[Advertisements⬇️]

MISBAH BOOK 2 CHAPTER 3 BY SA'ADATU WAZIRI - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MISBAH BOOK 2 CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 
a wurin. Don haka wannan ya bashi karfin gwiwar sa hannu, . ya yi cike-ciken da duk ya kamata tare da karbar (slip) don biyan kudin jinyar Deeni. Sun rabu akan washegari za su kawo shi.
A hankali ya turo kofar dakin nasa tamkar mai jin tsoron kofar, zuciyar sa na tsinkewa saboda tunanin wane hali zai samu dan nasa? Tsawon sati guda kenan bai leka shi ba, saboda gudun wani hali zai same shi.
Kamar kullum ya same shi makure a lungu guda tamkar mai jin tsoron kar azo a kama shi, fuskar sa daure tamau ba alamar fara’a a tare

da shi. In bai manta ba kayan da ya barshi da shi wancan satin har yanzu sune a jikinsa. Tuni idanunsa suka kada suka yi jawur.
“Deeni da na sani da tsafta da son gayu komai fes-fes, ba ma jikinsa ba, dakinsa, kayansa komai fes-fes suke, kuma cikin tsari. Amma yau rayuwa ce ta mai da Deeni haka, kuma ni ne sanadi”.
Ya yi haske amma ya fada, ya yi wata irin rama mara kyau, hasken da ya yima albarkacin zama wuri guda da yake yi ne, da kuma yanayi irin na Lagos. Tunda suka zo garin ko kofar gida bai fita ba, yana nan a dakinsa da aka ware masa. Mama bata fasa masa addu’a ba da nema
masa sauki da mafita a wurin Ubangiji. fa “Deeni”. Mahaifin nasa ya kira sunansa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Juyowa ya yi suka yi ido niyu, tuni kuwa ya kara daure fuska tamau, idanunsa suka jure alamar ɓacin rai ya bayyana karara a fuskar sa, ya yi saurin dauke kai.
Mahaifin nasa ya fahimci har yanzun yana cikin fushi da shi, ya matso

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


“Kayi hakuri Deeni, na maka laifi, zan yi iya dukkan kokarina inga na gyara kuskuren da na yi, Deeni kar ka hukuntani ta hanyar tsanantawa kanka da bata rayuwar ka a banza, Deeni wanne farin ciki ka tsinta a irin wannan rayuwar da kake?
Deeni, nasan ba zaka so ba kuma ba zaka yarda ba, sai dai zan fada maka ina son kaika inda rayuwar ka zata daidaita, wanda bayan nan na maka alkawari ba zan sake maka shisshigi a rayuwar ka ba, zan baka dama kayi rayuwar ka yadda kake so kuma yadda kaga dama. Ina so ka
shirya mu tafi don Allah”. Jin kalamansa da yayi na karshe ne ya juyo ya kalle shi, ya ce.
“Kai mahaifina ne, ba sai ka rokeni ba, zan maka biyayya. Ina kake so inje? Zan je amma kar ka taba zaton wai don kaina ne sai don kanka, kamar yadda ka dauko mana tun farko, ka sabar mana, bamu da zabi sai naka, to yanzu ma haka ne. Saboda ni kam yanzu a rayuwa ba abinda ya saura zaka min, baka da abinda zaka iya sake min ko bani ya sani farin ciki, ba abinda zaka min ya goge min bakin cikin da bacin ran da ke cikin kwakwalwata da zuciyata.Wannan abin da ku ka hadu ku ka min ba zai taba barina naji wani dadi a rayuwa ba, ba yadda za ayi in samu wani farin ciki ko kankani bayan cin amana da rashin kauna da kuntata mini da yaudarar da iyayena da dan uwana da wacce…”.
Maganar ta sarke, numfashinsa ya dinga fita sama-sama, bai ankara ba sai ganinsa yayi ya fadi ya suma. Cikin tashin hankali da damuwa suka yi asbiti da shi, asibitin da bai shiga yana cikin hankalinsa ba sai a sume. Www.bankinhausanovels.com.ng
Dokar farko na asibitin ya fara aiki akan su, wato su ajiye shi su tafi su barshi, kuma ba zasu sake waiwayar sa ba sai bayan wata shida wanda in ya samu wannan wata shidan za su iya zuwa bayan wata daddaya. Haka Haj. A’i da Alh. Umar suka tafi suka bar dansu cikin mawuyacin hali da ciwo, Mama tayi kuka har ta gode Allah, yayin da Alh. Umar bai yi ba, sai dai abinda yake ji a zuciyar sa yafi kuka ciwo.
