KASAR WAJE CHAPTER 5 BY MARYAM DATTI

Advertisements

_____

KASAR WAJE CHAPTER 5 BY MARYAM DATTI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Advertisements

_____

Tsayuwa yayi bakin k’ofar ganinta kan dadduma tana karatu da d’an k’aramin qur’ani.+

Tana kaiwa a ya ganinsa ta rufe qur’anin saidai ta kasa yi masa magana tana son gaishe shi
zama yayi gefen gadon yana kallonta yace “barka da safiya”!

d’an sunkwi da kai tayi tace “kaima haka” tayi shiru..

Mik’a mata wayar yayi yace gashi na saka miki sim a ciki

d’an d’agowa tayi tana kallonsa ganin wayarsa yake ba ta…

Yace karki damu na saya wani ke kuma na baki wannan

shiru ta kasa ansa kusan 5mnts ya mik’e ya mik’ar da ita ya rik’ota zuwa jikinsa yace “muje mu karya na wuce kada nayi latti”

a dole ta biyo shi suka shiga d’an kantar tare ta d’auko bread a fridge ta shafa musu butter shi kuma ya had’a musu tea suka fito suka zauna falon suka karya
Bayan sun gama 7:23am Yusuf ya rungumeta sosai jikinsa ya mata peck tsakiyar kanta ya wuce aiki

Bayan tafiyarsa tayi gyaran gida shara mopping da wanke-wanke da wankinta duka kusan 11:9am ta gama komai ta yi wanka tazo ta d’auka wayar tana kallo IPhone5 ce ita da ko iPhone7 ta taina
fara duba wayar tayi ta shiga wpp d’in ammah ta mata voice note na yadda take missing d’inta da yara duka


Sanann ta saka number suwaiba ta gaisheta, sannan ta shiga number salma baita ganin Yusuf bai goge ba bata onlyn don haka itama ta bar mata msg ta kashe data ta kwanta domin ita dama batada Facebook accnt ba tayi shiasa ba mata shiga ba.

Armando ya kira bunil ya fad’a masa yadda suka yi da hayfa
Bunil yace gaskiya in ba zata iyaba ka nemo wata ko mu aro Raudha daga India tunda kaga dama tanata tokarmu kaga sanyi ya fara nisa a ce har yanzu bamu saki summer collection ba

Armando yace kayi hakuri mu bata lokaci yau da gobe yarinyar k’arama ce sosai bana tunanin ko 18yrs tayi dole abin ya buk’aci tayi tunani yaso zamu sa mata zafi sai ayi show nn da 10dys
Bunil yace shikenan amma gaskia daga gobe kawai…

Armando yace don’t worry suka yi sallama
Tunani Armando ya fad’a Allah yasa hayfa ta amince domin bayan aikin summer ga collection d’insu na abaya na Kuwait da Dubai zai so suyi aikin da ita tunani ma yayi zai yiwa yarinyar dabara suyi contract da ita na 2yrs yadda da haka ba zata kub’uce musu ba da wannan tunanin yayi mutmushi
2:54  Yusuf yau ya gama aikinsa na yamma ya da wuri ya kira alhaji shamsu jikinsa yayi tsanani a India wani d’an alhajin ne ya ansa wayar sosai hankalin Yusuf ya tashi ya kira innarsa suka d’anyi hira tace ya gaida hayfa da haka ya dawo gida hankalinsa duk baya kwance da ciwon alhaji shamsu
Hayfa na falo da wani dogon riga mara hannu ta kama gashinta baya wani magazine take karantawa ta internet taji motsinsa
mik’ewa tayi za ta shiga d’akin saidai yanayin da ta ganshi jikinta ya d’anyi sanyi bata iya tanbayarsa ba amma ta kalleshi tace “sannu da zuwa”!

Nagode yace ya zauna ya d’an saki fuskarsa baya so ta gane komai, Ganin ma lokacin aikinta ya kusa ta shirya ta fito tace “zan wuce”!

d’an d’agowa yayi yana kallonta yace “kinci abinci”?

STORY CONTINUES BELOW
“Eh tace sauran na jiya na bar maka na ka”!

Murmushi yayi yace “nagode”! Ta juya ta wuce ya bi bayanta da kallon so

Sai bayan tafiyarta ya koma tunanin alhaji shamsu Allah ya baka lafiya yake ta nanatawa cikin ransa gashi wayarsa ba ta chart bace yana son magana da Aliy bari ya huta ya kirashi direct suyi magana

Hayfa na shiga café Armando na zaune yana jiranta yi tayi kamar bata ganshi ba yayi murmushi yarinyar akwai yanga yace a ransa

Ta wuce tukuna Clara tace “Khadija zan fita ina zuwa dama ke nake jira”!

Hayfa tace OK sai kin dawo..

Taje tayi gyare-gyaren teburan ta shirya y’an kayan filawoyin da suke shiryawa na gayu a tebur ta gama komai Armando na kallonta ta shiga kiching d’insu ta yi wasu aikace-aikacen ta gama ta fito kafin a gama girki customers su fara shigowa
Tana tsaye kanta gaban computer tana kallo tana rubutu Armando ya k’araso yace haba gimbiya ay kinsan dai munada appointment ko?

d’an share shi tayi kafin ta d’ago tace OK “ina zuwa”

Ya juya yana murmushi yarunyar nan wuta ce gaskiya yace a ransa

Yana zaune kusan 10mnts ta zo ta zauna tace “ina so kayimin bayanin yanda aikin zai kasance”!

d’an murmushi yayi yace za a miki tranning duk safiya coach d’in mu zai d’aukeki kuje gym d’inmu za kuyi aiki na 40mnts kullum a cikin 2wks sannan mu zamu rik’a baki kalan abincin da zaki ci sannan inaso ki amince muyi contract na 2yrs da ke koda ba zaki dawo gurinmu yanzu ba kina iya yin tunani duk lokacin da kika shirya dawowa sai ki dawo munada gidaje da yara matasa kamarki ana kula mana da su muna basu duk abinda suke so na duniya idan kika yi contract da mu zai zama bakida damar aiki da kowa sai contract d’inmu ya k’are sannan duk da zamu biya ki kud’in contract d’in ba zai hana a duk lokacin da aiki ya tashi zamu biyaki kudin aikin ba

Ajiyar zuciya hayfa tayi ga zak’i game harbi ta yaya zata fara gwada aikin tana zaune da Yusuf kuma a gaskiya tana so sai ta gane kanta tsaf da Toronto kafin ta rabu da Yusuf
Muryarsa ta jiyo “da iyayenki kike zaune har yanzu”?
tsintar kanta tayi da girgiza masa kai alamar ah ah shi kuma ya d’auka tana nufin “eh”

Ajiyar zuciya yayi yace in bakyaso su sani yanzu zanyi miki k’ok’ari a kan haka zuwa lokacin da zaki cika 18yrs kinada damar yin yadda kika ga dama koda basu so

Yace kamar k’arfe nawa iyayenki ke barin gida da safe?

Hayfa tace 7:30

Yace OK coach zai rik’a zuwa d’aukarki ko wani :09am ku ka gama ya ajiye ki kamfani kiyi tranning by 1:am duk kin gama driver ya dawo da ke gida saidai gaskiya da kiyi k’ok’ari kiyi magana ma da su sabida akwai yawan tafiye-tafiye a wannan aikin

Toh tace kawai
Yace yanzu contract na 2yrs zamu baki $25000 amma a ko wani show za’a biya ki kud’in aiki

Toh tace ya d’auko jakarsa ta laptop ya kunna laptop d’in yana tambayarta information tana bashi har ya gama shigar da komai ya d’auko wani fayel a jakarsa yayi rubutu sosai itama ya mik’a mata ta duba da kyaw ta ga duk inda ya kamata tayi signing ta fara saidai wani irin mugun fad’uwa taji k’injinta nayi, bata ankara ba ma ta fara hawaye sabida ji da tayi a karon farko a rayuwarta duk irin samari da suka rik’a juyawa da yaudara ita da mominsu ba ta tab’a damuwa domin tasha ganin nacinsu na sonta ya jawo musu abinda tayi musu saidai yau ta tsinci kanta da jin ba ta yiwa namiji adalciba namijin kuma (mijinta) share hawayen tayi ta kasa k’arasa signing d’in k’arshe

Armando yace karki damu zan taimaka miki yanzu bazan bar wani hanya da iyayenki zasu gane ba nasha samun matasa irinki daga Latino wanda sunason aikin amma iyayensu suqi sabida yadda wasu yaran ke fakewa da aikinmu suna lalata rayuwarsu anjuma ace aikin ne

STORY CONTINUES BELOW
Ajiyar zuciya hayfa ta sake yi tana tunano rayuwarsu da Yusuf daga ranar da ta shigo Canada zuwa yau tasan bata sonsa amma tasan abinda za tayi bai kamata ba da aurensa a kanta ita kuma dole ta nema kud’i don cikawa kanta da danginta burinsu domin ta sani ko yanzu ta koma Nigeria darajarta bazai zama kamar da ba gashi komai na y’an uwanta ya k’are a dalilinta

Muryar Armando ne ya dawo da ita daga tunaninta “ta yaya kike son kud’inki”? Cash ko ta banki?

Ajiyar zuciya tayi tace “za’a iya turawa ta accnt a Nigeria”?

Murmushi yayi yace sosai ma…

Tace bari nayi waya nazo

Yace OK

d’an mik’ewa tayi ta fita waje ta kunna wayarta ta jefa number ammah
Ammah da yanzu take fitowa aiki 2:pm a nageria 6:pm a Canada
Ammah ganin number waje ba suna tayi tunani itama k’ila su hayfa ne
Ta ansa y’an matana ya kike?

Hayfa ta gaisheta tace mominmu accnt d’inki na ja’iz zan miki saqo ko UBA?

Ammah cikin tsananin farin ciki tace na GT bari na turo miki bayan bikinki na bud’e sabida ke ance zaifi sauqin sha’ani

Hayfa tace toh ki turo yanzu zan kira da yamma
Ammah tace toh y’ar albarka Allah ya qarawa mijinki arziki ya barku tare ki yita masa biyayya sosai kinji?

Shiru hayfa tayi kafin tace “toh”

Suka yi sallama ammah ta kashe waya kai wannan aure kamar wasa gashi tun ba’aje ko ina ba sun fara fantamawa gurin malam ma zasu koma ya k’ara had’a kan hayfa da Yusuf da haka ta shiga napep ta nufi gida a napp ta yiwa hayfa msg d’in accnt number cike da farin ciki

Hayfa ta bawa Armando kamar wasa ya turawa ammah $25000 nan hayfa suka gama komai amma ta kalli Armando tace
Amma inaso zanci gaba da aiki a café

Dariya ya Saki yace ay yanzu kinfi k’arfin aiki a café saidai ma anjuma kad’an kema ki bud’e café wasu nayi miki aiki

D’an ajiyar zuciya tayi tace eh inaso naci gaba da yi kada a zargi komai har zuwa lokacin da zan warware komai

Yace OK babu damuwa ammah ranar show fa tun 7:am kina kamfani har bayan dinner

Tace toh suka yi sallama yace in kika zo office zan baki copy na documents da sauran kayan anfaninki za a nuna miki drower naki a kamfaninmu da zaki rik’a ajiyar komai a gurin da key d’inki da toilet d’inki duka

Tace toh ya wuce tana zaune sosai take tunanin Yusuf

A Nigeria ammah bayan ta shigo gida yara basu dawo ba laraba na girki ammah ta wuce ta cire kaya ta wuce wanka taji shigowar alert da mugun hanzari ta nufi wayar domin hayfa bata fad’a mata nawa zata turo mata ba
Murza idanu ammah tayi sosai tana kallon msg d’in gt bank
Zama ta koma tayi a gefen gadonta ta d’auko medical glass da take  marking d’alibai dashi ta k’ara karanata msg million ishirin da kusan dubu d’ari biyar?

Wani irin wawan tsalle tayi ta kama kanta ta dawo tana hawaye ta zauna shiru a yau ta k’ara farin ciki da godewa Allah ranar da ta had’u da Yusuf hak’ik’a wannan rana shine rana mafi alkairi a tarihin rayuwarsu duka har iyayensu
Haka ammah ta kwashe kusan 30mnts tana mamakin wani irin kud’i Yusuf yake dashi ta gode Allah da basu nuna masa zalama ba da wuri
Dole taje gun malam ya k’ara mallakawa hayfa Yusuf ita kad’ai babu kishia har abada
Sai kuma ta dawo ta fara lissafi zata biya bashinsu 2.700k sabida ribar banki sai y’an k’ananun bashi da basu taka kara sunkai 1M ba ta kira masu gini ko 2m ta kashe a maida gidansu ya dawo na zamani ta sawa iyayensu komai na zamani kujeru dinning ac gaz komai ta sayawa babnsu mota ta d’auko musu driver da mai aikin gida mace ta lissafa kashewa iyayen 5M sannan ta bawa Aunty suwaiba 5M ita sai ta rik’e 6.300k
Ay kuwa tashi zanyi daga kawo naji Luba tace da 3m dake luba gidanta na s/range ne kabala ana samu gida a kabala doki ita zan nema

Nan ta  kira luba
Luba tace yaya dai y’ar uwa yanzu kika isa gida kinga ni motata na bani kashi ina gun bakanike na

d’an ajiyar zuciya ammah tayi a ranta tace nima ina kan hanyar samun motar ay

Saidai a fili tace yawwa gida ne muke nema kince unguwarku harda 3m ana samun tsofaffi a gyara ko?

Luba cikin d’an mamaki tace “eh ana samu jiya ma baban walida yake fad’amin layin abaji nan k’asanmu akwai wani k’aramin gida 3bdrms da 2toilets da komai saidai tsoho ne sai anyi gyara
Ammah tace da mutane gidan?

Luba tace ah ah gidan mutum d’aya saidai babu gate saidai Wanda ya saya ya saka

Ammah tace nawa suke nema?

Luba tace wai 4.500 ammah tace OK ki kira baban walida mu had’u gidanki yanzu zanzo na biya

Cikin tsabar mamaki Luba tace na waye zai saya?

Ammah tace baban yara domin ita ammag sam bata bari y’an waje najin cikinta duk iskanci mijinta ta ke yiwa
Luba sanin zurfin cikin luba tace Allah ya sanya alkairi sai kinzo nima yanzu napp zan hau Na k’arasa gida zan bar mota suka gama zasu kawomin

Ammah tace OK suka yi sallama

Ta fara lissafi wannan gidan tunda na gado ne sa’idu yazo muyi shawara mu saida sai muyi gyaran wancan gidan sannan ta saya mota koda na 500k yaso zuwa gaba ta canza ta saya na 2M kujerun fata zan saya na 500k dinning na 150k na saya Ac uku na canza gaz in ta kama ma sai na biya banki rabi in ta sake turo wani kud’in na k’arasa musu kafin nan gaba kuma sai zuwa hajj mu da iyayenmu IA

Wani hawaye take sharewa na murna ganin abin take kamar mafarki tabbas Yusuf alkairi ne ga rayuwarsu Allah ya barku tare da hayfa har abada zanyi komai domin had’a kanku daga gidan luba gun malam zan wuceHaka ammah ta daure ta mik’e taje tayi wanka tana fitowa yara na dawowa makaranta laraba tanata hidimarsu+

Yaran suka shigo ganin yanayin mamansu suka ce mominmu bakyada lafiya ne?

Murmushi tayi tace ah ah ciwon farin ciki ne nake yi kunji maza kuje kuyi shirin islamiyya sai da yamma zan baku labari mai dad’i

Nan suka fito suna tsalle suka nufi kiching gurin laraba

Tana shiryawa ta sallami laraba ta wuce kabala

Hayfa na aiki duk hankalinta na kan tunanin Yusuf yau sam ya kasa barin k’wak’walwarta

Tanbayar kanta take mai yasa? Yanada mutunci sosai, mai yasa za tayi masa haka? nayi karatun addini na sani a yanzu a rayuwa Shi yafi kowa alhaki da hakkin sani da yanke hukuncin komai a kaina

kiching d’in café ta shiga ta b’oye fara kuka sosai ita bata san ya za tayi ba gaskiya

Yusuf bayan tafiyar hayfa café suka yi waya da aliy yake jaddada masa wlh shima abbansu ya dad’s masa jikin na alhaji shamsu sam babu dad’i

Yusuf yace Wlh Aliy na fi kowa jin ciwon alhaji..!

Aliy yace na sani amma kada ka damu IA zai samu lafiya, wai ma nawa ne yanzu ya rage?

kasan ni ko kayi aike ba tanbayar lawyer na ke ba saidai nayi signing kawai

Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace 8M ne da 368k..

Aliy yayi ajiyar zuciya yace kayi hakuri Yusuf da abinda zan fad’a amma gsky ne wlh don auren da kayi ne da tuni ka gama biyan naka har ka fara tara kadara a Nigeria

Bawai babu kyaw ba ne auren amma kayi gaggawa…

Ajiyar zuciya Yusuf yayi sam bayaso yaji koda innarsa na kushe aurensa da hayfa Yasir kusan ko yaushe sai yace yayi gaggawa aliy ma haka, shi yana son hayfa kuma ko bashin duniya ya d’auka ba zai tab’a dana sanin yin haka ba sabida ya mallaki hayfa

Aliy ne ya dawo dashi tunaninsa yace kada kasa damuwa kaddara ta riga fata Allah ya tashi kafad’ar alhaji ya baka ikon biyansa kaima ka fara yiwa kanka

Yusuf yace amin na gode Aliy ka gaidamin su Abba

Aliy yace za suji suka yi sallama Yusuf ya kashe wayar ya fad’a tunani

Shi burinsa ma yayi ya sama musu gida su fara rayiwa sosai shi da hayfa tunda yanzu ta sauko su gina rayuwarsu tare

d’an ajiyar zuciya ma yayi yaji yana son ganinta kafin su wuce club dama kuma zaiyi shopping na gida mik’ewa yayi yasa takalminsa ya fito ya nufi café

Koda ammah taga gida sosai gidan ya burgeta su kad’ai babu yawan mak’ota kamar a gidansu na kawo

Sorry na samu mistake na lissafin kid’in da hayfa ta aikowa ammah.

Kallon Luba ammah tayi tace yayi kiyiwa baban walid magana

Luba tace toh masha Allah suka fito yana mota shi da agent d’in gidan

Nan aka gama komai ammah ta biya gida da agency fees Luba na ta mamaki saidai sanin halin zurfin cikin amma luba tace maybe tuni suka samu kudin sayan gidan

STORY CONTINUES BELOW

A hanya luba na tuk’i ammah ta kalleta tace muje gun wannan cousin d’in naki da ke aiki (K’aura motors) ….

Luba dake tuk’i ta d’an juyo ta kalli ammah tace “mota kike so”?

Ammah tace “eh” amma mai sauk’in kud’i fa

Luba cike da mamaki tasan ammah ba zata fad’a mata cikinta ba amma tace “wai mai yake faruwa ne”?

Ammah tayi murmushi sanin cewa itama Luba yawanci yayarta maman kamal ke taimaka mata da hidindimun rayuwa don ko motar ta ma yayar tata ce ta bata

Ta kalli luba tace wlh hayfa ce mijinta ya bata kud’i kyawta shine ta raba mana

Luba ta jinjina Kai tace masha Allah, Allah ya k’ara masa bud’i ya k’ara musu zaman lafiya

Amin ya rabbi Ammah tace tana murmushi

Koda suka iso k’aura motors nan suka wuce office d’in cousin d’in luba mai suna Shu’aibu

Suka gaisa luba tace bro mota k’awata ta keso amma fa ba mai wuta ba

Dariya yayi kafin yace kamar na nawa haka?

Luba ta kalli ammah…

Ammah tace kamar 800k ko ma k’asa

Ajiyar zuciya yayi yace OK akwai wata k’aramar Kia milk ogan mu ya sayawa y’arsa tace ba taso amma ta fara anfani dashi kusan 2mths da zan sayawa madam d’ina oga yace na bada 1.200 to sai nazo na shiga hidima mamana tayi ciwo muka je Egypt so indai kinada kud’in ki cika ki d’aukeshi sabida gaskiya yanada kyaw kuma kalar mata ne

Kallon Luba ammah tayi

Luba tace shine wanda ka turamin rannan ta wpp kace na nema ciko nazo na ansa?

Yace eh..!

Ajiyar zuciya luba tayi domin kuwa taso motar sosai cikon 600k d’in ne da bata dashi yasa ta hak’ura

Ammah tace OK na d’auke shi

Murmushi yayi yace ba zakiyi nadama ba IA kuma anything ki rik’a nemana munada kanikawa anan kada ki yadda da ko wani bakanike

Ammah tace OK nagode, mamaki Luba ta keyi sosai shin wani irin kud’i mijin hayfa ke dashi haka ya basu kyawtar mak’udan kud’i haka

Ammah ta mik’awa shu’aib ATM d’inta suka kwashe kud’insu dama ta kota driving tun 5yrs ta iya sosai don haka anan ma aka gama mata komai plak suka yi sallama da luba da duk jininta ya daskare ganin irin facakar da ammah keyi da kud’i

Ammah ta shiga motarta ta nufi badarawa gidan suwaiba.

Koda Yusuf ya isa café yaga sandrine da Monica sunata aiki

Bayan sun gama gaisawa ya tanbayi sandrine ina hayfa dukda yaga Clara ma bata nan kuma da ita hayfa tafi shiri duk café d’in

Tunani ma yayi ko sun fita ne sabida sam duk café ana d’auka Yusuf yayan hayfa ne daga shi har ita babu wani abu da suke yi da yake nuna su ma’aurata ne

Sandrine tace “tana kiching ka shiga”!

Hayfa na duk’unk’une ta had’a kai da gwiwa tana kuka saidai yanzu sheshshek’a kawai take

Yusuf da d’an hanzari ya k’arasa ya tsuguna ya d’agota saidai ya tsorata da yadda yaga idanunta sun rine sun d’an kumbura wato kuka tayi sosai

Kallonta yake yana tanbayar kansa mai ya faru?  Saidai da kansa ya bawa kansa amsar tanbayar da cewa talaucinsa ne ke damunta har yanzu ta kasa sabawa

Nan yaji jikinsa ya mutu saidai ya daure ganin tuni ta sunkwi da kanta k’asa yace

Ki tashi muje ki wanke idanunki ki fara aiki nan private café ne ko wani minti da zaki b’ata yana iya shafar aikinki a yanke miki a kud’inki

STORY CONTINUES BELOW

kasa motsawa tayi mik’ewa yayi ya d’agota itama ya rungume ta jikinsa yana rad’a mata a kunnenta “ina sonki fiye da yadda zaki tab’a tsammani”!

d’an d’ago fuskarta yayi yana kallonta “yace ba zanyi miki alk’awarin komai ba amma IA ina fata ke da iyayenki wata rana kiyi alfahrin aurena koda hakan shi zai zama k’arshen abinda zanyi kafin na bar duniya

d’an kallonsa take idanunta cike da k’wallah domin sosai taji tausayinsa sannan kalamansa suka k’ara sanya mata sanyin jiki

Share mata hawayen yayi yace muje kiyi aiki karki manta saura 9dys kiyi albashi banaso su cire miki ko dala

d’an sunkwi da kai tayi ya rik’ota suka k’arasa gun zinc ya wanke mata fuska ya tsafe mata da rigarsa ya mata peck a goshi hayfa da bata sani ba ta tsinci hannunta a k’ugun Yusuf ta zagaye lokacin da yake mata peck

kallonta ya k’ara yi a hankali ya fara d’an kissing d’inta itama ta k’ara rik’eshi da kyaw suna tsotsar bakin juna a yau kam hayfa taya shi take da gaske

Jin d’an motsi babu mai shigowa sai ma’aikatan café da d’an kasala Yusuf ya sake ta dukda yasan nan turai ko ganinsu a kayi babu mai damuwa tunda ko titi haka mutane sharholiyar su

Peck ya k’ara mata yace sai da safe “zan wuce aiki yau da wuri”!

Ya fito ya wuce…

Hayfa da k’yar taja jikinta ta fito har an fara cika nan ta bawa su colleagues d’inta hak’uri na absence d’inta taje ta fara ansar orders

Koda ammah ta isa gidan suwaiba ta bata labarin kaf yadda suka yi da hayfa suwaiba ma nata d’urawa auren albarka sannan ta kalli ammah tace kada kiyi wani gyaran gida kidai d’aukarwa goggo mai aiki ki saya musu y’an kayan alatu mu bari idan ta sake aiko wani sak’on sai mu saida gidan mu cika a nema musu wani gidan mai kyaw ta nan kusa dani

Ammah tace toh shikenan Adda in haka ne babu damuwa Allah ya k’ara rufa mana asiri

Nan ammah ta kalli suwaiba tace to in haka ne Adda kema kinga nn gdan gadon babansu surayya ne shi da murtala da saliha  mai zai hana ki bar musu sai mu nema gida a kabalan koda na 3m sai ku koma yaso suma su goggo sai daga baya mu nema musu a can ko kuma ni inaso dama na biyawa Daddyn yara wani course na aikin architecture a jos wata tara kudin 700k ne dama shima ya fara tarawa sai na masa ciko in ya tafi sai kawai mu saida gida su inna su dawo kafin na samo nasu

Sosai suwaiba tayi murmushi tace shawararki tayi sosai Allah ya k’ara dafa mana, amma yaushe kike ganin zai wuce?

Ammah tace ay dama 5M nayi niyar kashewa su goggo kinga tunda mun canza shawara shiasa zan biya masa sabida tuntuni abokin babnsa alhaji tahir yace yayi course d’in zai samo masa aiki mai kyaw a kamfanin wani bature da ke Lekke irland Lagos

Suwaiba tace hakan yayi domin kinga samun aikinsa zai k’ara hab’aka arzikinku

Ammah tace Allah yasa, shima baban surayya da yake son harkar noma kinga ta k’ara yin aike sai muga yadda zamu tsara masa nasa babban jarin, sannan Adda kema zaki koma karatu IA koda diploma kiyi

Suwaiba tace kada ki damu komai daki-daki IA

Nan dai suwaiba ta fito waje tanata sawa motar ammah albarka suna farin ciki suna k’ara sawa auren Yusuf da hayfa albarka inda ganin yara duk suna islamiyya suwaiba da ammah suka k’arasa unguwar dosa a motar ammah gidan malam

Koda suka isa suka gaisa da malam ammah ta bashi labarin abin arzikin da hayfa ta musu tare da fad’a masa suna so a k’ara jona hayfa da Yusuf kamar kiss da taya babu rabuwa babu kuma mai shiga tsakaninsu

Bayan malam yayi bugun k’asa ya kalli ammah da suwaiba yana tunanin yadda zai musu bayani, domin abinda ya gani bashi suka fad’a masa ba tabbas akwai sark’ak’iya cikin lamarin

sannan tun ranar da suka fara zuwa gunsa yaga abinda ya kasa fad’a musu sabida yasan dayawa mata masu bin malamai in aka fad’a musu gaskiya basu yarda suna gani malam yanada mafita akan komai

Don haka ya k’ak’alo murmushi ya kallesu yace a gaskiya a kwai d’an rud’ani tsakaninsu amma

Suwaiba ta katseshi malam ayi komai domin had’in kansu da son junansu suji komai nene zai faru ba zasu iya rayuwa ba su tare ba wannan shine burinmu

Ajiyar zuciya malam yayi ya rasa ta ina zai fara domin ya lura yayyun hayfa basuson jin komai a yanzu inda sunsan ma mai zai fad’a musu

Kallonsu yayi yace shikenan amma a shawarata mu sanya kusanci tsakaninsu domin hakan yafi komai sanya soyayya tsakanin ma’aurata

Ammah tace kamar yaya?

Yace domin na gani har yanzu basu k’ara kusantar junansu ba, mu sanya musu fitinanniyar sha’awa da zasu rik’a yawan jin buk’atar junansu wannan zai sanya musu tsananin shak’uwa

d’an kunya su ammah da suwaiba suka ji, suwaiba tace ayi malam ai aure ke tsakaninsu dama ba haram za suyi ba

d’an mutmushi yayi matan na bashi mamaki har yanzu basu nemi sanin waye Yusuf ba toh kodai Allah ne ke da manufar shafe musu wannan tunanin daga k’wak’walwarsu

da haka dai suka daidaita amma ta masa tranffer na 150k suka masa godiya suka fito

Malam na cike da mamakin irin sakarkarun mata da suka yadda komai mu za muyi sai kace mu ne (Allah)

Suna mota suna hira har ammah ta sauke suwaiba gidanta akan gobe Zata kira agent d’in da suka saya gidansu ammah ya nemowa suwaiba itama nata sannan sauran kud’in suwaiba ta saya kayan furniture

Ita kuwa ammah parking tayi ta kira mai kujerunta zaizo ya kwashe wanda ta saya kwanaki tayi kakara ta saya kujerun fata ta sake kiran LG company tayi orders TV plasma 50entchs da 32enchs guda biyu na d’akinta da d’akin iyayenta da komai na kayan kallo tv palo Zata maidashi d’akin yara ta saya

tana motar ta k’ara kiran telan mijinta ta bashi orders kaya kala ishirin na babnta ya fada mata kudin ta masa transfer haka dai taita abubuwanta kaf kafin ta wuce gida tana jinta kamar a aljanna

Hayfa na gun aiki sun ma kusa yashi tana wanke-wanke taji jikinta na mata wani iri kanta ya wani sara mata ta d’an rik’e kan kafin ta rintse idanunta

Yusuf da aiki yayi zafi a club sunata sakawa masu shiga bracelet suna register da abin aiki kamar P.O.S yaji kansa ya sara masa yanayinsa wani iri gashi wata shed’aniyar baturiya da yake wa register zata shiga club tasha wani matsiyacin mini sicket har gabanta ana hangowa tuni ta juyewa Yusuf kamar hayfa yake gani+

kamar zai jawota jikinsa yasir ya hangoshi ya rik’oshi yace meye haka Yusuf?

Ajiyar zuciya Yusuf yayi cikin sanyi murya yace na d’auka itac… Yasir cikin mamaki yake kallon Yusuf

Yace OK in kanada buk’atar matarka kaje kasan dai ba kai ba d’an uwana har abokan aikinmu turawa muna karb’awa juna aiki idan buk’atar hakan ta taso

Kallonsa Yusuf yayi yayi shiru…

Yasir ya d’an Saki dariya yace is not aesy ay ko amarci fa dama ba kuyi ba kaje kawai sai mun had’u pool naga sak’on kud’in gida jiya a drower nagode wato kak’i dai ku zauna kyawta ko?

Yusuf yace bai kamata bane da ni kad’ai ne amma harda matata mu zauna kyawta bazai yuwu ba ka bari muci gaba a haka 50%50

Yasir yace ay shikenan! Suka yi sallama Yusuf ya nufo gida

Itama hayfa tunda ta dawo gida take jin sha’awa na fitina ta kunna wpp salma ta mata reply bata ansa ba ga shi tanason kiran mominsu ta mata bayanin yanda ta samu kud’i shima ta kasa tana kwance tayi shiru duk jikinta yayi wani iri taji motsi a tsorace ta tashi sanin su Yusuf na gun aiki sai safiya za su dawo yasa ta k’ara taorata ko b’arayi ne ta nufo falo a tsorace

Saidai ta bushe ganin Yusuf na cire takalminsa

Shima ganinta ya k’arasa cirewa ya d’ago yana mata wani irin kallo kamar zai had’iye ta riga ce doguwa na bacci kamfanin kitty dank pik mai dogon hannu yanada d’an nauyi rigar

Hayfa ma tuni gashin jikinta ya k’ara mik’ewa

A hankali ya k’arasa gabanta ya janyota jikinsa ko b’ata lokaci baiyi ba ya fara kissing d’inta inda itama take ta nuna masa dama itama a matse take

Wani irin mugun kissing suke na fitina yayinda suka mak’ale junansu sosai

Yusuf d’agowa yayi yana kallonta gaba d’aya a rikice take idanunta bai tab’a ganin abinda ya gani yanzun ba don haka nan da nan ya k’ara mannata da jikinsa ya cigaba da kissing suna tafiya a haka har d’akin

d’an gadon nasu mai kamar rai suka fad’a suna k’ara mak’alk’ale junansu

Yusuf da ke ta k’ok’arin cirewa hayfa riga yaga kamar rigar ta manne mata tak’i fita hannu yasa ta wuya gaba da baya ya yaga rigar ya sunkuya ya wawushi k’irjinta ganin bata rabuwa da brasia sabida girman k’irjinta yasa da brasiyar ya fara mata wasa da k’irjin tanata numfashi kamar mai nak’uda

Jin haka Yusuf ya k’ara zafin abinda yake wani irin tsotsin nipple d’inta yake tana nishi, ya rik’a rura mata fitina kala-kala babu inda bai kai bakinsa ba jikinta har k’asanta yana mata wani fitinannen wasa da gurin wani irin kuka ta sakar masa tana k’ara bud’e gurin inda shima yake ci gaba har dai yaga yadda da kanta tayi shirin karb’arsa kafin ya hauro ya k’ara maida bakinsa kan nata ya shigeta

Duk kuka suke yi Yusuf na surfata surfa na fitina dukda tana d’anjin zafi na rashin gogewar gaban nata amma hayfa kamar tayi hauka sabida kwata-kwata ta manta wacece ita Yusuf kawai take kallo yayinda yake ta mata hidima

STORY CONTINUES BELOW

Kusan 40mnts suka samu nutsuwa bacci ma ya d’aukesu hayfa na samansa

Kusan dab asuba hayfa ta fara d’an bud’e idanunta jikinta ne takejin wani mugun tsami Yusuf na bacci

Kallonsa ta tsaya yi jikinsa fatarsa kamar ta half cast d’an runtse idanunta tayi Yusuf kyakykyawa ne gaskiya ya fini kyaw tace a ranta

Cikinsa ta koma tana kallo nan taji wani sabon sha’awarsa ya taso mata bata san ya akayi ba ta kai hannunta cikinsa ganin kamar baya cin abinci

Yusuf da jin hannun hayfa a marar sa yasa fitina ta k’ara taso masa kamo hannunta kawai yayi ya jawota jikinsa suka koma sabun aiki

Tana jin zafi amma kawai ta kasa cewa ya bari domin ita ko had’uwar da jikinsu keyi ji take so take yi

Shidai Yusuf kakarsa ta yanke sak’a don kuwa maida hankali yayi ya k’ara dirzar hayfa son ransa musamman da yaga itama tana so

da k’yar da asubu ya d’auketa zuwa bayi ya taimaka mata tayi wanka ta zauna ruwan zafi kamar yadda ammah ta fad’a mata tun ranar da ta iso Canada tace idan wani abu ya shiga tsakanunta da Yusuf

A haka suka yi sallah Yusuf ya had’a mata tea tasha ya mata peck ya wuce café.

Koda ya isa pool har 8:24am yasir na ta aikinsa yana hango Yusuf ya fara dariya

Yusuf ya dake sabida dama fatansa ya iso ogansu bai iso ba sabida kwanaki ya masa gargad’i cewa ya fara wasa da aiki

Yana shiga gurin saka takalmin aiki da d’aukan kayan aiki yasir ya biyoshi yana taokana

Haba mutumina wai meye na wannan irin dakewa haka daga kawai ka rigani shiga duniyar manya sai a faramin yanga

dariya ne ya d’an  kub’ucewa Yusuf yace amma dai ba kada damuwa shiasa kake wannan abin

Yasir ya k’ara sakin dariya yace yo gaskiya mana ka ganka kuwa? Wlh ka wani yi kwarjini ne kamar ba kai ba

murmushi Yusuf yayi suka fito yasir yace bari na k’arasa nazo na taya ka

Hayfa na bacci taji a nata nucking k’ofa sosai tayi mamaki da k’yar ta d’aga jikinta ta saka hijabin sallah ta fito ta bud’e k’ofar

Ganin wani murd’add’en Latino da kayan k’wallo ta tuna address da ta rubuta a fayel d’in contract d’inta abinda zata fara yau d’an ajiyar zuciya tayi ga jikinta na mata ciwo har yanzu

d’an kallonta yayi yace Queen za muyi latti muje a dole ta kulle gidan suka shiga mota suka tafi

A kamfanin model d’in waje sosai babba kamar irin kamfanonin motsa jiki nan aka bawa hayfa dogon wando da rigarsa da takilmi sosai tayi kyaw suka fara exercise da injuna hayfa nayi tana hamma

1hr cif suka gama tayi wanka ta maida kayanta suka bata brkfst irin nasu model fresh salad da busachen bread

1:40pm suka gama tranning na show aka bata take away na launch inda coach ya fad’a mata ba zata ci komai ba bayan wannan da suka bata har gobe after exercise tace “toh” suka saka ta motar kamfani aka maidata gida

Sallah tayi kawai ta kwanta saura 3hrs ta tafi aiki tasa alarm ta b’oye abincin sai taje café za taci saidai tun bayan da tayi break d’in ma sha’awar Yusuf ya fara bijiro mata saidai ta d’an dauri jin har lokacin jikinta bai gama warwarewa ba

A pool Yusuf sosai yake jin nishad’i tare da jin k’arin son matarsa tuna yadda ya goga ta yasa yace bazai koma gida ba sai ya tashi gaba d’aya

4:35pm ta farka da sauri ta shiga tayi wanka tayi alwala tayi sallah ta saka kaya da sauri ta ta saka abincinta da wayarta a jaka ta fito zata wuce taga Yusuf na shigowa

STORY CONTINUES BELOW

Tsayawa yayi yana kallonta itama haka kafin ta d’an sunkwi da kanta

K’arasawa yayi wani mugun sonta da sha’awarta na fisgarsa ya fara kissing d’inta dukda ganin ta kusa latti amma ta biye masa ya karb’i jakarta ya ajiye kujera suka d’ora daga inda suka tsaya

Mugun tuntub’ar junansu suka shiga yi da zafin nama kowa nason fidda maitarsa da zalamarsa inda hayfa kamar tasha k’waya take k’ak’anme Yusuf haka suka koma d’akin suna sab’ulewa juna kaya inda suka koma kamar masifa suna gasar fitina

Haka dai har Yusuf ya shige gari suka k’ara zaucewa suna ajiyar zuciya

Sosai suka murji juna hayfa ta sakarwa Yusuf ragamar komai ya rik’a juyata son ransa har suka samu biyan buk’atun juna suna kwance rungume da juna

Taji muryarsa zaki iya zuwa aiki?

da sauri ta zame jikinta ta mik’e ta shiga bayi duk tayi laushi saidai haka ta daure tayi wanka ta fito

Kallonta Yusuf keyi yana jin kamar ya cinyeta ya huta

d’an kallonsa tayi kafin ta d’auki wata doguwar riga ta koma bayi tasa ta fito d’an dariya ta bawa Yusuf saidai ya basar bayason ya ruguza ainihin rayiwar auren da suka fara a jiya kaw. ai zuwa yau

bayan ta gama shiri ta kalleshi a kunyace tace “zan wuce”!

A hankali ya taso yazo ya kama kanta ya mata peck a goshi yace “Allah yayi miki albarka”!

Hayfa d’agowa tayi tana kallonsa tasha ji malaminsu saleh almannar na fad’an yadda Allah yake bud’ewa matar da mijinta ya shi mata albarka k’ofofin aljanna da yawan ladan da Allah zai bata akan duk abinda tayiwa mijin har ya sa mata albarkar

d’an rik’o hannunsa tayi ta shafa fuskarta shima yana kallonta ya janyota ya rungumeta kusan minti uku kafin ya sake ta ta fito gidan

Wanka shima ya shiga yayi ya fito yayi magrib yasan itama za tayi a café

Tana isa café a tsorace saidai Clara tace ay an kira oga ance dama yau za kiyi latti wai inji abokinsa

Ajiyar zuciya tayi tasa t.shirt kan doguwar rigarta ta fara aiki.

Haka kwanaki suka shud’e hayfa da Yusuf abubuwansu kullum k’aruwa suke domin kullum sai sun dirji juna in basu yi da dare ba to sunyi da safe abindai ba sauk’i sam

A yayinda hakan kuwa ya fara kawo wani zazzafan kusanci tsakaninsu domin ko wanne da k’yar yake daure nisa da d’an uwansa dukda har zuwa wannan lokacin hayfa ta kasa gane kamuwa tayi da son Yusuf ko kuma jikinsa ne ba zata iya jure rasawa ba domin kuwa sosai take jin masifar son saduwa dashi tun tana jin zafi har a wannan kwanaki goman tana jinta kamar ta shekara da fara saduwa da shi

A gefe duk wannan zalamar da take wa Yusuf bai ruguza mata burinta na yin arziki da azurta iyayenta ba domin kuwa Armando ya fad’a mata akwai ayyuka hud’u bayan wannan sannan duk ya samo mata kwangilar in tayi zata k’ara shahara a duniyar d’inkunan duniya sannan sunanta zai fito uwa uba zata samu kud’i na fitar hankali

Sosai hayfa ke cikin farin ciki tare da ganin yadda rayuwarta ta sanja lokaci d’aya shi kansa Yusuf yanzu tana jin zata iya zama dashi indai zasu ci gaba da kwanciya tana samun gamsuwa yadda yake mata domin kuwa har tazo yanzu tama fishi jaraba shima abin har mamaki yake bashi sam ko yaushe yazo sai yaga itama jiransa take!

Inda a gefe tsabar son saduwa da Yusuf da tsananin jarabarsa da hayfa ta kamu dashi yasa ita da kanta ta fasa gayawa y’an uwanta komai game dashi tunda kud’i ne matsalarmu kuma ta samu hanyar samun kud’in dukda har zuwa yanzun tana k’ok’arin kamewa

Hayfa na café suna aiki Armando yazo yace Queen gobe driver zai fito 7:am zai fara kaiki kamfani Ku gama abubuwanku acan kafin ku k’arasa akwai wannan yarinyar raudha ay kin gane ta ko?

Hayfa ta d’an girgiza kai

Yace kinsan itama da munada contract da ita amma taje wani abokin adawarmu ya hure mata kunne ta b’ata contract ta koma zaman kanta

Hayfa da bata fahimci manufarsa ba “tace kamar yaya zaman kanta”?

Yace yawwa ma’ana yawancinmu masu kamfanonin d’inkunan duniya kamar Dolce gabana, ZaRa, Pacco Rabbane, Versace, Luis Vilton, Christian Dior, and a lot mu kan saya matasa kamar ki mu raine su da kanmu kamar yaranmu muna basu komai amma ba zasu rik’a aiki da kowa ba sai mu haka duk abinda za suyi sai da saninmu koda aure ne kin gane?

Hayfa kanta ya buga “koda aure ne”

Yaci gaba to da raudha mu muka sayeta har kasarta India naje na siyota amma mai kamfanin Pacco Rabbane ya hud’ubeta inda taci amanarmu ta koma gunsa shi kuma ya ci amanarta suka rabu shine yanzu batada contract da kowa saidai in wani daga cikin yaranmu baya da lafiya ko uzuri mai gitma kuma munada show sai mu gayyace ta aikin kawai ana gamawa ta tafi, abinda yasa na miki maganarta ita kad’ai sabida sam bata ji sannan tanada wayo sosai gashi ta tab’a zama gidan kula da masu shan alcohol kuma ganin ta k’ware sosai tare da sanin sirrin duniyar d’inki matasa dayawa na son k’awance da ita ke kuma hankalina ya kwanta da ke banaso ki yadda ko kad’an ki shak’u da ita kinji?

Hayfa sosai jikinta ya mutu domin kuwa kwanan nn har sun fara shak’uwa da raudha a gym..

Ya sake maimaitawa jiya Rodriguez coach yace kun fara shak’uwa da ita ko?

Shiru hayfa tayi…

Yace bawai nace kada ki mata magana ba amma kiyi da kulawa sosai pls…

Hayfa tace “toh” suka yi sallama ya wuce hayfa na zaune cike da tunani kala-kala

Yusuf da yasir suma sun tashi pool suna ta hira ganin magrib ta gabato suka nufo gida inda Yusuf duk kewar gimbiyarsa ya isheshi domin kuwa yau ya makara aiki basu mori safiyar su ba

A hanya suka tsaya supermarket suka yi shopping inda bayan sun gama yasir na waya da k’awarsa hamdiya Yusuf ya koma gefe shima suna waya da innarsa sun dad’e kafin suka yi sallama suka nufo gida

Alwala suka yi suka yi sallah Yusuf ya d’ora musu abinci bayan ya gama yasir yaci yayi nak yana dariya yana tsokanar Yusuf da cewa

Q

Wannan girkin dai na madam ne na kwashi albarka wanann irin romo ya k’ara fashewa da dariya

Macaroni ce da peppersoup d’in naman gongoni da vegetables domin yanzu Yusuf ya gwammace yayi tracking ya rage tafiya in zashi aiki kud’in ya sayawa hayfa kifi ko naman gongoni ganin tana so sosai don ma su a turan ba tsada bane dashi kawai yawan nauyin kansa ke hanashi yin a lot tink

Murmushi Yusuf yayi yace gobe in aka sallamemu a club zan biya kud’in course d’ina IA

Yasir yace masha Allah gaskiya nayi murna to yaushe zaka fara karatun?

Yusuf yace dana biya zan zab’a tym table d’in da zai tafi da lokacin da nake free haka taarinsu yake kowa shi yake zab’ar lokacinsa

Yasir yace yayi kyaw sosai gaskiya

Yusuf yace nagode

Yasir yace da ka fara aikin supermarket duk yadda nauyi zai maka yawa ka daure mu nema jami’a domin nima plan d’ina kenan da zarar na gama biyan su Mama koma ban gama ba wlh farawa zanyi

Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace toh IA amma da na so ita ta far… Yasir ya katseshi ka daina yawan duba matarka Kaine fa mai nauyi don haka kai ya kamata ka fara zuwa sama kafin ita…

Shiru Yusuf yayi yabbas yasir na da gaskiya amma yana matuk’ar tausaywa hayfa na yadda baya wadata da kayan more rayuwa na duniya

Kallonsa yasir yayi yace muyi ishaa ni zan wuce yau akwai wata babe y’ar etopia munada appointment tazo club jiya muka had’u

Yusuf yace aji tsoron Allah dai.. .

Yasir ya fashe da dariya yace tunda kai kana hutawa iya rai ay dole ni kacemin haka

Yusuf yayi murmushi yace to kayi aure kaima ka huta nifa shiasa banason aikin nan

Yasir yace ay tab ni ina club har sai nafara jami’a zan bar aikin ko banyi ba ai da dad’i kallon bulus

Yusuf ya saki d’an dariya yace Allah ya shiryeka

Yasir ma dariya yayi suka shiga suka yi alwala suka tada sallah

Bayan sun idar Yusuf da yasir suka fita saida yasir ya samu taxi kafin Yusuf ya dawo gida jiran hayfa.¹⁵

Advertisements

_____

About AIS

Check Also

KASAR WAJE CHAPTER 15 BY MARYAM DATTI

Advertisements _____ KASAR WAJE CHAPTER 15 BY MARYAM DATTI Www.bankinhausanovels.com.ng  Advertisements _____ Tana saka d’an …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *