[Advertisements⬇️]

KASAR WAJE CHAPTER 3 BY MARYAM DATTI - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

KASAR WAJE CHAPTER 3 BY MARYAM DATTI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Duhu ya fara sosai 10:37 taxi ya sauke su k’ofar gidan yasir

Duk irin ginin gidansu Yusuf ne dogo kamar motel saidai wannan unguwar yafi na su Yusuf d’an cikar gidaje+

kallon hayfa yayi yace mun iso..

Ya bud’e ya fito yaje suka sauke kaya ya sallami wancan ya dawo nan hayfa da k’yar ta bud’e ta fito saidai mugun bugawa k’irjinta yayi a ranta tace “meye haka kuma”?

Yusuf ya sallami mai taxi ya fara d’aukar akwatunan yana kaiwa k’ofar yasir da ya zama no 2 a layin gidajen

Sosai hankalin hayfa ya tashi wai me ke faruwa ne wannan mafarkin nata ya kasa k’arewa

Tsabar tashin hankali ma hawaye ta fara a gurin tana kallon Yusuf ya gama kai akwatunan duka yasa hannu cikin vase ya d’auka key ya bud’e ya shiga da duka kayan ya tsaya yana kallonta tanata hawaye

d’an ajiyar zuciya yayi ya shiga ya bar k’ofar a bud’e

Gidan kamar kusan na Yusuf ne shima doguwar kujera ce a falon saidai na yasir akwai desktop sai kanta shima na kiching komai kamar na Yusuf d’akin Yusuf ya shiga yaga babu komai yasir ya kwashe duk kayansa don haka ya shirya mata akwatunanta ya fito still bata shigo ba ya tsaya kanta ya had’a tea ya zauna kujerar yana sha

Hayfa kuwa a waje kuka take sosai harda sheshsheka jin haushin karnuka tsoro ya sata ta shigo a dole tanata kukanta a hankali

Yusuf na falo bai d’ago ya kalleta ba itama ta wuce d’aki taga kayanta zama tayi gadon ta fara sabon kuka sosai harda sheshsheka

Sosai kukunta ke damun Yusuf amma ya share ya mik’e ko kaya bai canza ba kada ya makara aiki yanzu dole sai ya hau taxi kafin yana zuwa café.

Tuntse idanunsa yayi saidai sam baccin ya kasa d’aukarsa, yana son hayfa amma ba zai yadda yanayin rayuwarsa yasa ya zama k’ask’antacce ba a gurinta.

A d’aki hayfa tasha kuka kusan 3:am da kyar ta samu ta kwanta kanta na ciwo kamar ya fashe da tunanin ta yaya za ta cikawa y’an uwanta burin rayuwarsu!

5:43am Yusuf ya mik’e jin har lokacin yasir bai dawo ba yayi sallah ya kirashi

Yasir da ke bacci a d’aya daga kujerun club d’in da yake aiki ya farka da sauri ya d’auki wayar

Yusuf yace kana ina?

Yasir yace gun aiki yanzu zanyi wanka na taho!

Yusuf baiji dad’i ba domin yasan yasir yayi haka ne don yana tsammanin zasu keb’e shi da hayfa

Yusuf yace in ka k’ara yin irin haka zamu tafi gaskiya 4:am kace min kana dawowa gida

Yasir yace no wlh somtym daga can nake wucewa pool sabida bayan an gama nyt muna gyara cikin club sai cleaners sunzo muke tashi kuma su sai 5:30 ko 6:am suke zuwa

Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace shikenan ni zan wuce café sai mun had’u pool

Yasir yace no ka bari nazo yanzu mu wuce tare

Yusuf yace to kayi sauri suka yi sallama.

Hayfa da itama jinta jik’e sharkaf ta farka sam ta manta period d’inta yazo tsabar bak’in cikin da take ciki zama tayi ta fara sabon kuka sabida batada pad

A hankali Yusuf ya shiga d’akin ya tsaya yana kallonta ganinsa ta mik’e zata shiga bayi ya dawo da ita saidai shima ya bushe ganin yadda duk jikinta ya b’aci da jini

STORY CONTINUES BELOW

d’an kallonta yayi kuka take sosai ya saketa ya fito ya saka takalmansa ya fita

Tafiya yayi sosai har wani k’aramin mall da a lokacin ma suke bud’ewa ya tsaya suka bud’e ya tanbayi pad suka nuna masa yaje ya d’auka k’arami mai goma yazo biya yaji arha sosai yayi mamaki don haka ya koma ya d’auko mata mai talatin ya biya abinda baikai #500 nera ba ya kamo hanya yana sauri domin lokaci ya tafi yayi latin café kuma bayaso yasir ya isa gidan kafin shi lol Yusuf ga kishi

Cikin sa’a yana isowa yasir ma haka a shiryensa suka shiga ya shiga tana wanka ya ajiye mata pads d’in suka had’a tea da cake suka ci suna saka takalma hayfa ta fito wanka cike da mamaki jin muryar mutane biyu shi da waye?

d’aure da tawul iya gwiwa ta nufi falon

Yusuf da ya fara hangota da sauri ya mik’e ya tareta ya maidata d’akin

Yasir kam yana gama saka takalmin ya fita waje

Kallonta Yusuf yayi fiskarsa sam babu walwala yace ” nan gidan ba namu ba ne mu kad’ai ni da ke ne da abokina mun bar miki d’aki don haka ki kula sosai banason shirme”!

ya juya zai fita yaji muryarta ” wallahi sai ka sakeni bazan iyaba” kasan bakada k’arfin yin aure mai yasa za kaje ka yaudaremu a baka aurena bayan ko…. Ya juyo yana kallonta da wani irin yanayi ta kasa k’arasawa..

Ya k’ara takawa har gabanta kafin yace “karki manta ke kika fara shigemin kuma yadda Allah ya k’addari auren ba tare da ni kaina na shirya ma hakan ba haka in lokacin mutuwansa yayi zai mutu, kuma bari kiji abinda baki sani ba shi kansa iznin zamanki a k’asarnan ya k’are ina don haka in kika yi tunanin yin shirme kika fita hukuma ta kamaki zaki gane zamanmu a gidan nan ma rufin asirin Allah ne ya fito ya barta tana hawaye sosai

Can yaga yasir ya tsaida musu taxi suka kama hanya inda sunyi lati dole sai taxi train d’in farko tuni ya wuce

Yusuf ya sauka café yasir ya wuce pool.

A café yana aiki zuciyarsa na wani irin tafasa saidai yana daurewa ya gama ya wuce zaije pool daga nan zai je ammbassad maganr kansa shi da yake fita nema kafin ya had’a kud’in na hayfa.

A Nigeria ammah a office ta kalli k’awarta luba tace “wallahi inda zaki min adalci kinfi kowa sanin matar mutum kabarinsa tun da can ban raba hayfa da kamal ba sai yanzu?

Luba tayi tsaki tace Amina wlh na dad’e da gane bakison hayfa da kamal kowai kin barsu ne don kinga ya nace amma ni na rasa mai kamal yayi da kika hanashi k’anwarki kika bawa wani d’an kano sannan yana zaune can har wata k’asa

Meye aibun kamal? Jst 27yrs yayi karatu har masters yana aiki albashinsa ko mata hudu yake so zai aura tunda yanada gida sannan iyayensa na dashi wallahi Amina kinci amanar amincin da ke tsakaninmu yanzu ga kamal Aunty Zuwaira tace tun bayan auren hayfa ya zama kamar tab’abb’e

Ajiyar zuciya ammah tayi tace pls Lubabatu ki fahimceni kimin adalci bani nasa auren nan ba Allah ne ya k’addara tun farko su ba ma’auratan juna ba ne

Pls ki k’ara bawa Aunty zuwaira hakuri idan ta huce zanzo da kaina ni da Adda suwaiba mu basu hakuri

Ajiyar zuciya Luba tayi tun Kasu suke tare da ammah tare suka gama karatu suka samu aiki tare dukda a k’awancensu tuni ta gane ammah na mata zurfin ciki bata fad’a mata komai na ta sab’anin ita Luba komai tana fad’awa ammah saidai Luba tasha danganta hakan da jinin fulani da ammah ke dashi su basu tab’a amincewa da mutum d’ari bisa d’ari

Kuma sosai Luba ke k’aunar ammah don haka a dole ta sakko bayan fushin da tayi da ammah tun fara bikin hayfa da haka suka fara hirarsu ta taakaninsu suna d’an dariya saidai ammah a k’asan zuciyarta tanata addu’a kada Allah yasa Luba tazo gidanta taga wayan har sai hayfa ta fara turo mata kud’i ta saya fiye da kayanta na DA inda ita Luba da kanta zata gane hayfa ta auri wanda yafi kamal arziki

Luba ta kalli Ammah tace kunsha hidimar biki dukda ina fushi lokacin nayita tuna ki Amiran GRP tace kin ansa 2m ko?

Ammah tayi yak’e tace “eh” sabida iyayen ango sunyi hidima dayawa gashi lefen yayi yawa gashi naji ance shi kansa tafiyar hayfa ashe kud’i ne sosai shiasa na hana hayfa k’ara tanbayar komai a gun angon

Luba tace haka ne naji su rabi da y’an art sunata labarin lefen wai kamar na d’iyar Lema Jibril

Ammah tayi murmushi tace wlh sosai suka yi k’ok’ari lefen

Itama murmushi Luba tayi tace Allah ya basu zaman lafiya!

Ammah tace amin

Luba tace ni wai ina hayfa suka had’u da mijin na ta?

d’an bugawa k’irjin ammah yayi kafin tace school d’insu ya ganta lokacin graduation shima yaje na k’anwarsa lokacin yazo hutu

Luba tace “eyyah” amma gaskiya yayi gaggawa kenan duka basu fi wata da had’uwa ba suka yi aure?

Ammah tace eh ya nace a lokacin nima na ki sai iyayensa suka je gun baba

Luba tace Allah yasa haka shine alkairi shima kamal Allah yasa masa dangana ya bashi rabonsa

Amin ammah tace!

Sosai bayan fitar Yusuf hayfa tasha kuka kamar ta mutu har zazzab’i ta fara ta lallab’a ta kwanta lamo…

Bayan Yusuf ya tashi pool aikin yamma yaje embassy ya tsaya café aikin dare inda yasir after pool shima ya tsaya café nan suka yi jam’i suka yi sallah bayan Yusuf ya gama aikin yamma kusan 9:11 pm suka nufo gida

Hayfa na kwance zazzab’i sosai dama yasir tuni ya yanke hukuncin da ke sunada d’akin ma’aikata a club so can zai rik’a wanka yana saka kayan aiki domin tun ranar da su Yusuf zasu dawo ya kwashe rabin kayansa ya maida drowersa ta ma’aikata a can zai rika shirin zuwa pool ma

Suna falo yasir ya kalli Yusuf yace “gimbiyarka fa”?

Yasuf ya d’anyi ajiyar zuciya yace maybe tayi bacci

Yasir yace OK suka mik’e duka suka nufi kanta taliya Yusuf ya musu jolof da sardin suka ci suka sha tea sabida lokacin sanyi ne kusan 25mnts 10:04

Yasir yayiwa Yusuf sallama ya wuce aiki

Bayan tafiyar yasir yana son shiga ya duba ta ya kasa saidai ya daure ya mik’e ya shiga tana kwance tana rawar sanyi

da sauri Yusuf ya k’arasa ya yaye mata hijap d’in da ta lullub’a yana tab’a wuyanta sosai ta bashi tausayi ya d’agota jikinsa yana shafa goshinta wani irin numfashin zafi rau take fitarwa

Kallonta yake cike da so saidai shi bashida abinda take tsammanin shine farin cikin duniya wato “kudi”

Ya dad’e da ita kwance jikinsa kafin ya mik’e gani yayi ko kayan sanyi batada tana buk’ata domin ko sanyi Nigeria dole sai da kayan sanyi bare nan da ake k’ank’ara ba

Bayi ya shiga ya kunna heather sabida na yasir nayi ba kamar na gidansa ba ya dawo d’akin ya d’agota tuni ma ta bud’e idanunta da kansa ya cire mata kayan tas itama duk bata da wani sauran kuzari ya d’auketa har bayin ya saka cikin bafh

