[Advertisements⬇️]

HEEDAYA CHAPTER 48 BY By Khaleesat Haiydar - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HEEDAYA CHAPTER 48 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kuka kawai Heedayah take ta kasa cewa komai duk da hayaniyar da kaka da Yakumbo ke mata suna tsaye a kanta, 

Farida dai na rakube gefe banda kuka bbu abinda take, DCP dake tsaye kusa da Baffan Junaid ya kwantar da murya 

yana kallon Heedayah yace “Xa ki gane gidan nasa na Abuja yanxu?” Heedayah ta girgixa masa kai kawai, yace “Da 

yaushe ya gaya maki su suka ta6a dauke ki?” Heedayah ta harari Farida amma taki cewa komai, DCP yace “Talk to 

me young lady, da yaushe ku ka yi xancen da shi?” K’in cewa komai Heedayah tayi still, Ammi ta sauke mata wani 

mari a fusace tace “Baxa ki bude baki kiyi ma mutane magana ba” Heedayah ta rufe fuskarta tana kuka sosai tace “Ni ba shi ne ya daukeni ba fahh” Mumy dake tsaye ita ma parlon tace “Haba Hajiya ai bin ta xa ayi a hankali, duka 

ba shine mafita ba a yanxu, idan aka lallabata duk sai ta buda mana abubuwan da Faridar ta fada yanxu” Abba na 

kallon Heedayah yace “Tashi xaune” Mikewa xaune tayi a hankali hawaye na sakkowa idonta, yace “Da yaushe ku 

ka yi magana da shi yace maki shi ya dauke ki years back” A hankali ta girgixa masa kai tace “Ni ba shine ya 

daukeni ba Abba” DCP yace “To wa ya dauke ki” Cikin rawar murya tace “Wasu mutane ne ba shi ba” Ya daure 

fuska yace “Amma yar uwarki ta ce kince mata shi ne ya ajiye ki gefen hanya bayan ya daukeki daga wajensu” 

Heedayah ta girgixa kai tace “She’s not saying the truth, ni ba haka nace mata ba” cikin kuka Farida tace “Karya take 

sir, ce min tayi yace mata shi kidnaper ne” Heedayah ta jefa mata wani kallo tace “He is not!!! Ni bance maki haka 

ba” DCP ya xauna yana facing dinta da kyau yace “You are not saying the truth young lady, baki son a ceto Mum din 

ki ne??” Heedayah ta fashe da kuka sosai gaba daya she look confused, Farida tace “Sir she’s lying, ya sanar mata 

shi kidnaper ne, da bakinta ta fada min haka wllh” Kuka sosai Farida take, Heedayah dai hawaye sai sakko mata 

yake taki cewa komai, DCP yace “Xaki xama suspect dinmu kenan, and we have no choice then to go with u to the 

station….” Abba yayi kasa da murya yace “She’s only confused sir, a bata sometimes xata yi magana idan Allah ya 

yrda” Junaid dake xaune ya sauke ajiyar xuciya yace “Lkcn da aka kwantar da shi a asibitin Abuja, the phone call his 

frnd is always making is highly suspicious, bbu gaskiya a kiraye kirayen sa, and idan yyi noticing dina a waje baya 

sakewa yyi magana, tun a lkcn na fara xarginsa amma ban kawo wani abu a kan shi Khaleel din ba” Baffansa yace 

“Abokin barawo ai barawo ne” Junaid yace “Ban yi tunanin Mami xata sake da shi Khaleel din har nan Kaduna ba, I 

once told her wnn mutumin stranger ne bai kamata tana jawosa jiki haka ba tunda ba saninsa tayi ba, she don’t know 

him but Mami didn’t listen to me, Dinar ma tayi mata magana bata saurareta ba…” Kaka na Shessheka tace “Mu dai 

daga ita har Heedayar sun kai mu sun baro mu muna xaman xamanmu ana shirye shiryen tafiya Gwamnet house, 

yanxu gidan ubanwa xa a samo wani shegen dubu miliyan hamsin idan ba Heedayar xa a kai kasuwa ba, ko ubanta 

dake da mukamin gwamna ynxu bashi da dubu miliyan hamsin balle mu karere, ni ban ta6a ganin yaron ba da sai na 

gane barawo ne tun kan aje ko ina wllh” Cikin rawar murya Heedayah tace “Ba barawo bane” wani Marin Ammi ta 

kara sauke mata, Abba yace “Subhanallah kar ki sake Hajiya” DCP da Baffan Junaid ma duk suka yi ma Ammi 

magana, Yakumbo ta fashe da kuka tace “Idan nayi magana sai a dinga min kallon me ta6in hankali, ranan farko da 

na fara ganin mutumin nan sai da nace ban yarda da shi ba yyi kalan yan satan mutane, amma bbu wanda ya dau 

maganata da muhimmanci, to yau ga dai abinda na fada ya fito, yanxu ya xa muyi fisabilillahi ga yar yarinya ko 

abinci nasan bata ci ba har ynxu, wani kai rahotu gidan radio da talabijin da gidan yan sanda duk ba shi bane wllh, 

fatana su fito cikin aminci, Ashnaah bata minti ashirin bata sha yagwat ba, to uban wa xai bata a can, Amadi daga 

komawarsa kujeransa yau sai yaji wnn mummunan labari mai cike da tashin hankali, don ma gwamnan kaduna bai 

bar maganar a haka ba shi ma yana bakin kokarinsa, ai wllh kashin yan kinnafas din nan ya bushe, xa su san har da 

‘yar gwamna suka dauke, don nasan da sun san yar gwamna ce Ashnaah baxa suyi gigin ta6a ta ba, dama an hada da 

Heedayar an tafi wllh da hankalina bai tashi haka ba tunda ita sun saba dauketa dama, ynxu banda xuciyar 

musulunci kina tunanin Junaidu xai yarda ya aureki bayan kwamushe uwarsa da aka yi ta dalilin ki, don ubanki 

gwamna ne ai ba ke bace gwamnan da xaki ja ma mata fitina tana xaman xaman ta…” Mumy sai da taji gabanta yace 

rasss jin abinda Yakumbo tace kan Junaid sai ya fasa auren Heedayah, Ammi dai ko kallon Yakumbo bata yi ba, 

Abba na rike da wayar Junaid yana ta kiran layin da aka kira da shi amma a kashe, Dr ya sauke ajiyar xuciya yace 

“Xa su kira Barrister, we have to calm down” Oga Arne na xaune parlor kan kujerarsa ya gama zuke zukensa Salim 

ya mika masa wayar da aka yi amfani da shi wajen kiran Junaid daxu, canxa layi yyi ya kunna wayar ya sake dialing 

Number Junaid, yana fara ringing Abba ya daga daya bangaren ganin bakon layi, Arne yace “Na kira in sanar maku 

inda xa ku kai mana kudin ku ajiye….” Abba yace “Yallabai ba mu da miliyan hamsin ynxu haka, ku fadi abinda xa 

mu iya baku domin Allah” Arne yace “Motar hawanta kadai ma xai yi miliyan 12, kada ku raina mana hankali, da 

alamar kun gaji da rayuwarta a doron kasa, xuwa karfe sha biyu gobe sae dai a dinga wani labarin ba wnn ba” Abba 

yace “Ka saurareni” katse wayar Arne yyi ya kashe gaba daya ya jefa ma Salim, Khaleel dake tsaye for almost an 

hour jikin pillar din dinning area din parlon ya rasa me ke masa ddi ya daga jajayen idanuwansa yana kallon Arne, 

wani dariya Arne yyi, Khaleel ya karaso cikin parlon yana dubansa sosai yace “A janye maganar kudin fansar ni xan 

baku….” Arne yace “Kana da wani alaka da ita ne da xaka bada kudin fansan?” Khaleel yace “Xan bada saboda a ta 

dalilina ku ka dauketa, snn they can’t afford that amount” Arne ya mike yace “Naga alama after all this baxa ka rabu 

