su akai masa sutura aka kaishi gidansa na gaskiya, yayin da mahaifiyarsa ta yafe masa tare da abinsa da addu’a.
Gidan Bahijja suka dawo aka yi ta karbar gaisuwa, yayin da maganar rasuwar ta baza ko ina, saboda Doctor Mislihu yayi suna kwarai, haka yana da jama’a. Ya yi suna ba don yanada kudi ba sai don kwarewar sa ta wurin aikinsa da sunan da yayi saboda asibitin su.
Kwana uku aka yi ana karbar gaisuwa, mahaifiyar sa ta ce su za su tattara su koma Kano, don ita har yanzu ba wai tana son Bahijjabane, asali ma ta dauka nauyin mutuwar danta akantasaboda tace ita ta sa shi zama a Lagos yaki komawa can gida Kano, ya guje su. Tunda tayi sanadin sa to za su kwace danshi su tafi da shi ta dinga ganin jikanta. Kuma ta ce ko da wasa Bahijja kar tayi tunanin cewa zata zo ko da ganinsa balle daukar sa.
Anan fa ciwon ya yiwa bahijja bibbiyu, hankalinta ya mummunan tashi. Ta yaya za a rabata da Muhammad da bai fi wata takwas a duniya ba?
Ba irin rokon da bata yi musu ba har ta musu alkawarin kawo shi in ta yaye shi, amma fir mahaifiyar Mislihu ta ki. Haka ta tattara shi suka koma Kano yana kuka Bahijja na kuka suka rabu.
A wannan lokacin Bahijja tayi dan karmain hauka, ko dai ta dinga jin muryar Doctor Mislihu, ko kukan Muhammad. Zuciyarta tayi rauni sosai, kullum tana cikin kuka, bata iya kulla komai. Daga karshe ita ke tashi ta share hawayenta, tayi karfin halin lallashin kanta.
Ta so ta bi iyayen Mislihu Kano, sai dai kuma ta tsai da kanta, ko me za su mata ba zata taba fada da su ko shari’a da su ba albarkacin dansu da take so take ganin girma da darajarsa fiye da kowane namiji a duniya. Don haka ta sawa kanta hakuri, kamar yadda ta jure rashin mijinta shima dan nata zata jure rashin sa, in da rabon haduwar su kuma da rai da lafiya to Allah Zai hada su wata rana. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka Bahijja ta hau takaba, kullum kwana take tana zubar da hawaye tana yiwa mijinta da danta addu’a tare da fatan Allah Ya kara mata hakuri da juriya.
Daga ita sai Baba Andi a gidan wacce take rainon Muhammad, kasancewar mata kyautatawa da take mata ta dauketa kamar uwarta, yasa itama ta zauna tare da ita tana mata hidima tare da bata shawarwari da bata baki da lallashi. Tana matukar tausaya mata.
Bahijja ta kasance bata da kawa ko wata ‘yar uwa ko wata da suke da kusanci na sosai, saboda a RAYUWAR BAHIJJA ba (space) na kawaye, wato ba fili ko lokacin yin kawancee a rayuwarta, saboda ayyukanta da rubuce rubucenta. Mijinta da danta sune kawayenta, sune rayuwarta.Don haka yanzu rayuwa tayi mata wahalar gaske wanda daga rubutun har aikin sai da suka gagareta, damuwa da yawan tunani suka sako ta a gaba, ta rasa inda zata sa ranta taji dadi. Tuni ta koma ga Allah, kullum tana cikin karatun Alkur’ani da addu’o’i tare da yawan istigfari don neman waraka daga halin da ta shiga.
Wani lokacin takan rufe ido ta dinga tuno da kalaman Doctor wanda suke kara mata karfin gwiwa, taji tana son mikewa tayi wani abu me amfaniz da rayuwarta bayan kuka da bacin rai.
Da haka a cikin wannan halin da yanayin ta gama takabar, sai dai duk da hakan ba tayi yukurin fita fara wani aiki ba.
Bayan rasuwar Mislihu Alh. Umar ya samu labari don haka ya zo ya dauki Deeni, bayan ya farfado ya samu sauki na jiki amma fa kwakwalwar sa tamkar ya farka da sabon abu, kullum yana cikin firgita da yin wasu abubuwa tamkar yana tsorace.
Haka mahaifinsa yasa ana yi masa addu’a su ma suna masa, har ya dan samu sauki, amma kam har yanızun yana da matsala. Yayin da kotu ta yankewa Dr. Yasir da sauran ma’aikatan asibitin hukuncin daurin rai da rai. Allah Ka tsare mu da son zuciya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Asibitin ya tsaya na dan wani lokaci saboda abinda ya faru wanda da gidan da asibitin duk sun shiga gado, sai dai dama asibitin nasu ne su biyu da shi, sannan itama tana da gadonsa. A takaice dai wurin ya dawo nata da danta Muhammad, wanda tayi alkawarin kula masa da shi ta damka masa kayansa wataran in tana da rai. Don haka ta shirya komai a rubuce saboda mutuwa ta kuma nemi (lawyer) na Musulunci da Alkali suka zama shaida.
Watanni shida da rasuwar Doctor Mislihu bayan gama takabarta ta hau shirye-shiryen yadda za ta farfado da asibitin ya fara aiki, ya dawo kamar da, a niyyarta ma har yafi da, saboda tsaro da tantance malaikata sai yafi nada.
Bahijja kenan mace mai kamar maza, haka ta dage tana ta shiga da fita ba zama, tana neman taimako da yadda za ayi komai ya farfado, wanda gudun tunani da bacin rai yasa ta dage dazama (busy) yau bata nan gobe bata can har sai da ta tabbatar komai ya dai daita mata kamar yadda take so, komai ya farfado ya soma aiki, sannan ta samu nutsuwa kadan.
A kullum ta zauna maganar Deeni ke fado mata, da sako da amanar taimakon sa da mijinta ya damka mata.
“Ya zama dole in nemo shi inji ya ya kare? Sannan in sake duba (case) dinsa inga wane irin (treatment) ya kamata a masa”.
Bata ɓata lokaci ba ta fara da binciko (file) din Deeni wanda ta riga da dama tasan wannan (case) din, sai kari akan (wrong treatment) din da aka yi ta masa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan ta binciki (address) dinsa, sannan ta sake zuwa asibitin da aka kwantar dashi tare da Doctor ta sake bincike akan (treatment) dinsa, sannan ta sake stabbatar da (address) dinsa. Daga nan ta daura damarar niyyar taimakon sa har sai inda karfinta ya kare, in ta tabbatar ya samu lafiya zata samu kwanciyar hankali, burinta da na mijinta ya cika, daga nan zata ci gaba da cika burin mijinta da nata har ta Allah ta kasance akanta, idan kuwa Muhammad ya girma ta damka masa dukiyar sa, ta ci gaba da masa addu’a da shi da mahaifinsa. Wannan shi ne burin Bahijja da kuma kudurinta, bayan shi ba komai a zuciyarta da tunaninta, daga aikinta sai rubuce-rubucenta.
Haj. A’i na zaune a falo ita daya tayi nisa sosai cikin tunani, tana tuna yadda rayuwar su take da da ta yanzu, lokaci guda rayuwar su ta canja, sun baro yankinsu cikin ‘yan uwa da abokan arziki, inda suka saba da rayuwar su da komai, sunyi nesa da dansu da ‘yan jikokinta guda biyu da duk da suna zuwa lokaci-lokaci, ga rayuwar Deeni ta canja gaba daya. Duk kokarin da suke yi akan Deeni ba wani canji, yadda Deeni yake rayuwa yana matukar kona mata rai. Lukman ne take dan gani taji dama-dama, shima tunda ya kammala karatunsa na jami’a kullum yana tare da mahaifinsa wurin harkar kasuwancin sa, rayuwar su na cike da kewa ba wani walwala.
Mai musu aiki ce ta katse mata tunani, “Hajiya kina da bakuwa”,
“Wace ce haka? Daga ina take?”
“Gata nan”. Ta bata amsa, sannan ta juya. Bahijja tayi sallama tare da karasowa cikin falon, Hajiya ta amsa tana mata maraba tare da mata kallon rashin sani.
Bayan sun gaisa Bahijja ta kallcta, tace. “Nasan za ki yi mamakin ganina, saboda baki sanni ba. Sunana Doctor Bahijja, ni likita ce a asibitin da aka kai Deeni kwanakin baya, asibitin Doctor Mislihu. Ni matarsa ce da muke aiki tare, bayan rasuwar sa ni na ci gaba da kula da asibitin.
Kafin ya rasu burinsa ya ga ya taimaki Deeni, sai dai burin nasabai kai ga cika ba ta Allah ta kasance akan sa. Ina fatan cika masa wannan burin, don haka nake son taimakon Deeni da dukkan kokarina har sai naga ya samu lafiya”.
Ba ma bukatar taimakon ki”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Suka ji muryar Alhaji kamar daga sama.
Dukkansu suka mai da kallon su kanAlhajin, ya ci gaba da fada.
“Yau ce rana ta karshe da zaki sake tako gidan nan, kowa yasan irin yadda ku ka kara

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]