[Advertisements⬇️]

HEEDAYA CHAPTER 49 BY By Khaleesat Haiydar - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HEEDAYA CHAPTER 49 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Juyowa Khaleel yyi ya mika masa hannu yana kallonsa, Shuraim ya ki amsa fuskarsa daure yace “Why are you 

here? And who are you?” Khaleel bai ce masa komai ba ya mika ma junaid da ke tsaye shi ma hannu, Junaid yayi 

jim ya ki mika masa nasa, sai kuma ya mika masa dai, Khaleel yace “Na xo wajen Mami ne” Junaid ya girgixa masa 

kai yace “Bata nan, she is in Abuja” Khaleel yace “Mai gadi yace min tana ciki” Shuraim ya cakumo kwalar rigarsa 

yana masa wani kallo yace “Karya yyi maka kenan??” Kallonsa kawai Khaleel yake ko kiftawa babu, Shuraim ya 

turasa da karfi har sai da ya isa bango, snn ya juya ya tafi waje gun sojoji fuskarsa a murtuke xai yi instructing dinsu 

su shigo su fitar da Khaleel din, Khaleel ya kalli Junaid dake ta kallonsa snn ya xaga ta parking space din ya nufi 

entrance din shiga parlon walking so fast, bude kofar parlon yyi ya shiga ya sa makulli ganin Sojojin sun biyosa a 

guje, Heedayah ta fito daga kitchen kenan da plate din ‘yar shinkafa da ta debo bisa umarnin Mami, wani firgitattcen 

ihu ta saki bayan sun yi ido hudu da shi, ta saki plate din hannunta jikinta na rawa ta dinga kurma ihun tana xaro ido, tsaye yyi bakin kofar yana kallonta, a guje ta koma kitchen din ta sa makulli hakan kuma bai sa ta fasa ihun da take 

ba, Farida na sakkowa stairs jin ihun da Heedayah ke yi suka yi ido hudu da shi ita ma, xaro ido tayi ta kwala ihun 

ita ma a tsorace ta koma sama a guje tana kwalo ma Mami kira, Mami ta fito bedroom dinta kenan jin ihun, suka ci 

karo da Farida bakin kofa, a rikice Mami ke kallonta tace “Me ya faru?? Ihun uban meye haka ku ke yi?” Farida na 

mayar da numfashi ta fashe da kuka sosai ta riko hannun Mami tace “Mami shi ne….” Mami tace “Shi wa?” Da kyar 

tace “Khaleel, gashi can a parlor wllh” Still Mami tayi tana kallonta don ita ma sai da gabanta ya fadi ba kadan ba, 

Farida ta kara rushewa da kuka tace “Mami wllh he is downstairs ya shigo mana parlor, su Yaya kuma sun fita” Da 

kyar Mami tace “Where is Heedayah?” Farida na nuna mata kasa cikin rawar murya tace “Taje debo abinci a kitchen, 

I heard her shouting shi ne na sauka, and I saw him at the parlor….” Mami ta xaro ido bata san lkcn da ta nufi 

downstairs din da sauri ba Farida na rikota a rikice tana cewa kar ta je, Mami ta warce Hijab dinta ta wuce, har 

sannan Khaleel na tsaye bakin kofar parlon da ake ta bubbugawa da karfi kamar xa a balla, Mami na sakkowa parlon 

ta kasa karasawa ciki tana tsaye daga bakin stairs din gabanta na faduwa tayi gathering courage tana kallon Khaleel 

dake kallonta tace “Me kake bukata daga garemu kuma bawan Allah?” Shiru yyi bai ce komai ba har sannan yana 

kallonta, hawaye ne ya shiga sakko mata tace “Me ya kawo gidana bawan Allah? Baka tsoron Allah ne? Me kuma 

kake so a wajena” Khaleel ya sauke idonsa da ya kada sosai, lkci daya ya nufeta, sosai xuciyarta ya shiga bugawa ta 

fara matsawa daga wajen tana kallonsa a tsorace, har lkcn Heedayah bata daina ihun da take tana kwalo ma Junaid 

kira ya xo ya taimake su ba, Haka ma Farida dake sama tana nata ihun, Khaleel na isa gaban Mami ya duka with 

both kneels a kasa yana kallonta a sanyaye yace “Ki gafarceni Ummi, it wasn’t intentional I was blackmailed, i was 

forced and threatened to do what I did, ba yin kai na bane wllh, ko da ina yin hakan baxan maki ba Ummi…” 

Hawaye ne ya kawo idonsa ya kasa kallon Mami, Mami dai sai kallonsa take har sannan gabanta bai daina bugawa 

ba, tace “Kana ma yi kenan?” Ya daga kansa yana kallonta cikin sanyin murya yace “Ina yi” Xaro ido Mami tayi 

tana kallonsa, hawaye ya shiga kai komo a idonta tana girgixa kai tace “Kana nufin kai Kidnapper din ne dai??” Ya 

gyada mata kai trying hard not to allow the tears in his eyes to flow, a sanyaye Mami tace “Why did u choose such 

life for your self Khaleel” Hawayen da yake ta avoiding ya shiga sakko masa, Mami na hawayen ita ma tace “Ka 

gaya min me yasa ka xabi wnn rayuwar Khaleel, me ya shigar da kai wannan mummunar harkan?” Cikin rawar 

murya yace “I was raised such way Mami, a haka na taso, a cikinsu na taso, a cikinsu na rayu…” Mami tace 

“Iyayenka fa?” Sauke kansa yyi kasa hawaye na sakko masa sosai yace “I was never opportune to know them, ban 

ta6a saninsu ba, ban san iyayena ba” Ya daura fuskarsa a kafarta tana jin saukan hawayensa yana shessheka da kyar 

yace “Su ne iyayena, bani da kowa a duniya sai su Ummi, da su na gan ni,” Dukawa Mami tayi ta xauna bakin stairs 

ta dago kansa with shock tace “How is that Khaleel?” Kasa bata amsa yyi hawaye na sauka idonsa xuciyarsa na 

masa xafi sosai, tace “Kayi min magana Khaleel” cike da karfin hali yace “Ban san me xance ba Ummi” Kuka sosai 

Mami take tace “Tell me more about you Khaleel” Ya share hawayen idonsa yace “Zayyad knows better, suna cikin 

manyan mu a lkcn don Zayyad is 45 now” Mami tace “Baka ta6a tambayarsa ko yasan wani abu a kanka ba” Khaleel 

ya girgixa mata kai wasu sabbin hawayen na xubowa idonsa…. Xuwa yanxu gaba daya sojojin dake layin na 

entrance din parlon Mami ana kokarin cire kofar, Gaba daya junaid ya shiga tashin hankalin da ya wuce misali, har 

snn kuma suna jin ihun Heedayah da Farida a ciki kamar xa su tsaga gidan, sbda rudewa ya ma mance da kofar 

kitchen dake ta baya duk da bai ma san Heedayah na kitchen din ba, lkci daya Shuraim ya xaga xuwa bayan gidan 

jin kamar ta nan Heedayah ke ihu, yana isa kofar ya bubbuga da karfi, Heedayah ta juya a mugun tsorace ta kara 

kwala wani sabon ihun tana cewa ta shiga uku, gaba daya ta mance da akwai kofa a kitchen din ita ma, yace “It’s me 

ki bude kofar” da sauri ta karasa gun kofar ta bude hannunta na rawa, tana ganin Shuraim ta rikosa cikin kuka tace 

