[Advertisements⬇️]

KASAR WAJE CHAPTER 8 BY MARYAM DATTI - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

KASAR WAJE CHAPTER 8 BY MARYAM DATTI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Sosai hayfa ke horuwa a gurin coach umarnin Armando sabida ta gingije sosai+

A yayinda Yusuf shima sosai yayi busy ga pool ga club ga online lecture sun gama sai tranning da suka fara inda yana tashi pool 4:pm yake wucewa tranning ya tashi 8:pm ya dawo gida ya jira hayfa suci abinci tare ya d’an huta 10:30pm ya wuce club sai asuba kuma

Sosai hayfa ke tausaya masa ganin yadda sam baya hutawa gashi ya d’an zube dukda itama ba wani hutawar ta keyi ba tana neman kudin ne y’an Nageria na hutawa

Tana dawowa café Yusuf na gama had’a musu abinci yasir ya tsaya gun Tiffun wai ana bufday d’in budurwar tiffun d’in daga can Tiffun da yasir zasu wuce club

ganinsa yana girkin da d’an sanyin jiki ta shiga kantar tana kallonsa tace “mai yasa baka bari na dawo nayi ba”?

Murmushi yayi yace naga dare zaiyi ay kafin ki fita kike yi tunda kinyi lati gara nayi

d’an matsawa tayi gabansa tana shafa k’irjinsa tace “pls 4give me bacci nayi na kusa lattin aiki shiasa”…!

d’an murmushi yayi shima yana shafa fuskarta yace “kada ki damu”…!

Rik’o hannunta yayi suka fito kantar ta zaunar dashi ta koma ta juye musu jolof d’in shinkafar da naman gongoni ta kawo musu suka zauna suka fara ci…

Bayan sun gama ta kwashe kayan tana shirin shiga tayi wanka ta canza kaya ya dawo da ita jikinsa ta fad’o

d’an kallonsa tayi ta sunkwi da kai, “yace muje muyi wanka”

d’an fidda idanu tayi yayi murmushi ya dagata kamar baby suka shiga d’akin

da kansa ya zame mata kayan jikinta tanata d’an cijewa harta hak’ura zame nasa shima yayi ya k’ara d’aukarta suka shiga bayin

A bayin ma da kansa ya mata wanka tas shima yayi nasa ya k’ara d’aukarta suka fito inda cikin nutsuwa ya shinfid’eta gadon ya mata rumfa yana kallonta

itama kallonsa take dukda d’an kunyar da take ji a hankali ya fara kissing d’inta yana shafa k’irjinta

d’an d’agowa yayi yana kallonta idanunta na lumshe ya d’an lashi kumatunta kafin ya koma kissing d’inta haka dai a hankali itama ta fara tayashi inda suka tsunduma suka gamsar da junansu saidai Yusuf yana shigar yana jin d’an abu na sokinsa kamar allura ko igiyar roba saidai tsananin ni’ima da shauk’in da yake ciki na lokacin ya sashi share sukar da akanji a gabansa in yana shigarta

sosai suke manne a matse sabida k’ank’antar gadon

Can agogon wayar Yusuf ya buga 10:pm d’an d’agowa hayfa tayi cikin kunya tace “kada kayi lati”…

shafa bayanta yayi yace “kin k’osa na tafi”..?

Ah ah tace da sauri…

d’an mutmushi yayi yace IA mun kusa fara baccinmu na dare tare kamar yadda ya kamata

a hankali tace “Allah yasa”…

amin yace a hankali ya d’an d’agota ya mata peck a goshi ya mik’e zuwa bayi

Bayan ya fito wanka d’an mayafin gadon ta d’auka ta nannad’e jikinta ta mik’e ya biyoshi falo inda ya ke saka kaya sabida har lokacin komai nasu shi da yasir a falo yake

STORY CONTINUES BELOW

Yana shirin saka riga ta fito k’arasawa tayi ta karb’a rigar ta d’ora kan akwatin ta rungume shi tana jin tana shafa k’itjinsa

d’an ajiyar zuciya yayi yace “ke kika ce fa zanyi lati”

d’an d’agowa tayi cikin shagwab’a tace “to na janye maganata ka ma fasa zuwa”

d’an dariya yayi yace “wayo zakimin ke kinyi aiki ni na zauna ko”?

tureshi tayi ta matsa zata koma d’aki ya rik’o hannunta ya dawo da ita suna kallon juna.. Yace da gaske baki so na tafi?

d’an k’wallah ta fara bata bashi ansa ba..

Oh yace mai yayi zafi daga tanbaya” kalli na fasa zuwa pls ki tsaida hawayen”

d’an murmushi tayi tace a falo kuma zamu yi bacci

Yace yadda duk kika ce, haka suka juya ko rigar bai saka ba ya kaita ya mata wanka ya saka mata kayan sanyi da suck suka fito da katifa sabida sanyi yayiwa yasir test cewa Robin ya karb’a masa aiki sai shima ya maida masa gobe

Roben shi aikinsa lissafin adadin bracelet d’in da suka sayar na club Yusuf da yasir na sawa yana lissafawa tiffun kuma sakawa wanda basushan alcohol dayawa bracelet da ke controlin shansu da zasu sha ya wuce gona da iri bracelet d’in zai fara busa sai manyan club d’in su gani a computer office d’insu

Haka suka kwanta manne da juna Yusuf na bawa hayfa labarin k’anninsa da innarsa inda yake bata labarin ainihin babansa buzu ne gudun hijira kakansa yayi shi da y’an uwansa su hud’u koda suka shigo Nageria wai sai k’aramin k’aninsu ya b’ata a tashar sokoto inda su kuma suka sauka sokkoto a nan suka kafa tushe har aka haifa iyayenmu

d’an shiru yayi yana kallonta yace “ke fa kullum bakya bani labarinki..”

d’an ajiyar zuciya tayi kafin a hankali ta kalleshi yanda ya shigar da idanunsa cikin na ta tace “ni kawai mamana ta rasu tun lokacin da ta haifeni ko hr banyi ba haka naji

cikin tausayawa ya rik’e hab’arta yace “Allah ya jikanta”

Amin tace suka yi shiru kafin yace wancan momin na ki fa?

d’an shiru tayi kafin tace “Yayata ce ita ta raineni itace nake gani matsayi mamana na”

d’an shiru shima yayi sabida baima san mai zaice ba yau 8mths yana auren juna su duka basu san kusan komai ba game da junansu

Jinsa shiru taci gaba “babanmu d’aya amma ban tab’a fuskantar matsala ko bak’in y’an uba ba daga gun y’an uwana har zuwa yau

shiru tayi tana jin k’wallah domin tunawa da tayi da yadda suka d’ebi shekaru suna sadaukar da burukansu sabida gina ta, shin dukda tana tura musu kud’i in suka san Yusuf talaka ne zasu barta da aurensa kuwa

Jin shirunta yayi yawa ya d’ago fuskarta yana kallonta bai iya cewa komai ba ya kwantar da ita k’irjinsa ta saki ajiyar zuciya a hankali

Shiru ko wannensu da tunanin da yake a zuviyarsa ita hayfa tunaninta yadda zata ci gaba da aiki da Armando har su gama hidimar bud’e babban Butik a Jabi rd kamar yadda ammah tace mata in suka bud’e Butik d’in to har rayuwa IA basuda alaqa da talauci

Butik d’in akwai b’angaren kayan yara manya na waje da takalma da kayan decisions na gida da ga b’agaren saida labulaye na waje domin wai ammah zata fara shiga Dubai da China tana shigo da kaya to sun samu gurin sun fara biyan kud’in domin gurin na gomnati ne wani d’an kasuwa ya saya ya k’ara riba zai saida 130M inda ammah tuni ta bada 70M. Ajiyar zuciya yaji ta k’ara yi..  Still bai magana ba yasan a dole tana d’an damuwa da yanayin rayuwar aurensu idan yayi la’akari da nauyin da ke kansa yasa ko gidan kansu basuda suna sharing gida da aboki tabbas tayi gwaninta wajen jurewa shima fatansa yana fara aikin supermarket ya kama musu nasu gidan ko da 1room ne ba self contained ba

STORY CONTINUES BELOW

itama jin shirunsa kuma taga ba bacci yake ba ta d’ago tana kallonsa yayi nisa sosai wajen tunaninsa

d’an k’ara manna kanta tayi a k’irjinsa taji yayi ajiyar zuciya ya kalleta suka kalli junansu kusan 3mnts ta sunkwi da na ta shi kuma ya mata peck a tsakiyar gashinta da ta tufke can samn kanta suka fara bacci…

da asuba suka yi wanka tare suka maida katifa d’aki suka yi sallah tare suka sake d’an komawa kafin yasir ya iso su karya su wuce pool

Cikin baccin 6:40am yasir ya buga Yusuf ya mik’e ya d’aga hayfa kad’an domin baccin dole sai sun manne kafin su wadata da gadon rabin jikin hayfa na kan na Yusuf haka suke bacci a gadon

Yana bud’e k’ofar yasir ya saki dariya yace kaidai gaskiya kwai jababbe dama kakata na yawan fad’a wai mazan da basu cika magana fitinar tsiya garesu

Yusuf yacet kaidai bakada M zaka rage murya ko sai ka tasarmin mata daga bacci?

Yasir ya kyakyale da dariya yace yayi da kyaw ka gasa mata gajiya dole tayi bacci, ni yunwa nake ji mu karya mu wuce in yauma ba zaka aikin ba nayi gaba abina kasan kai yanzu aikin ka a gida yake sai ka gama zazzage k’warinka a gida ka kirani kana rage murya wai bakada lfiya

Yusuf baisan sanda ya saki y’ar dariya yace “Allah ya shirye ka” kuma ni a gajiye na ke matata ma haka ka shiga kiching ka taimaki kanka yana fad’a yana zama kujera

yasir ya wuce kanta ya bud’e fridge ya ga fridge d’in mak’il hayfa shekaran jiya tayi shopping babu abinda bata saka musu a fridge d’in yanzu har abinda su basuma tab’a saya ba shi da Yusuf saidai a rok’ar yasir take tace yace shi yayi shopping d’in kuma dukda haka Yusuf yayi ta fushi sai shima yaje yayi musu shopping na su detergents na wanki da etc ya tashi wanki ya wanke harda Na yasir dake washing machine ne

Naman Roba ya d’auka ya had’a musu Mushuwarnet wani abincin Italiyawa da dankalin turawa da salad da albasa da tattasai kore ya gama had’awa da sauri ya had’a musu coffee ya kawo suka karya ya shiga still hayfa na ta baccinta d’an zama yayi gefenta ya sunkuya ya manna mata peck ya furta “I love you”

a hankali cikin bacci yaji ta ansa “love you too”

d’an murmushi yayi ya k’ara mata peck a kumatu ya fito suka wuce..

2hrs bayan fitarsu itama aka zo d’aukarta a dole ta mik’e ta shirya suka wuce direct inda limousines d’in da zata d’ibesu take koda ta isa kallonta su raudha keyi ganinta sanye da atamfa gown ta d’ora abaya kai dukda shigarta kenan yawanci sun sani saidai yarinyar na basu mamaki da kullum dole sai ta nuna ita mai musulma ce mai tarbiya

Gaishesu tayi Fabiola ce da Luna suka ansa Raudha da Liliana nata iya shegensu ta shiga driver ya tayar dama ita kad’ai ake jira suka Kama hanya

Anyi show yayi kyaw ya k’watu inda aka sakawa models wandunan pencils jeas da takalmin da za suyi tallarsa takalmin yanada gashi a samansa tsawonsa ya wuce idanun k’afafuwa sosai gashi harda zip a gefensa sosai su duka y’an matan suka yi kyaw inda y’an jaridun Paris da Milan da alt america Kimora Lee Simons tazo haka taron ya tara shahararrun gidanjen d’inkunan turai

A gefe hayfa ta k’ara samun shiga sosai domin Kamfani biyar suka yiwa Armando maganarta tun ana taron inda ko b’ata lokaci baiyi ba wajen karb’ar tayinsu a matsayinsa na agent d’inta dukda Suma sun fara shirin aikinsu kuma bunil yace masa a watanni biyu masu zuwa kada ya k’ara karb’arwa hayfa wani aiki har sai sun gama nasu na Gala d’in Milan dukda dama Armando ya nemar mata alfarmar aiki da wasu sabida ta shahara da sauri kuma ta samu kud’i

2:37am anata taro su raudha na ta iya shege inda hayfa hankalinta ya gama komawa gida dukda tasan Yusuf sai asuba zai dawo domin da suka dawo pool ya iso gida ya kirata tace aiki ya musu yawa a café shiasa yaso ma shima ya biya cafén saidai baccin da yayi bayan magrib ya sashi yin latti sai 11pm ya farka da sauri ya shirya tuni yasir ya wuce

Ko kafin ya fita aiki ya k’ara kiran hayfa wayarta na ta ringing babu ansa

Ji yayi kamar ya bita café saidai tunani ya fad’o masa ya kira number ogan su na café

Oga da dama tuni Armando ya gargad’eshi sabida irin wannan ranar

Yusuf yace “khadija”

Ogan yace wani aikin contract muka samu na wani babban mutum sunata aikin za tayi dare kafin ta dawo kuma inaga bata kusa da wayanta nima bana kusa da su

Yusuf yace “OK” pls ka kula da su..

Oga yace don’t worry tana hannu mai kyaw

Yusuf yace Nagode..!

Sosai Yusuf ya k’ara tausayawa rayiwar hayfa yadda aurensa bai zo mata da sauk’i ba aiki har dare haka

Cike da tausayinta ya fara rubuta mata test

My Lovely precious amazing wyf! 

Samunki shine arziki mafi daraja da Allah yayi min ki k’ara hak’uri da yafewa mijinki halin da kike ciki na rayuwa a hannunsa, Allah yayi maki albarka. Love u

Ya kashe wayar ya wuce club saura 11dys ya fara aikin supermarket

Armando ke ta neman hayfa sabida anata interview an gamawa su Raudha duka saura ita

Ko ina ya tanbaya bata nan sai a k’arshe ya shiga d’akin kwalliya na gurin tana zaune tanata kuka ta d’ora abaya da d’an kwalinsa ta cire hular sanyin da suka yi aiki dashi

dama rigar sanyi ce doguwa har kusan gwiwa da pencil jeans da  takalmn da suka yi talansa

da sauri ya k’arasa yana tanbayarta kukan me take

Bata bashi ansa ba tayi shiru

d’an zama yayi k’asa yace khadija wai meye damuwarki kullum akayi aiki kiyita kuka maimakon farin ciki?

Kinsan nasaran da kike samu kuwa a idanun duniya saura k’iris ki fara shiga ko wani duniyar kayan sakawa banda kud’i da kike yi kamar a mafarki dukda na rasa mai yasa ma har yanzu kike zuwa café alhalin ko mai cafen yanzu bazai miki tak’amar kud’i ba domin bayan har yanzu bakida takardar k’asarnan da kin isa ki bud’e cafén da yafi nasa ma girma

Jin shiru ta kasa magana still sai kuka yace “ko iyayenki ne kike tsoro”?

A hankali ta d’ago tace ah ah

Yace to mai yake saka ki kuka bayan kud’i kike samu da wani zai rayu shekara hamsin yana aiki bazai tara abinda kika samu a watanni biyar d’in nan ba

Jin still tak’i magana yace “khadija ni kamat k’anwata nake ganinki mai yake damunki”?

a hankali tace “mijina”!

Cikin mugun mamaki ya kalleta yace “wane”?

sunkwi da kai tayi ta maimaita “mijina”

d’an kallon k’ofa yayi ya tabbatar babu mai zuwa kafin ya mik’e ya kulle k’ofar ya zauna yana kallonta yace “pls khadija gayamin gaskiya”

A hankali tace inada miji anyi mana aure daga gida Nigeria muna tare ne anan

Kama kansa yayi yace to mai yasa tun farkon had’uwarmu baki fad’amin ba?d’an ajiyar zuciya tayi ta kasa magana..+

Armando yace khadija ki d’aukeni kaman yayanki ko ma babanki domin Rashel tana kusan shekarunki

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Inaso ki yadda dani zan taimaka miki ki bani labarinki babu k’arya ko yaudara nayi miki alk’awarin rik’e sirrinki da amana sannan zan taimaka miki yadda zan iya dukda babancin addini da ke tsakaninmu

d’an shiru yayi yana jiran hayfa tayi magana..

Tunani tayi tabbas Armando yanada kirki domin tasha jin yadda su raudha ke zaginsa wai daga tsintarta yana fifitata a kansu da ya sansu tuntuni

d’an ajiyar zuciya tayi ta fara bashi labarin rayuwarsu da y’an uwanta zuwa abinda ta sani na  aurenta da Yusuf

d’an d’agowa yayi yana kallonta yace “toh ke kina son ci gaba da rayuwa da shi a haka ba tare da ya san komai na rayuwarki ba yana mijinki”?

kasa bashi ansa tayi….

Yace ni namiji ne bari na fad’a miki gaskiya idan matata bata fad’amin komai na ta duk ranar da na gane zan d’auka sona ne ba tayi shiasa

d’an shiru yayi kafin ya k’ara kallonta inda ya fahimci tana son Yusuf domin hakan yasa take ganin tana yin laifi a duk sadda tayi aiki amma gara ta gaya masa gaskiya domin ta tsarkake aurenta

Abin mamaki wanda ma ba musulmi ba yasan aure amana ce da gaskiya!

d’an ajiyar zuciya yayi yace “Na san so wani abu ne da baya buk’atar komai na duniya kafin ya shiga zukata amma kinga iyayenki da y’an uwanki na da buri a kanki sannan gaskiyar y’an uwanki idan baku had’a kai kun tallafawa zuri’arku ba haka talauci zaici gaba da yad’uwa a zuri’arku saidai a ra’ayina da kinyi magana da mijinki sabida baki san ranar da zaki daina aiki ba kuma koma kin sani ya kamata ki fad’a masa domin nan ba jimawa zaki yi shaharar da ba abin mamaki bane yana tafiya titi yaga poster da hotonki domin wannan contract d’in ma ina daf da samo miki na kamfanin wani jikan king Faisal nx yr zai saki sabon collection d’insa na abaya wanda mu ya bawa contract d’in sa na last yr

Sannan inaso ki gyara kuskuren y’an uwanki na tunanin mace ba ta d’aukaka sai da arzikin namiji sam ba gaskiya ba ne wannan dama ce Allah ya baki da zaki yi aiki tuk’uru domin kafa future d’inki da na danginki domin ina tabbatar miki ko jikokinki in kika yi aiki sosai to ba zasu yi kukan talauci ba a rayuwarsu koda mahaifinsu ba ya dashi kuma yanada kyaw kiyi aiki ki tara da kanki koda shugaban k’asa kike aure

sannan dalili na biyu maganar babu wani gidan d’inki da zasu yadda aiki da ke alhalin kinada aure domin gani za suyi hidimar aure ba zata baki damar maida hankali akan aikinki ba shiasa ko y’an mata basu yin ciki da contract d’inmu a kansu

Dalili na uku manyan mutane shahararru na duniya na zuwa taron nan karkiyi mamaki harma shahararru naku na Nigeria yaran ministoci da gomnoni da ma shugaban k’asa domin 6mth b4 collection ko wani kamfani ke fara tallan ticket d’in shiga show inda online daga k’asashen duniya a kafi saya a kan ma k’asar da ke da taron shiasa muke biyanku da tsada sabida da kud’in ticket mu ke tara mafi yawan kud’ad’e  sabida ku kama y’an k’wallon k’afa kuke

Zaki iya ganin kowa ko ki had’u da kowa sannan abu ne mai sauk’i aikinki da hotonki ya je zuwa k’asarki ko yanzu haka ansanki a k’asanshen da dama da baza ki iya tsammani ba

STORY CONTINUES BELOW

A k’arshe idan kina son mijinki zaki iya jure zama da shi a yadda ya ke abu ne mai kyaw da tushe domin mafi yawan couple da kad’an suka fara zuwa d’aukaka sannan ya kamata ya zama babu wani sirri tsakaninku

ajiyar zuciya tayi tabbas abinda armando ya fad’a duka gaskiya ne sannan ta k’ara tsorata da kada Yusuf ya san aikinta daga waje ba daga gunta ba “to amma zai barta taci gaba in ya sani”?

In ya qi ta yaya zata ci gaba da wadata y’an uwanta?

Haka dai Armando yayi ta bata magana a k’arshe yace kuma ko a wasa kada ki bari wani a kamfani yasan wannan zancen har sai kin kammala wannan contract d’in yaso ni zansan yadda zan b’ullowa bunil a sabon contract d’inki bayan wannan

Toh tace Nagode

Yace muje a kaiki gida sai munyi waya

Nagode ta k’ara cewa

Dariya yayi yace k’arama da ke kin iya soyayya ko

Sunkwi da kai tayi tana share hawaye

Yace yanzu na gane dalilin dayasa kike ajiye duk kyawtutukan da kike samu na kaya turarruka a drawer kamfani bakya kaiwa gida.

d’an sauran hawayenta ta share suka bi ta bayan hall d’in da a kayi taron har mota Armando ya raka ta driver ya bud’e mata ta shiga ya tayar

A mota sosai take ta tunanin maganganunsu da Armando tana share hawaye, ita kanta yanzu yadda take jin Yusuf kamar numfashinta har ta daina jin nauyin nuna masa ta sani idan har Ammah tasan matsayin Yusuf da kuma cewa ita take aiki don ta wadata su babu abinda zaisa ba zata raba su idan ta tuna wanda suka fi Yusuf sau 100 a arziki sun neme ta Ammah na korarsu da zimmar arzikinsu basu kai ta auri  kamar su ba shima kamal darajar Luba ammah ta rik’a kyalesu

Kuka ta saki domin tasani yanzu itama bata tab’a jin abinda take ji na Yusuf ba akan kamal kai ko rabin abinda take ji na Yusuf bata tab’a ji akan kamal ba

Kukanta take sosai tama manta da wani driver saida suka kawo gida ya mata magana harda lallashi kafin da k’yar ta fito ta masa sallama ta shiga gidan shiru ta kulle sai rigar Yusuf a kan kujera

d’an zama tayi ta d’auka rigar ta rungume a k’irjinta tana kuka sosai domin tana tunani ta yaya zata fara fad’a masa alhalin shi ya fara samo mata aiki har ya bar mata nasa dukda ya fita buk’atar aikin

Haka take zaune gurin tanata kuka kamar wacce aka aikowa rasuwa har kusan 4:30am

Yusuf da suka tashi aiki yasir da tiffun na ta lissafi sannan su tsabar son kud’i dama yawanci sai sun jira cleaners sunzo suke barin club sabida yawanci sukan tsinta kud’ad’e a club na wanda suka yi rawa ya zube

sallama ya musu ya nufo gida sabida dama haka yayi aikin duk hankalinsa baya jikinsa na rashin waya da hayfa

Koda ya iso gida har lokacin hayfa na zaune tanata hawaye duk idanunta sun kumbura hawaye duk a bushe a fuskarta sabida dama ga makeup

da sauri Yusuf ya k’arasa ya rik’ota yana tanbaya “mai ya same ki”?

d’an shiru tayi da gunjin kukan

d’ago fuskarta yayi yana kallonta itama kallonsa take duk bata cikin hankalinta

Cikin yanayin damuwa yace “wani abu ya faru da ke”?

Girgiza kai tayi alamar ah ah

Yace aikin ne ya miki yawa ko? Kin gaji?

d’an shiru yayi yana kallon shigarta yayi mamaki domin takalmin k’afarta da gani mai wutar tsada ne irin wanda ake nunawa a magazine

Saidai bai zargi komai tunawa da yayi oganta yace sunje aikin wani babba maybe a can aka basu kaya

Rik’e hab’arta yayi yace “pls drew-drop ki fad’amin abinda ya saka ki cikin wannan halin ko kinaso hankalina ya fi na ki tashi”?

STORY CONTINUES BELOW

da sauri ta girgiza kai alamar ah ah

Yace to ki daina wannan kukan sannan ki fad’amin na san laifina ne da na kaiki kina aiki babu hutu ni kaina na fiki damuwar aikin ganin yadda bakya samun hutawa sosai sannan nauyina ne na biya miki duka buk’atunki a k’arshe tsananin kishin da nake ji na ki zab’i ne kawai bani dashi na barki kina aikin kowa yana kallon min ke

ajiyar zuciya tayi domin bata ma tab’a ganinsa yayi magana mai tsawo haka ba

Saidai ta rasa ta yaya zata masa bayani kai bazan iya ba tace ta d’ago tana kallonsa cikin muryar da ta gama disashewa da kuka tace

Na dawo nagaji sai na rik’ajin kukan wani abu a waje yana bani tsoro

d’an ajiyar zuciya yayi yace ” sorry laifina ne amma saura k’iris na daina aikin kwana kinji”?

Girgiza kai tayi..

Yace pls ki k’ara hak’uri

Shiru tayi..

Mik’ewa yayi yace bari na watsa ruwa na zo yanzu ki jirani

Toh tace ya mata peck a goshi ya shiga

Sai bayan shigarsa ta bud’e jakarta tana son duba tym taga a lot call d’insa da na ammah sai msg ta bud’e ta karanta hawaye ta k’ara matsewa sosai na tausayin kanta da kuma mijinta

Kashe wayar tayi ta maida jakarta jin motsin fitowarsa ta mik’e itama ta shiga d’akin yana tsaye yana goge ruwan kansa na wanka daga shi sai boxer

K’arasawa tayi gabansa a hankali tasa hannunta ta zagaye k’ugunsa tare da kwantar da kanta a cikinsa kasancewar duk tsawonta Yusuf ya fita

Sunkuyawa yayi yana shanshana kanta ganin gyaran gashin kanta kamar wata baturiya ga k’anshi kala-kala

Sun dad’e a haka ta d’ago tana kallonsa da alamar magana saidai ta kasa

Shima bai ce mata ba ya rik’o hannunta yace “mu d’an yi bacci kafin ayi sallah

Gadon suka hau ya d’orata jikinsa ya rungume hannunsu na sark’e da ke kuwa duk a gajiyen suke nan da nan bacci ya kwashe su.

Hayfa ce dama baccin ba mai nauyi ba ne ya d’auketa ta fara farkawa jin alarm d’in wayar Yusuf

d’an bud’e idanunta tayi domin ko cikin d’an baccin mafarki tayi da maman ta bata tab’a gani ba tazo mata da fushi ko kafin ta tanbaye ta mai ya sanyata cikin fushin ta b’ace saidai kafin ta b’ace taji ta kira sunan “Yusuf”

Idanunta na bud’e amma kamar mai bacci domin motsi ma ya gagareta daga yanayin da take illa d’an mafarkin da take tariyowa har ma ta fara hawaye tunda ta zubda cikin nan sam ta kasa samun nutsuwar k’wak’walwa da ta zuciya

Hawaye ta matse a hankali tana tsoron tashin Yusuf ganin yadda yake bacci kamar jariri sosai yana buk’atar hutu

K’ara matse hawayen tayi ta d’an kama goshinta da taji kanta ya fara mata ciwo, saidai shi Yusuf tuni ya fara jin kukanta domin hawayenta mai d’umi da ya d’iga a yatsan hannunsa

a hankali ya tab’a fuskarta ya kuwa ji hawayen bai d’ago da ka kwancen ba yayi shiru shin me ke damunta da ba zata iya fad’a masa ba idan har gaskiya ne tana sonsa kamar yadda ta fara furta masa…

Saidai a hankali ya d’aga ta gefe ya mik’e ya shiga bayi kallonsa ta shiga yi domin ta gane fushi yayi da ita na ganin kukan ta yaqi k’arewa

Bayan yayi alwalan ya fito tsayuwa yayi kan dadduma zai tayar da sallah ta mik’e da sauri tace ” pls ka jirani”…!

d’an kallonta yayi ya cire kansa da d’an hanzari taje tayi alwala ta fito ya tayar da sallah..

Bayan sun idar ya shiga bayi yayi wanka tana zaune still kan dadduma ko kallonta baiyi ba ya wuce falo ya fara saka kayansa yana cikin saka takalmi ta fito a hankali tana kallonsa yi yayi kamar bai san tana gurin ba ya saka d’ayan takalmin ya d’ago zai wuce da d’an hanzari tazo ta tsaya gabansa

K’in kallonta yayi…

Pls 4give me tace..!

Still baiyi magana ya matsa zai wuce ta rungumoshi hannu yasa yana son cireta daga jiknsa Yasir ya fara k’wank’wasa musu k’ofa a hankali ta cire jiknta tana kallonsa a yayinda ya nufi k’ofa ya juyo yana kallonta alamar ta koma ciki  juyawa tayi ta shiga jiki babu k’wari

Yasir na shigowa ya kalli Yusuf yace ” yau an shirya da wuri inajin rabon da naga ka shirya haka da wuri tun kafin kayi aure

Hayfa na jinsa itama d’an hawaye ta k’ara saki tana zama gefen gado. Hayfa ce dama baccin ba mai nauyi ba ne ya d’auketa ta fara farkawa jin alarm d’in wayar Yusuf

d’an bud’e idanunta tayi domin ko cikin d’an baccin mafarki tayi da maman ta bata tab’a gani ba tazo mata da fushi ko kafin ta tanbaye ta mai ya sanyata cikin fushin ta b’ace saidai kafin ta b’ace taji ta kira sunan “Yusuf”

Idanunta na bud’e amma kamar mai bacci domin motsi ma ya gagareta daga yanayin da take illa d’an mafarkin da take tariyowa har ma ta fara hawaye tunda ta zubda cikin nan sam ta kasa samun nutsuwar k’wak’walwa da ta zuciya

Hawaye ta matse a hankali tana tsoron tashin Yusuf ganin yadda yake bacci kamar jariri sosai yana buk’atar hutu

K’ara matse hawayen tayi ta d’an kama goshinta da taji kanta ya fara mata ciwo, saidai shi Yusuf tuni ya fara jin kukanta domin hawayenta mai d’umi da ya d’iga a yatsan hannunsa

a hankali ya tab’a fuskarta ya kuwa ji hawayen bai d’ago da ka kwancen ba yayi shiru shin me ke damunta da ba zata iya fad’a masa ba idan har gaskiya ne tana sonsa kamar yadda ta fara furta masa…

Saidai a hankali ya d’aga ta gefe ya mik’e ya shiga bayi kallonsa ta shiga yi domin ta gane fushi yayi da ita na ganin kukan ta yaqi k’arewa

Bayan yayi alwalan ya fito tsayuwa yayi kan dadduma zai tayar da sallah ta mik’e da sauri tace ” pls ka jirani”…!

d’an kallonta yayi ya cire kansa da d’an hanzari taje tayi alwala ta fito ya tayar da sallah..

Bayan sun idar ya shiga bayi yayi wanka tana zaune still kan dadduma ko kallonta baiyi ba ya wuce falo ya fara saka kayansa yana cikin saka takalmi ta fito a hankali tana kallonsa yi yayi kamar bai san tana gurin ba ya saka d’ayan takalmin ya d’ago zai wuce da d’an hanzari tazo ta tsaya gabansa

K’in kallonta yayi…

Pls 4give me tace..!

Still baiyi magana ya matsa zai wuce ta rungumoshi hannu yasa yana son cireta daga jiknsa Yasir ya fara k’wank’wasa musu k’ofa a hankali ta cire jiknta tana kallonsa a yayinda ya nufi k’ofa ya juyo yana kallonta alamar ta koma ciki  juyawa tayi ta shiga jiki babu k’wari

Yasir na shigowa ya kalli Yusuf yace ” yau an shirya da wuri inajin rabon da naga ka shirya haka da wuri tun kafin kayi aure

Hayfa na jinsa itama d’an hawaye ta k’ara saki tana zama gefen gado.

A falo Yasir ya kalli Yusuf yace “ni fa yunwa na keji”…

Yusuf yayi d’an ajiyar zuciya yace kayi kai kad’ai ni bana jin cin komai

Yasir ya ce OK nima ba dayawa zan ci ba ya shiga kanta zai fara aikin girkin hayfa ta fito da d’an murmushi kad’an ta gayar da Yasir  ya ansa Yusuf kamar baya gurin don ko kallon inda suke baiyi ba

A hankali tace bari na had’a muku….!

Yasir ya kalli Yusuf kafin yace no ba komai nagode ki barshi nima bread kawai zanci….

Cikin nutsuwa tace “bari na had’a muku wani abu sai ku tafi da shi..”

Yusuf dai kamar baya gurin Yasir ya fito kantar ta shiga

Zama yayi kusa da Yusuf ya bud’e data ya shiga duniyar Media

A kanta hayfa ta fitar da sardines ta tafasa taliya ta juye ta yanka vegetables da albasa ta saka maggi da kayan k’ashi ta d’an saka ruwa kad’an ya tafasa ta zuba taliyar kafin ta juye babban gwangwanib sardines irin na turai ba namu k”ananan gwangwani ba

Bayan ta gama ta juye musu ta nad’e kafin ta had’a musu coffee da bread da butter

A hankali ta jera musu gabansu tana satar kallon mijinta da sam yayi kamar baisan tana gurin ba²²

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]