[Advertisements⬇️]

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 10 BY ZAINAB LAWAN BIRGET - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 10 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Rashin sanin ainihin lokacin da Sulaiman zai karaso domin daukatarne yasa ta sauke girman kai ta amsa bukatar Kamal din ta amince ta shiga motarshi, mikewa tsaye tayi ta dauki Jakarta ta rataya a kafada ya yi gaba ita kuma tabi bayansa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Gaban motar ya bude mata ta shiga su kuma su Laila suna baya. Hakan ne ya bashi damar ci gaba da neman kan Safinar, babu laifi ya samu lambar wayarta. Sun kusan zuwa gida Sulaiman ya sake kiranta a lokacin aka gama yi masa gyaran ya kirata ne domin ya sanar da ita ya kusa karasowa a lokacin take fada masa cewar tana tare da kawayenta sun ma kusa zuwa gida.

Bai ji wata damuwa a ranshi ba tunda da ma dan ita yake saurin tunda kuma ta samu ragin hanya ai shikenan.
in Kamal ba shi ne yake zuwa daukar kannenshi ba, direbane yake zuwa daukar su, yauma rasuwa aka yi a kauyensu yaje gaisuwa shi ne Kamal din ya zo kuma ya zo a sa’a ya yi gamo, tun daga wannan ranar Kamal yake zuwa B.U.K ba dan ya dauko su Laila ba sai dan Safina, tuni direban su Laila ya dawo kuma ya ci gaba da aikin dauko su.
Zuwa yanzu da kanta Safina tana jin dadin zuwa da Kamal yake yi daukarta,hakanan ta haramtawa kanta shiga motar da Sulaiman yake zuwa daukarta don a yanzu tana ganin tafi karfin shiga irin’ wadannan kananan motocin, lokuta da dama idan Sulaiman ya zo daukarta takan ji kunya ta kamata idan ta tuna bashi da kudin motar bata da tsada, ta rasa yanda zata yi ya daina zuwa daukarta domin tunda ta hadu da Kamal kunya take ji a dinga ganinta da Sulaiman daga bisani dai ta yanke shawarar daina shiga motar kwata-kwata idan ya zo daukarta sai ta buya, kawayenta ta suce mai tatafi gida ko kuma ta shige cikin makaranta ta

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

kashe wayarta idan ya kira yaji a kashe wayarta, idan ya kira ya ji a kashe sai ya yi ta jira har sai ya gaji ya tafi, a haka tasamu ya hakura ya daina zuwa daukarta amma duk da haka baidana hidima da ita ba, ko da bashi da sana’a Www.bankinhausanovels.com.ng yana ‘yan buge-bugen da zai samu kudi, kuma komai ya samu akanta yake karewa sabida baya so ta samu sauyin rayuwa shi yasa yake fita yana aikin karfi don ya samu rufin asiri, domin yanzu ba hidimar kanshi ce ta dame shi ba kamar irin bukatar Safina. Don haka zai iyayin kowanne aikin karfi dan ganin ya dauki dawainiyarta tunda shi ya sabar mata, domin babu abinda yafi so a duniya kamar Safina, shi dai burinshi a kullum ya ganta cikin farin ciki, babu abu mafi soyuwa a gurinsa irin yaga tana rayuwa cikin yanayi mai kyau, Allah sarki sai dai shì abinda bai sani ba a yanzu komai nashi ya daina burge Safina, duk kuwa da kokarin da yake akanta. Komai ya yi baya mata gwaninta tunda Kamal yanayi mata fiye da haka domin tunda ta hadu da Kamal ta fara raina Sulaiman da abin hannunsa balle kuma dataji sun samu matsala da ubangidansa yabar kasuwa, duk sai taji ya fice daga ranta, ban da hanyar rabuwa dashi babu abinda take nema, amma ta rasa yanda zata yi saboda nacinshi ya yi yawa har yanzu sonta daduwa yake a zuciyarshi, ita kuwa yanzu Sulaiman da duk abinda ya mallaka basa gabanta, Kamal ne kawai a zuciyarta, ta damu da shi sosai musamman daya bugo waya ya sanar da ita zai yi tafiya zuwa Ingila, daya ke shi yake aiwatar da duk harkokin Alhajinsu, shi yasa baya zama kullum cikin tafiye-tafiye yake yana shigo da kaya, domin Alhajin kamfanin gareshi mai suna Lamido computer and Electronic Enterprises suna siyar da comfutoci kamar personal computers, laptops, printers fax machines, suna kuma kwangilas saka computoci a makaranta musamman da ake koyar da ilimin na’ura mai Www.bankinhausanovels.com.ng
kwakwalwa, shiyasa Alhaji Lamido ya tura su Laila su karanci computer science. Shi kuma Kamal tunda ya kammala karatunsa a Sweden ya dawo gida Nigeria shi yake gudanar da zirga zirgar shigowa da sababbin kaya yanzu ma tafiyace ta same shi zuwa kasar Ingila don shigo da wasu computoci sababbi ya yi wadanda aka basu kwangilar sawa a wani kamfani.
A wannan karon sam Safina bata ji dadin tafiyarsa ba, saboda tafara shakuwa da shi, ji take yi kamar tayi tsuntsuwa ta bishi har Allah Allah take suyi aure ya rika fita da ita kasashen waje, dama haka take so mijinta ya kasance mai fita kasashen duniya, kuma gashi ta samu dan haka take alfahari da haduwarta da Kamal domin gayen ya hadu da yawa, ga kudi ga Ilimi gashi dan soyayya ya iya soyayya kwarai saboda wayewa baya shakkar nuna mata soyayya ko a gaban waye domin Kamal wayayye ne na karshe, ya yi yawo kasashen da yawa sosai, idanunsa sun bude ba kamar Sulaiman da yake cikin gidadanci ba, bai taba fita kasar waje ba iyakacin tafiye tafiyen shi Lagos da Abuja kawai, ko kwatano bai taba fita ba don haka take ganin gara ta rabu da Sulaiman ta zaɓi Kamal ko ba komai zata yi tutiya da kece rai ni a cikin kawayenta domin Kamal zai burge kowa don miji na kece raini, na nunawa sa’a, sai dai cikas danta daya yanda kowa ya santa da Sulaiman, gashi ta rasa yanda zata yi ta rabu da shi,tayi masa wulakanci, tayi masa kora da halin amma yaki ya ganewa balle ya rabu da ita, ita kuma tana jin kunyar tafito kiri-kiri tace ta fasa aurensa, surutun mutanen gidansu kadai ya isheta, domin suna son shi kwarai su Naja’atu kwarai suna girmama shi. Www.bankinhausanovels.com.ng Domin kowa yasan irin hidimomin da yake yi mata, wannan shi ne ya hana Safina ta fito kiri-kiri ta kori Sulaiman, zata barshi a haka har sai ya gaji ya kori kanshi da kanshi domin ta lura jama’a sunsa mata ido da yawa, A can bayama kuruciya ce tasa take tunanin zata iya auren Sulaiman domin babu abinda ta tsana irin rayuwar talauci balle yanzu da take ganin bashi da komai, bashi da sana’a balle ya samu kudin da zai dinga yimata facaka irin yanda take so. Bata kara tsinkewa da al’amarin talaucinba sai yau data taso daga makaranta tasha wahala sosai kafin ta karasa gida duk ta galabaita da zafin rana, a rayuwa irin ta Nigaria da aka saba da rashin ruwa, rashin wuta da matsalar manfetur duk Safina bata taba kula da taskun da talakan Nigeria yake ciki ba sai yau, data dandana wahala takaici duk ya dameta domin yau rana bata mata dadi ba sabida ta dandana kadan daga cikin taskun talaka yakan tsinci kansa.
Abubwan data ji talakawa suna korafi sam bata saka su a cikin lisafi amma a yau da abubuwan suka shafeta haushi data sha ba kadan bane, da farko dai tun tasowarta daga makaranta take jiran mota a bakin titi amma har ta gaji da jira bata samu motar haya ba, don kowace ta zo wucewa a cike take taf tun tana zaben
irin motar da zata hau tasi ta koma bus din da zata hau amma ta rasa, data tambayi dalilin wahalar motar aka ce mata ai ana fama da matsalar man fetur haka taci gaba da tsayawa a bakin titin tana jira, duk ta gaji ta soma kosawa da tsayuwa a rana gashi lokacin bazara ne tsakiyar watan April damina bata sauka ba, ana tsananin kwalla rana zafin kamar zai haukata mutum, hakan ya damu Safina ta yanke shawarar ta soma tafiya a kafa ko zata rage tafiya, tana tafiya tana waige-waige zafin rana yana gasata, amman bata samu mota ba tun tana dubawa har ta samu wata inuwa ta zauna tana hutawa, saboda azabar ta isa zafin Www.bankinhausanovels.com.ng rana ya gama galabaitar da ita, ga yunwa ga kishirwa sun dameta, gata bata iya jure wahala, ko mai jure wahala ce nisan ya yi yawa babu yanda za ta yi ta iya komawa gida a kafa, tundaga B.U.K Har zuwa Kawo, tunda ta shiga makaranta bata taba haduwa da wahala irin ta yau ba, tun farko Sulaiman ne yake zuwa daukarta duk ranar da ba zai samu damar zuwa ba ta sanar da yaya Abbas ya zo ya dauketa, da Sulaiman ya daina zuwa bata rasa masu zuwa daukarta ba lokuta da dama takanci sa’a a cikinn sababin samarinta a samu mai zuwa daukota ko kuma a cikin dalibai abokanta takan samu masu rage mata hanya, duk saurayin data gani da mota mai tsada to sun fi damawa dashi saboda hawa tsadadun motoci yasa ta raina motar Sulaiman yake zuwa daukarta kuma dama ita ba ma’abociyar shiga motar haya ba dan haka duk sa’ar da tafiya ta kamata a ckin motar haya takan ji kunya sosai tayita mita tana kunkuni, gashi ita ba ‘yar masu kudi ba balle a siya mata mota, karewa ma mota daya ce a cikin gidan da ita ake duk wata zirga-zirga da kai yara makaranta da cefanen gida, wannan abun yana ci mata tuwo a kwarya lokuta da dama takanyi tunanin da ita wata ‘yar wani attajiri ce da yanzu an mallaka mata motar kanta, duk wajen da zata bata da matsala sai dai ta tuka ta tafi, da yake duniya juyi-juyi ce sai gashi yau an wayi gari motar hayarma ta gagari Safina balle irin kananan motocin marasa tsada data raina a yau ta dandana kudarta, zafin rana da wahalar tafiya kamar zata kife a hanya.
Ba ita ta samu mota ba sai da tayi tafiya mai nisan gaske sannan gashi wata tsohuwar bus, itama a cike sai akan maleji ta zauna a matse, ita dai data samu aka isa wajen da zata sauka tayi hamdala ta sauka ta karasa gida a gajiye matuka, tana isa ruwa ta soma nema ta sha, sannan ta nemi na wanka donta watsa a jikinta ta ji sanyi, ta kunna famfo taga karaf ashe an dauke ruwan,taja wani dogon tsaki ta dauki bokiti ta nufi durum din ruwansu, tana budewa taga nan ma babu ruwan an riga an yi amfani da shi, duka ta kuma jan wani tsakin, ta nemi almajirin gidansu ta turashi ya nemo mata mai ruwa, ta zauna tana jiran mai ruwan shiru shiru bai zo ba, sai can almajirin ya dawo shi kadai yace mata wai bai samu mai ruwan ba, haushi ya kamata ta saka hijabi ta tafi neman mai ruwa bata samu ba sai da kyar wani mutum daya samo mai ruwan ya yi mata alfarma ya bata jarka biyu ganin ita macece, ta dai samu tayi wanka, ta sallaci Www.bankinhausanovels.com.ng azahar harda la’asar da lokacinta ya karato, saboda tsabar gajiya ko abinci bata nema ba tabi lafiyar gado ta kwanta, bata jima da kwanciya ba suma nepa suka dauke wuta fanka ta daina yi, nan da nan zafi ya bakunci dakin, ta tashi ta dauki mafici ta shiga fifita, a takaice dai sai hakura tayi da bacci, sabida ba zata iya bacci a irin wannan yanayin ba. Nan da nan ta shiga cikin kogin tunanin wai shin me yasa talakan Nigeria yake rayuwa a cikin kunci? Idan haka rayuwar talaka zata ci gaba da tafiya ita tayi alkawarin babu ita babu auren talaka domin babu yanda zata yi ta kubucewa irin wannan rayuwa idan ba mai kudi ta aura ba, auren mai kudi ne kurum zai fitar da ita daga irin wannan rayuwar ta rashin ruwa, rashin wuta, matsalar man fetur matsalar shiga motar haya da rashin abubuwan more rayuwa, hakan nan tana son kaucewa tsananin zafin garinan dan duk wadanan matsalolin data lisafa akan talaka kawai suke karewa basa shafar masu hannu da shuni, saboda gidajen su koda an dauke ruwan famfo ba a rasa ruwa a tanki, haka nan idan aka dauke nepa ba a rasa inji ko kuma solar, kuma idan gari ya dauki zafin rana su suna cikin A.c, a gida A.c a mota A.c, a Ofis A.c a cikin tunanin ta sake jan wani tsaki tana neman tsari da talauci, Allah wadaran talauci domin ita dai bata ga ranar talauci ba.
Komai na duniya yana da ranarsa amman banda talauci domin talauci baya yiwa dan adam rana, talauci bai taba tsinanawa mutum komai ba face taskun rayuwa Allah ya tsare mu da talauci, talaucin ma irin wanda talakan Nigeria yake ciki, komai najin dadin rayuwa bashi da shi sai dai yagani ko kuma ya ji labara, wannan wacce irin rayuwa ce haka? Ita dai idan haka rayuwar talaka take babu ita babu rayuwa a gidan talaka domin babu abinda yake burgeta a gidan talaka, dan haka zata yi ta adawa da shi har sai tayi hannun riga da shi, damacan Safina ta tsani talauci a rayuwarta ba kasafai take son rabar talaka ba, ta manta da arziki da tashin hankali gwara tsiya da kwanciyar hankali, tana ganin gidansu suna da rufin asiri amman abinda ya faru da ita yau ya firgitata ya saka ta kara tsanar rayuwa irin ta talakawa suke ciki domin ita kanta da nata iyayen wasu shahararrun masu kudi ne da bata tsinci kanta a cikin yanayin data tsinta ba, domin da tana da motar kanta ko tana da direba mai zuwa daukota da bata sha wahalar tafiya a kafa ba kuma da bata ji takaicin rasa motar haya ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da wannan takaicin ta kwana, amman washe gari cikin farin ciki ta farka sabida wayar Kamal ce ta tasheta daga bacci, kuma ya fada mata maganganu masu dadi, bayan sun gaisa farin ciki ya mamaye zuciyarta domin tun tafiyarsa bai kirata a wayaba, ganin tsararrun nambobin kasar waje yasata murmushin jin dadi cikin nishadi tana daga kwance ta manna wayar a kunnenta ta dan kwantar da murya tana dariya, “Hello Kamal yaya kana lafiya?” Daga daya ɓangaren yace.
“Yaya mutanen Nigeria da fatan kowa yana lafiya?”. Tace “Kwarai kowa yananan lafiya”.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]