“Ya Shureen wllh Kidnapper ne shi, Mami tace min shine yayi kidnapping dinta amma kar in gaya ma kowa, wllh 

yana parlon ya kulle kofa…..” Saketa Shuraim yyi ya nufi kofar kitchen din ya bude ya fita xuwa cikin parlon, sai a 

snn sojojin duk suka xagayo suka shigo gidan ta cikin kitchen din su ma, Mami ta mike da sauri daga bakin stairs da 

take xaune ganin Shuraim ya nufo su just as the soldier he is, tana kallon Khaleel a hankali tace “Don’t ever admit 

you a Kidnapper, deny that” bata jira Khaleel yace komai ba ta nufi Shuraim kafin ya iso su tace “Listen Shuraim, 

magana muke yi da shi…..” Kin sauraranta Shuraim yyi, ya bi ta gefenta ya isa gun Khaleel ya fincikosa ya kai masa 

wani wawan naushi biyu yana huci, Mami ta rikesa tace “Ban isa in maka magana bane Shuraim…. Are you alright 

ina magana baxa ka saurareni ba??” Turasa Shuraim yyi yana kallon sojojin da ke parlon yace “Seize him….” Sojojin 

suka nufesa, shi kuma ya fice daga parlon ta kitchen Mami ta bi sa da kallo, Heedayah na rakube jikin kofar kitchen 

ta waje har lkcn tana hawaye, tana ganinsa ta rikosa cikin rawar murya tace “Kun fita da shi ya Shureen?? Wllh 

Kidnapper ne, yana bindiga na ta6a gani…” wani kallo ya jefa mata yace “Waye ya kawosa gidan tun farko?? Ta 

dalilin wa ya samu fuskar fara shigowa gidan?” Hawaye na sauka idonta a hankali tace “Ni ce” wani kallo ya dinga 

yi mata, can ya fixgota har tana jin saukan numfashinsa a fuskarta yace “Da yaushe Mami ta gaya maki shi 

Kidnapper ne?” Kasa cewa komai tayi, ya hade rai yace “Baxa ki bani amsa ba” Da kyar tace “To… to ka sakeni” 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

saketa yyi ta koma baya taki hada ido da shi, yace “Answer my question now” Tace “Daxu ta gaya min” Juyawa yyi 

xai bar wajen ta bi sa da gudu ta fashe da kuka tace “Yaya Shureen is he still inside plss” Bai ce mata komai ba ta ci gaba da bin sa, ta kofar main parlor sojojin suka fito da Khaleel, Duk yanda Mami tayi da su su sakesa basu 

saurareta ba don it’s an instruction they are following, Junaid dai na tsaye balcony shi ma sai kallon Khaleel yake, A 

mugun fusace Mami ta nufi Shuraim tace “Baka da hankali dama Shuraim?? ban isa in gaya maka ka ji ba ashe??” 

Ba tare da ya kalleta ba yace “Mami wnn mutumin Kidnapper ne, kin sani, na sani, warce ta dalilinta ya fara 

shigowa gidan nan ta sani, So why are you covering up for him? beside you and people around you…. he is also very 

harmful to the society today, kin fi ni sanin wannan Mami, you are a lawyer, dole he have to be arrested ayi masa 

hukunci dai dai da abinda yake aikatawa, yanxu station xa a kai sa dole, I am sorry Mami, for your good, for our 

good, for the good of the society, babu xancen tausayi a case din nan, da xa a dinga bin tausayi da baxa ayi shari’a ba 

a duniyar gaba daya, he is guilty… kin boye shi yyi kidnapping dinki for a reason I never want to know, me yasa 

haka Mami??” Kallonsa kawai Mami take ko kiftawa babu gabanta na faduwa, can tace “Who told you that he is a 

Kidnapper?” yana kallonta a takaice yace “Heedayah, she said you told her everything today, he kidnaped you and 

requested the ransom of 30 million, which he was given….” Kallonsa kawai Mami ke ta yi, yyi kasa da kansa yace “I 

am sorry Mami, you can’t cover him up anymore” yana fadin haka ya juya ya nufi gate, Junaid ya sakko balcony ya 

taho gun Mami yace “Mami this is just the right thing to do, babu xancen tausayi a lamarin nan, he deserves this, 

idan ba rashin kunya ba gidan da kayi garkuwa da mutane ka sake dawowa, me ya dawo yi har da rufe kofar parlor? 

is he even alright….” Hawaye ne ke sauka idon Mami ta ki ce masa komai ta wuce ciki da sauri, Heedayah da Farida 

na rakube waje daya a parlon ko wannensu na xare ido, har sannan a tsorace suke gaba daya, ko kallonsu Mami bata 

yi ba ta wuce sama xuwa dakinta, ta dau wayarta ta shiga dialing number Barrister, Abba na parlonsa tare da Mumy 

da gaba daya ta daina fahimtar bayanin da yake mata na cewar gobe xa su tafi kai ma Junaid gaisuwan Heedayah a 

kano, ganin yanda tayi still Abba yace “Are you there?” Da sauri ta dawo tunanin da ta tafi ta mike tsaye tace 

“Junaid kuma?” Abba yace “Eh Junaid” Mumy tace “Gobe goben nan?” Abba yace “In sha Allah” xufa ne ya shiga 

karyo mata duk da Ac dake aiki a dakin, Ita fa ko jiya ita da Sadiya da Salima sai da suka sake komawa gun 

Mutumin nan na Salima suka kara masa kudi ya kuma tabbatar masu Shuraim sai ya auri Heedayah, kuma sai ynda 

tayi da Heedayah, xa kuma ta dinga mingling da manya manyan matan kasar suna fita kasashe tare, xa tayi suna 

sosai a kasar, Wani murmushi tayi ta girgixa kai sanin xuwa kai gaisuwar ba ma abinda xai yiwu bane, sae dai idan 

ba uban kudinta ta kai jiya ba, Abba ya jawo wayarsa dake ring, da yake tana gefensa ta saci kallon screen din wayar 

taga an sa Barr Rahinah, Abba ya daga kiran ya kai kunne tare da sallama, Mami tace “I need this favor from you pls 

Barrister…” Abba dake sauraronta jin yanayinta yace “Are you okay Rahinah?” Tace “Ka kira Shuraim yanxu don 

Allah ka dakatar da shi abinda yake shirin yi, do that now plss Barrister” da mamaki Abba yace “Me yake shirin yi” 

Mami ta sakar masa kuka tace “Do that before it’s too late Barrister, ka dakatar da shi, ni ya ki saurarata….” Abba yyi 

confuse da xancen Mami sosai, bayan Mami ta katse wayar yayi dialing number Shuraim yana fara ring Shuraim ya 

daga, Abba yace “Where are you? And what is happening Shuraim?” Shuraim yace “Bana kusa Abba, is there any 

problem?” Abba yace “Ohk, ko me kake yi I am instructing you to hold on to it, and come back home now” Shuraim 

yace “No Abba, it’s something important yanxu haka mun kusa station…” Abba yace “Station? Me ke faruwa?” 

Shuraim yace “Kidnapper din da yyi kidnapping Mami ne ya dawo gidan yau, anyi nasaran kamasa yanxu haka 

muna hanyar police station” Mikewa Abba yyi yace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, ina Rahinar da yaran suke 

yanxu?” Shuraim yace “They are safe home, but Mami na nuna a kyalesa but I didn’t listen to her being that it will 

be the greatest mistake to make…” Abba ya kasa cewa komai, a ransa kuwa tunani yake is Rahinah even okay? can 

yace “You don’t worry, Kar ka biyeta ku yi tafiyar ku gani nan xuwa nima yanxu” daga haka Abba ya katse wayar, 

ya dau makullin motarsa Mumy ta bi bayansa da sauri tana cewa “Me ke faruwa barrister?” Yace “Idan na dawo xan 

maki bayani, I have to leave now” Abba na shiga motarsa ya bar gidan ya dau hanyar station din da Shuraim ya 

sanar masa xa su je, a hanya ya kira Baffan Junaid ya sanar masa abinda ke faruwa da Dakta…. Khaleel na xaune an 

sa masa handcuffs both legs and hands a inda xa ayi interrogating dinsa cikin Police station din… Bin Shuraim kawai 

Khaleel ke yi da ido har Mami ta iso tare da Heedayah kamar yanda aka yi instructing Yan sanda biyu su tafi su taho 

da su station din, Dpo na kallon Mami bayan duk sun xauna ya nuna mata Khaleel yace “Kin san wancan Mutumin 

Hajiya?” Mami ta kalli Khaleel da ya sauke idonsa kasa tace “Na san sa” Dpo ya kalli Heedayah yace “Ke fa young 

lady?” Heedayah ta gyada kanta a hankali, Dpo na kallon Mami yace “Yana cikin Kidnappers din da suka dauke ki 

few days ago ko?” Mami ta girgixa kai tace “Aa baya cikinsu, bai kuma san komai kan xancen ba ma” Abba ya kalli 

Shuraim ya girgixa kai kawai, Shuraim dai sai kallon Mami yake da mamaki ko kiftawa bbu, Dpo ya kalli Heedayah 

yace “Ke kin tabbata dai wnn mutumin Kidnapper ne ko?” Heedayah ta daga kai tana kallon Khaleel da ya kafeta da 

idonsa, sauke idonta tayi da sauri ta kalli Shuraim dake kallonta shi ma, can ta girgixa kai tace “Ni dai ina xaton 

Kidnapper ne shi, ban san ko haka ne ko ba haka bane” Dpo yace “Xato? To me yasa har kika yi xaton haka?” Ta 

sauke kanta kasa tace “Because he is huge, and….” Murmushi Dpo din yyi ya nuna mata Shuraim yace “Isn’t he 

Huge?” Ta kalli Shuraim sannan ta sunkuyar da kanta, Dpo yace “And what?” Tayi kasa da murya tace “And naga ya 

kwana biyu bai xo gidanmu ba kuma sai aka yi kidnapping Mamin mu, sai yau ya dawo” Juyawa Shuraim yyi ya 

fice daga wajen kamar xai tashi sama, Junaid ya bi bayansa, Abba dai ya ma rasa abun tofawa mamaki duk ya ishesa, Dpo na kallon Khaleel yace “Kai me xaka ce game da xargin da ake maka na xama Kidnapper?” Khaleel ya kalli 

Mami dake kallonsa, ya girgixa kai yace “Xargin da suka min ba laifi bane don na kwana biyu bana garin at the time 

da abun ya faru, Ina jin kuma a ranan da na bar garin lamarin ya faru” Dpo yace “Ina ka tafi?” Khaleel yace “Naje 

wani aiki ne a kudu” Dpo yace “Wani aiki kenan” Khaleel ya nuna masa ID card dinsa dake ajiye da counter dinsa a 

gefe daya abinda kadai aka gani a aljihunsa knn, Dpo ya dau ID card din yana dubawa, can ya gyada kai cikin 

gamsuwa yana kallon Khaleel…. daga karshe dai Khaleel have to be released bbu wani proof yana da laifi tunda 

daga Mami har Heedayah sun yi shunning laifin da ake xarginsa da. Bayan sun fita daga station din wanda tuni 

Junaid da Shuraim suka yi wucewarsu, Mami na kallon Abba da Baffansu Junaid a hankali tace “I am sorry….” Abba 

dai bai ce mata komai ba, ya nufi motarsa haka ma Baffan Junaid, Mami ta jira har Khaleel ya karaso amma ya kasa 

kallonta, tana kallonsa cikin sanyin murya tace “Ku taho tare da Zayyad gobe, I want to know everything about you, 

amma bani kadai xan saurari labarin ka ba Khaleel, har Barrister da kuma duk wani wanda ke tare da ni, nayi 

alkawarin in har baka da wani laifi xa mu rufa maka asiri xa mu taimake ka Khaleel, and it’s not too late to still 

search for ur parent….”

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]