[Advertisements⬇️]

MALIKA MALIK CHAPTER 12 BY JANAFTY - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MALIKA MALIK CHAPTER 12 BY JANAFTY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Abangaren gidansu Zahra ne Shirye Shiryen yafi yawa saboda itace uwar gayyah,Tun ana saura sati daya biki Hajiya Saratu momi ta dauko hayar wata Falmata mai gyara amare daga maiduguri,wacce zata gyara Zahra ciki da bai kafin ranar bikin yazo,Hakika bakaramin burgeta momi tayi ba,haka takasa boye murnata afili dama ita burinta taje ta rikita Saleem wanda zai manta da kowa da komai sai ita shalele Fatimatul zahra’u.

Bangaren gidansu Saleem kuwa Abbi shima ya saki aljihu ana ta Shiryen shiryen biki,Tunda daga kano Abuja za’a kawo zahra sai ta kwana washegari su Wuto zamfara da ita,wannan Auren na musamman ne,domin yazoma Saleema akan gaba,sun gama Final Exams dinsu ta tararro ta dawo gida aka Shiga shagali da ita tayi alqawari sai ta chusama Malika haushi Sosai da sosai,Balle ma Da Sadiq ya sanar da ita itama Zahran ba baya ba akwai kyau ga iya kwalliya da Iya tsara kalamai,Kawai sai taji lokaci ta burgeta saboda neman suna harda karban nombarta ta kirata suka gaisa.

Itako Zahra an samu nayi ai sai aka zare an samu kanwar miji abagas,abun takaichi ma Saleema bataji kunya sanar da Zahra duka sirranka auren Saleem da Malika wanda batasan dasu ba,yazamana Family issues ne,itako zahra kanta ya fashe harda daukan ma Saleema alqawarin sai inda karfinta yakare game da mallakan Saleem,harda ikirarin sai malika ta barmata gidan🤔.,Saboda munafuncinsu yazo daya,sai ga Saleema ta Shirya kayanta tsab tatafi kano gidansu zahra tace chan biki zai fi dadi,Allah barshi in Za”a kawota sai ta biyosu su dawo tare,Ummi da Abbi basu zargi komai ba sun zata dama kila chan kawayene suna da kyakyawan alaqa duba da itama Saleema zamanta yafi yawa akano,basu san ko kullewan ta munafunci bane.

Duk wannan Abun Saleem bai san dashi ba don babu wanda ya sanar dashi,Dayake ma Saleema yanzu bata gabanshi Tunda sukayi karon nan da ita agida yadaina mata dariya,gabda bikin yaga kiranta ammh sai ya Shareta bai daga kiran ba kuma bai calling dinta back,sai ana gobe biki yana Shirin tahowa Abuja inda zasu hadu anan gidan Abbi su Tafi daurin Aure,Zahra ta kirashi tana rokonshi don Allah ya iso kano yau ya hallarci Dinner dasuka Shirya,kawai sai yaji kamar muryan Saleema cike da mamaki yake tambayan Zahra murya wa yakeji kamarta kanwarsa Saleema..?Zahra na mirmishi ta sanar dashi itace,gabansa ya fadi hannunsa bisa bakinsa,yana jinjina al”amarin na Saleema   tsoro ya darsu ranshi rai bace yace zahra tabata waya nan akaba Saleema waya ta karba tana gaisheshi bai iya amsa gaisuwanta ba ya kira sunanta a kakkaushe..

   “Saleema,Don ubanki uban me kikazo yi gidan su Zahra..? Tana tabe baki tace”Yo laifi ne don nazo gidansu matar da zaka aura,Don mutaru muyi shagalin biki tare..? yana Numfarfashi ya tare ta yana Fadin”Ke rufemin baki munafuka,kinsan Allah Saleema kinsan dai nasan halinki wlh tallahi in naji wata mgana ta Fito to nasan daga bakinki ne,Kuma sai naci ubanki na kakakkrya ki shegiya Mai dogon baki kawai..”Yafada yana huci ya yanke kiran,Tabe baki Saleema tayi kafin tace acikin ranta”Ni ba munafuka bace..”Tafada tana murguda baki kamar tana gabanshi,Nadira ce ke tambayanta ko lafiya,sai ta barsa tace bakomai..,”

Abangaren Malika ma,Joda da Maman Abba suna ta gudanar da Shiryen Shiryen zuwa amarya ta ango,Maman Abba da kanta ta karbi kayan Malika wajen kala biyar taba telanta ya tsaro mata dinkuna na gani na fada,kuma saleem yabada kudin da kanshi,kuma zahirin batu dinki sun Fita sosai,Gashi yayi mata masu yalwar saboda cikin jikinta.

Duk da Malika na boye kishinta bata bayyanashi ammh yau kam takasa control din kanta,balle dataga Saleem ya Shirya kayansa Zai Wuce Abuja bazai dawo ba sai jibi in sun taho da amarya,tana zaune agefen gado sanye da doguwar rigar Atamfa cikin dunkunan da Maman Abba ta dinkomata,tayi mata kyau sosai balle da cikinta yakara tsufa,sai ta dan kumbura kadan fuskarta ta cika sai takara kyau,tagumi ta zabga hannu biyu tana kallonshi yana kokarin saka botir din gaban wani yadinsa Fari ammh Shara shara ne,domin hatta Farar vest dinsa ana gani,Hulansa ya dauko xanna bukar,mai adon baki ajiki domin aikin jikin rigar baki ne,Yadorata akai agogonsa baki na fatar damisa yake daurawa kafin hankalinsa ya koma kan Malika wacce idanuwanta suka fara cika da kwallah.

Yadade yana kallonta kafin ya saki ajiyar zuciya ya karisa kusa da ita,har ya durkusa gabanta bata Sani ba,sai da sanya hannu ya ciremata hannuwan datayi tagumin dasu,kana ta dago tana kallonshi ido cikin ido, Kwabe Fuska yayi yana kallonta yace”Why…? Haba Amanata meyesa kikeson Allah ya kamani ne? ehe kina tagumi abunda kikasan babu kyau meyasa kikeyi..? Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonshi dukar da kai tayi saboda bazata jure kallon kwayan idonshi saboda suna dauke da wasu sirranka wanda suke haddasamata wasu irin yanayi atare da ita.

Kanta na kasa tace”Na daina..”Ta fada tana sosa hanci dan mirmishi yayi kafin ya saka hannu ya dago habarta yana Fadin”Mejego..Uhmmm..Menene fadamin naji..? Yafada yana shafa lebenta da hannunshi guda daya,rikemai hannu tayi tana kokarin maida kwailarta tace”Katashi katafi kada kayi dare a hanya..”,Kwayan idonta yake son gani,ammh sai taki ta rinka kauda kai,shikuma yana binta da ido,ganin haka yasa yatashi tsaye yasa hannu ya dagata tsaye yana Kallonta cike da kulawa,bai bata zarafin mgana ba, ya budemata hannuwanta tafada,lokaci daya ta saki kukan data ke rikewa Tun dazu..”matseta yayi yana shinshinar Wuyarta cike da salo,lokaci daya yana Shafa cikin jikinta,Tunda dama ta gefe ya Rumgumeta,saboda cikin daya yi mishi shamaki.

Sai da tayi kukanta ya isheta kana tayi Shuru tana Ajiyar Zuciya,tare da sauke Numfashi,Mirmishi yayi yana Kara gyara mata daurin dankwalinta bayan ya bata Sumbata asaman tsakar kanta yake fadin”Kamar kada natafi Amanata,inaji ajikina zanyi kewarki sosai..”Da sauri ta dago kanta tana kallonshi kafin tace cikin sauri”are u Sure zaka yi kewata mallam..? Yana kallon cikin kwayan idanuwanta yace”Very Sure..Kefa zaki kewata..?Bata iya bashi amsa ba,sai kawai tayi dage ta kama lebenshi tana tsotsa da sauri rike kanta da hannu daya yayi,hannu daya kuma yakara mtseta cikin maranshi cike da salo Malika take sumbatarshi har sai da suka gaji kama suka saki juna suna maida numfashi,bisa kirjinsa ta lafe tana Fadin”Zanyi kewarka sau ba adadi mallam,kariga ka zama jinin jikina,rayuwata bazata iya tafiya ba sai da kai,ina nace maka bani son zama dakai akoda yaushe wlh nayi karya mallam,i so much luv u,don Allah karka bani ko bayan kayi aure..”Tafada hawaye na wanke mata Fuska.

   

Wani sanyi yaji ya Shiga cikin ransa,cike da farinciki ya damki Fuskarta da hannu biyu yana kallonta yace”Da gaske kina sona malika..”?Gyada mai kai tayi hawaye suna kwaranyomata,Bakinta ya sumbata kafin yace”Duk da yadda na lalata rayuwarki na toxartaki keda mahaifinki..? Hannayenshi ta damke tana Fadin”Da shine ma nakejin ka mamaye duka raina,kayi sanadiyar Chanza malika zuwa wata malikar dabam,in ko hakane ka taka muhimman rawa arayuwata mallam,ka koyar dani abubuwa dama,wanda ni banda bakin godemaka sai dai nayita maka addu”an Allah ya saka maka da gidan aljannah Firdausi..”

Bai samu zarafin mgana ba,illah matseta dayayi ajikinsa yana shakan kamshin Turarenta,cikin wata murya yake fadin”kinsa me? bai bata zarafin mgana ba ya cigaba da cewa”Nima sai daga baya nadinga jin Abunda na aikata gareki ban kyauta ba,mussama ranar danaje daukanki agidanku naji matukar kunyar yadda Daddy ya karbeni batare da yayi Duba da irin Tozarcin dana miki ba ya karbeni hannu bibbiyu kuma wani karin nadamar tawa yadda yabani ke batare da Gaddama ba,ranar naji kunya sosai..”Mirmishi tayi kafin tace”Ni kuma abu daya ke ban haushi a abunda kayi min in na tuna..? 

Dago kanta yayi yana Fadin”Menene shi..? Gira ta matse tana Fadin”Har ka manta..”Tafada tana hararanshi,ware ido yayi kafin yace”Srry gayamin don Allah..”Yafada yana Shafa dogon hancinta zuwa karamin bakinta,Shagwabe Fuska tayi kafin tace”Yadda ka karbi Virginity na da karfin Tsiya mana..”Tafada tana Wulkamai ido cike da salo,Mirmishi ne ya Subucemai wanda sai da duka fararen hakoransa suka bayyana awaje,hannunta ya riko yana Shafawa har zuwa saman kirjinta yana mirmishi kafin ya gangaro zuwa katon cikinta,cikin husky voice yace”Ni kinga wannan daren D Unforgtable Night and moment kenan bazan taba manta wannan Daren ba..”Yafada yana Shafa cikinta yana wani munafikin dariya.

Fuska ta kwabe tana kallonshi kafin tace”Saboda mene…? Hannunsa ya dora bisa lebenta yana zagaya babban yatsanshi dashi yace”Baki sani ba..? ta gyada kai tana kallonshi Yar dariya yayi kafin yace”Dare ne mai cike da Tarihi ,dare ne da kika Shayar dani wata zuma mai dadi wanda banta zaton akwaita ba,Wlh tallahi i can Explain buh abu daya na sani ke ta dabamce domin Haryanzu kina kan Shayar dani wannan zumar,sai dai na ranar is so Sweet and special..”Yafada yana kanne mata ido daya,Dariya da kunya suka kamata,sai takaimai duka Kirji tana mai kukan Shagwaba dariya yake yana Fadin”Allah am Serious,ko zaki karamin ne,sai na kara tabbatarwa..”Wata uwar harara ta makamai kafin ta warci hannunta tana kallonshi,Juyawa tayi ta dauki yar jakarsa wacce ya sanya kaya ta rataya tana Fadin”Ni..? ai yanzu mun tsufa abari amarya tazo sai tabaka sabuwar zumar,muje na takamaka kaga dare nayi kuma,sadiq karya ga kamar ni na tsaidaka..”

Yana dariyanshi na Nishadi yabiyo bayanta tana tafe da kyar yace”Ai wlh kece kika tsaidani ko ya tambayeni haka zancemai,mganar zumar amarya kuma nidai Taki nasani ki bari in tazo na dandani tata,sai na tantance..”Yafada yana shafa gemunsa na rashin kunya cike da Nishadi tana jinsa tayimai banza ta Fito daga dakin tana mirmishi cikin ranta.

Har cikin kichen din yabi Su maman Abba yayi musu sallama,sukai mai fatan isa lafiya,da kuma Fatan Allah yasa adaura aure lafiya,Tare suka Fito da malika har haraban gidan ita da kanta budemai mota ta turashi,saboda taga bai da niyyar Tafiya sai kwakwumarta yake jakar kayansa ta sakamai akujera mai zaman banza kafin Tarufe mai kofar mota taja gefe tana dagamai hannu,Jagale yayi yana kallonta kafin ya bude murfin motan ya Fito,kawai sai ji tayi ya Rumgumeta kam kam,yana Sumbatar wuyanta,itama matseshi tayi tana kokarin maida kwallarta Sai da suka dau tsawon lokaci kafin ya saketa yana Riko hannunta yace”Ki saka ashafa miki wannan jan Abun na mata,zai yi kyau da hannunki..”Bata kalleshi ba tace”Toh..”Yana kallon Fuskarta yace”Kinji..Don Allah kiyi ko don ni kinji Amanata..”Muryanta cikin sanyi tace”Zanyi insha Allahu..”Mirmishi ya saki kafin ya duka ya Sumbaci bakinta,yana dagamata hannu ya fada mota,ya daura Set belt ya tada motan yana kallonta tana dagamai hannu,shima dagamata yayi kafin yayi Riverse da motar yazuba hon megadi yataso da sauri ya wangalemai get ya sulala waje Malika ta dagamai hannu,sai da ya karisa Ficewa megadi ya maida get ya Rufe kana ta juya zuwa cikin gidan tana Share kwallar data zubo mata.

Tana shigowa sai ta Wuce dakinta tashige tiolet taci kukanta kafin ta wanko Fuskarta ta Fito,cikin kichen din tabi su Maman Abba,wadanda ke ta aikin soye soyen miya da naman kaji bakin da zasu yan kawo amarya Tunda su ba taro zasuyi ba,Abunda yayima malika dadi da Hajiya binta ta mata waya tace Goggon  daga  malumfashi,  da Wata zaliha wacce take ya ga Daddy zasu zo mata gobe,Ho zo kuga murna har bakinta yaki Rufuwa ko bakomai ashe dangi ma suna da ranarsu,gashi zasu suyi mata rana lalle duk wanda baisan darajan dan adam ba,yana tare da Nadama duniya da lahira.

Nan take tambayan joda wani abu ne ake sanya ma Hannu yayi ja,Mallam yace tasaka,Maman Abba da joda suka sanya dariya harda tafawa,Joda ne tace”La Anty Malika Kunshi fa yake nufi..”Maman Abba ta karbe da cewa”sha kuruminki dama nayi ma wata Mami mai lalli na kusa damu mgaba tana kitso tana kunshi,so gobe zan kawota tazo ta Chanchare min ke,yadda Acp zai ka rikice yakasa gane Amarya da uwargida..”Dukkansu suka sanya dariya suna cigaba da aikinsu suna hira ita kuma malika na zaune tana tayasu da hira,gefe daya kuma tana sakin mirmishi ita kadai.

  *****************

Koda Saleem ya isa Abuja ya tarar da gida cike da Yan”uwansu wadanda suka zo daga kumo,maza da mata,wadanda zasu tafi daurin aure gobe,Koda yaje Sadiq ya gaji da jiransa har yayi Fushi ko takanshi baibi ba,saboda haushin dayake bashi na yadda yake wani rawan kafa,akan aure,Abun takaichi ma sai mutum yaga yadda Su Nadira suka maidashi kamar wani kakansu komai suke so shi suke kira suna rawan kafa gayamusu shi kuma yana rawan baki sanar dashi,harda mai masifan kin zuwa da Wuri su wuce kano ayau su samu Dinner dasu Zahra suka Shirya,wani dogon tsaki yajama Sadiq bai kara tankanshi ba,ya Cigaba da laluban nombar wayar Malika yana so ya sanar da ita Ya iso lafiya.

  Abokan wasansu kuwa sai tsiya suke mai,suna fadin yayi rawan kafa,da Son mata ko kuma suce mai jaraba ne,Akanannan Shekararunsa har yatara mata biyu,Dariya kawai yake musu yana Fadin”Kunga alamun cewa Saleem lafiyayye ne,don da bani da karfin mazantaka da ba’a kara bani wata matar..”Rufe baki sukayi suna sunne kai sunji mganar dayafi karfinsu,Dariyan mugunta yakeyi cikin ranshi,dama da gangan yayi saboda ya kashe bakinsu.

   Ya marwan kuwa da bai samu zuwa ba,ya taimaki kanshi don haka suka tasa mai tsiyan yaki aure har kaninshi yana Shirin yin na biyu raggo kawai har suna Fadin in bai lahiya ne ya sanar su neman mai mgani,dariya takama Sadiq yayi ta darawa har sai da yakira Marwan din yabashi lbrin,dariya yayi kafin yace”Kamar yasan za’a rina,shiyasa ya noke wannan karon,ammh shima insha Allah da zarar yahadu da wacce yakeso zai yunkuro..”

   ******************

Washegari da karfe 11:30 na Safe aka daura Auren *SALEEM KABIR KUMO*

Da Amaryanshi *ZAHRA BUKAR MADA* akan sadaki mafi daraja Dubu Dari da hamsin,wanda aka daura akofar gidan Alkalin Alkalai bukar mada,daurin auren daya samu hallarta kusoshin gwannati dadama wanda sai dai wasu ka gansu acikin jarida ko gidan talabijin.

Bayan gama Daura auren aka Shiga gaggaisawa,musamman Abbi wanda yake ta sallaman jama’a wadanda suka zo dominshi,shiko angon Amaarya yana gefe,sanye da wata Navy blue din Shadda wacce taji aiki,riga da wando har da babban Riga,sai hulanshi zannah bukar,Shida Sadiq suka sha anko wanda Sadiq din ya Siya shaddan ya kuma dinka musu suka sanya,Sadiq ne keta hada hadar jam’a bakinshi yaki Rufuwa ammh banda Saleem,wanda ya wani hade rau,in kaga yayi dariyan yake toh anzo an bashi hannu ne,ana tayashi murna da Allah sanya alheri.

Su Abbi basu Wuce ba,sai da Bukar mada yatsayar dasu sukayi walima acikin babbann falon gidanshi,wanda sukaci suka sha,suka tashi suna fatan Allah yabada zaman lafiya,Suko su Saleem da sauran abokanshi basu bi tawagar su Abbi su zasu tsaya su taho da amarya..

    

  Tun after 1 Saleem ke masifan Yakamata su Fito su dau hanya,saboda kada suyi dare,don shi yagaji da jira,ammh kuma tawagar amarya suka ki fitowa,Dole tasa Sadiq yajasu da sauran abokan aikinshi zuwa cikin gidansu Zahra suka gaida iyaye da baki,Amarya suna wani bangaren na gidan,sukaji lbrin Shigowar ango cikin gidan,ai zahra dake zaune ana gyara mata Fuska wacce aka Firgita Fuskarta da kwalliya kamar wata aljanna,tana sanye da wani leshi dinki riga da sikat,wanda ya Fito da Suran jikinta,saboda yadda kayan suka kamata,bata ma jira sauran kawaye ba,ta fito Mayafi ahannu,su Nadira ne suka biyo ta da gudu da jakarta suna kokarin gyara mata mayafi.

Lokacin da Saleem yaci karo da Zahra da farko ya tsorata da Fuskarta ganin yadda aka chabamata abubuwa babu kyan gani,kamar wata aljannah,Abunda yafi bashi mamaki babu kunyar Amaren zamani afalon gidansu gaban dubban jama’a ta rikoshi tana mai mgana cike da shagwaba,Sagale yayi mata ammh kuma ya chanza Annurin Fuskarshi kwata kwata ya tsani mace mara aji da kamun kai,shi Tunda kan malika yadaina ma mata kallon goro,toh ji dai malika bai taba zata zai sameta aburduwa ba,ammh sai gashi ta bashi mamaki,Ammh kalli zahra Da yake ganin tatashi cikin hausawa ammh ji Abunda take kamar ba diyar hausa Fulani ba.

Haka ta matsamai suka yi hotuna tana manne dashi,Kawayenta ma duk sunyi hotuna da Sauran abokanshi,Saleema ma tashigo sunyi hoto,ammh fa yanayi yana hararanta,saboda haushinta yakeji,ganin yadda ake Kiranta ko’ina kyace gidan ubanta ne,ko wata kanwar uwarta,Chan suka ja gefe da Sadiq suna gulmansu na fama yana kallonsu aranshi yace”Munafukai kawai…

Suna gama hotuna aka zo aka ja Zahra aka kaita wajen Babanta yayi mata nasiha daganan sai dakin Hajiya saratu momi,itama tayi mata nasiha daidai gwargwardo,acikin nasihan nata taja kunnanta kan ta rage rawan kan nan nata,da shigen Fi’ili da kuma tsiwarta,don wasu mazan basu son Rawan kai,daga karshe ta mata Fadan tabi mijinta,ta kuma zauna da abokiyar zamanta lafiya,kada taji wani baraka ya bullo daga barayinta,Zahra na dunkunkune cikin mayafi kamar ta Allah nan ko Allah Allah take  asadata cikin mota don Nasihar Momi ba Shiganta yake ba,Cikin ranta fadi take”Kishiyar ne zan bi ? Hala ita ta auroni tabdijam ai kowa tashi ta Fisshine..”Take fada babu ko alamun Nasihan ya Shigeta.

Haka aka Fito da zahra,ko hawaye babu a idonta,koda na gulmar da amaren zamani keyi ita batayi ba,idonta kir,sai da Nadira ta maketa ta ja mayafinta ta Rufe mata Fuska tana mata mgana cikin kunne kana ta daina Fito da kanta waje😂,Motoci hudu ne suka tafi Abuja,Domin bukar mada yace bayason bidi’an nan duk maison zuwa daga baya yaje ganin daki,duk da dama ango yace amayar kadai yake bukata basai an kawomai wani kaya ba,toh dayake Duniya tana cike da yan boko da masu dashi,shiyasa suma iyayenta basu damu ba.

Motar Sadiq aka sanya amarya Saleem Tun da yaga ana bata lokaci yabi motar wani abokinshi Dcp Sulaiman gidado(Na kishin mata),kusan dama abokai ne😂 ,kuma halinsu yazo daya suna da Shigen jinkai da rainin wayau,suka kamo hanyar Abuja su biyu suna tafe hiransu ta abokai suna Shekewa da dariya,shi gidado shi kebama Saleem wasu dabarun zama da mata biyu,saboda shi yariga yin gaba,Hafsa da Jameela suna fafatawa dashi,duk ya da tara daya gida har yana ba Saleem shawaran duk wacce ta kawo wargi ya bata takarda ya sanda ta gida😂

  Dangin mamanta biyu sai na babanta daya,sai kawayenta biyu sai Nadira da Saleema sai zahra su kenan,Suka kamo hanyar Abuja,Zahra tana ji kamar ta bude ido taga sun isa,don ma Nadira ta kwabeta da farko tafara gaddama bazata Shiga motar kowa ba,sai ta angonta wanda tuni yakara gaba,kujimin Amaryar zamani gaakiya Zahra zamanki cikin gidan Saleem akwai shan kallo…”!.

****************

 Sai bayan mangariba suka iso gidansu Saleem,nan fa kallo yakoma sama domin ganin tsaruwa na gidansu Saleem,zahra tana cikin mayafi ammh tana kokarin Fito da kai,sai da Nadira ta damketa dakyau tana mata Fada,Ummi da kanta ita da kawayenta suka Fito suka tarbi amarya da yan’uwanta cike da Farinciki da murna,suka dumguma zuwa cikin gidan inda akayi musu masauki adakin na mussaman da’a gyara domin su.

  Nan da nan Aka fara jera musu abincin da ababan Sha da’aka tanadar domin su,wasun su ne suka fara gudanar da sallar kafin sufara cin abinci,ammh irinsu Saleema da Nadira sai da sukaci suyi nat,Abunda zai baka mamaki sai ganin  Zahra ta cire dankwali ta Cire sikat tana zaune daga ita sai rigan Leshin jikinta da Underwears,ta Iyayen ciki suka mata mgana sai tace,zafi takeji bazata iya zama da Sikat din ba,Ai nan gidan iyayen mijinta ne,So kamar gidan Mijinta ne,Rike baki kadai sukayi suna mamakinta,basu gama mamaki ba sai gashi ta Fito da wani hadin gumbar mata tanaji,Duk kyafta mata idon Nadira keyi saboda Saleema awajen bata gane ba,Da wata kanwar Babanta ta mata mgana sai takara narke Fuska tace’Yo ni goggo Shatu,in bantashi tsaye na taimaki kaina ba,kawai sai na zauna tunda dai kun kasa,ai ni sai nayi Tunda gidan kishiya zan Shiga abun sai da tanadi..”

  

Tafada hankalinta kwance,daganan ba wacce ta sake mata mgana,Kowacce ta kama kanta,tunda sunsanta bata da kunya ko kadan,Itako zahra harda tafawa da Saleema tana kara zugata,Nadira dai Shuru tayi tana tsoron kada Zahra ta tafka kuskure,koda wani abu ya bullo Saleema yar”uwanshi ce, bazai taba rabuwa da ita,itafa Yana da ikon da zai yarda kwallan mangwaro ya Huta da guda…”

  “”””Har Dare Zahra bataga Angonta ya leko ba,sai tafara damuwa,Saleema ce tace mata tayi hakuri zasu Shigo Shida da Sadiq kila idon mutane, ne yahansu shigowa tun dazu,Da farko tabar damuwa ammh data ga har pass 9 ai sai ta dau wayarta ta laluboshi sai taji ya sakata a call waiting.,lokacin yana waya da Malika ne,yana gani ya Shareta saboda yasan ko ya katse kiran, ba wata mgana bace mai muhimmanci ba,Shirme ne kawai da Shiririta.

Zahra ko kamar ta Fashe saboda takaichi da bakinciki gefe guda,kuma wani Tarnakakin kishi ke dawainiya da ita gashi taki hakura da kira sai kira take yana sata a call waiting,ranta ko ya kara baci kamar ta Fashe ita kadai,kuma bai kirata ba,sai da yagama waya Da malika kana ya kirata,lokacin har kwalla sun Fara taruwa a idanuwanta.

Tana Dauka Sai ta Fashemai da kuka,Shuru yayi yana Sauraranta cike da mamaki yace”Topha…Lafiyanki kuwa..? Tana Shesshekan kuka tace”Shine..Shine ina ta kiranka kaki dauka kana chan kana waya da wata ko..? Mele baki yayi kafin yace”Da wata kuma..? Ni bada wata nake mgana ba da yayarki ne,kuma bisa adalci duk wunin yau ban kirata ba,Kinga ko takirani ai na dauka na bata hakuri ko..? 

Wani bacin rai ya Shiga zahra sai ta danne kafin tace”Ok..Shine najika Shuru baka Shigo waje na ba..”,Mamakin kalamanta yayi kafin yace”Haba don Allah Zahra mena ke ci na baka na zuba,akwai saboda rashin kunya sai na Wuce gaban Ummi da Abbi zuwa inda kike,tsayama su bakin dake dakin in na Shigo ina zasu..? Yafada cike da Dattako,Tura baki tayi kai tsaye tace”Toh su Fita mana..”Baki yakama kafin yace”Toh badani za’ayi haka ba,duk Abunda kikema Rawan kafa in inkinyi hakuri zaki sameshi zuwa gobe,sai kin barmin Abun Fada ba..”

Ko ajikinta sai ma kara narkemai datayi tana Fadin”Toh Tunda  kasan Abunda nakema rawan kafa mai zai hana ka min kwatantancen dakin sai nazo kabani ka Huta da Rawan kafan..”,Tafada tana wani shafa Bakinta,Zaro ido yayi bai mata mgana ba kawai ya yanke kiran gabadaya yana kiran Sunan Allah,har Sadiq dake gefenshi yana waya da Saleema ya dago yana kallonsa,bai mai mgana ba,ganin ya dauki wayarsa ya Shige Tiolet,shiko wayar ya dauka saboda kada zahra takara kira,sai ya sanya Nombarta cikin blacklist ya dauro alwala ya Fito..

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Jin ya kashe wayarsa,bai sa tagane tabargazan datayi ba,saima kara kokarin kiranshi datake,ammh ta gaza samunshi,tayi tayi taki Shiga kwata kwata,cikin damuwa ta Fito Falo ta Samu Saleema kan kujera tana waya ta daga mata duka tana Fadin”Ke kanwar Miji tashi ki rakani dakin yayanki yanzu..”Ba Saleema kadai hatta Nadira dake gefe tana charting sai da ta dago tana kallon Zahra cikin wani yanayi mai kama da kinyi hauka..

Saleema tayi Saurin yanke kiran tana kallon Zahra tace”Dakin yaya Saleem,lafiya kuwa..? Yamutsa Fuska tayi kafin tace”Kawai ina son ganinshi ne,ko laifi ne don nace kirakani dakinsa,ai naga dai an daura aure yazama mijina..”Tafada tana kallon Nadira,wacce ke kallonta cike da takaichi.

Saleema tayi dariya tana kallon Zahra kafin tace”A”a ko daya,sai dai ni bazan iya wucewa dake zuwa dakin yaya Saleem ba,Su Ummi fa na falo,kuma bama haka ba wlh Yaya Saleem zai iya marina in na rakaki gwara kiyi hakuri ki kirashi ta waya..”Tafada tana sakin hamma,Jagale Zahra tayi kafin tace”Ina ta kiransa ban samesa ba…Tafada kamar zatayi kuka.

Batama bama Saleema damar mgana ba,ta mike tana Fadin”Tunda bazaki rakani ba,ni bari naje da kaina,nasan bazan bata ba..”Tafada ta na kama hanyar Fita daga dakin,Nadira ta mike data ga rashin hankalin na Zahra ba karami bane,itako Saleema Abun ne ya bata mamaki,domin bata zata Zahran takai haka Wauta ba,Nadira ta sha gabanta tana Fadin”Wlh in kika Fita daga dakin nan,sai na kira Momi na sanar da ita,haba kidinga Abu kamar Wata mara Tunani da ilimi,in kin fasa Fita kin zama shegiya…”Tafada cike da masifa.,tana gama Fadin haka ta juya ta koma ta zauna tana sakin huci,

Jin Abunda Nadira tace ne,yasa Zahra takasa Fita,sai ta joyu afusace tajuya koma ciki tana kunkuni,Sauran iyayenta kuwa kanzil ba wanda tace musu,sun so ne sai ta Fita wlh gari na wayewa su tatarra su koma Kano suce amarya ta Hutar dasu takai kanta daki,Saleema tabi zahra da kallo tana wani Tunani aranta na indai zahra ahaka take Tunanin Sace zuciyar Saleem,to da sake domin Yaya Saleem ba irin sauran sakarkarun mazan data sani bane,Mutum ne mai aji da takama,da Wuya su Shirya matukar bata gyara takunta ba,ganin haka yasa ta mike tabi bayanta,koda taje ta isketa ta kumbura kamar ta Fashe,saboda Fushi ita ta zauna tana ta bata hakuri tana kara nuna mata sai fa ta rage wani abu saboda tsaro,ammh suk zahra bataji tana ganin Abunda takeyi Shine Daidai.

  

******************

Washegari Tun bayan Angabatar musu da Abun kari suka karya sukayi wanka kowa ya Shirya saboda su isa da Wuri don bazasu kwana a zamfara ba dagachan zasu juya kano ne,Itako zahra an cakare cikin wata Shadda Ash colour dinkin Riga da Sikat,kayan Sun fita da ita ba laifi,Ummi ce ta Shigo gaida amarya da baki,Allah ya kyauta lokacin tana Sanye da mayafi da anyi Abun kunya,ammh fa ita kanta Ummi tayi mamaki ganin amarya tana gaisheta zaune kan kujera ta mike kafa idonta kyar akanta babu alamun kunyar nan ta Surukai,Abun ya daure mata kai sai dai batayi mgana ba ta Share,ammh aranta tana Fadin”Wannan wata amaryace Saleem ya kwaso kuma..? 

Magana tayi akan Zata tafi da zahra chan wajen Abbi zai hadasu ita da Saleem yayi musu Nasiha ko gama Rufe baki Ummi batayi ba Zahra ta mike zumbur tana gyara mayafi tace”Yauwa Ummi muje..”Tafada tana yin gaba,ba Ummi kadai ba duk mutanen dakin sai da sukaji kunya,Tun ballatana Nadira taji kamar ta dora hannu aka ta yanka ihu,Saleema ko Wani iri taji don bataso ace wacce take goyon baya tana irin wannan Ba,duk zata bata musu Shirinsu Malikar ma ta Fita samun Fada wajensu Ummi.

Ummi ko Yaken Dole tayi tabi bayan Zahra tana kallonta cike da mamakinta,gefe daya kuma tana Tur da wayewa irinta yan matan zamani,don yanzu sai ace wannan ba komai bane wayewar zamani ce,ganin Sun Fita kuma batasan hanyar ba,shiyasa tabama Ummi dama ta Shiga gaba suka hau sama har Falon Abbi inda yake zaune bisa kujera Saleem wanda ke sanye da Farar Shadda dinki Muhammed,Aikin jikinta baki ne hakama hulan kanshi baka ce,yana zaune akasa kusa da kafafuwan Abbi kansa akasa alamun biyayyah da ladabi.

   

  Suna Shiga Falon Tunda zahra ta hangi Masoyinta ta fara washe baki,sai kawai tatafi kusa dashi zata zauna,kanshi na kasa ya dago yana hararanta cike da takaichi,ganin haka yasa Abbi fadin”Kyaleshi diyata dawo nan..”Ya fada yana nuna mata dayan gefen,Ranta baiso ba takoma nan ta zauna tana kallon Saleem cikin so da kauna kamar ta jawoshi ta Rumgume haka takeji,balle yadda yayi mata kyau yau sosai..

   Ummi dake tsaye gefe ta rike haba tana Fadin Cikin ranta”Allah mai zamani…”Zahra saboda shagala da kallon Saleem bata iya gaida Abbi ba,sai Shine yake gaisheta yana tambayanta ya kwanan bakunta,sai lokacin ta danji kunya ta sunkuyar dakai tana ansawa,ammh kuma ta gefen ido tana kallon Saleem,shiko kunyar Duniyace ta isheshi gaban Ummi da Abbi,kan Abunda zahra tayi gabadaya sai yaji auren ma ya Fitarmai aka yarinya kamar mai tabuwar junnu.

  Nasiha sosai Abbi yayi musu,Yayima Saleem nasihan adalci a tsakanin matansa,Tunda Nauyi ya hau kanshi sai ya dage,banda nuna bambamci kowani wariya ga daya daga cikinsu duka matanshi ne,daga karshe  yajamasa kunnen sai ya jajirce dole yazama na Namiji don zama da mata biyu babu sauki,don ko Shi da yake ubanshi daya gareshi,Yayima zahra Fadan tabi mijinta tamai biyayyah Shine Ribanta da Tsiranta aduniyama Har zuwa ranar Gobe kiyama.

Kuma yayi mata nasihan ta zauna da abokiyar zamanta Lafiya ta kuma bata girmanta,wanda ko Ummi ma da Abbi yabata damar mgana Abunda tayi ta jadaddamata kenan,Sakale tayi kawai tana jinsu ammh azahirin batu hankalinta baya tare dasu yana chan tana Tunanin yarda zata ci uban Malika ne hankali kwance,Duk Nasihan da suke mata bata jiba,Domin tace duk suyi su gama miji dai natane ita take da ikon Sarrafashi yadda taga dama basai wasu sun tsara mata ba.

  Bayan su Abbi su sallamesu Saleem ya Dukar dakai yana godiya kafin su tashi su Fita,suna Fita zahra tayi zaraf ta riko hannunshi tana sakin mai mirmishi cike da salon makirci,Fizge hannunshi yayi yana kallonta kai tsaye yace”Zahra..Wai mike kanki ne? nan fa gidan iyayena,haba kidinga Abu kamar wata kilakin karuwa,dubi abunda kikayi dazu agaban su Abbi,yanzu Fisabillahi haka h amare masu kunya keyi tsakani fa ga Allah..”Ya fada cikin bacinrai.

Tura baki tayi kafin tace”To menayi kuma? ai ba Rashin kunya bane,suma su ummi murna zasuyi Ina son dansu sosai..”Kuramata ido yayi kafin yajamata wani dogon tsaki ya Kama hanya yana saukowa daga Steps da hanzari ta biyoshi har suka sauko hanyar dakinshi ya nufa,tako biyoshi jin tana biye dashi ne yasa ya waigo yana kallonta ganin ya tsaya ne,yasa itama ta tsaya tana kallonshi,Fuskarshi ba fara”a yace”Lafiya ina zaki naga kina bina ne…? 

Rausayar dakai tayi kafin tace”Ina kuwa..? inda zaka mana..”Turbene Fuska yayi kafin ya nuna mata hannu yana Fadin”Kinga malama Wuce ki koma daki yanzu zamu tafi gidanmu sai kije chan kiyi ta rashin kunyarki,ammh wlh bazan bari ki barmin Abun Fada gaban dangi da iyaye na ba,karki sake ki Biyoni wlh..”Yafada yana Jadadda bayaninsa,Kafin ya juya ya Shige dakinsa ya banko kofa yana Ma kanshi jajen ya auro ma kansa jaraba da kudinsa.

  Ganin ya Shige ya barta yasa taja kafafunta takoma cikin dakin tana wani bata rai,ba wanda ya kalleta sai Saleema,wacce ke mata kirari cike da Iya Shege,nan da nan ta Shiga washe baki kamar wata sakarya,Yadda suka zo haka suka dauki hanyar Zamfara,ammh wannan karon babu  Saleema,wacce har ta Shiga mota Saleem yamata jan ido yace ta Fito,Tana tura baki ta Fita yayi mata kaca kaca,lokacin da Tajema Ummi tana kukan yahanata zuwa gidanshi,Shiko yace sai dai ta mutu Tunda ba uwar wani Zatamai ba intaje,dole ta hakura tanaji tana gani suka Fice daga haraban gidansu.

Sadiq shi ya sake daukan amarya sai motar gidansu Abbi da direba guda daya,Sai motar haya guda daya,wacce Saleem yayi tashanta,daganan Zamfara Kano zata Wuce dasu,Sun riga Saleem yin gaba,don shi kadai yataho amorarshi ammh bayan ya kira Malika ya sanar da ita suna bisa hanya,Ummi ko bata barsu haka ba,ta basu Turamen zani guda goma,da Turaren Wuta,dana daki,sai kudi ta ba masu kawo amayar aka rabu cikin girma da arziki.

  ******************

Lokacin da Saleem ya kira Malika Tuni har an gama mata kunshinta ja da baki da kitsonta 2Steps😂,wanda yayi mata kyau over sai wanda yagani kunsan Farin fata yana karban Jan abu da baki atare,sai kitsonta wanda ya kasance yiri yiri ne,dama akwai gashi sai ta fito ras da ita,Abu daya yayimata cika katon Tulalen cikinta,wanda tayi wanka ta Shirya cikin leshinta riga da zani ta kashe daure bakace Malika malik din nan bace mai sanya kananun kaya masu Fitar da tsiraici.

Tun jiya su goggo hadiza suka iso ita Zulai tare da suka taru dasu Maman Abba suka sha bikinsu ajiya,suna kuma kokarin Debemata kewa sosai,wanda yayi nasaran ragemata damuwa,da kuma kishi,duk da taji abun,mussaman da lokacin daura aure ya kusanto har yazo ya Wuce,taji Abun aranta,ammh basu barta Tashiga halin damuwa ba,Hatta Hajiya binta dake gida tana takaba sai da ta kira Malika tana kara tausanta,Mirmushi kawai malika take aranta tana Fadin”To in batayi hakuri ba, ina zata da wannan cikin,ko tabar  gidan Saleem bamai kwasanta ya zauna da ita don Allah,saboda haka hakuri yazama dole gareta.

  Yana sanar da ita tasowarsu ta sanar dasu Joda,suka fara shiryen Shiryen taransu,duk da dama chan ashirye suke,gidan suka kara gyarashi sosai kafin su shiga kichen su dukufa wajen shiryama yan kawo amarya delious mai dadi cikin mutumci da kima.

Basu iso ba sai wajen 2 na rana suka iso,wanda Malika najin Sautin hon dinsu da kuma karar bude get,gabanta ya amsa ta tashi da Sauri Ta shige daki tana kokarin danne Abunda ya tasomata,Su joda da Maman Abba ne da Su zulai suka Fita suka tarbesu,Zahra dake cikin mayafi hankalinta na kan karema gidan da kallo,Haka take bin ko’ina da kallo har suka Shiga falon gidan suka zazzauna ana gaisawa ana tambayan gajiyan hanya,Joda ce kan gaba ta nuna musu dakin Zahra wanda ke kusa dana Malikan suka tashi suka Shiga da Zahra ciki,wacce dama ta kagu akaita dakinta taga wani iri ne.

Dakinta yana da girma,Shimfide da wani cafet mai taushi,wanda ya mamaye dakin gabadaya sai makeken rolay bed dinta da kuma Wardrope mai girma da Fadi,sai dressing mirror,sai kofar Tiolet,zahra a wulakance take bin dakin da kallo,Bawai dakin bai mata bane a”a so take taga na ita malikan ya yake? don ita zatonta Saleem ya raina mata wayau Ne Shiyasata ya sanya  awannan dakin wanda da kadan yafi na gidansu inda take kwana.

Joda da Maman Abba da Zulai su suka dinga kwaso musu kololin abinci zuwa cikin dakin Zahra inda suka ga Abun mamaki amarya ta zaune kan tsakiyar gado ta cire dankwali shigen gashinta mai kama da Hammatan dan iska awaje,duk ya mike Kallo kowa daya daya take tana wani girgiza kafa,Maman Abba da joda suka kalli juna suna mamakin wannan al’amarin daga zuwa har za”a nuna hali,sai da suka Fita zahra ta kalli Nadira take cemata”Wai  yan biki kenan,? hala bata da wasu dangi ne ita Malikar,koda yake sai dai in taron arna..,”

Tafada tana yar karamar  dariya,Tsaki Nadira taja tana Fadin”kedai kike kidanki da rawanki,in banda Shiga Abunda bai shafi mutum ba,ina Ruwanki da danginta,kedai tafi wajen Shigen rawan kanki da Shisshiginki miji ya ram miiki,kinga ko kya ga karshen Rawan kai..”Goggo Shatu tace”Kwarai da ma gaske,ai tama baras,Nadira tunda ta yada hali gaban Uwar miji,mai ya rage kuma,ai babu Shi Nadira,Allah dai kawai ya sauwake…”

Zahra ta tura baki ta kauda kai tana dauko wayarta tacigaba da Laluban Nombar, Saleem ammh har yanzu bata Shiga kuma,sadiq yace batare suka taho ba shi yana baya gajiya tayi da kira ta hakura takoma gefe tana kallonsu Nadira na cin abinci,Farar Shinkafa,da miyan nama,sai Fride rice,sai kunun aya mai sanyi,da ferfesun Naman kaji,kallonsu take don ita babu abinci agabanta so take ma suyi su tafi abarta daga ita sai angonta.

   Sadiq kuwa Joda tayi ta dawainiya dashi,bayan tabashi na Direban da zai maida Su Nadira ya kaimai,ya dawo yazauna falo yana cin abinci yana ma Joda hira har yana tambayanta Shi bai santa ba? tace mai ita kanwar Malika ce gidansu daya,Sai alokacin Malika ta Fito tana taku dakyar suka gaisa Da Sadiq yana kara kallonta kamar ba ita, ba kamar wata zara acikin wata,shi baima san cikinta ya tsufa ba haka don Saleem baya yarda yayi mganan Malika dashi,koshi ya jawo hirar Kauceta yake,ya basar.

  Suna cikin gaisawa da Sadiq din sai ga Saleem ya Shigo gidan yana waya,yana sagale da yar jakan kayansa,Sai da ya katse wayar ya kariso garesu yana bama Sadiq hannu suka tafa yana Fadin”Kai mutumina kayi Wuta ahanya fa..”Yar dariya Saleem yayi kafin yace”Ah to mezan jira,ai ban saka lerna ba,balle na dinga na lallaba Titi..”Yafada yana kallon Malika dake tsaye tana gyara zaman mayafin kanta,Kwabemata Fuska yayi kafin yace”Ba sannu da zuwa Yar Amanata..”Batayi mgana ba,illah karisawa datayi gareshi tana saka hannu ta karbi jakan hannunsa tana Fadin”Yanzu fa ka shigo..”Sannu da zuwa..”Kin sakin mata jakan yayi saima Rumgumota dayayi ta gefe yana Shafa fuskarta yace”Bar jakanan kawai kinyi Nauyi dayawa kada na zama mara tsausayi..”

Ya fada yana shafa cikinta lokaci daya yake Fadin”Kai cikin nan yayi kasa sosai,koda yau zai Fito Duniya..? Sadiq ne yace”hhh karma kayi Fatan haka don zaka tashi daga angon amarya ka koma angon karni,wlh baka ba kwanan dakin Amarya sai dai kwanan Asibiti..”Dariya joda ta saka,shiko murmusaa kawai yayi Malika bata hakura ba jakar ta sake karba ya sakarmata yana kallonta Mirmishi tayimai tana Fadin”Kada kahanani samun lada awajen Allah…”Hannunsa ya daga yana Fadin”Wane ni? ai ban isa ba,Allah yabamu ladan dukkanmu..”

Batayi mgana ba. ta Wuce zuwa dakinshi,shi kuma ya tsaya suna gaisawa  da joda da maman Abba data Fito yanzu sai Zulai wanda dama Malika ta sanar dashi zuwansu,har dakin Malika ya shiga suka gaisa da Goggo hadiza yana mata godiya,Yana Fitowa dakinsa na yawuce yabar Sadiq zaune yana mai tsiya,koda ya Shiga dakinsa nasa,ya tarar da har Malika ta hadamai Ruwan wanka,Mamaki ta bashi yadda yaga cikinta ya tsufa dayayi mata  mgana sai tace zai hanata neman lada,sai ya kyaleta bai samu lokacin yaba lalliinta da kitson ta ba,sai da yayi wanka yayi sallah yaci abinci kana,haka yadinga Sumbatar hannu yana Shafa kanta,nan take ya bata 5k yace tabama wacce tamata lalli da kitso,domin zahirin batu yagani kuma ya yaba.

   Sai wajen biyar na yammah yan kano sukayi Shirin tafiya,bayan sun gama jerama Zahra akwatunta sun mata yan nasihu duk da sun san baji zatayi ba,Nadira tayi kwaba tayi kwaban kamar bakinta zai Cire,ammh Zahra sai ta nuna taji,ammh kuma nan ko bata jin zata dauki mganarta,da zasu tafi sukace Zahra ta Fito su mika amanarta ga Malika,ammh sai zahra tace Allah ya kyauta tabi kishiya,sai dai in Malikar ta matsu ta shigo dakinta ayi mganar,ganin haka yasa babu wanda yakara bi ta kanta,da zasu tafi har dakin malika suka shiga don su gaisa lokacin tana dakin Saleem,sai da joda ta Fita taje ta kwankwansa musu ta kirata tazo suka gaisa cikin mutumci,daga karshe sukace ga Zahra nan kanwata take gareta,don Allah tayi hakuri da ita,su zauna lafiya da juna,don su samar ma mijinsu zaman da kwanciyar Hankali,sunji dadin yadda Malika ta karbesu sai sukaji ta burgesu sosai,domin ba haka suka samu lbrinta ba,domin ance bata da dabi”a sam,sai suka ga sabanin Tunaninsa,dazasu tafi haka sukayi ta sakamata Albarka da fatan Allah ya sauwaketa lafiya.

Sai da suka Fita haraban gidan kana Saleem ya Fito sukayi sallama ya basu kudi 3k sukuma Su joda suka Fito da Musu da kaji da meatpie da donout,din da sukayi musu wanda sukayi raping dinsu,suka basu suna ta godiya,Nadira dai mamakin ganin Malika take da ciki,don batajin ko Zahra tasan da cikin nan,don data sani da ta sanar da ita,Abun mamaki sai ga amarya acikin yan rakiya tana Rumgumesu tana daga musu hannu ammh Fuskarta babu alamun Rashin jin dadi ko Kuka ko damuwa,a’a fuskarta cike da Annuri.

Suna tsaye motarsu tatashi suka Fice daga  haraban gidan Zahra na daga musu hannu,sai alokacin taga Malika wacce datake bayan Saleem,sai yanzu ta Fito ta gefenshi gabanta ne ya Fadi ganinta da turtsetsen ciki,wani karin Abun takaichin ma hannayensu sarke dana juna suna mgana kasa,kasa malika ke sakin mirmishi Daga ganin Wata mgana mai dadi yake gayamata.

Duk da ahoto tataba ganin Malika bata zata afili tafi kyau ba,koda ita da datake amarya bazata Nuna ma malika kyau ba,duk da ko cikin jikinta wanda yake hanata kwalliya,Babu karya kyanta ya daki zahra sosai balle ma cikin dake jikinta wanda ko Saleem bata sanar da ita ba.

Itako Malika Tana kallon Zahra ne cikin ilimi da wayewa,daga sama har kasa,tabe baki kawai tayi cikin ranta batace komai ba,Ganin yadda ta kura musu ido ne yasa Malika tayi kokarin Fizge hannunta tana nuna mai Zahra da baki,dagowa yayi yana kallon Zahra wacce ta harde hannu akirji tana kallonsu Fuskarta babu Fara’a ko kadan.

  Da Sauri Malika ta isa ga Zahra tana mata Fara’a tace”Sannu da zuwa amaryarmu…”Tafada tana bata hannu su gaisa,baya zahra tayi da hannunta tana ma malika wani kaskastancen kallo na Wucin gadi kafin ta mele baki tana Fadin”,Yauwa sannu dai buh found of correction Hajiya malika amarya Saleem kabir kumo kidaina saka min jaye..”

Tafada tana wani yamutsa Fuska kamar taga kashi,wani nauyi da kunya suka kama Malika ta sauke hannunta asanyaye tana mirmishin yake kafin ta kada kai kawai ta Wuce cikin tanajin yau fa kenan,? lalle akwai aiki ja agabanta game da amaryan mallam,Shiko Saleem waya ya tsaya yanayi wanda Sadiq ne ya kirashi yana sanar dashi har ya kusa isa garin Abuja motarshi ta samu mtsala,ammh zaiyi ma bakanikensa waya,shiko yanzu zai bi motar haya zuwa Abuja,so duk Abunda yafaru baida masaniya,yana kokarin yanke kiran ne yaga Malika ta wuce cikin gida,itakuma ta zahra ta matso inda yake tana mai wani kallo kamar ta lasheshi danye bai gasu ba 

  Tana karisowa kusa dashi ya yanke wayar yana binta da kallo,riko  gefen hannunshi takama Tana Fadin”,Haba Honey Shikenan kuma tun jiya bankara ganinka ba…”Tafada tana saka kanta bisa kafadanshi,ganin megadi awajen karya dizgata yasa yadan riketa suna tafiya zuwa cikin gida yace”Ai yanzu ina tsammanin korafi ya kare ko? Tunda gaki gani,naga Yar Amanata taje kun gaisa,hop kin gaisheta da kyau Antynki kenan Malika Abdulmalik dankasuwa matata ta farko kuma uwar ya’yana..’

mganar ta zafeta Shiyasa ta tabe baki batace komai,shima ganin haka sai yaja bakinshi yayi Shuru,suna shiga falon suka iske Joda da Maman Abba,sunsaka hijabai zasu Fita da alama zataje gidan Maman Abba gabadayansu ganin Zahra rike da angonta Abun yabasu matukar mamaki sudai a al’adan bahaushe amarya tana kunshe adaki tana fargaban zuwan angonta,wasu ma saboda kunya ko siyan bakin akayi basu iya budeshi suyi mgana,ammh yau agidan Saleem suke ganin wani sabon salo,ai Tusa da lasifika😂

 

Irin kallon da suke binsu dashi ne,yasa Saleem dan jin kunya yana kokarin raba rikon da Zahra tamai ammh taki sakinshi saima kara kwantar da kanta take bisa kafadanta,Girgiza kai kawai yayi yana basarwa nan sukayi sallama da Maman Abba,wai ashe Zulai da joda ta dauke zasuje gidanta su tayata kwana Abba da babanshi suna zaria wajen maman mijinta,Goggo Hadiza kadai aka bari,wacce duk kunya saleem ya takuramata tana cikin dakin Malika bata ko Fitowa falo,takuma gayama malika gobe da Safe zasu koma malumfashi insha Allah.

Har su joda suka Fice bata sakeshi ba bai sake mata mgana ba,illah hanyar  dakinta daya nufa,sai da yabari sun Shiga kana ya Saketa yana kallonta kafin yace'”Wai miye haka…? Sakarni alwala zanje nayi na samu jam’i kema ki gagggauta yin naki sallar..”Tura baki tayi tace”Toh ina zaka? baga tiolet anan ba,ka shiga muyi alwalan tare..”Tafada tana kokarin kwantomai bisa kirji,ganin haka yasa yayi Saurin Fadawa tiolet ta biyo bayanshi sukayi alwala yana Fitowa yayi hanyar Fita tayi zaraf zata biyoshi ya waigo cikin haushi yana Fadin”Ina kuma zaki bini..Ehe..? 

  Diddira kafa tahauyi kafin tace”Inda zaka mana,don naga baka da niyyar sauken alqawarin dakama iyayena wajen kula dani da rike amanata…”,Tafada harda matso kwallar Karya,kansa ya dafe kafin ya karisa gareta ya riko hannunta yana Fadin”Injiwa… ? wayaga miki bazan kula dake,kinga ana kiran sallar mangariba,sauri nake naje na samu sallar cikin jam’i ko baki son ace mijinki yana kokarin yin sallar cikin jam’i..”Kallonsa tayi kafin tace”Ina so mana..”Da hanzari yace”Toh kibarni naje nayi na dawo,saurin mekike,yau ba tare zamu kwana ba..”,Da hanzari ta gyadamai tana Mai wani kallo,Sakin hannunta yayi yana gyara hulan dake kanshi yake Fadin”To kingani,oya Kema kiyi sallah asakemin wata sabuwar kwalliyan wannan ban Amince inci amarci da ita ba.,Sai na dawo..”Ya fada yana karisa Ficewa daga dakin,Sufa tayi ta haye kan gado tana Rumgume Filo cike da murna,cikin rawan jiki tatashi tayi sallar ta Tube kaya ta Fada tiolet tayo wanka akazo aka shafama lotion kafin abi kowani lungu da sako na jikinta da Turare,Wai saboda rashin hankalin zahra wai Tunda Saleem yace ta sake kwalliya to kwalliyan kayan barci yake Nufi batayi sanya ba ta bude akwatunta na inners ta zabo wata arniyar riga wacce tsawonta bazai gaza cinyarta ba,gata da budadden gaba,gata kuma raga raga,pant kawai ta sanya babu bara,sai ko gabadaya halittan kirjinta suka bayyana waje,tana kallon kanta amadubi tana jujjuyawa take fadin”Haba dole ya raina kansa in yaga wannan kayan,yasan nawa ba irin nata bane…”

  *****************

 Shiko Saleem bai dawo gida ba,sai da yayi sallar issha’i kana ya dawo,kuma koda ya dawo bai Shiga dakin kowa ba sai yawuce dakinsa yayi wanka ya sanya jallabiyansa Mai Ruwan toka kafin ya dauki wayarsa ya kira Malika yace tazo dakinsa ta sameshi yanzu,bayan ita sai ya kira Zahra yace itama tazo dakinshi ta sameshi yanzu,Jin kiran dayake mata sai bata kawo cewa harda Malika ya kira ba,ita atunaninta kila chan ne zasu first nigt dinsu😂ai bata tsaya sauyawa kaya ba sai ta kara gyara fuskarta gyalen kawai ta yafama kanta,bata kuma Fito ba,sai da ta kada wani garin mgani tasha da madara kana tafito tana rarraba ido,ganin dakin daya ke hari dazu sai ta sa aranta nan ne dakin saleem din.

 Da confident dinta ta Shiga,Cikin Siririyar Sallamarta,Turus tayi ganin Malika zaune akasa ta mike kafafunta,Shikuma Saleem yana rawan jikin jeramata Filulluka,bayan yagama yakoma mtsamata kafa,yana mata mgana kasa kasa,cikin ran zahra tace durun uwa Salatin Arna😂😹ita za”a torzata,tsaye kawai tayi hannunta bisa kugunta tana jifansu Da wani mugun kallo,Malika ce ta ankare da ita sai ta tabo Saleem ta nunamai Zahra,ganinta ahaka kafafu duk awaje yasa ya zaro ido😳😳Lokaci daya yana Fadin”,Zahra lafiyanki kalau kuwa..? Kinga yadda kika Fito marabanki da tsirara kadan ne..”

 ,_*Hhhhhh…Kuna bani dariya masu cewa kila Zahra ba budurwa bane,? waya sanar daku haka,? ai bance Zahra na bin maza ba,Nadai ce Tana da rawan kai da Iyayi da Feleki,Sai kuma rashin wayau dake damunta,in kun lura akwai irinsu Zahra sangartattu marasa wayau da badon ta samu jajircewan Uwa da uba ba,ga kuma Nadira dake kwabamata ba,da yanzu tafi haka Wauta itafa duk Abunda take yi gani take Shine zai sa Saleem yasota fiye da malika ya haukace mata,ita bata Tunanin tana kashe kanta ne,irin sune inda a kauye aka Haifesu da yanzu sun Fara Shiga Daji*_😂😘²⁴

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]