Doctor Mislihu ne tsaye kan Deeni tare da sauran likitocin da ke aiki a karkashinsa, dasauran ma’aikatan asibitin suna iya dukkan kokarin su don ganin ya farfado. Sai dai fa abin ya ci tura, ba irin dabarar da basu yi ba hakan yasa ya nemi taimakon gaggawa daga sauran ‘yan uwansa wadanda suke manyansa ne ta hanyar wayar sadarwa.
Tabbas duk kokarin ka da kwarewar ka wataran sai aikinka ya kunyata ka, kwarewa da dai dai sai Allah. Dr. Mislihu bai kasa ba kuma bai yi kasa a gwiwa ba ya ci gaba da ba da himmar sa da kokarin sa, bai ji dar ko tsoro ba, sai dai abin ya matukar daure masa kai, saboda shi yasan ya sha fuskantar masu ciwo irin na Deeni.
Da taimakon Allah yana addu’a tare da yakini a zuciyar sa ya samu Deeni ya farfado da wani bakon yanayi, yana cikin tsananin ciwo da rudani, idanunsa sunyi jawur, hawaye kawai ke zuba ba kakkautawa, haka nan ya rike kansa gam alamar yana jin azabar ciwo, abin har ya kaishi ga yana doka kansa jikin karfen gadon da yake kwance.
An masa allurar da ya kamata anyi masa ya samu nutsuwa kadan, da kyar suka samu bacciya dauke shi. Baccin da ya kamata ya yi na wuni guda kafin ya farka, amma awa biyu zuwa uku kawai allurar take masa aiki, haka nan magani ba ya aiki a jikinsa.
A wannan dare Doctor Mislihu ya koma a gajiye tare da wannan damuwar a tare da shi Bahijja na ganinsa ta san ba lafiya, ta riga da tasan yanayin aiki irin nasu, akwai gajiyarwa, saboda jikinka da kwakwalwar ka da zuciyar ka duk sai sun jigata, sun wahala.
Ta shirya masa ruwa ya yi wanka, bayan ya fito tayi kokarin sauke masa gajiyar sa da (tention) dinsa ta hanyar masa matsa a gabban jikinsa tare da kansa, tana (massaging) cikin nutsuwa yadda zai ji dadinsa, kuma ya yi masa aiki.Yaji dadin hakan kwarai, ya jawo hannunta. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Na gode Bahijja, naji dadi sosai, naji dadin wannan abinda kike min don ya bani nutsuwa tare da sauke min wani (tention) din”. Tayi murmushi tare da shafa shi, tace Burina kenan inga na rage maka damuwa, naga yau kana cikin zafi, bari in kawo maka abincinka daki”.
Nan ta fita ta dawo hannunta dauke da babban (tray) ta shirya masa duk wani abinda zai bukata. (Coffee) mai zafi ta fara bashi sannan ta zuba masa abincin wanda kadan ya ci shima don ta matsa masa ne, kafin ma ta ce wani abu aka masa waya ya nufi asibitin a rude.
Wannan al’amari ya daurewa Bahijja kai, “To shin me ke faruwa ne?”
Nan ta buga waya asibitin don taji me ke faruwa? A nan aka bata labarin sabon mara lafiya da aka kawo wanda ya ta da hankalin oga.
Haka ta dinga kaiwa da kawowa har ya dawo, ta tare shi da tambayoyi amma bai amsa mata ba, ya nuna ta kyale shi akwai binciken da zai yi, in ya gama zai sanar da ita.
Wannan abu ya daure mata kai, sam bata jin dadin ganinsa haka. Ya dawo kullum yana cikin karatu da bincike saboda matsalar Deeni ta zame masa sabo, ya zama kamar (challenge) ne a tare dashi.Abokinsa Doctor Yasir ya nemo wanda
suka yi karatu tare, kuma sunyi aiki tare a da lokacin da suke (Teaching hospital) wanda shi bayan bude asibitin su ne suka rabu. Sai dai dama lokaci lokaci sukan hada kai suyi karatu.
Dr. Yasir kamar aboki ne a gare shi, kuma abokin aikinsa, don haka ya roki Alfarmar ya zo su binciki (case) din Deeni tare. Da farko ya so yasa Bahijja ciki, sai dai
baya son wahalar da ita, sannan tana cikin hutu ne, gara ta zauna ta bawa Muhammad kyakkyawar kulawar da yake bukata. Kuma yasan Bahijja sarai da daukan zafi, tana iya watsar da komai ta tsunduma kanta ciki, don haka ya yanke shawarar yayi aikinsa da kansa.
Wata guda suna bawa Deeni (treatment) amma ba wani cigaba, babbar damuwar sa yana cikin ciwo balle har a samu nutsuwar da za a saita hankalinsa da tunaninsa, balle har a san matsayin da kwakwalwar sa da zuciyar sa suke ciki. Wannan abu ya mumniunan daga hankalin Doctor Mislihu da sa shi cikin damuwa, duk maganin da ya bashi baya aiki dai dai a jikinsa yadda ya kamata yayi.
Gaba daya ya rasa nutsuwa da kwanciyar hankali, kullum bashi nan bashi can neman yadda za a samu waraka, haka ya dauki (case) din Deeni da zafi tamkar na wani dan uwansa na jini, ya ci alwashin sai inda karfinsa ya kare. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya dawo ba ya bawa kowane mara lafiya kulawa kamar yadda yake bawa Deeni, tausayin sa da kaunar sa ya shiga ransa, musamman in yaga yadda wataran Deeni ke zura masa ido yana kallon sa tamkar mai kokarin fada masa wani abu, tamkar yana ce masa “ka taimake ni” tamkar dukkan tsammaninsa na kansa. Haka wani lokaci hawaye zai yi ta zuba masa, lokaci guda kuma ya kuma rikicewa.
Abin na Deeni sai gaba-gaba yake, don haka Doctor Yasir ya bashi wata shawara akan abinda za su masa, amma fa sam ya ki yarda, yaki amincewa, saboda yana ga akwai garaje ciki, sannan ciwon Deeni bai kai har hakan ba. Amma a hankali Doctor Yasir ya dinga nuna masa dukkan wani (treatment) da za su masa sun masa, amma baya (responding), wannan shi ne (option) da ya rage dashi.
Ya tuna ya yiwa kansa alkawarin yin duk abinda zai yi don ya taimake shi, haka iyayen yaron na da dukkan wani tsammanin su akan shi. Da kyar Dr. Yasir ya shawo kansa ya amince.
Nan ya hau shirye-shirye, yasa lokaci da rana, ya gama amincewa kansa amma duk da hakan sai yaji zuciyarsa na fada masa ya nemi shawarar matarsa, ya sanar da ita, ko ba komai tana da ilimi akan ciwon Deeni sosai kamar yadda yake da shi. Da wannan tunanin ya dauki waya ya buga mata. Bahijja”.
“Yes my dear, kana hanya ne na kira ka shiru, (hope) dai lafiya”.
Ya yi mata murmushi tamkar tana kallonsa, ya ce
“Lafiya Bahijja, wani aiki ne yasha kaina da na gama zan taho. Dama ra’ayinki nake son ji akan wani abu da zan yiwa (patient) dina”.
Tayi masa dariya ta ce, “Zan yi farin ciki da baka shawara mai kyau, na lura kana cikin damuwa akan wannan mara lafiyar, kar ka damu nasan ko me zaka yi (you are the best on it)”.
Ya ce, “Duk da haka dai ina neman kwarin gwiwa a wurin ki”. Ta ce “To ina jinka, mene ne matsalar
A hankali ya labarta mata (case) din Deeni da yadda yayi ta fama da shi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta dan yi dogon shiru tana tunanin ai indai wanda ta karanta (file) dinsa ne (case) dinsa ba haka bane, abinda (report) dinsa ya ce daban abinda kuma Doctor ya fada mata yanzu da irin (treatment) din da suke masa daban.Bahijja”.Muryarsa ta katse mata tunani.Kina jina kuwa?” “Eh ina ji”.
Ta fada cikin muryar damuwa, sannan tace
“To yanzu wane shawara ka yanke? Me kake ganin zaka masa?” “Shawarar da muka yanke yanzu ni da
Doctor Yasir shi ne, zamu masa (E.C.T)”.
Tace “Whattttttt!”.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]