[Advertisements⬇️]

KASAR WAJE CHAPTER 2 BY MARYAM DATTI - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

KASAR WAJE CHAPTER 2 BY MARYAM DATTI

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Sannan amma ta bata wayarta tace ki masa flashing yanzu zai kiraki kuma ki saki jikinki kamar kun shekara tare

“Toh” kawai hayfa tace batason mijin amma jin zata k’ara kece raini da kuma burinsu da yayyunta zai cika yasa ta amince dukda gaskiya taso a ce shi ya biyota, kuma sam bata tunanin kamal duk da ya kan fad’o mata wani sa’in

Yusuf na kiching d’insa yana dafa shinkafa wayarsa ta fara ringing ko kafin ya d’auka tsinke

Da ya duba yaga Nigeria ne number da aunty ammah ta bashi ya maida kiran

Hayfa na son yin yangarta da ta saba zazzagawa maza suna binta kamar wawaye

ammah ta daka mata tsawa ta ansa wayar saidai ta kasa magana

Yusuf jin shiru yayi sallama a cikin muryarsa kamar ba namiji ba

ta ansa sallamar

Kusan suma Yusuf yayi domin muryarta kawai ya k’ara kunna masa wani gobarar Sonta

Gaisheshi tayi kawai tayi shiru su ammah na kallonta

Ayyanawa Yusuf keyi a zuciyarsa tafi surutu a chart kalla yanzu direct call tak’i magana sai yaji ta k’ara burgeshi

shiru shima ba gwanin surutu ba yace “zanci abinci yanzu mu had’u online anjuma”

“Toh tace suka yi sallma”

Su ammah suka k’ara ja mata kunne yadda zata saki jikinta dashi domin kusan mijinta ne ma shi yanzu

Ita hayfa da aunty amma ta koyar da ita jiji da kai na fitina da ko masu kud’i suka biyota haka take taka su koda zata saurari mutum amma kawai wannan ace ita zata rik’a lallab’ashi ay bazai yuwu ba gara shima ko waye ubansa yasan ita bata wasa bace

Abin mamaki wann duk yarinya mai 17yrs ke da bak’in buri da son duniya haka

Da yamma suka had’u a wpp sama-sama take bashi ansa

shi Yusuf mamaki ne ya isheshi kamar ba itace ke nace suyi ta chart ba nan ta bashi aunty ammah suka gaisa yayi mata bayanin zai turo magabatansa ta amunce

Kamar da wasa alhaji sammani yazo neman auren hayfa gun mujin ammah domin babnsu hayfa yace ya bawa mijin wuka da nama tunda su suka raine ta duk da kuwa shi ba wata tsiya yake tsinana mata ba iyakarta zaman gidan sa hasalima basu sashi cikin harkar samarin hayfa sabida shi ya dad’e yana cewa ammah ta bawa kamal hayfa ganin hidimar da yake da hayfa ba gajiyawa gashi shima iyayensa masu kud’ine sanan shima mai kud’ine gashi har gidan kansa yanada sannan ance albashisa ya kai 500k

amma ammah tace ko a mafarki hayfa tafi k’arfin auren kamar kamal, haka ya zuba musu ido!

Mijin ammah ke bata labarin yasan alhaji sammani babban attajiri ne yana harkar estate  kema bakyajin sunansa?

“Eh” tace inaji nan ta k’ara sakankancewa Yusuf d’an wani k’usan mai kud’i ne

Aka saka rana inda za ‘a kai amarya gidan alhaji sammani daga can ranar da zata bar Nigeria zata wuce kano sai Toronto

Haka kuwa akayi dukda maman Yusuf na cikin rashi hidima ta musu yawa aliy ne ma ke zuwa ya bata d’an 3k ko 5k Yusuf 4mths kenan bai musu aike ba, sai k’anninsa maza bayan sun dawo boko suna zuwa dako aliy ya sama musu da ke suma sunada zuciya kamar Yusuf da haka suke taimakawa kansu suka ma daina tsammani da ga Yusuf

STORY CONTINUES BELOW

Haka ta tashi ita da wata goggonsu da tazo da d’an uwan babn Yusuf suka wuce Kaduna gidan sammani itama matar alhaji sammani jin yanzu Yusuf na k’asar waje da girmamawa ta karb’i mamansa da danginsa tace ayi komai gidanta

Ta b’angarensu hayfa Alhaji sammani ya bada tasa gudunmawa inda ya biya halls biyar da za’ayi shagalin biki

anyi party kala biyar, murtala square, a arewa house, Assa pyramid, hotel17, Adeyomo Event!

anyi arabiyan nyt bridel shower, Fulani day, kanuri day, sisters day, su ammah an kashe kud’i a dole ta nunawa duniya k’anwarta na auren d’an attajiri dake zaune k’asar waje

Inda sosai suka b’ata ita da k’awarta k’nwar maman maman, inda shi kamal bai damu ba sabida asirin da suka musu shi da hayfa

Ammah da kanta ta fad’awa Yusuf akwati 12 suke so kuma na kamfanin Luis vilton na ainahin zuwan France basuson komai bayan haka tunda amarya tafiya za tayi.

haka Yusuf da ba ya cikin hayyacinsa ya  fad’awa alhaji shamsu buk’atar iyayen amarya aka had’a masa kaya kala 223 less atmfa da shadda materials da dai kaya na fitar hankali da jankunkuna takalma designers inda alhaji shamsu ya masa lissafin lefe yaci kusan 6M sai kud’in hidimar shigarta Toronto 3M haka aliy yaje da lauyansu kamar yadda Yusuf yace suka yi signing da lauyan alhaji yanzu alhaji shamsu na bin Yusuf kusan 13M

Haka aliy ya kai lefe Kaduna gidan alhaji sammani kamar yadda Yusuf ya bashi umarni dukda sosai ya girgiza da al’amarin auren na Yusuf kai abin dai ya girmi hankalin kowa jama’a sai san barka suke

ita maman Yusuf sabida kunya na Fulani kuma d’an fari bata ko je inda lefen ya ke ba!.

   Bayan su Aliy sun wuce Kano aka fara shirin kai lefe gidan Ammah

matar alhaji sammani ta gayyaci manyan gungun k’awayenta y’an bokon kaduna  masu kudin Kaduna zuwa kai lefe gidan Aunty ammah motoci 11 na gidanta da na k’awayenta ne suka d’unguma kai lefen

Gidan ammah cike yake da danginsu na iyaye da mak’ota y’an unguwa dayawa ma y’an gulma ne

Ammah Amira rentals ta kaiwa hidimar kayan ciye-ciyen karb’ar masu kawo lefe

An kawo lefe jama’a sai san barka suke wasu na fad’ar lallai burin ammah ya cika na yadda ta raini k’anwarta kamar y’ar attajirai yarinya sai shegen jiji da Kan tsiya bata bar mata ba bare mata ita a dole tafi k’arfin kowa a kawo

haka a hidimar bikin babu ko budurwa d’aya y’ar kawo ko badarawa yaran mak’otan gidan iyayenta.

….

Duk sai y’an zamani college da almannar motoci kawai ke zuwa dire y’an mata yaran manya anzo biki

K’awarta salma baita ta fitar musu da ashobi na y’an zamani college 35k kuma babu wacce bata saya ba.

A gefe ammah da suwaiba suka k’ara zuwa grp d’in taimako na gurin aikin ammah suka ci bashin 1M za a rika cirewa a albashinta suka sallami y’an kawo lefe da 150k inda matar alhaji smmani da k’awayenta suka yita mita sun raina haka dai aka rabu babu dad’i sosai.

inda itama matar alhaji sammani ta ansa kudi sosai gun mijinta tayi taro a gidanta domin wani buri da itama ta k’udire tunda dai yanzu Yusuf na kasar waje yayi kudi

Kwana biyar su ammah suka yi taro shima alhaji sammani a karon farko yayiwa amininsa kara inda ya turawa su ammah saniya da kayan abinci buhun shinkafa biyu da su carton taliya couscous macaroni dadai alot da kudi 100k na kayan miya

Abin mmaki mafi yawan mutane a wannan zamanin ba suyin kyawta sai ga mai shi domin suna tsammanin wata rana ya maida musu kamar yadda yanzu suke wa Yusuf hidima a tsammanin mai kud’i ne

STORY CONTINUES BELOW

Yau juma’a bayan sallar juma’a aka d’aura auren Yusuf da hayfa a masallacin sultan bello akan sadaki 100k alhaji sammani ya biya inda dama an gamawa amarya komai na wucewa gurin mijinta a washegarin ranar

Da yamma iyayenta da dangi suka mata nasiha sosai yayinda yayyunta suka k’ara keb’ewa suka jaddada mata hud’ubar da suke mata tun tana 11yrs cewa auren wanke musu talauci za tayi

Sosai suka k’ara tuna mata hidimar da suka dad’e suna kashe Kansu sabida ta samu irin mijin da ta samu yanzu don haka tana zuwa ta maida hankali wajen turo abin duniya da daloli sannan ta fara school tana isa sabida karatun shima tabbaci ne na k’arin arzikinsu

Haka suka sha kuka su duka uku kafin da kansu suka kaita har gidan alhaji sammani a aliyu turaki rd inda gidan ya k’ara susuta su ammah sabida girma da kyawunsa

An kai amarya d’akin innarsu Yusuf da danginsu suka mata nasiha kanta na k’asa saidai innarsu Yusuf hankalinta ya d’an tashi ganin irin mutanen da suka zo kawo kayan gara ga garar kamar za’a bud’e shago a kasuwa  yarinyar y’ar manya ce anya Yusuf zai iya..

Haka dai aka gama nasiha aka kai amarya d’akin wata y’ar alhaji sammani da za suyi sa’oi da hayfa

Saidai tsabar jiji da kai irin na hayfa bata wani saki jiki da yarinyar ba mai suna Ramlat itama ta gama school a future leaders international.

da safe alhaji sammani ya bada motoci hud’u hayfa da tulin akwatunanta 15 da danginsu Yusuf inda za’a sauke hayfa airport tukuna suma a saukesu gidansu Yusuf

Ammah tazo a gurguje suka k’ara sallama da hayfa Haka hayfa ta wuce tanata hawaye domin batada waya duk wayoyinta sun sayar a hidimar biki yayyunta sunce tana isa Yusuf zai saya mata wanda yaci uban iPhone 11 din da kamal ke saya mata duk wata hud’u.

A Toronto Yusuf yayi shara mopping wankin toilet dama kiching falo ne don haka bai da niyar turawa alhaji shamsu kud’i wannan watan shopping yaje yayi babu laifi ya zuba fridge ya wuce aiki bai fad’awa Yasir ba

Ganin jirginsu hayfa ya kusa sauka ya gama aiki da wuri aka biyashi ya wuto gida cike da murnar zuwan amaryar tasa

Wanka yayi ya saka wata shaddarsa da aliy ya d’inka masa da zaizo Toronto dark blue daidai jikinsa yasha kyaw yasa cover shoe bak’i babu safa abinka da fari yayi kyaw domin sosai Yusuf ya canza shigowarsa Canada zaka tsammanin yayi shekaru sabida yayi kyaw abinsa kamar wani halfcast yayi fresh saidai rashin takatdun hatkar duniya lol

Ya saka hularsa Kube mai arhar yaje mirror din toilet yana kallon kansa d’an murmushi yayi sosai yake jin nishad’i a ransa yana mamakin wai shine yau shine ango da haka ya fito ya nufi airport….2

Koda jirginsu hayfa ya sauka a Toronto tana zaune kan wani benci ga akwatunanta a lode a gabanta ga sanyi na fitina a nayi duk takaici ya isheta har yanzu baizo ba bai turo driver ba

Abin dariya nace “wasa farin girki”

taxi na saukeshi ya nufi cikin airport d’in da d’an hanzari yana kalle-kalle ya kuwa hangota domin Aunty ammah ta tura masa pic d’in kayan da hayfan zata shigo Toronto dashi

A hankali ya k’arasa yana tsaye yana kallonta zuciyarsa na wani mugun harbawa sosai yarinyar ta tafi da imaninsa saidai baya so ta gane da wuri sai sun k’ara fahimtar juna

A hankali da idanun gajiya ta d’ago jin wani siririn k’anshi a kanta tasan turaren yanada arha sosai wani d’an class d’insu Marwan yana anfani da shi su salma baita su yita masa dariya suna tsokanarsa

Idanunta suka fad’a cikin nasa d’an bugawa taji k’irjinta yayi wai miji sai yau ta fara ganinsa tayi maza ta cire idanunta ta d’aure fuska

Jin muryarsa tayi a hankali “sannu da zuwa”

Bata ce k’ala ba ya fito ya kira taxi biyu d’aya ya kwashe mata rabin kayanta d’ayan kuma suka shiga tare da sauran kayan

Kasa rufe k’ofar taxi d’in yayi ganin hayfa tsaye

Kallonta yake a hankali yace “ki shigo muje”

A dole ta shiga ta manna jikinta ta b’angaren window saidai tunani

A zuciyarta tana tanbayar kanta shi to ina motarsa ko ta gidansu da zai saka mutane shiga taxi

Tana can tanata tunani taji yace “mun iso”

Kallonsa tayi kusan 5mnts kafin ta fito a hankali ya zaga ya rufe ya fito da wallet ya sallami taxi din kafin tana tsaye ya k’arasa gun wanda ya kwaso kaya shima ya sallameshi wallet din nasa ya zama empty!

Tana tsaye taga yanata d’aga akwatinanta yana ajiyewa k’ofar wani d’aki

Kallon gurin tayi dogon ginine sosai yakai k’ofa 8 saidai ko wani dakalin k’ofa anyi d’an tsakani da katako irin nasu na turai

Mamaki ne ya isheta hotel ko motel ya kawota maimakon gidansu saidai bari yanzu tana gajiye za taga iya gudun ruwansa

Ya gama jera akwatunan tana tsaye turawa makota na ta wucewa ganin ta k’i motsawa ya k’araso ya rik’o hannunta ta fusge ya d’ago yana kallonta ta dalla masa harara saidai a dole sabida gajiya da take ji tayi bakin k’ofar ta tsaya yazo ya bud’e suka shiga

Wani irin k’ululun bak’in ciki ne ya k’ara tokare mata k’irji wai meye wannan guy d’in yake nufi ne?

ya kawota wannan akurkin falo ko mutum biyu baza su sake ba a ciki

ya gama shiga mata da akwatinanta da tuni suka cika bedroom tam babu wani sauran space

Bayan ya gama shiga mata da akwatinan ya fito falo tana inda ya barta tana k’arewa falon kallo fuskar nn sam babu annuri+

babu komai sai wata siririyar 3sitters da k’aramin carpet sai hanger na katako a manne a bango na rataye jacket da jaka in mutum ya dawo gida ta juya taga y’ar k’aramar kanta da aka zagaye da k’aramin fridge manne da gas mai burnner biyu sai kanta layi d’aya a sama d’auke da y’an k’ananan tarkacen kiching

Wani irin takaicine ya cika zuciyar hayfa wai nan akurkin waye ya kawo ta

Muryarsa ta jiyo “muje kiyi wanka kiyi sallah kici abinci sai ki huta”

A dole ta bishi suka shiga d’an bedroom d’in mai kama da d’akin kiwon kaji babu ma hanyar da zasu wuce ta shiga ciki a dole ya kwashe akwatunan ya dorasu kan gado wani kan wani cikin tsananin b’acin rai hayfa ta wuce ta shiga bayin

Ganin haka Yusuf ya saka akwatunan cikin d’an wardrobe d’in wani kan wani guda shida tunda dama shi akwatinsa d’aya ne k’arami wasu a dole ya dawo dasu falo sabida babu guri a bdrm falon ma babu guri

Kiching d’in ya tsaya ya d’ora shinkafa sannan ya fitar da fresh nik’ak’en kayan miya yayi mata stew da sardin kafin kace me har falon ya gauraye da k’anshi ya zauna ya fara tunanin yanayin da take masa tunda ta iso kamar ba ita ta nace masa ba saidai a k’arshe yace k’ila gajiya ce zata warware

Bayan hayfa ta fito wanka ta zauna gefen gado duk ranta a b’ace a dole ta bud’e d’ayan akwatin dake gefen wardrobe ta fito da wata rigar shadda ta saka bata shafa komai ba ta saka hijabi ta fara sallah d’an surk’ukin guri a gefen gadon ganin yadda ya bar dardumar ta gane nan ne gabas

Bayan ya gama girkin ya zuba a plate ya jera ya yanka mata fruits a wani plate da d’an k’aramin drink na roba ya kai mata har d’akin

Mugun kallo tabishi dashi ta cire idanunta..

A hankali ta tsinci muryarsa “ki daure kici sai kiyi baccin gaba d’aya ki huta”!

Banza tayi dashi saidai gaskiya tanajin yunwa don haka ya bar mata ya dawo falo!

A dole ta daure ta d’anci abincin ta sha fruits sosai domin dama ita mai son fruits ce

Bayan ta gama ko kwashe kwanukan bata yi ba domin haka ta saba a gidansu ta karkad’e gadon tayi kwanciyarta ta runguma da fillow

Yusuf jin shirunta yayi yawa ya lek’a ga mamakinsa ya ganta gado tanata bacci hankali kwance

Tsayuwa yayi yana kallonta kusan 5mnts ya kwashe kayan ya fito yayi shiri shima ya kwanta falo dukda kujerar a takure yake babu fad’i sannan tsawonsa yafi kujerar.

da asuba bayan tayi sallah ta sake komawa saidai sanyi ya addabeta ta fito da wata abayarta ta lullub’a ganin ko arzikin bargo Yusuf baida

Sosai take tunani sannan ranta a matuk’ar b’ace wai mafarki ta keyi ne mai yake faruwa da wannan guy d’in?

Shima Yusuf dama da yayi sallah yake fita aiki sabida train yafi sauk’in kud’i akan taxi in kuma baka fita da asuba ba sai kayi missing train

Akwai bread da d’an abubuwa na abinci don haka ya rubuta mata d’an note “ina fata kin tashi lafiya?” Na wuce aiki.

Yana aiki yana tunani dole ya nema wani aiki sam in ba haka ba bazai kai labari ba

Yasir yazo yana kallonsa yace wai mutumina kwana biyu duk ka zama wani iri har yanzu akan yarinayr ne?

STORY CONTINUES BELOW

Yusuf yayi d’an yak’e yace no ina missing d’in innata ne da k’anninna

Yasir yace ay dole nima haka nake fama kuma in mutum yanaso ya sami takardar kasa dole zai zauna cikin kasar tsawon 8yrs baije ko inaba har kasarsa kafin ya samu takardun zama d’an kasa

Zaro idanu Yusuf yayi yace kai?

Yasir yace Allah wannan tsarin haka yake a America France Canada germany spain italy brasil australia belgieum da wasu dayawa daga k’asashen turawa.

Shiru Yusuf yayi tab ashe aiki ne sosai gabansa.

Kallonsa Yasir yayi yace wai kai kullum kak’i zuwa gidana sannan kak’i kaini naka saidai mu yita had’uwa nan haka bai kamata ba!

Kallonsa Yusuf yayi yace kai yanzu shekararka nawa anan?

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Yasir yace 27mths visa ta ta 3yrs nayi amma na fara tara kudin sabon visa da zarar wannan ya k’are sabida na biya yayata kudinsu kusan rabi yanzu dukda kudin dayawa, nima yayata ta bani bashin gadon yaranta sai mamata ta saida wani filinta tamin ciko duk haka na ke biyansu ko wani wata

Shiru Yusuf yayi tab abin babu sauk’i ga visarsa ta kusa k’arewa ga na hayfa tare zai k’are da nasa

d’an dafa shi Yasir yayi yace karka damu kaidai kabar maganar mace yanzu sai bayan kayi satlin k’afarka ta kama k’asa sai kayi

Shiru Yusuf yayi domin ya rasa mai zai cewa Yasir shi sam baya jin nadamar auren hayfa ko na second duk kuwa da har yanzu baisan yadda aka yi suka yi auren cikin gaggawa haka ba saidai fatansa ya warware basusukansa.  Koda hayfa ta tashi tayi wanka ta jefa doguwar riga ta fito falo hango k’aramar red paper tayi a gefen kantar gas ta d’auka ta karanta tayi tsaki

d’an zama tayi kujerar tana tunani itafa bata gane inda guy d’in ya nufa ba yana nufin nan ne zasu zauna?

Da sauri tace ina bazai yuwu ba ay ko gidan da kamal ya fara gyara mata tace bataso ya sanja gidan na halliru d’an toro rd unguwar rimi gidan 3bdrms ne da 4toilets d’aya a falo sannan ko wane room da nasa ga falo uku ga stor biyu

sannan ta auri d’an attajiri ya kawo ta nan sabida wulak’anci hala y’an gulma sun fad’a masa iyayenta talakawa ne shiasa ay kuwa bari ya dawo ita ba zata d’auki raini ba gaskiya saidai kasuwar ta watse

Abin mamaki ashe ma auren kasuwanci ne Allah ya kyawta!

Bayan Yusuf ya tashi aiki ya d’an tsaya ya saya musu fruit kad’an sabida kada kud’in yayi k’asa dayawa yanaso komai yaya ya daure yayiwa alhaji aiki nx mth

Bayan hayfa tayi magrib ta d’an had’a cornflakes tasha ta kwanta har yanzu dakwai gajiyar biki da hanya jikinta tanason waya da aunty ammah saidai babu dama tana jira ya dawo ta fad’a masa gaskiya a gobe ya sayo mata waya

Yusuf yayi lattin samun train sai kusan 8pm ya k’araso gida hayfa na d’aki tana bacci tunda ko TV babu a gidan

Bayan ya shigo ya lek’a yaga tana bacci ya dawo falo ya d’umama sauran shinkafar jiya ya ci yasha tea ya shiga wanka ko da ya fito ya ganta ta farka

Tsayiwa yayi yana kallonta doguwar rigar material ce jikinta ya d’ameta a hankali kamar babu domin duk hallitarta a waje take

d’aure da tawul a k’ugunsa ya k’arasa inda take kwance ta runtse idanu ba bacci take ba ya sani

Shafa fuskarta ya fara yi a hankali idanunta na rufe, hayfa da itama shock d’in da su ammah suka had’a yayi d’an tasiri a kanta ta tsinci kanta da kasa hana Yusuf abinda yake

Ci gaba yayi dukda shima farkonsa kenan wato d’an koyo

A hankali ya rik’a bin jikinta yana shafawa ta d’an fara tsorata amma ikon Allah ta kasa hanashi shi kuwa yaci gaba

Hardai al’amari yayi nisa sosai sai ga Yusuf ya cire mata rigarta yana kallon cikkaken k’irjinta harda had’iyar yawu

Shafata yake sosai ya cire mata bra d’in ya wani wawushi k’irjin da hannunsa ganin girmansu yana shafawa ya kai bakinsa yana tsotsa

D’an nishi ta fara yana ci gaba abin mamaki haka ya hillaceta ya samu ya fara k’ok’arin shigarta saidai jinta a kulle ya k’ara azama inda hayfa ta saki k’arar azaba Yusuf jin k’arar da sauri ya zare abinsa a hankali cikin tausayawa yana kallonta

Saidai yana zarewa daga jikinta yaji kansa ya wani irin sarawa harda jiri ya sunkuya hannunsa rik’e da kansa idanunsa a runtse

Ita kuwa hayfa tanata hawayen azaba

Kusan 1hr Yusuf kansa ya lafa ya d’ago yana kallon hayfa saidai yanata tunani me ya kawota nan yaushe kuma tazo?

K’ara rik’e kansa yayi, yayi shiru ya dad’e tunani nan komai ya fara dawo masa daga ranar da suka fara chart da ammah

Kallon d’akin yayi da kyaw yaga akwatina a lot sam ya kasa gane komai a hankali ya mik’e ya nufi falo ya d’auki wayarsa ya yiwa Aliy flashn ma’ana ya hau online

Wannan al’adarsu ce in d’ayansu ya hau online d’ayan bayanan

Aliy na ganin haka ya hau ya fara tsokanarsa da “ango kasha k’anshi”

Mamaki Yusuf yayi sosai ango?

Daurewa yayi yace aure kuma Aliy?

Aliy yace amma dai kai d’an rainin wayo ne, ko sati kayi dayin aure ba nan kasa alhaji ya had’a lefe na duniya kamar zaka auri y’ar Dantata ba nayi maka magana kace babu komai amaryarce tace haka zaka had’a lefen sannan ina alhajine yayi mata komai ta zo

Yusuf na ta sauraron aliy lallai yayi tab’argazar da bai sani ba shi yanzu yaci bashin har kusan 12M innalillahi kawai yake maimaitawa yaji muryar aliy

Gaskiya abokina nasan soyayya amma kayi gaggawa da ka bari atlst ka gama biyan naka kafin kayi aure yanzu shekara nawa za kayi kana biyan alhaji bare har ka fara tara na kanka ni nama yi mamaki yadda ya amince maka gaskiya

Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace mu had’u gobe kaina na ciwo sosai ya kashe datar ya kama kansa

Yana gun har asuba bai runtsa ba hayfa kuwa azaba ya sata baccin dole

da asuba da k’yar ta d’aga jikinta ta fito ta d’ora ruwa gaz taje ta gasa jikinta sannan tayi tsarki da ruwa mai d’umi sosai kafin taji dama tayi sallah ta koma bacci

da asuba Yusuf zazzab’i ne ya dameshi ya kira Yasir yace yayi masa aikin safe zaizo na hantsi baya jin dad’i

Yana falo wajajen 11:am hayfa ta fito sanye da wani irin doguwar rigar super ya d’ameta kamar ma da k’yar take numfashi

kallonsa tayi a yatsine tace “inada magana”

d’an d’agowa yayi shima yana kallonta sosai a karon farko sosai yake jin sonta

tabbas tun ranar da ya fara ganin hotunanta ya kamu da sonta amma yanda akayi ya aureta ne da sauri haka ya kasa fahimta

Jin shiru baice k’ala ba tace “da farko ina buk’atar a sayamin waya yau kuma gaskiya ka kaini gidan da ya dace dani bazan iya zama a wannan ramin ba

sosai Yusuf ke kallonta tana maganar babu annuri ko kad’an a fuskarta

a hankali yace inace mace tana zama ne duk inda mijinta ya ajiyeta?

Tsaki tayi tace “ni banyi aure don inzo zama irin wannan ramin ba ko a Nigeria ban tab’a saurayin da yake rayuwa akurki kamar nan ba bare a kasar waje sannan wai miji

Shima d’an tsaki yayi tun jiya ya lura yarinyar na da jiji da kai dayawa duk son da yake mata ba zai d’auki raini ba

Yace haka ne!

amma yanzu nine mijinki kuma nan nake zaune na ke rayuwa don haka nan ne gidanki Mugun harara ta masa ta rasa mai zata k’ara ce masa lura da tayi shima mugun jiji da kai ne dashi+

Mik’ewa yayi ya k’arasa har gabanta yana kallonta yace “sannan ya kamata ki gane ni ba saurayinki ba ne mijinki ne so ki gyara takunki don bazan d’auki iskanci ba ko kad’an ya wuce d’akin yaje yayi wanka ya saka kaya ya wuce tana tsaye inda ya barta

Sai bayan fitarsa ta zauna gurin ta fara hawaye sosai mai yake faruwa da ita? Sam babu wanda ya tab’a k’ask’antata kamar haka iya tsawon rayuwarta kuku ta fashe da shi sosai

Nigeria

Kamal na office yaji kansa ya sara masa nan ya fara tunano hayfa sosai ina take kuma mai ya faru da ita?

d’an ajiyar zuciya yayi sosai yake matuk’ar son hayfa zaiyi komai domin ita tunani ya koma na ranar da ya fara ganinta sunje gaida mamarsa lokacin haihuwar k’aninsa ita da aunty ammah da k’anwar mamansa Aunty Luba lokacin hayfa na jst 14yrs tana js2

Tunawa yayi da yadda yayi ta korar masoyanta ba tare ma da saninta ba ya tuna yadda suka b’ata kwatakwata shi da abokinsa Faisal babansa ambassador ne a dalilin Faisal din ya kamu da son hayfa

Shiru yayi yana kiyasta irin son da yake mata mara iyaka yana tashi office zai wuce gidansu ya dubata da haka ya ci gaba da aiki cike da begen hayfa.

ammah na kwance tana tunanin inda zata tura laraba ta samo mata caji ta nema hayfa ganin sun kwana babu nepa ita kuma ta sayar da generator d’inta wajen hidimar biki ga daddyn yara tun kan ta tashi ya fita a dole ta koma ta kwanta tana jiran zuwan laraba domin tasan hayfa anacan ana amarci kila ma sun bar kasar da sunje yawon kasashen duniya honeymoon, d’an murmushi tayi tana k’ara godewa Allah da ya cika musu burinsu cikin sauk’i da rufin asiri da haka ta koma ta kwanta yara duk sunje makaranta.

Hayfa tasha kuka sosai kusan 2hrs babu d’an adam da ya tab’a sata kuka kamar haka sai Yusuf tabbas zata rama kuma dole kasuwar ta watse tunda k’arya ya musu shi ba mai kud’i bane to ita da bata da waya ya za tayi tayi magana da mominsu?

Mik’ewa tayi a hankali zata shiga d’aki saidai cikin mamaki ta hangi wayar Yusuf a gefen kujera da alama mantawa yayi

da sauri ta k’arasa ta d’auka ta kunna haske taga babu wani security code ko Patten a wayar don haka jikinta na d’an rawa ta fara shigar da number aunty ammah

Saidai cikin rashin sa’a wayar na kashe tayi Ya kai sau biyar a kashe da saura ta fara shigar da na sa’idu mijin ammah wanda suke kira da daddy ita da yaransa da ke ta haddace number ammah da nasa da na kamal da na k’awarta salma baita

Jefa kiran tayi ya fara ringing tayi ajiyar zuciya

Daddy na zaune shagon surukinsa yazo gaisheshi da ciwon k’afa wayarsa ta fara ringing ya d’aga

hayfa ta masa sallama ya ansa ta masa tanbaye-tanbaye da kowa ya mata ban gajiya tace

Daddy mominmu fa? Na kira layinta baya shiga

Yace eh mun kwana babu wuta har yanzu kuma generator yana gun gyara domin haka ammah ta fad’a masa

Ajiyar zuciya tayi za tayi magana yace ina gurin baba ne gashi ki gaisheshi ya mik’awa babanta waya,  Sallama tayi a hankali ya ansa

Tace baba kuna lafiya? Yace lafiya lau auta!

Yace kin isa lafiya ko? Eh tace tayi shiru…

daddy ya mik’e yad’an yi nesa da tunanin k’ila hayfa suyi magana ta d’a da mahaifi da babanta

STORY CONTINUES BELOW

Ajiyar zuciya malam haladu yayi yace auta dama inaso na k’ara miki nasiha bayan wacce duk dangi da y’an uwa suka miki

Ajiyar zuciya hayfa tayi tai shiru…

Yace inaso kiyi koyi da y’an uwanki wajen juriya da jajircewa y’an uwanki ban musu kwatan gatan da suka miki ba makarantar gomnati suka yi daga farko har k’arshe, lokacin aurensu ban basu komai ba su da gogonsu suka yi komai inda bayan aurensu ammah ta saida kayan d’akinta tas ta biyawa kanta karatu jami’a bayan haka kina kallo yadda tun kina gabana su suke hidimarki basu tab’a nuna ba cikinku d’aya ba

Kuka hayfa ta fara a hankali..  Yaci gaba inaso kiyi koyi da su ki jure wahalar aure kinga ma ke kinfisu sa’a mijinki na da hali sannan gaki zaman aure har kasar waje to don Allah ki taimakamin na samu aljannata a dalilin haihuwarku kuma ki zauna lafiya y’an uwanki suyi alfahari da tarbiyarki ki jure yadda suka jure komai zai faru ki iya samawa kanki mafita kamar yadda suke yi kada ki zama yaran zamani Abu kad’an su kashe aure

Hayfa kuka take sosai a hankali… Yaci gaba kuma ki rik’e y’an uwanki har abada duniya ba kida kamarsu ko bayan raina kada ki tab’a bari Dan Adam ko abin duniya ya shiga tsakaninku ki zama mai kyawtata musu da girmamasu koda me kika zama a rayuwa. Allah yayi muku albarka duka ki gaida maigidanki ya tsinke wayar domin tuni ya ke jin kukan na ta

Tunda ya tsinke wayar hayfa ke kuka kamar ranta zai fita… Ta yaya yanzu zata tayarwa aunty ammah hankali ta fad’a mata Yusuf yaudararsu yayi shi ba mai kud’i ba ne bayan ko farfad’owa daga wahala da hidimar biki basu yi ba.  Kuka ta k’ara saki ta shiga uku Yusuf ya yaudaresu take maimaitawa a zuciyarta..

Yana train ya tuna ya bar wallet da wayarsa a gida gashi sun iso pool a dole ya matsa gun mai bada tickets ya masa bayani ya manta wallet a gida da ke ya san Yusuf kullum yana bin train ya bashi recit yace da yamma in ya tashi aiki sai ya biya duka

Yusuf ya masa godia ya sauka tun daga nesa yasir yasha jinin jikinsa kwanan nn akwai abinda ke damun Yusuf saidai yayi tsaki sanin halin zurfin cikin Yusuf d’in yanzu yana tanbayansa zai ce babu komai

Yana tunanin Yusuf ya masa sallama yana zama shima gefensa wani d’an guri ne can bayan pool gurin kamar na k’wallo idan suka gama aikin safe basu son komawa gida sai yamma nan suke zama su yita hira har suyi sallah tare in lokacin sallah yayi

Kallonsa yasir yayi yace “zaune ka kwana ne”?

Yusuf yace eh bana jin dad’in jikina ne!

Yasir yace yanzu kusan 2yrs muna tare a kasar da ba tamu ba ya kamata muna tallafawa junanmu a kowa ne hali sabida wanda kake kusa dashi a ko’ina ne a duniya shine d’an uwanka ka duba yare kamar yarbawa, ibira, Igala, inyamurai zaka samu in suka hadu a kasashen waje har k’ungiya suke yi domin k’ara zumunci da kusanci tsakaninsu alhalin a Nigeria babu abinda ya had’asu.  Pls Yusuf mu d’auki kanmu kamar uwa d’aya uba d’aya mu daina b’oyewa damuwa koda ba zaka fad’amin duka ba ka fad’amin wata k’ila na taimaka maka da shawarar da zata anfaneka

Ajiyar zuciya Yusuf yayi ya d’an kalli Yusuf kafin ya fara bashi labarin aurensa da hayfa sannan ya fad’a masa visa d’insu ta kusa k’arewa gashi pool kad’ai bazai ishesu rayuwa shi da hayfa ba

Sosai yasir ya girgiza saidai ya lura Yusuf ba k’aramin kamuwa yayi da son hayfa ba ammah daga yadda ya fahimta hayfa tayi zaton Yusuf d’an masu kud’i ne saidai yak’i nunawa Yusuf wanan b’angaren

Kallon Yusuf yayi yace a gaskiya ina bayan kada ka k’ara neman wani bashi daga alhaji kayi k’ok’ari ka gama da na kanka, sannan ko shugaban Nigeria ne babanta dole tayi hak’uri tunda aure ya riga ya had’aku

Sannan shawarar k’arshe itace idan kanaso ka samu sauk’i na amince ku dawo gidana sai mu bar mata bedrm, Ni da kai mu dawo da kayanmu falo tunda dama ni dama ba kwana nake ba koda zaku buk’aci keb’ewa ya k’arasa yana d’an dariya

Shiru Yusuf yayi ya kasa magana gaskiya bazai iya wannan ba

Sai jin muryar yasir yayi a kasashen waje zaka samu a lot bak’ak’e da suka san abinda ya kawo su kasashen waje a takure suke rayuwar wallahi sai kaga kamar gidana mutum hud’u kai har biyar

Kallonsa Yusuf yayi a hankali yace “amma ni da kai da matata kana ganin hakan ya dace”?

Shiru kad’an shima yasir yayi kafin yace za muyi yadda nace mu bar mata room mu muna falo yaso mu rik’a wanka kafin mu dawo gida kaga zai rage mana shiga bayin sai ta rik’a anfani dashi ita kad’ai

Yaci gaba yaso da zarar ka sama muku sabon residents permi sai ka fara tara kud’in sabon gida nan zuwa 3mths haka IA sai ku tashi kaga kud’in zai taimaka maka sosai su taru kabar maganar yiwa alhaji aike sai bayan ka gama duka biyun nn yaso sai ka nema aiki na biyu kaima

Sai yanzu Yusuf ya gamsu da shawarar yasir yayi masa godia amma yace sai yayi tunani zai yanke hukunci na k’arshe

Yasir yace babu damuwa suka mik’e za suyi alwala suyi zuhr.

da k’yar hayfa ta d’aga jikinta ta shiga d’aki ta cire kaya za tayi wanka tayi sallah idanunta duk sun gama kumvurewa har d’an zazzab’I take ji.  Koda kamal ya tashi aiki gidan ammah ya wuce saidai batanan sai mijinta yara na islamiyya sosai yayi mamakin da tausayin ganin kamal

Fitowa kamal yayi daga motarsa range Rover 2015 dark blue daddy na zaune wajen gidansa da jarida

Har k’asa ya durk’usa ya gaisheshi tare da tanbayar hayfa

Sosai daddy yayi mamaki kodai yaron ya zautu ne ya manta hayfa tayi aure, ajiyar zuciya yayi ya kalli kamal ya fara magana

Haba kamal kai fa musulmi ne ya kamata ka rungumi k’addara wani baya auren matar wani

Mugun d’agowa kamal yayi cikin gigicewa yana kallon daddy bai gane ba

Nan dai daddy ya lallasheshi sosai kamal ya gane hayfa tayi aure saidai zuciyarsa na fad’a masa auren dole ammah tayi mata don haka dole hayfa ta dawo gareshi zaiyi komai don haka

Muryar daddy ta dawo dashi tunaninsa yayi wa daddy sallama ya mik’e duk jikinsa ya saki daddy na tausaya masa yaron ya dad’e yana bautawa ammah da hayfa ammah matar mutum kabarinsa..

Kusan 5mints ya figi motarsa.

Kamar zai tashi sama ya bar harabar gidan zuciyarsa kamar ta tarwatse.

Bayan tayi wanka ta daure tayi sallah ta d’an sha tea da fruits ta kwanta zuciyarta na tariyo mata rayuwarta da burukanta ita da y’an uwanta shin kenan komai ya rushe?

Hawaye ta matse sam kwakwalwarta ta kasa fad’a mata matakin da ya kamata ta d’auka dole tana buk’atar lokaci tayi tunani ga kewar kamal da taji shima ya bijiro mata sosai

Yadda ya kullum in suna hira cikin tsara yadda zai wadata mata rayuwarta yadda burinsa ya mallaka mata komai a rayuwa

Runtse idanunta tayi tana hawaye sosai tana cikin tsaka mai wuya!

Bayan sun tashi aiki Yusuf yana train yana tunanin maganarsu da yasir tabbas yana buk’atar ya k’ara matse aljuhunsa domin ya d’an warware nauyin da zai k’ara fuskanta a y’an wannan lokacin

d’an lumshe idanunsa yayi bayan da ya tuno gimbiyar tasa saidai ya basar domin yana son kame kansa sosai daga fiskantar k’ask’anci daga gare ta.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]