MALIKA MALIK CHAPTER 11 BY JANAFTY

Advertisements

_____

MALIKA MALIK CHAPTER 11 BY JANAFTY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Advertisements

_____

   Karfe 10 da wani abu suka isa anguwan su Malika,wanda Tundaga farkon layin har karshe jerin gwanon motoci ne na gani na Fada,anguwan tacika makil,Malika ko Tunda suka baro Zamfara take kuka har zuka iso katsina,Tun Saleem na bata baki har ya gaji ya kyaLeta.

Bai samu damar Shiga da motar ciikin haraban gidan ba,sakamakon yadda aka wangale get din Mutane sunyi Dafifi kowa nata daura alwala saboda lokacin Jana’iza ya kusa,Malika dataji kanta na sarawa ta dago kanta tana bin ko”ina da kallo,Zuruf tayi zata bude Murfin motan sai taji hannun Saleem bisa nata ya damke,waigowa tayi tana kallonshi wasu hawaye suna zubomata Kara damke hannunta yayi yana kallonta kai tsaye kafin yace.

“Kiyi min wata alfarma plz..? Girgiza kai tayi tana Kokarin kwace hannunta,shiko yaki sakinta ganin haka yasa ya Bude baki yana Fadin”kada ki yi kuka sosai,kinga fa Tundaga Zamfara kike kuka,har muka iso nan,don Allah in kika Shiga ciki ki tararro juriyanki kada kiyima Daddy kuka,ayanzu haka yafi bukatar addu’anki Fiye da na kowama..”Runtse ido tayi hawaye suna kwaranyomata kai ta gyada mai alamun taji,mirmishin yake ya saki kafin ya Kai hannun nata bakinshi ya sakarma wani light kiss,kafin ya saketa ta bude murfin motan da hanzari Ta fice tana Rufe Fuskarta da Gefen hijabinta kuka na kwace mata.

Shi kuma ya Fito daga motan  ya nufi haraban gidan inda su Abbi ke tsaye shida sauran yan”uwan Daddy na Malumfashi,gaisawa sukayi yana kara musu gaisuwa,kafin shima ya koma gefe yasamu buta yafara daura alwala domin har an kammallah yima Daddy Sutura ana jiran lokaci ne ya cika a sallaceshi zuwa gidansa na gaskiya,kowa ka kallah awajen Fuska babu Annuri kowa yayi tagumi yana alhinin wannan Rasuwa ta Alhaji Abdulmalik Dankasuwa….

Itako Malika na Shiga Falon gidan ta tsaya cak tana bin kowa da kallo,gabadaya dangin Daddyn natane yan malumfashi suka cika Falon suna koke kokensu,wanda ada sune in ta gansu sun zo gidansu tayi ta fadan cewa sun zo maula sun cika musu gida,sai gashi yau sune suka zo su taru suyi kukan rashin da kuma Faduwar bango garesu gabadaya.

Nan idanuwanta suka kai kan Hajiya binta dake zaune gefe da dogon Hijabi ta carbi tana ja,Fuskarta ta kumbura saboda kuka,gefenta kuma Joda ce itama sanye da hijabi tana Sharan kwallah,Shigowar Malika shiya sa Falon ya dau Shuru kowa ya juyo yana kallonta cike da tsausaya domin ansa babu wanda akama mutuwa kamar ita.

Hajiya ta kalleta idanuwanta da suka sukayi jawur cike da kuka tace”Malika..”Takira sunanta cikin raunin da karayan zuciya,ai da gudu malika tatafi gareta ta Fada jikinta tana Fashewa da kuka,Rumgumeta hajiya tayi itama kukan take tana Fadin”Mun rasa Alhaji malika,mun rasashi lokacin da da ni dake muka fi kowa bukatarshi,wayyo Allah mutuwa tamana yankan kauna ta daukemana Alhaji lokacin da muke tsakar bukatarshi..”Take Fada tana kuka,Malika dake jikinta ta kara fashewa da kuka,cikin muryan kuka wacce ta Dishe take Fadin.

 “Dama da gaske mallam yake Daddylove ya tafi ya barni..? Why..? meyasa zai min haka ? zai tafi ya barni cikin wannan Duniya mai cike da kunci ni kadai,ya rayuwata zata kare,wayyo ni Malika dama Allah ya dauki raina,nima na mutu abinne gawata kusa data Daddyna,domin babu Abunda zan tsinta aduniyar indan na zauna ba ni da kowa sai shi,gashi yanzu Babu shiii..”Tafada tana kara kife kanta akasa tana kuka harda jijjiga.

Wata wacce take kanwa ga Daddy tataso daga inda take ta riko Malika itama tana hawayen tace”Ashh malika bar Fadin irin wannan kalaman basu dace ba sam,ki na zaton Allah daya bamu shi bai Fimu sonshi bane? karki Manta gawan Mahaifinki na cikin gidanan kuma sai ki sakamai da mganganun banza da koke koke,yanzu ne fa zamu nuna mai mu masoyanshi ne ta hanyar neman masa gafaran Allah,gashi kema baki da lafiya ko so kike kijama kanki mtsala muna alhinin rashin Mahaifinki mukoma alhinin shiganki wani hali..? Girgizamata kai Malika tayi tana toshe bakinta da hannun kada kukanta ya Fito,Zaunar da ita tayi tana zama kusa da ita carbin hannunta ta mika tana Fadin”,Yita salati acikin ranki,Kibar kukan nan hakannan kada kijama kanki wata mtsalan Abdulmalik tashi ta kare ,sai dai mune muke cikin kila wa kalan Yaushe zamu mutu? yau ne gobe ne? bamu sani ba..”Take Fada tana Share kwallah.

 Gabadayan Falon sai da kalamanta yasasu ta kwallah,itako Malika batayi gaddama ta karbin chasbawan tana karanta innalillahi bakinta na motsi ammh hawaye sun gaza daina gudu bisa kuncinta,haka Hajiya binta ma ana ta bata baki,ana mata Fadan tadaina kuka ita da zata Tallafin Raunin malika,ammh itama ta koma tana biye mata suna kukan da bashi da amfani,dole suka hadiye kukansu ammh fa zukata sun Raunana,gabba sun yi rauni suma.

Tashin hankali bai kara ziyartansu ba sai da akace Hajiya da Malika su fito su zo Falon waje inda aka shirya Daddy,domin sumai addu”a da ganin karshe,lokacin da Malika taci karo da gawan Daddynta kasa control din kanta tayi haka ta fada kanshi ta kamkameshi tana kuka mai taba zuciya kamar zata Shide,hajiya ce kadai ta samu daurewar yimai addu”an Fatan dacewa da kyakyawan mtsayi.

Malika kin sakin Gawan Daddy tayi Fadi take ita, Daddynta bai mutu kada su Fitar dashi,gashi ta rike makaran dakyau taki saki,sai da Abbi ya fita waje ya kira saleem yazo da karfi gaske ya bambareta jikin makaran yana lallashinta,ammh ita hankalinta ya bar jikinta,ganin tana Fizge fizge ne yasa ya Kara tsaurara rikon dayayi mata,har sukayi baya suna neman Faduwa,neman kwatan kanta take ita sai taje ta riko daddynta kada su Fita dashi,ammh Saleem bai barta ba sai da ya tabbatar da sun Fita da gawan waje kana ya Sausauta rikon nata yana Fadin”Haka mukayi dake..? Haba Malika stop don Allah baki ganin halin da kike ciki ne?”…Yafada yana kallonta cike da tsausayinta.

Kuri tayimai kafin kawai yaga tayi luu zata Fadi ya tarota yana Salati,ashe suma tayi sai da wadanda ke kusa suka taimako da Ruwa ya Shafamata kana ta Farfado,wannan karon babu kuka da baki sai dai kukan zucci da Fitowar hawaye,kamar an bude fanfo ammh ba mgana,Gashi ta makaleshi gam taki sakinshi,dakyar ta yarda ta koma jikin Joda,ammh sai da ya ce mata zashi jana’iza ne da an kai Daddy gidanshi na gaskiya zai dawo gareta,kana ta sakeshi ya Fice kamar ya mata kwallah.

Amsallacin jumma’an dake anguwan aka Sallaci Daddy,wanda ya tara dimbin jama”a iya kallanka mallam,agaskiya Daddy ya dace kama daga yadda Annabi ya kwatanta mana Dacen musulmi na kwarai,uwa uba ga Shedan mutane daya samu Abun sai wanda yagani,Amgakabarta ko ba”a matsaka tsinke wasu ma har aka binneshi basu hango ba,saboda tsabar jama”a,Saleem yana daya daga cikin shakikan Daddy wadanda suka sanya kanshi cikin kabari suka turbene da kasa,saboda imanin da Tunanin shima watarana nan za”a kawoshi yan”uwanshi na jini na gani  zasu Rufe kanshi da kasa,kai Allah ka Shirya damu kasa mu dace Duniya da lahira.

Bayan an kaishi gidansa na gaskiya aka dawo ana cigaba da karban gaisuwa bayan an saka Rufunan manya manya cikin haraban gidan da waje saboda mutane,Su Abbi sune gaba gaba wajen karban gaisuwa,Saleem ko yana tare da Sadiq dayazo bayan angama jana”izar Daddy,da wasu yan’uwansu matasa irinsu yan malumfashi,Ba dadewa sai ga su Ummi sun iso,har cikin gida suka shiga inda suka iske malika zaune inda Saleem ya barta tana kwallah ammh ba”a mgana,Ummi ta zauna kusa da ita ta Rumgumota tana ta lallashinta da mata nasiha masu ratsa jiki,hakama Hajiya itama ta dora danata hadda hajiya binta basu kyale ba,suna ta bata baki,don babu shakka mutuwar Alhaji itama ta daketa.

Sai yammah kana su Ummi suka koma Abuja,haka akacigaba da amsan gaisuwa daga bangarori dadama,ciki harda manajojin gidajen man Alhaji Abdulmalik dankasuwa,tare dana kamfafonimshi,Malika kuwa tunda aka Fita da gawan Daddy bata kara ma kowa mgana ba,sai dai kawai aga hawaye suna zubomata,sallah kadai ke tada ita daga inda take,Abinci ma In Joda ta matsa mata taci sai kawai tarashi ta Shige tiolet ta kulle kanta tana kuka,data gaji da halin data ke ciki ne ta Fita waje taje ta sanar da Saleem,shima Hankalinshi tashe yazo yana magiyan Ta bude,ammh malika taki,yayi yayi,sai ya koma daga ban baki zuwa yimata Fada cikin zafi,ammh kememe Malika taki budewa kuma yanajin kara sesshekan kukanta,wanda ke tafasa mai rai.

Kada kai kawai yayi ya Fita daga dakin bayan ya Umarci Joda data rabu da ita ta samu natsuwa zata bude da kanta,haka ko akayi sai da tagaji da zaman bayin kana ta Fito tana goge kwallah,ganin ban tsausayi ga cikinta ya girma Tunda ya Shiga watanshi na bakwai kenan,sai daddare kana Malika ta iya shan madaran hollandian da kaza,shima Saleem ne ya ritsata kuma ya matseta ya dinga Turamata abaki,bayan ya gama yakoma aikin lallashi,tana Rumgume ajikinsa,Joda dake kula da Malika in ta gansu awannan yanayin sai ta dinga mamakin yadda aurensu ya kasance,ammh kalli yadda Saleem yake kafa kafa da malika Bayason ya barta tana kuka,Baya barinta sai ya tabbatar da ko bata bar kuka ba toh hankalinta ya kwanta,ta bar koken koken takoma tana ajiyar Zuciya.

Ranar da”akayi sadakar ukune sai ga Maman Abba ita da megidanta sun zoma Malika da Saleem gaisuwa,Zahrin gaskiya Malika taji dadi sosai haka ta Rumgume Maman Abba tana Fadin”Maman Abba kinga yadda Rayuwata tadawo ko? Babu uwa,uban dani ke kallo amtsayin madubina shima yatafi ya barni..”Take Fada tana kuka,bayanta Maman Abba ta shiga bugawa tana Fadin”Kina da wani Madubin Malika,mijinki shima bangon kine,ina mai tabbatar miki Allah bazai dauke Daddy kuma yahanaki soyayyar Saleem da kulawanshi ba,sai dai ya daukeshi don gwada imaninki,kiyi tawakalli sai kiga Allah ya Dubeki da idon Rahama ya haska rayuwarki,wanda Daddy na cikin kabari Allah zai nuna mishi ke,kuma yayi alfahari dake..”Kalaman Maman Abba ya sanyayama malika rai har sai da ta murmusa tana digan hawaye,sake Rumgume juna sukayi tana kara lallashinsa.

Joda dake gefe kuwa sai tayi mamaki ganin yadda Malika ta saki jikinta da Maman Abba,wacce ke ta bata baki tare da wasu shawarwari,Itako Malika sai gyada kai take tana nuna alamun gamsuwa,sai yammah sukayi Shirin tafiya,Har waje Malika ta rako Maman Abba tana mata godiya,wanda ganinta haka bakaramin Dadi Saleem yaji ba,kura mata ido yayi yana kallonta,Itako kallo daya tayimai ta kauda kai tana Jin kunya ganin Abokinshi Sadiq na wajen ga sauran Manyan mutane irinsu Abbi.

Suna sallama da Maman Abba,shiko Saleem shida Sadiq suna musabaha da Baban Abban,ammh kacokan hakalin Saleem naga Malika ganin yadda kawai yaga ta wani rame,kodon bai kara ganinta cikin rana bane,? Sadiq ne ya lura da kallon da yake mata,shima ya kalleta aranshi yana yaba kyanta ba karya,har motar su Maman Abbah ta Fice daga gidan bata koma ciki ba ita da Joda,Ganin haka yasa Sadiq ya zunguri Saleem yana Fadin”Haba Acp wannan dogon kallon ai ya wuce na Shari”a..”?

