[Advertisements⬇️]

INAAYA CHAPTER 7 - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

INAAYA CHAPTER 7

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ba su suka dawo ba sai bayan sallah isha duk sun gaji saida suka yi selecting decor suka duba cakes su ma sukayi selecting sai kuma suka duba dresses na brides duk suka zaban masu wani evening gown peach zuka zaban ma aleesha sai aleena da ummi suma iri dayane but different colors na aleena leaf green sai na ummi sky blue. Suna shiga daki sallah kawai sukayi kowa ya fara neman abinci saida suka gama cii sannan suka samu kansu inaaya dake zaune a kasa tace “waii! Allah my legs are hurting wlh hidiman biki da wahala” dariya sukayi mata nan suka fara taba fira kafin farhaana ta tashi tace tana zuwa sai hanifa tace “uhmm mu dai ki ce mana sai mun ganki sana’ar naki zaki tafi” dariya duk yen dakin sukayi ita kuwa farhaana tayi kaman bata ji ta ba ma ta yi tafiyan ta not long da tafiyanta wayan mimi yayi ringing tayi answering ta shige closet baa jima ba ta fito tana dan zare ido daka ganta kasan akwai wani abu sai tace intee please we need to talk dariya inteesar tayi tace “Allah yasa lafiya” closet ta ja ta sannan tace “intee I don’t know what to do ya habeeb ne yazo and yanzu dana fita kowa sai ya sani” dariya inteesar tayi tace “toh! Wa yake bin ki bashi zance haramun ne?” Tafada in teasing tone ita kuwa mimi dan

bigeta tayi tace “please mana” sai tace “toh me zan miki? calling me was a bad idea sultaana ya kamata ki kira ki gaya mata sai ku fita tare kuce kayanta ne brothern ta ya kawo mata zaku karba” ajiyar zuciya tayi tace “thanks love” sai suka fito mimi tace “sultaana please two minutes” closet suka koma ta gaya mata yanda akayi sai tace ok tou su je, a tare suka fito har sun kai kofa aleena tace “wane munafunci ake yi ina zakuje” mimi tayi saurin cewa “uhmm ya lee kayan ta zani raka ta ta karba” aleena tace “waya kawo mata kaya da daren nan sai sultaana tace “my brother” dariya aleena tayi tace ” yara kenan kice kawai yayanki yazo zance zaki rakata kuyi pretending” dariya inteesar tayi ta kasa yin shiru aleena ma dariya tayi tace “see ba sultaana dawo ki zauna ke kuma mimi go and meet your lover ko kin manta lokacin last meeting lnteesar ta gaya wa anty fareeha kuma duk muna zaune” kunya duk ya kama mimi saboda ma ta manta she was embarrassed haka sum sum ta fita suka sakin mata dariya sultaana kuma ta dawo ta zauna suna zaune nan sai sound din message ya shigo wayan khady ta duba tayi shiru for some minutes sai ta tashi tace “ina zuwa” dariya aleena tayi tace “ku dai kuka sani ji yanda mukayita fama da ita ta saurari fareed kinga yanzu da aka kulle mu ake cewa ina zuwa, ahh children of now adays” dariya aleesha tayi tace “hmm help me see oo sai forming” dariya sukayi wata friend din aleesha, suhaila tace “wlh kuna shan drama I really admire your family” smiling sukayi shiru few minutes sai aleena tace “yanzu dai mun san su waye singles a ciki inaaya da intee sai haneefa and sultaana too” dariya sukayi kawai sai ummi tace “uhmm waace haneefan ba dai wannan ba” aleena tayi dariya tace “ai fa ita kuwa idan ba ita ba wa” ummi tace “lallai kina ganinta shiru shiru dinnan ai kila sai dai kiji ansa biki ko za azo neman aure ai ciki duk tafi su” hanifa smiling kawai tayi sai aleena tace “sis gayan in ji waye ake yayi ne” dariya aleesha tayi tace “shaqa ma na maana” ummi tayi dariya tace “le cousin ne fa from side din mama idan kikaje kaduna hutu zaki gane abunda nake ce miki duk ta fisu, guy dinnan kullum yana gidan baba idan yana kd ai bacci kawai ke raba su idan tun safe har 10 na dare sannan za ayi bacci to haka suna tare aci abinci tare sallah kawai zai tafi masallaci ya dawo ita tayi nata a parlour a zauna ke danaje kaduna har gajiya nayi hanifa batada lokacin ka at all sai idan ta dawo daki bacci kar kice zakuyi fira da ita aa wani waya zasu fara kuma sai 12 a kwanta ko ta zauna tayi fira da kai ko ta kaika yawo aa gara ma idan ishaq na nan shi ya fidda kai but hanifa saidai idan an samu baya kd kuma idan zaya tafi! Wayyo Allah zo kiga kuka nace kutt lallai hanifa” dariya sukayi sosai ba kadan ba ita kuwa haneefa blushing kawai takeyi sai aleena tace “kice mana ita babba ce to miyasa da anty fareeha ta tambayeta ta ce babu kowa” ummi tayi dariya tace “bari na tona kinsan irin dan misunderstanding din nan na couples shi aka samu sai hanifa tayi fushi shiyasa” dariya sukayi mata aleena tace “gaskiya gobe zamu saka labule muyi magana hanee” fira suka ci gaba har sai wurin 10:30 duk su mimi da khady da farhana sun dawo wurin 11 aleesha tace “let’s sleep wlh tomorrow is going to be a long day” aleena tace “gaskiya kam we should” amsawa sukayi kowa ya nufa inda zaya kwana dan ba daki daya suke kwana ba dama kawai suna zama nan ne saboda fira.

+

Tunda sukayi asuba suka koma bacci karfe 8 aleena ta tashi dakin inaaya ta nufa duk ta tada su kaman basu san tashi haka suka tashi suna ta hade fuska su a dole sun gaji a haka suka fara shiga wanka one by one suka gama around 10 har sun gama breakfast henna artists din da suka kirawo duk sunzo kowace amarya da wacce zatayi mata sai wadda zatayi wa brides maids and sisters, in no time aka fara ma amare MashaaAllah design din yana kyau sunyi red a tafin kafa da hannu sai baki a kan hannu yayi masu kyau sosai duk da ba son hennan sukeyi sosai ba.

Gidan baffah na nan cike da mutane anata shige da ficce hidima ta kankama sosai anyi decorating din gidan irin traditional decoration dinnan saboda a nan ne za ayi henna party din, ummi ba zama bata nan bata can da anty fareeha da tun da satin bikin ya kama ta dawo gidansu tana kwana saboda hidima tarbar baki da sauransu, on the other hand wani guesthouse din daddy ammi take itama tana hidiman nata acan da dangin mahaifin aleena da duk suka zo biki, haka itama mommy hidima ta shiga sosai mutane dayawa sunzo daga kano tana hidima dasu sosai. Abbah ne sai daddy da baffah da baba zaune a parlour din baffah na sama wanda shi kadai ne babu hayaniya a cikin gidan parlour din gyare yake tsab! Sai sanyin ac dake tashi da kamshin turaren wuta baffah naji yace “toh! Yanzu tunda mun gama sai mu samu a kira iyayen mata duk mu sanar masu shima aliyu a kirashi a sanar mishi sauran yaran kuma ina ganin a bari daga baya duk sai kowa yaji” abbah yace “Aa sai nake ganin ba Aliyu kadai ba yakamata a sanar ma wadda abun ya shafa itama” sai daddy yace “Aa babu wani abu ni nafi ganin ayi yanda baffah yace daga baya sai a gaya ma sauran yaran tunda abu ne ba zai taba zama boyayye ba” baba yayi Murmushi yace “hakane Allah ya taimaka mana ya kara mana zumunci” da amin duk suka amsa kafin suka ci gaba da firarrakinsu na maza.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Sai da lallen nasu yayi 4hours na amaren sannan aka wanke shi kuma ya fito yayi kyau sosai kaman lokacin aka zana shi, har lokacin baa gama na bride maids da sisters ba inaaya dake zaune tace “ni wlh na gaji ma kaman na fasa yin lallen” dariya sukayi mata aleena tace “kuma wlh baki isa ba” mai lallen da tayi wa aleena flott beauty tace “habaa yan mata gaskiya bai kamata ki fasa ba kizo ni nayi miki wannan kyau da kikasha kinata glowing kaman kece amaryan” smiling inaaya tayi ta kuwa nufa wurin ta zauna tana mika hannunta nan matan ta fara tsara mata nata kaman zatayiwa wata amarya inaaya tace “amma fa kadan za ayi mani banason dayawa” to tace mata taci gaba tayi mata mai kyau black da ja yana da yawa ba dai sosai ba inaaya kuwa tayita admiring lallen nata. Sai wurin 3 suka gama shirya wa amare sunyi kyau sun saka irin fulani saki dinnan wanda yasha stones da light makeup dazeita tayi masu kowacce tayi kyau cikinsu na aleesha blue din ne sai aleena maroon sai ummi peach din ne sosai sisters din nasu da friends sukayita admiring nasu suna snapping nasu, su kuma friends sunyi anko shima na fulani saki din ne amma su rigansu na atamfa ne sai head na saaki ne friends din aleesha nada blue na aleena maroon na ummi peach sunsha kyau ba kadan ba su ma sisters da nasu ankon barakallah sunyi kyau su ma saaki ne dukkansu kowane peer group da color din nasu su Khady and co maroon sai inaaya and co blue sai aneesah da salima peach haka suka rarraba sauran cousins din amaren from other side of there parents ma duk irin ankon sukayi kowa na peer group dinshi saida suka jima suna pictures, wayan aleesha yayi ringing tana dubawa taga ummi ce ta gaishe ta sai ummi tace mata “wai ku baku zuwa hakanan a fara event din nan kunsan cewa 7 magrib yayi” aleesha tace “yi hakuri ummi yanzu zamuzo” kashe wayan ummi tayi nan da nan duk suka kira mazajen nasu aka turo motoci nan aka fara shiga ana tafiya amare ne karshen tafiya duk saida kowa yatafi sannan suka shiga mota suma suka tafi zuwa gidan baffah inda za ayi event din.Bayan sun isa gidan baffah suka tarar cike duk mutane sun zo ga wuri yayi kyau yasha decoration ga masu ki’da nan na gargajiya sai bayan zuwansu aka fara saida aka kira mamii ta bude musu taro da addua sannan akace masu asoebe zasu shigo da amaren ai kuwa haka kowa color din anko dinka zaiyi determining amaryan haka suka jero gwanin ban shaawa aleesha ce farko da yen team din ta sai aleena sai ummi abun yayi kyau ba kadan ba suna ta dan takawa har suka isa inda aka tanadar wa kowace amarya na zama su kuma suka zauna kan carpet da aka sa tuntuna a gefen kowace amarya acikin tent din.anata ci ana sha jamaa nata rawa harda amaren aka gayyato a fili suma sunyi rawa ba laifi it was so fun don sun sha rawa traditional dance ba kadan ba party din ya musu dadi sai karfe 6 duk yawanci aka watse ya rage yasu yasu ne kawai yan uwa nan su inaaya dasu khady suka fara sabewa one by one domin suje su shirya lokacin surprise din su ya kusa dan ma kar su yi suspecting nasu duk sun kai kayan da zasu saka gidan abbah don haka can suka nufa kawai saida sukayi sallah suka dan huta sannan suka fara shiga suna wanka.

A bangaren su aleesha kuwa sun sha mamaki da kowacce soon to be husband dinta ya kirata akan cewa zasu fita dinner su duka uku brides din da mazajen nasu har gaya musu sukayi dama sun shirya har gowns suka saya musu for the outing iri daya and mai makeup zatazo please they should get ready in 2hours sun sha mamaki amma basuce komai ba sunyi recieving gowns din yayi masu kyau sosai kowa tanason na ta sai ga me makeup rjt tazo saida sukayi sallah da wanka suka fara shiri ana yi masu makeup aleena tace “kinga yaran nan kuma gidan abbah suka nufa yau su nan a tunaninsu su barmu da kadaici to ai gashi nan yanzu saidai suji labari” yar dariya sukayi aleesha tace ahh to, simple makeup tayi masu kaman ba na brides ba ta daura masu turban different styles saida suka gama shiri tsab sannan suka sanar wa grooms to be, ba da jimawa ba kowanne yazo ya dauka amaryan tasa suna yaba irin kyawun da sukayi hilal yake cewa aleena “qalb I really can’t wait for this Saturday to come when the imam will announce it that you’re officially mine when i say mine i mean miine alone all mine” cheeks din aleena ya koma red saboda blushing, mubarak kuwa tunda ya dauka aleesha ya kasa ma magana sai furta Alhamdulillah Alhamdulillah kawai yakeyi its kuwa kasa tayi da kanta she was shy, haka ya ummi ma tana shigowa motan yace “I’ll never stop thanking Allah for having you in my life aeesh(his nick name for her)” smiling tayi tana cewa “kai ya nazeer you’re making me feel shy” yace “ya nazeer’s babyy I can’t help it you look amazing i am feeling like asking you out all over again” dariya kawai tayi. A gidan abbah duk yan matan sun gama shirin nasu suna ta clicking pictures sun sha wani cocktail gown iri daya but different colors wasu da makeup wasu babu but idan ka gansu su duka abun gwanin burgewa suma nan cikin kankanin lokaci suka nufa venue din for the surprise. Wani hall ne ba babba sosai ba yasha decoration duka white ya tsaru iya tsaruwa da yen seats ba masu yawa ba saboda ba event din mutane ne dayawa ba duk sun isa hall din da friends din amaren da duk suka bari gidan daddy suka fita dinner da grooms din su, da cousins din su duka suna cikin hall din saida mubarak ya kira khady yace mata “eh” kawai ita kuwa ta gane duk suka kashe wuta can hall din yayi duhu, su kuwa amare sun iso wurin suna waje aleesha tace “hall ne fa a nan gurin babe” smiling mubarak yayi mata yace no akwai restaurant mai kyau a baya but sai an shiga ta cikin hall din sai a fita ta dayan kofan hall din kafin kaga restaurant din saboda it’s dark kar mu bi ta cikin flowers din is better mu shiga ta hall din” su kuwa gyade kai kawai sukayi cikin gamsuwa a tare suka tun kari hall din suna shiga ashe duk grooms din sun samu sun gudu aleena tace “wai what is this duhu everywhere ya zamuyi” aleesha tace “eh mana gashi this guys are no where to be found ina suke?” Ummi ta bude baki zatayi magana kawai sukaga an kunna wutace hasken dan kashe masu ido yayi sai daga baya suka bude suna kallon decoration din a bayansu sukaji ana cewa “surpriseeeeeeeeee” baki suka kama suna kallon yan uwan nasu da abokan nasu aleena tace “OMG!! I’m going to cry” dariya sukayi sai khady tace “we planned everything so sisters let’s have fun its a bridal shower for you darlings” dariya aleesha tayi tace “this is so beautiful we’re so grateful for you guys” ummi tace “yess we are and we love you guys so much” su duka ukun sukayi kaman kuka zasuyi nan aka fara hugging session kafin khady tace “enough of the huggings now let’s party” dariya sukayi su duka nan dj yasa waka ta fara tashi party scatter by fireboy habaa kan kace me duk sun fara rawa harda amaren, ranan was like the best day of there lives they had so much fun sun sha rawa they ate lots of snacks,cakes,donuts,ice cream, parfait and lots more sun sha rawa kuma kaman ba gobe harda dai inaaya da bata cika rawa ba sun sha rawa har takai ana cire takalma saboda ciwon kafa, sai photo session kuma shima yayi lasting for an hour sunyi inviting photographer mace giwar mata photography sunsha pose iri iri da hotuna sai karfe 11 sannan suka tashi event din shima mamii ta kirasu ta dan masu fada suna mata su kai 11 su kadai suna event, koda suka dawo gidan shiru dan haka kowa ya wuce dakin barcin sa a gajiye masu bacci nayi masu wanka nayi har suka gama duka suka kwanta bacci a gajiye gashi hidiman biki dole su tashi early in the morning duk da babu event din rana sai yamma, basu jima da kwanciya ba dukkansu bacci yayi gaba dasu.¹⁸

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]