[Advertisements⬇️]

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 5 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya} - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 5 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Washe gari, misalin 4:30am nayi Mika tareda salati na bude idona, Yaya na hango kan dadduma Yana karatun Alkur’ani me girma cikin suratul TAUBA, Allah me girma na fada Acikin Raina domin karatun na zaga sako da lungu na jikina, can Naga yamike yafita da Alamu masallaci yatafi, Nima tashi nayi shiga toilet, nayi Alwala nazo nayi sallah, dakin nakuma gyarawa nashare shi fes wani room freshner nagani dauka nayi tareda feshe dakin dashi, Nan take koina yadauki kamshi, daga Nan nashiga toilet nanma Saida wanke shi tas sannan nadawo falon shima na gyara, bayan nagama nashiga kitcheen din dake manne Afalon mamakine yaka mani ganin komai na Aiki Aciki tamkar da mace Agidan, fridge na bude sakin baki nayi saboda ganin nama iri-iri da Kuma kayan Abincin da ba’aso sulalace. 

Dana Bude drowan kitchen din kuwa kayan Abincine. danginsu shinkafa, semovita, taliya, macaroni, dadai sauransu ban tsaya dogon wani tunaniba na dafa tea Wanda yaji na’a na’a da tumeric sannan NASA Masa lemon grass, bayan na hada, nayi Masa farfesun kan rago Wanda yaji kayan kamshi sannan nasoya chips bayanna kammala nawuce toilet nayi wanka nadauki wasu riga da zani nawa na atamfa rigace da zani anmata din yarbawa, saboda dogon hannu gareta Kuma me Fadi sannan zanin Akan rigar Ake daurashi sannan nazo nazan Zara daurina, 

Ban jira yayaba nazauna nayi break fast dina, Agogon dakin naduba karfe bakwai da minti goma, miikewq nayi na yafa mayafina, nadau school bag Dina nazauna jiran Yaya bayan wasu mintuna naji yayi sallama yashigo direct toilet  yawuce Ina ganin Haka natashi na koma falo bayan wasu mintuna Naga yafito yanata zuba kamshi, hanyar fita Naga yayi, Aida sauri nabishi nace Masa Yaya ga break fa dawowa yayi yazauna nazuba Masa balaifi yadanci sosai, sannan yamike, dasauri nace yayanmu inzo Dan Allah ka Ajiyeni A school kallan bakida hankali yay min sannan yace “yau za’ayi Aiki abangarennan inaso kafin masu Ayki suzo kishirya min Abinci kikawomin Asibiti mukulli ya Ajiyemin nace Mai Yaya Toni Amezanzo murmushi yayi yacemin A  Abinda kikazo rannan sannan yay ficewar sauri sauri nayi na hada mishi Abincin falon kawai nakulle nabar sauran guraren Abude nafito Zan fitane naci karo da kawar ummy hajiya Amina zata shigo rissinawa nayi nagaisheta ta amsa ranta Ahade Kamar ta kurma ihu ni kuwa fita nayi natare napep Sai Asibiti.

Hajiya Amina kuwa tanashiga tasamu Aminyarta tayi tagumi Abin duniyar ya dameta Ai ummy naganinta Sai hawaye Aidole kiyi kuka rahanatu kuka bazai Kare Miki ba saikin karar da zuri’ar gidannan kinsan wanima Abin takaici dazan shigo Naga kodaddiyar yarinyar Nan da kayan Abinci Niki niki da Alama yaron zata kaiwa ummice ta katse haj. Amina tace “Dan Allah kibari Aminiyata Kar zuciyata ta buga jiya Haka naita fama da isma’il Akan yaraba Aurannan yaki Dana dameshima cewa yayi Inna matsu da rabuwar Auran naje nasamu iya nagaya Mata Kuma shi yasan iya bazata taba Amincewa da raba wannan Auranba.

Hajiya Aminace tai wata dariyar mugunta yayinda ummi tai sakato tana kallonta, sannan tace rahanatu kawo kunnanku kiji wata shawara kunne ummi ta Mika Mata saikuma suka sheke da wata dariyar Ai insun San wata Basu San wataba cewar ummmy Dani suke maganar har ubannasu Kamal ne cikin toilet din Abinda suke fada yagir gizashi Kuma yay kudrin gayawa Abba saboda shi da ma  be dauko halin momyba.

Ina Isa Asibiti direct nayi office din yayanmu Raina duk Abace yake saboda ya hanani zuwa school, da sallama Abakina nashiga dagowa yayi batareda ya amsaba wani bakin ciki yaji ganina da mayafi gashi harda wani Jan baki, mikewa yayi Yana huci yazo daf Dani, har inajin hucin numfashinsa shiyarasa ma wane hukunci zai yankemin kawai hannunsa naji  kan lips Dina wannan Zaki goge daga yau karna Kara gani kinsa sannan hijabi Zaki Dinga sawa daga yau, bamu Ankaraba Sai ganin meerah mukayi Akanmu tanata huci Kamar zakanya…

Meerah ce tashigo ta tsaya Akanmu Kamar wata zakanya figoni tayi tareda gallamin kyawawan Mari guda 2 shi kuwa Yaya office dinma yabari gaba daya saboda shi bayasan fitina inyanan rigimar tsawo zatai Dan ya fahimci meerah bakaramin so take masaba zata iyayin komai domin shi.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Jikina na fisge Kuma nakasa Rama Marin dataimin, wato Yaya ko kasheni zatayi ta kasheni shiba ruwansa, meerah ce takalleni tareda nunani da yatsa Heedaya kike kowa kiyi gaggawar karbar takardar sakin ki hannun shuriem, inba hakaba nakarba da Kaina nabaki, saboda ni baki Kai matsayin dazan kishi dakeba Dan Haka tun wuri kibi wani sarkin tunda gashi shuriem din dakansa yanuna ba Kya gabansa maganganu tai ta yabamin nikuwa Banga laifin taba Sai na Yaya watoshi ko kasheni za’ayibabu ruwansa, dama kiyayyar dayakemin takai Haka, kuka ne yakeso yataho wata zuciyarce ta tunamin cewa Agaban kishiya kike Heedaya be kamata taga hawayankiba, kukanq na hadiye na nufi hanyar fita, ita kuwa Meera biyoni tayi Naga Alama so take na kulata nikuma bazan kulataba hakan saiyafi komai Yi Mata ciwo Arai, da sauri nafice ko takan Yaya banbiba nayi tafiyata gida, Ina shiga natarar masu Aiki nata fama Anata fashe fashe, wucewa nayi part din momy, bakowa A falon Sai nawuce bedroom dinta, Ai Ina shiga nayi Arba da Anty saudat Ai dagudu na fada jikinta inai Mata oyoyo , itama da murna tatareni,  momyce cikin fada tace Heedaya narasa sanda Zaki girma kullum me bakida Ayki Sai aikin kuruciya dagata karki karyata, Anty saudat ce tace Kai momy me ya’ta tayi mikine kinbi kin takura Mata tayi aure ma bazaki barta tasakeba Koda yake Bari naki Dan yadawo narama Akansa, momy ko jin an ambaci shuriem da sauri tace Allah yabaku hakuri Abin Ay be Kai hakaba.

Tashi nayi nawuce bayi donyin Alwala su Kuma suka cigaba da hirarsu suna tsara yadda biki zai kasance momyce takalli Anty saudat tace  “ni ganina karmu biyewa yarannan Dan banasan wata dinner gaskiya, kiyi hakuri Abune na lokaci cewar Anty saudat nidai kawai mutsaida ranar da zamuje hado kayan lefe kawai Ay Anty saudat Bata Gama rufe bakintaba, saiga Kamal yashigo Yana ta kuka kamashi sukai suna tambayrsa meyasameshi, kwabe fuska Kamal yayi yace ba tunda safe nake neman Abba ba Kuma banganshiba, Anty saudat ce takama hannunsa Banda Abinka Kamal me Abba zeyi A gida da Rana kasan Yana kasuwa, yanzu me kakeso gayamin ni se insiyo maka, Kamal ne ya kallesu duka ni ba Abinda nakeso tome yasaka kuka cewar momy, kuka yakuma sakawa, dama ummyce naji tana cewa Anty Amina Wai zata kashe Yaya da Abba Kuma tace dayan Antyn dazai auro su sukasa ya aureta shiyasa naji tsoro karta kasheshi kafin yadawo momyce tajashi jikinta tareda shafa kansa tace haba Kamal yarona wasa takeyi maka Kuma karka sake kagayawa Abba kaji Heedaya najiyo momy ta kwalamin kira  Aidasauri nafito dama na Gama Abinda nake a toilet din,   kallona tayi   tacemin dauko Masa sweet me dadi kibashi A cikin jakata gatacan Arataye, daukowa nayi nabude nabashi da yawa shi kuwa tsalle yakamayi yana cewa Anty Heedaya shiyasa nafi sonki Akan yaya shuriem dukkanmu  dariya Kamal yabamu momyce tace tunda bakasan yaya shuriem bani Alawata Ay ni nabaka ba hedayaba Ai dagudu Kamal yay hanyar fita sannan yajiyo yace momy Ay Nima dankine  ba Yaya shuriem kawai dankiba Kuma shi baya dariyama kullum cikin fushi yake sannan ya fice da gudu dukkanmu dariya yabamu, Anty saudat ce takalli momy tace Anya kuwa momyn Yara yaronnan zeyi karya Dan gaskiya hankalina yatashi, momyce ta kalli Heedaya tace bamu wuri zamuyi magana Anty saudat ce tayi saurin cewa Babu inda zata momy maganfa Ake Akan Rayuwar mijinta to Dole ta tsaya musamo mafita duka momy ce tanisa tace Heedaya ita tafara jin wannan zancan saina kwabeta Ina ganin Zan iya daukan mataki ni kadai Ashe Abun ba Haka yakeba yanzu meye mafita, Anty saudat ce ta nisa tace ” fasa Auran shuriem baze zama mafitaba mubarshi ya Aureta Amma Heedaya kisa ido sosai Akanta Kuma wannan maganar inaso tazama iya mu 3 banaso wani yashigo ciki sannan duk wani shige da ficen meerah kiringa sanar Dani Heedaya Kuma kema ki kirkiri hanyar dazaki Kare mijinki, batareda sun San kinsan shirunsuba.

Haka su momy sukyita tsara komai nidai nawa idone Sai to da nake cewa in bani umarni Sai wajen 5:30 yaya  taufiq yazo yadauki Anty saudat, nikuma momy tace na koma part din Yaya, tunda dare yayi, bayan na koma wanka nayi bannemi Abinciba tunda naci nakoshi Kuma yau banida niyyar yin girki Dan Yaya ya matukar bani haushi, Ina Zaune Ina kallon mbc 3 domin ni Haka kawai inason tashar bacci yasoma daukata Akan kujera, jinayi Anzungureni da kafa, firgigit na Mike tsaye Yaya naganin Yana wani zare ido, sannu da zuwa nace Masa kin Amsawa yayi yace wayace kiringayin Abu bada izininaba kin taho daga Asibiti bada izininaba, Kuma kin wuni A gida bada izininaba, Dan Haka inasauraranki ko kifadi Abinda Zaki Kare kanki Kona lallasaki kindai San halina,Yana Gama fadin Haka yajuya yay hanyar bedroom dinsa…..✍🏻

Inkin karanta daure kiyi comment

Inayi muku tallan littafina me suna yaki Asoyayya insha Allahu dana Gama Heedaya shuriem Zan posting dinsa game neman karin bayani yay min magana ta WhatsApp numberta👉08163983688 ²⁹ ³⁰

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]