da mutanen nan ba, I think the best thing is just to send her to her early grave snn mu bi duk wani nata mu kashe, 

hakan kadai xai sa hankalin ka ya dawo jikin ka, amsan kudin fansa da 6ata maka suna a wajensu duk ba shi bane, 

xaka iya yin komai don ganin ka koma garesu, I mean xaka yi brain washing dinsu su kuma su kara amsar ka, 

kasheta shine kadai mafita a yanxu…..” Khaleel da xuciyarsa yyi masa nauyi ya duka nan kasa da kyar yace “Kada 

ka kasheta Oga, don’t forget she is a barrister idan nace xan koma gun daughter dinta xata yi exposing dina a idon 

duniya, xata tona min asiri, Kar ka manta bbu uwa ta gari da xata so tarayyar ‘yar ta da hoodlum, ni kuma hoodlum 

ne, don haka kun riga da kun rabani da su don’t go further then this plss, kar ku kasheta….” Arne dake ta sauraronsa 

yace “Toh idan ka kuskura ka sake cewa xaka bada kudin fansa sai na aika wnn yar yarinyar dake tare da ita lahira” Khaleel ya sauke kansa kasa hawaye na sauka idonsa bai ce komai ba, Arne ya koma ya xauna yana huci, Khaleel ya 

daga kai bayan few seconds yana kallonsa da kyar yace “To a taimaka a basu wani abun su ci ko su sha….” Arne ya 

mike yana masa wani kallo yace “You cannot break our rule all of a sudden Brainiac….” Mikewa Khaleel yyi a 

hankali ya koma inda yake tsaye ya jingina da pillar din ya runtse idonsa. Karfe sha biyu na dare Arne ya sake kiran 

Abba, nan Abba ya nemi alfarman su bar kudin miliyan talatin, da kyar da kyar Arne ya amince bayan cin mutunci 

iri iri a waya snn ya bukaci Motorcycle guda biyu sababbi dal a hada da kudin, nan ya sanar masu inda xa su tafi su 

ajiye masu kudin da safe. Washegari da sassafe Junaid ya tafi tare da Abba da Baffansa sai DCP a cikin motar Abba 

kai kudin inda Arne yace su kai a wani kauye cikin garin kano, wata motar kaya ce a bayansu dauke da Motorcycle 

guda biyu, a cikin motar motorcycle din kuma Yan sanda ne gudu hudu duk sanye da mofti, banda motar dake bayan 

motar Motorcycle din dake cike da sojoji, wayar Junaid dake hannun Abba ne ya fara ring ganin sabon Number ya 

daga ya sa handsfree, muryar Manga ne ya cika motar yace “Kai ku koma da kudin ku, snn karfe hudu na yamma ku 

duba can karshen layin gidanku xa mu ajiye maku gawarsu a can, sbda raini xaku kawo kudi sai kun yi xuga har da 

motoci uku, mu xa ayi ma wasa da hankali, mu xa a raina ma wayo, to wllh wllh kasheta xa mu yi idan mutum daya 

baxai taho da kudin ba” DCP sai kalle kallen hanya yake don ko Zaria basu karasa ba kuma motoci dai dai ne a 

hanyar ke tafiya, Junaid ya jinginar da kansa jikin kujeran motar hankalinsa a tashe, Parking Abba ya samu gefe yyi 

sauran motocin bayansa ma duk suka tsaya ganin haka, DCP yace “Mu je kawai Barrister kyale yan Iska suna biye 

da mu ne….” Baffan Junaid yace “Aa kamar dai yanda yace Sbda lafiyar Rahinah da yarinyar wajenta mutum daya 

kawai ya kai kudin yallabai, further investigations should follow forth, yanxu dai the life of Rahinah and the little 

girl matters first, ba imani ne da su ba xa su iya aikata abinda suke fada” Abba yace “Haka ne, ni xan tafi in kai masu 

kudin, kamar yanda Alhaji Imran ya fada further investigation should follow forth, their lives first” Junaid yace “Let 

me go instead Abba, ni xan kai masu kudin” DCP yace “Junaid ya tafi, and you have to be very very vigilant and 

careful junaid” Junaid yace “In sha Allah” Abba ya bude motar ya sauka sauran ma duk suka sauka, motar da Babur 

din ke ciki duk suka nufa, bayan an yi ma drivern motar bayani ya sauka Junaid ya shiga, Abba ya mika masa 

wayarsa yace “Be careful Junaid, and kayi ta addu’a, Allah ya tsare” Junaid ya amshi wayar ya ajiye gefensa yace 

“Ameen Abba” snn ya tada motar ya ci gaba da tafiya xuwa garin kano. Dai dai wani matattacen gidan mai na 

Bulasawa da aka yi abandoning baya aiki suka sa Junaid ya ajiye masu kudin ya sauke duk mashinan, wayarsa ne 

ya fara ring ya fiddo ya daga, “Malam ka gama aikinka, maxa ka bar wajen nan da mintuna biyu kacal” Junaid yace 

“Toh Mahaifiyar tawa fa?” Aka ce “Xata riga ka isa gida ma” Daga haka aka katse wayar, shiga motar junaid yyi ya

tada ya bar wajen cikin few seconds. Sai bayan awa kusan hudu Junaid ya isa Kaduna sbda motar da yake driving, 2 

hours ago Abba ya kirasa ya sanar masa Mami and Ashnaah are home, Hamdala Junaid yyi lkci daya hankalinsa ya 

kwanta sosai, tun da ya iso anguwar tasu yake ganin motocin sojoji har ya isa layinsu, sai da aka yi interrogating 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

dinsa snn ya shiga layin yyi parking kofar gida ya gaida sojojin snn ya shiga gidan, Duk su Abba na parlon ya shiga, 

Sai bayan awa kusan hudu Junaid ya isa Kaduna sbda motar da yake ja, 2 hours ago Abba ya kirasa ya sanar masa 

Mami and Ashnaah are home, Hamdala Junaid yyi lkci daya hankalinsa ya kwanta sosai, tun da ya iso anguwar tasu 

yake ganin motocin sojoji har ya isa layinsu, sai da aka yi interrogating dinsa snn ya shiga layin yyi parking kofar 

gida ya gaida sojojin snn ya shiga gidan, Duk su Abba na parlon ya shiga, Kaka na ganinsa da karfi tace 

“Alhamdulillahi, na shiga bandaki yyi sau ashirin sbda tunanin ka Junaidu” Shi dai gaba daya hankalinsa na kan ya 

ga Maminsa, gaba daya occupant din parlon look very happy seeing him, kaka tace “To a xubo masa abinci ya ci ya 

koshi dai tukun” Yyi kasa da murya yana kallonta yace “Mami da Babyn fa” Kaka tace “Tana can sama tana bacci, 

har yanxu dai a tsorace take baiwar Allah, manya manyan likitoci gwamnan kaduna ya turo su dubata, ita kuma 

yarinyar tana can ana mata karin ruwa ta galabaita da yunwa, fitinanniyar matar can na kanta da uwarta” Sama 

Junaid ya nufa sai da ya fara shiga dakin da Ammin Heedayah ke ciki snn ya fito bayan minti sha biyar ya shiga 

dakin Mami, bacci ya sameta tana yi ya karasa ciki ya xauna gefenta yana kallonta.Mami na xaune parlor bayan Magrib da hijab din da tayi sllh har kasa da carbi a hannunta, gaisawa suka yi da DCP 

dake parlon shi ma wnda sbda shi ta sakko downstairs, Abba na xaune parlon kusa da DCP shi ma, kaka da 

Yakumbo na xaune daga gefe daya su ma ko wannensu na kallonta, sai Ammi dake rungume da Ashnaah dake bacci, 

matar Baffan Junaid na rike da Ashfah, sai wata colleague din Mami a kusa da ita, Heedayah dai na bayan kujera ta 

ki yarda ta hada ido da kowa tun dawowar Mami, Junaid na tsaye yana kallon Mami da gaba daya tayi sanyi, DCP 

yace “Hajiya xaki iya gane gidan da aka kai ki jiya?” Mami ta girgixa kai tace “Aa” DCP yace “Tun farkon fara 

tafiyar taku baki lura da anguwar da ku ka shiga ba ko wajejen da ku ka bi??” Mami tace “Duk ban lura da hakan ba 

don hankalina baya jikina a lkcn” Shiru yyi na wasu sakwanni sannan yace “Toh su nawa ne Kidnappers din?” Tace 

“Ban kirga su ba amma suna da yawa” Yace “A cikinsu akwai wanda kika sani?” Mami bata ce komai ba, kowa na 

parlon kallonta yake, DCP yace “Feel free to talk to me Madam, akwai idon sani a cikinsu?” Ganin Mami tayi shiru, 

Kaka tace “Yau naga bala’i ana tambayar ki abun arxiki kin yi shiru” firgit Mami ta dawo daga duniyar tunanin da ta 

lula tunda DCP ya jefo mata tambayar, DCP yace “Kada ki damu Hajiya bbu wani abun da xai sameki you are safe, 

ki gaya min a cikinsu akwai wanda kika sani?” Mami ta girgixa kai a hankali tace “Babu” Idanuwa aka xuba mata a 

parlon barin junaid, DCP yace “Kina nufin bbu wanda kika sani ko kika ta6a gani a cikinsu?” Ta gyada masa kai tace 

“Duk ban san su ba” Yakumbo tace “Ya xa ki ce baki san su ba, nan nan Farida tace wnn rusheshen mutumin dake 

xuwa gidan nan wajen Heedayah d’an kinnafa ne, kuma Heedayar ce ta sanar mata hakan, hatta Junaid ya shaida 

hakan shi ma, to wa xai dauke ki idan ba Mutumin ba? Wllh shi ne, idan ma tsoro kike ji ga dai jami’an tsaro duk an 

watsa a anguwar nan, lungu da sako” Mami ta kalli Junaid dake ta kallonta tace “A ina ka shaida hakan??” Junaid ya 

kasa cewa komai, can ya girgixa mata kai yace “Aa I was talking of his frnd” Mami tace “To babu wanda na sani 

cikinsu” Kaka tace “Toh ai dama mutumin baxai yarda ki gansa ba, hauka yake xai bari ki san har da shi cikin 

kinnafas din, mu dai ba ya cucemu ya raba bayin Allah da basu ji ba basu gani ba da miliyoyin kudinsu, daga karshe 

ma sai ni na cika kudin wllh, Allah dai ya isa, tunda kuma abu ya xama haka ayi maza gaskiya a sa ma Deedayah 

rana da Junaidu kowa ya huta don duk dalilinta wnn tashin hankali da asaran ya faru, Kuma wllh a yanda Farida ta 

nuna Mutumin sonta yake yi…. Kuma tun da yana shigowa gidan yana ganin baja baja ai dole yyi cuta” DCP yace 

“You need rest Madam, ki tafi sama gobe sai ku taho station da Barrister” Kamar Mami jira take ta mike tace 

“Nagode yallabai, sai da safe” Tana kallon Abba tayi masa sai da safe shi ma sannan tayi hanyar stairs, ido hudu 

suka yi da Heedayah dake bayan kujera har snn, Heedayah ta sauke kanta kasa, Mami ta wuce sama. Bayan kwana

biyu da faruwan lamarin Ammi suka koma Kano tare da Kaka da Yakumbo, bbu wanda yace Heedayah ta bi su, 

Yakumbo ma cewa tayi ita ba ruwanta su tafi da ita a sake biyowa a kwashesu gaba daya, kana ganin Heedayah 

kasan tana cikin damuwa sosai, gaba daya ta rame, bata da aiki sai xaman bayan compound, ko abincin kirki bata ci, 

har lkcn taki yrda xaman waje daya ya hadata da Mami, iyakarta da ita gaisuwa, duk da Mamin ma tana bedroom 

dinta always ko fitowa parlor bata yi, har snn kuma a sanyaye Mami take, Bayan tafiyarsu Ammi Farida na parlor 

tana danne danne a system dinta aka yi knocking kofar parlon, ganin mai aikinsu na dakinta yasa ta mike ta isa kofar 

ta bude, Shuraim ne tsaye bakin kofar, tun faruwan incident din sai ranan ya xo, he look pale, kana ganin sa kasan he 

just recovered, ta basa hanya tace “Good evening” ya shiga parlon yace “How are you?” Tace “I’m fine” yace “Mami 

fa?” Tace “She’s sleeping, ta sha magani ne” yace “Ohk” xaunawa yayi saman kujera, ta tafi gun system dinta ta 

xauna ta ci gaba da abinda take, lkci lkci take kallonsa ta gefen ido, bayan few minutes ya juyo suka hada ido, dauke 

idonsa yyi yace “Heedayah fa?” Tace “She’s outside” Yace “What is she doing outside?” Tace “I don’t know” Bayan 

few minutes yace “Outside where?” Tace “Ta backyard” Mikewa yayi ya fita daga parlon, can bayan gidan ya 

sameta xaune a karamin garden din tana xane da karamin iccen hannunta a kasan dake shimfide wajen, jin taku ta 

juya da sauri, suna hada ido ta dauke kanta ta ci gaba da abinda take, ganin bata ga ya karaso ba ta d’an saci kallon 

hanyar taga ba kowa, juyawa tayi tana kallon wajen, can ta ci gaba da xanen da take a kasa, Farida na ganin Shuraim 

ya dawo parlon yyi xamansa ta mike ta wuce kitchen, ruwa ta kawo masa a tray ta ajiye nan gabansa, ta koma gun 

system dinta, yace “Thank you” Ba tare da ta kallesa ba tace “You are wlcm” Xuba ruwan yyi a glass cup ya sha ya 

ajiye snn yace “Wani course kike yi a schl” Ita dai idonta na kan system sai taji kamar ba da ita yake ba, can ta juya 

ganin kallonta yake tace “Biochemistry” Ya d’an buda ido yace “Why biochemistry?” Tace “Kawai” Yace “Xa ki iya 

kuwa?” Ta kallesa ta d’an yi murmushi tace “Gashi ina yi” Ya daga kafada yace “Allah ya bada sa’a” Tace “Ameen” 

Bude kofar parlon aka yi, Heedayah ta shigo, ba tare da ta kallesa ba ta wucesa snn ta gaishesa ta haura sama. Da 

daddare Heedayah ta fito daga wanka Mami ta shigo dakin, tunda Heedayah ta kalleta sau daya ta kasa ci gaba da 

kallonta, Mami ta xauna gefen gadon tana kallon Farida tace “Excuse us dear” Mikewa Heedayah tayi ta fita, Mami 

na kallon Heedayah ta nuna mata gefen gado, a sanyaye Heedayah ta karaso ta xauna gefen gadon tana kallon Mami, 

lkci daya hawaye ya kawo idonta cikin rawar murya tace “I am sorry Mami I caused you everything, I don’t know……” Sai kuma ta fashe da kuka sosai ta rufe fuskarta da gadon, Mami ta dagota tace “You caused me nothing, 

now tell me, me da me Khaleel ya gaya maki a kansa” Hawaye na sauka idon Heedayah tace “Ce min yyi shi ya fito 

da ni daga wajen Kidnappers” Mami tace “So he told you he is also a Kidnapper” Heedayah ta girgixa kai tace “Aa 

he wasn’t straight, but I suspect that” Mami tayi shirun Wani lkci snn ta sauke ajiyar xuciya cikin sanyin murya tace 

“Khaleel Kidnapper ne Heedayah, he is a hoodlum with large gang, but this should be between just I and you, kada 

ki fada ma kowa koda Farida kuwa” Heedayah ta fashe da sabon kuka tace “Mami shi ya dauke ku ko? Shine yyi 

kidnapping din ku ko?” Mami dake kokarin ganin hawaye bai kawo idonta ba tace “Shi yasa aka dauke mu 

