[Advertisements⬇️]

KASAR WAJE CHAPTER 6 BY MARYAM DATTI - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

KASAR WAJE CHAPTER 6 BY MARYAM DATTI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wanka ma yayi ya maida dogon wandonsa ya fito falo akwatinsa ya d’auka riga hayfa ta shigo+
Kallon juna suka tsaya yi inda hayfa har wani gauron numfashi taja ganin cikakken namijin a namijinsa
d’an kama kanta taso yi amma tuni Yusuf ya harbo jirginta ya fara k’arasawa gabanta ta sunkwi da kai
Janyota kawai yayi ta fad’o jikinsa ta saki wani marayan ajiyar zuciya ya d’ago fuskarta ya saka idanunsa cikin nata ji tayi tsigar jikinta na wani fitinannen tashi, bakinta ya kama ya lalubo harshenta take ta kama nasa itama domin dama haka suke da yayi mata abu sai ta kwaikwaya tayi masa shima tun da ya gane haka sai ya shiga koyar da ita ta haka shima a internet yake shiga ya koya wani ma a wayar yasir zai shiga yayi karance-karancensa na koyan saduwa ya gama ya share komai ya maidawa yasir wayarsa

Ganin yadda suka d’auki zafi da junansu a tsayen ma tuni ya sab’ulewa hayfa gown d’in jikinta sai pant da bra
Kwantar da ita yayi a falon inda ya zame dogon wandon sa sai boxers suka koma tuni ta k’ara mak’ale shi
shima dai hidima ya fara mata kamar yadda ya gane a y’an kwanakin nan tana so

Komai yayi mata ta rama masa abin dai babu wani sauk’i kamar ba yara k’anana ba su duka yadda suke jin santin abin har yatsun k’afafuwansu
Haka dai suka zuk’e junansu tas kamar yadda yanzun ya zame musu jiki
Suna kwance gurin ita hayfa da gajiya ma tabar café amma jaraba ya hanata jin gajiyar sai bayan da buk’atunsu ya biya ta samu bacci inda Yusuf ya daure ya mik’e yaje yayi wanka ya shirya yazo ya zauna yana kallonta kusan 5mnts yana jin kamar ya zauna su k’arasa baccinsu har safiya saidai a dole ya mata peck a goshi ya nufi club

hayfa sai kusan 5:am ta farka da k’yar ta wuce tayi wanka tayi sallah tana zaune kan dadduma duk tunani ya isheta

A club ogansu Yusuf na club yayiwa Yusuf tsiya sabida an aiki yasir hakan ya jawo aka gano lattin Yusuf inda ogan yace sai Yusuf ya maida masa 3hrs d’insa a aikin yau ko ya yanke a kud’insa
Ma’ana Yusuf maimakon 10:pm da suke zuwa aiki dole yaje 7:pm Yusuf yace babu damuwa zai maida
da safe yasir ma daga club su duka suka wuce pool
Hayfa da bacci ya d’an fara d’ibarta kan dadduma tayi mamakin rashin dawowar su Yusuf yau har safe taji wayarta na ringing da d’an hanzari ta fito da tunanin ko Armando ne

Jin muryar Yusuf ya mata sallama

Wani ajiyar zuciya tayi tare da jin wani irin yanayi da wani abu yana zagaya mata jiki
A hankali ta ansa sallamar
Yace kin tashi lafiya?

Eh tace…

Yace pls kiyi hakuri nayi latti jiya yau bama zan dawo gida ba sai asuba gobe IA

Ajiyar zuciya tayi tana son tanbayarsa why ta kasa

Yace ki kula da kanki za muyi ta waya

Toh tace….

A hankali yace zanyi kewarki…

d’an shiru tayi kafin ta tsinci bakinta da cewa nima haka…

Ajiyar zuciya yayi sosai yaji dad’i saidai hayfa tana fad’ar haka ta kashe wayar sabida kunya da taji da haushin kanta…

STORY CONTINUES BELOW
Kallon wayar yayi yayi murmushi.
Haka ta zauna itama kujerar cike da tunanin yanayin sabuwar rayuwarsu da Yusuf… Tana cikin tunanin aka fara mata nucking
Da sauri ta mik’e ta koma d’aki ta cire hijabin sallah ta yane kanta da mayafi ta d’auka jakarta ta fito ta kulle k’ofa driver na kamfanin ya bud’e mata mota suka wuce

A kamfanin suka yi break tare da duk wasu ma’aikata y’an fashion parade d’in kamar ita na kamfanin

Saidai yau tanata kamewa ganin yadda raudha ke kallonta har suka gama aka kwashesu a babbar motar models na kamfanin suka nufi inda za a yi fashion parade d’in

A wani babban daji ne mai tsinannen sanyi da bishiyoyi da duwatsu farare masu kyaw
A nan masu yi musu gyaran gashi suka fara inda sosai aka samu matsala da hayfa ganin wani k’aton namiji ne wai zai tab’a mata gashi

Rarrashinta Armando yayi yace daga wannan zaiyi arrangement na cewa ko wani parade mace za ta rik’a yi mata gyaran
Da haka hayfa ta hak’ura aka yi mata gyaran gashin tayi kyaw na tsiya inda aka musu simple makeup aka fara shirya su
Kayan sanyi ne y’an ubansu gashi manyan mutane duk sunzo irin royale families na turawa suisse, Thailand, England, dadai wasu masu kud’in turawa da celebrities

Hayfa tasha wani rigar sanyi dogo ya wuce gwiwarta an saka mata lagging a ciki fari mai safa da wani takalmi mai gashi tayi mugun kyaw

Haka aka fara parade d’in inda ba’azo kan hayfa ba duk ta gama tsorata dukda tasha tranning saidai tanata tunanin Yusuf ne
A haka aka iso kanta shiru bata fito ba kusan 10mnts y’an jarida har sun fara tsegumi bunill ya Kalli Armando

Armando ya mik’e ya shiga tana zaune tayi shiru idanunta cike da k’wallah
Armando yace pls Queen kiyi hak’uri ki fito a gama daga baya zamu yi magana yanzu mutane na jiranmu

Hawaye ta k’ara saki
A dole ya zauna ya lallasheta da k’yar ta goge hawaye aka k’ara gyara mata makeup ta fito ta fara
Mugun tafi aka fara y’an jarida na ta hoto manyan sauran masu kamfanonin d’inkuna kuwa kallonta suke suna ayyana dole suma suyi aiki da wannan angel beauty d’in
Haka tayi nata zagayen ta shiga
Kafin aka k’ara canza musu kaya raudha na ta kallon hayfa takaici ya isheta da alama yarinyar ta shigo duniyar d’inki da k’afar dama

Haka suka k’ara zagaye suka k’arayi kusan sau hud’u suka canza kaya.  Duba wayarta tayi taga miss call biyar na Yusuf biyu na Ammah cikin tsananin fargaba ta k’ara matsawa nesa da gurin saida ta tabbatar babu hayaniya kafin ta jefa kiran Yusuf
Yusuf da shima sunyi busy sosai wajen aiki sunata sanyawa masu shiga club bracelet wanda ke nuna mai shigan adult ne gashi wayarsa na silence har ya tsinke baiji ba

Hayfa ta maida wayar jakar ta mik’e ta koma cikin gurin taron anata sha’ani inda su raudha wai su sunma tafi club can zasu kwana

Armando na ganin hayfa ya k’araso yace yaya dai Queen? d’an rage kallonsa tayi tace zan koma gida ne

d”an juyawa yayi ya kalli gurin duk an ragu yace “OK”  gobe mu jirgin safe zamu bi zuwa Paris mun samu orders sannan akwai hira da za muyi da y’an jaridun can akan ki

Ajiyar zuciya hayfa tayi ba tace komai ba…

Yace yawwa kud’inki ta wannan account na Nigeria zan tura?

STORY CONTINUES BELOW
“Eh” kawai tace
Yace OK zamu rik’a waya sannan zaki ci gaba da zuwa gym saidai yanzu bayan ko wani 3dys ne zai rik’a zuwa d’aukanki kafin mu gama aikin sabon project d’inmu sannan akwai contract da na ansar miki na tallan takalman da kika saka yau a taro amma ba mu gama yarjejeniya da mai kamfanin ba sai na dawo Paris

Hayfa tace OK duk hankalinta ya koma gida
Armando ganin haka yace “bari na kira driver zamu k’arasa magana gobe ta waya
Nan driver yazo suke wuce gida duk hankalinta ya gama barin jikinta har suka iso
Driver ne ya bud’e kafin ta farga ta fito ta bud’e gidan babu kowa ta shiga
Zama tayi kujerar falon tayi shiru gashi ko magrib da ishaa bata yi ba mik’ewa tayi ta shiga tayi alwala tazo tayi sallah tana zaune kan daddumar tanata tunani har bacci ya kwasheta

Yusuf da yasir na ta aiki grp d’insu raudha suka iso ita da Liliana da Fabiola sunsha mini gown driver na bud’e musu mota k’ofar club d’in yasir da Yusuf suka shagala kallinsu
Yasir ya kalli liliana ya had’iyi yawu sabida tsabar cikar k’irjinta, Itama kifta masa idanu tayi suka k’arasa gurinsu yin register shiga club d’in saidai wani sabon fitina raudha na d’ora idanu kan Yusuf taji wani mugun sonsa ya shigeta
Cikin salon yaudara da jan hankali ta mik’a masa hannu zai saka mata electronic bracelet d’in da yake nuna mai shiga club d’in adult ne

Cire idanu Yusuf yayi yana mak’a mata da gangan tayi kamar zata fad’a jikinsa ya kauce yasir ya fashe da dariya yayinda shima ya gama sakawa liliana da fabiola inda liliana ta tura masa katinta a aljuhu suka shige club d’in Yusuf kuwa da k’yar ya kora raudha da ke ta iya shege don taja hankalinsa dukda daga Yusuf har yasir sun saba da y’an mata suyi ta fitinarsu in suka zo saka musu bracelet d’in wannan dalilin yasa Yusuf ke son barin aikin dukda aikin yama fi pool basu kud’i

Bayan shigarsu raudha yasir ya kalli Yusuf yace wannan yaran da ganinsu basu ji kuma da alama masu kud’i ne kayan jikinsu designed ne

Yusuf yayi tsaki yace kai muyi ta addu’a Allah ya raba mu da aikin nan lafiya amma gsky akwai matsala a aikin

Yasir yace amin amma fa blond d’in tamin gsky ko ba harka in ta nemi mu jone na b’ata lokacina ya kiftawa Yusuf idanu

Yusuf yace kai ka sani dai
Suna cikin hirar shima driver ya fito mota ya k’araso gun su Yusuf suka gaisa ganinsu Yusuf musulmai ne ya gabatar musu da Kansa

Ni sunana Zakir d’an Qatar
Yasir yace ni sunana yasir d’an uwana Yusuf..

Zakir yace OK ni na kawo wannan yaran zan iya zama tare da ku na jira su?

Yasir yace babu komai bisimilla

Nan dai hira ta b’arke tsakanin yasir da zakir shidai Yusuf kamar baya gun tunani ya dame shi ko hayfa bata da lafiya ne.  Yana ta kiran layinta ba ansa can yaji zakir na bawa yasir labarin su raudha cewa ay su models ne

Yasir yace kuma ita raudha musulma ce?

Zakir yace sosai ma iyayenta y’an Pakistan ne amma suna zaune India

Yasir yace tab Allah ya kyawta kuma da saninsu take wannan rayuwar?

Zakir yace ay shi aikin model dama ko turawa masu tarbiya basu barin yaransu yi dukda kud’i da aikin ke kawowa sosai kasan su kamar y’an k’wallon k’afa suke

Yusuf da gaba d’aya yanzu hankalinsa ya k’ara komawa kan hirar yasir da zakir nan yaji tsanar raudha ta rasa aikin da za tayi sai yad’a kammaninta a duniya don yiwa Allah butulci.  Zakir yace saifa kaga wannan zagayen sau d’aya kawai in suka yi da kaya y’an jarida da manyan mutanen duniya na kallonsu ko waccensu a biya ta kud’in da wani ma’aikacin zaiyi shekara goma yana aiki bai tara ba

STORY CONTINUES BELOW
Yasir yace tab shiasa yawanci za kagansu sun zama y’an k’waya ay ina ganinsu a E news ana nuna su

Hira dai sosai tsakanin yasir da zakir kamar sun shekara da sanin juna

A cikin club raudha da liliana na zaune kantar shan alcohol fabiola na can ta had’u da wani shege sunata rawar tsiya

Liliana ta kalli raudha tace gaskiya gayun nan sun had’u diba d’ayan kamar Suarez da mu kayi aikin last yr dashi a Milan kyawunsu da tsawonsu d’aya kawai banbancin fata

Raudha taja numfashi tace “ni ay na samu saurayi 4lyf in na sameshi zan kori duk su Antonio da Fabien
Liliana ta Saki dariya kai k’awa haka kika fad’a?

Raudha tace da gaske kuma indai muka fahimci juna har aurensa zan iya

Liliana tayi dariya tace banga laifinki ba gaskiya ya had’u fa, amma da alama baida abubuwan kashewa fa

Tsaki raudha tayi tace to sai me ni ba sai nayi ta aiki ina tara mana ba

Dariya sosai liliana tayi tace ay kuwa kinga yanzu muje mu d’anyi rawa lokaci ya tafi fa

Raudha tace no ni rawar ma ta fita kaina bari naje na ganshi sai kun fito

Liliana tace “ok” raudha ta fito

Zakir na ganinta ya mik’e yace “ranki ya dad’e wani gurin zan kaiki”?

Tsaki tayi tace ka koma mota kawai ina zuwa
OK yace yayiwa su yasir sallama ya koma mota

d’an kallon yasir tayi tace “pls zaka iya bamu mintina zanyi magana da d’an uwanka”!

Yasir ya kalli Yusuf yace “OK” zai tafi suka ji muryar Yusuf

…ki fad’a ko meye a gabansa tare kika ganmu ay
d’an shiru tayi kafin tace “pls dama number ka nake so”!

Yusuf ya kalleta cikin k’ask’anci yace wani dalili ni kuma zan baki?

d’an shiru tayi kafin tace zan maka bayani in na kira
Tsaki yayi yace “to bazan bayar ba”!

Kallonsa yasir yayi kafin ya kalli raudha yace “kije za muyi magana da shi sai ni na miki magana IA”

Ta dad’e kafin taja jiki ta wuce mota ta zauna ranta duk a jagule

kallonsa yasir yayi yace ka sani ko aiki zata baka?

Yusuf yace wannan ay iskanci ne daga ganina yaushe ta sanni har zata bani aiki?

Yasir yace amma fa haka ne tun kana saka mata bracelet naga iya shegen da take yi

Nan dai suka watsar da zancen suka shiga hirarsu ta rayuwa

A mota tunani ya fad’owa raudha ay gama hanya mai sauk’i da zata cusa kanta gun Yusuf tunda tagansu suna hira da zakir da shi za tayi anfani amma ba yanzu ba sai an kwan biyu sun manta ma abinda ya faru yau

Haka 5:am su liliana suka fito club da gangan ta fad’i jikin yasir tsabar iskanci tana shafa masa d’uwawu Yusuf ne ya janye yasir d’in da shima har ya fara lumshe idanu
Haka ta wuce tana sakarwa yasir murmushi tana kifta masa idanu shima dai haka
Suna shiga ita raudha bacci ma tayi a motar zakir ya tada suka wuce

Koda su Yusuf suka tashi club yasir shiga yayi d’akin ma’aikata yayi kwanciyarsa kafin cleaners suzo yayiwa Yusuf sallama sai sun had’u pool

Yusuf yana shiga gida sosai yayi mamakin ganin hayfa kan dadduma a falo tana bacci da d’an saurinsa ya kulle k’ofar ya k’arasa gurinta

Ganin ko kayan bacci bata saka ba yayi mamaki ga wannan dank’ak’areren abaya na nunawa duniya a jikinta

Dama k’aidar gidajen d’inkunan duniya ne bayan an gama fashion parade suna bawa y’an matan damar zab’ar kayan da ransu ke so domin dinner ko reception na taron inda ita hayfa ta zab’a wannan abayar ta collection d’in Marwan bn Faisal Fation na saudiya abayar kud’inya ya kai $10000
Saidai Yusuf ya cire mamakinsa tuna hayfa y’ar manya ce tazo da kaya har 15akwati da baima san ko kwatan kayanta ba

d’agata yayi ya d’ora cinyarsa yana kallonta inda tayi wani fitinannen kyaw ga wani k’anshi na tashi jikinta ga gashinta yasha gyara shima sai k’anshi yake

d’an murmushi yayi maybe taji yin gayu ne abinta tayi
Itama hayfa hannunta da ya gogu da na Yusuf ya sata d’an bud’e idanunta inda suka fad’a cikin na sa

Ajiyar zuciya ta d’anyi ta k’ara bud’e idanun still yana kallonta

d’agota yayi suna kallon juna inda ya fara shafa fuskarta, lumshe idanunta tayi tanajin wani abu na ratsa mata duk ilahirin jikinta
Kallonta yake yadda ta lumshe idanun
d’ora bakinsa yayi kan nata kamar tana jiransa ta kama nan suka fara aikin na su

Inda ya zare mata abayar tsayawa yayi yana kallon wani matsiyacin bodysuit mai bra da pant dake jikinta wanda shima duk cikin kayan da aka basu ne a parade
Kamar wawa haka ya fara shafata inda ta k’ara bank’aro masa jikinta sosai yana shafawa

Haka dai suka luntsuma suka fara aikin da suka saba sosai suka kwashi junansu Yusuf wani irin surfa yake mata ita kuma tana k’ara bashi had’in kai har suka isa inda suke so kafin suka kwanta shiru a gurin gashi an fara sallah

da k’yar shi ya fara tashi yaje yayi wanka ya fito da kansa ya d’agota ya raka ta har bayin ya zauna gefen gadon jiranta ta fito suyi sallah

Suka yi sallah ba damar yin bacci Yusuf yace zai had’a musu break tace ita ba yanzu ba

Zama yayi kusa da ita yana kallonta yace “IA kin kusa daina aikin café da zarar na kammala wani abu kinji”?

d’an kallonsa tayi ta sunkwi da kai…

Rik’o hannunta yayi yace ” kina cikin mayan burukuna na rayuwa ba na fatan rasa ki pls kiyi hak’uri da yadda muke IA ba zamu dawwama haka ba kinji”?

Kuka ta saki sosai

Shiru shima yayi yana tunani tare da fatan bud’i a rayuwarsa+
a hankali ya d’ago fuskarta yana kallonta yace “pls kada ki tab’a nadamar aurena IA ko bani da komai samunki a rayuwata babban arziki ne”

Hawayen dai take still inda cikin dakiya ta fad’a k’irjinsa inda shima ya k’ara rungume ta sosai

Kusan 5mnts ta d’ago daga jikinsa kanta na k’asa rik’o hannunta yayi yace “zanje aiki amma IA zan dawo da wuri na raka ki aiki”!

Ya mik’e tana zaune yanda take kanta na k’asa peck ya mata a tsakiyar kan ya fito d’akin shima bai karya ba ya wuce.

Tunda ya fita still hawaye take sosai ta fara jin tausayinsa da yadda kula da ita dukda rashin wadatarsa
Haka ta kwanta shiru tana kwance ne taji wayarta na ringing ta mik’e ta bud’e jakar ta d’auka
da sauri ta ansa ganin ammah ke Kira

Mominmu kuna lafiya? shekarn jiya muna magana wayar ta katse netwok, Ammah tayi d’an murmushi tace “yaya kuke y’an matana ya mijinki”?

Hayfa tace lafiya mominmu, ya daddy?
Ammah tace yana lafiya yana gaisheki Adda suwaiba tace shekaran jiya kin kirata ko?

Hayfa tace eh…

Ammah tace komai lafiya dai ko?

hayfa tayi ajiyar zuciya tana son fad’awa ammah maganar aikinta yadda take samun kud’i saidai sam yanzu yadda ta fara jin kusanci da Yusuf ba tason yin wani abu da zai kawo musu sab’ani cikin rayuwarsu domin ta tabbata in ammah tasan shi talaka ne dole su rabu
Ammah ce ta dawo da ita daga tunaninta “amma inaso ki k’ara kulawa kinga yadda yake mana hidima daga aurenku ko shekara ba kuyi ba ki rik’a masa biyayya komai yake so kinji?

Hayfa tace “toh”

Tace kuma komai k’ank’antar matsala in kikaga yafi k’arfinku ki fad’amin sabida na nema mafita da wuri kafin wasu su shigo ciki su ruguza muku rayuwa
Hayfa dai shiru tanata sauraro

Ammah tace “ya maganar karatu kunyi? Yaushe zaki fara?

Hayfa tayi ajiyar zuciya saidai ta kasa magana
Ammah tace shikenan kada ki takura masa ki k’yaleshi wata k’ila so yake sai kin k’ara hutawa kin saba da k’asar tukuna, ki maida hankalinki ki rik’a kula da mijinki kinga dai yadda na keyi da daddynku shi da ma baida komai amma ina bashi duk hakkokinsa na miji komai yace nayi yi nake komai yace na bari bari nake sabida Mace daga zarar tayi aure mijinta shine duniyarta da lahirarta dukkan wani iko na rayuwarta yana hannunsa koda mijin baida komai bare wanda yake maka hidima ba sassauci babu bak’in ciki, sabida kinga wani mijin bazai sauke maka hakkinka da ke kansa ba sannan kuma bazai barka ka nema ka yiwa kanka ba, ina matuk’ar farin ciki da yadda Allah ya baki wannan mijin na ki gashi da tarbiya domin baya 3dys bai kirani ko yayimin text na gaisuwa ba
Tunda ammah ta fara magana hayfa ke hawaye
Ammah taci gaba kinga yadda mukaita wahalar rayuwar aure ni da Adda mu yiwa kanmu da yaranmu amma mu ka hak’ura muna zaune domin munsan ko ta hanyar waye wata rana Allah zai canza mana rayuwa gashi yanzu Allah ya canza mana ta dalilinki, don Allah y’an matana ki rik’e mijinki kinga tun baku je ko’ina ba rayuwarmu ta fara canzawa kada ki tab’a yadda wani abu da zai kawo rabuwa tsakaninku ya gitta kinji?

STORY CONTINUES BELOW
Cikin kuka hayfa tace “toh” domin ta rasa mai ma za tace, Ammah taci gaba ki ta addu’a Allah ya sanya miki son mijinki nasan baki sonsa lokacin aurenku amma karki manta kyawtatawa na janyo soyayya sannan kyakykyawa ne matashi ne cike da k’uriciya ya ma fi kamal kyaw nesa ba kusa ba kin sani kiyi k’ok’ari ku zauna lafiya kinji…?

Hayfa tace “toh” cikin kuka, haka ammah taci gaba da yi mata nasiha inda ammah tace “ina tunani nan zuwa wani lokaci mu bud’e wani gurin sana’a mu zuba y’an aiki ana tara miki kud’i kinji”?

Hayfa cikin kuka tace “toh” kawai
Haka suka dad’e kafin suka yi sallama ta kashe wayar

Ammah ma tunani ta d’an fad’a malam yace zai sanya yawan sha’awa taakaninsu domin su rik’a yawan samun kusanci amma soyayya sai in su da kansu suka ji sun da son junansu, ga hayfa da bak’in jiji da kai tace
Allah yasa su so junansu tace tana shafa addu’ar a fuskarta

Tunda suka gama waya da ammah take kuka tabbas tana cikin tsaka mai wuya domin ita kanta yanzu wani irin jin Yusuf ta fara yi a rayuwarta

Tanata kukan kiran Armando shima ya shigo ta dad’e kafin ta goge fuskarta ta d’aga yace “congratulations Queen”!

Tayi ajiyart zuciya…!

Yace ya gajiya? Albishirinki wannan kamfanin takalman d’azu ya kirani muna airport ya baki contract na talakman sannan da wandon takalman shima collection d’in summer ne don haka nan da 5dys zakiyi aikin sannan kud’inki $50000 sai na aikinmu 50000 shima yanzu zan tura miki $100000
“Toh” tace..! Yace dana dawo jibi zamu fara aikin wancan mutumin
“Toh” ta k’ara cewa suka yi sallama…

Tana zaune gurin yunwa take ji amma ta kasa tashi tana tunanin yadda zata ci gaba da aiki ba tare da Yusuf ya tab’a sani ba

da k’yar dai ta mik’e taje ta gasa bread ta had’a tea ta karya kafin ta fara gyaran gidan aiki tayi sosai ta gyara gidan ko’ina ta kunna turaren wuta sai k’anshi

Ammah na office tana marking litattafan d’alibai taji shigowar msg ta d’aga wayar saidai mugun mamaki ne ya baibayeta sosai ta d’an cire glass ta murza idanunta
Tabbas kud’ine 43M daga hayfa domin d same information da kud’in da ta turo rannan tsabar mamaki ta ajiye biron hannunta ta shiga neman lamba saidai tama rasa wa zata kira
Tunani tayi tab wani irin kud’i Yusuf ya gada haka, saidai tace d’an Nigeria tara kud’i a gunsa ba komai bane haka kashe kud’in domin a Nigeria ne za kaga mai kud’i ko d’an siyasa budurwarsa ma ya bata kyawtar millions ba komai bane bare matarsa kai na gode Allah da ya cikamin burina “Allah ka k’ara had’a kan hayfa da Yusuf”!

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Da wannan farin cikin taci gaba da tunani dama sai nx mth zasu tare sabon gidansu sabida gyare-gyare da akewa gidan game na Adda suwaiba ana nema tukuna kuma tafi so su tare kabala tare shima daddyn yara sai nan da 3mths zasu fara registration na course d’insu
Tunani tayi taga wani makeken gida a Kuse rd nan dai kabala kusa da gidan Sanata shehu Sani bari ta kira agent taji nawa ne gidan sai ta sayawa su goggo yaso da sunan hayfa yadda hakan zai zama ta fara Tarawa itama hayfa kadarori
d’aukar wayarta tayi ta jefa layin agent d’in tayi sallama

Ansawa yayi yace hajiya kiyi hak’uri kinjini shiru wlh a kabala yanzu gidaje darajarsu kullum k’aruwa take shiasa har yanzu ban samu na y’ar uwarki ba
Ajiyar zuciya tayi tace babu komai ba ma wannan yasa na kiraka ba,
Yace “OK”..
Tace gida nake so babba amma
STORY CONTINUES BELOW
Yace kamar na nawa?

Tace 25M ko 30M
Mugun ajiyar zuciya agent d’in yayi gaskiya yana farin cikin had’uwa da hajiyarnan
Yace a wace unguwa? Domin akwai wani gida nan kabala kuse rd shima 32M  ake so kuma hajiya wlh gidan yakai 35M kawai an rage ne gidan Ali gusau ne wani yaronsa mara jin magana zai saida
Ammah tace OK to kaje Ku shirya mu had’u 3:pm na biya
Yace to ranki ya dad’e Allah ya k’ara girma
Murmushi tayi tace kaima zan maka saqo yanzu….!
Yace godiya nake hajiya Allah ya qara arziki suka yi sallama

Tunani ta fad’a in suka je taga gidan sai Adda suwaiba ma sai a nema mata na koda 7M haka dai ta fara tunane-tunanenta da lissafi kamar ko yaushe gashi sun biya bashi kaf sun ansa takardun gidansu dukda shima saidawa za suyi da wannan tunanin ta mik’e ganin an ma kusa tashi ta nufi gidan iyayenta inda ta kira babansu tace masa tana zuwa akwai magana sannan ta kira suwaiba tace su had’u can

A gidan tana parking suwaiba ma na fitowa daga napep suka d’unguma gaba d’aya cikin gidan

Bayan sun gama gaisa da iyayensu ammah ta kalli iyayensu tace “Abba dama hayfa ce ta turo da kud’i shine zan saya muku gida babba a maimakon yadda da zaku koma gurina kafin a samu k’arami
Babansu ya kalleta yace toh madallah Allah yayi mata albarka da ku duka ya qara musu zaman lafiya da mijinta

Amin duk suka ce…

Ammah tace Abba ko kanada shawarar yadda za’ayi daban?

Mutmushi yayi yace duk yadda kuka yi daidaine nan kuka rik’eta kuka yi mata komai sai yanzu ne don ta samu d’aukaka zan karb’i ikonta? Allah yayi muku albarka kinji ku tsara komai yadda kuke yi

Ammah tace to Abba kafin ku tare gidan zan biya muku umrah kuka dawo bayan sallah sai kawai ku tare gidan

Suwaiba tace hakan yayi sosai
Goggo tace kai masha Allah, Allah yayi muku albarka

Suka ansa amin nan dai ammah ta fad’a musu yadda ta tsara komai sannan su duka kabalan zasu tare
sun dad’e kafin suka yiwa iyayensu sallama suka fito a hanya ammah na tuk’i suna hira domin sosai kansu yake had’e su duka basu sakin jikinsu da kowa sai da junansu har itama hayfa haka ta tashi yadda taga suna yi

A gidan suwaiba suka ci abincin rana suka yi sallah kafin tare suka kama hanyar ganin gida

Suna kan s/range agent d’in ya k’araso suka bi motarsa a baya dama ammah ta masa transfer na 100k tace yasha mai

Gaskiya gidan ya had’u baida mugun girma amma ya had’u domin mai saidawa saida ya gyara komai kafin yasa kasuwa
Babban main house ne a gaba da an bud’e gate ayi tafiya kad’an sai sai BQ. a can baya d’akuna uku da bayi biyu yadda dai aka san BQ a gidajen masu kud’i
k’ofar gaban shiga falon duflet 5bdrms ne a sama sai 1single room da toilet a k’asa sai babban makeken falo da dinning kusa da kiching da stor sai sama d’akunan ko wanne da bayi sai d’an falo a saman da corido da babban balcony gidan dai masha Allah yayi inda ammah babu b’ata lokaci tace ta karb’a aka agent ya kira wanda gidan ke hannunsa da lawyoyi aka cike komai ammah da sunan hayfa ta cike komai ta biya aka bata makullanta dukda tanajin sai an can za mata pentin gate d’in suka yi sallama da agent inda tace masa zata kirashi akan wancan na 3M ya barshi ya nemo na 7M

cikin farin-cikin yadda kwanan nn yake ci a jikin ammah yace yanzu ma zan bazama nemo miki IA
OK tace suka yi sallama suka shiga mota ita da suwaiba inda take fad’awa suwaiba cewa zasu saya babbar sienna wacce zata rik’a kai yaransu makaranta su duka da nata da na suwaibar domin zata maida yaran duka essence international
Suwaiba tace toh haka yayi Allah ya k’ara dafa mana, amma kinsan mai nayi tunani?

Ammah na tuk’i tace ah ah

Suwaiba tace mu nema abinda zamu zuba jari sabida muna juya kud’i kinsan babu abinda yake dawwama ma’ana yanzu kinga suna amarci ne shiasa yake ta sakar mata kinga koda daga baya baya sakar mata dayawa munsan mun samu matsaya
Ammah tace gaskiya ne nima nayi tunanin amma ni da nace mu yita sayan gidaje muna zuba haya kinsan gidaje na bada kud’i a kaduna sosai bare irin wannan eriyar ta kabala da haya ke da tsadar tsiya

Suwaiba tace to in haka ne mai zai hana ku tare wannan gidan ke da su goggo kinga shi kansa BQ d’in qato ne kalla d’akunan manya wlh ya ishesu har yayi yawa tunda komai akwai, Sannan ko rabin BQ d’in gidanmu na badarawa bai kai ba sannan karki manta sa’idu d’an uwanmu ne ko ba ke yake aure ba shi mai ajiye su goggo ne gidansa bare muma zaifi sauk’ak’a mana kula da su
Sosai maganganun suwaiba suka shigeta inda ta kalli suwaiba tace to Adda in haka ne ke kuma sai ki koma inda zan koma yaso wanda za a samo sai musa haya kuma kinsan daddy yara ya ce nayi furniture da kud’in gidanmu na kawo sai nasa agent ya nemo gidan koda 10M sai musa haya
Suwaiba tace yayi nan ma suka wuce gurin shu’aibu inda suka saya sienna suka biya aka gama komai amma zata d’auka driver da masu aiki biyu babba da k’arama sannan suka wuce gurin mai funuteres ammah ta canza kujeru zuwa kunerun 1.200 da dinning 500k da carfet goma dadai kaya over duniya sabuwa suka nufo gida kusan magrib sai bayan sunyi sallah laraba raka suwaiba ammah ta bata ATM ta d’auka mata drop napep ya kaita gida dama ammah ta bud’e mata account a first bank ta zuba mata 3m a ciki banda kayan funuteres da hidimar yaranta da ammah tace yanzu komansu na hannunta gobe za taje ta gama musu komai na komawa essence dukda surayya saura 3yrs ta gama secondary…

Bayan tafiyar suwaiba amma ta kalli laraba tace kinsan na fad’a miki kafin azumi zamu tashi ko?

Laraba tace eh hajiya

Ammah tace yawwa ki samomin yarinyar budurwa ba sosai ba da zaku rik’a aiki tare sannan ina neman driver ma duk ki samomin
Laraba tace hajiya akwai k’anwata mairoji sai na d’aukota
Ammah tace toh shikenan sai kiyiwa mai kawo ku magana ina buk’atar driver
Laraba tace ay akwai murtala yaron goggota dama inda yake aiki mai gidan ya rasu sun dakatar
dashi
Ammah tace to ki turomin shi gobe muyi magana
Laraba tace toh hajiya godiya nake Allah ya k’ara arziki
Amin ammah tace, tace jiya wata ya k’are ga kud’inki na k’ara miki 20k kiyi wata buk’atar sannan wannan wayar da Yusra ke wasa dashi ki d’auka naga taki ta fashe ko?

Laraba cikin farin ciki tace eh hajiya nagode Allah ya k’ara girma da d’aukaka…

Hayfa bayan sun gama waya da Armando tayi kuka ta gaji tayi bacci sai pass 3:pm ta tashi tayi wanka tayi sallah tasa wani laggins da rigar sanyin gun Yusuf gaskiya ba zata iya zuwa aiki ba gashi jiya Clara tace an bada albashinta ta ajiye mata

Tunani tayi a karon farko bari tayiwa mijinta wani abu special da zai ci da wannan tunanin ta mik’e ta jefa abaya ta yane kanta tayiwa Yusuf text cewa zata je café amma ba zata dad’e ba+

Ya mata reply ki kulamin da kanki….!

Koda ta isa café Clara ta samu tana had’a cake da ke ita Clara full tym take aiki suka gaisa

Clara tace “khadija Oga yace wai yau ba zaki zo aiki ba”..

Khadija tace eh na zo karb’an sak’ona ne..

Clara tace ay nayi miki msg nace zanzo gidanki na kawo miki wato bakya so nazo ko?

Hayfa ta d’anyi murmushi tace No ba haka bane zanyi shopping ne shiasa..

Clara tace OK tace ki duba drawer na envelope d’in yana ciki

Hayfa taje ta jawo ta d’auka ta kalli Clara tace tnx zanje ina sauri mu yi waya anjuma

Clara tace OK bye..

Shopping hayfa tayi musu sosai da duk kud’in aikinta bata san ma nawa bane sai dai inta d’iba kaya taga ta biya kud’in ya saura ta koma haka tayi ta yi har kud’in suka k’are duka

Ta saya Irish da d’anyen nama da vegetables ma ta nufi gida

Taxi na ajiyeta Yusuf da Yasir na isowa suma tsayiwa suka yi duka suna mamakin ganinta da ledoji dayawa na cefane

Yasir ya d’an kalli Yusuf yace bari na duba Amjad wani mak’ocin yasir ne balarabe yayi haka ne don ya bawa hayfa da Yusuf sarari

Yusuf yace “OK” kawai idanunsa na kan hayfa da itama na ta na kansa..

a hankali yazo ya wuce ya shiga gidan ya barta gurin

Jiki babu k’wari ta fara kwashe kayan ta shigo gida ta ajiye ta koma ta kwaso sauran ta gama shigo da kayan ta kulle gidan ganin baya d’an falon ta nufi d’akin

Fuskarsa babu walwala yace “kayan waye wannan”?

cikin tsoro ta kasa bashi ansa ya daka mata tsawa ….

Tace na mu…!

Yace na baki kud’i ki siyo?

Shiru tayi…

Yace da ke nake magana…?

Tuni idanunta har sunyi k’wallah tace “kud’in aiki ne aka bani a café shin… Ya katse yace na ce ki rik’a yin wani abu a gidan nan?

Kuka ta fara….

Baya son jin kukanta a hankali ya k’arasa har inda take tsaye ya rik’o hannunta suka zauna bakin gado ya d’ago fuskarta yana kallonta yace “mai yasa kika yi haka bayan ni ke da nauyin yi…?

cikin kukan tace nayi ne sabida na faranta maka rai kuma ay aikinka ne ka bani….

Bata tab’a yi masa magana mai dad’i ba kamar yau,

d’an murmushi yayi yace “Nagode”…!  amma nafi so ki rik’a anfani da kud’inki wajen k’ananun buk’atunki na kanki da ni bazan iya yi miki ba kinji…?

Shiru ba tace komai ba…

Yace magrib ta kusa ba muje muyi alwala ya mik’e tana zaune ya shiga wanka ma yayi yayi alwala ya fito da tawul a k’ugunsa yace kije kiyi alwala kizo muyi sallah

STORY CONTINUES BELOW

d’ago kanta tayi tana kallonsa wani numfashi taja tana ayyana Yusuf kyakykyawa ne sosai gashi da kwarjini sam in yana tsaye baka bashi shekarunsa sabida kwarjini da cikar hallitarsa ya gama zama cikakken namiji

d’an murmushi yayi ganin ta tafi duniyar tunani ya k’arasa gabanta a hankali ya mik’ar da ita yana kallonta sai lokacin ta farga ta sunkwi da kai, hannunsa yasa ya d’ago fuskarta ya kama bakinta ya fara tsotso inda itama tasa hannayenta ta rik’o k’ugunsa suka fara susuta junansu bayan shi har alwala yayi

Fad’awa suka yi gadon suna tumurmusar juna inda ya ko rigarta bai cire ba ya tura hannunsa yana mutse mata k’irjin tana nishi a tare yana ja tana jan d’aya tana jan d’aya k’afan wandon jikinta suka cire Yusuf da hanzarinsa ya fisge mata pant d’in ya saita jikinsa zuwa na ta

K’ank’ameshi tayi sosai tana k’ara bud’a jikinta yana shigarta shi nan dai suka lula babban garin ma’aurata inda suka farantawa junansu sosai har suka samu biyan buk’atarsu

Suna kwance gadon da ba ma isarsu yake ba suka ji motsin k’wank’wasa k’ofa suka tabbatar yasir ne

Yusuf ya mik’e ya d’aura tawul ya nufi falo ya d’auki wayarsa ya jefa layin yasir

Dariya ce ta kub’ucewa yasir da ke tsaye k’ofar d’akin ya ansa kiran

Yace amma dai kai d’an wulak’anci ne, shine kaje kana hutawa ka manta da cewa tun pool na ke kukan yunwa ko?

Yusuf ya saki k’aramar dariya yace yanzu kaje gun Amjad kayi magrib ka dawo muci abinci abinda kake so zan dafa maka

Yasir ya k’ara sokin dariya yace ay shikenan suka yi sallama ya nufi d’akin hayfa na zaune ta maida abayarta ta rufe jikinta

mik’ar da ita yayi yace muje yau tare za muyi wanka

Kallonsa tayi da alamar tsoro, ya d’anyi dariya yace “mai nene ya saura tsakaninmu”?

Sunkwi da kai tayi…

Ya d’ago fuskarta yace “mu mallakin junanmu ne don haka komai ya halatta tsakaninmu kinji?

Girgiza kai tayi domin itama tasan komai game da aure tun tana 15yrs da ta fara almannar ana yawan yi musu bayani akan aure inda aka basu tarihima cewa manzon saw da nana Aisha har wanka suna yi tare

Shi ya dawo da ita tunaninta jin yana zare mata abayar da babu komai cikinsa da sauri ta sunkwi da kai ita in suna saduwa mantawa take da kanta kwata-kwata tayi ta yin komai amma da zarar sun gama sai ta fara jin nauyinsa

Kallon jikinta ya tsaya yi inda tasa hannunta ta rufe k’irjinta ta runtse idanunta

Sosai take burgeshi jikinta na mugun d’aukar hankalinsa yanayinta jikinta na masa kamanni da matan da suka je club jiya komai na su na inda ya kamata ya gode Allah da bayada komai amma ya bashi mace kamar hayfa

Sunkuyawa yayi yana lasar wuyanta ta k’ara runtse idanunta, ” yace ina sonki sosai”….!

Ya d’ago yana kallonta a hankali itama ta bud’e idanunta tana kallonsa yayinda ta tsinci kanta da rungumarsa shima ya k’ara rungume ta sosai sun kai 5mnts kafin ya d’ago ya rik’o hannunta suka shiga bayin tare suka yi wankan dukda kunya da take ta d’anji har suka gama kowa yayi na tsarki suka fito da kansa ya d’auko mata rigar sanyi mai kyaw tasa said sicket ta saka hijabi shima yasa wata jallabiyarsa ta sallah da safa a d’aki ya musu jam’i suka yi sallah kafin suka fito yana rik’e da hannunta kallonta yayi yace mai zaki ci?

ta d’anyi shiru kafin tace “ka bari inaso na rik’a yin girki”…

Jawota yayi yana kallonta yace kin tabbata?

girgiza masa kai tayi…

Peck ya mata a kumatu yace “Allah yayi miki albarka”!

Itama cikin jin kunya ta masa a kumatu tace “amin”

STORY CONTINUES BELOW

d’an dariya yayi kafin yace bari na nemo yasir..!

Yana fita ta fara bud’e shopping ta jera duk kayan abincin a drawer da suke jerarwa su taliya da dai a lot tink da taga yasir ko Yusuf na siyowa na gida kafin ta fito da Irish ta b’are ta wanke nama ta yanka shi k’anana haka vegetables duk ta d’ora tukunya ta d’an dafa Irish d’in sama-sama ta sauke ta tsiyaye ruwan ta d’ora nama shima da kayan k’anshi ya nuna ta sauke ta soya ta sake maida tukunyar ta zuba butter ta gasa Irish d’in ta kwashe ta zuba nik’ak’en tumatur da tarugu da koren tattasai da sauransu maggi gishiri tym suka nuna kamar dai pepper soup kafin tazo ta zuba Irish ko minti 3 bata yi da zuba Irish d’inba ta sauke abincin

A waje yasir da Yusuf da amjad anata fira shi yasir akwai son mutane shiasa ka ganshi a Canada sai ka d’auka yayi shekaru dayawa yasan mutane sosai da gurare

Can amjad da shima yana aiki ne wani restaurant ya kalli yasir da Yusuf yace y’an uwa sai kuma gobe hirarnan tayi dad’i da ma haka muk’e had’uwa in muka samu free tym

Yasir yace karka damu zamu fara daga yau IA, yace Allah yasa suka yi sallama inda su yasir suka nufo nasu

Suna bud’e falon k’anshin turaren wuta sabida hayfa ganin k’anshin girkin ya cika falo tayi turaren wuta

Itama wanka ta sake tasa doguwar rigar shadda ja tayi kyaw ta yane kanta da k’aramin gyale sabida yasir

Kallon Yusuf yasir yayi yace yau gidan nn sai naji kamar k’anshinsa ya canza

Yusuf yace muje dai kaci abinci…

Dariya yasir yayi yace nidai anamin yanga da mata wlh aure nima zanyi na huta

Dariya shima Yusuf ya saki kad’an saidai idanunsa suka sauka kan hayfa da ke fitowa d’aki tayi wani fitinannen kyaw har walkia take. Kallonta ya tsaya yi tsaf ya manta da wani yasir agefensa saida yasir ya tab’ashi cewa Alhaji yunwa na keji ka bari naci na tafi tukuna

Duka Yusuf ya kai masa a kafad’a hayfa ta k’arasa fitowa suka gaisa da yasir ta wuce kanta ta fara fito musu da abincin ta jera musu k’asan carfet ta kawo musu drink ta ajiye komai ta koma d’aki tana ji kamar yau ne ta fara aikinta na matar aure, d’an murmushi tayi na jin dad’i wai yau tayiwa mijinta abinci

Yaye gyalenta tayi ta kwanta gadon ta d’auki wayarta ta kunna data suka fara chart da Salma

Salma tace haba sisto ki turomin hotunanki da ma na angonmu insa a Zamani group kinsan kowa na complain wai mun b’oye mijinki k’ila mummuna ne gara mu saka musu a wuce gurin

Pls mana wlh I so mch miss u bare tunda na iso Egypt ji nake kamar bazan k’ara ganinki ba

d’an emoji hayfa ta tura mata na dariya kafin ta shiga gallery d’in wayar inda taga hotunan ta harda na skull da islamiyya tayi mamaki sosai kafin ta ga wanda yasir yayi musu ranar bufday d’in Yusuf cake d’in k’arami amma yayi kyaw arha a turai amma a nja cake d’in zaiyi kud’i

Kallon hotunan ta tsaya yi ita kanta bata cikin fara’a ranar saidai sunyi kyaw don haka ta turawa salma sannan ta tura mata hotunan Yusuf zafafa wanda daga cikinsu ne itama ammah ta gani ta zauce

Emoji salma ta turowa hayfa kai sisto kin samu duniya fa mijinki akwai kyaw gaskiya kuma da alama zaiyi wutan wasa

Emoji hayfa ta tura na anger….

Emoji na dariya salma ta turo mata tace wlh kinga yadda yake kallonki kamar yana shirin had’iye ki…

Hayfa tace “kin fiya iskanci…”

Salma tace kinga ni in yanada aboki pls ki shigar dani inzo mu had’e nima na canza Kamar ke gaskiya duniya nayi da ke first lady

Hayfa tace tnx! Amma kinsan dai bazan yadda ki fara neman namiji ba shi ya ganki ba ko?

STORY CONTINUES BELOW

Salma ta saki dariya tace kinsan dai ni ba ke bace don haka babu ruwanki in kika shigar dani na koya masa sona daga baya in muka yi aure

Haka dai sunata chart har Yusuf ya shigo yana kallonta bata ma sani ba

Domin gani tayi msg na ta shigowa daga wasu number da taga ansa Qassim sai wani Aliy ta kuma share tak’i bud’ewa bare tayi reply ta gyara zata kwanta da kyaw taga Yusuf tsaye.

Ta kalli gaz mai bunner takwas ga fridge mai wadrope wato mai k’ofa biyu ga kayan alatun duniya mak’il a kiching kafin ta k’ara sandarewa a falo tana kallo kafin suka haura sama lallai k’ila d’an wani tsohon k’usan gomnati hayfa ke aure domin suke kashe kud’i kamar iska sabida sun gama satar kud’in gomnati sun rasa yadda zasu kashe sai suyita rabawa y’an matansu da yaransu da matansu

haka taita kallo ammah na kula da ita saidai ta d’anyi murmushi har luba tazo zata tafi ammah ta mata transfer na 100k tace kisha drink ki sayawa su walid biscuits suka yi sallama

Luba na tuk’i tana mamakin yadda rayiwarsu ammah ta canza daga auren hayfa lallai shiasa ammah tak’i bawa kamal auren hayfa ashe sunada plan da wanda ya fishi

Haka su ammah suka fara rayiwarsu a kabala yayinda yaransu kaf suka fara karatu a essence international ammah ita yanzu ma tunanin yin masters take daga mijinta ya wuce nasa karatun

a Canada ma hayfa tana ta ayyukanta har biyu ba kama hannun yaro domin bata bar café ba kada Yusuf ya ganota inda suka yanke hukunci da Armando idan aiki ya samu a wajen Canada zasu had’a baki da ogan café sabida abokin Armando ne ya cewa Yusuf zai tura su hayfa wani course na k’arfafa aikinsu da ilminsu a harkar abinci

A gefe yanzu ba k’aramin gurbi Yusuf ke dashi ba a zuciyar hayfa dukda tana k’in yadda da abinda zuciyarta ke fad’a mata na cewa ta kamu da son mijin nata wanda sam yanzu burinta kullum taganshi cikin walwala..!

Yau watansu biyar suna dirzar rayuwar aure na gaskiya ma’ana suna kwanciyar aure tana masa girki da y’an ayyukan gida domin yusuf ya fara course d’insa wata biyu kenan nx mth zai gama shiasa basu tashi gidan yasir ba sabida sun k’ara sayan visa dukda ita hayfa armando sunso bata takardar zaman k’asa tace ah ah  wai kada iyayenta su gane

zuwa yanzu hayfa tayi kud’i sosai domin tayi aiki sunkai kala takwas a cikin Canada wanda a Nigeria kud’i ne masu d’inbin yawa domin ammah ta saya keke napep biyar mota doguwar golf biyu ana aiki Kaduna Kano katsina sannan ta k’ara sayan k’ananan gidaje biyu d’aya jabi road U/Rimi d’aya ashiru road y’an majalisu Kaduna duk an zuba haya banda suma rayuwa suke kamar attajiran asali

Sannan iyayensu da suwaiba sunyi umra da hajj jama’a y’an badarawa sai mamaki akeyi har yanzu na arzikin nasu dukda labarin anfi yad’ashi akan sun mallake mijin hayfa ne yanata kashe musu kud’i sauk’inta ma ba unguwar suke ba a kabala babu wanda yasan labarinsu haka suke ta ci gaba abinsu….!

Yau hayfa na café tana aiki duk kwanan nan bata jin dad’in jikinta saidai bata zargin komai illa rashin isashen hutu a wannan tsakankanin gashi nx wk tanada wani aiki da wani kamfanin agogo anjuma ma Armando zai kawo mata fayel ta cike

Jin muryar Clara tayi tana “khadija ina wannan cake d’in na banana”?

Hayfa tace yana kwalinshi kince 6:pm za suzo ansa shiasa na fito dashi..

Clara tace eh gasunan ma sunzo pls ki kawo musu..

Hayfa tace “OK” ta mik’e taje d’aukowa inda ganin kwalaye dayawa ta fara bud’ewa ta gane wanda take nema saidai wani gigitacen amai ne ya taso mata ta rufe kwalin da sauri ta nufi bayin café d’in

Amai tayi sosai ta wanke fuska da bakinta ta fito saidai suka yi karo da Armando da yazo nemanta aka ce tana bayi shima yanata jiyo kakarin amanta gashi yanzu ta fito idanunta duk a tsume kallonta yake da alamar tanbaya domin d’an duniya ne ya saba case sosai da matasa y’an aikinsu bayan sun kwaso ciki

d’an kallonta yayi yace sannu kizo muyi magana na wuce inada appointment ana jirana

“OK” tace ta kalli Clara da niyar magana taga cake a gaban Clara sai ta wuce zuwa tebur d”in Armando

Kallonta yayi da kyaw yace “mai yake damunki”?

d’an sunkwi da kai tayi tace gajiya ne ban huta ba kwanan nan

Ajiyar zuciya yayi yace “OK” amma still gobe in kika zo kamfani Dr d’in mu zai duba ki kinga munada aiki a gabanmu ya kamata ki zama cikin k’oshin lafiya gashi duniyar d’inki ta fara alfahari da ke kada ki yadda wani abu da zai jawo miki rushewar shahararki domin kina shahara darajar albashinki na k’aruwa ki kiyaye naji dad’i bakya harkar club da alcohol so ki kiyaye shirme in ma kinada saurayi kuna kwanciya tare wannan ba damuwa bane is normal amma kada abin ya wuce kwanciyar kin gane?

d’an shiru tayi wannan aikin ya fara isarta k’aidoji da sharid’a ba zata ci kaza ba ah ah ba za tayi kaza ba kenan duk ranar da suka san tanada aure aikin zai tsaya kenan… Armando ne ya dawo da ita tunaninta inda yace sanann kinsan babban gala na Milan nan da 5mths ne kuma muna fata k’ungiyar d’inkunan duniya su bamu wannan shekarar ma in suka bamu ke za kiyi aikin har bangon

Ajiyar zuciya tayi tace “toh” suka yi sallama yace sai sun had’u gym gobe¹⁸

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]