[Advertisements⬇️]

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 10 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya} - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 10 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yaya ne ya iso da sauri yadaga meerah  hankalinsa jini Sai zuba yake Ajikinta gashi kamarma Bata numfashi mota ya nufa da ita Nima nabishi Ina cewa yabari na d’auko hijab mutafi tare ko saura Rona beyiba ya sakata Amota  nikuma Ina ganin haka na koma na d’auko hijabina da gudu na fito natarar har yaja yatafi.

Ko mawa nayi nadauko kudi da wayata na rufe part din San nan nayi waje Ina Isa bakin titi me napep na tare na Gaya masa inda ze kaini nayi hankalinsa duk Baya jikina.

Muna isowa Asibitin Yaya na Ciro dari biyar na bashi har na fice yanata cemin ma na tsaya na karbi canjin nace yabarshi kawai, nashige.

Sister umaima na Fara nema saboda ita kadai nasani Wani daki Aka nuna min Akace tana can Ina shiga Meerah nagani  kwance Kan gado Ba inda yake motsi Ajikinta, cikinta kawai zaka kallah kaga Yana dagawa shine zai tabbatar maka cewa Akwai numfashi Ajikinta,  Sai Sister umaima tsaye A gefenta da Alamun da muwa A fuskarta tambayarta nashigayi me yake faruwa Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta dubeni Tace” Heedaya har yanzu bamusan me ke da muntaba.

Ina Yaya na tambaya cike da kaguwa tacemin yana office din Dr. Suhail  da sauri na fita daga dakin na tambayi wata Nurse Dan Allah inane office din Dr. Suhail kwatance taimin nawuce Ina zuwa ko izini ban jira Anbani ba na shige.

Yaya nagani zaune Kan kujera Dr. Suhail nacan Yana Yi Mai bayani Akan Rashin lafiyar Anty Meerah, Ai yanajin  shigo wata ya Mike ya zabgan Mari ya kuma zabga min kuncina na da fe saboda Marin ya shi geni nuna ni yayi da yatsansa sannan yace min” fita heedaya bana san ganinki.

Fita nayi Ina ta kuka Numbern momy na lalubo na kirata inajin ta daga nace Mata muna Asibitin Yaya Anty Meerah ba lafiya, Meya sameta Ina kuma shuriem din ta Fada hankalinta Atashe can kuma tace” kashe wayar Bari nakira shuriem din.

Kashe wayar nayi na nemi wasu kujeru nazauna Ina jiran tsammani cikin mintuna kalilan saiga momy ko saura Rona batayiba Naga  tayi hanyar office din Dr. Suhail can kuma saiga Yaya taufiq shida Anty saudat da gudu naje na rungu meta.

Momy ce ta fito ita da Yaya  Ransu duk Abace yake Anty saudat ce ta shiga tambayar momy Amma momy ta kasa magana hannun shuriem ta Kamo suka Zauna Tace Masa kayi hakuri son kadaure kuje Ayi Mata Aykin haka Naga yatashi sukuku ya tafi, momy ce ta Kira Anty saudat gefe bansan me suka tattau naba Sai ji nayi Anty saudat na sallallami.

Ni dai na kagu naji Abinda ke damun Anty Meerah Amma bawanda yagaya min can wurin yamma saiga Abba da Iya da Sadiya sunzo ganinsu yasa na danji dadi har muna taba Hira da sadiya domin na Dade bangan taba, can kuma saiga Maman Meerah ita da Ummi da haj. Amina kamar wasu ma haukata Ai suna shigowa da Maman Meerah Tayo kaina kamar wata Mai jinnu Yaya taufiq ne yay Azamar janyeni yace” baiwar Allah lafiya, Afusace Maman Meerah Tace malam wai meye naka kabarni na nakasta ta yadda ta na kastamin ya’, Sai kuma ta fashe da kuka meerah kadai na mallaka Arayuwata bani da wani d’a bayanta wallahi bazan yarda ba Sai na Rama Akan shegiyar yar’ Nan da ba’asan Asalintaba.

Iyace da Abba suka fito daga dakin Aka Kai meerah bayan An fito da ita daga theater room.

Iyace takaraso Dan taga wainar da Ake toyawa Yaya taufiq ne yay wa iya bayani Abinda ya faru, Aikuwa iya ta hau bala’i tana cewa” ke bakisan kaddara bane wallahi kina taba heedaya saina sa taufiq yay Miki shegen duka A wurinnan shege kafasa gaki Nan gata, Abbane ya shiga Basu hakuri Dan yasan halin iya zata iya sawa taufiq ya nada Mata na jaki Agurin, kuyi hakuri wannan Abu k’adda race kuma bawanda ze wuce tasa k’addarar kuyi hakuri Dan Allah Kinga Nan Asibiti kubari mukoma gida Sai muyi maganar Ay Maman Meerah ji tayi kamar ya watsa Mata fetur kallansu tayi daya bayan daya sannan Tace” Dukkanku ku saurareni wannan Abu daya faru bashi kuka dauka wallahi wallahi Sai na lalata rayuwar yar’ku wannan Alkawarina nane Sai tayi nada mar Abinda Ta Aikatawa Ya’ta wannan bashine kuma Akwai Ranar biyansa……

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

     Kuka Naringa Yi Ina ta magan ganu ”Ni Heedaya Ina zan sa kaina, na shiga uku, shi kenan Tsau tsayi da kuma ta kura tasa na Yi Abin  da ba dai_dai  ba Ni kuwa Yan zu, ya zanyi, haka dai nayi ta suru tai iri- iri momy ce ta dokemin Baki ta Fara magana kamar haka” kiyi min shiru wawuyar ban za wadda Bata iya sarra fa Kan ta idan tayi fushi ba”

“Yanzu me gari ya waya iyi Heedaya ga shi kinja wo Mana tashin Hankalin da bamu taba ga Niba, ko da labari ban taba jin irin wannan ba”.

   “Ummy ce Tai saurin karb’ewa dama Ai Hali ta gado irinnaki Nima wace kiti mur mura ce Baki shuka min ba, Amma da yake Allah ya tsare ni baga Shiba da Ace bani da tsari Atare da Ni yan zu kuma Sai buzuna”.

Abba ne ya daka Mata tsawa sannan yace” tabar Asabitin  ta koma gida yanzu_yanzu tun da fitina ta kawota, she ke ke ta kalleshi Tace” ni Ai kawata na Rak’o ba gurinku na zoba ”  Haj. Amina ce ta zungureta san nan ta tuna ta yi Kato b’ara, su kuwa da kallo kowa yabita kowa da irin tuna nin da yake.

Maman Meerah ce tsaye gefe gadon Yar’ta tana ta faman kuka, ga Meerah Nan kwance tamkar Bata numfashi, Dr. Suhail ne ya shigo d’akin ya kuma dubata har yan zu Bata far fad’o ba shi dai Kam Abin ya Fara bashi tsoro Yan zu fa sunkai A wa 6 da fitowa da ita da dakin thearter Amma still ko motsi Bata Yi Kara Duba ta ya yi ya tabbatar da tana num fashi tsoran sa daya karta Fada doguwar Suma ko kuma daga haka zata iya mutuwa, Maman tace ta shiga tambayarsa wane hali take ciki yanzu kwantar Mata da Hankali Ya yi sannan yace” insha Allahu zuwa dare zata far fad’o.

Shiru_shiru muna zau ne har bayan Isha’i Amma Meerah shiru kakeji Abba ne yace” lallai muzo mutafi gida gobe da safe ma kuma da wowa”  Momy kuwa ka fewa tayi baza ta tafi tabar Shuriem ba saboda Kota koma gida tuna ni baze barta tayi barci haka muka tafi muka barta, Amma Anty Saudat tace zata bimu ta kwana Damu saboda baban Taufiq Baya gari, Yaya Taufiq ne ya d’auko mu Amotarsa har gida.

Ba yan munyi parking Anty Saudat Tace yaje gida yadauko Mata kayanta Amsawa ya yi mukuma muka sauka shi kuma ya juya.

Bayan mun shiga ne dukkan mu Alwala muka Yi sannan Mukayi sallar Isha’i Mukayi wanka don gaskiya kowa ya gaji, Abinci Muka shiga muka da fa nida Sadiya muka zo muka Jerashi A Dining Anty nakira Ad’akin Momy tazo ta Duba Abincin san nan Tace” muzu ba kowa yaci tana kallo nidai da kyar na ringa hadiye wa saboda badan tana Nan ba gaskiya bazan ci Abincin ba.

Muna cikin ci Sai ga Ya ya Taufiq ya dawo daga dau kowa Anty kayan ta, Shima Abinci Nazuba Masa nace ya zau na yaci Sosa Kai Naga ya kamayi yana kallan Anty Murmushi kawai tayi ta mike ta koma daki don dama ita taga ma gani nayi yaja kujerar gefen Sadiya ya zauna Yace Rabin Raina zubamin Naci don gaskiya nafi bukatar Wanda ya fito daga hannunki Sadiya naga tana faman Murmushi taja pate ta zuba masa suna ta Hira Abinsu Da’alamu ma Ni sun mance Dani Awurin Table din na buga dukkansu hankalinsa ya dawo kaina.

Kallan tuhuma na Kama Yi musu sannan nace” wai in tambaye ku duk yau she kuka shirya wannan Abun ban sani ba”, Sadiya ce tayi caraf Tace” sanda kuka shirya kanku ke da Ya ya Shuriem”, Raina ne ya Soma baci saboda Naga suna Shirin Raina min hankali duka na kaiwa Sadiya ta goce Ai kwa Ya ya Taufiq ya bini Ni kuwa Nagudu D’akin Momy gun Anty dana Tabbatar Na shige juyowa nayi nai Masa gwalo, girgiza Kai Ya yi Yace zan kamaki san nan ya juya.

 Da sallama na shiga dakin Anty nagani zau ne gefen gado tana magana fuskarta d’auke da damuwa Nima gefen gadon na nema na Zau na kusa da ita.

Bayan ta gama wayar Na fuskance ta sosai Nace Mata” Anty Ina son magana da ke” Ina sauranki Tace Dani, cigaba nayi da magana “Anty Dan Allah so nake kigayamin Me yake faruwa da Anty Meerah?”.

Shiru tayi nad’an lokaci sannan Tace” saka makon faduwar da Meerah tayi ta fadi ne Akan cikin kuma hakan yasa  Sai da Aka cire cikin dake jikinta kuma Mahai farta ta samu Matsala Wanda hakan ne yajawo Akai Mata Aiki ko Allah zai sa ta dawo yadda take, Yan zu Momyn Yara ta kirani take cemin Meerah ta farfad’o Amma Shuriem yace Mahaifar Meerah bazata kuma daukan ciki ba, Sai dai in Ana San ta haihu Sai dai in ta warke Asa mu wata macen da ban Ahada sparm Nata Dana shuriem Asa Acikin Maihaifarta to in Anyi dace yin hakan ya Samar da d’a to Meerah zata iya ganin kwanta Aduniya Amma yace yiwuwar hakanma da wahala”……⁴⁹,⁵⁰

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]