[Advertisements⬇️]

DEEMAH CHAPTER 8 BY ZAHRATEEY - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

DEEMAH CHAPTER 8 BY ZAHRATEEY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Cikin ikon Allah muka gama jarabawar mu lafiya, yanzu ma shirye shiryen komawa _Bauchi_ mukeyi, _Alaja_ kuma tana shirin tafiya _Lagos_, _Hindatu_ kuma an riga an sallame ta, a ranar da zamu tafi itama zata wuce garinsu.

+

Sati guda muka kara a cikin garin _Sokoto_ kafin jirgin mu ya d’aga zuwa _Bauchi_, _Alaja_ ce ta biya mana tace muma mu d’ana, sosai munaji dadin hakan kuma muka mata godiya. Tunda muka shiga jirgin yaran sukayi tsit cike da tsoro dama daker suka shiga dan kuka sukayi tayi wai ba zasu shiga ba. Shuru nayi ina tunanin zuwan mu wanda ya kasance kowa na cikin kunci, sai ga shi yau zamu koma cikin nasara da farin ciki.

Ban san cewa nayi barci ba sai da _Kisma_ ta tashe ni tana cewa mun iso, kallon ko ina nayi naga mutane sai fita sukeyi, nima cikin sauri na d’auki jakata na rataya sannan nabi bayan _Kisma_. Ina zuwa na samu har yayan mu ya iso d’aukarmu da motan daya saya kwanan nan, sienna ce me kyau kalar ruwan toka, cike da murna muka zuba kayan mu a bayan motar kafin muka shiga ciki ya tuka zuwa gida.

Komai lafiya muka samu a cikin gidan, su _Ya Kolo_ sunyi kokari gida ne me kyau suka saya dai-dai talaka, d’akunan zaure na yara mazan ne sai kuma cikin gidan kitchen dinsu a waje haka band’aki shima a waje sai babban falo da d’akuna biyar a jere da juna, d’akin _Mama Qudi_ muka ajiye kayan mu, bayan an gama gaisuwa anci abinci shine _Inna Suwaiba_ tace zata wuce, da sauri su _Ya Kolo_ suka ce babu inda zata ko da ace ba’a mai da auren su da _Baba K_ ba, ba zasu bari ta tafi ba balle kuma an riga da an maida auren, sosai nida _Kisma_ mukaji dadin hakan sa6anin _Inna Suwaiba_ data 6ata rai tace zata zauna ne dan su amma ba sai dan ita d’in tana da auren ba dan bata san me zata zauna yi tare da wanda bai san daraja da kimar iyalansa ba, sosai tayi masifa san ranta ta gaggayawa _Baba K_ maganganu masu zafi a matsayinta na yar uwarsa ba wai a matarsa ba, mu dai namu ido, bayan komai ya kara suka shiga bada hakuri har da kuka shi da _Inna Abu_ ni dai kawai ina jinsu ne domin nasan tabbas idan da zasu sake samun guri tsaf zasu koma gidan jiya…

_Kisma_ d’akin _Ya Kolo_ ta maida kayanta kamar yadda ta umurceta, sai yaran suka zauna gurin _Inna Suwaiba_ ni kuma ina d’akin _Mama Qudi_ _Inna Abu_ kuma tana tare da _Goggo Fulera_ sai d’aki guda na _Baba K_, wai su baban mu anji duniya duk ya lalace ya rame ya zama gwanin ban tausayi ga wani gashi daya tara a fuska kamar tsohon mahaukaci, idan da ace _Baba K_ ba irin mutanen dake d’aukan wanka suna buga gayu bane da tuni anyi ram da shi zuwa gidan mahaukata a yadda yake dinnan, ni tunda muka zo kawai sai kallonsa nakeyi, ni dai dama na yafe musu tun tuni ban rikesu a zuciya ba, _Kisma_ irin mutanen dake rike mutum a zuciya ko da ba’a ita akayi wa laifi ba matukar ya shafi wani nata, har zuwa yanzu ina kokarin ganin cewa na cire mata wannan akidar domin ba abu ne me kyau ba amma abin yaki yuyuwa, ba laifi ta rage zafin zuciya amma fannin riko sai abin da ya yi gaba dan ko gaishe da _Baba K_ na lura batayi ba balle su _Inna Abu_.

STORY CONTINUES BELOW

Washe gari da safe yan uwan mu sukayi ta zuwa da yan cikin _Bauchi_ da yan _Kari_ sosai mukaji dadin ganinsu masu min kallon banzan ma duk sun rusuna kowa sai haba-haba yakeyi da yarana, abin kuwa yamin dadi dan babu abin da nake so kamar a nuna so da kulawa ga yarana, a haka har suka watse bayan sallar la’asar, muma mukayi musu alkawarin zuwa idan mun huta, na lura yanzu cewa yawancin abubuwan cikin rayuwata sun sauya, musanman kalle-kallen da nakeyi sai yanzu na k’ara yarda cewa akwai aikin aljanu a tare dani, dama kanin _Baba K_ yace zamuje a dubani a cikin satin nan domin akwai abubuwa da yawa dake damun rayuwata, nima kaina yanzu ina son zuwa dan in san ko kawai shafar aljannun ne ko kuma da hannun wani nawa a cikin durkushewar rayuwata.

Bayan kwana uku da zuwan mu kannen _Baba K_ biyu suka zo muka tafi _Kari_ domin ganawa da wani malami, ko da muka je mun samu ba kowa sai almajiransa, bayan yasa anyi mana shinfidin tabarma a cikin gidansa sai muka shiga, gaisuwa sukayi da kawunai na, daga nan nima na gaishe shi, kallona yayi yace “Tabbas akwai mutanen 6oye a tare da ita sai dai kuma irin wad’annan aljannun akwai malamai na musanman masu iyawa dasu, zan baku adireshin wani malamina a wani karamin kauyen dake hanyar _Jos_ da izinin Allah idan har kuka samu zuwa gurinsa komai zai zo karshe. Bayanai yayi musu da dama akan aljanu iri daban daban wanda ko wani irin malami yake ji da irinsu da kuma irin wanda sai malamai na musanman sune suke iya kawar dasu da izinin ubangiji, mun dad’e sosai sannan ya bamu adireshin muka tafi, ni motar _Bauchi_ na shiga su kuma suka koma gida akan sati me zuwa zasu zo sai mu shirya mu tafi, sosai na musu godiya sannan na shiga motar.

Cikin lokaci kad’an muka shiga _Bauchi_ daga tasha na hau napep zuwa gida duk da cewa sai da na kira _Kisma_ aka sakemin kwatance dan gidan akwai lunguna da yawa kuma gidajen kusan gini d’aya ne, ina zuwa nayi wanka nayi salla sannan na musu bayanin duk abin da ake ciki, addua sukayi akan Allah yasa a dace idan munje chan din. Shuru gidan banji hayaniyar yaran ba sai chan gasu sun dawo tare da _Khalil_ wai sunje sayan cakuleti.

_________________________

_Asalin su_

_Malam Madu Mahmud_ da _Malam Ilu Mahmud_  yan asalin garin _Bauchi_ ne kabilar _Gerawa_ tun asalin kaka da kakanni gidansu an sansu da kasuwanci, kuma sosai suke samu a kan hakan domin Allah ya albarkaci kasuwancin nasu. _Malam Madu_ da d’an uwansa _Malam Ilu_ sun kasance tagwaye ne haka zalika matansu yan uwa juna ne kuma tagwaye wanda suke yan wa da kani, babansu _Malam Madu_ shine babba sai baban matayen su shine karami kuma sun kasance su kad’ai Allah ya azurta iya yensu da samu. Matar _Malam Madu_  sunanta _Khadija_ suna kiranta da _Inna Dija_, na  _Malam Ilu_ kuma _Zuwaira_ ana kiranta _Inna Zuwai_.

_Malam Madu_ Allah ya azurtashi da samun yara biyu _Muhammad Sudais_ da kuma _Naja’atu_ sai _Malam Ilu_ Allah ya azurtashi da yara uku _Sadis, Samir_ da _Salman_. Sun taso cikin so da kaunar juna, ko me suke so iyayen su suna iya bakin kokarinsu gurin sama musu shi, duk sunyi karatun bako daga matakin farko zuwa jami’a amma banda Naja’atu wacce a iya karamar secondary ta tsaya sannan aka mata aure, ta auri wani dan kabilar shuwa arab kuma  makaniki da matarsa d’aya _Rahima_ wacce ta rasu gurin haihuwa bayan auren da watanni biyar, sosai _Naja’atu_ tayi kuka saboda shakuwar da sukayi da matar dan akwaita da saukin kai da son jama’a, shiyasa duk wani na kusa dana nesa sunji mutuwarta sosai.

Cikin ikon Allah, Allah ya bud’a musu har suka sayi gidan kansu suka koma inda anan Naja’atu ta haifi diyarta mace ta had’a da yaran marigayiya su uku maza biyu da mace d’aya duk ta rikesu. Bayan haihuwarta akayi bikin Yayyinta biyu da _Sudais_ da _Sadis_. Bayan watanni tara matar _Sadis_ ta haifa d’iyarta mace ita kuma matar _Sudais_ ko 6atan wata ba tayi ba, a haka har matar _Sadis_ ta sake haihuwan d’iya mace a lokacin kuma _Samir_ shima yayi aure bayan auren da wata biyu _Sudais_ da _Sadis_ suka kara aure, matar _Sudais_ yar _Niger_ banufiya ita kuma matar _Sadis_ yar _Nasarawa_ kabilar gwandarawa, cikin shekaran matar _Samir_ ta haihu bai dade ba amare suma suka haihu duk y’ay’a mata, bayan shekaru biyu _Salman_ shima yayi aure inda aka had’a dana yayansa _Samir_ shima ya kara mata yar _Kogi_ ibira, daganan akayi ta gasar haihuwa amma banda _Lami_ da batada ko d’aya da kuma _Maryam_ da take da _Aisha_, bayan shekara shida _Salman_ shima ya kara aure ya auri yar _Kano_ bahaushiya, a lokacin ne aka haifi _Sufyan_ sai kannensa hudu a d’akin _Anty amarya_ daganan babu wacce ta sake haihuwa.Bayan auren _Samir_ iyayensu maza suka rasu, bayan an raba gado shine suka yanke shawaran sayan fili babba sukayi gini me kyau da tsari wanda kowa aka mishi side dinsa daban, _Sadis_ likitane yana aiki a wani babban asibiti dake cikin garin _Bauchi_ shi kuma _Samir_ Babban lauya ne me zaman kansa, _Salman_ kuma manager ne a wani banki sa6anin _Sudais_ daya cigaba da harkan kasuwanci kuma sosai harkan ya kar6eshi har ya gina masana’antu da gurin wasan yara. Cikin ikon Allah arzikinsa ya dinga ha6aka a lokacin ne aka haifi _Sufyan_.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Cikin shekaru goma suka tara yara mata guda ishirin da biyar sai d’a namiji d’aya, a 6angaren _Naja’atu_ kuma ta haifi yara uku bayan na farkon da yan biyu mata da kuma namiji d’aya, bayan haka bata sake haihuwa ba, a lokacin mijinta ya kara aure, ya aro babarbariya, tunda tazo ko 6atan wata bata ta6ayi ba sai bayan kusan shekaru bakwai a sannan ne ta haifi d’iya mace me suna _Hauwa Jidda_ daga nan kuma kofa ya bude mata ta haifi yara hud’u mata maza biyu, a haihuwarta na karshe Allah ya kar6i ranta sosai sukayi jimamin rashinta ko ba komai mutum rahama ne ko da zaman babu dadi, daganan yaran suka koma hannun _Hajy Naja_ inda ta had’a duka da yaranta ta rike cikin so da kauna ba tare da nuna banbanci ba, bayan rasuwan amarya suka tare a sabon gidansu dake GRA, dama Allah ya yi baza’a shiga da Amarya ba.

Tunda aka haifi _Sufyan_ sai dai a d’aga a kwantar, a lokacin daya dace ya fara zama sam-sam baya zama sai kwanciya, haka zalika lokacin daya dace ya fara rarrafe shi ma baya yi, har ya kai shekaru biyu baya zama baya tafiya sai dai kwanciya, tun abin baya damun _Hajja_ har yazo ya fara damunta, dai-dai ku ne a gidan abin bai yi musu dadi ba kuma suma duk hankalinsu a tashe amma sauran duk sunji dadin hakan duk da cewa ba’a bayyane suke nunawa ba. Mazan gidan kuwa duk hankalinsu a tashe yake, sam-sam babu hassada ko kyashi a zuqatansu yadda suka taso suna son junansu hakan yake har zuwa tsufansu, basu ta6a kullatan juna akan wani abin ba, amma matansu mutane hudu ne kachal suke son _Hajja_ da d’anta sauran basu ki ace duk su mutu ba.
Ganin yanda abin nashi yake kara cigaba yasa suka kai shi asibiti, an duba ko ina amma babu alamun wani nak’asa a tare da shi, hakan tasa suka koma na gargajiya anan ne kuma aka gane cewa shafar aljanu ne, sosai aka sha wahala a kansa kafin ya samu ya warke, a lokacin yana da shekaru takwas a duniya kuma ko makaranta bai fara ba, sai dai iya wanda  _Anty Aisha_ take koya mishi ya rike, yana shekara takwas aka sa shi a makaranta inda ya fara daga aji d’aya na firanari, abu d’aya ne bai iya ba wato fannin lissafi (maths) a haka har ya gama firamari, ya shiga secondary shima duk dai d’aya ya kasa iya lissafi, har ya gama karamar sakandiri ya shiga babba, yana aji biyu a babban sakandiri ya had’u da _Jidda_ lokacin tana aji daya ita kuma, da abota suka fara kafin soyayya, sosai shakuwa ya shiga tsakanin su. wani zuwa da ya yi gidan _Umma_ wato _Hajy Naja_ shine ya san cewa ashe yar gidan ce, sosai yaji dadin hakan kuma ya yi mamakin yadda akayi bai ta6a sanin a gidan take ba, ko da ya tambaye ta shine take ce mishi ai ita tana gidan yayan mahaifinta ne tun bayan rasuwar mahaifiyarta sai matarsa tace tana so a bata ita.
Ya gama secondary yana da shekaru goma sha tara a lokacin kuma _Jidda_ tana da shekaru goma sha hudu tana aji na biyu a secondary. Duk da cewa ya tafi ya barta amma yana yawan zuwa gidan yayan babanta, suma kasancewar sun san ko shi waye shiyasa basu damu ba, ko yaushe yana mak’ale da gidan kamar zai tare achan baki daya. A jamiar Abuja yayi karatunsa, hakan yasa itama ta nace sai da aka kaita chan din. yana ajin karshe a lokacin ita kuma tana aji na hud’u kuma dukansu karatun likitanci sukayi a fannin tiyata domin san su zama kwararrun (surgeon).
Bayan ya gama ya dawo aka fara maganar aurensu, a lokacin yana da shekaru ishirin da shida ita kuma tana da shekaru ishirin da d’aya, sosai iyayensu sukayi farin ciki, yan bakin ciki ma sun nuna farin ciki a fili amma zuciyarsu naci da wuta domin sun so ace a cikin yaransu ya za6a, _Lami_ wato _Mama_ tafi kowa bakin cikin wannan lamari dan bata da burin barinsa ya yi aure, sai dai zata dakata da shirinta har sai ya yi auren tukunna, a lokacin akwai d’iyar y’ar uwarta wacce ta dade tana son shi amma dan tsanar da _Mama_ ta mishi yasa taki amincewa, _Hanifa_ ta taso a gurin _Mama_ tun tana karama kuma duk wani halin banza na iyayenta babu wanda bata gado ba, sai dai nata a duhu yake babu wanda ya san aihinin abin da yake ranta.
Kafin bikinsu _Daddy_ ya ware mishi part guda ya mishi gini irin nasu, tun tasowar yaron nasa ya fahimci cewa yayi gado a gurin su domin bai ta6a sawa ransa auren mace d’aya ba, ya taso da son auren mata biyu ko ma fiye da hakan, shiyasa da _Daddy_ ya tashi mishi gini sai ya mishi part uku shima. Sosai aka shirya wa bikin kasancewarsa namiji d’aya tilo a cikin ahalinsu, bayan hutun zango na biyu wanda ya yi dai-dai da lokacin auren nasu ta dawo gida.
Sosai akayi shagalin biki na musaman, bayan aure amarya ta tare a 6angarenta na cikin gidan kafin ta koma makaranta. Cikin ikon Allah suke zamansu lafiye cike da so da kaunar juna, wata uku tayi sannan ta koma makaranta a lokacin tana da karamin ciki na wata guda. A cikin hutun zango na biyu na wannan sabon ajin ta haihu inda ta samu yara biyu maza masu kama da ita, sai dai kafin murnan ya yi nisa ya koma ciki domin yaran sun koma, _Mama_ kuma itace silar hakan domin had’a baki tayi da wata malamar asibiti aka d’ura musu wani magani wanda yafi karfin jininsu, sosai akayi jimami tare da tawakkali. A cikin shekara na biyu da aurensu ta sake haihuwar yaranta na biyu suma yan biyu maza masu kama da mahaifin su, abin da ya faru wancan lokacin shi ya kuma faruwa amma sai da sukayi kwana biyu kafin suka koma, sosai _Jidda_ ta shiga tashin hankali har hakan ya kusa affecting karatunta domin saura watanni kad’an ta kammala ta zama kwararriyar likita a fannin tiyata. Da rokon Allah aka samu ta dawo dai-dai.
A lokacin da akayi bikin yaye d’alibai _Sufyan_ ya shammace ta ta hanyar bud’e wani babban asibiti a garin _Bauchi_ da sunanta, sosai tayi farin ciki harda kukanta, duk da cewa tare suke aiki a cikin asibitin amma ya kasance asibitinta ne halak malak, sosai suke burge mutane saboda yanayin soyayyarsu da hazakarsu ta fannin aikinsu, komai tare suke yi sai dai idan wani abin ya taso na rashin lafiya ga waninsu, a cikin shekaranne ta haifi _Abdulhamid_ me sunan mahaifinta suna kiransa da _Anas_, a lokacin an san dai da haihuwarta amma ba’a san cewa yaron yana raye ko baya raye ba, kasancewar ta san yaron ta yana raye sai bata wani damu ba _Sufyan_ ne kawai ya damu har ya zo ya wartsake, shine ta nemi daya kara auren da yace zai karan amma yace mata ba yanzu ba, bayan shekaru biyu ta haifi _Muhammad_ da _Iliyas_ masu sunan kakannin _Sufyan_ ana kiransu da _Shureim_ da _Muslim_ suma kuma a lokacin ba wanda ya san ta haifesu da rai dan mijin nata ya tafi Abuja wani aiki sai abin yayi sauki aka kai su gurin _Umma_ aka had’a da _Anas_. yayyinta da kannenta ne suka san da yaran bayan su sai ita da _Anty Aisha_, _Umma_ da kuma babanta ko _Hajja_ batasan dasu ba, kuma duk wani abin da akeyi a gidan 6angaren kakansu ake kaisu a ajiyesu.
Haihuwarta na karshe ne kawai suka barta ta huta saboda haihuwar mata da tayi, ita kanta sai da tayi ajiyar zuciya a lokacin data ga yaran, sosai tausayinta ya kama _Umma_ da _Anty Aisha_ domin su kad’ai suka fahimci kwanciyar hankalin da tayi ganin yara mata a gabanta, ko da _Mama_ tazo ta ga yaran sosai tayi farin ciki domin dama yara maza ne bata son a sake haifa a cikin zuriar mijinta, _Sufyan_ har da azumi domin nuna godiyarsa ga Allah madaukakin sarki, a lokacin kuma _Jidda_ taji ta karaya taji tana son ta nuna mishi sauran y’ay’ansa sai dai kuma abin da zai iya biyo baya take tsaro shiyasa tayi gum da bakinta tana kukan zuciya.
Sosai akayi shagalin suna aka kashe naira sai dai ba’ayi yanda abinci zasu wulakanta ba, abubuwa aka kai gidan marayu aka raba domin nuna farin ciki da godiya ga wannan kyauta da aka samu, duk da cewa duk yan gidan kowa na haihuwar y’ay’a maza da mata amma na _Sufyan_ ya banbanta domin yaran basa zama shiyasa yan matan suka sha gata daga 6angarori daban-daban.
Bayan shekara guda aka sake shirya mishi wani abin inda gabad’aya idanunsa suka daina aiki, haka bakinsa ya daina aiki daga kunnensa sai hanci da yake shankar numfashi amma kafarsa ma duk ya kasa takawa daga zama sai kwanciya, sosai _Jidda_ ta sha wahala gurin jinyarsa ga yara ga ubansu, duk sai da ta rame ta zama abin tausayi, aiki ma dama ta daina zuwa abokansa biyu da suke aiki a gurin sune suke rike da asibitin cikin kulawa da rikon amana. Duk wani asibiti na gida dana waje babu abin da suka gano a tare dashi a haka suka hakura aka koma na gargajiya inda aka fahimci cewa aljanu ne suka sake shafarsa, kusan shekara uku yayi a kwance kafin Allah ya bashi lafiya, sosai _Jidda_ ta sha wahalarsa shiyasa duk duniya bayan mahaifiyarsa itace mace ta biyu da yake matukar so da kauna…
________________________

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]