[Advertisements⬇️]

DAN WAYE? CHAPTER 15 BY ZAHRA'U BABA YAKASAI - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

DAN WAYE? CHAPTER 15 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Misalin karfe takwas suka iso asibitin kaf ‘yan (group) din su, Dr. Shuriem ya kalle su ya zo shigowa, ya ce.”Ku ba an sallame ku ba?”Mubarak ya ce, “Likita korar mu ake?”  Ya ce, “No ba wai korar ku nake ba, ku Www.bankinhausanovels.com.ng
din ne akwai cafta”. Suka ce, “To ai ba cinya ba kafar baya”.
Ya ce, “Ni fa ban gane ba”.”To ka sallami Musty kun rike mai dakinsa”.
“Oh! Ai ban sani ba, yaushe aka kawo ta? Yau ina AKTH ban jima da shigowa ba”.

Alpha ya ce, “Ai fata muke”.

Dr. Shuriem yayi dariya, suka shiga tare. Surayya da Izzat kadai a dakin, Musty ya samu gefen gadon ya zauna, Izzat tayi masa wani irin kallo wanda sai da yaji shi a jikin sa, sannan
sai ta juya baya.
Ya ce, “Sury, ya mai jikin?”Ta ce, “Da sauki”.
Ya ce, “Ina Umma?”Ta ce, “Yanzu za su iso ita da Abban mu”.
Ya riko hannun Izzat, tayi saurin janyewa tare da juyowa suka zubawa juna ido.
Ya kalle ta, “Ba ki so na ko?” Ya langwabe kai, “Ni mai laifi ne”.
Kawai sai yaga hawaye na zuba a idonta, a Www.bankinhausanovels.com.ng
lokacin ya juyo ya ga duk sun fice, ya ce.
“Izzat, ina son ki son da ban taba yiwa wata ‘ya mace ba, sai gashi kin guje ni, ba ki sona, kin tsane ni. Hakan ya janyo min jini na ya hau”.Ta kura masa ido tana kallon bakin sa, tace.
“Mustapha, kai ka dasa min kinka, gashi Allah Ya dora min sonka. Ina sonka, sai dai ina shakku a yanda mata ke son ka, gaka da izza, anya za ka soni?”
Ya ce, “Wa ya ce miki mata na so na?” Ta ce, “Ai na gani”.
Ya ce, “Ki sanya a ranki Mustapha naki ne, Izzat kin huce za ki soni? Kin yafe min?” Ya ce, “In ba ki hakura ba ki rama marin
ki”.
Ta ce, “Ya zanyi Mustapha tunda ina sonka? Na so in tursasa zuciyata ta rabu da kai amma ta ki, anya ban yi son rai ba? Ina jiyewa kaina tsoron kada iyayen ka su kini”.
Ya ce, “Iyayena baza su ki ka ba, domin na fada musu, don bana son sai magana tayi nisa su sani”.
Ta kalle shi ido cikin ido, ta ce. “Su suka ce?”
Ya ce, “Sun amince da ke, sai dai na ce baki sona”.
Ta ce, “Wa ya ce bana sonka?” “Ke ce ki ka fada”. .
Tayi murmushi ta ce, “To amma ka fada

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


musu kaine ka ci zalina?” Ya tsura mata ido, “Kamar yaya?” Ta ce, “Ka mare ni, ina da lalura zan yi magana a gane, amma sam bana ji, kai kuma ina kula ba ka da hakuri, anya zaman mu zai dai daita?”
Ta rangwadar da kai, sannan ta ce. “Zama dani sai mai hakuri”.
Ya kura mata ido yana jin yanda sonta yake shiga zuciyar sa, ashe so na da dadi. Murmushi ya subuce masa.
“Na koyi hakuri tunda ki ka ce baki sona”. “Shi yasa ka  waya na ringa tura sakwanni shiru? Hakan yasa ni damuwa, nake jin in na rasa ka na hadu da kuncin rayuwa”.Ya yi murmushin dake fidda asalin
kyawun sa, ya ce. “Me yake damun ki har ya kai ki kwanciya a asibiti?”
Ta nuna shi, “Kai ne Musty na, tunanin ka ya hana ni sukuni, ni kuma na rasa yadda zan manta marin da kayi min. Lokacin da Mubarak ya ce baka da lafiya ban yi bacci ba, nayi ta tura sakwanni amma shiru babu bayani”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin zolaya ya ce, “Izzat, na gano tausayina kike ji, kinji ance son ki zai kashe ni”.Ta ce, “Hakika zuciyata ta shiga rudani, don ta tsinci kanta da makanuniyar soyayya wacce na nutse a ciki, daga karshe na afka cikin rudani. Son ka da kiyayyar ka dole son ya rinjayi kin, saboda na kula kaine mahadin rayuwa ta”.
Mamaki ya kusan sumar da Mustapha, kai ashe dai Izzat ta iya barin kala? Maganar gaskiya wannan da tana da kunne lallai da anyi manyan mata a fagen iya soyayya.
A dai dai wannan lokacin Umman su da Alh. Habib Salga suka shigo, ya dubi Mustapha ya ce.
“A’a, wa nake gani kamar Yallabai?” Mustapha ya ringa dariya, don ya gano Izzat diyar sa ce, shi kuma babban ma’aikcin kamfanin su na robobi dake Sharada ne.
Ya risina ya gai da shi, ya ce. “Sannu, kar dai kaine Mustaphan da ka marar min baby na?” Ya ce, “Afuwan Abba, na ce ta rama”.
Ya fada yana shafa fuskar sa, Umma ta dara ta ce.
“Ai ta hakura”.
a lokacin Surayya suka shigo, Abba yace.
“Daga ina ki ke?”Ta ce, “Ina zaune naga kun shige ni, ina ta magana ba kuji ba”,
Mustapha ya fidda (cheque) yayi rubutu ya ajiye, saboda ba su siyo komai ba, suka yi sallama da su.
Mubarak yake tukin mota, Alpha yana gefen sa, shi ko Musty na baya ya sa hannu ya rungumi kujerar da Barek ke kaiya ce.
“Allah abin godiya, wai yau ni Izzat ke cewa tana so? Abinda ban taɓa tunanin samu ba, lallai Allah abin godiya. Na san Abbanta ma’aikacinmu ne”.
Alpha ya ce, “Mu ma Surayya ke bamu labarin halin da ta shiga, saboda rashin samun wayar ka”.Haka ne”.
Mubarak yace, “Dama sai wani ya rasa wani yake samu. Sai wani ya zubar wani zai dauka”.”Kamar yaya?” Ya ce, “Ni kuma nayi rashin abar sona,
rashi na har abada”. Alpha ya ce, “Suhaila mutuwa tayi?”
Ya ce, “No, tana gidan mijinta mai Naira, na rasa soyayyar dan Adam da kudi, mutum yana son kudi kamar ransa, wani ma fiye da ransa. Don da yawa jama’a sun rasa rayuwar su a dalilin kudi, wasu rasa wani bangare na jikin su a dalilin kudi. Ni kuma soyayya ta da kudi bata kai haka ba, domin ni nafi son rufin asiri kada in nema agun wani, kuma ni ina daraja dan Adam fiye da kudi”.
Alpha ya ce, “Mubarak ‘yan matan yanzu sunfi son mai kudi fiye da kansu, şhi yasa samarin yanzų in kaga sun sakarwa yarinya, to lallai itama ta saki layi, ban gishiri in baka manda ita ce rayuwar samartakar yanzu”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Mubarak ya ce, “To ko in haka ne gaba daya daga mazan har matan ba ma yiwa kanmu adalci ba, don in bamu gyara ba lallai mun dauko hanyar lalata rayuwar mu gaba daya, domin babu yadda rayuwar al’umma zata ci gaba bayan zinace-zinace yana yawa cikin al’umma”. Mustapha yayi shiru, can ya ja dogon tsaki
ya ce. “Shi yasa sam bana son soyayya, ban da Allah Ya hada ni da wacce nake so, amma so nayi Daddy ya zaɓo min wacce zamu yi dai dai”.
Alpha ya fashe da dariya, ya ce. “Shege Musty, Allah Ya kama ka, matan
da ka wulakanta suna da yawa, gashi sakayyar Allah sai ka kamu da son kurma. Kai Allah Buwayi Gagara misali”.
Mustapha ya sha kunu, ya ce. “Ba na son wulakanci, ai ni kurmar ta fiye
min mai baki, don su ba gulma bare munafurci”. Ya ce, “Ai kam gashi nan, in kana magana tayi maka kuri da ido tamkar wacce ta warke daga makanta”.
Mubarak ya ce, “Ai da kallo take gane me kake cewa, in bata kalli bakin ka ba, baza ta san me kake cewa ba”. Mustapha ya ce, “Wai Haj. Hadiza da gaske take kudi ya fi zumunci ko?” Ya ce, “To ya za’a yi?”Ya ce, “Kyale ta, akwai ranar kin
dillanci”.
Suhaila gashi dai ana cikin daula, ta kudiri aniyar zama da mijinta don tayi bautar aure tunda duk abinda take tunkaho da shi Musbahu ya gama da shi, to me zata yi ta burge shi? Ta hakura ta fauwalawa Allah (S.W.T), don ta kula Mominta akwai son kudi, to da abban su bashi da kudi za ta zauna da shi?
Tayi kiran duk lambobin Mubarak amma ba ta same shi ba, ita kuwa Baba Halima ba ta da ita. Tayi alkawarin siyawa Mah waya, don su ringa gaisawa. Shigowar Khalid ta sanya ta dawowa daga tunani, aguje ya fada jikinta.
“Aunty Mari”.Haka yake kiranta. Ta ce, “Boy, ka dawo?”
Ya daga kai, ta soma kokarin cire masa safa, yana kokarin fidda littafin sa daga jaka, yana nuna mata aiyukan da aka yi musu, da (home work) din da zai yi.
Ta ce, “Ajiye su kayi wanka, ka ci abinci.
Idan ka dawo daga Islamiyya sai muyi”.
Shigowar maigidan nata ta gani, ta ce. “Abban Khalid, sannu da zuwa”. Ta mike ta karbi jakar hannun sa, ya zube
kan kujera ya dafe kai, ya ce. “Wash!”.
Ta mai da dukkan hankalin ta kansa, ta ce. “Ba dai gajiya ba?”
Ya bude jajayen idanun sa ya kalle ta, tace.
“Anya lafiya kake? Ji yanda idanun ka suka rine”.
Ya ce, “Kaina na min ciwo, kada ki damu, nan da zuwa gobe zan watstsake”.Ta ce, “To ka sha magani”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “Ko na sha ma ba dainawa yake ba, shi yasa duk sanda ya tashi sai dai in kwanta kawai”.
Cikin jin tausayi ta ce, “To sannu, Allah Ya baka lafiya”.
Ya ce, “Amin”.
Juma’atu babbar rana, bayan sun fito daga masallacin Juma’a ne suka nufi gidan Hajiya Lami kakar Mustapha, sun kai su bakwai.i Al’adar su matasan akwai su da zumunci duk akan zaga gidajen ‘yan uwa, duk inda suka je sai Mustapha yayi yayyafin Naira, don shi mutum ne mai kyauta.  Hajiya Lami ta ce, “A’a sannun ku da zuwa”.
Gaba daya suna zaune a falo sun gaisa da ita, sun shiga kwasar hira Www.bankinhausanovels.com.ng
Sallamar (yan biyu) ce ta dauki hankalin su, Weesal ce a gaba Wedeyan a baya, ‘yan biyu masu kama daya tamkar ‘ya’yan Larabawa. Baban su ne kwara, mahaifiyar su ma sai tayi da gaske take gane su, don komai nasu daya.
Weesal ke da dumpil daya, yayin da Wediyan ke da biyu, shi ne bambancin su. Hatta magana, kallon su tsahon gashin su duk daya ne, daya na da yawan magana da son budawa. Indai suka zauna suka yi shiru, to babu mai gane su, ko laifi suka yi da wuya a gane, su sai su. shi yasa lamarin
Shi dama Mustapha ba ya shiga sabgar su, Weesal ce mai nacin kaunar sa, ita ko Weediyan ta ce ita ba zata auri talaka ba, sai mai kudi, mai kudin ma sai wanda yayi suna cikin jerin masu

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]