[Advertisements⬇️]

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 12 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya} - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 12 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Maman Meerah harta Fara masifar data Saba Amma tanajin furucin Momy Sai ta tuna da d’auka fansar daza suyi haka ta hakura Akai maida ita gidanta.

 Ina kwance A falo Abin Duniya ya da meni na rasa me yakemin dad’i Yaya Baya kulani kullum da Azabar da yake Gana min, shi ya ki daukan kadd’ara bansan ya zanyi dashiba wani hawaye me dumi naji Yana bin kuncina tausayin rayuwata ne ya ka Mani Ina zansa kaina, Ina cikin wan Nan yanayin naji Anturo Koda Nasan ya yan mune Amma nayi biris kamar banjishiba saboda zuciyata ta Fara bushewa nagaji da wan nan ta kurar tasa, ya Dade A tsaye Akaina Yana nazarina, can kuma naklji ya shureni da k’afarsa Ina daga kwance na daga kaina na kalleshi Shima Ni yake kallo bakiji shigowa ta bane ya Fada cikin muryar me dauke da muwa, naji, nabashi Amsa Atakaice d’aki kawai ya wuce Dan yaga inya tsaya nima kuma b’ata Mai Rai zanyi, saboda Abinda ya faru A Asibiti Yayi matukar b’ata Masa Rai.

Hayani ya nadinga juyowa sama sama Sai kuma Naga Ana shigowa da Kaya Momy ce ta Fara Sallama Sai kuma Anty Saudat da iya Sai Meerah da Mamanta tashi nayi nai musu sannu da zuwa naje kusa da Anty Meerah na gaisheta nai Mata ya jiki, Amma duk Bata Amsaba tashi nayi nakawo musu ruwa da drinks dasu snacks.

Bayan sun D’an jima Sannan Momy ta fuskanci Maman Meerah  Fara magana Kamar haka” Hajiya Laila Mun San munyi Miki laifi san nan A madadina da iyalan gidan nan Muna Msu Baki hakuri  Kan Abinda ya faru kiyi hakuri Ansan da ciwo Amma haka Allah ya shirya…

Gurin tsit Yayi inkin tanka Maman Meerah ta tanka, Meeran ce ma ta cewa Maman ta tashi su Shiga ciki, tashi sukayi suka barsu A falon, iya kuwa da Bata gani ta kyale Saida tayi me isarta su Anty Saudat nata Rarrashinta da kyar ta hakura Tace sutashi suta fi Subar musu gidan haka suka tashi zasu tafi nikuwa kuka NASA nace zan bisu Momy ce ta wurgomin wani kallo iya kuwa Tace na D’auko hijab mutafi, da murna ta na dauko hijab d’ina Daman zaman kadaici ya dameni, Yaya ya fito cikin kana nun kayansa Masu kyau sunyi matukar Amsarsa baiwa kowa maganaba haka be kalli kowa ba hanyar fitarsa ya nufa har yaje bakin kofa ya tsaya batare da ya juyoba yace” wallahi in kika sake kika fita daga k’ofar falon Nan Heedaya wallahi Inna dawo Sai ranki Yayi matu Kar b’aci.

Ka kasheta nace Dan Allah inta dawo karka barta da Rai wato Ni ka Raina su iyayenka in sunyi magana ba ka iya Yi musu_ musu Koh saini marai niyar wayanka to Sai taje.

Sauri Ya yi ya fice don inya tsaya Momy na iya sawa ya barta saboda Kar iya tayi fushi, tsugun nawa nayi na rushe da kuka Ai kuwa Momy taja hannun Anty Saudat suka fice, zuciyarta fess yaronta ya Fara iya tsare gida haka ta keso, Amma Bata so ya gwada Akan iya ba Dan saita shekara tana mita…

Bayan wata 2 Anty Meerah ta warke fess Amma kuma Ni Ina Shan bakar wahala komai Ni na  ke yi mata, wani Aikinma dagani na mugunta ne, Abinda na fuskanta daga wurin Ya ya Yazame wa Anty Meera tamkar rakumi da Akala Sai Abinda Tace Masa Dan harta d’akin Ya ya tasa Ya hanani shiga, kullum  Sai yay ta korata innaje d’akinsa haka na hakura Dan kaina Sai yace wai in inason kwa Nan d’akin naje na tambayi Anty Meerah, Ni kuwa da naje na tambayeta wallahi gwara na mutu ban kwana d’akinba saboda Nasan bazata bariba ma Sai wulak’anci da zai biyo Baya.

Meerah ce zaune gefen Shuriem tanayi Masa Hira shi kuma Yana Duba wasu files na narasa lafiya daza Ai musu bizar Egypt za’ay musu Ayki kuma ta fiyar ta Kama harda shi kuma zasu Kai kimanin wata 3 Acan, Meerah ce ta kalli shuriem cikin kissa Tace dear inason muyi wata magana Ajiye Aykin  Ya yi ya fuskanceta domin Yanzu Shuriem  Yaza mewa Meerah rakumi da’akala.

Ina saura ranki yace Mata, fari tayi da fararan idonta Masu d’aukar hankali sannan Tace”Dama maganar ta fiyar daza kayine nakeso mutafi tare, sannan maganar d’aukar fansarmu ko ka fasane, D’an Jim yayi Sannan yace” A Ah ban fasaba farin ciki fal zuciyarta ta cigaba da cewa” Meze Hana tunda Heedaya ita Tai sana diyyar faruwar wannan lamarin in zai yiwu mutafi da’ita can Egypt d’in Ayi Mata dashen Acan kaga In Allah yasa cikin ya  Zauna bawanda ze zargemu kaga shikenan kafin mudawo cikin Ya Fara girma kaga inta haihu Sai mu karbe D’an nida Kai kaga shikenan ta girbi Abinda ta shuka……..

……..Shiru Ya yi Yana nazari can kuma Sai yace” na Amince” shi kansa Yana mamakin yanda Baya iya yiwa Meerah musu Kan Abu buwa da dama.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Ai tana jin haka ta rungu meshi sun jima Ahaka San nan ta d’ago Tace dear nagode Allah yabarmu tare, yanzu tunda saura sati 1 ta fiyarmu Ina so inje gida yau, kaga Inna dawo sai na Fara shiri, Bari naje dear mikewa tayi, tayi hanyar waje shi kuwa Shuriem ba bakin magana har ta Kai bakin k’ofa Sai kuma ta juyo Tace kacewa wan Nan yarinyar itama tashiga cikin gida tayi musu sallama.

Kar Azargi wani Abu tana kaiwa Nan ta juya ta fita shi kuwa Shuriem Zama yayi ya Shiga tuna nin Duniya, Aikin ma kasaci gaba yayi, yarufe computer d’in, wayarsa ce tayi k’ara, yad’an jima tana ringing San nan ya d’auka ya Kara Akunne, Assalamu Alaikum, daga can b’angaran Aka Amsa masa.

Cigaba yayi da magana Kai D’an rainin hankali, bana gida, gwauron banza, gwauran wofi, d’an shiru yayi Alamun Yana saurare San nan yace” to saika shigo.

Komawa yayi yaci gaba da tunaninsa knocking yaji Anyi, shigo yace, Taufiq ne ya shigo tareda sallama, Amsawa yayi San nan yace” wayace kashigo min d’aki Kai tsaye Kai bakasan da matana Agidan nan ba kake shigo min k’ato da Kai ba Neman izini, dariya Taufiq ya kwashe da ita San nan yace” kasa ranka A inuwa Nima na kusa Auren kaga Sai Gori ya k’are” wuri ya nema ya Zauna san nan yace” bro wai meye labarine D’an Jim Shuriem Yayi San nan yace” Rana ita yau zan tafi Egypt tareda wasu marasa lafiya San nan inaso mutafi tareda da Meerah da heedaya, D’an Jim Taufiq Yayi Yana nazarin Shuriem San nan yace” to su Heedaya Me zasuyi da zakaje Dasu duka, shiru Ya yi Yana tunanin Abin Fad’a gashi be iya karya ba, can dai yace” Akwai Aikin Dana keso zanyiwa Heedaya domin batada cikakkiyar lafiya kaga Inna tafi da Meerah saita Tai maka Mata.

Kuma tafiyar zata d’aukemu tsawon wata 3, gaban Taufiq ne yay wani mummunan faduwa Amma saiya maze yace”Allah ya Bata lafiya      kaga Nima inasan in D’an fita wasu kasa shen nagaji da Zama A Nija kamar wani kifin Rijiya me zai Hana 

Na bika mutafi tare kaga na gano gari daga can.

Wata Dariya  Shuriem Yayi harda rik’e ciki  San nan yace” wai wayaga su Taufiq A egypt, Shima Taufiq dariyarce ta k’wace Masa Nan dai sukayi ta dariya Abinsu can dai Shuriem ya tsai gaita yaci serious san nan yace” wai dagaske ne zakaje” wallahi da gaske nake Taufiq yabashi Amsa.

To naji yanzu kaje ka Fara shiri cewar Shuriem, Murna Taufiq ya shigayi tareda gode masa, nu tsuwa sukayi suka cigaba da tsara yadda tafiyar zata kasance.

Yau ta Kama Sunday Wanda yay dai_dai da gobe tafiyarsu Su Shuriem, nayi Aikin gida nagaji Ina zaune Ina hutawa, ji nayi Anturo k’ofar d’akina Ana sand’a kaina na d’aga daga kwancen Dana ke Yaya nagani Yana shigowa kamar Yana tsoran Kar wani ya Ganshi.

Saida yazo dab Dani yace” Heedaya kitashi kije kiyiwa Momy sallama gobe zamuje Egypt nida ke da Meerah, tashi nayi daga kwancen danake Amma ko k’wak’kk’waran motsi na kasayi saboda mamaki.

Tsawa yadakamin bazaki Mike bane, tashi nayi Ina k’unk’uni dama da hijab Ajikina na wuce cikin gida.

A falo nasamu Momy tana zaune Kan ku jera, Sadiya na zaune ka’sa na yanka Mata fruit tana sha, Aiko cikakkiyar sallama ban tsayaba na shige Kai tsaye Abuna.

Momy ce tacemin” to sarkin hankali lafiya, k’arasawa nayi na tsugunna na gai sheta, Amsawa tayi San nan tace” kun Gama Shirin tafiyarne, A Ah yanzu zanje na had’a kayana dama nazo nai Miki sallamane, nace Mata, Murmushi tayi tace” kitashi kije Sadiya ta rakaki kiyiwa ummy Sallama saiki je kiyiwa iya, saiku wuce Tata yaki had’a kayan karki manta da wani Abun.

Albarka tasa mun San nan tace” kitashi kuje, mikewa Mukayi muka nufi part d’in ummy, mun tarar Bata Nan Sai su Kamal.

Daga Nan Kai tsaye b’angaran iya muka wuce, iya harda kukanta zata rabu Dani, Nima kukan nakama Yi domin harga Allah Ina k’aunar iya cikin Raina.

Haka muka rabu zuciyo yinmu badad’i,  Part dinmu muka wuce Kaya muka Shiga had’awa bayan wani lokaci muka gama, mikewa tayi zata tafi nace” Aikuwa hakuri zakiyi yau kitayani kwana Murmushi tayi tace” so kike Yaya yaha d’amu yazane mu duka, danaga dai ta d’au maganata da wasa, Kiran Momy nayi Awaya nagaya mata, nayi sa’a kuwa ta Amince ranar kwana Mukayi hira.

Ranar nayi kwanan farin ciki sosai Dan har makara Mukayi, bayan munyi sallah Agurguje Mukayi break Yaya nata mita shi bayasan jira.

Mun Isa Airport da wuri lokacin Saura 15mnts jirginmu ya tashi, lokacin da’aka kiramu zamu Shiga jirgi kuka na saka da kyar Aka b’an b’areni jikin Momy, Abba ma Yasmin Albarka sosai tare da yima fatan sauka lafiya.

Tunda muka Shiga jirgi Meerah ke tayimin kallon banza, nikuwa hira nakamayi da Yaya Taufiq tambayarsa nayi nace” Ya ya me zakaje Yi A egypt ne, Murmushi yayi yace”hutu kawai zanje murmushin jin dad’i nayi Araina nace” koba komai zan ringa ganin jinina Ina jin da dad’i kallan Anty Meerah nayi Ido cikin Ido nace” Araina ke kuma kishiryar Kar b’ar uk’uba ta wallahi indai suna na Heedaya Sai kinyi Dana sanin Abinda ki kaimin dama saboda Momy nake raga muku daga ke har mijinna ki yanzu muka Fara wasan daga Randa kika da k’afarki A egypt daga ranar kwanakin bakin cikinki zau Fara…….⁵⁷ ⁵⁸

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]