Ajiyar zuciya tayi ta k’ank’ame jikinta ya barta ya fito ya d’ora mata sauran taliyar ya d’umama ya had’a mata coffee ya fito ya kawo d’akin ya ajiye ya koma bayin ya rik’ota ta gama wankan sosai taji dad’in jikinta ta fito ta fara shafa lotion ya fito falo ya bud’e akwatinsa ya d’auko mata wata suwaitarsa mai wuya da suck ya mik’a mata a dole ta ansa shima jst suwaita shida gareshi kaya na da arha sosai a kasar amma shi nauyinsa ya hanashi tara kayan

Fitowa yayi falo ya bud’e wallet d’insa yaga kud’in sa na wk na pool da ya fara tarawa sayan visa dole ya sayawa hayfa suwaita gobe koda guda 3 da haka ya d’an mik’e domin tunani yayi in yaje pharmacy yanzu kud’in zasu tab’u dayawaKasa baccin ma yayi ya fad’a tunani zaiyi k’ok’ari ya sama musu visa tare yaso sai idan Gizela ta wuce Argentine ya bawa hayfa aikinta shi ya k’ara neman wani a wani gurin ya zama aiki uku idan nauyi na bazai barni na wadata ba aikin zai taimaka mata samun kud’in kashewa da yiwa iyayenta ihsani da wannan tunanin yaji nutsuwa ya same shi ya fara bacci+

bayan hayfa taci abincin ta saka suwaita da wani leggings bak’i tasa suck ta hau gado ta d’anji zuciyarya wasai

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Saidai ta kasa runtsawa yau wata kwana 13 sauran yanzu idan wata ya k’are bata yiwa mominsu aike ba ya za tayi gashi momin tace salarynta yanzu jst 20k take ansa na cire 50k na bashinta ga takardun gidansu a banki kuma momin tace lokaci na tafiya ribar banki na karuwa a kansu

Kuka ta saki sosai cikin bacci Yusuf yaji kukan na ta kamar ya share ta ya mik’e ya zauna ya rik’e kansa

Sosai kukan ke damunsa sam bayason jin kukan ta yanaji kamar yaje ya lallasheta  a dole  k’arshe ya kwanta baccin rabi da rabi yayi har asuba ya shiga tana kwance ya shiga yayi wanka ya shirya yayi sallah yana shan tea yasir ya dawo suka karya tare suka fice domin a shirye yasir ya iso gidan

A café Gizela take fad’awa Yusuf tayi magana da oga ya amince saidai ita jibi xata tsaida aiki sabida zata tsaya cubec daga can zata wuce Argentine

Yusuf cikin farin ciki yace babu damuwa yayi mata godiya ya gama aiki ya wuce pool a pool ya bawa yasir labarin yadda ya tsara sosai yasir ya tayashi murna yace ba kai ba ko anan matasa kamar mu y’an k’asarma in suka yi aure haka suke yi sabida rayuwarsu tafi sauk’i

Yusuf yace eh haka ne ammah ni banaso ta tayani biyan komai ni zan rik’a baka kud’in hayarmu sannan ni zanci gaba da d’aukar nauyinta a matsayinta na matata nauyinta yana wuyana kome ta mallaka

Shagala yasir yayi yana kallonsa yace to in ba zata tayaka d’aukar nauyin rayuwarku ba meye anfanin aikin?

Ni wlh ko Nigeria na auri mace tayi karatu ta samu aiki dole muyi 50%50

Yusuf yace kuskuren dayawan mazan zamani kenan sabida nauyin mace Allah ya riga ya d’aurashi akan namiji saidai matan zamani sun kasance masu yawan sha’awa da k’yale-k’yale na duniya da zamani so namiji bai kamata yasa idanunsa akan samunta ba yak’i sauke mata hakkinta da ke kansa ya barta kawai samunta taji da nata buk’atun wanda basu zama nauyinsa ba a shari’ar aure saidai in don kanta tayi niyya tana taimaka masa da wasu hudimomin gida amma sam ba adalci ba ne kuma bai kamata namiji don kawai matarsa na aiki yace su raba nauyin gidansu da yaransu ba

Ajiyar zuciya yasir yayi yace kace wannan gimbiyar taka zata k’ara fad’in rai in ka fara samun kud’i

Murmushi Yusuf yayi yace Allah yayi mana jagora ga baki d’aya

Yasir yace “amin”

Yasir ya kalleshi yace amma fa gimbiyarka k’arshe ce a had’uwa a yadda naga hotunanta dukda har yau kak’i bari na ganta a zahiri yana dariya

Yusuf ma d’an dariya yayi

Yasir yace kana ganin zata yadda tayi aikin goge tebur da serving d’in mutane?

d’an shiru Yusuf yayi kafin yace “Inshaa Allah”!

Yasir yace kk suka ci gaba da aikinsu.

   A gida hayfa ganin yanzu ba su kad’ai bane gidan ta tsani rainin wayo kada abokin ya d’auketa k’azama

STORY CONTINUES BELOW

ja jiki ta fito har falon ta ga d’an falon duk cike da kayansu tsayawa ta fara yi tana kallo kafin ta fara gyarawa Yusuf akwatinsa da ke bud’e ta rufe rigarsa da ke kan akwatin ta ninke ta d’ora kan akwatin ta jera masa takalmansa domin tasan nasa duka sannan ta matsa gefen akwatin yasir shima guda biyu k’anana ta d’ora d’aya kan d’aya ta jera masa nasa takalman ta d’aga yalolon curtain d’in na window da alama ma daga Nigeria yasir yazo dashi

Kanta taje Ta zuba liquid soap a cup ta zuba ruwa da soso tazo ta wanke glass din window ta gyara falon tas taje ta bud’e akwatinta da aka zuba mata turaren wuta ta d’auko ta d’auki wani silver plate ta saka cakul d’aya na dubai ta kunna ta zuba tuaren mai fitinannen k’anshi

Ta koma ta gyara fridge ta wanke duk aikin nan tana yi tana zaman hutu ko wani 30mnts kafin taci gaba.  bayan Su Yusuf sun tashi pool bayan asar tare suka fara tsayuwa wani butik yusuf ya sayawa hayfa suwaita masu kyaw da sauk’in kudi guda hud’u kafin suka tsaya wuce café inda yasir na ta chart a wayarsa Yusuf na aiki

Bayan hayfa ta gama aiki tuni tayi wanka ta maida suwaitar gurin Yusuf da wani wandon pencil jeans tasa hula da suck tsabar gajiya bata iya jagwalgwala komai ba duk itama tana jin yunwa a dole cornflakes ta sha ta kwanta ganin kusan 9:12pm saidai ma ba bacci take ba duk tunani ne ya isheta na rayuwarta a karon farko taji kewar mahaifiyarta da bata sani ba ta fara hawaye

Bayan sun baro café suna taxi suna hira har suka k’araso gida, jin gidan shiru ba suyi mamaki ba saidai yasir na kunna fitilar falon duk suka shagala da kallon falon

d’an juyawa yasir yayi yana kallon Yusuf inda shi Yusuf ke kallon ko ina na falon ga wani k’anshi na fitina da gidan ke yi

K’arasawa duk suka yi suka zauna Yusuf sosai k’anshin ya tafi da zuciyarsa yana ta lumshe idanu saidai yunwa ya mik’e ya dafa musu wani abu ganin yasir ya kusa wucewa aiki

Yana bud’e fridge dinma yaga yadda yayi tas komai ta jera ya k’ara lumshe idanu sosai yaji sonta ya k’aru masa haka ya dafa musu noodle da sauri ya zubawa yasir sannan ya zuba nasa ya barwa hayfa na ta a tukunta domin ya gane ba tayi girki ba

Suna ci yasir ya kalli Yusuf yace kasan tunda nazo kasarnan ban tab’a gyaran gidan nn ba?

Yusuf yace ko?

Yasir yace saidai sama-sama nayi shara na fice kalli yadda gidan ya zama sabo yau, saidai ya d’an saki dariya kuma yace ko da yake sabuwar mutum ta shigo gidan shiasa

D’an murmushi Yusuf yayi yace ka cika zolaya

Kallon agogo yasir yayi ya mik’e da sauri yace zanyi latti sai da safe

Yusuf yace ka daure ka k’arasa abincin tukuna

A tsaye yasir ya tura sabida duk iskancinsa baya son lattin aiki sabida ya gano d’aya daga cikin dokokin turawa shine zuwa aiki akan lokaci

Yana gamawa ya d’ora plate d’in akan kanta yayiwa Yusuf sallama yace ka gaidamin gimbiyarka ya fice

Bayan fitarsa Yusuf da kansa ya mik’e ya d’auki jakar suwaitar hayfa ya nufi d’akin d’an tsayuwa yayi yana kallonta kusan 3mnts kafin yayi sallama

a hankali ta ansa amma bata d’ago ba

Yace d’ora mata ledar a kan gado yace “gashi” sannan akwai abinci in zaki ci ya fito d’akin.

Mik’ewa yayi kujera ya yiwa aliy flashing ya kunna data suka fara chart kusan 20mnts ganin bata fito ba shima ya share yayiwa aliy sallama ya kashe data zai kwanta yaji k’anshinta ya d’an d’ago kansa yana kallonta

Itama kallonsa tayi ta shiga kantar ta d’auka plate ta juye sauran noodle d’in ta fito daga kantar zata wuce taji muryarsa,  In kika gama kizo muyi magana…

STORY CONTINUES BELOW

Bata ce k’ala ba yana gamawa ta shiga d’akin

Kusan 20mnts after bayan ta gama ta k’ara fitowa d’akin tazo ta ajiye plate d’an ta d’an jingina jikinta da kanta tana kallonsa

Shima d’agowa yayi yana kallonta kafin ya mik’e a hankali tana kallonsa a zuciyarta tana ayyana gaskiya kyakykyawa ne saidai ni bana sonsa sannan uwa uba bayada dalilin da zan soshi wato “kudi”

har gabanta ya tsaya yana kallonta yasa hannu yana shafa fuskarta yace “na san banida kud’in biya miki duk buk’atunki amma ba zance banida k’arfin aurenki ba sabida ubangiji da ya k’addari mu kasance ma’aurata ya ga dacewar hakan shiasa, wata k’ila baya cikin tsarinki auren talaka amma ki gwada karb’ar k’addara ko hakan zaisa Allah ya nuna miki hikimarsa na had’aki da talaka

Ya d’anyi shiru yana kallonta duk jikinta ya fara sanyi sabida a islamiyyar su sosai ake musu wa’azi akan duniya da rayuwa tasan komai daidai gwargwado saidai gaskiya sun rigada sun tsara rayuwarsu akan mai kud’i zata aura

shi ya dawo da ita tunaninta… Ki karb’i k’addarar aurenmu kamar yadda nima na karb’a wata k’ila Allah zaifi sama miki mafita akan kome kike so

d’agowa tayi tana kallonsa “yace bance ki soni dole ba ko ki zauna da ni dole ba amma kada kiyi gaggawar yanke hukunci akan hukunci Allah.

Sosai maganar ta shige ta

Yace na san baki saba wahala ba amma banida yanda zanyi na canza tsarin Allah ki shirya na samo miki aiki jibi zaki fara

da sauri ta d’ago tana kallonsa

Yace eh amma bawai na samo miki bane don ki rika d’aukar nauyin kanki ah ah nine Allah ya d’aurawa nauyinki kuma zanci gaba a daidai abinda Allah ya huwacemin saidai na samo miki aikin ne don ki rik’a samun kud’in kashewa ko na yiwa iyayenki ihsani idan buk’atar hakan ta taso

Sannan ga wancan wayar na saka miki drower idan kinason anfani da shi kafin….

da sauri itama tace ah ah ba zanyi anfani da shi ba zan turawa momina

Kallonta yayi cike da mamaki saidai ya basar yace shikenan ki bani address d’inku na gida gobe zan tura mata in na fita

ita hayfa bata san ma sadda ta fad’a masa haka tsabar son da take taga ta fara yiwa ammah aike na kud’i da komai ma inda zata samu

shiru basu k’ara magana ba ya koma ya zauna yayinda itama ta ja jikinta a hankali ta wuce d’aki

da sauri ta jawo k’aramin akwatinta ta d’auki Biro da paper ta rubuta masa komai na address d’insu da sunan ammah da lambar ID card d’inta ta fito a hankali yana mik’e kujera ta mik’a masa saidai Yusuf da yau hayfa ta sashi farin ciki ta nunawa yasir matsayinsa na mijinta abinda bata tab’a yi ba a wancan gidansu tayi anan sosai Yusuf ke jin sonta

Maimakon ya karb’a paper sai ya had’a da hannunta ya jawota ta fad’o jikinsa ya rungume ta sosai yana ajiyar zuciya

Tana son zamewa ta kasa jin yadda zuciyarsa ke harbawa kan nata zuciyar d’an shiru kawai tayi ta kwantar da kanta k’irjinsa

Kamar wasa kujerar babu wani dad’in bacci a haka bacci ya kwashesu sai daf asuba hayfa ta farka pad d’inta ya jik’e zata canza

Shima farkawa yayi ta mik’e ta wuce d’akin shima ya mik’e ya zauna yana tunanin idan ya cigaba da lallab’ata kamar haka ya tabbata zai mallaketa saidai raini ne bayaso ba kuma zai d’auka ba sai kuma yana jin bazai tab’a iya jure rayiwa babu ita ba.  Mik’ewa yayi ya nufi bayin hayfa fitowarta wanka kenan tana saka pant da pad ya wuce bayin

Kusan 25mnts ya fito ta saka wani jan gown shadda yayi mata mugun kyaw d’an kallonta yayi ya wuce falo ya shirya yayi sallah ya had’a tea yana cikin soya kwai yasir ya dawo a shiryensa suka fara karyawa saidai Yusuf ya tsinci kansa da son kasancewa da matarsa ya d’an kalli yasir yace bari na zo ya mik’e

Plate ya d’auka yasa mata slides bread uku da kwai ya had’a mata coffee d’in tana zaune da wani american novel ya shiga d’an d’agowa tayi jin k’anshinsa saidai ta sunkwi da kai haka kawai ta fara jin nauyinsa

d’an tsayuwa yayi yace “zaki karya yanzu”?

ah ah tace cikin sassanyar muryarta da tsabar yangar nan na ta

“OK” yace ya k’arasa inda ta ke yayi mata peck a kumatu ya fito.

Shagala tayi tana kallon bayansa har ya fito…

Yana fitowa suka wuce yasir na ta tsokanarsa gaskiya kana ji da wannan madam d’in ta ka

Haka kamar kullum Yusuf ya tsaya café yasir ya wuce pool bayan Yusuf ya gama da café ya wuce kamfanin Fidex na tura sak’o inda ya aikawa da ammah wayar ya basu number ta zasu tura mata txt na ansar sak’on

Ammah na office lokacin 11:03 am duk tunani ya isheta yanzu hayfa kusan 2mths da aure basu fara rage bashi ba banda na albashinta kawai kuma tasan laifin hayfa ne da ke addaba mijinta da girman kai in ba haka ba tunda suka yi aure yaron ta lura yadda yake girmamata domin yana yawan kiranta ba ma tare da sanin hayfa ba

dake tazarar 4hrs ne tsakaninsu da hayfa ammah na cikin tunanin  taga shigowar text daga kamfanin fidex ta bud’e taga wai tanada sak’o daga Toronto

Cikin rawar jiki ta jawo jakarta tana Allah yayiwa hayfa albarka lek’ewa tayi office d’in luba tace mata tana zuwa dama ta gamawa yara period d’inta

Koda ta isa ta cike form suka bata kwalin bata bud’e ba saida ta dawo office d’inta ta kulle ta bud’e saidai wani mugun ajiyar zuciya tayi ganin iPhone 11 pro ba k’aramin murna ammah tayi ba ko babu kud’i wannan ta saida yanzu sosai zata fara kashe wutar gidanta domin kudinsa tasan ya bawa 300k baya

Sosai ta k’ara sawa auren hayfa da Yusuf albarka tare da fatan mutuwa ce kawai zata raba su.

Waya ta d’auka ta kira suwaiba ta bata labarin hayfa ta fara yiwa miji biyyaya suna dab da cika burinkansu nan suka kara farin ciki da samun Yusuf a matsayin cikar burinsu

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]