IN AN KI JI. (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 6 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

IN AN KI JI. (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 6 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

sallamarsa, kafin ya samu wurin zama Mallam Adamu yace “Ba nace zan nemeka da kaina ba? ko ba kaine yaron nan na wajen Alhaji ba?” Cikin girmamawa Sulaiman yace “Eh ni ne” Mallam Adamu yace “Ai na shaidaka, kaje ni da kaina zan nemeka da zarar abin ya tabbata”.
Sulaiman ya fito a sanyaye jikinsa babu kwari, gani yake yanda jama’a suka yiwa Mallam Adamu yawa zai iya mantawan da shi, wani sashe na zuciyarsa yace “To kai me zai dameka tunda

gashi ya ganeka kuma yace da kanshi zai nemeka, ai yana sane da kai tunda kaga bai mantaka ba”. Ji ya yi wani kwarin gwiwa ya shige shi ya kama hanya ya tafi cike da karsashi.
Bayan kwana biyar sai Sulaiman ya ji ya kasa hakuri, dan haka washe gari shirya ya sake komawa ofis din Mallam Adamu sai dai ya yi rashin sa’a ofis din a garkame alamun baya nan, koda ya tambayi wani masinja sai yace masa ya zo amma ya fita, ganin Safiya ce sai Sulaiman ya yi tsamanin wani wajen yaje zai dawo, kan haka ya nemi wuri ya zauna zaman jiranshi, shiru-shiru babu shi babu alamarshi amma duk da haka. Sulaiman bai hakura ba, zuwa ya yi yaci abinci ya yi sallar Azahar ya dawo ya ci gaba da zaman jira, a hankali mutanen dake wurin suka fara tafiya daya bayan daya suka bar Sulaiman anan, sai bayan la’asar ya tabbatarwa kansa cewar Mallam Adamu ba zai dawo ba, haka ya bar wajen zuciyarshi na kuna saboda takaici Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka ya ci gaba da jaular zuwa ofis din Mallam Adamu tun yana kirgawa har ya daina, wani

lokacin ya same shi wani lokacin kuma ya tadda Ofis dina garkame, ko ya same shin ma kullum maganar daya ce.”Kai me yasa baka da hakuri ne? Ban ce ni da kaina zan neme ka ba?” Kullum wannan maganarce ke raba Sulaiman da Mallam Adamu.
Abin duniya ya taru ya yiwa Sulaiman yawa, baya son wannan hanyar ta kubce masa domin bai san inda zai samu wata ba, ya rasa abinda zai cewa Safina gashi a kullum hura masa wuta take ganin lokaci na kara kurewa, zirga Zirga da zullumi suka sa ya yi zuru-zuru ya rame kamar wanda ya kwanta rashin lafiya, ga kuma wata babbar damuwar ta kunno kai a kasuwa domin kuwa sun gudanar da lissafinsu na shekara kuma bai haifar da sakamako mai kyau ba, babu karuwar da aka samu sai ma faduwa, kayan da aka riska basu kai wadanda aka bari bara ba,hakan bai rasa nasaba da kudaden da ya rika kashewa da kuma saka ido da baya yi akan sauran yaran shagon sakamakon zaman da baya yi ba, hakan ne ya basu damar cin karensu babu babbaka, hakan ne ya kawo nakasu da koma bayan da aka samu. Duk da dai shi Alhaji bai nuna fushinsa akan haka ba ba kasancewar wannan shi ne karo na farko da hakan ya faru tun da aka bude shagon, sai dai ya yi musu nasiha sosai akan su tsaya su maida hankali akan harkar dan gudun kar a kara samun haka a gabamusamman ma Sulaiman dake jagorantar wajen, bayan da ya yi musu nasiha ta bai daya sai daya wareshi ya sake yi masa tashi shi kadai domin ya lura daga bangarensa aka samu matsalar data haifar da asarar da aka yi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sulaiman ya tsinci kansa a cikin wani irin yanayi, ya rasa dalilin da yasa ya sauya, ya kasa gane irin son da yake yiwa Safina, bai iya shallake duk wata bukatarta data gabatar a gareshi ba, hakan kuma bai rasa nasaba da irin matsanancin son da yake yi mata wanda ya hadu da matsanancin burin da take da shi.
Haka Sulaiman ya kara wanke kafarshi ranar Laraba ya koma ofis din Mallam Adamu Galadanci bai tarar da kowa a bakin ofis din ba dan haka ya wuce ciki kai tsaye, wasu manya mutane biyu ya tarar zaune a cikin ofis din shi kuma Mallam Adamu ya sunkuya suna kus-kus ya yin da mutumin ya mika masa wani emvelope mai dan tudu wanda Sulaiman ke kyautata zaton kudine a ciki. Sallamar din sa ce ta sanya dukkansu suka juyo.
A fusace Mallam Adamu yace “Wai kai wane irin mutum ne mara tunani, an gaya maka haka ake shigowa without excuse? Ban ce makani da kaina zan nemeka ba? Ko kuwa zaka yi min dole ne? get out stupid!”.
Cikin matukar bacin rai Sulaiman ya fice tare da takaicin wulakanci da aka yi masa a gaban mutanen, daga nan ya lashi takobin ba zai kara komawa ofis din Adamu Galadanci ba koda kuwa certicate din Aljanna yake rabawa. Wani abin mamaki shi ne Sulaiman ko kadan bai ji haushin Safina ba wacce a dalilin bukatarta ne aka yi masa wannan wulakanci, wani abin al’ajabi ma sai ya zamana tamkar kara masa kaimi aka yi, domin kuwa alwashin ya yina ci gaba da fafutikar ganin ya cikawa Safina burinta na yin karatun jami’a babu shakka hausawa sun yi gaskiya da suka ce ‘So hana ganin laifi’.
Yana zaune cikin yanayin damuwa a kofar gida Iliyas ya zo, sallama ya yi amma tare da bashi hannu suka tafa amma sai ya gano rashin kuzari da kuma damuwa a tare da abokin nasa, bai yi nauyi baki ba yace “Abokina yaya dai? Kasuwar ce ko kuma Safina?”.
“Kasuwa komai normal, Safina ma babu matsala, matsalar dai ta karatun Safina ce”. Iliyas yace “Na fada maka fa idan har tana son ka da gaske zata yarda ta aureka in ya so daga bisani ta ci gaba da karatun a gidanka”.Sulaiman yace “Duk ba wannan bane domin nima na yadda shawarar taka, zan so ta fara yin karatun ne tukuna kafin nan nima na gama duk shirye-shiryena”. “Tunda ka me yarda kuma matsalar?”
Sulaiman yace “Ka san dai Safina ta yi jamb kuma ta samu fiye da makin da ake nema haka ma ta yi post-utme kuma ta samu nasara, sai dai ina gudun kar ayi releasing din admission list, babu sunanta ka dai san sha’anin kasar nan, shi ne naketa ‘yan buge-buge domin kamun kafa amma shiru babu labari”. Nan ya baiwa ‘Iliyas labarin zaryarsa a ofis din Mallam Sale da kuma Adamu Galadanci. Www.bankinhausanovels.com.ng
Mamaki ya kama Iliyas domin Sulaiman bai taba shawarta shi akan batun ba, wato yanzu Safina ta zarce kowa a wajen abokin nashi? Sai kuma wani abu ya bashi dariya, ya yi dariya sannan yace “Lallai har yanzu baka san dawan garin nan bashi yasa kake ta wannan zaryar, amma karya suke suce an rasa admission, ai duk Mallami abokin Mallami ne, kuma suna yiwa junansu alfarma, kai ne baka yi musu abinda suke so ba”.Cikin zakuwa Sulaiman yace “Me suke SO?”.
“Cin hanci mana, ka sandai yanzu kasar nan ta zama, wannan ne yasa Mallam Sale ya yi ta yi maka hanya-hanya saboda yana jin kunyar yace ka bada wani abu, shima, Mallam Adamu Galadanci wannan ne dalilin da yasa yayi maka wulakanci”.
Cikin mamaki Sulaiman yace “Mallam
Sale fa aminin yayana ne?” “Koma yaya suke da shi, zai iya yin abinda yafi haka in dai akan kudi ne, gashi nan kiri-kiri shima Mallam Adamu ya ki yiwa Alhaji Alfarma saboda baka bashi komai ba”.Sulaiman ya yi Allah wadai da wannan lamarin sannan yace “Yanzu shikenan zan komain kai musu kudin in dai za a samu admission din” Iliyas yace “Wannan kuma ta wuce, tun farko daka tuntubeni dabaka sha wannan wahalar ba domin akwai mutanen da zan hadaka da su, amma yanzu ma bata …ďaci ba, akwai wani professor dana yi m,sc a wajensa nasan zai taimaka amma dan gudun kar a sake kwatawa sai ka tanadi kudi”.Cikin zumudi Sulaiman yace “Kamar nawa zan tanada?”.
“Ka dai tanadi masu kauri duk da dai na san bashi da matsala domin mutumina ne”.
“Yaushe za mu je?” Inji Sulaiman. “Duk lokacin daka shirya sai muje har gida mu same shi, idan kuma baka da hali karka
takura kanka”.Sulaiman yace “Ai in dai akan Safina ne ko bashi sai in ciyo in dai burinta zai cika”. Iliyas ya bishi da wani irin kallo da yake bashi mamaki sabida ganin irin yanda ya zake akan Safina.
Washe gari ya shirya kudi a emvelope kamar yanda yaga an bawa Mallam Adamu Galadanci, kudi masu yawa ya zuba fiye da yadda Iliyas yace, so yake kudin su yiwa Mallamin kwarjini ya taimaka nan da nan Safina ta samu admission, shi yasa ya zuba kudi bana wasa ba, ko Iliyas din bai yarda ya nunawa ba saboda ya san in ya gani zai yi fada.
Da daddare suka je gidan professor a Yusuf road da yake an san da zuwan su tare suka yi dinner da iyalansa, da ma can Iliyas ya saba kai masa ziyara har gida, tuni ya gama zama dangida a wurin Iliyas mallamin suna cin abinci Mallam sai tambayoyi yake yiwa Iliyas game da harkokin ci gaban rayuwarsa tare da bashi shawarwari mamaki ne ya kama Sulaiman saboda yanda ya ji Mallam na ta faman koda abokin nasa a matsayin dalibi mai hazaka da sanin ya kamata ga kuma uwa-uba girmama na gaba.
Bayan sun kamala cin abinci ne suka kebe Iliyas ya yi masa bayanin duk abinda yake faruwa da su, ya karbi takardun Safina ya dudduba cike da yabawa bayan yagama dubawa ne ya basu tabbacin samun cikakken tallafi daga ‘gare shi wajen ganin an samarwa Safina admission. Sai da za su tafi Sulaiman ya ajiye masa emvelope din yace “Mallam ga wannan a saiwa yara alawa…” Ya katse shi “A’a kar muyi haka da ku ai ku ‘ya ‘yana ne, ku dauki kudin ku”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Suka yi suka yi amman yaki karba da kyar suka yi sa;a ya karba suka yi masa godiya suka tafi, ba karamin dadi suka jiba daya yarda ya karba saboda ko babu komai ai su ihisani suka yi a gareshi kuma ai su suka yi niyya ba tambayarsu ya yi ba.Ya zamewa Mallam Yusuf Mahaifin su Safina al’ada a duk lokacin da wani muhimmin abu ya taso yakan tara daukacin ahalinsa manyansu da kananansu domin sutattauna musamman ma idan abin su ya shafa kai tsaye, mutam ne mai neman shawara da bai cika zartar da wani abu shi kadai ba.
Bayan da suka gama hallara ne Mallam Yusuf ya fara Magana da yiwa Allah godiya sannan ya dora akai da cewar “Wata muhimiyar Magana ce ta taso, wato yaron dake neman auren Rahama ne ya turo min manyansa akan batun neman aurenta, sun zone akan a tsayar da Magana lokacin aure, sai dai ban amince musu ba a lokacin na nemi su bani lokaci domin na yi shawara sabida dalilai guda biyu,na farko dai ina son na tuntubeta ita kanta naji tana son yaron ko a’a kuma na tambayeta hakan ni da ita kuma ta tabbatar min tana son shi, dalili na biyu kuma shi ne abinda ya taramu a nan, ina ganin zai fi kyau a hadasu ita da yayarta Safina a aurar da su lokaci daya tunda dau tana da manemi, dan haka ki sanar das hi cewar ya turo da magabatansa ayi komai lokaci daya a huta”.
Kunya ta kama Rahama ta sunkuyar da kanta ta kasa hada ido da kowa a falon. Ita kuwaSafina kantane ya kulle, babu shakka maganar ta zo mata da bazata, rasa abinda zata fada tayi, ita yaushe ta shirya yin aure yanzu? Mamakin yanda aka yi su Rahama suka shirya wannan al’amarin ba tare da saninta ba.
Yaya Abbas ya kalleta “Ya dai Safina, baki ce komai ba”.
Babban yaya wato Isma’il ma ya tofa tasa “Kar dai ace yaron nan ba da gaske yake nemanki ba duk dadewar da ya yi yana zuwa wurinki?”..
Wata dabara ta fado mata gudun kar su sakata a kwana da tambayoyinsu na kwakwa sai tayi maza tace “Kamar ma yasan za mu yi wannan zaman shekaran jiya yake sanar min na dan kara hakuri akwai shirye-shiryen da yake yi kuma da kuma da zarar ya hada su zai turo ayi Magana”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Abba na su yace “To shikenan babu matsala, idan Allah yasa yagama shirin nashi sai ayi maganar, yanzu zan sa ranar auren Rahama in yaso ke ko bayan kin fara karatu ne sai asa duk da dai na so ace auren ne ya gabaci karatun amma tunda haka ne ya samu babu damuwa”. Da gama fadar haka ya mike ya bar musu falon ya tafi turakarsa.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK 2 CHAPTER 5 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK 2 CHAPTER 5 BY ZAINAB …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *