[Advertisements⬇️]

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 15 BY ZAINAB LAWAN BIRGET - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 15 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

rashin damuwa amma shi kadai yasan irin zogin da zuciyar shi take yi.
“Duk naji bayanin ki kuma na fahimci inda suka dosa ni musulmi ne na kwarai don haka na yarda da kaddara mai kyau da mara kyau, nasan Allah ne ya nufa ke ba matata bace shi ya

sa al’amuran suka juye suka zama haka sai dai naçe Allah ya saka haka shi ne yafi zama mana alheri, ubangiji ya hada kowa da rabonsa”. Nan da nan Safina ta tsinci kanta a cikin wani yanayi na jin kunya, ta sunkuyar da kai ta kasa dagowa, da Sulaiman ya fahimci halin da take ciki sai ya ci gaba da Magana “Amma kafin mu rabu ina son na yi miki wasu tambayoyi”. Nan ma tayi shiru ba amsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Shin Safina me yasa kika nemi mu rabu ta wannan hanyar? Me yasa kika zaɓi mu rabu cikin salon karya da yaudara? Me yasa kika shirya kalaman karya bayan a zuciyarki abin ba haka yake ba? Me yasa kike son dole sai mun rabu cikin yaudara bayan kina da Kalmar da za ki iya fada min na rabu dake amma kika zauna kina batawa kanki lokaci kika zauna kina ta kame kame saboda karya da yaudarar kai domin kanki. kike yaudara tunda an riga anyi walkiya ta haske duhu, tun farko kamata ya yi kice Sulaiman kayi hakuri ka janye

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

soyayyarka ba zan iya aurenka ba domin na samu mai kudi wanda ya fika, ko kice Sulaiman yanzu bana sonka kudi nake so kuma nasamu masu bani abinda yafi wanda kake bani, don haka kaje ka nemi wata, idan kika yimin wannan bayanin duk irin son da nake yi miki zan iya hakura dake koda hakan na nufin soyayyarki ita ce ajalina, amman sabida tsabar yaudara sai kika nemi ki ɓata min lokaci ki ɓatawa kanki wai shin wanne irin laifi na yi miki da kika zabi ki hukunta ni ta wannan hanyar? Ina zaton saboda bani da mahaukacin kudin da kike muradi, idan haka ne Safina kinyi gaggawa a rayuwa kuwa ba a yi mata gaggawa yau kawai muka gani, amma babu wanda yasan gobe sai Allah, bazan iya cewa ko mai akan rayuwar duniya ba domin bansan irin tanadin da Allah ya yi min a gaba ba, kuma ina tabbatar miki rashin Www.bankinhausanovels.com.ng aurenki bazai zama ta waya a wajena ba, ina rokon Allah ya yi min sauyi mafi alheri, hakika na so ki Safina so mai tsanani, amma a yau na barki bari kuwa na har abada, barin dabazan kuma dawowa gareki ba koda ke kadaice mace da kika rage a duniya”. Yana gama fadin haka ya janyo hannun Iliyas cikin wani yanayi na tsananin bacin rai mara misaltuwa, yana tafiya yana rangaji ya na sassarfa har suka bar kofar gidansu Safina bai sake waiwayo wa ya kalleta ba, Safina tana tsaye tana binsu da kallo ta kasa koda daga kafarta maimakon ta yi farin ciki sai duk jikinta ya yi sanyi ta rasa wanne irin yanayi take ciki bakin ciki ne ko akasin haka, fuskarta na dauke da wani irin yanayi, kwallar nadama da rashin kyautawa ce kawai take digowa daga gefen idanunta, ya yin da gumi yagama jika goshinta kamar an kwara mata ruwa, Nafisa ta gaji da jira tahowarta don haka ita ta zo ta finciki hannunta fada take cewa.
“Ba dai akan wannan banza kike asarar hawayenki ba? Amman lallai kin bada mata, ke da kika samu kika yadda kwallon mangwaro kika huta da kuda shi ne don asaranci za ki zauna kina bata lokaci akan talaka? Allah ya sawake miki”, taja wani matsiyacin tsaki Safina cikin shessheka tace “Rabu da ni Nafisa na koka Sulaiman yafi karfin abin banza, ni nasan wanene Sulaiman dole ce tasa zan barshi ba don bana son shi ba”.
Tunda suka tada mota suka fara tafiya babu abinda Iliyas yake banda rarrashin Sulaiman da bashi baki, shi dai Sulaiman baice komai ba domin yana cikin wani irin yanayi na tsananin bacin raid a tafasar zuciya, ji yake kamar zuciyarshi zata fasa kirjinsa ta fito, lokaci zuwa lokaci idanunshi suna digar da hawayen Www.bankinhausanovels.com.ng bakin ciki, harshen shi ya yi mishi nauyi banda daci babu abinda yake yi, sam ya kasa cewa komai, makogwaron shi sai suya yake yi, a haka har suka isa gida, Iliyas ya samu waje ya yi parking sannan ya fito Sulaiman shima ya buda marfin motar yana kokarin fitowa amman sai jiri ya soma diban shi ya yi baya zai fadi, Iliyas ya yi saurin tare shi ya rike shi har suka shiga dakinsa dake zauren gidansu, bayan ya kwanta ya dubi Iliyas da kyar da kanshi da yake tsananin sarawa yace masa.
“Kaina sarawa yake yi ina jinsa kamar zai rabe gida biyu”. Iliyas ya taba wuyan sa yaji ya dauki zafi sosai “Sannu abokina ina ganin banda ciwon kai harma da zazzabi, bari na samu maka magani”. Nan da nar ya sake shiga motarsa ya tafi wani babban phyrmacy ya hado mishi magunguna ya bashi yasha amma duk da haka zazzaɓi bai sauka ba, sai faman karkarwa sanyi yake yi, a haka kaninshi Ahmad ya iske su, ya gaida Iliyas sannan cikin kulawa ya dubi Sulaiman yana tambayar me ya faru?.
“Wallahi munje wata unguwa a hanya zazzaɓi ya rufe shi, amman alhamdulillahi yasha magunguna insha Allahu zai sauka”. Cikin damuwa Ahmad ya ce “Allah ya bashi lafiya bari na je na shaidawa Hajiya domin tun da zu da magariba naji tana neman shi”. Sulaiman ya yunkura cikin karfin hali ya tashi zaune yace. “Ahmad karka fadawa kowa ciwon kai ne kawai idan ya dan lafa zan shigo cikin gidan da kaina” Ya juya ya fita ya juya ga Iliyas yace masa “Kaima ka tafi gida kada dare ya yi nisa”. Iliyas ya girgiza kansa “Sam ba zan iya tafiya na barka a cikin wannan halin ba domin koda na tafi hankalina ba zai kwanta ba”. “Kar ka damu abokina ciwon kan ma ya
soma sauka”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“To shikenan ka karbi abinci ka ci” Ya yamutsa fuska “Bana jin yunwa ka manta na ci abinci a gidanku, yanzu dai sallah nake son nayi kasan banyi sallah isha ba”.
“Zaka iya tashi kayi alwala?”. “Zan iya mana ai yanzu na daina ganin
jirin”. Nan ya tashi ya dauki buta ya dauro alwala ya koma cikin shagon Iliyas yace ya dan jira shi su yi sallah tare, shima yaje ya yi alwala suka tada sallah, Iliyas ne ya jasu bayan sun idar suka karanto inganttun addu’o’i na yayewar bakin ciki da tafiyar damuwa wanda Manzon Rahama ya koyar damu, bayan sun idar Iliyas yace.Yaya kake jin jikin naka yanzu? Mene
ne yafi damunka?”
“Zazzabin ya sauka amma duk jikina ciwo yake yi kuma ina jin zuciyata tana bugawa fiye da kima tamkar zata fasa kirjina ta fito, ina fargabatar kardai ciwon zuciya ne yake barazanar kamani?” Cikin sauri Iliyas yace masa. “Insha Allahu zaka warware, damuwa ce kurum ba komai ba”.
“Aa abokina ina tsoron kodai bacin raine silar ajalina, domin ban san ranar da zan daina jin ciwon abinda Safina ta yi min ba”. Iliyas yace “Wato dai har yanzu ba zaka daina ambaton sunan Safina ba saboda it ace a ranka ko?”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ba haka bane ka daina tunanin Safina tana raina, domin na riga na shafe babin rayuwarta, idan har zanci gaba da sonta to na gwamace son nata ya kashe ni dana koma gareta saboda na yi alkawarion har abada ba zan sake zuwa kofar gidansu ba domin babu abinda na manta balle na ‘koma na dauko” Iliyas ya ji matukar dadin kalamansa sai a yanzu ya samu nutsuwa yace “To abokina tunda haka ne ina son kayi kokarin goge duk wani abu daya shafi Safina daga zuciyarka, ka dage ka kuma jajirce ka yakice ta daga ranka, ba ita ba ma duk wata mace ina son ka bata hutu, aure kuwa ba yanzu ba ka barshi nan da wani dan lokaci nasan daman huldar mata ba halayyarka bace, dan haka ka nutsu ka tattara hankalinka waje daya so nake ka watsar da al’amuran soyayya ka koma makaranta ka rungumi karatu domin ka samo kwalin digirinka tunda kwalinka na Diploma ne, ni zan dauki nauyin komai tundaga nemar maka admission zuwa duk wasu hidimomin karatu”. Sulaiman ya buda baki zai yi Magana Iliyas ya dakatar da shi.
“Sannan koda ka koma makaranta ba zaka bar kasuwancin ka ba, a yanzu ina son mu hada karfi da karfe mu fara kasuwanci gadan gadan”. Sulaiman ya saukar da wata ajiyar zuciya.
“Kwarai na yarda da shawarar ka abokina zan koma karatu kamar yanda ka bukata domin na lura yanzu zamani ya ci gaba kowa yana kokari yake yaga ya wadatu da ilimi wanda bashi dashi yana kokarin ya nema wanda yake dashi kuma yana kokarin ya’ zurfafa iliminsa to amma shawara ta biyu tayaya kake zaton zamu fara kasuwanci gadan-gadan alhalin kasan babu wasu kudi a kasa, dan kudaden da nake da su basu da wani yawa” Iliyas ya dafa masa kafada. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Kada ka damu ni ina da kudade, banda kudin da yake ajiye a accout dina har filayena zan saida domin mu samu wadataccen jari”. Sulaiman yace “Idan haka ne nima zan saida gidan dana gina sai mu zuba a ciki”.”Aa ba zan so ka saida gidanka ba domin shi kadai ka mallaka amma ni fa kada ka manta ina da wasu kadarorin don na saida filaye ba wani abu bane”. Sulaiman yace.
“Ai da kudi ake neman kudi, ka tuna nima fa na gina shi ne dan na saka Safina yanzu kuma babu ita ta guje ni to mene amfaninsa ya zama bakin gida a gare ni, bani da burin saka ko wacce mace a ciki, bana tunanin ma zan sake neman aure a rayuwata”. Iliyas ya yi shiru cike da tausayin abokinsa yasan dai akwai babban aiki a gabansa kafin ya raba Sulaiman da ambaton Safina domin son yarinyar ya riga ya masa illa sosai ya nakasta zuciyar abokinsa amma zai yi iya bakın kokarinsa domin ya raba Sulaiman da ambaton Safina, sai ya yi iya yinsa domi ya yakice Safina daga zuciyar abokinsa da duk wani abu daya shafeta. Yaje ya nemo Ahmad kanin Sulaiman domin ya zauna dashi saboda yanayin jikinsa sannan ya yi sallama da su ya tafi.
Iliyas koda ya koma gida bai samu barci ba saboda tunane-tunane da suka addabil kwakwalwarsa, sai jujjuya al’amarin yake yana ganinsa kamar a shirin film,. wai me yasa wasu daga cikin kyawawan mata basu fiye halarci a soyayya ba? Ya sani tun farko abokin shi yazarme a soyayyar Safina da yawa shi yasa ya kasa gano illolinta, shi yasa tuntunin lamarin mata yake bashi tsoro, sam baya shiga shirginsu.
Har asuba yana ta sake-sake dan tunano hanyoyyin da zai bi domin dawo da farin ciki a zuciyar abokinsa, sai bayan ya yi sallah sannan bacci mai nauyi ya dauke shi, ya dade yana bacci domin har ya dan makara saida kiran wayar Sulaiman ya tashe shi, ya amsa wayar cikin fargaba da yaji murya Ahmad ne ba Sulaiman ba. “Yaya ne babu lafiya baka ga yanda muka kwana ba jikin babu dadi”. Iliyas yace “Zazzabin ne ya sake dawowa ko kuma ciwon kan?”.  Www.bankinhausanovels.com.ng
“Aa duka basu bane yanzu kuma ciwon kirji ne ya kama shi, numfashinsa da kyar yake fita”. Cikin sauri Iliyas yace masa “To ganinan zuwa, ku shirya shi daga nan sai mu wuce asibiti”. Nan take ya wartsake daga baccin ko wanka bai yi baya sauya kayan jikinsa ya dauki makullin mota yana tuki yana zancen zuci damuwa karara akan fuskarsa jefi-jefi hawaye sukan zubo masa amman bai damu daya share ba.
“Kaicon ki Safina sam baki zama masoyiya ta kwarai ba, baki cancanci abokina yasoki ba duk abinda ya same shi kece sila, idan har ya mutu a dalilinki ba zan taba yi miki afuwa ba, ba zan taba yafe miki ba, wayyo inama Allah bai halice ki ba a doron kasa balle har abokina ya tsinci kanshi cikin matsanaciyar kaunarki, da yanzu bai tsinci kanshi cikin halin da yake ciki ba, yana tafe yana wannan surutun har ya isa gidansu Sulaiman ko kashe motar bai yi ba ya shiga ta kofar waje ya samu duka mutanen gidan sun taru akan shi suna masa sannu, a tsaitsaye ya gaishe su sannan suka taitayo Sulaiman din shi da wani kaninsa Umar suka nufi asibiti kai tsaye asibitin da ‘yan gidan su Iliyas suke zuwa ya kai shi, a office din likita bayan ya yi ‘yan gwaje-gwajensa sanna ya farada tambayar previous medical history din Sulaiman domin yaga jininshi ya yi mugun hawa fiye da kima, Sulaiman yace “A gaskiya a baya bani da hawan jinni sai dai yanzu na hadu da shi”. Likita yace. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Zai iya yuwuwa a yanzu jinin naka ya hau sakamakon wata razana da ka yi ko kuma wata matsananciyar damuwa daka tsinci kanka a ciki, amma kar ka damu insha Allahu zamu shawo kan matsalar, idan har kabi shawarwarin da za mu baka ka kiyaye ka’idojin tunda abin baiyi nisa ba, kayi kokari ka rage yawan tunani, sannan ka

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]