[Advertisements⬇️]

INAAYA CHAPTER 9 - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

INAAYA CHAPTER 9

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wurin karfe goma duk sun gama shiryawa cikin white gowns dinsu aleesha gown ne na lace anyi hannun da net lace din white da golden sai jewelry dinga na gold ne tasha an daura mata turban an hada shi da dankwalin lace din sai bridal veil din nan kaman net haka tayi kyau sosai makeup din dan nude haka, sai aleena kuma wani mermaid gown ne na fabric white shima an daura mata turban dinta itama jewelries dinta na gold ne sai ummi lace ne white da golden yellow tayi A-line gown itama an daura mata turban an hada da dankwalin ta tayi kyau sosai da jewelries na gold itama duk sunyi kyau ba karya amma daka gansu kaga jiki a sanyaye karfe 4 ne jirgin zuwa gombe da an gama daurin aure zaa tafi da aleena sai ummi kuma 4:30 ne flight din sai aleesha da a nan abuja zaa ajiyeta saida yamma za a kaita. Duk anata shiri yan matan yau friends kowa kayanshi ya saka sukuma sisters ankon lace ne kowane peer group da color din su but same design ne dinkin skirt da riga peplum sukayi inaaya dai hakanan take komai ba karfi saboda ita dai gata nan wani iri iri takeji tunda ta tashi ga yanda takejin zuciyan nata na bugawa da sauri sauri,basuyi makeup ba yau yan matan duk simple.

+

              Tunda aliyu ta tashi yau yake jin ba dadi a ranshi kuma hakan yana da hadi da abunda su baffah suka kirashi suka sanar mishi kwana biyu da suka wuce duk komai jiki ba kwari yakeyinshi karfe 11 amma bai shirya ma daurin auren ba sai ga fareed yazo ya shigo dakin nashi ya tarar dashi zaune yace “habaa mana aliyu ya akayi baka shiryaba ni da ba daurin auren gidan mu ba ma na shirya har na fito saboda 11 yanzu already kuma 12 ne daurin auren aliyu kallonshi kawai yayi ya kada kai yace “fareed at first banyi niyyan gaya maka ba but now i just felt the urge to tell you i have a problem” kallonshi fareed ya tsaya yi sannan yace “problem kuma aliyu wani irin problem na me and why didn’t you tell me all this while” shiru yayi

baice komai ba sai kuma nan ya fara sanar mishi halin da yake ciki. Cikin mota daya suke fareed na driving aliyu a gaba yasa wani sabon shadda fari da aikin golden yasa matching hula da takalma daka gansu kaga tsadaddu ga agogonshi designer sai kamshin turaren nashi daya saba yakeyi dolce and gabana  ko kai ka ganshi sai ya burgeka ka kara kallonshi the only thing missing was smile kwata kwata babu smile a fuskan shi kuma ba daurewa yayi ba just a straight face 11:40 suka isa an noor mosque wanda yake cike cike da jama’a duk girman masallacin saida mutane suka cikashi wasu har a waje anata gaisawa da iyayen amaren da duk sukenan su baffah da mahaifin aleena da mahaifin ummi, daurin auren dai an samu halartan din bin manyan mutane.

          Karfe 12:00pm dot aka daura auren Fatima isah sani gamawa da Hilal muhammad damagum daidai lokacin message ya shigo wayan aleena suna zaune hilal ne ya turo mata “Alhamdulillah officially mine” ai kuwa kuka ta fashe dashi nan aka fara bata hakuri inaaya kuwa ta na zaune tunda aleena ta fashe da kuka bayan ta duba wayanta sai kuma taga 12 yayi zuciyan ya dunga bugawa itama heart dinta na squeezing ta rasa dalili, mubarak ne shima yayi ma aleesha message “finally mine and only mine” itama water works din nata ya fara ai ummi tun kafin tayi receiving wani message itama sai kuka ana ta lallashin su can sai ga message din nazeer ya shigo “babyn ya nazeer it’s official i own you see you soon i love you” ai kaman ana tunzura su kuka anty fareeha tace “dillah can kun cika ma mutane kunne da kuka ana baku hakuri ma baku ji ba ku kuka ce kuna so ba habaa” dariya kowa yayi banda amaren da inaaya da tunda 12 din ta buga duk ta kara shiga wani rudu ta rasa miye dalilin ji takeyi kaman wani abun ya sameta duk bata a cikin hayyacin ta ta rasa gane miyasa kawai wani uneasiness takeji.

        A cikin babban masallacin nan waliyyan amare da na anguna sukayi exchanging maganganu aka daura aure imam ne ya fara anouncing an daura auren fatima isah sani gamawa da angon ta hilal muhammad damagum a bisa sadaki dubu dari biyu da hamsin, sai akayi anouncing na aleesha cewa an daura auren maryam usman abubakar geidam da angon ta mubarak hassan malumfashi abisa sadaki dubu dari da hamsin, sai akayi anouncing na ummi an daura auren Aishatu sanusi bichi da angonta nazeer Mukhtar kofar mata abisa sadaki dubu dari uku bayan an gama anouncing mutane kowa ya zata shine na karshe sai suka ji anyi anouncing wani da yasa duk wanda suka sani zare idanu suna contemplating abun kamar a mafarki sukaji ana anouncing “AN DAURA AUREN FADIMATU UMAR ABUBAKAR GEIDAM DA ALIYU IBRAHIM ABUBAKAR GEIDAM A BISA SADAKI DUBU DARI BIYU” duk su adnan, naseer,sameer,abby da sa’id da duk sauran yan uwan suka fara kallon juna cikin rudu tashin hankali da rashin fahimta kan furucin da sukaji anyi if they’re not mistaken sunan aliyu sukaji da kuma na inaaya kuma aure? Kowa da tambayoyi kala kala a ranshi suka juyo su duka suna kallon ya aliyu shi kuwa ana anouncing ya rufe idanunshi yana jin yanda heart dinshi ke yi sai ya fara tuno abunda ya faru *flash back

Aliyu yana zaune bayan zuwansu nigeria an fara hidindimun biki ranan Wednesday sai yaga abbah na kiranshi a waya ya dauka sai yace “ka samemu a parlour na na sama yanzun nan” ba bata lokaci ya nufa parlourn abbah yana zuwa yaga abbah da daddy da baffah da baba ya gaidasu cikin girmamawa ya zauna kasa sai baffah yayi gyaran murya yace “aliyu watanni kusan 5 dasuka wuce mukace mun baka wata biyu ka fiddo mata ko ba haka ba” zuciyar aliyu ta buga ya gyada ma baffah kai yace eh sai baffah ya ci gaba da cewa “toh! Miyasa bakayi abunda muka saka ka ba?” Yace “baffah ayi hakurii ban samu ba ne” sai baffah yace “to kasan bazamu saka maka ido ba ko shekara 30 zakayi ba mata kullum sai kunci kakeyi akan abunda ya faru shekara shidda da suka wuce ka ki daukar kaddara har yana barazana da lafiyar ka, dan haka kaman yanda muka baka wata biyu yanzu har wata kusan shidda ma kenan mun yanke hukunci zamu aura maka matar da muka zaba maka” wani abu ya hadiye a makoshi ya dago yana kallon baffah cikin rudani ya fara kaman zai bada hakuri abbah yace “dakata aliyu babu abunda zakayi ya canza abunda muka yanke kuma munyi hakanne saboda kai da lafiyar ka kuma munsan cewa za kayi mana biyayya” kasa samun bakin magana yayi bayan abunda abbah ya furta sai kawai yasamu kanshi da cewa “wacece” baba yace “yar uwarka ce fatima ta wurin daddy” da wani tashin hankali ya dago yana dubansu yace “abbah dan Allah kuyi hakuri kar ku aura mun ita wallahi yarinya ce shekararta duka bata wuce 16 ko karatu bata gamaba dan allah ku barta tayi karatun ta ni naji ku aura mun ko wacece zan zauna da ita na maku biyayya” daddy yace “ya isa aliyu idan bakaso muna iya fasawa amma saboda mun damu da kai mukaga hakan ya dace domin kai da ita dukkaninku need a spouse” abbah ya dakatar da daddy yana cewa “babu maganar fasawa a cikin wannan maganar InshaaAllah aliyu bakada mata sai inaaya  don haka saidai idan rashin kunya zakayi mana kace baka auren ta” kada kai yayi idanunshi sunyi jaa yace “aa abbah kayi hakuri bata kai haka ba Allah yasa haka ne mafi Alkhairi ya kara girma” Murmushin jin dadi sukayi abbah yace “I’ll forever be proud of you my son Allah ya cigaba da yi maka albarka” ciki ciki aliyu ya amsa sai baffah yace “mun yanke shawaran zaa daura aurenku tareda danasu aleesha amma sai bayan tayi hutun semester sannan za ta tare dakinta” aliyu ko fahimtar su bayayi kada kai kawai yakeyi sai ya samu kanshi da cewa “amma baffah an sanar ma yarinyar ne itama ai yakamata dan kar a shiga hakkinta” daddy yayi saurin cewa “duk abinda nacewa fatima bazata bijire mani ba dan haka babu matsala” kada kai kawai aliyu yayi ta fito daga parlour ya nufa part dinshi ya fada kan gado ya rasa me yake mashi dadi ko two minutes baayi ba sai ga ammah ta shigo dakin nashi ta karaso ta zauna kan gado tace “aliyu nasan kayi magana da abbahn naka shiyasa kake haka inaso nace maka kayi hakurii komi mai wucewa ne kuma duk abunda Allah yayi sai ya faru don haka sai ka rungumi kaddara hannu biyu inaaya yarinya ce mai hankali karama kuma nasan halinta na san ta zatayi maka biyayya sam batada fitina idan har ka sameta ka dace mata ta gari kuma uwa ta gari ma yaranka” yana jin ammah na magana ya dai kasa cewa komai yana kwance ammah tasa hannu cikin gashinshi tadan baje shi kaman karamin yawo sai ta tashi zata tafi a hankali ya kira sunan ta ta taso yayi hugging dinta tayi hugging danta back kafin ta bar dakin shi kuwa alwala ya dauro ya zo ya dinga salloli har da istikhara yayi da karatun qurani sai ya samu saukin abunda yakeji a ranshi.

*end of flashback

A hankali ya bude idanunshi ya sauke su kan yan uwan nashi da suke kallon shi kasa kawai yayi da kai sannan ya juya ya kalli fareed da yayi mashi smiling assuringly da murmushi shima ya kakalo yayi ma fareed din sai ya tuna maganan su na daxu kafin a tafi daurin auren da yagaya ma fareed

*flashback

“Wane irin problem gareka aliyu” fareed ya tambaya sai ya fara ce mishi “fareed su baffah aure zasu man kuma yau zaa daura auren” kallon kana lafiya fareed ya shiga yi mishi yace “what! Aliyu aure yau shine kake gaya mani yanzu” yace “sorry man I couldn’t tell you saboda nima just two days ago suka gaya mani and that too yarinyan daddy wallahi I’m just pitying her she’s just young ko karatu yanzu ta fara I’m way too older than her ina laifin su sama yar 24/25 haka idan ma hadani auren zasuyi” fareed dai da mamaki yake kallon aliyu da keta maganan yace “sorry bro kayita addua Allah yasan abunda yasa hakan ya faru yasan itace Alkhairin ka ba wata ba I’ll advice you ka rungumi aurenka da za a maka she’s young zatayi maka biyayya sosai I barely know her but wallahi she’s a nice girl so cool and simple also she’ll make a good wife for you zakaga tana iya abunda yar 24 bata iyawa age is just a number she’s matured enough” tsaki aliyu yayi yace “I’m telling you the problem kana ce mun haka told you she’s too young tsaran su inteesar fa ce how do you expect me to live  with her as a wife just how? she’s a sister to me” fareed yace “pls ango tashi ka shirya ni dai na baka shawara” hararanshi aliyu yayi ya tashi ya shiga closet domin shiryawa.

*end of flashback

Mutane da yawa sai zuwa suke suna ma su baffah murna suma angwayen abokannan su sai murna ake yi masu aliyu kuwa yanuwan nashi suka zo suka tsaya su ji mi ke faruwa sai bayansu suka ji baffah na cewa duk kowa mu hadu gidan daddy bayan reception ya wuce kawai sun sha mamaki amma ba yanda zasuyi haka suka nufa wurin reception jiki a sanyaye.

           Da kyar aka sa amaren sukayi shiru sannan aka dan kara gyara masu makeup jamaa sai shigowa akeyi ana congratulating din su wasu guda sukeyi, inaaya tun da ta shirya gadai ta nan kawai har anty fareeha ta kalleta tace “inee lafiya” ta kakalo murmushi tace “lafiya lau” kallon tausai kawai fareeha ta dan yi mata domin ummi ta sanar mata abunda ke shirin faruwa bayan su baffah sun gaya masu, ta bude kofan closet ta shiga kan kujeran dake a closet ta zauna jingina kanta a kujera ta na rufe ido tasa hannunta daidai saitin zuciyarta tana jin wani iri, karfe 1:00 khady ta shigo tace ga angwaye su sauko ayi hotuna a parlour din daddy dake kasa aka saukesu kawayen su sukayi masu rakiya sannan suka bar su suka basu wuri. Saida suka yi maganan su for like 10minutes sannan wani abokin mubarak, shamsu yace to lovey dovey din ya isa haka dariya kawai sukayi ya shigo da photographer aka fara hotuna sisters, cousins, friends da family da kyar su inteesar suka samu inaaya ta sauko ayi hoton bayan mamii ta tambaya ina take ta sauko picture bai fi uku tayi ba taja ta tsaya gefe mamii tace “inaaya lafiya mi ya sameki ko kin ji wani abu ne” kallon mamii tayi da confusion tace “mamii wani abu wane abu kuma? Ni banjin dadi ne shiyasa” gyade mata kai kawai mamii tayi sai ta dan bata tausayi.

            Duk kowa ya ka gara yaji abunda ke faruwa dukkansu gidan daddy suka wuce straight bayan reception suka tarar ana photo session suka shiga akayi da su sannan suka wuce parlour din daddy dake sama cux yafi shiru suna zuwa suka tarar da iyayen nasu maza duk suka samu wuri suka zauna sai baffah ya kallesu yace ahmad kaje ka ce wa fareeha duk yan matan suzo banda inaaya ahmad ya amsa da to yaje ya gayawa anty fareeha nan da nan ta hado kansu har da amaren banda inaaya da ta koma closet abunta ta zauna duk suma parlour din suka samu wuri suka zauna baffah yayi gyaran murya yace ” toh godiya ta tabbata ga Allah(SWT) da ya nuna mana wannan ranan muka aurar da yaran mu Allah yayi maku albarka” amin suka amsa a hankali nan ya dora da yi ma amare nasiha sosai akan aure ya masu fada da gargadi sai kuma yace “nasan ku matan bakusan abunda ke faruwa ba mazan kawai suka sani dasukaje daurin auren, a yau ba ku uku kawai muka daurawa aure ba bayan shawarwarin da mukayi mu duka da iyayenku mata mukayi coming up da solution, lokacin da na ba su ummi lokaci baku kadai ba aliyu ma na bashi sannan sai bai fiddo ba kafin lokacin shine muka bashi mata muka yanke shawara hada shi da ita sannan kuma muka daura auren a yau amma ba zata tare ba sai nan da yan watanni” kallon mamaki sukeyi ma baffah sannan suka juya suna kallon ya aliyu da yayi kasa da kanshi mazan kuwa wani rudu suka shiga  saboda sunsan da wa aka daura, khady tace “toh baffah amma wacece amaryan” murmushi yayi yace “ba wata bace ba illa yar uwarku gaba daya inaaya” wani irin tashin hankali kusan duk mutuwan zaune sukayi a wurin inteesar da mimi har wani shaking hannayyensu keyi saboda tashin hankali ba su da ko bakin magana daddy kuma ganin haka yace “ku tashi kuje Allah yayi maku albarka, sannan ku kira ita inaayan da mamiin ku nan” dakyar suka iya barin parlour din kowa shi yasan tashin hankalin da ya shiga tuni inteesar da mimi sun fara hawaye haka suka isa dakin inaaya sultaana ce zaune kan bed suna shigowa duk ta kula yanda suke taga mimi da inteesar na hawaye tuni hankalin ta ya tashi ta fara magana tana stammering “miii….m…mii me ya faru wani ya rasu ko wani abu ya fara” kada mata kai kawai khady ta iyayi inteesar din ce ta shiga closet din da inaaya take duk hawaye ya jike mata fuska kawai ta fada ta rungumeta tana sakin wani kuka mai cin rai ita kuwa inaaya kasa gane mata tayi sai tace “intee what is it kike kuka wani abun ya faru ne” da kyar tayi gathering courage tace “su baffah na kiranki suna parlourn daddy na sama” dum! Taji zuciyanta ya buga sai tace “intee ki gaya mani me ya faru miyasa su baffah ke nema na ki gaya mani intee” inaaya ta fada hawayen dake idanunta suna saukowa dan daidaita kanta inteesar tayi tace babu komai tashi ki je, tashi tayi ta fito dakin tana goge hawayen taga duk fuskokinsu ba walwala hankalin ta ya kara tashi taga mimi tayi sauri ta juya mata baya hawaye na saukowa a idonta sai kallon tausayi sukeyi mata a haka jiki ba kwari ta dinga takawa a hankali har ta isa parlour din tana shiga taga su baffah zazzaune da mamii da Ammah kasan carpet ta samu ta zauna tana gaishesu kanta a kasa amma zuciyanta sai bugawa takeyi daddy ne ya fara magana “mamaana, kinsan ita rayuwa a kullum ba yadda ka tsara ta take tafiya ba sai yanda Allah ya tsara maka kuma no body can change it” gyade kai tayi daddy ya cigaba yace “duk musulmi ana son ya zama mai daukan qaddara mai kyau da mara kyau idan Allah ya tsara maka abu kasaka a ranka shine mafi Alkhairi a gareka ka yita gode mishi” nan ma kai ta gyade ita ta fara kagara taji me ke faruwa haka mamii ta dinga gaya mata jiya to mi yake faruwa daddy yaci gaba da cewa “ina so ki zama me tawakkali mamana da hakuri kuma kisan cewa mu iyayen ki ne masu sonki bazamu taba cutar dake ba” tace “eh daddy nasani” baffah ya ce “toh! Inaaya a yau munyi daurin aure amma ba yanda kuka sani ba na mutun uku na mutun hudu mukayi, sannan ke ce ta hudun A yau mun ga mun isa dake mu iyayenki ne muka yanke hukunci kuma mun daura aurenki da yayan ku ALIYU”ai inaaya ji tayi kaman tana mafarki kwata kwata taji kanta ya na wani juya kaman ba a parlourn take ba dum! Dum! Dum! Zuciyanta ke bugawa da karfi kafin kace me idanunta sun kada sunyi jajjawur kusa 5minutes sannan ta dago tayi murmushi tace “abbah abbahna da wasa suke ko” kallonta sukayi da tausayi ta juya tace “mamii kinji me baffah yace wasa yake shi da daddy wasa suke mani ko” mamii ta shiga kada mata kai alamun aa rudu ba karami inaaya take ciki ba hawaye ya fara zuba daga idanuwanta ta tashi tsaye wani juyawa taji kanta yayi kafin taga blackout ta fadi a firgice mamii tayo kanta tana kiran “inaaya inaaya” tana jijjigata ammah ta tashi da sauri ta bude fridge din dake parlourn ta jawo roban ruwa ta mika ma mamii, mamii ma duk ta rude da kyar ta iya bude roban tasa a hannunta tana yayyafa mata shiru bata tashi ba mamii ta dunga yayyafa mata har kayanta ya jike dan ta kusa juye ruwan roban, tana kara yayyafa ma ta amma shiru duk suka rude ammah na cewa “mu kai ta asibiti dan Allah kar wani abun ya sameta” mamii kuwa ko magana ta kasa saboda tashin hankali daddy yace “ahh umm..umm yan..yan..zu a kira Aliyu” duk ya rude yake maganan abbah ne ya samu natsuwan dauko wayan shi yana kiran aliyu yana dauka yace mishi yazo yanzu ba bata lokaci ya amsa da to mamii na rike da yar tata tana ta jijjigata tana kiran sunan nata Amma ko motsi batayi suna cikin tashin hankalin nan aliyu ne ya shigo da sallama a bakinsa ko amsa masu basu samu sunyi ba Ammah ce ta taso tana rike aliyun tana cewa “Aliy kaa..kka..ka duba ta bata motsi bamu san me ya sameta ba” shima aliyu wani shock ya dan sameshi yana takowa a hankali inda mamii ke rike da ita hannunta ya rike ya taba wurin pulse dinta yaji normal ya taba chest dinta yaji heartbeat dinta na tafiya duk da da sauri sauri daukanta yayi cak ya ajiye kan kujera yasa hannu ya danna chest din nata ya mata sprinkling ruwa a fuska amma shiru bata tashi ba yayi repeating haka kusan so biyar Abbah yace “kunga mu kai ta asibiti tunda bazaya iya ba kar wani abun ya sameta” mamii dai tsaye take gefe daya kaman an dasa ta ko motsi ta kasa ga hawaye idanunta, wannan karon hannu duka biyu aliyu yasa da danna chest din yayi sprinkling ruwan ai kuwa sai ta ga ta ja wani dogon numfashi ta na bude idanunta a hankali duk wani numfashi su baffah suka saki da basusan suna rike wa ba, tana gama bude idanunta suka sauka a kan Aliyu wata kara ta saki mamii tayi saurin zuwa tana riketa Aliyu ya matsa gefe abunda ya faru duk ya dawo mata sai ta fashe da kuka tana kankame mamii tana cewa “mamii danAllah wasa ne ko mamii kicema daddy ya bar irin wannan wasan” mamii da dan karfi tace “get a hold of your self inaaya wa yake miki wasa a nan wurin” kuka takeyi mai cin rai tana ta “mamii, ammah ku ba su daddy hakuri dan Allah su bar ni in zauna da mamii kar suyi mani haka” abbah yayi ma ammah alamu da hannu su tafi da ita mamii tayi gaba sai daddy yace ma ammah “danAllah ku bata baki sannan ta shirya mai hoto zayazo yayi masu hoto ita da aliyun saboda tarihi, kai ammah ta daga tace to sannan tabi bayan mamii suka bar su daddy sai abbah yake cewa “gaskiya sai nake ganin kaman bamu kyauta wa yarinyar nan ba munyi kuskure” daddy ne yace “aa babu wani kuskuren da mukayi in Allah ya yarda kawai shock ne da take ciki ba wani abu ba” baffah da baba suka amsa alamun eh haka ne.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

+

STORY CONTINUES BELOW

       Shiru kakejin dakin kaman ba mutane dukkansu kowa da abunda yake tunani amma duk akan inaaya ne suna tausaya mata saida anty fareeha ta zauna ta dunga lallashin inteesar da mimi da sultaana saboda sai kuka sukeyi tayi masu nasiha akan kaddara ce haka Allah ya kaddaro ma inaayan tace yanzu su sunyi haka ita inaaya ina zata samu strength idan su sunyi breaking down ita fa tayi ta yi masu waazi dai. Bayan mamii ta ja ta dakin ta ta kaita ta zaunar da ita a kan bed ta dauko ruwa mai sanyi ta bude ta bata ta sha karba tayi stil tana kuka tana girgiza ma mamii kai tasha kadan ta fara sakin ajiyar zuciya sai mamii ta fara ce mata “habaa inaaya me na gaya miki jiya akan kaddara da tawakkali? Shine duk zaki manta su kiyi behaving haka iyayenki yanzu sai kija su dinga feeling guilty inaso ki sa hakuri a ranki ki dauka haka ne mafi Alkhairi a gareki, kuma baa ce miki yanzu zaki tafi ba aure ne aka daura amma sai kin gama first semester zaayi bikin nan da watanni dan haka inaso dake ki kwantar da hankalin ki ki dunga addua Aliyu yaro ne mai hankali da natsuwa he’ll be the best husband you’ll forever get Allah bazai taba sa ki tabe ba idan kikayi ma iyayenki biyayya akan abunda suke so kin faranta masu sai kema Allah ya faranta maki, ki daure ki yi ta addu’a cikin ran ki kiyi wa mijin naki kuma yayanki biyayya Sai Allah ya zaunar da ku lafiya” ajiyar zuciya kawai inaaya take saki irin jan da idanunta sukayi baya misaltuwa amma ta dan fara jin saukin abunda takeji a zuciyanta saboda yanda nasihan mamii take shiganta sosai ga hawayen nata sun tsaya sosai mamii ta dauka lokaci tana mata nasiha sannan tace ta shiga tayi wanka a nan toilet dinta ba musu ta tashi a sanyaye ta shiga wanka, ammah ce da tun dazu tana bakin kofa tana sauraron yanda mamii ke mata waazi ta shigo murmushi tayi ma mamii da godiya mamii tace miye na mata godiya duk daya suke sai mamii ta nufa dakin inaaya ta tarar dasu zuru duka tana shigowa inteesar ce ta taso ta rungume mamii sai kuka ai kuwa mamii ta zaunar da ita tayi masu fada su ma tace ba abun kuka bane lokacin farin ciki ne amma duk sun bata fuska nan da nan duk sai da tasaka su dariya sannan tace ma aleena “aleena danAllah ki turo mai kwalliyar ku dakina yanzu kuma duk ku wanke fuska su mimi ku gyara kwalliyan ku kuje kuyi hoto da aminiyar taku today is her big day” amsa mata sukayi da to nan da nan kuwa duk suka tashi suka fara gyarawa.

            Tunda abbah ya sallamesu yan mazan duk part din sa’id suka nufa kowa nata mamaki basu dai da bakin magana uncle adnan ne ya fara congratulating aliyu “yace congrats bro handle our sister with care” kawai murmushi ya kakalo yana masu duk wanda yayi magana naseer ne harda hugging dinshi yace “I’m happy for you ni dama ni aka kawai daura ma wa da farhana yau din nan” duk dariya ya ba kowa sukayi ta dariya sa’id yace “ahh yayi naseer ka kagara dayawa”  nan dai suka dan warware suna dariya sai abbah ya kira aliyu yace “yazo yanzu” aliyu yayi sensing tashin hankali a muryan abbah da sauri ya tashi yana excusing kanshi ya nufa cikin gidan, abunda ya gani ne yasa hankalinshi ya tashi me yasa yarinyarnan wannan dogon suman haka sai bayan ta farfado ya gane cewa su baffah sun mata breaking labarin shiyasa ta suma cike da tausayin ta Aliyu ya bisu da ido har su mamii suka fita da ita tana kuka mai taba zuciya abbah ne ya kalleshi yace “ya shirya yadawo parlourn yanzu mai hoto zayazo suyi na tarihi” har a ranshi baiso ba taya za ayi wai kawai ya tafi wurin yar yarinyan nan kanwa ta can baya wai suyi picture a matsayin miji da mata amma babu yanda ya iya haka ya koma dakin ya dan gyara sai ya sanar ma fareed su duka suka nufa parlourn da suka baro. Bayan inaaya ta fito wanka ta iske ammah zaune a hankali ta karaso ammah tayi hugging dinta tana lallashinta har dan kunyan Ammah inaaya taji saiga mamii tashigo da mai makeup a bayanta inaaya dai bin su kawai take da kallo kaman ba reality ba mami ta ciro mata wani lace ta fito dashi daga closet dinta white and golden ne lace din dinkin fitted buba da zani rigan ne akayi ma style hannu umbrella ne ansa wani satin da stones masu shining da jewelries din gold sarka da dan kunne da bangles ta mika mata a sanyaye ta karba tana mamakin duk yaushe mamii tayi wannan ta karba ta shiga closet ta saka kayan kuwa sun karbeta das! Ta daura zanin saman rigan tayi kyau tana fitowa Ammah ta fara MashaaAllah sai mami tace ma me makeup tayi mata da farko cewa tayi aa saida mamii tace bata son shirme sannan ta yarda tace ma mai makeup very light takeso, haka ta tsantsara mata makeup very light amma yayi kyau na gaske ta hada turban da dankwalin ta daura mata sosai inaaya tayi kyau ta fito a amarya sak gwanin burgewa sai mamii ta dauko wani bridal veil fari ta bata ta yafa sai ta ja ta zuwa parlourn daddy ita kuwa bin mamii kawai takeyi amma ji takeyi kaman ba ita ba kaman komai dream ne bin komai take da ido kawai dan gaba daya she’s confused kaman anyi exchanging dinta wai yau ita inaaya aka daurawa aure sai taji abun wani iri ma har suka isa parlour kan ta na a kasa ko dagowa batayi ba tasan dai akwai mutane a parlour din su kuwa duk sun kura mata ido banda Aliyu da yayi kasa da kanshi fareed yana taba shi da kafada ya dago ya harareshi shi kuwa nuni yake mashi da inaaya amma yaki kallon inda take photographer ne artilary nan da nan aka fara photo session da amarya da angon babu mai dariya hakanan dai akeyi saidai photographer yayi magana sannan suka dan kakalo smile da kyar wadda bata kai zuci ba duk saida sukayi hoto da kowa duk su baffah sun bar parlour din da su mamii ya rage yaran nasu ne kawai sai fareed yace “toh! Ko dai naga kamar ya kamata mu basu wuri ayi masu pictures din su kadai duk nan da nan suka bar parlourn aliyu ya bi fareed da harara shi kuwa yana gani amma sai yayi dariya ciki ciki kawai ya fita, bayan sun fita sai photographer yace dasu su gyara su zauna kan kujeran dake parlourn ba dan rai yaso ba haka suka zauna two seater ne har lokacin kan inaaya kasa nan yayi clicking kusan 10 sannan yace inaaya ta dago fuska da kyar ta dago nan ma yayi snapping sai kuma yace to su kalla juna sun kusa 5minutes kafin ya kara masu magana a hankali ta fara dago fuskanta tana sauke idanunta a kan fuskan aliyu taji wani irin bugu da heart dinta ya fara ba shiri ta maida kai kasa heart dinta na beating sosai da kyar mai hoton yasamu suka kalli juna yayi snapping nasu sannan yace ma aliyu yayi pecking dinta a goshi sam! Aliyu yaki yayi kaman bai ji ba sau da ya gaji da tsayuwa yaga dai photographer din dan naci ne tana tsaye dan nesa dashi kawai ji tayi an fixgo ta wani shock yabi jikinta dan ta kusa fadawa kan aliyu a hankali ya kai bakinshi a goshinta rufe idanu tayi gam! Har wani  shaking jikinta yake saboda shock, aliyu ma saida yaji wani abu na mishi yawo da ya daura lips din nashi a goshinta ya lumshe ido sun kusan 7minutes haka sannan aliyu ya saketa ya dan matsa mai hoton yayi Murmushi yace just perfect! Sai kuma yace inaaya tayi resting kanta a chest din aliyu ayi snapping ta kafe ta ki yi don har lokacin jikinta bai bar rawa ba bayanda photographer din ya iya  haka yayi ta snapping dinsu sauran hotunan wasu a tsaye wasu a zaune ya gama ta tattara kayanshi ya tafi inaaya na zaune kan kujera kaman an dasa ta takasa motsi gashi turaren aliyu sai hawan mata kai yakeyi ga zuciyanta dake faman bugawa ba ita ta tashi ba sai da ya tashi ya fita sannan a hankali ta tashi ta fito tana ta tafiya a hankali har ta isa dakinta tana budewa taga yan uwan nata yanda aka saba zama ayi raha sai kawai taji hawaye na zubo mata aleena ce ta tashi ta rungumeta tana cewa “sorry sister let it out cry it out i know it must be hurting” tana rungume a jikinta tafara wannan kukan mai cin rai tana cewa “ya leena why me? Why? Meyasa su baffah suka zabe ni miyasa ba ya khady ba ko ya farhana ko ya haneefah even mimi meyasa sai ni it’s hurting akwai zafi sosai” sai ga anty fareeha ta shigo tace ma su aleena, aleesha, ummi duk ku tashi yanzu zaa tafi daku gidan baffah kuyi hotuna da su ummi mama ammi da mommy daga can zaa wuce da ku kunga 3:00 ya kusa already kuma flight din naku 4 ne tana fadan haka duk sai hawaye kowanne cikin su yanda aleena ke rungume da inaaya itama ta fara nata kukan a hankali tace ma inaaya “take care sis I’ll call you InshaaAllah and take heart ya aliyu will be a great husband” ta gama fada sannan ta sake ta aleesha ma tayi hugging dinta tace “have sabr sis everything will be alright” ummi ma da hawaye sukayi hugging juna tace “believe in destiny inaaya it shall be well InshaaAllah” sai ga anty fareeha ta shigo da ammah nan aka fito dasu sukayi waje suka shiga motoci suka kama hanyan gidan baffah, inaaya kuwa closet ta shiga ta rufe kofan ta kwanta tana ta kuka kaman ranta zaya fita su mimi har suka gaji da knocking ta ki ta bude masu.

Karfe 4 har sun shiga jirgi zuwa gombe da kawayen amarya da yan uwan mahaifinta sai anty fareeha, sai feenah, aneesah da saleema sai yan dauka amarya, amarya tasha kuka bayan sun isa gidan baffah sukayi pictures da iyayensu mata wurin karfe  3:20 duk aka saka suka canza kaya wani filtex atamfa suka saka da lafayya ba makeup a fuskokinsu duk sun goge aka kaisu parlour wurin su baffah harda mahaifin aleena da na ummi fada da nasiha akayi masu sosai sannan aka nufa dasu wurin iyayen su mata su ma suka dora da nasu aleena tasha kuka da kyar aka rabota da jikin ammi tasha kuka sosai, haka itama ummi tasha kuka sosai ba kadan ba itama ta rirrike mommy sai aleesha itama haka sun sha kuka har da sisters din nasu su khady duk sunsha kuka baffah da kanshi ya kai aleesha gidanta bayan an tafi da ummi da aleena  a gidan ta da ke karsana east a garin abuja  kawayenta da iyaye suka rakata bayan baffah ya kaita.
+
             Karfe 5 akayi budan kai na amaryar sameer a gidan abbah dayake akwai fili sosai duk dangin da suka rage sun halarta budan kai din su khady ma duk sun je banda su mimi da suke can gidan su inaaya sai lallashin kawar tasu sukeyi tana kuka. Alhamdulillah an watse taron budan kai lafiya sai kuma shirin dinner da za ayi a daren rannan kowa ya tafi domin yin shirin shi na dinner amaryan ma da kawayen ta da danginta duk suna can zasuyi shiri. Aliyu tunda ya koma gida ya shiga part dinshi ya rufe da key ya sakan ma kanshi shower ya kwanta idanunshi rufe amma ba bacci yakeyi ba kawai tunanin halin rayuwan nashi yake yanda zaya koma yana tunanin yanzu ya su abbah suke so yayi taya zaya fara kallon karamar kanwarshi wadda sanda aka haifeta da wayanshi ya dauketa a cikin shawl amatsayin matarsa ta ina suke tunanin zaya iya zaman aure da ita? Duk tunanin da yake kenan ya ma rasa ya zaiyi har magrib tayi ya tashi yayi sallah ya kwanta again sai ga ammah ta shigo dakin dauke da kulolin abinci da kyar tasaka aliyu dole yaci abinci kadan sannan tace ya tashi ya shirya dinner din dan uwan nashi, badan yaso ba haka ya tashi yace to sannan ta fita daga dakin.
          Su inteesar sun sha lallashi har suka godewa Allah itama dai inaaya tayi kuka idanunta sun kumbura sunyi ja ga fuskanta yayi ja ga ciwon kai da wani zazzabi da ya taso mata tayi kuka har ta godewa Allah ta hakura tayi shiru har magrib yayi sukayo alwala kowa yayi sallah inaaya ta jima kanta kasa wurin sujjada tana kai ma Allah kukanta, ta gama suna zaune mamii ta shigo da mai aiki a bayanta da kulolin abinci ta jera ta tafi sai mamii dukkansu hudun tasaka su dole su ci abinci suka samu suka tuttura, da ka kalla inaaya sai kaga canji kaman ba ita ba sai mamii tace duk suyi shirin dinner zaa tafi amsa mata sukayi da toh! Banda inaaya ta tace “mamii dan Allah ku bar ni a gida” hade rai mami tayi duk da tausayin yar tata tace bata zama gida hawaye na ziraro mata tace “mamii dan Allah ki bar ni na zauna kaina na mun ciwo kuma ina jin daci a zuciyana” mamii daurewa kawai take batayi breaking down ba ta tashi ta fita ta dawo da magani taba inaayan ta sha sannan tace su shirya yanzu zata samu sauki ba yanda inaaya ta iya haka suka tashi sai bayan sunyi sallar isha sannan suka fara shiri wani anko ne sukayi na sisters ash color da head ash yayi kyau sosai suka saka kayan nasu inaaya dai bata so ba haka ta saka kayan mimi ta daura mata head din yayi kyau simple gown ne kasan shi kaman fish sai abun peplum wurin gaban rigan, makeup sukayi sunyi kyau banda inaaya da ko kwalli babu a idanunta saida mimi ta takura mata sannan ta barta ta dan gyara mata fuskan ta tayi normal kaman ba ita tasha kuka ba tayi kyau sosai sai sultaana tace yakamata muyi pictures nan suka fara clicking pictures inaaya dai daka ganta batada walwala. Sun sauko kasa gidan duk an gyara ba mutane kaman ba shine aka sha hidima ba suka tarar da mamii ta gama shirin nata itama ta kallesu sunyi kyau sosai sai ta kalla inaaya tace mata “inaaya ina zaki fita haka?” Kallon mamii tayi na rashin fahimta sai mamii tace “wuce ki je ki nemi gyale ki saka” wasu irin zafafan hawaye taji sun zubo mata da gudu tayi sama tana taresu bata san tayi kuka closet din ta nufa ta bude side din veils ta dauko wani ash medium veil ta yafa shi duka a jikinta sannan ta sauko kasa aminnan nata na mata kallon tausayi sai mamii tace to su tafi suka shiga mota suka nufa event centre din. Inaaya zaune tayi cikin mota akan ita bazata shiga ba saida mamii tayi mata fada sosai sannan ta fito suka shiga tare dasu mimi suka samu seat table daya suka zauna dukkansu shiru tunda suka zauna amarya da angon suka shigo suka zauna sunyi kyau they looked so happy and cute together event ya fara saiga yayyen nasu maza sun zo ciki harda aliyu da fareed aliyu yasha wani shadda ash color da matching hula da black takalma yayi kyau sosai suna shigowa fareed ta taboshi yana nuna mishi inaaya a hankali yace “perfect couple look har kaya same color kuka saka” aliyu baice mashi komai ba yayi gaba zuwa table din da akayi masu reserving suka zazzauna coincidentally inda ya zauna yayi daidai da inda inaaya take zaune dayake table din side by side suke nan fareed abunso ya samu ya dunga tsoka nan shi har waya ya jawo ya dunga snapping dinsu countless pictures ita kuwa inaaya yana zama tun bata san waye ba kamshin turarensa ya daki hancin ta saida zuciyan ya buga. Event din passed before you know it, it was enjoyable banda inaaya da ko tashi bata yi ba har saida aka gama sannan suka tashi tafiya gida wurin karfe 11:00pm.
          Duk sunyi shirin kwanciya suna zaune a daki mimi tace “yanda Allah ke abubuwan shi daban ne wlh ni ji nake kaman it’s all a dream zaa tada mu mutashi” sultaana tace “seriously har yanzu I’m finding it hard to believe” inteesar ma tace “yeah kaman a mafarki wallahi” inaaya dai duk da ido ta bi su dan itama bata yadda da abun ba haka sukayita fira  jefi jefi su kadai har bacci ya daukesu inaaya kuwa sam ba bacci a idonta sai wani kishin ruwa taji ta tashi ta sauko kasa ta yafa veil saman pj’s din ta zata dauka ruwa saboda babu ruwa a fridge din dakinta haske tagani parlour tazo zata wuce taji muryan daddy yace “mamana” a hankali ta tako zuwa parlour wurin daddy taganshi zaune da ya sa’id kusa da daddy ta samu ta zauna daddy yace “fushi mamana takeyi dani ko” shiru tayi batace komai ba yace “kiyi hakuri ki bar fushi da daddynki komi kika gani Allah ya tsaro babu yanda za muyi nasan ke me hakuri ce da biyayya kuma InshaaAllah zakiga sakamakon biyayya nan gaba, ke da aliyu duk yarana ne kuma duk nasan halayyarku kuma i can assure you aliyu ba zaya taba cutar da ke ba baya da matsala saidai kowa 9 yake bai cika goma ba da kun yi hakuri kun zauna da juna zaku ga ribar abun” hawayen daya sauko mata ta goge tace “daddy ni ba fushi nakeyi dakai ba” murmushi yayi ya dan yi hugging diyar ta sa yace “mu iyayenki ne a kullum masu sanki ne bazamu taba cutar da ke ba forget sa’id aneesah and twins you’re the real favorite” sa’id dake dayan kujeran yayi gayaran murya yace “daddy i can hear that” duk dariya sukayi a tare whole heartedly tayi dariyan wanda duk a ranan yau bata yi ba sa’id ya dawo inda suke ya yi hugging din inaaya yace “don’t be unhappy baby sis daddy is right everything happens just as Allah planned have sabr it’ll be good InshaaAllah” murmushi tayi ma ya sa’id ta amsa masa da yes sai ta tashi tace dasu ruwa zata dauka ta tafi daki tayi masu saida safe ya sa’id yace “ohh abun mamaki lil sis is all grown up it’s unbelievable yanzu daddy before you know it sai ka fara ganin yan jikoki na yawo ace yaran inaaya ne wow!” Dariya daddy yayi ita kuwa inaaya ta bata rai tana turo baki sai daddy yace “sa’id kar ta takura wa mamana fa kaima kaine next saida kaji mun daura maka auren” gwalo tayi mishi ta nufa kitchen ta dauko ruwa tazo ta wuce daki tasha ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]