Wani banzan kallo ya jefamai kafin ya cigaba da kallon Malika so yake su hada ido ita kuma tana lura dashi sai taki yarda,dariya Sadiq ya Sheke dashi kafin yace”Kuma gaskiya Ba laifi Matar naka akwai kyau,gata jinin Turawa ko banza zakuyita haihuwan Jajayen Fata kyakyawa..”Saleem bai san Dalili ba,kawai yaji mganar Sadiq ta cakanmai rai sosa,wani takaichi ya kumeshi,Kirne Fuska yayi kafin ya fara takawa zuwa kusa da malika wacce ke Shirin juyawa zata koma gida,bai ce mata kala ba,ammh yana biye dasu har suka Shiga Falon gidan,wanda joda ta dingama Malika radan ga Saleem nan na binsu abaya,bata juyo ba,ammh ita kadai tana Sakin mirmishi domin da babu Saleem arayuwarta wannan Rashin ya faru,kila itama da yanzu tana kwance,shiyasa akowani lokaci take jinjina ga gwarzon maza Wato Saleem domin ya zama zakara ne acikin zaratan maza.

 Sai da yaga sun Shige kana ya dawo wajen Sadiq yana kallonshi duka hannunwanshi cikin aljihunsa yake Fadin”,Dazu kace ina kallonta? matarka na kallah ko matata? kuma dakake yaba kyanta uban wa yakai idonka Akan matata? plz mallam wlh karka kara,In so kake ka yaba kyan mace sai kayi aure kaga sai ka yaba naka…”Daga haka yayi Wucewarsa zuwa Rumfar dayake zaune,shiko Sadiq baki ya rike yana Fadin”Au abun harda gori,toh muna kwana nawane inda rai da rabo.

Washegari sai ga Baban Zahra yazo gaisuwa wato tsohon Alkalin alkalai na kasa gabadaya,Zahirin gaskiya Saleem yaji dadi sosai wanda har cikin gida ya shiga dashi yayi ma hajiya da Malika gaisuwa,bai jima ba ya Tafi,bayan tafiyan ne Sadiq da Abbu suma suka dau hanyar Abuja bayan ya Shiga har ciki an kiramai Hajiya Binta da malika yayi ta musu Nasihan mai ratsa jiki,wanda ta Shigesu,haka suke hawaye kawai don yadda zukata suka raunana babu wani abunda baki ya isa ya Furta,gashi tun yau hudu da rasuwar Daddy mutane duk sun fara watsewa za”a barsu su kadai Abun yazo ya rafkesu.

 Sun tafi ba Dadewa Saleem ya nemi gnin Malika,ganin da Jama”a sosai a baban Falon gidan nasu gashi ita kuma tana sama ne,ita da joda,sai Yan alqawarin nata mery da Dose,Umartan Joda tayi data bude mata wani falo dake ta waje ya shigo,aiko haka akayi Joda ta bude Kofar Falon Saleem ya Shigo sai ga Malika ta Shigo da cikinta gaba,tana sanye da wata doguwar riga mai Tsukakken hannun kamar roba.

Batama kariso ba ya isa gareta ya riko hannunta suka zauna bisa daya daga cikin kujerin Falon,kura mata ido yayi ita kuma kanta na kasa,ajiyar zuciya ya sauke kafin yace”Ya hakurinmu..? fata dai kinci abinci baki zauna da yunwa ba..? Kai ta gyada mai kafin tace”Hakuri mungode Allah..’Tafada idonta na cikowa da kwallah,Baki ya sake kafin ya dafa duka kafadunta da hanuwanshi biyu yana Fadin”Toh kuma miye Abun kuka? ashe bakijin mgana na,har saunawa zan fadamiki kuka bashine zai dawo da Daddy ba,yatafi kenan sai dai mu tayashi da addu”a Allah yasa chan yafiye masa nan..”Hawayen datake rikewa suka zubomata ta sanya hannu ta share tana Fadin”Na bari insha Allahu..’Tafada cikin wani yanayi.

 Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace”Dama na nemi ganinki ne,saboda ina so na Wuce zamfara yanzu,shine nake so na tambayeki ranar bakwai zaki koma gida,ko kuwa sai kin kara wani satin..? Dagowa tayi tana kallonshi cikin Rauni tace”Yau kuma..? gyada mata kai yayi kafin yace”Eh Tun jiyama naso tafiya,so rashin Tafiyar su Abbi ajin ne shi yadakatar dani,.”Jikinta ne yayi sanyi kwal kwal da ido tana so tayi kwallah,bata fuska yayi kafin ya nunata da yatsa”Karki kuskura hawayen nan su zoba..,Haba don Allah ya kikeso nayi da raina ne,Kullm kuka kullum kuka,Ehe ko kin taba tambayanta yadda kukanki ke kona kin rai ehe..? Yafada yana sakarmata manyan idanuwanshi.

Rudewa tayi ganin yadda bacin ranshi ya Fito sarari,Kukan take son hana kanta sai kawai ta fada jikinsa da karfi tana tura kanta cikin Faffadan kirjinsa,tana hana kanta kukan dayakeson kwacemata, Riketa yayi saboda tabashi haushi,ammh jin yadda take kara kamkameshi ne yasa ya tabbatar da hakuri take bashi,hannuwansa yasa duka biyun ya Rumgumota yana Sakin ajiyar zuciya yake Fadin”Toh wai miye na kuka daga nace zan Tafi yanzu? kodai baki san na tafi ne..? 

Dagowa tayi ta daga ga mai tana kokarin maida hawayenta,Zuru yayi mata da ido kafin yace”Meyasa baki san na tafi,alhalin kinsan cewa zan koma bakin aiki..”Rau rau takara yi kafin tace”Kabari sai gobe ka tafi don Allah..!Ina son kasancewa tare dakai..”Tafada tana maida kanta jikin kirjinsa Rumgumeta yayi yana sakin wani munafikin mirmishi,Shafa bayanta yake yakasa mgana Lokaci daya ya dago kanta yana kallon kwayan idonta,Kasa juran kallon tayi sai ta hau lumshe ido tana kokarin maida kanta kirjinsa,Bai bata dama ba,sai ma Lebenshi dayakai kan lebenta yana tsotsa cikin wani salo,bata mai gaddama ba,sai ma kara rikeshi datayi tamikamai Harshenta ya kama yana tsotsa cike da kwarewa, kan cinyarsa ya maidata,shikuma ya cigaba da kissing dinta yana Shafa ko’ina ajikinta musassaman cikinta zuwa kasan mararta,Tuni ta Birkicemai lokaci daya itama take maida mai martani tana shafa kanshi zuwa bayanshi hannayenta na kara kaina bisa kirjinsa tana shafa kan Nipples dinshi,Shan yaji Saleem yafarayi saboda jin wani abu na zirgamai,Lafe mata yayi ajiki yana maida Numfashi,hannayeta ya rike cikin wani yanayi yake Fadin”Bari kina tadamin da hankali..”Yafada yana kamkameta cikin wani yanayi.

Da idonta wadanda ke cike da bukatuwa ta kalleshi,shima ita yake kallo batayi musu ba ta daina tabashi,ammh sai ta kai bakinta saitin Kunnanshi tana Fadin”Am here for u Only mallam..”Tafada tana Shafa keyarshi da hannunta guda daya jin haka yasa ya Birkitota yana kallonta da idanuwansa wadanda suka chanza launi yace”Really….”Yafada cikin wani Shauki kunya ce ta kamata sai ta kauda kai tana kokarin tashi daga jikinsa bai bata dama kawai sai ya mikar da ita tsaye,bai mata mgana ba ya koma ya kulle kofar falon yana dawowa ya Cire riganshi yana kallonta ido cikin ido,kafin ya sanya hannu ya zare mata hijabin jikinta yana binta da kallo,Wuyan doguwar rigar ya sabule mata dama tana babban Wuyane,sai gata tayi kasa zata fadi,da hanzari ta rikota tana kallonshi 

Shishige mata yafarayi yana wani kankance ido,Tokareta yayi da kafarsa hade da kujera yana kama Fuskarta da hannu biyu yashiga bata wani kiss mai zafi yafi minti biyar yana tsotsan bakinta kafin ya Kwantar da ita ahankali bisa kujeran shima yazo ya kwanta akanta,ammh sai yayi gefe saboda cikin jikinta,Tana kallon kwayan idonshi ta dauki hannunshi ta aza bisa boobs dinta,kafin ta rumgumeshi tana Shafa kirjinsa cike da salo da kwarewa,cikin lokaci suka rikita juna bakacin sautin komai sai na tashin Numfashinsu,Saleem yasamu Abunda yakeso,Rumgume yake da ita yana maida Numfashi Dadi da wahala lokaci daya..

 Saboda jaraba irinta Saleem da samun waje kakumarta yasake yi,Yakara second round,domin kwata kwata baya gajiya da tsaga jikin malika tana da wani sirri dake rikitashi sosai wanda ko yanzu yagama Having Sex da ita,toh sha’awarta zata dawo mai sabuwa,sai gashi tare sukayi wanka a bedroom din dake dakin dama akwai bedroom Saleem ne yake ra”ayin yau din Asaman kujeran za”a kashe arnan??suna gamawa Ya je mota ya Dauko kayanshi ya sauya kafin yakoma ciki yayi ma su Hajiya sallam,kunga Malika yadda ta makaleshi gabansu Hajiya da Joda da yan Malumfashi tana kuka Wurjajan,Wai bazai tafi ba,shi yau yaga ikon Allah,Dakyar da Sodin goshi ya lallasheta ta sakeshi shima sai da yayi mata alqawarin Ranar bakwai zai zo ya ganta,duk da haka bata ga tafiyarshi ba daki ta koma tana kuka,shikanshi jikinsa ba Dadi ya tafi bai san dalili ba yanaji kamar Malika ta dauwama dashi har karshen rayuwarsa ba,bai yi Kukan rashi da kewarta ba sai da ya koma gida yayi kwance kan gado yana Tunaninta,Zahra ko tana ta nacin kira yaki daga kiranta saboda  in yana cikin halin Kewa da Tunanin malika baya bama komai muhallin hanashi ko dakatar dashi.

_______________________

*BAYAN KWANA BAKWAI..*.

Ranar addu”an bakwai da Wuri Saleem yazo,shima Abbi yazo shida Ummi ammh basu jima ba suka tafi,shima saleem bayan gama addu”ar yace joda ta kiramai Malika shi zai koma,Kin fitowa tayi tana chan saman dakinta tana kuka,dole tasa Saleem ya Shiga har saman da kanshi yadda ya ganta Abun bai mai dadi ba duk takara ramewa akan yarda ya barta Ranshi ya baci ya fara mata Fadanshi da bataso,Ai sai ta Rude ta sauko daga kan gado tana bashi hakuri ammh yayi banza da ita ta inda yake Shiga batanan yake Fita ba,daga karshe yace indai tana mai Taurin kai Allah bazasu shirya ba.

Hanyar Fita yakama da hanzari ta mike ta isa ta bayanshi ta Rumgumoshi tana kuka take Fadin”Don’t leave me..Don’t..”Take Fada tana kuka cak ya tsaya yana jin kukanta na ratsa ranshi,Juyo wa yayi yana Riketa da wani karfi ta fada jikinsa ta kamkameshi tana kuka,Shima maida hannuwanshi bayanta yayi yana sakin ajiyar Zuciya,Shafa bayanta yake zuwa kasa Tudun hip dinta cikin wani salon lallashi yake Fadin”Fisabillahi Yanzu Abunda kikeyi daidai ne? Sau nawa zan fadamiki Kidaina wannan koke koken,? Kokuwa dai wulakanci da kuma raini ne ke damunki Tunda nace bani son kukanki wato in mutuwa zanyi na mutu ko..?”Da sauri ta dago kanta tana girgixamai tana hawaye,hannu ya sanya ya Sharemata hawaye yana fadin”I already tell u no more kuka indai ina tare dake,to meyasa kike yi koda yaushe.?.”Tana rike hannunshi tana kara share kwallah tace”Nabari..Nadaina wlh..”Tafada cikin sanyin murya,Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya Rumgumota jikinsa yana kamkameta Idanuwansa suna Rufe yaji ta Furta”I miss u…”Shikanshi Shaukin kewarta ne yasa ya Furta mata”Me tooo…”Cikin muryan So da muradi.

Bai mata komai ba ranar ammh kafin yatafi sai da yalugwigwitata son ranshi,Kuma yayi mata wanka ya bata abinci kafin ya tafi ya barta wajen Hajiya da joda zuwa wani satin yazo ya tafi da ita,bai bari tasan tafiyarshi ba daga Fita salla ne bai dawo ba,sai dai ya kirata awaya yace yatafi,saboda yasan sai tayi kuka,shikuma kukan tane sam bayaso,Akwai sunsha kuka ranar ita da hajiya barima da duka jama’ar Malumfashi duk suka koma aranar ko mazan dake waje ba kowa,Tuni kowa ya watse,wadanda suka tsaya shakikan Alhajin ne Na Malumfashi,ranar mutuwar ta dawo musu sabuwa gida yayi rakwa rakwa,ranar Malika da zazzabi ta kwana saboda kuka,da Joda ta mtsamata tasha panadol taki sai tace mata zata kira Saleem ai da hanzari tatashi da karba tasha takoma ta kwanta tana maida numfashi lokaci daya da hawaye,itako Joda sai da murmusa tana yaba tsarin wannan Soyayyar mai cike basarwa domin duk wanda ya kalli malika yasan Tana cikin mayen son mijinta,haka shima soyayyar Malika bata boyiwa acikin idanuwansa ba,sai dai shine yake kokarin boyeta da karyata kanshi da wai amanace gareshi gata marainiya ba Uwa ba uba.

Haka suka ciga da zama ita da hajiya da joda Da su merry wanda zuwa kwana goma kowa ya watse sai wata goggo talatu kanwa take ga Hajiya suma zaune tare,Tun zuciyoyi na kuka suna bayyana digan hawaye har suka gaji suka dau dangana suka koma kukan zucci,Ranar da Daddy ya cika kwana 14 da rasuwar tun Safe Malika tayi Shirin komawa ita da Joda wanda Hajiya tace su tafi tare ta rinka taimakamata da wani abu saboda yanayin Jikin na malika,aiko taji dadi sosai,Saleem ya kirata yace Direba yakawo ta shi bazai samu zuwa Meeting suke dashi..

Da zata tafi haka ta kamkame hajiya ta kuka dakyar aka bambareta daga jikin hajiya,wacce itama kukan mutuwar ta dawo mata sabuwa,mota kawai Malika ta Shige tana kuka mai ban tsausayi dayake dama already sun Saka duka akwatun nan kayansu cikin booth din motar wanda Direba zai kaisu,cikin daya daga cikin motocin malika ne sanda tana ganiyarta.

  Sai da suka iso gida kana Malika ta kira Saleem ta fada mishi isowarsu,azahirin gaskiya ya nuna murnan sosai,har saida sautin mirmishinsa ya Fito Fili,joda ko gyaran gidan tafara harda kichen sai da ta share ta goge datayi mganar girki ne malika tace tabari Mallam ya dawo don ita tunda tazo bata taba girki ba,Tunda bama iyawa tayi ba.

Sun idar da sallar mangariba kenan sukaji hon din Shi megadi ya wangalemai get ya Shigo,jikin malika na rawa ta mike daga kan Darduma datake tana sakin Mirmishin jin dadi ga cikimta wanda yayi girma cikin doguwar rigar Material dake jikinta,da kallo joda ta bita,tana mamakin babu Abunda ke sanya Malika mirmishi sai Saleem Tun bayan rasuwar nan shine ganinshi ke sanyata mirmishi,kuma tafiyarshi ta sanyata kuka 

 Joda bata gama mamaki ba,sai gashi yayi sallama bayan ya sawo kanshi cikin daki yana sanye da Uniform dinsa Harda hulanshi hannayenshi rike da manyan lodojin reasaurant har guda bayu,da malika yaci karo tana tsaye tana kallonshi cike da kewa,cogewa yayi yana binta da kallon Sha”awa baisan dalili ba,duk sanda yaga malika sai yaji yafi kowani Namiji sa’an mace mai kyau da tsarin jiki na mata.

Yadda ya saki baki ne yana kallonta yabama Joda dariya,wanda tana ma gaisheshi bai ji ba,yana chan ya saki baki yana bin Malika da kallon sha”awa bata gama dariyan ba taga ya ijiye lodojin hannunshi asaman cafet din daki ya ware ma Malika hannu yana Fadin”Oya *YAR AMANATA..* Come here…’Yake fada yana sakin mata wani kayatattacen mirmishi.

 Itako kunya duk sai ya kamata ganin Joda tsaye,ganin taki zuwa ne yasa ya isa gareta da sassarfa ya Rumgumeta kam yana Fadin”Idanuwanki suna cike da kewata,ammh kinki ki Nunamin yadda kikayi kewata ko? Yafada yana tusa kanshi jikin Wuyanta 

Da hanzari joda ta bude kofa ta Fice tana yar dariya ita kadai.

    Malika taga Fitan Joda da sauri Abun sai ya bata dariya,ganin tana dariya ne yasa ya dagota yana kallonta Tunkafin yayi mgana Malika tace”Joda ce ta Fita da sauri..”

Ido ya ware yana kallonta kafin ya kalli kofa yana Fadin”Wai dama ku biyu ne adakin nan..? Yafada kai tsaye yana shafa gemunsa,Dariya yabama malika sai da dan dara,Kumatunta ya shafa yana Fadin”Eh mana,dole na tambayan kinsan ke kadai nagani..”Mirmishi ta sakarmai kafin tace”,”Ai tama Fice Abunta,Sannu da zuwa..”Yana zama gefen gado yace”Yauwa ya hanya? kun dawo lafiya,ya karin hakurinmu..? 

Yake Fada yana rikota bai mata mazauni ako’ina ba sai akan cinyarsa,Yana zaunar da ita,Kanta na kasa ta zauna tana Fadin”Mungode Allah..”Kanta ya aza bisa faffadan kirjinsa yana Shafa kanta yake fadin”Allah yajikan Daddy da rahama yasa yana kyakyawan mtsayi..”Da Ameen ta amsa muryanta asanyaye 

Sun dade ahaka kafin ya tada ita zaune ledan Takeway din dayazo dashi ya dauko yana riko hannunta yake Fadin”Muje falo,na gaisa da joda,sai kuma naje nayi taking shower ko..?gyada mai kai tayi kafin ta rike hannunshi gam,su Fice daga Dakin yana rike da ita….

Joda na zaune suka Fito mikewa tayi tana dariya take kara gaishe da Saleem,ledojin hannunshi ya mika mata yana Fadin”Yauwa Hajiya Joda,barka da zuwa garin zamfarawa,Kiyi hakuri fa dazu ban ganki ba,kinsan Abunda akace amanace gareka toh dole sai ka kiyaye,kinsan Malika amana take awajena,shiyasa idona ya rufe bana ganin kowa sai ita..”Ba Joda kadai ba hatta malika sai da ta murmusa,karban ledan Joda tayi tana Fadin”Eh lalle naga alama,gaskiya acigaba da kularmana da Amanar Daddynmu muna son haka..”Tafada tana yar dariya 

   Mirmishin yake yayi yana Fadin”Au kema kin bada goyon baya kenan,? Da hanzari Joda tace”Sosai ma..”Kada kai yayi kafin yace”Toh Allah bani ikon Kula da Amanar taku,ammh itama yar Amanar naku bata jin mgana,tacika taurin kai..”Yafada yana kallon Malika adage,hannu daya kuma yana Sosa dan sajensa,Dariya Joda tayi tana kallon Malika data shagala da kallon Saleem saboda yadda yayi mata kyau cikin Uniform dinsa na kakin yan sanda?

  Taimakama Malika yayi ta zauna bisa kujera kiss ya sakarmata a goshi kafin ya mike yana Fadin”Let me go and take Shower na dawo kinji..? Gyada mai kai tayi kafin tace”Toh…”bai kara mgana ba ya juya cikin takunsa na isa ya nufi dakinsa,daidai sanda wayarsa dake aljihu ta dau Tsuwan Neman agaji,Tana gani ya ciro wayar daga Aljihu yakara akunne daidai sanda yake Tura kofar dakinshi ya Shige tanajin sanda yake Furta”Amin Afuwa Madam..”

Wani Yam taji acikin ranta,Nan da nan Zuciyarta suka raya mata abar sonshi ce Ta kirashi ma”ana amaryanshi,wani takukin abu takeji yana mata wayau bisa kirjinta,har sai da wasu siraran hawaye suka zobomata tayi hanzari sanya hannu ta share tana kokarin daidaita kanta,lokacin dataji sawun tafiyar Joda wacce ta Fito daga kichen dauke da Filet din data Juye musu abincin da Saleem ya taho musu dashi.

Waina ce da miya sai Ferfesun kayan ciki,wanda shi din nema malika taci ba laifi tasha ruwa takoma tana maida Numfashi,itako Joda wainarta taci takoshi tanayi tana kallon katon talabijin dake Falon inda ake haska Shirin akushi da rufi daga Tashar Arewa24,tuwon Shinkafa ake koyawa nan da nan Joda tace”Anty malika gaskiya yakamata bayan kin haihu ki zage ki koyi girki ba dadi ace kullum ya Saleem na bisa hanyar Restaurant zuwa Siyo abinci alhalin kowa yasan yana da mata..”

 Tafada tana kallon Malika,wacce tayi zuru ta kurama Talabijin ido,Abunda Joda ta fada gaskiya itama tayi wannan Tunanin ammh rashin wanda zata fadamawa ne yasata tayi Shuru da bakinta,ammh Tunda har Joda tayi mgana bari tace wani abu,Cikin sanyinta na kullum tace”Tabbas hakane Joda na dade da wannan Tunanin araina,arayuwata na rasa abubuwa dadama daza”ace mace ta gari ta mallakesu,shiyasa Mallam zai kara aure..”Tafada tana Sharan kwallah,Ido waje Joda ke kallonta kafin tace”Wani mallam din..? Malika na kallonta tace”Saleem…”da hanzari Joda ta tsame hannunta daga Filet din wainar datakeci tace cikin tashin hankali..”Ki bari don Allah,? Wlh bansani ba yaushe zai yi auren? kuma wata yarinya ce..?

Malika na Yamutsa fuskar takaichi tace”Karki ga laifinshi Joda wlh yayi kokarin sosai,samun Namijin da zai zauna dani Awannan zamanin wlh irinsu sunyi karanci,Bansan yaushe bane bikin ammh kamar Ummi tacemin wata uku akasa yanzu kuma da gayamin za’a kai wata Tunkafin rasuwar Daddy..”Tafada cikin rauni,Cak joda ta Dauki Filet din wainarta ta maida kichen taje ta wanko hannayenta tadawo falon kusa da Malika ta zauna tana Fadin”Anty Don Allah kidaina damuwa,Kinga Fa halin dakike ciki,kada kibari wannan mganar tasaki cikin damuwa..”Mirmishin yake Malika tayi kafin tace”Kinga na damu ne Joda? ni tsorona Daya yadda rayuwata zata dawo acikin gidan da zarar mallam ya samu nasarar auren wacce yakeso..”Zuru Joda tayi mata da ido kafin ta sanya hannu ta dafa kafadanta tana Fadin.

  “”Wlh bazaki Wulakanta ba Anty malika,haba aiko yadda yaya Saleem ke miki dagani yana cikin mayen sonki ne..”Idon Malika na maiko tace”uhmm haka kike gani dai,ammh babu soyayyata acikin ranshi sai dai tsausayi da kuma girmama girman Amanar da Daddy ya barmai..”Wani Shu’umin Mirmishi Joda tayi kafin tace”Haba Anty malika Kifa daina gaddama akan wai yaya saleem baya sonki…? Ai tsausayi shine ginshikin Soyayyaha,Tunda dai yana tsausayinki toh ina mai tabbatar miki da cewa yana Sonki har cikin ransa..”Tabe baki Malika tayi batayi mgana ba,sai ma ta yunkura ta mike tana mikama Joda Filet din Ferfesun kayan cikin data ke ci tana Fadin”Sakamin shi A fridge gobe da safe zanci..”Mikewa joda tayi tana Fadin”Toh Allah ya kaimu,ammh yakamata kima yaya Saleem mgana ayo cefene sai na dinga girkawa ni,ya huta yawon siyo abinci..”.

Malika na tafiya zuwa hanyar dakinta tace”Ki mai mgana mana..”Tafada cikin Kufula saboda harta Saleem din saboda kishi haushinsa takeji yanzu,Da kallon tsausayi Joda ta bita kafin ta kada kai zuwa kichen tana Fadin”Insha Allahu Anty malika zaki Farinciki arayuwarki,domin nima sai inda karfina ya kare na ganin kinyima sauran mata zarra agidan mazajensu.

Shiko Saleem yana Shiga daki yafada gado suna cigaba da waya da zahra,wacce ke mai kukan Shagwaban Tun jiya ya manta da ita,shi dariya ma ta bashi,tana wani sangarta duk don ta burgeshi,shiko acikin ranshi yana Fadin”Duk sangartanki naga Malikata?,ammh azahiri sai ya biyemata yana lallashinta da bata bakin tarinka hakuri dashi tasan yanayin aikinshi ko yayarta ta gidama hakuri take dashi Tunda tasan yanayin aikinshi,Zahra batasan dalili ba daya ambaci Malika sai taji ranta ya baci,ta alura akomai akace sai yace Malika kaza,abun na bata haushi Duk da ta riga tasan yadda badakalan aurensu ya faru,wanda abaya taso ta taso mai da mganar tana tambayanshi,Daure mata Fuska yayi yace kada ta sake tafara Shiga hurumin da ba nata ba,bayason rainin hankali sam,kuma a yarda ya nuna mata,bazai dauki ta raina mai malika,don zata samu matsala babba ma kuwa itako Zahra arawan kanta tagananin Malika bata da wani anfani wajen Saleem Tunda ya aureta ya saketa adaren Farko,sai daga baya ne ya dawo da ita,akwai ko ahaka tayi mata zarra??

Dakyar ta bari yashiga yayi wanka ya Fito bayan ya dauro alwala yazo yayi sallar issha’in data Subucemai,Shafa’i da Wuturin daya sabayi yau baiyi ba saboda nacin Zahra kawai biyemata yayi saboda sun kwana biyu basu wayar dare ba,koda Ranar ma sama sama suke mganar,Hira suke tasha tana bashi lbrin irin tanada tanadan datayima bikinsu wanda takejin kamar tajawo ranar biki zuwa gobe saboda Zumudi,Shi ko zumudin bayayi ammh ita datake budurwa rawan kafanta yayi  yawa Shi har mamakinta yakeyi,tunda yake baitaba ganin Amarya mai Shigen rawan kafa ba irin Zahra,wanda halittace domin da zata bari data bari Tunda Momi na mata Fada,hakama Nadira wani lokacin kamar ta maketa takeji in tayi wani abun,shiyasa basa shiri da Yaya Nadir,saboda yadda bata komai cikin natsuwa..’lalle zahra kin samu mtsala?

Bata barshi ba sai wajen 12 koda ya Fito Falo Tun har sun kashe komai na kayan Wuta sun Shige daki sun kwanta,bai shiga dakin ba ya dawo dakin yayi Shirin barci ya kwanta cike da Tunanin yadda zai Tunkari Malika da zencen kara aurenshi,bayaso yakara tadamata da hankali kan wanda take ciki,bata gama warwarewa,ammh ya yanke shawaran zai sanar da ita,ammh zuwa gaba kan lokaci ta dan saki ranta.

   *************

 Washegari Da Saleem zai Fita office,Joda tayi mai mganar Cefane,hakika Saleem yaji dadi ko bakomai yanzu Duniya andaina kiwon Dabba kamar da,yanzu duniya cike take da masu saka ido,yanzu haka Allah kadai yasan mutanen da sukayi zundenshi na Siyan abincin dayake Tafe yi kullum ba ranar banza,Musamman yan wajen aikinsu yasan baza”a rasa masu dogon baki ba?.

  Har afuska ya Nuna ma Joda jin dadinsa akwai yana Fita ba dadewa sai ga Sargent musa ya Kawo kayan Cefena niki niki,Joda ta karba ta kai kichen ta sanya komai cikin muhallinshi,da ta bude store din kichen din wanda ke shake da kayan abinci kala kala Nau’i Nau’i,nan da nan Joda ta zage damtse tana hada hadar Dora,girki ita kuma Malika tana daki yau ko Falo bata Fito yan mulkin sun motsa,shiyasa ko Saleem daya Shigo dubata da safe barci karya tayimai,har ya fice basu gaisa ba sai da ya Fita kana ta bude ido,tana bin bayanshi da kallo cike da Soyayyarsa mai Cike da muradi da sadaukarwa.

 Sai da Maman Abba ta Shigo kana Malika ta Fito da katon cikinta suka gaisa tana mata sannu,Joda ma dake kichen ta Fito suka gaisa kafin takoma ta cigaba da aikinta don Malika tace tayi mata Tuwon Shinkafa miyar Ganye,Maman Abba taji dadin ganin yadda Malika ta chanza ta cire damuwar komai acikin ranta,har ta nuna mata ta hanyar Furta mata,daga karshe tabata Shawaran ta rinka zuwa kichen din duk da haka tana kallon Abunda Joda keyi tana koya da haka zata sha mamakin abunda zata Tsinta kafin Allah ya sauketa lafiya,Malika taji dadin haka tace daman zaman kadaichi ya isheta in Joda ta Shige kichen ta barta ita kadai,gashi ita kallo bai dameta ba.

Sai da Joda tagama Tuwon nan Maman Abba taci kuma tatafi dashi saboda yadda Tuwon yayi mata dadi,Malika ko taci taci takara kamar cikinta zai Fashe,wanda ya ragu Joda ta ijema Saleem,malika ta dauke tace shi zataci da daddare,dole Joda ta girkama Saleem farar Shinkafa da miyat kaji,Koda ya dawo Joda ta gabatar da abinci bakinshi ya kasa rufuwa nan Falon ya zauna dirshan yana cin abinci,ammh sai yaga Malika nacin Tuwo daya tambayi Joda ina Amanarshi ta samu Tuwo,nan take sanar dashi ita tayi dazu kuma yar Rigimar nasa ta dauke tace shi zata ci kafin ta kwanta.

Kura ma malika ido yayi yana kallonta tana cin Tuwonta cike da Sanyinta yadda ta saba,mirmishi kawai yayi yana Fadin’,Tunda itace zataci toh nayi mata afuwa,ammh da wani ne yau Allah bazan barmai ba..”Yafada yana Hade giransa waje daya Dariya joda ta dinga musu tana Fadin”Kunfi kusa aie..In ma zaka karbi kayanka ne babu Ruwan Joda aciki..”Yana cin abinsa bai sake mgana ba,saboda yaga yau din Mulkin Malikar ya motsa ne,ganin haka yasa joda ta Shige daki ta barsu anan.

Shima yana kammallah jin abincin da kanshi ya kwashe kololin zuwa kichen ya wanke hannayenshi ya dawo Falon yana kallon Malika tana wani yamutsa baki,gabanta ya karisa yana kallonta kafin yace”Ya..? kin koshi ne..? Kai ta gyada mai akarkace,Filet din Tuwon ya dauke ya nufi kichen dashi da sauri tace”Don Allah asamin a fridge gobe zan karya dashi..”bai juyo ba,kuma bai yi mgana ba ya Shiga kichen din yasanya mata shi cikin  Fridge din ya Fito.

Yana zuwa gabanta baiyi wata wata taji ya daga cak,ya sakata cikin kirjinsa da ita,kuri tayi mai da ido tana binshi da kallo ganin hanyar dakinshi ya dosa da ita,shiyasa tace”Ban wanke hannu ba Mallam..”Bai mata mgana ba sai da ya direta bisa gadonshi kafin ya durkusa kusa da ita ya Dauki hannun damanta wanda taci tuwon dashi ya saka abakinshi yara lasheshi daya bayan daya,sai da ya sule hannun tas,yana yi yana kallon kwayan idanuwanta,Lumshe ido take tana jin wani yanayi yana Shiga jikinta.

Sai da yagama lashe hannun kafin ya mike yana kallonta yace”Daga yau kinga makwancinki nan,ke ko kunyar Joda bakiyi ga dakin mijinki ammh kina kwana da wata katuwar mace..”Yafada yana Shafa gemunsa daya Tsirowa na rashin kunya?,Ware ido tayi tana kallonshi kafin ma ta samu zarafin mgana ya Fada tiolet yayi wanka ya wanke baki kafin ya dauro alwala koda ya Fito jikinsa babu riga,sai dogon wandonshi Jikinsa gabadaya yana digan Ruwa,jallabiyansa ya sanya ya shimfida sallaya ya tada sallar Shafa’i da Wututri yayi kafin ya rufe a addu’o,insa,Koda ya idar da Sallan Malika ta dade da yi barci,shiyasa yana tashi ya dauketa yakaita tsakiyar gadon ya gyara mata kwanciya,shima cire jallabiyan yayi da dogon wandon jikinsa,Ya bar kanshi daga shi sai gajeron wando ya Kwanta kusa da Malika ya Rumgumota kam,yana sakin ajiyar Zuciya,itama cikin barci ta zagaye hannayenta bisa cikinsa ta rikeshi gam,Blanket ya Rufa musu yana shafa maran Malika zuwa saman Tulelen cikinsa haka kurum yakejin Nishadi na Shigansa,yana jin wayarsa na Dukan neman agaji ammh ya share don yasan zahra ce,shi haushin datake bashi ta manta yana da mata ne? ammh sai ta dinga kiranshi duk sanda taga dama,Tsaki yaja aransa yana Fadin dole ya tashi tsaye don ya lura sam zahra bata da adalci.

  *****************

Kwanaki suna ta gangarawa ayayinda muketa cinye kwanakinmu Aduniya,Ahaka ne har gashi auren Zahra da Saleem yana ta matsowa har yarage saura 4weeks ta kowani bangare anata Shirye shirye musamman ma bangaren uwar gayyah zahra,tun akwanakin da suka rage tafara banke banken mganugunar mata kamar hauka,wannan kuma shawarar Nadira ce itace kan gaba wajen amsomata tana duramata ammh basu bar momi tagani ba don susan zasu ci ubansu.

Ta bangaren Saleem ko baya wani Shirye Shirye domin ayanzu yafi jin dadin rayuwarsa Fiye data kullum,Domin shakuwa mai cike da salon soyayya ta shiga tsakanin Malika da Saleem,wanda shi Saleem din bai Fahimci haka ba,Sakamakon zuwan Joda shi yakara musu kusanci da juna,shine sanadin kwanansu waje daya wanda yayi sanadiyar kara musu Shakuwa da kusantan Juna.

 Duk da halin da malika ke ciki da zarar Saleem ya nemeta bata iya mai gaddama zata bashi dukkan Hadin kai da zai samu natsuwa,shikuma yana son binta ahankali saboda cikin jikinta ammh kuma zumarta ne ke janshi wanda indai zata kwana cikin jikinsa bai ya kauda ido akanta sai ya lalubeta ko kadan ne,ita kuma bata iyamai gaddama,domin yakoya mata jarabanshi bata iya hakuri dashi indai yana nan tana kakume dashi.

Daga bangarenshi babu Shirye shiryen dayake gudanarwa ko kudin kayan aure ma Ummi ya tura kudi a banki ta bada oder kayan akwatuna,tsarin Shirye shiryen bangaren amarya kuwa sai da ya bude musu Wuta ita da Nadira,Abun takaichi aure kamar wani auren Mawaki,Evets wajen goma suka lissafomai baki ya sake yana kallonsu daga karshe ya Rufe bakinsu da Fadin Shidai banda daurin aure babu Abunda zai hallata,so in ma sun Shirya bidi’o’insu toh shi dai bandashi ayi lafiya 3hundered thausand ya tura musu yace suyi Abunda ya zama dole,sai kuma yahadasu da Sadiq tunda yaga yamatsamai Shiyasa ya hadasu don yaga shima dan Rawan kan ne kamar su.

 Baita yarda yayi ma malika mganar ba,itama batayimai ba,sai ranar Suna kwance bayan sungama Samun Natsuwa tana kwance bisa kirjinsa,wayar Saleem tayi ta daukan daukin kira,wanda lokacin after 11 na dare ne,yana ji ammh sai ya dauki wayar ya kashe,ganin haka yasa Malika cewa”Ka daga kiran ka Mallaam..”Tafada cikin karfin hali.

  

Yana jinta yayi mata Shuru ammh kuma yana Rumgume da ita yana Shafa gashin kanta zuwa bayanta,Cikin kasalattaciyar murya yace”In dauka fa kikace?kinsan waye ke kiran ne..?Kai tsaye tace”Na sani ba amaryanka bane..”Abazata yaji mganar nata,duk ya ji wani iri ammh sai ya dake cikin karfi hali yace”Waya fadamiki zan kara aure..”Kai tsaye tace”Ummi ta sanar dani tun lokacin da aka sanya ranar..”

Shuru yayi bai kara mgana ba,itama sai taja bakinta ta tsuke,still kuma Zahran bata hakura ta daina kira ba,afusace ya dauki wayar ya kasheta gabadaya yana tsaki cikin ranshi,har ta Fidda rai da zai mata mgana taji yace”Ammh meyasa baki taba Nuna min Ummi ta sanar dake ba..”Tana kwance bisa kirjinsa bata dago ba tace”Saboda baka bani damar haka ba,bansani ba ko kana Tunanin cewa zan hanaka kara aure ne,nikuma ko daya babu yarda zan ce ka zauna dani ni daya mallam,Allah yabada zaman lafiya yasa ayi sha’ani lafiya agama..”takarishe Fada tana Sharan kwallah.

Tsausayinta ya kamashi,Fuskarta ya dago yana Share mata hawaye yake Fadin”will tok later,juz sleep now kinji..”,Gyada mai kai kawai tayi takoma bisa kirjinsa ta lafe,shikuma yana ta lallashinta ta hanyar Shafa bayanta zuwa kugunta cike da salon lallashi,har barci ya kwasheta shiko idanuwansa biyu yana Tunanin yadda yanayin zamansu zai kasance irin zahra ta Shigo rayuwarsu.

  ***************

Bai kara tada mata da mganar ba,shiyasa itama tayi mai Shuru,bata karamai mganar ba sai da taga yafara gyaran gidan,gabadaya dakunansu zuwa falon duk an chanza komai da komai anyi sabon Fenti,kuma daga yammah daga Falon ya Fitar da dakinsa,aka gyara aka zuba komai da Malika taga haka sai tamai mganan cewa badai anan zai saka amarya ba,sai ya bata amsa da cewa eh anan gidan zata zauna,ammh adakinsa,shi kuma Zai koma sabon dakin daya gyara,sai Malika tace Me zai hana su koma gidan da Daddy ya bashi su zauna dukkansu,sai ya dinga zuwa musu Weeked.

 Ya dade yana kallonta cike da mamaki kafin ya girgiza yace mata”Bazai yuyu ba,bai zauna da ita acikin gidan da akabashi saboda ita ba,cin Fuska ne wannan kawai ta barshi tazo nan su zauna,kuma Shi baya ra”ayin zama shi kadai yafison ya hadashi matanshi waje daya ta bari in tana so ta zauna agidan ta bari sai ta haihu sai su rinka zuwa suna hutunsu achan,data mtsamai sai ya bata Fuska yace tadaina ma Damunshi Dole Abunda ya tsara shi za”ayi.

   ***************

Biki saura Sati biyu Aka kai akwatunan aure kano,wanda Ummi da ita da wata kawarta da wasu goggonin Saleem yan kumo suka kai kayan,akwati takwas,shake da kayan arziki  wanda aka karbesu hannun bibbiyu Abunda sai wanda yagani,Suma achan din anyi musu kara sosai sunci sun sha,kuma sunyi guzurin Abun soye soyen da’akayi musu basu ci ba,Takwaichin Turaman atamfafi ashirin Hajiya Saratu momi ta basu da kudi 50k,Daga kano zamfara suka Wuce suka kaima Malika kayanta wanda aka hadamata dana Haihuwa,Dayake tayi scanning ance mace zata haifa,akwati hudu nata uku kuma kayan bbys ne Abun sai wanda yagani,Malika taji dadin zuwansu ba kadan,ita da ada take jin haushin baki suzo gidansu,ammh sai gashi yau Malika tana neman ma bako yazo wajenta koda daga kauye ne..

Ba Aranar suka koma ba,sai washegari suka koma Abuja,wanda kafin tafiyarsu sai da suka tara Saleem da Malika suka yi musu nasihan da fatan su xauna lafiya da junansu,Amarya kuma Ummi tace ranar da za’a dauko ta daga kano Abuja za”a kawota sai ta kwana kana washegari su wuto zamfara da ita.²²

Advertisements

_____

About AIS

Check Also

MALIKA MALIK CHAPTER 17 BY JANAFTY

Advertisements _____ MALIKA MALIK CHAPTER 17 BY JANAFTY Www.bankinhausanovels.com.ng  Advertisements _____ ……………….”””Rayuwar Farinciki tare da Wata …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *