[Advertisements⬇️]

INAAYA CHAPTER 6 - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

INAAYA CHAPTER 6

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Washegari wurin karfe 10 suka tashi na safe suna tashi suka tayar an hada breakfast kosai da kunu sai masa da miya da tea breakfast dinsu sukayi sannan sukayi wanka suka shirya suka fito parlour duk kowa ya fito banda Aliyu nan daada take cewa “ni kam banga mijin nawa ba ko yana ina” baffah yace “ai mijin naki baya son mutane sosai bansan me yake damunshi ba” murmushi daada tayi sannan tace to azo a kai mishi breakfast har daki mamii ta kalla su inaaya tace su dauka su kai mishi haka suka dauka kulolin suka nufa dakin sukayi knocking shiru sannan suka bude suka nufa kan centre table suka ajiye kulolin suka fito suka koma parlour.

+

They spent four days in yobe sun yi visiting Yan distant family dinsu na can anyi zumunci sosai ranan sunday suka dawo washe garin ranan ya sa’id ya koma US saboda kammala karatun nashi dama ba wani hutu ne me tsayi ba, su aneesah duk sun koma school shiyasa gidan baya ma inaaya dadi dan haka tatattara ta koma gidan su inteesar tana kwana a can. Lokaci gudu yake sosai har ya kama ranan da ya rage saura one day su inteesar su koma switzerland sunyi visiting lots of places su duka 4 best friends din sunyi having fun sosai, inaaya da inteesar ne zaune a daki inaaya nata faman taya inteesar packing ba da kaya dayawa tazo ba but saboda shopping din da suka sha yasa kayan nata sukayi yawa inaaya ta kalle ta with teary eyes tace “intee I’m going to miss you so much I can’t believe su daddy refused to let us study in the same school tho i know haka Allah yayi but I’ll miss you so much I won’t be seeing you till next year” smiling inteesar tayi mata tace “come here love” tafada tana dan hugging din inaaya ta side sai tace mata “sorry babes we wilk talk everyday chat call FaceTime duka and you know it won’t be in a year akwai ya sameer’s wedding in 3months and if ya leena and ya leesha’s wedding is fixed we’ll come I’m sure” dan smile kawai inaaya tayi ta gyada kai to lighten up the mood inteesar tace “or even mimi’s wedding” dariya sosai inaaya ta shiga yi sannan tace “yeah mimi’s yanda takejin ya habeeb din nan ai bata ki anyi fixing ba I’m sure duk sai ta riga mu a cikin peer group din mu” dariya itama inteesar tayi tace “mimz my girl ikr but kina iya ki rigata fa” tana ma inaaya winking, dan dukan wasa tayi mata suka ci gaba da packing kayan suka gama they ate lunch suka koma a daki sai bayan sallahn laasar sai ga mimi da sultaana sunzo dama sunyi zasu kwana a nan saboda next day inteesar zasu koma so suna son suyi spending time together.

Fareed da aliyu ne zaune a parlour din dake part din aliyu yana ce mishi “man duk ta kare zani kara zama dan family naku sosai sosai yanzu fa twice naje wurin khadija gidan baffah and things are going good between us so far and I’m so happy, kallonshi aliyu yayi ya kakaro murmushi sai yace “it’s so nice I’m so happy for you man Allah ya zaba mafi Alkhairi” amsa mishi fareed yayi da amin sannan ya sake kallonshi yaga yanda face nashi yayi sai yace “aliyu why are you doing this to yourself kai baka yadda da qaddara bane, yana cikin articles of faith believe in destiny whether good or bad you don’t know miye Allah ya tanadar maka da ya dauke wancan sai ka yi ta mishi godiya saboda bai baka abunda kakeso ba sai ya tanadar maka abunda yaga yafi maka, all this thing won’t help kace you’ll live your life this way magana ma sai tazama necessary zaka yi ta, smile! Be free enjoy the moments of your life! Be happy” nan ma kakalo murmushi aliyu yayi yace “thats what I’m trying to do fareed, but it’s so hard like extremely hard it’s the hardest thing I’ve ever come accross in my entire life I don’t know how i fell so deep for her that it’s hurting me so bad stopping me from being the real me” dafa shi fareed yayi yace “you need to try harder and I think the only solution to your problem is to get someone in your life open up to her let her in and I’m sure you’ll move on and forget everything not completely tho.” Gyade mashi kai kawai aliyu yayi sannan fareed yaciga da ce mishi “ai maybe next zuwan ka nigeria ma aurena ne zakazo” hitting nashi aliyu yayi yace shameless! Haka suka yi ta firan su na abokai har lokaci ya wuce.

Sun sha pictures more than hundred da ciye ciye sosai sukayi having last day fun dinsu har different games sukayi playing sai 2 na dare sannan suka bacci saboda flight din karfe 3:00pm ne na washe gari. Da safe tunda suka tashi wurin 11 duk da kaga daya daga cikinsu jiki sanyaye saboda missing din junan da zasuyi duk jika ba kwari suka shirya wurin karfe 12 suka fita daga gida gidan su inaaya aka fara nufa sannan duk a tare dasu daddy suka nufa sunny vale gidan baffah inda yafi kusa da airport a can ma hadu wa sukayi suka wuce airport, koda suka isa 2:30pm lokacin a airport din suka tsaya duka har aka fara announcing zasu fara boarding har kuka suka sha su inaaya mimi inteesar da sultaana at first da inteesar taga sunyi breaking down tayi kokari itama kar tayi amma in vain bata san sanda hawaye suka zubo mata ba da kyar suka rabu da juna sukayi sallama da kowa sannan suka tafi sukayi boarding suka shiga jirgi karfe 3:10 jirgi nasu ya tashi haka with heavy heart duk suka nufa motocin su kowa ya nufa gidan sa.

STORY CONTINUES BELOW

*one week later

Inaaya ce kwance kan gado tana kallo a macbook dinta tana kallon yolo wayanta taji yayi ringing ta duba kawai taga inteesar ce da murna ta dauka suka sha firan su sannan ta kashe wayan taci gaba da kallonta kawai sai taji an bude kofan dakin nata tana juyowa taga mamii ce sai tayi pausing kallon tatashi tana murmushi tace “ohh mamii kin tashi baccin naje dakinki naga kina bacci sai ban tashe ki ba” smiling tayi tace “eh nima yanzu natashi saboda wayana da yayi kara ummin ki ce ta kirani wai za azo neman auren su aleena,aleesha da ummi ranar Saturday” wani irin murmushi a fuskan inaaya tace “wow mamii da gaske kaiii wedding bells I’m so so happy wallahi I can’t wait” dariya mummy tayi mata tace “ai kuwa dai kuma wai idan sunzo zasu zo duka da goron saka rana and kawai za a hade shi da na sameer saidai kawai ayi differentiating time din daurin auren kaman Friday a yi na sameer a can kano su kuma su ukun su baffah sunyi magana da iyayen nasu maza ayi a abuja kawai tunda duk abu daya ne akan ace aje yobe a daura na aleesha aje bauch ayi na aleena sannan a dawo kano ayi na ummi, so yanzu duk abuja za ayi bikin idan an gama sai a raba kowa wasu su kai wannan wasu su kai waccan wasu su tsaya budan kai na amaryan sameer” gyade kai inaaya tayi tana cewa “lallai kam akwai hidima sosai mamii” dariya kawai mamii tayi suka ci gaba da fira da diyar ta ta har mamii tace “ai saukin abun ita ummi da an kaita za a dawo saboda su yan kano ba sa wani walima ko budan kai so kinga ana iya kai ta sai the next day tunda safe a biyo jirgin safe to abuja sai ayi waliman aleesha sai budan kan sameer ranan Saturday bayan an tafi da su aleena ita aleena ce kawai dole sai wasu sun tsaya a can gombe a gama budan kai sannan” inaaya tace “ai kuwa hakane mamii gaskiya I’m so happy Allah yasa Alkhairi” mamii tace “amiin ya nuna mana da rai da lafiya sune masu wahalan ya kuma ci da ku yan baya” smiling inaaya tayi tana blushing ta rufe fuska wai ita kunya tana cewa “kaii mamii as small as i am” dariya mamii kawai tayi tace “ja’ira zaki sani ko ba karama ba kowace uwa nason taga ta rabu da yaranta mata lafiya tayi masu aure” bata sake cewa komai ba mamii kuwa tashi tayi ta nufa kitchen.wurin karfe 7:00pm na dare bayan inaaya ta gama sallah ta kira sultaana ta face time suna ta fira tana gaya mata yanda za a saka ranar aurensu aleesha har dai mimi da inteesar sukayi adding cikin call din suka sha firan su sunyi ya fi one hour sannan suka kashe wayan tayi sallahn isha ta sauka parlour ta tarar da mamii twins da aneesah zaune a parlour cikinsu taje ta zauna suka fara fira a haka sukayi dinner din su saboda daddy baya nan yayi tafiya.

Aliyu ne zaune kan sofa dake dakinshi ya na ta faman packing kaya wayanshi yayi ringing yana dubawa yaga abbah ne nan da nan ya dauka yana gaisheshi da girma mawa a dayan bangaren kuma abbah yace “MashaaAllah aliyu!Ka gama shirin na ka ko” yace “eh abbah na gama flight din karfe 5:30 ne yanzu ma haka abubuwa kadan zani ida na wuce airport” abbah yace “to shikenan yayi kyau Allah ya kiyaye finally! Zaa baro London kuma nan switzerland din ma ba dadi ne dashi ba sai godiya kawai” murmushi aliyu yayi yace “eh abbah amma ai nafi son switzerland!” Abbah yace “to madallah saidai ka iso Allah ya tsare” ya amsa ma abbah da amin ya kashe wayan ya saki ajiyan zuciya yana jin dadi finally zaya koma switzerland da aiki yasamu wani a can don dama ya gaji da london din.

*two weeks later

Inaaya na bacci kawai taji wayanta na ringing tsaki tayi saboda batason tashi ta mika hannu ta kashe ringing din sai 11 ta tashi taga 10misssed calls from sultaana kiranta tayi tana dauka tace “ke lafiya tunda safe kika wani tada mutane daga bacci” dariya sultaana tayi tace “useless this your sleep ya kusa ya kare guess what?” Rolling eyes inaaya tayi tace “what” da ihuuu sultaana tace “admission is ouuuuuuuuut and yeah sun bani medicine” da karfi inaaya tace “woooooow! Wooooooow!!! Doctor sultaana in the making I can’t believe this finally we’re going to the university” nan sukayi ta murnan admission din da kawarta ta samu itama inaaya tace zata tambaya daddy idan na baze university ya fito a haka suka kashe wayan, tana kashewa ta sauka kasa da saurin da taga babu kowa kawai sai ta juya ta nufa dakin daddy tayi knocking aka bata izini ta shiga yana zaune kan study chair nashi da laptop a gabansa kaman aiki yakeyi mamii kuma na zaune a kan bed din dakin zuwa tayi ta rungume daddy tana cewa “daddy sultaana just called me tace admission nasu ya fito nile university an bata medicine mu kam namu har yanzu bai fito ne ba?” Murmushi yayi yace “our great hacker is already eager to start going to unii be that?” Murmushi tayi tace “yess daddy” sai yace “to dama abunda nake gaya ma mamiin naki kenan jiya ya fito Alhamdulillah an baki computer science mimi kuma Law duk dai abunda kukeso” tsalle tayi tana ihun murna tace “thank you soo much daddy na I love you” Murmushi kawai yayi mata sai ta koma ga mamii tayi hugging nata tana ta jin dadi ta fita zuwa dakin ta aguje don ta sanar ma mimi. Tana zuwa tayi dialing number mimi tana dauka ko sallama babu tace “mimzzzzzzzzz guess what” tace mata what? sai tace “admission is out yanzu daddy ya gaya mani an baki law and ni kuma computer science” nan itama mimi tasa ihun nata sukayi ta murna nan ma ta sanar mata da sultaana ma tasamu a nile nan suka hada conference call sukayita rejoicing har planning sukayi on going for university shopping they were so happy.After two days dafitowan admission din nasu inteesar ma take sanar dasu nasu ya fito ita da ahmad a nan university of zurich a switzerland ahmad architecture ita kuma inteesar medical laboratory joy dinsu ya karu sosai they were all happy for each other and praying for the best a school life din nasu da zasu fara.three months later

Inaaaya kinyi sauri kin sauko ko sai na zo nan dakin na sauko da ke yarinyar sai nawa kullum idan za a fita sai kin bata wa mutane lokaci baki komai on time mamii ta fada sai ga inaaya na saukowa da sauri daga stairs sanye da wani lace maroon da blue dinkin fitting gown da blue veil sai silver jewelry da wristwatch da bag blue tayi kyau sosai ta kara haske bawani make up a fuskan nata she was just glowing abun ta tana tafe tana cewa “sorry mamii wlh dankwali na tsaya daurawa kar na dauko shi hakanan ki mun fada” dan hararanta kawai mamii tayi tayi gaba abunta.Alot has happened cikin four months din nan Daya wuce including bikin ya sarah two months back sun sha biki sosai amarya tayi kyau an kai ta garki a nan abuja suma ba a barsu a baya ba don su inaaya sunyi kyau sosai har wurin dinner din wani abokin ango yayi ta bin inaaya ta bashi numbern ta tace mishi ai ansa mata biki a lokacin tace mishi saura 4months ayi aure babu yanda ya iya yayi mata Allah yasa Alkhairi ya barta su mimi kam da sultaana sukayi ta mata dariya har sultaana tace “ko ba four months ba to Allah yasa a aurar da ke nan da four months din” ita kuwa dariya tayi tace Allah ya sawake haka sunji dadin bikin sosai saidai videos dayawa sukayi ma inteesar saboda tayi missing alot,bayan bikin abubuwa shima da dama sun faru anata shirye shiryen bikin su aleesha ciki harda fara lectures din su inaaya one month ago makarantan is good so far har inaaya tayi wata friend ihsan yar maiduguri ce yarinyan amma a nan abuja suke zama, duk cikin department din nasu ihsan ce kadai friend dinta itama ihsan babu ruwanta sai fara’a tanada fara’a sosai,mimi ma quiet alright tana enjoying makarantan tayi wata friend mai suna firdausi tana da kirki ba kadan ba ita yar katsina ce a hostel take zaune cikin school, haka sultaana ma tayi lots of friends a makarantan nasu saboda akwai ta akwai kawaye babu ruwata, so far everything is good a rayuwansu relationship din mimi da ya habeeb kullum kara karfi yakeyi har ta kai they can’t sleep without seeing each other kullum sai sun hadu haka haka dai rayuwar tasu ta kasance, khadija ma da fareed sun fara getting along sosai. Yanzu ya rage saura kwana 10 bikinsu aleesha yau ne zaa kawo kayan lefen aleeshan a gidan baffah shiyasa mamii ke ta sauri suje su ida shirye shiryen tarban baki and in a week abbah zayazo nigeria da iyalanshi saboda auren yaran nasu. Mota suka nufa suka shiga twins ne a gaba sai mamii da aneesah da inaaya a baya shiru kake jin motan har suka isa gidan baffah suna shiga suka tarar da motan baba nan sunsan cewa su mama da haneefa sun iso definitely suna shiga kuwa suka tarar dasu a parlour suka gaisa sannan inaaya tayi sama dakin mimi, wurin 4 zasuzo bakin, tun 2:00 aleesha naji na gani aka sa ta bar gidan saboda a al’adar su idan zaa kawo kayan lefe amarya bata zama a gida, gidan wata kawarta ta tafi sukayi catching up har sai bayan isha da ta kira ta tabbata sun tafi ta dawo. Tunda ta tunkaro kofar take jin maganganun mutane wasu nata guda gida cike da mutane kaman bikin akeyi duk family an taru har da dangin ummi suma sunzo da yawansu tana shigowa aka fara shewa ana cewa “ahh ga amaryan tamu fa ta dawo amarya tayi goshi wallahi” wata kanwar ummi anty sakina ta jawo aleesha tana cewa “aleeelee you need to see the boxes MashaaAllah mubarak yayi kokari kinyi goshi yanda ya kamata diyata 12boxes da kit 2 komai na ciki designers MashaaAllah ai abun baya faduwa sai an gani Allah ya tabbatar da Alkhairi a wannan auren” dan nokewa aleesha tayi tana jin kunya cikin zuciyan ta tace “amiin” haka anty sakina ta zaunar da ita nan parlour din ta dinga bata labarin lefen nata da yan uwan mijin nata da sukazo. Sai karfe 9:00 na dare sannan su inaaya suka koma gida nan suka hada conference su hudun dasuka saba suka yita labarin lefen and how it was inteesar dai ta kagara suzo don at first bazata zo bikin ba saboda school so, sai tasamu mid semester break sai abbah yace zasu iya zuwa taji dadi ba kadan ba shiyasa yanzu she can’t wait for lokacin.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

A gajiye aliyu ya fito daga aiki yau saboda patients dayawa motanshi ya nufa ya shiga ya tada ta ya nufa gida yana zuwa dakinshi ya nufa saida ya sakin ma kanshi shower sannan ya fito hade da yin sallah sannan ya dan kwanta ya huta kan bed saboda gajiya rufe idanuwan sa yayi kamar mai bacci sai kawai abun ya fado mishi a zuciyan shi yana cewa “does this means su baffah sun bar mani maganan aure ne cux sunce sun bani two months it’s been like 4months already basuyi mun magana ba sanan kuma basu yi hooking di na up with any girl ba, oww how I wish hakane basu sake mun maganan” duk ya gama fadi a cikin zuciyar shi sannan ya fada wani tunani daban about his past kafin kace mi idanunshi sun rikida sun yi jajjawur sai numfashi yake da sauri sauri jikinshi nata shaking yana ta fadin “why jaan why whyy” sai ga ammah ta shigo dakin nashi tana ganin condition din shi ta fita a guje tana kiran abbah, abbah na zuwa da kyar suka sa shi mota suka nufa asibiti dashi suna zuwa doctor yayi admitting nashi yasa masa drip yace yanzu za azo ayi mishi test aga me ne yake damunshi. Gwaje gwaje dayawa kusan two hours kafin doctor din ya fito bature ne doctors din yace ma abbah su je office nashi suyi magana abbah ya amsa da to ya bi bayanshi ammah kuma dakin ta shiga ta duba dan nata suna shiga office din ya nuna ma abbah sit ya zauna shima ya zauna sannan yace “Sir your son is alright for now he just needs rest because he has malaria fever but also I observe one thing since you brought him to this hospital he’s shaking and murmuring something and i came to the conclusion that what he is saying might be related to his sickness,  he got a panic attack which I relate it to maybe something happened to him that caused it  maybe he thinks alot he doesn’t open up to anyone,he’s depressed,he lost something or someone he values alot or something related to these incidents I mentioned. so, I’ll advice you to lure him out of this state by talking to him almost all the times to stop him from having time to think and make him open up to you, if something happened to him advice him on it if it’s something he lost assure him he’ll get even better thing than what he lost he’s keeping lots of things to himself

That’s why he’s depressed and if you try this things I just told you I’m sure he’ll be fine by god’s grace” godiya abbah yayi ma doctor din yace “InshaaAllah I’ll doctor thank you i appreciate” Murmushi likitan yayi ma abbah har abbah ya tashi zai tafi sai doctor din yace “it’s nothing sir, but also advisingly if he has a wife she should take that responsibility cux she’s like the closest person to him cus they stay together that is if he has one” Murmushi kawai abbah yayi yace ok sannan ya fita office din ya nufa dakin da aliyu yake yana shiga yaga ammah zaune bakin gadon hawaye ya silalo mata a fuskan ta abbah ya matso kusa da ita ya dafa ta ta juyo a hankali yace mata “habaa ammahn aliy he’s alright nan da two hours za a sallameshi bacci yakeyi” murmushi kawai ammah ta kakalo sannan ta gyada kai sai yake gaya mata duk yanda sukayi da doctor din ta jinjina maganan sosai sannan ta kalla abbah tace to yanzu ya za ayi dan jim abbah yayi sannan yace “toh! Zanyi magana da su baffah idan munje nigeria, zamuyi meeting mu ga yanda zamuyi” gyade kai ammah tayi. Sai bayan two hours lokacin har tashi yayi ammah tasashi dole yaci abinci sannan aka yi discharging din su suka koma gida, bayan two days kaman ba shi ba har aiki ya koma yaji sauki sosai ya warware.

STORY CONTINUES BELOW

Shiri kawai kowa yake yi na bikin da za ayi inaaya ma ba a barta a baya ba wurin shirin dan ma dai school na tare ta wasu abubuwan sai ta je school tayi lectures daga school wata rana ta ke wucewa gidan baffah, gashi har yanzu tana da dinki na anko guda biyu da bata karba ba sai bayan kwana uku ne ranan fitting, ta kai ma kulu abuja dinkin nata. Tafe take tana sauri zata je class saboda tayi late sai sauri takeyi tana zuwa taci sa’a prof. Ali khan ne babu ruwan shi da kora ta shiga class din ta samu empty seat bayan ihsan ta zauna, sai bayan two hours ya gama lecture din nashi ya fita yana fita ihsan ta juyo tacewa inaaya “inaaya how comes you were late” tace mata “kedai bari ihsan wlh hidima ne yayi yawa kinsan saura one week biki so sai a hankali” dariya ihsan tayi tace “sannu inaaya yanda kikasan ke za a yi wa bikin nan yanda kike fadin hidima hidima” dariya inaaya tayi kawai tace “kinga yanzu ma gidan baffah zani wuce we are going somewhere with mimi” smiling ihsan tayi tace “ohhk oo ni kam gida nayi yanzu my regards to mimi” amsa mata inaaya tayi da to! Suka nufa parking lot inaaya ta shiga mota ta tada ihsan kuma driver yazo daukanta ta shiga suka tafi.gidansu mimi inaaya ta nufa ta shiga a parlour ta tarar da anty sakina ta gaisheta sannan ta nufa sama tana shiga dakin mimi ta ga mimi tsab ta shirya tana jiranta sai aleesha zaune a gefe tana chatting a wayanta tana ta smiling sai inaaya tace “wow! Wow! Wow! Ya leesha wai kin ganki ne OMG! Your skin kanshi abun kallo ne kinga yanda kika koma gaskiya ya mubarak idan ya ganki sai ya kusa faduwa saboda yanda kikayi kyau” dariya aleesha tayi tace “useless pikin kun cika gulma fa yaran nan ina ruwanku da yanda na koma” mimi tace “uhmm inee let’s go fa yanzu ya leesha zata yita gaya miki ina ruwanki da yanda ta koma shiyasa nima na bar hyping din nata” smiling sukayi sannan suka fita suna ce mata sai sun dawo suna fita inaaya ke driving suka nufa wurin event planner duk basa son brides din su sani they were secretly planning a bridal shower for them su duka cousins din har asoebe na bridal shower sun fitar suka samu event planner ita keyi musu planning surprise din nan event uku ne dama zasuyi amaren sai su kuma su inaaya zasuyi masu surprise din daya, za suyi henna party ranan Wednesday , sai kamu on Thursday and then dinner ranan Friday sai ranan Saturday after nikah kowa za a tafi da ita matrimonial home din nata, shine suke shirya bridal shower ranan Wednesday night just few friends din amaren sai su cousins shike nan.

A kwana a tashi yau ta kama Tuesday ana gobe ranan da za a fara events kuma ranan da abbah zayazo da iyalanshi hidima sosai akeyi gida cike kowa yazo daga garin da yake domin taya murna yan uwan ummi daga yola sunzo dayawa guest house aka kai dayawansu saboda cikan da gidan yayi su aleena ma duk suna abuja inda za ayi bikin nasu da dangin mahaifinta daga bauchi suma da yawansu haka itama ummi duk yan uwan mahaifinta sunzo daga garin kano gidan baffah ya cika sosai da ka shigo layin gidan zakaga yanda ya cika da motoci, amare kam saidai gidan daddy dukkansu suka tattara suka koma da kawayensu da masu yi masu gyaran jiki. Jirginsu abbah da safe ne wurin 10 sukayi landing da abbah da ammah da aliyu da inteesar da ahmad banda naseer da ya dade a nigeria ya kusa one month tun bayan kammala karatunshi dayayi ya zo nigeria yana kano, tunda suka iso driver ya dauko su wannan karon saboda hidima inteesar ta kasa rufe baki ko gida bata je ba tace a sauketa gidan daddy inda aminnan nata ke jiranta sai a ranan zasuje spa first then to the saloon suyi gyaran gashi da pedicure ko da aka sauketa gidan daddy da dan gudunta ta shigo tana shiga few people ta gani a parlour ciki harda mamii tayi hugging din ta tana cewa “ahh diyan mamii har an sauka” amsa mata tayi da eh ta gaishe da sauran mutanen sannan ta hau sama da gudu dakin inaaya ta bude kawai sai taganshi a cike duk mutane kawai sai taji muryan mimi tana cewa “inteeeeeeeeeeeeeee” can karshen dakin take zaune kaman waya takeyi ta taso tana hugging intee “how I missed you babe” sun mamanta da yan dakin saida suka saki juna sannan tace “oww sorry sannunku mutanen daki an wuni lafiya” dariya sukayi mata sai aleena tace “sannu intee sai yanzu kika san yan daki” dariya intee tayi don sai a lokacin ta kula duk su aleena na nan da aleesha da ummi da friends din su gaisawa tayi dasu tazo zata zauna kawai sai inaaya ta fito daga closet tana cewa “mimz lets get going” bata ida rufa baki ba sai taga intee ihuu tayi tana cewa “inteeeee when did you get here OMG!! I missed you so much” hugging juna sukayi kafin suka tashi suka nufa hanyan waje suna cewa su aleena sai sun gansu don yau kam sunada alot to do zasu bude kofa sukaga an bude khady ce tashigo ita da haneefa da farhana hugging din inteesar sukayi sai suke ce masu saloon and spa zasuje but zasu fara zuwa su dauko sultaana from there zasuje wurare sai khady tace “call me idan kun gama da saloon we have somewhere to be” amsa mata sukayi da toh sannan suka fita a kasa suka ga mamii suka ce mata sun fita sannan sukayi waje inaaya ke driving sai da suka je suka dauko sultaana itama taji dadin ganin inteesar they hugged each other sannan suka fito suka nufa spa for body treatment bayan nan zasu shiga saloon din dake kusa da spa din a asokoro.

Suna zuwa spa din sun ci sa’a babu mutane sosai nan da nan aka farayi musu abunda ya kai su it’s female only duk ma aikatan mata ne sukayi setting bathtub din cikin 20minutes da different scents da abubuwa cikin 1hour 30 minutes suka gama da spa din sunyi kyau sosai their skin was so soft and glowing sosai kaman su ne amaren saida suka gama suka nufa saloon din mimi inteesar da sultaana su ka yi retouching gashin su inaaya kuma tayi steaming and stretching saboda bata amfani da relaxer, bayan sun gama a saloon din akayi masu pedicure sai da suka gama tsab zasu tafi sai inaaya taga wata zaune ana yi mata kitso a saloon din tiny braids sai ya burgeta tace masu “seriously guys I’m braiding my hair and you’ll have to wait for me” mimi tace “to yau mun shiga uku sai dare zamu bar wurin nan” yarinya da ake yiwa kitson tayi smiling tace “habaa ai mai kitson ba daya ba kuma wlh sunada sauri” smiling kawai sukayi mata inaaya ta zauna wata tazo wacce zatayi mata kitson ta fara mata kana na kana na gashi abunka da mai gashi har suka gaji kowa na rike da wayanta tana chatting ita kuwa mimi tana aikin wayan ta da ya habeeb tana shagwabe fuska kaman tana gabanshi “ya habeeb ni I’m tired and hungry fa ka gaya musu su mai dani gida” murmushi mai sauti habeeb yayi yace “come on baby don’t cry I’ll be at your service now what will you like to eat? Besides dama inason ganin ki cux tunda aka fara hidiman bikin nan bana ganin ki sosai and I missed you so much my love” kara narke murya mimi tayi sukaci gaba da waya tace mishi tana son shawarma na chicken capitol da ice cream sannan tayi mishi describing saloon din sannan ta kashe wayan inteesar ta kalleta ta tabe baki tace “uhmm Allah ya bamu masoyan nan mu ma dai” sultaana tace “hmm! Ke dai bari intee ai muna ganin abu keda baki nan ma” dariya kawai mimi tayi sai kusan after an hour ya kirata yace he’s outside sannan ta fita yana cikin motanshi tunda ta fito yake kallonta har ta shigo motan ya furta MashaaAllah a ran shi sai yace “OMG!! Love I’m falling in love all over again kin ganki kuwa” blushing mimi ta fara yi ta gaisheshi kan ta a kasa yace mata “look at me mimi” dan dagowa tayi ta kalleshi tayi saurin dauke kanta yace “ohh no wannan kunyan naki just look at me for one minute dakyar aka samu ta iya yace “i love you mimi” ai ba shiri ta duke kai saboda yanda kalaman nashi suka daka zuciyanta, smiling yayi yace “my love is so shy but gaskiya kin mun kyau kaman na sace ki na tafi dake I don’t want anyone to see you kinsan wurin biki da anga fine baby sai a fara bin ta” smiling tayi tace “kai ya habeeb ai sai nace musu am taken” yaji dadin furucin nata sosai a haka sukayita magana har video da pictures yayi mata secretly idan tana blushing har a snapchat dinshi yayi posting wani video amma ya rufe fuskan ta ba a gani yasa caption “the queen herself”. Sultaana dake zaune tana ta faman kallon stories a snapchat kawai taga ya habeeb yayi update tana budewa tace “ohh ni hafsatu intee come and see this shameless lovers” da sauri inteesar ta taso tana gani tace “ohh love dadi mimi ta kone wlh” ta fadi tana dariya inaaya ta karba ta gani itama tace “yo ai su duka suka kone” dariya sukayi gaba daya. saida mimi tayi 30minutes sannan ta shigo da ledoji a hannunta shawarma ne guda 6 na chicken capitol da ice cream 5 cups sai wani pack da galzed donuts a ciki dadi mimi saboda san donuts tace “uhh he’s such a darling” dariya sukayi sultaana tace “ohh ni wai ko kunya ta bakiji mimi ya ya na ne fa” dariya mimi tayi tace “kunya my foot” sukayi dariya duk kowa ya dauka shawarma ya fara ci dama yunwa sukeji, har dayar yarinya da akewa kitso sukayi ma tayi taci donut daya sai da sukayi 3hours aka gama ma inaaya kitso a tare suka furta “MashaaAllah kitson yayi kyau gashi kanana ga gashin sai shining yake yana kamshi gashi black sosai ga tsayi ga shi natural hair ne yana da cika sosai.

Wurin fitting suka nufa bayan sun gama da saloon din komai yayi suka karba duka kayansu na bikin suka nufa gida sai a kan hanyansu wayan inaaya yayi ringing khady ce ta kirata tana dauka tace “hello sorry ya khady gashi nan zamu zo gida we’ll pray and then go out” khady tace mata “ohhk dama ana neman key din guest part ne mamii tace a tambaye ki” inaaya tace “ohhk wallahi na manta yana a handbag dina sai nazo yanzu baki za a saukar ne” khady ce tace “ohhk barshi ma ba baki za a sauke ba dama ni nakeso zanyi bako me I’ll use ya sa’ids part naga an gyara shi” inaaya tace “ohhk eh an gyara ai shima gobe zayazo InshaaAllah, uhmm ya khady wane bako za ayi ya fareed ne” inaaya ta fada tana dariya ita kam Khady tsaki tayi mata tace “ina ruwanki” sannan ta kashe wayan. Sai after one hour suka iso gida saboda hold up din daya tare su ba laifi gidan nasu ya dan fara cika su ma daki suka nufa suka tarar da su ya leesha duk da friends din nasu ga abinci kala kala da snacks da drinks an kawo masu aleesha tace “ahh MashaaAllah babies kun ganku kuwa kaman ku ne amaren especially inaaya wannan kitso haka kaman wata amarya yayi kyau and your skin is just glowing” smiling sukayi ta yi ana ta cewa sunyi kyau har da kawayen su aleesha din, sallah sukayi suna gamawa wayan inaaya dake hannun aleesha tayi ringing a jiki taga E.planner sai tace “inaaya wacece E.planner kuma” ba shiri inaaya tayi sauri ta karba wayan ta fita saida ta gama answering ta dawo sai ya aleesha ta kara tambayan ta miye wani E.planner inee sai inaaya tana dan stammering tace “erm…ermm….uhmm dama event planner ne” da surprise a fuskan su aleesha sai aleena tace “me kikeyi da event planner ke kuwa?” Sai inaaya tace “uhmm mamii ce fa da mama suka ce mu nema musu event planner na budan kai din ya sameer” sai a sannan su mimi da su haneefa suka saki ajiyan zuciya sai su aleesha suka ce “ohhh ok” suka ci gaba da firansu sai inaaya tace ma haneefa ina ya farhana da ya khady? Sai haneefa tace “uhmm suna can suna what they can do best mana” ta fada sacarstically dariya su inaaya sukayi sukace “suna ina” sai hanifa tace “part din ya sa’id mana” fita inaaya tayi ta nufa part din ya sa’id tana shiga kuwa ta gansu dayake parlour din nada girma can gefe daya ya naseer ne da farhana dayan gefen kuma ya fareed da ya khady sai zancen su sukeyi sallama inaaya tayi ganin duk hankalinsu baya nan tayi gyaran muryan su mimi kuwa dariya sukayi sai inaaya tace “assalam alaikum lovers munata knocking anyi shiru” dariya suka yi su duka sai inteesar tace “ai bari next time bikinsu zamusha sai mukaisu suyita love love dinsu can” harara khady ta watsa mata tace “to ku kuma sarakan sa ido” dariya sukayi suka gaishesu sai ya fareed yace “sannunku yan mata” smiling sukayi inaaya tace “uhmm ya fareed zaka bamu aron ya khady for few minutes yanzu zamu maido maka ita fa” smiling yayi yace “na baku amma in ku ka jima zan biyo ku” dariya sukayi suka ce toh sai ta juya tace “ya nass kai ai na gida ma ne baza mu tambaya permission ba zamu dauka ya farhana few minutes” dariya kawai yayi ya kada kai yace “ohh ni bansan san da inaaya ta fara magana haka ba” dariya kawai tayi sai suka dan fita waje inaaya tace “ya khady event planner ta kirani tace muzo muyi checking out wasu decors muyi selecting finally wanda muke so da kuma cakes sai gowns din da amare zasu saka” farhana tace “to let’s get going mana bamuda time gobe da rana akwai event we won’t get time to go yanzu yakamata a yi komai” inteesar tace “yess shiyasa ai mukazo amma ku you’re busy ma dai” farhana tace “I’ll tell ya naseer zamuje wani abu came up he’ll understand” sai khady tace “yess me too you guys give me 10minutes”. Sai bayan 10minutes sai ga khadija da ya fareed sun fito yayi musu sallama har yace “kun dai dauketa duka ba na few minutes ba” dariya mimi tayi tace “sorry yaaya inlaw hakuri zaka mana” murmushi yayi ya tafi sai farhana ta fito tace to muje ya naseer yana nan gidan zayaje wurin su abbah anjima” ok suka amsa sannan suka nufa mota su duka bakwai dayake sienna ce ta daukesu su duka khady na driving sai farhaana a gaba sai tsakiya haneefa da mimi da sultaana sai baya inaaya da inteesar suka tafi gurin event planner.¹⁶

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]