[Advertisements⬇️]

DEEMAH CHAPTER 9 BY ZAHRATEEY - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

DEEMAH CHAPTER 9 BY ZAHRATEEY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Bayan wad’annan wahalhalun daya sha ya warke shine aka sake jefa mishi wani na barin gida baki d’aya, dama ya tafi abuja wani aiki daga nan suka nemeshi suka rasa shi. Abubuwa biyu suka had’a mishi na farko sun so sunansa ya 6aci ta hanyar haifar dan gaba da fatiya sannan kuma ya 6ata 6acewa na har abada, fatansu na farko bai yiyu ba domin daya tashi sai Allah ya bashi tunanin auren wadda yayi tarayya da itan, na biyu kuma 6atar nasa ya sake zama alkairi inda ya had’u da malamin musulunci ya d’aura akan karatun da bai samu ya yi ba na addini, domin hankalinsa gaba daya akan boko ya bayar kuma wannan shine laifi na farko kin bada hankali da kulawa akan sanin addini, kuma yana d’aya daga cikin dalilan da suka jefa shi a halin daya dinga shiga saboda babu wani adduar tsari a tare da shi, (misali alwala da ake so mutum ya kasance yana da shi a ko da yaushe, adduar safe dana rana dana dare domin samun kariyar ubangiji a duk inda mutum yake, wasu sun d’auka kawai kayi salla ka guji aikata alfasha sune kawai abin da ake bukatan musulmi ya kiyaye, sun kasa fahimtar cewa addu’o’i suna daya daga cikin kariyar da zasu samu a cikin rayuwarsu, domin wani zaiyi salla amma zaman adduar sai ya gagareshi, ga kuma yan kananun abubuwan da mutane basu dauka a komai ba wato sadaka yawan sadaka shima wani abin ne acikin rayuwar dan adam, yawan tasbihi da hailala, abubuwa da dama wanda ake bukatan musulmi ya rike amma sai ya zama wahala suna daya daga cikin abin da yake lalata rayuwar dan adam ko kuma miyagun mutane suke samun galaba akansa, duk da cewa akwai kaddara amma silar itace abin dubawa).

+

Abubuwa irin haka su suka jefa _Sufyan_ cikin gararin rayuwa yayinda a 6angaren _Jidda_ ta taso da sanin addini sosai dan iyayenta basu barta kara zube ba, tun sanda take gidansu ta sauke alqurani me girma haka duka yan gidansu sun sauke hadda ne dai ita kad’ai Allah ya bawa ikon haddacewa baki d’aya amma yayyinta da kannenta daga masu izu goma, goma sha biyar, ishirin sai kuma talatin. Ita kuma silar samun cikekken hadda shine zaman gidan yayan babanta kasancewarsa malamin addini sosai ya daura gidansa akan tarbiyya me kyau, gaba daya yaransa mahaddatar alqurani ne haka littafai da yawa duk ya musu dan yace meye amfanin naka basu sani ba amma kayi kokarin koyar da wasu na waje, da haka ya samu karfin gwiwar d’aura yaransa a kan turba ta gaskiya dan za’a iya cewa _Jidda_ rainonsa ce, yarda da kaddara, hakuri da juriya barin ubangiji ya dauki mataki akan duk wanda ya cuce ka domin nashi shine dai-dai kuma sakayyarsa yafi ko wanne, abubuwa da yawa wanda za’a tsinta a cikin halayyar _Jidda_ duk tarbiyyar da ta samu ne, shiyasa yana da kyau iyaye su kasance masu ilimi da kuma tarbiyya domin su d’aura y’ay’an su akan turba na gaskiya saboda rayuwarsu ya zama yana tafiya kan tsarin addinin musulunci bisa kawar da son zuciya da hassada da kuma yarda da kaddara me kyau ko mara kyau da kai zuciya nesa gurin dogaro ga ubangiji da kokarin aikata abinda yake me kyau.

Duk yadda _Mama_ suka so cutar da ita abin baya yuyuwa domin ta kasance me riko da addini, sallar dare ko da raka’a biyu ne baya wuce ta, yawan sadaka, zama sa alwala, yawan hailala da tarbihi, yawan karatun alkurani adduo’in safe yamma da kuma dare duk babu wanda yake wuceta face wani lalura idan ya zama dole, misali fashin salla amma duk da haka tana kasancewa da alwala, duk wadannan abubuwan sune suka zama kariya a gareta da kuma kariyar ubangiji domin komai sai Allah ya nufa yake samun bawa amma kamar yadda muka ce silar itace abin dubawa, a 6angaren _Jidda_ sun kasa da ita saboda riko da addini a 6angaren _Sufyan_ kuma sakaci da addua da kiyaye wasu dokoki shine silar jefa shi a halin da yake ciki.

Shiyasa akace idan kaga mutane suna cikin jin dadi kawai ka barsu ka fuskanci naka matsalar domin baka san suma abin da rayuwarsu ya kunsa ba, mutane da dama suna ganin cewa babu wani damuwa a cikin rayuwar ma’aurata biyun saboda yadda suke so da kaunar junansu tare da nunawa duniya cewa suna cikin natsuwa da kwanciyar hankali sai dai kuma wannan shine matsalarsu tun _Jidda_ tana maganar har ta gaji ta daina fad’ansu baya wuce akan ire iren abubuwan nan, idan ta tashi salla ta tashe shi zai ce ta barshi a gajiye yake, idan yayi sallar asuba da yayi adduoinsa shikenan babu karanta litattafai irinsu hisnul muslim, sadaka ne dai wannan ta san yana yawan yi, amma azkar yana mishi wahala na safe yamma da dare, wani lokaci har kin kula shi takeyi dan kawai ya fahimci laifin na shi me girma ne amma sai dai su gama fad’an ba zai wani sauya ba, haka karatun alkurani bai wuce yayi sau daya a sati ba, duk sanda tace suyi zai ce ya gaji ko kuma zai yi anjima ko yana jin barci a haka shikenan ba zai yi ba har sai ta sake magana sai ya yi dan kar ranta ya kara 6aci.

Har zuwa yanzu an kasa gane cewa akwai sa hannun na gidan akan gararin rayuwar _Sufyan_ bayan _Hajja_, _Jidda_ _Umma_ da _Anty_ Aisha babu wani wanda ya san cewa duk aikin _Mama_ ne, sau da dama _Anty Aisha_ na son fayyace wasu _Daddy_ komai sai dai _Hajja_ ce take hanata, takance mata ai rana tara ne kachal na 6arawo rana daya kuma na mai shi, su zubawa sarautan Allah ido shi zai bi musu hakkinsu ta inda basuyi tsammani ba, gwara suyi tuban gaskiya idan Allah ne ya zartar da hukunci akansu akan suyi na muzuri idan dan adam ne ya tona musu asiri, haka zalika _Jidda_ bata ta6a goyon bayan a tona musu asiri ba dan ta san cewa Allah ba azzalumin sarki bane da sannu komai zai bayyana kansa, hakan shine tarbiyan gidan kawunta ba’a d’aukan mataki idan ana son ganin hukuncin daya fi ko wanne tsanani ga wanda ya maka rashin kautawa da sannu Allah zai bi maka hakkinka ta hanya mafi sauki kuma me matukar radadi ga wanda ya cuceka.

    *Wannan kenan*…

________________________

Zaune take a falo kamar kullun tana d’ora musu karatu a inda suka tsaya, yaran akwai kokari sosai kuma wani abin da yake sa suke bada himma shine idan tace duk wanda yafi kokari Allah zai sa shi a aljanna, bayan sum gama karatun suka maida litatafan inda suka dauko shi, domin ta koya musu adana komai a inda aka d’auka ba wai a ajiye a duk inda ake so ba. Bayan sun mayar suka dawo kusa da ita suka zauna sannan sukace mata yaushe babansu zai dawo. Wannan tambayar da suke yawan mata shine yake tarwatsa zuciyarta domin bata da masaniya akan ina baban nasu yake balle kuma har ta san lokacin dawowarsa.

Shigowar _Hanifa_ shine ya ceceta daga tambayoyin da suke mata, cikin sauri suka tashi suka bar gurin bayan sun gaisheta, saboda hakan shine tarbiyyansu, idan manya suna guri basa zama balle har ayi magana su tsoma baki ( iyaye suna wannan sakacin gurin barin yara a guri idan aka tautaunawa, idan abin ya kasance mara dadi tsakanin iyayensu sai kuga sun rike a rai, idan kuma wasu maganganu ne mara kyau sai su rike su haddace, idan kuma suka taso da zama a tsakanin manya sai kaga a hankali a hankali har sun fara tsoma baki a zance, idan suka fara haka kuma ba’a nuna musu kuskurensu ba shikenan kuma haka zasu taso a ko ina sukayi suna ganin babu wani matsala tunda ba’a ta6a kwa6arsu ba).

Bayan fitansu suka gaisa da _Hanifa_ sannan suka shiga hiran duniya, daga nan kuma ta sake sako mata zancen kai kararsu _Mama_ a gurin _Daddy_ domin su san abin yi akan 6atan _Sufyan_ ita dai _Jidda_ kawai ta amsa mata ne da to zatayi tunani a kai saboda tana son su bar maganar, ita kuma _Hanifa_ tana son _Jidda_ tayi hakan ne saboda hankalinsu _Mama_ ya koma kanta su samu damar kawar da ita daga doron kasa dan hakan shine fatanta kuma burinta domin ta zauna ita kad’ai a gidan _Sufyan_ dinta.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

________________________Yau mun wayi gari da rashin mutane har biyu yayarmu _Fauziyya_ da kuma matar yayan mu _Faisal_ duk yan d’akin _Ya kolo_ kuma duk a gurin haihuwa, ita matar yayan mu asibitin da aka kaita ne wai saboda a lokacin duk a rikice _Ya Faisal_ yake sai ya manta ya fita da kud’i dan ba’a cikin watan ma suke sa ran haihuwar ba sai wata me zuwa, shine suka ki kar6anta wai sai ya kawo kud’i yace musu suyi hakuri yanzu zai je ya dawo, wai ai k’arya ne ire irensu suna zuwa suna k’arya daganan ma ba za’a sake ganinsu ba, to a tsakanin ya koma gida ya d’auko ya dawo shine ta rasu, ita kuma abin da ya taso mata da nakudar rasuwar mahaifiyarta ne da aka sanar da ita sunyi hatsari a hanyar dawowa daga ta’aziyya a _Zaria_ kafin ta fad’awa yayan mu tuni har tashin hankali yasa ta shiga wani yanani jininta ya hau sosai a kokarin fitowarta ta zame ta fad’i akan cikinta, shi kuma ya shigo ya dubata shine ya same ta a wannan yanayin, cikin tashin hankali ya dauketa zuwa asibiti mafi kusa dasu, a k’ar6eta an tsaya zancen kud’i shi kuma kafin yaje ya d’auko kudin har ta cika. (Akwai irin wannan matsalar sosai a asibitocin mu, saboda kudi sai ran dan adam ya salwanta, wai su masu kula da lafiya amma kuma abin duniyar yafi musu rayuwar dan adam, da yawan mutane za’a kai su asibiti amma saboda sakacin malaman asibiti sai su rasa rayukansu, kaddara ne mutuwar tasu amma sakacin malam asibiti ne sanadi, domin idan suka cika wanda ya kai su ba zai tuna cewa lokacin su ne ya cika ba sai dai yace malaman asibiti ne suka wulakantasu, a gaskiya hakan ba kyautawa bane malaman asibiti da tausayi aka sansu bada bakin zuciya ba, komai dai nada ya banbanta da rayuwar yanzu, domin rayuwar da akwai ababen koyi masu yawan gaske, ga tausayi ga jin kai ga maida kowa ma naka, amma wannan rayuwar kudi da abin duniya sune kawai azuciyar mutane).

+

6angaren yayarmu kuma jahilin mijinta da jahilar uwar mijinta sune silar komai, duk haihuwarta a gida takeyi kuma bai ta6a zuwa da matsala ba sai a wannan karon shima saboda yawan 6arin da tayi kafin haihuwarta na karshe shine mahaifarta yayi weak, zuwanta asibiti a 6oye likita ya tabbatar mata da cewa ba zata iya haihuwa da kanta ba, damuwan yanda zata fahimtar dasu shine a ranta, a haka har ta kai lokacin da likita yace zata koma asibiti shine tayi kokarin fahimtar da su, uwar mijin tace wato ta dade tana cin amanar su dan haka dole ne d’an ta ya sake ta, har sai da tace zata tsine mishi shine ya sake ta, bakin cikin sakinta da yayi yasa jininta ya hau ga kuma halin da take ciki ba taimako a haka harta fara nakuda da kanta kafin wani lokaci kuma ta zubar da jini sosai ga shi babu wani cigaba, a lokacin da mijin ya tsorata yake kokarin kai ta asibiti shine rai yayi halinsa. (Mutane muna sakaci sosai ta wannan fannin, idan su iyayen wancan zamanin sun kasa fahimtar amfanin zuwa asibiti kamata ya yi ku fahimtar dasu ba wai a hada harda ku mazaje ana azabtar da baiwar Allah ba, wancan zamani da wannan zamani ya banbanta, idan ma zaman kauye ne ya dace ku wayar musu da kai ko kuma ku dauki matanku ku sama musu mafita, dan a irin sakacin ku ake rasa mata da yawa gurin haihuwa, iyayen miji mata kuma kuji tsoron Allah kuyi tunanin idan ace naku yaran ne a cikin wannan yanayin ya zakuyi, mafi yawanci ba za’a ta6a cewa uban miji ne sanadin mutuwar auren dansa ba sai dai uwar miji wacce ko tana mantawa cewa nata y’ay’an ma zasu iya fuskantar hakan ne oho, idan kuma batada y’ay’a mata bata tunanin mugun halinta ya kare a kan jikokinta ko wani nata mafi kusa? Gaskiya iyaye kuna shiga hakkin matan y’ay’an ku sosai da sosai, ku abin da ba’a muku ba shi kuke musu ko kuma abin da ba zakuji dadi ba idan an muku ko anyi wa y’ay’an ku shi kuke musu, suma fa mutane ne kuma haifarsu akayi kuma iyayensu na son su ba wai rashin so ne yasa aka baku su ba, dan haka ku rinka abu tsakani da Allah, kuma idan akace abu kaza shine ya dace ku rinka kiyayewa kuna bada goyon baya dan samun zaman lafiya a cikin rayuwarku domin wasu suna da sani kawai bakar zuciyace dasu da kuma kyashi shine sila).

Gida biyu muka rarrabu wasu gidan yayarmu wasu kuma gidan yayan mu, idan kaga _Ya Kolo_ dole ka tausaya mata, ko da yake bata ta6a rashin d’a ko y’a ba shiyasa sai dai taji anayi a wani guri ko kuma a tsakanin yaran baban mu, abin bai ta6a shafar yan d’akin ta ba, baban abin ma shine mafi soyuwar d’iya a cikin y’ay’anta itace ta tafi ta barta. Sosai ta shiga tashin hankali daker aka iya tausarta tayi tawakkali tare da dangana, babban abin bakin cikin ma sakin da aka mata a wannan yanayin. Kwana uku mukayi a 6angaren yayarmu kafin mukayi canje da yan 6angaren yayan mu, a haka akayi kwana bakwai sannan muka koma gida, yaran ma kin barinsu _Ya Kolo_ tayi duk tare dasu muka dawo wai karsu koyo bakin halin kakarsu, tun a lokacin kuwa matar ta fara dana sani domin a ranar da zamu taho irin abin da ya faru tsakanin ta da yayarmu shine ya faru tsakanin yar autanta da uwar mijinta, ita kam sai da ta iso gida ta rasu a dakin mahaifiyarta, sai a lokacin matar ta fahimci zafin da _Ya Kolo_ taji a cikin ranta ga mari ga tsinka jaka, sosai tayi kuka tare da rokon _Ya Kolo_ damu kanmu gafara, ganin ita ma ta dandana yasa zukatan mu sukayi sanyi muka yafe mata, dama haka rayuwa yake kayi a maka a lokacin zaka fahimci duniyar, Allah yasa mu cika da imani.

Rasuwar da akayi shine ya jinkirta tafiyarmu, aka barshi akan sai bayan wata guda sai mu tafi dan ba’a san ko kwanaki nawa zamu iya d’auka ba, ga kuma bikin _Kisma_ da za’a fara a cikin sati me zuwa, hakan yasa muka fara hidima duk da cewa babu wani walwala sosai a tare damu saboda rashin da akayi, shiyasa ma muka shirya walima kawai muka bar duk wani bidi’a, sosai _Ya Kolo_ taji dadin karan da muka mata, _Baba K_ dai har yanzu ana kwance an sha bugun yar bariki abin yaki yiyuwa kullun yana jibge kamar kayan wanki.

Cikin ikon Allah aka fara hidimar bikin _Kisma_ duk da cewa ba wani abin mukayi ba amma komai yana tafiya dai-dai, nida wasu yayyin mu ne mukaje _Sokoto_ muka mata jere gaskiya ta samu kaya sosai mafi yawanci _Alaja_ ce ta saya mata tun muna can _Sokoton_ shiyasa bamu wani kashe kud’i ba gurin sayan wasu abubuwan. Cikin kwanaki uku muka gama komai kuma dawo cikin koshin lafiya, daga nan aka fara shagalin biki sosai yan uwa da abokan arziki sukazo, _Hajiya_ dai ta aiko sako amma bata samu zuwa ba saboda rashi da akayi musu suma na kannenta guda biyu wai gobara ya kama a 6angarensu cikin dare kuma an rasa taya abin ya faru, mun so muje musu gaisuwa amma tace mu barshi kawai ta gode muma ai akwai abubuwa da yawa a gaban mu, duk da haka dai _Inna Suwaiba_ da _Mama Qudi_ sunje musu gaisuwa, bayan dawowan sune na fahimci akwai magana a bakin _Inna Suwaiba_ sai dare naje na sameta.

Bayan sallar ishai na sameta a d’akin ta, yaran duk sunyi barci sunyi wani kane kane a gadon kamar d’akinsu, gaisheta nayi sannan na tambaye ta ko tafiya, ni kaina abin yana min banbara kwai domin ba abune dana sabayi ba, na saba idan na kalli idon mutum zan karanci komai amma yanzu dole sai na nemi jin abin da yake faruwa, murmushi nayi tunowa da mijina domin shine silar wargaza komai na cikin rayuwata, kallona _Inna Suwaiba_ tayi sannan tace min yau sunje gidan me _A&S_ dama na sani ai tunda gidansu _Hajiya_ kenan, tace abin al’ajabi yaran gidan duk suna yanayi da juna, babban abin mamakin shine kamar dangin yan ukuna, domin suna matukar kama da yan gidan, sai a lokacin na tuna kamannin _Hajiya_ tabbas da ita suke kama na dade ina tunanin a ina na san irin fuskarsu bayan na mahaifinsu ashe itace, maganar _Inna Suwaiba_ ne ya dawo da hankalina gurinta “inaga kila suna da dangantaka da yan gidan, dan ganin _Hajiya_ shine ya kara tabbatar min da cewa yarannan jininsu ne, amma dai mu cigaba da addua lokaci na zuwa komai zai bayyana kansa” ta fad’a tana kara kallon yaran, nima ban musa ba kila suna da dangantaka ta wani gurin domin akwai kama sosai tsakaninsu da yaran _Hajiya_.

A yau aka d’aura auren _Kisma_ akan sadaki dubu hamsin, sai dai fatan Allah ya basu zaman lafiya ya kade sharrin dake cikinta, ya kuma basu zuria nagari dayyiba. Tunda aka saka ranarsu da _Dr_ sai yau naga tayi murmushin da ya kai zuciyarta, tabbas na san _Harun_ ta tuna kuma tsoron kar abin da ya faru ya sake aukuwa yasa duk jikinta yayi sanyi, kallonta nayi nace yau dai sai ayi dariya da kyau za’a tafi a bar _Baba K_ tunda an riga an daura tafiya ya tabbata kuwa, kukan da naga tanayi ne yasa na bar tsokalar ta na shiga rarrashinta, mun dade a zaune ina rarrashinta tare da bata shawarwari dai-dai gwargwado kafin yayarmu ta shigo dan kaita gurin iyaye saboda tafiyan wuri zasuyi. Karfe Hud’u motocinsu ya bar kofar gidan mu, sai a lokacin kukan nawa yazo, ban ma dauki tafiyar nata a gaske ba sai da naga motocinsu na barin kofar gidan, a zaman da mukayi mun shaku sosai da junan mu, tabbas sabo turken wawa ga shi yau aure ya raba mu, sosai naci kuka na gode Allah sannan na koma ajiyar zuciya tare da mata fatan alkairi a cikin rayuwar da zata fara.

________________________

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]