[Advertisements⬇️]

DEEMAH CHAPTER 16 BY ZAHRATEEY - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

DEEMAH CHAPTER 16 BY ZAHRATEEY

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

_Mamitaaa_!!! “Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ya hayyu ya qayyum” kallon hagu da dama nayi inaso in gano inda nake, yar budurwan dake kusa dani na kalla ina mamakin wai duk wannan ihun da nayi bataji ba? Kaina na rike ina son tuno da yadda akayi na tsinci kaina a wannan gidan dan ban ga alamun fuskar wacce na sani a tare da yarinyar ba, d’akin na bi da kallo ko ina tsaf tsaf ne babu wani tarkace da yawa, zama nayi ina kallonta can kuma na tashi na fita daga d’akin. Ko ina shuru babu motsin mutane sai kukan karnuka da kuma tsuntsaye jefi jefi, zama nayi a wani dakali “mun baro gida nida kawunai na, mun shiga mota nayi barci na farka naga wasu maza biyu a zagaye dani mun fito na fahimci cewa 6arayi ne, sun sanya tsofi a mota dan amayar dasu _Bauchi_ mu kuma suka tafi damu daganan kuma na manta duk wani abin da ya faru ” wayyo Allah na ni kam na shiga uku daga wannan bala’in sai wancan, nan kuma ina ne a ina nake ya ilahi?” Rike kaina nayi saboda ciwon da yakemin, so nake sai na tuno da abubuwan da suka faru bayan mun bar garin _Abuja_ amma na kasa tuna komai, tashi nayi na koma d’akin na kwanta daker barci ya yi awun gaba dani.

Washe gari da safe na tashi da wani irin ciwon kai sai da aka dangana da asibiti inda sukayi min alluran barci na kwanaki uku wai saboda in samu saukin tunanin daya addabi kwakwalwata. Bayan kwanaki uku na farka, a hankali nake bude ido na da sukayi min nauyi, sosai naji dadin kan nawa dan ya rage min ciwo, wannan yarinyar na gani wacce muka kwana a daki daya duk hankalinta a tashe, tana juyowa muka had’a ido “Alhamdulillah _Anty_ kin tashi, wallahi har kin ban tsoro! wannan wani irin ciwo ne ya kamaki a dare d’aya, Amma dai yanzu kinji sauki ko? Bari inje in kira likita yazo ya dubaki” bata jira nace komai ba ta fita cike da zumud’i, ni duk mamaki ya kasheni a ina na zama _Antynta_? Ikon Allah kenan, murmushi nayi tunowa da yar uwata _Mamita_ lailai ina matukar son yar uwata tunda da ita na farka a raina kuma sunanta na fara ambata, itama _Anty_ take cemin kuma ita kad’ai ke kirana da _Anty_ ba tare data had’a da sunana ba sai kuma wannan baiwar Allahn da nagani.

Ina kwance suka dawo tare da likita, dubani ya yi tare da yimin tambayoyi ina amsa mishi, sai da ya gama sannan yace ta biyo shi office din shi, bayan kamar mintina goma ta dawo rike da wani fallen takarda guda biyu, “d’aya na sallama be d’aya na magungunan da za’a saya, ki jirani bari inje in sayo sai in taro mana me adaidaita” har na fara gyangyad’i naji bude kofa, da ita nayi tozali ta shigo rike da ledan magungunan, had’a mana kayan dake gurin tayi sannan ta taimakamin na sauka daga gadon dan har yanzu ina jin jiri, a hankali muke takawa har zuwa in da me adaidaitan yake, sai da na fara shiga kafin ta ajiye kayan ta can baya sannan ta shiga ita ma, _Anguwar Basa_ tace mishi, munyi tafiya me nisa kafin muka isa gidan bayan mun sauka ta ba shi kudinshi sannan muka shiga gida. A bakin famfo muka taras da wata mata tana zaune “sannunku da zuwa, wai yanzu nake son in gama kwashe abincin sai muje nida _Asiya_ mu duba jikin nata, sannu _Asma’u_ ya karfin jikin naki yanzu? Allah ya baki lafiya” ta fad’a tana gyara d’aurin zaninta ” _Ummulu_ maza kai mata ruwan dumi ta d’an watsa ni zan shiga gidan _Saude_ d’iyarta ta haihu d’an ba rai” da to kawai yarinyar ta bita sannan ta shiga kitchen ta d’auko bokiti ta juye ruwan ni kuma na shiga d’akin da muka kwana randa na dawo cikin tunani na, na lura na manta komai ne a baya yanzu kuma na tuna amma kuma na manta abubuwan da suka faru a rayuwar da nayi a wannan gidan da nake, bayan na cire kaya na d’auro zani da hijabi sannan na fito na shiga band’akin tare da yiwa _Ummulu_ godiya.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan na fito na saka kayan dana gani a saman katifan sannan na zauna ina tunanin rayuwa ” _Anty_ kici abincin ki sha magani kuma kinga _Likita_ yace ki rage yawan damuwa dan shine yasa miki ciwon kai me tsanani har fa jininki sai da ya hau” banyi musu ba na bude abincin _Shinkafa_ da _Wake_ da _Mai_ da _Yaji_ ne yasa _Salad_ da _Tumatir_. Sosai naci abincin dan _Yajin_ yamin dadi sosai, ina gamawa ta bani magani na sha sannan ta fita da kwanon. Bata dad’e ba ta dawo ta zauna kusa dani tana cewa ” _Anty_ ansa bikin mu da _Ya Yaro_ sati biyu idan na gama jarabawa, bikin _Asiya_ kuma a dakatar sai ta haihu za’ayi” kallonta nayi zanyi magana sai ga wata tsohuwa tsohuwa ta shigo “ke ina kika ajiyemin abinci na? Ai kin iya gayyar sod’i gayyar na ayya kin kawo mata nata amma ni me juna biyu kin barni da yunwa ko _Ummulu_ ya yi kyau ” tana gama fad’a ta juya ta wuce kamar zata tashi sama, _Ummulu_ ta mara mata baya ni kuma na kwanta dan naji kaina ya fara ciwo kad’an kad’an.

Ban tashi ba sai bayan magriba, ban damu ba saboda ina fashin salla, wanka na sakeyi na saka kaya sannan na fita waje inda suke zaune, ina zama wani mutumi ya shigo rike da leda a hannun sa, na gane shi dan tare dashi aka kaini asibiti, yaron dake biye dashi a baya ne ban gane ba, bayan ya zauna ya tambayi lafiyata na amsa mishi sannan nace “kuyi hakuri dan Allah amma ni duk ban gane ku ba” zaro ido _Ummulu_ tayi duk jikinta ya yi sanyi tace “har dani kenan _Anty_ nima kin manta dani?” Ta tambaya kamar zatayi kuka, tausayi ta bani nima banso hakan ba amma yaya zanyi na kasa tuna komai ” _Baba_ tunawan da nake kokarin yin shine yake sani ciwon kai me tsanani shiyasa na hakura kawai amma zanso inji yadda akayi nazo nan kuma kafin nan nima zan sanar daku koni wacece” labarina na basu harda auren dake kaina da kuma yarana dana haifa babu ragi ba k’ari sai da na fad’a musu komai da kuma iya abin da zan iya tunawa shine fita daga garin _Abuja_ da mukayi daganan na manta komai, mamaki ne ya kamasu wai ina da aure harda yara na, sosai sukayi ta al’ajabin irin rayuwar da nayi a baya sannan _Ummulu_ ta fara bani labarin zuwana gidan su da rayuwar da nayi a gidan, har dasu _Alhaji me gwanjo_ da abinci da muke kaiwa _Yaro_ a 6oye duk sai da ta fad’a sai a lokacin _Malam_ ya san cewa ga irin rayuwar da _Yaro_ yakeyi a gidan, sosai nima rayuwar da nayi a gidan su ya bani mamaki da al’ajabi kuma na kasa tuno da komai, ranar hira mukayi sosai kafin mukaci abinci muka kwanta, _Mama_ taji haushin _Ummulu_ data fad’awa _Malam_ abin da takeyi wa _Yaro_ shi kuma _Yaro_ tunanin cewa ashe ni matar aure ce shine ya addabe shi karshe dai ya sawa zuciyarsa salama ya kama yar uwarsa hannun bibbiyu tunda ya ga babu damar samuna.

_________________________

Sosai _Baba K_ ya tsure ya rasa madafa, kallonta kawai yakeyi yana tuna _Lami_ “wallahi uwarki ta cuceni ta cuci rayuwata, ashe da aurenta ta bari mukayi tarayya da juna? Sai bayan da cikin ki ya bayyana shine take sanar dani cewa ai da auren ta amma kuma bazata ta6a zubarwa ba dole ne ta haifeki amma ba a gidan ba” ya fad’a yana share zufa, _Dr Nasir_ ne yace ya rabawa yara abincin sai su tafi shi zai biyashi kudin idan yaso sai su samu guri me sirri suyi magana a can. Ba tare da musu ba ya amince duk jikinsa na rawa ya rabar da abincin kafin suka taya shi kwashe kayan, bayan sun isa parking space suka saka kayan a booth sannan suka shiga mota suka wuce gidan _Dr Nasir_.

Bayan sun isa gidan suka shiga daga ciki, a falon suka zauna _Baba K_ duk ya rasa meke mishi dadi shikam son kudi ya janyo mishi bala’i ya kai shi ya baro shi, wannan abin kunyan dame ya yi kama ya ilahi “Yarinya me kike nema a gurina? Kin ganni nan bani da ko sisi nema nake kokarin yi domin in rufawa kaina asiri, ki rufa min asiri karki tonamin, ki kama gabanki ki cigaba da zama da uwarki, tabbas mun aikata kuskure dagani har _Lami_ amma ta fini laifi domin da aurenta ta aikata wannan danyen aikin” kallon shi _Hanifa_ takeyi tana mamakin me _Mama_ ta gani ajikin shi da har ya burgeta.

Ruwan da _Dr Nasir_ ya ajiye musu ne ta dauka ta kur6a sannan tace “ai aikin gama ya riga daya gama tunda har aka haifeni, dama burina in san waye mahaifina in kuma san waye ainihin mahaifiyata tunda sun 6oyemin amma tunda yau naji sunan mahaifiya ta a bakin ka shikenan na yarda na kuma fahimci ko wacece mahaifiyata a tsakanin mata biyun, kai kuma tunda na ganka na tabbatar da waye kai din shikenan banda abin da zanyi da kai sai dai idan bukatar hakan ta taso, da ace kana da wani abin tunkaho ne dana zamu gurin zama amma tunda fatara kakeyi babu gurin zama a gidan ka domin ban taso a talauci ba, ba kuma zan zauna a cikin talaucin ba” ajiyar zuciya ya yi da yaji cewa kawai sanin shi take son yi ba wai wani abin ba.

“Ina son sanin wacece _Mamana_ a gurinka, a ina kuka hadu har akayi cikina?” Kallonta ya yi sai zufa yakeyi kamar an sa shi a bakin wuta, alhali fanka da ac duk suna aiki a lokaci guda ” _Lami_ budurwata ce tun kafin inyi auren fari, kaddaran aurenta da mijinta shine ya raba mu, bayan wani lokaci me tsawo muka sake haduwa da ita, nayi mamakin irin daular da take ciki sai dai banyi tunanin tambayarta ba, ganin yanayina yasa ta bani adireshinta tacemin in sameta a gidanta dake kusa da _Jifatu_ banyi musu ba nace mata to zanzo, a lokacin matana hudu cif, kuma matata ta karshe haihuwarta na fari kenan karayar arziki ya sameni, bayan naje gurinta ta bani kud’ad’e masu yawa tace inyi amfani dasu amma sai na biya mata bukata zata dankamin kudaden, son kudi da sharrin shaidan yasa na amince tunda har a lokacin ina sonta kuma babu damar auren ta domin babu wacce zan iya saka a cikin mata na ko wacce tana da yara sannan bana bukatan ace saki ne ya raba sai dai mutuwa dan ba zan so matata ta fita ta auri wani ba, bayan komai ya faru a tsakanin mu ta bani kudin tayi min godiya na tafi, daganan bamu sake haduwa ba sai lokacin da cikin ki ya bayyana a jikinta kuma sanin kanta ne cewa bana mijinta bane, bayan ta fadamin na bata shawaran zubarwa shine tace ba zata zubar ba ni kuma nace babu ruwana karta sake nuna ta sanni ko da a hanya muka had’u, 6acin raina ma da ta fadamin cewa ashe da aurenta mukayi wannan aika aikan, dalilin cikin ki yasa tayi wani tafiyar karya ita da kanwarta zuwa kasar waje a lokacin cikin nata nada wata biyar kasancewarta mace me jiki sai yabi jikin ta babu wanda ya san tana da ciki, bayan zuwan su data haihu shine ta sanar dani cewa ta haihu amma baki zo da rai ba, sosai nayi farin ciki domin ni bana fatan haihuwar dan gaba da fatiya kuma ma da matar da take da aure a kanta”.

Kallonsa tayi cikin takaici “Ina so ka zama cikin shiri domin a ko da yaushe zan iya nemanka, sanin kan ka ne nasan gidan ka na kuma san gurin sana’arka, aurena zai iya zuwa cikin lokaci k’ank’ani dan haka ka zama cikin shiri dan akwai abin da nake shiryawa. Sannan kuma zan baka numbern _Mama_ ina son ka neme ta a waya ka tambayeta ajiyarka dake gurinta, kar kace min a’a domin idan ka fad’a kune a ruwa dan asirinku ne zai tonu, ni abin kunya gaba na bashi ba baya ba dan haka ko a k’olar rigata, ina son ka kirata yau da yamma gurin karfe biyar lokacin ina gida, idan kuma baka kira ba na riga dana fad’a maka abin da zan iya yi, na san dai yan gidanka basu san dani amatsayin yarka ba, idan kana son duk su sani sai ka tsallake magana ta” ta fad’a tare da d’aukan jakarta da mayafinta, jakar ta bud’e ta ciro yan dubu-dubu da wani fefa me d’auke da lambar _Mama_ ta watsa mishi sannan tayi gaba tana cewa _Dr Nasir_ sai sunyi waya.

Bayan tafiyarta ya d’auki kudin yasa a aljuhu tare da fefan sannan yace wa _Dr Nasir_ zai tafi “ka jira in sauke ka saboda nima fita zanyi” bayan ya canjo kaya ya d’auko key din motarsa sannan suka wuce “Kar kayi gigin kin yin abin da tace kayi tunanin ko barazana ne, tabbas ba barazana bane domin _Hanifa_ ta wuce tunaninka zata iya aikata komai, kamar yadda ta fad’a maka abin kunya gaba ta bashi ba baya ba haka abin yake, tsatson ta tun daga farko bame kyau bane, kuma baku kyauta mata ba daga kai har mahaifiyata, nan da kake ganinta ta zubar da ciki babu iyaka,  tantiriyar yar duniya ce me fuska biyu, kayi tunanin abin da zata iya aikata maka idan bakayi yadda tace din ba” yana gama fad’a suka iso junction din gidan _Baba K_, anan ya saukeshi tare da ba shi kudin daya mishi alkawarin sannan ya yi tafiyarsa.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Suna zaune a falo suna kallon tashar BBC taji wayarta ya d’au k’ara, ganin sabuwar lamba shiyasa bata d’auka ba sai da akayi mata kira biyar sannan ta d’auka tana cewa “wai waye ne yake ta damuna? Idan akayi kira daya biyu uku akaji shiru ai sai a hakura ko?” Cikin d’an rawan murya yace “ni ni nine ni nine K…” Tsaki taja cike da 6acin rai “kai kai wa? sai wani ni ni nine kake tayi kamar bebe, gwara ka sake duba lambar da kyau kila bani kake nema ba shashasha kawai” ta fad’a tare da datse kiran.
Mintina biyar tsakani ya aro dauriya ya yafa kafin ya sake kiranta, “nine dai _K³_” wani irin zabura tayi ta dafe kirji cire da tashin hankali tace “kai kai kai kaine K³” cikin jin dadi ya samu damar rama zagin data mishi yace “ya kike ta abu kamar bebiya ko shashasha? Sannan Ina ajiyata da kika ce ta rasu alhalin karya ne ?” Kashe wayan tayi duk gumi ya jika mata fuska, safa da marwa ta hau yi a cikin falon ta rasa natsuwarta gaba d’aya ” _Yaya_ meya tashi hankalinki haka ne? Ki zauna muyi magana a tsanake” _Anty Mansura_ ta fad’a tana zaunar da ita a kan kujera, sai data kur6i ruwa sosai sannan ta kalli _Hanifa_ wanda ta maka earpiece a kunne da gani waka takeji “ke _Hanifa_” taji shuru “ke _Hanifa_!!” Shima shuru, ajiyar zuciyar tayi sannan ta kalli kanwartata tace “mu dai mun shiga uku mun lalace _Mansura_ _Khamisu_ nefa ya kirani yana cewa ina ajiyarsa da nace ta mutu alhalin karya ne” zaro ido itama tayi ” _Khamisu_ dai uban _Hanifa_ mun shiga Tara ne ba uku ba ai _Yaya_ to shi ina yaji zancen da har ya kira ki kuma ina ma ya samu lambarki?” Shuru sukayi suna jimami ita kuma _Hanifa_ duk tana jin su babu wani wakan data zaka a earpiece din kawai tayi haka ne dan taji cikinsu.
“Yanzu _Yaya_ meye ne mafita?” Karan wayarta ne ya sake dagula mata lissafi ganin layin _K³_ ne ya sake shigowa, sai da ya kira sai uku sannan ta d’auka jikinta a sanyaye “baki bani amsa ba kika kashe wayar ko ta sake mutuwa ne?” Kokarin saita kanta tayi “ni ban san ma wace ajiya kake magana a kai na, kafin ka kira matar aure kuma ya kamata ka samu izininta dan haka bana son irin wannan shashancin ka fita a rayuwata kamar yadda na fita a naka” ta fad’a tare da katse kiran  sannan ta kashe wayan gaba daya, “dole musa boka ya mana aiki a kan shi dole ne yanzu a gama dashi kafin mu koma kan sauran aikin mu” ta fad’a cike da 6acin rai. Sosai _Hanifa_ taji dadin lamarin dama abin da take so kenan su fita a lamarin su _Sufyan_.
Haka ranar suka wuni cikin bakin ciki dan boka ba’a ganinsa a wannan ranar sai a washe gari, _Hanifa_ kuwa dadi kan dadi yau ta samu ubanta kuma ta san wacece mahaifiyarta na gaskiya. Yanzu hankalinta zai koma kan aurensu da _Sufyan_ alkawarin da _Jidda_ tayi dole ne ta cika duk da cewa ta san ta bata ta6a alkawari ba tare data cika din ba, gobe zata mata tuni kan maganarsu domin ta san ta inda zata fara aikinta, _Sufyan_ dai suna da kyakyawar alaka domin yana mata kallon mutuniyar kwarai kuma yana tausaya mata idan _Mama_ tayi mata wani abin shiyasa suke d’an d’asawa dashi dan haka yanzu ma ta san ba zai ki auren ta ba musanman idan _Jidda_ ce ta nemi wannan alfarman.
Washe gari da safe su _Mama_ suka tafi gurin bokansu ita kuma taje 6angaren _Jidda_ dan yau ance mata bata fita ba batajin dadin jikinta, shuru 6angaren nata duk yara sun tafi makaranta, a kwance ta sameta a falo, bayan ta shiga da sallama ta samu guri ta zauna tana yiwa _Jidda_ sannu, ta dade a zaune kafin tace “ni kam _Anty Jidda_ ya maganar mu ta kwanaki, su _Mama_ sun sani a gaba wai sai dai ta auramin wani dan uwana kuma ni sam bana son shi saboda bashi da hali me kyau” tunda _Hanifa_ ta fara maganar duk taji babu dadi sai dai kuma alkawari ta d’auka wanda ya zama dole ta cika dan ita ba mutun ce me karya alkawari ba, “karki damu ina sane da hakan kuma idan ya dawo zanyi mishi magana a yau dinnan duk yadda mukayi zan sanar dake, kisa a ranki kamar har ya amince ne da yardan Allah” sosai _Hanifa_ taji dadin hakan godiya tayi mata tare da fatan Allah ya bata lafiya amma a zuciya fatan mutuwa take mata, sannan tayi mata sallama ta tafi.
_________________________
A yau na gama shirina na komawa gida, ban kira su _Mama Qudi_ ba saboda mamaki nake so in basu sai dai kawai su ganni a gida, sai dai na bawa su _Ummulu_ lambar akan zuwa dare sai su kira suji kona isa _Bauchi_, zanyi kewarsu musanman ma _Ummulu_ dan a labarin data bani da kuma d’an zaman da nayi dasu na kwana biyu kafin in fara shirin tafiya na fahimci tana da dadin sha’ani _Maman_ ma bata da wani matsala sosai sai na son y’ay’anta, haka shima _Malam_ mutum ne ne son jama’a, na dai yi musu alkawarin cewa zan dawo bikin su _Yaro_ idan Allah ya yarda, har kuka _Ummulu_ tayi nima sai data sani hawaye, akwai ta da shiga rai dan kyawawan halayyarta, har tasha suka rakani na hau motar Abuja daga can zan hau na _Bauchi_.
Tunda muka fara tafiya nake ta tunanin gida da kuma _Sufyan_ Allah sarki ko a ina zan gan shi? “Ya Allah kasa ya soni kuma karya sakeni mu zauna tare da yaran mu cikin aminci” ta fad’a a cikin zuciyar ta, Allah ya gani tana son mijinta tamkar yadda take son rayuwarta, ko wani minti ko wani bugun zuciyarta da son shi yake bugawa haka ko wani numfashin da take shaka da son shi da kaunarshi take shaka ita kachokan rayuwarta ma dan shi takeyi a halin yanzu, babu wani gurbin da zata iya bawa wani d’a namiji a zuciyarta domin mijinta ya riga daya mamaye ko ina kuma ko da ace zata karas da rayuwarta babu aure ne ba zata damu ba ranta sadaukarwa ne ga rayuwar y’ay’anta.
Tafiya sukayi me nisa sosai har suka isa garin _Abuja_, duk da cewa tafiyar awa biyu ne amma gajiyar zaman guri d’aya a mota duk ya ishi mutum. A tasha suka sauka dan haka a nan ta samu motar _Bauchi_ ita da wata mata da d’iyarta yar budurwa zatayi sha hudu sha biyar. Su biyar ne kawai a motar saboda shata sukayi dan basu son takura, daga ita da matar da d’iyarta a baya sai direba da wani d’an saurayi a gaba. Hanyar _Kaduna_ suka ga mutumin ya d’auka ko da suka tambayi dalilin sai yace ai hanyar _Bauchi_ ne babu kyau yanzu ta _Kano_ ake zagaye, ba tare da damuwa ba suka ce Allah ya kaisu lafiya.
Cikin awa biyu suka isa _Kaduna_ kasancewar duk musulmai ne sai suka tsaya sukayi salla daganan sukaci abinci kafin suka cigaba da tafiya. Awa hud’u ya kai su _Kano_ saboda motar ya samu matsala har sau biyu a hanya. A kano sukayi la’asar sannan aka gyara musu motar daganan suka cigaba da tafiya, tsire d’an saurayin nan ya saya ya ajiye daya agaba ya basu guda daya suma a baya, babu wani damuwa suka kar6a tare da godiya domin tunda suka shiga motar yake ta bin kira’ar karatun kur’ani alama dai ya nuna shi din hafizi ne, wannan yasa basu kawo komai a ran su ba suka hau fizgar nama, mintina talatin tsakani duk sukayi barci, kallon direba ya yi yace “babu matsala har mu isa baza su tashi ba kai dai kara wuta kawai” murmushi direba ya yi yace ” _Malam_ zai yaba da aikin ka musanman yar shilar da za’a kai mishi” ya fad’a yana nuna yar budurwan dake jikin mamanta.
Basu isa _Maiduguri_ ba sai guraren sha biyu na dare, a kauyen _Bama_ suka yada zango, kamar dai yadda ya fad’a din hakan ne ya faru dan har suka isa babu wacce ta farka a cikinsu, d’aukan su wasu manyan mata sukayi d’aya bayan d’aya zuwa wani d’aki inda mata ire irensu suke ciki, wasu suna barci wasu sun zuba tagumi wasu suna kukan zuciya dan basu isa suyi a fili ba yanzu jikinsu zai gaya musu shurun shine alkairi. Bayan sun ajiye su sun fita suka wuce 6angaren _Malam Ula_ suka sanar dashi an samu adadin da ake bukata, kai kawai ya d’aga musu sannan suka fita suka bashi guri.Kamar yadda tace su kira zuwa dare hakan ne ya faru. Su _Inna Suwaiba_ suna zaune suna hira wayar _Mama Qudi_ ya hau kara, kafin ta d’auka har ya tsinke, sake kira akayi cikin sauri ta dauka tare dayin sallama, cike da farin ciki _Ummulu_ ta gaisheta, bayan ta amsa ta nemi sanin ko waye, ba tare da 6ata lokaci ba _Ummulu_ tayi bayanin kanta tare da tambayar ko _Khadeemah_ ta isa lafiya, cike da jin dadin cewa _Khadeemah_ na hanya _Mama Qudi_ har da taka rawa sannan ta saka wayar a speaker ta bawa _Inna Suwaiba_ a kunne ta saka bayan sun gaisa ta sake tambayar _Inna Suwaiba_ ko ta isa, a nan tace mata sai dai idan har yanzu suna kan hanya amma bata iso ba, tambayarta tayi ko meye had’inta da _Khadeemah_ anan ta fara bayanin duk abin da ta sani game da _Khadeemah_ da tsintar ta da _Malam_ ya yi har zuwa irin zaman da tayi a gidan da kuma dawowa hayyacinta da tayi har ta manta dasu, komai dai sai da ta sanar har zuwa tafiyar _Khadeemah_ a yau da kuma cewa da tayi su kira ta zuwa dare suji kota isa, mamaki ne ya kama kowa tare da tausayin _Khadeemah_ akan irin matsalolin da take samu a rayuwarta, daganan suka musu godiya suka ce tana iso wa zasu kira su sanar dasu.
+
Su _Khadeemah_ Basu farka ba sai washe gari da safe inda suka tsinci kansu a wata rayuwa, da kallo suka bi d’akin tare da bin duka matan da ido suna mamakin yadda akayi suka zo gurin, kafin suyi tambayan inane nan jibga jibgan matan jiya suka shigo da manyan bokitai guda biyar ko wacce da guda d’aya, wata ce ta shigo da kofuna na roba ta ajiye ta fita, bayan ta fita suka bud’e bokitan suka zuzzuba musu abin da yake ciki suka mikawa kowa, cike da tsoro wadanda suka kwana biyu a gidan suka kar6a suka kafa kai wadanda kuma aka kawo su Jiya suka so yin taurin kai ciki harda _Khadeemah_ ai kuwa sun sha duka ba shiri suma suka kafa kai suka hau kwankwad’a ba tare da sanin ko meye ba domin ba takamanman dandano guda daya da zasu kama.
A 6angaren su _Mama Qudi_ tun sunayi suna ta kirga lokaci har suka fara tsorata da lamarin, ranar babu wanda ya rintsa a cikinsu har zuwa safiya babu alamun ta, hakan yasa aka kira _Sufyan_ aka sanar dashi, lambar su _Ummulu_ ya bukata bayan an tura mishi ya kira ta ya mata bayanin kan shi sannan yace ta fad’a mishi abin data sani, babu jinkiri tayi bayanin komai kamar yadda ta fadawa su _Inna Suwaiba_ godiya ya mata tare da cewa ta kwantar da hankalinta insha Allah za’a sameta, bayan sun gama wayan shima duk hankalin shi a tashe, ba shiri ya kama hanyar _Abuja_ a jirgi, bayan ya isa ya nemi ganin sunayen mutanen da suka sauka a mota a nan yaga sunan ta a rubuce kenan ta isa _Abuja_ lafiya, tambayarsu ya yi ko akwai motar da ya yi _bauchi_? Sukace eh akwai mota d’aya wanda ya d’auki fasinja zuwa _Bauchi_ sai dai ance hanyar ba kyau ana gyara shiyasa ya bi _Kaduna_, tambayarsu ya yi ko zai samu lambar mutumin, babu musu suka bashi sai da ya bar gurin kafin ya kirashi, bayan ya dauka suka gaisa yace mishi yana ina ne yace mishi _Kano_ ya sake tambayar ko yaushe zai dawo yace mishi gobe saboda za’a mishi gyara a mota. Bayan ya kashe ya hau jirgin _Kano_ yana isa ya kirashi da lambar wani me taxi direba cikin ikon Allah sunan shi ya bayyana, bawa me taxi din ya yi yace ya tambayeshi yana ina, bayan ya fad’a mishi suka kama hanyar garejin da yake.
Mintina goma ya kai su garejin, suna zuwa gurin shi abokin nashi ya riko hannunsa zuwa wajen motarsa, a lokacin shi kuma _Sufyan_ ya fito kallon mutumin ya yi na yan mintina kafin yace “ina ka kai min matata? Kar kayi tunanin yimin karya domin yanzu zan hadaka da yan sanda, naje har tashar ku na _Abuja_ an tabbatar min da cewa kai kad’ai ne ka d’auki mutane zuwa _Bauchi_ a jiya dan haka gwara ka fadamin gaskiya” ganin babu wasa a lamarin _Sufyan_ kuma da ganin shi kasan akwai naira yasa ba shiri ya sanar dashi gaskiya cewan _Maiduguri_ ya kai su inda yake kai mutane ko yaushe a wani babban _Malami_ yana anfani dasu wasu kuma yana sayar dasu a yan ta’adda, mamakine ya kama su duka, nan danan suka tasa kyeyarsa zuwa ofishin yan sanda, sosai abokinshi yaji haushinsa domin bai ta6a sanin cewa sana’ar da yakeyi ba kenan, bayanin komai ya musu game da _Malam_ da kuma inda yake, yana gamawa wani kumfa ya fara fita a bakin shi daganan ya fad’i a gurin babu alamun rai a jikin shi, waya yan sanda sukayi da ofishinsu na Abuja suka sanar dasu abin da yake faruwa tare da sawa a kama shugaban wannan tashar ta _Abuja_ shi kuma aka kai gawarsa gida dan abokinsa ya sanar da cewa shi d’an _Kano_ ne kuma ya san gidanshi.
A 6angaren Ogan tasha na _Abuja_ bayan an kai shi ofishi ya musu bayanin cewa bai ta6a sanin cewa ana irin wannan abin a tashar ba duba da cewa babu wani wanda ya ta6a kawo k’orafin wani nasa ya 6ata, maganganu ya yi masu gamsarwa daga nan aka kawo sauran ma’aikatan kowa ya bada shaidar cewa babu abin da ya sani sai mutum guda wanda yace tsoron kar ya cutar mishi da yara shine silar shurunsa domin ya ta6a kama shi dumu dumu yana zancen an samu yaran da za’a kai, daya yi niyar tona mishi asiri sai ya sanar dashi cewa yin hakan na dai-dai da rasa yaransa yan mata uku dake karatu a jami’ar _Maiduguri_ tsoron kar hakan ya faru da yaransa yasa ya yi shiru amma kullun da abin yake kwana yake tashi ya rasa mafita, kasancewarsa tsoho shiyasa ba’a mishi horo ba aka kyaleshi sannan aka fara shirin zuwa can _Maiduguri_ domin binciken _Malam_ tunda yanzu an san inda yake. Sai dai abin da basu sani ba _Malam_ nada ido a kan duk wani ma’aikacin sa hakan yasa ya kashe wannan mutumin domin ya tono mishi asiri sannan suka canja guri daga gurin da yace suke suka koma _Chibok_ a wannan ranar.
Cikin kankanin lokaci sukayi booking zuwa _Kano_ daganan suka shiga jirgin _Maiduguri_. Suna isa sukayi _Bama_ a cikin motar yan sandar daya zo daukansu, tashin hankali da ba’a sa mishi rana duk kan _Sufyan_ ya d’au zafi ya rasa mafita domin sunje sun samu gidan ba kowa sai wani wasika da aka bar musu “nafi karfin duk wani jami’in tsaro, kamani sai Allah ba dai mutum ba, kuma kun tafka kuskuren bincike a kaina domin kun jawa wacce ake nema horo me tsanani” duk iya bincikensu har da mazaunan gurin babu wanda suka iya samun bayanai me gamsarwa daga gurinsa, karshe dai aka zuba jami’ai domin tsaurara bincike su kuma suka koma bakin aikinsu.
_Sufyan_ sai da ya yi kwana uku a _Maiduguri_ kafin ya koma _Bauchi_ dan babu wani cigaba da aka samu a cikin binciken da akeyi, hakan kuma ya faru ne saboda gur6atattun yan sanda da sojoji da suke tare da _Malam_ din dan duk wani hanya da zai sada su da shi sun toshe ta. Ko da _Sufyan_ ya koma gida ya sanar dasu abin da yake faruwa sabuwar tashin hankali ne ya wanzu a tsakanin ahali biyu, _Jidda_ uwar tausayi wani sabon zazza6ine ya kamata saboda tausayin _Triple_, _Hanifa_ kuwa bakin ciki ne ya mata yawa domin ta san a wannan halin da ake ciki babu yadda za’a yi _Jidda_ ta mishi maganarta kuma dole zancen aure sai dai wani lokaci amma ba zai bada dama a yanzu ba, babban 6acin ranta yadda ta ga ya nuna damuwa sosai alamun yana son matarsa kenan, ko wacce tana da matsayi a zuciyarsa duk yana son matansa to ita kuma a ina zai sata kenan? Babban burinta a duniya shine ta samu zuciyarsa gabadaya kuma ta kawar da ko wace mace a cikin rayuwarsa daga baya zata san yadda zatayi da yaransa.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]