Heedayah, Shuraim ya ta6a gaya min he don’t trust him not even for a second, haka ma Junaid amma duk ban dau 

xancen su da muhimmanci ba, sai gashi, Khaleel is beyond ur thought dear, he is thug…” Heedayah ta fada jikin 

Mami tana kuka sosai tace “I am happy he didn’t hurt you Mami, ni na jawo maku kiyi hakuri ki yafe min, I don’t 

know why I trusted him all of a sudden” Mami ta goge hawayen da ya sakko nata idon a hankali tace “I don’t think 

we are safe together anymore a gidan nan Heedayah, nayi ma Amminki magana xaki koma can kano cikin satin nan, 

don bana son wani abu ya sameki, Kar ya ci gaba da bibiyarki ya cuce ki…” cikin rawar murya Heedayah tace 

“Mami mu tafi kanon gaba daya plss, kema u are not safe anymore” Mami tace “Aa… am going no where dear, ke 

kam xaki koma wajen Amminki, I don’t want you to be here” Heedayah ta shiga goge idonta bata dai ce komai ba, 

Mami tace “And ki fada min gaskiya do you have any feeling for Junaid, bana son a shiga hakkin ki, don matsayinki 

daya da junaid a wajena” Heedayah ta dago da sauri tana kallon Mami, Mami tace “Yes, tell me” Sauke idonta tayi 

ta kasa cewa komai, mamaki ya cikata, Mami tace “Kar ki ji komai ki gaya min gaskiya” Heedayah dai ta ma rasa 

abinda xata ce, Mami tace “Sbda incident din nan da ya faru Yakumbon ki tace xa ayi maki aure kada ya ci gaba da 

bibiyanki, I think ana komawa xa ayi magana, so tell me ur mind now….” Jin Heedayah ta ki cewa komai still, Mami 

ta kamo hannunta tace “Toh ki gaya ma Farida gobe ta gaya min kin ji??” Heedayah dai sai kallonta take ko kiftawa 

bbu, Mami ta mike tace “Good night dear” daga haka ta fita dakin ta kullo kofar, Heedayah ta fashe da wani kuka 

tana imagining wai Junaid, da wani idon ma xata iya cewa Mami bata son Junaid, she just can’t, kuka take sosai sai 

dai ba xancen Mami na karshe ne ke sata kuka ba, taji xuciyarta yyi mata xafi she wish this is a dream na cewa 

Khaleel Kidnapper ne….. Khaleel ya sauka kan napep ya ba mai napep din kudinsa snn ya karasa layin walking 

calmly, karfe takwas da yan mintuna ne na dare, sojoji ne bakin layin a xaune, ga motarsu daga gefe a tsaye, ya 

fiddo ID card dinsa ya nuna masu snn ya shiga layin a hankali yake tafiya har ya isa bakin gate din gidan, sojoji ne 

tsaye a gate din, suka tambayesa wa yake nema, yana kallonsu yace “My aunt…” yana fadin haka ya ciro iD dinsa ya 

nuna masu su ma, daya sojan ya bude gate din Mai gadi ya taso da sauri, Khaleel ya dake yana kallon Mai gadin 

dake kallonsa shi ma yace “Wa kake nema?” A nutse yace “Mami” Bai jira cewar Mai gadin ba ya shiga ciki yana 

maida ID dinsa aljihu, dai dai nan aka bude kofar main parlor, Shuraim ya fito tare da Junaid, lkci daya Khaleel ya 

juya ya fiddo wayarsa ya nufi parking space ya kara wayar a kunne kamar me receiving din call yana tsaye parking 

space din, Shuraim ya karaso compound din tare da junaid yana kallon Khaleel da ya juya masu baya wayarsa a 

kunnensa har lkcn, ya kalli sojojin dake tsaye bakin gate snn ya sake kallon parking space din, ta madubi Khaleel ya 

ga Shuraim ya nufo sa…..

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]