HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 6 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

Advertisements

_____

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 6 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Advertisements

_____

Ina nan tsaye inata saka da war wara, Wai Wanan wana irin mutum  ne Agabansa fa nasha maruka Amma shi ba ruwansa wannan shine Adakeka Ahanaka kuka, dama Haka Auran yake takurace kawai Acikinsa.

Inacikin tunani naji ya bude kofa da sauri na kalleshi, yacanza daga manyan kayan dayasa zuwa kayan bacci da’alama ma wanka yayi, Ina tsaka da tunani naji yayanmu na magana, Amsar tambayoyina nake jira Danni lokacin baccina yayi, Sai asannan nadawo da hankalina gareshi, tsugumnawa nayi na sunkuyar da Kaina na Fara magana Kamar haka “nafarko Yaya kana kallo wannan ta office dinnaka tamareni Amma baka ramaminba nikuma Raina yabaci shiyasa kawai nataho , shikuma shiga cikin gida Naga masu Ayki Basu tafiba shiyasa nashiga.

Dago kanki naji yace dagowa nayi in sauraransa ni shuriem da kike gani ba sha Shan namiji bane dazaki Dinga yin Abu batare da izini naba Kuma daga yau ban baki izinin fitaba harse ankawomin Amaryata.

Ay Yana ambatar Amaryarsa naji wuta ta tadauke Kamar majigi Haka nadinga kallonsa bana fahimtar ma me yake cewa Sai gani nayi kawai yatashi yashige bedroom dinsa.

Kukane ya kwace mun da gudu nabishi bedroom din natarar har yashige bargo,

Saboda tsabar bacin Rai bansan sanda na yaye bargonba shi kuwa yaya shuriem da sauri yatashi yana kallona cike da mamaki.

Yaya nakira sunansa Atsawace, ba Amarya zakayiba to kadade bakayi Amaryarba wallahi ni Heedaya bazaka birgeniba saika auro Mata hudu uku lokaci guda kaga sannan Sai intabbatar da cewa kacika shuriem Aiban karasaba naji yawani kwarfeni  jina NAyi Akasa Tim na Fadi baki na Ware Zan kurma ihu da sauri ya dokemin bakina sannan ya Fara magana, ke wato  marar hankali,  rashin kunyar taki takai Haka to wallahi aure na da meerah ba fashi saidaiki mutu, Kuma darajar mahaifiyarmu kikaci yasa na aureki data nuna Bata so ke baki Isa na Aurekiba saboda Kinga na rufa Miki Asiri, shine Zaki Bude babin rashin mutumci koh banza wadda batasan darajar mujiba cak yadaukeni Kamar wata kayan wanki yawatsani falo sannan yasawa kofarsa key, kuka nayi tayi Awurin har bacci yadaukeni Akasa shi kuwa shuriem komawa yayi ya haye gadonsa Sai bacci.

Shirye shiryen biki yanata kan Kama na lura da Yaya har wani zumudin  Auran yake Yaya taupiq kullum zezo yadauki Yaya su fita ni kuwa idone nawa, momy da Anty saudat sun hado Mana kayan lefe nagani nafada l, gaskiya nayi mamaki gyaran da akayiwa part din Yaya, Akwai babbar kofa A farko daka shigo Sai passage sannan kofar babban falo Acikinsa Akwai wurin dining sannan Akwai kitcheen me girma sosai, sannan Akwai toilet A falon Sai wasu kofofi guda 2 suna kallan juna kowace kofa Akwai madaidaicin falo Aciki da kitchen  da Kuma beddroom da toilet, Sai wata kofa Dana hango Acan cikin babban falon nanma kamar yadda wadannan dakunan suke Haka shima yake shine Wanda Yaya yadauka yazama NASA, ranar da aka gayawa su Meera Agidansu shuriem ze zauna Ai bakaramin tashin hankali sukayiba saboda sunsai Kaya hardana hauka, don ita Atunanin maman meerah Wai jari tazuba tana dab da kwashe riba.

Da Farko sunce meerah bazata zauna agidanba Saida iya Nene tayi tsalle tadire tace ita bazata yarda dawannan rainin ba saidai A fasa Auran Haka suka hakura Dan basuda yadda zasuyi.

Yaune za’ayi kamu Anty saudat ce tazo tadaukeni tareda hadamin kayan dazan bukata, Acewarta bazan Kuma dawowa part din yayaba Sai angama biki.

Gurin saloon muka Fara zuwa Aka wankemin Kaina da Kuma kafata, daga Nan ta wuce Dani gidan wata Mata me gyaran jiki Haka Ina kallo Aka ringa turareni da wasu turarruka masu kamshi Akaimin dilka, Nan da Nan nadawo wata balarabiya Abinka da farin mutum.

Yammace tai Mana Anty saudat taroki matar Akan tazo gobe da jibi ta karasmun Agida da kyar matar ta yarda domin tanada Ayyuka dayawa, Haka mukawuce gurin wata me kunshi Akaimin baki da ja,

Masha Allah nikaina nasan na fito bamu muka dawo gidaba Sai wajen karfe 10pm nadare, ko da muka shigo gidan Acike yake da mutane raba ido naitayi inda zanga gano sadiya Canna ganota ta taho da gudu kuwa ta rungumeni kamani tayi muka shiga dakinmu muka zauna gefen gado hirar yaushe gamo muka farayi, sannan nace Mata Ance min yau za’ayi kamu Amma ni ba’a kamaniba.

Murmushi tayi tace Heedaya kenan kinsan momy batasan kida kidenan tace gobe me wa’azi zata kirawo ta Tara mutane Ayi wa’azi aci Asha kowa yakoma gidansa.

Kwabe fuskata nayi Kamar zanyi kuka nace niyanzu momy bazataimin bikin yar’gataba ni kadaicefa Yar’ data Haifa sadiya kuwa shekewa tayi da dariya tace kinfiya shirme Heedaya to muma dabata haifaba baza tayi manaba, ko kinsan Haka shine dai dai tanasone Auranku yayi Albarka tabe baki nayi Amma shi Dan gaban goshinta yanacan Yana NASA wa!  Wai Yaya shuriem kike nufi toshine ma babban Wanda zata Hana tunda shine babban danta kinsan kuwa ta hanashi yin dinner Wai inya sake ya hada Mata da maza guri days Albarkar Auransa tafiya zatayi.

Tabe baki nayi namike ina fadin sadiya Hirar Nan tamu bazata Karena gwara naje nagaida momy sainazo mucigaba, dakin momy na nufa natura kofar da sallamata Yaya nagani kwance kan gadon momy ya lulluba da bargo ga cup da maganin ciwan Kai Akan side drower. Ji nayi anturo kofa Anty saudat nagani itada momy da Kuma iya Sai Abba Abayansu kallan mamaki na bisu dashi……..✍?

         Page 33-34

Binsu nayi da kallo kowanne da damuwa dauke A fuskarsa, Abbane yazauna kan side drowern dake dakin yaye bargon da yayanmu ke ciki yayi, yace sannu shuriem Allah yabaka lafiya, Da Ameen suka Amsa, nidai binsu kawai nakeda ido, Abbane yakama Yaya yatai maka Masa yatashi, sannan yadauko wata leda A aljihunsa yakalli Anty saudat yace “takawo ruwa juyawa tayi tafita ba’ajimaba tadawo daukeda jug da kuma glass cup Ahannunta mikawa Abba ruwan tayi tace “gashi Yaya.

Bawa Heedaya ruwan yafada Yana mikamin ledar maganin rissinawa nayi nakarba, da mugunta nakalli Yaya Naga yanata langwabewa, da nice datuni yayi ta masifa Yana cewa banida dauriya, dasauri na haye gadon na ballo maganin hannu ya miko zai karba ni Kuma nai saurin Kai maganin bakinsa, Abbane yace son Bude bakin Mana Aikafin Abba yarufe baki NASA maganin cikin yatsuna na cusa Masa maganin saidana tabbatar yafara jikewa nadauke hannuna NASA Masa cup din ruwan.

Kara matsawa nayi kusa dashi na Kuma ballo kwalli daya ummyce Tai saurin dakamin tsawa waike Heedaya bakida kunyane bakiga iyayanki Atsaye Akankibane saiwani shigewa kike kurya, habawa iya kuwa tace dawa Allah yahadani inbadake, saboda masifa idan iya Harkankan cewa sukayi ke momyn Yara kifita daga idona narufe wlh Ina saura ra Miki Akan Heedaya ne saboda ke Kika haifeta Amma badan hakaba da Kinga yadda Akeyinta wlh, Anty saudat ce tashiga Bata hakuri, iya Kara fusata tayi tace Ai duk ku kuke Goya Mata baya take Mata Abinda taga dama Dan Haka dukkan kufuce isma’ila kaima tashi mufita inma zataci namansa danye taci Ai mijintane Aikafin iya tarufe baki duk sun bace Adakin Dan sun San halin iya ga gida da baki yan’ biki, suna fita Kuma naji wani tsoro yakamani sakamakon wani wata harara daya watsamin baya naja naballo maganin na Mika masa matso yace Dani kibani yanda kikai Agabansu Abbaz, inba hakaba Sai yay kwafa, Ai inajin Haka na matso da sauri nakai maganin bakinsa karba yayi yacika bakinsa da ruwa ban Ankaraba naji Yaya na fesheni da ruwan bakinsa sannan hakan dayaga bai isheshiba yakarbi cup din yakarasa juye ruwan Akaina.

Sauka yace Dani sauka nayi Ina kunkuni, murmushin mugunta yayi Heedaya yakira sunana cikin muryar marasa lafiya, kallansa kawai nayi batareda na amsaba cigaba yay da maganarsa kinsan cewa gobe iyanzu Ankawomin Abar kaunata har cikin dakina, Abunda bakisaniba shine tuni nawuce wa tunaninki duk nagane mekike nufi su Abbane kawai Basu fahimtaba nikuwa nagama ganoki fita yanunamin kofa da sauri nafice natafi dakinmu, sadiya natarar tafara bacci duka na daka Mata tatashi firgigit saiyanzu Kika dawo eh wallahi nahadu da wanki ne yanataimin wani muzurai sadiya kuwa mezatayi inba dariyaba, sannan tace kwama Gama Raina Mana hankali, duka nakai mata da sauri ta goce Haka naita binta ni Ala Dole saina daketa Muna cikin Haka saiga iya tayo sallama, to shasha kitsaya kallon ruwa kwado yay Miki kafa yanzu naje dubaku natarar yanata waya da dayar matar tasa shine na bazamo nataho nemanki, jinayi gabana yayanke yafadi duk Daba nasan Yaya Amma banaso naji Ana hadashi da wata.

Jinayi kawai iya ta figi hannuna bamu tsaya ko inaba Sai dakin momy Muna Shiga ta kalli yayanmu tace “tunda kannaka yayi sauki Ai saika tashi kutafi dare Yana karayi, kallonta yayi yace haba iya nida gadon babata Abarni na kwana Mana Naga iya nanba dakinki bane, to tabba tacce saika tashi bazaka kwana Adakinnanba Sai dakinka tashi maza maza naraka ku, mikewa yayi saboda yasan masifar iya, iyace tace heedaya kamashi karya Fadi kinsan ba karfi Ajikinsa Haka Muna ji Muna gani muke bin Umarnin iya saboda gudun masifarta.

Haka nakama Yaya muka fito Yan biki kuwa Sai sannu suke Masa Anty saudat ce tahangomu da sauri ta karaso gurinmu iya Ina zasu da daddarennan wata harara iya ta wurgawa Anty saudat tace ” to uwata gidansu zasu tafi” Anty saudat Bata Kuma daddaraba tace iya Dana Bari kikayi gobe Kamar yadda Ake Kai kowace Amarya itama Akaita, iya kuwa tazo wuya to naki bazan yaddaba yaron beda lafiya za’a barshi ya kwana shi kadai baze yiyuba tana kaiwa Nan tace Mana muje nakarasa daku.

Haka muka fito har farfajiyar gidanmu ummy muka gani kwatsam Agabanmu ranta Ahade tanaganin iya Kuma saitasaki ranta rissinawa tayi tagaida iya, ita Kuma iya ta amsa Mata bayabo ba fallasa matsawa tayi tabamu Hanya muka wuce tana kallo Muka Bude part dinmu muka shige sannan iya tadawo ran ummi bakaramin baci yayiba da sauri tabar gurin Kar iya tazo tasameta.

Muna shiga ya fincike yayi hanyar dakinsa tsayawa nayi Ina kallon part din gaskiya ya kayatu nashagala da kallon Fallon naji anjefeni da mukulli da sauri nadawo hayyacina ga part dinki yanunamin na bangaran dama sannan ya juya ya koma, key din nadauka jikina Asanyaye nabude part din gaskiya an narkamin dukiya Allah yasakawa Abbanmu da Alkairi, domin shiyace bawanda ze siyi ko cokali, kawuna ma daya matsa Akan shi zeyi kayan dakin da iya yahadashi shikuma yanajin nauyinta Haka yakira yabarwa Abba,Allah yasaka maka da Alkairi, Abba baka barni nayi kuka rashin mahaifiba Ina Alfahari dakai, shiga nayi na duba ko Ina komai yayimin yadda nakeso komai na part Dina purple and Ash ne Haka naita kallo Kamar wata sauna, danaga kalle kallen baze munba tashi nayi naje nayi wanka, nayi Alwala nazo kwanta Sai barci.

Washe gari, da Asuba natashi nai sallah nayi shara da mopping duk daba wani kura Agurin, wanka naje nacancada na dauko wani Dan ubansun less da momy ta dinkamin blue and white yakarbeni dinkin  riga da siket, feshe jikina nayi da turare na fito babbaban falo domin nakudiri niyyar nadena yadda yaya ya yaringa wula kantani.

Nadan Jima Azaune Naga yafito cikin manyan Kaya ga kamshi da yake zabgawa Araina nace gaskiya badan girman kan yayaba dayake Kara masa Muni gaskiya shidin hadaddene da sauri na Mike nace Masa Ina kwana lfy ya amsa atakaice yafice bakin taga naje Ina lekensa naji abokan wasansa suna tsoka narsa  bana jiyo me suke fada Sai Kuma Naga Anatashiga mota wata zuciyarce tagayamin daurin Aure zasu kuka NASA nadawo part Dina na kulle kofa hardare bawanda yalekoni domin wannan hukuncin iyane Haka nawuni nikadai Sai bayan magrib Yan uwana suka Fara shigowa.

Saiga Anty saudat  tazo Kama hannuna tayi ta zaunar Dani tayi tana tayimin nasiha Akan zaman Aure sannan ta jaddamin cewa NASA ido Akan meerah sosai.

Bayan munyi sallar Isha’i Ina Zaune kan dadduma mukaji guda ALAMIN Amarya meerah ta iso……³³,³⁴

Advertisements

_____

About AIS

Check Also

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 14 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

Advertisements _____ Www.bankinhausanovels.com.ng             D’aukan papern Yaya Shuriem Yayi ya kekke …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *