[Advertisements⬇️]

DAN WAYE? CHAPTER 11 BY ZAHRA'U BABA YAKASAI - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

DAN WAYE? CHAPTER 11 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

A’a ku ne?”  Ya gyada kai tamkar marayan da yake neman agaji, tayi murmushi. Ya tsira mata ido, ya ce.

“Ki rarrasar min rayuwa ta tayi murmushi”. Taji ta amince da son da yake yiwa lazzat, lallai duk ajinsa da girman kansa yayi sanyi. Shi kuwa Mubarak ya tsaya da Izzat, ta

kalle shi cike da hargagi irin na kurame ta ce. “Me ka rako shi yayi a gurina? Ko kun zo ya rufe ni da duka ne? Na kula ku masu kunne ba ku

tausayin marasa ji, sam bakwa yi mana adalci ta inda ba kwa ajiye komai ba sai gulma da munafurci. Ku sani, in mu ba ma jinku Allah Yana jinku.

To yanzu me ku ke nufi dani? So ku ke ku kashe ni, don na san ba wai son gaskiya ya kawo shi gurina ba, ya zo ya cimma wani burinsa ne”. Kawai sai ta fashe da kuka, ta juya ta shige

gida.

Kai tsaye falo ta shiga, Umma na kwance sai ji tayi an fada mata, ta ce.

“Lafiya Izzat?”

Ta ce, “Mustapha ne”.

Ta rungume ta tana lallashin ta. Ita ko Surayya tana tsaye da Mustapha, ya

bata tausayi, ya ce.
“yanzu ke ba ki shawo min kanta ba? Hakika na wulakanta mata masu sona, gashi nima na tsinci kaina da son wacce ba zata soni ba. Ina tausayin rayuwa ta”.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


Ta kalle shi ta ce, “Kayi hakuri, ka san yanayin rayuwa sai a hankali, na san Izzat tayi soyayya da kai a waya, makauniyar soyayya, domin tana son Mustapha haka tana kin ka a dalilin marin da kayi mata. Ni dai abinda nake tunani shi ne kayi hakuri ka rabu da ita ka samu wadda ta dace da kai”.
Wani irin kallo ya yi mata, ya ce “Surayya, ashe ba ki da hankali, ba ki da tausayi? Ba ki san irin kalaman da ya dace ki fada min ba, za ki iya kisan kai fa, don zuciya ta zata tarwatse ne sosai ta inda zan iya mutuwar farat daya”.
Dai dai lokacin Mubarak ya karaso, ta dube
shi ta ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ka lallashi abokin ka, don Izzat ba zata so shi ba, idan yana sonta na farko kurma ce, dole sai ya koyi hakuri zai iya zama da ita, sannan anya ma ba zata samu matsala da iyayen sa ba? Bana son rayuwar Izzat ta shiga hadari, domin ita din abar tausayi ce, don da ba kurma bace daga baya ta tsinci kanta a haka.
Kuyi hakuri, zan yi duk iya bakin iyawa ta
don ganin na rarrashe ta. Zamu yi waya”. Ta juya agur guje tayi gida.
Sun jima a tsaye, Mubarak ya kama “Abokina, kada ka damu, komai mai wucewa ne kaji?”Ya gyada kai, don ba shi da bakin magana. Mubarak ya ja mota suka nufi gidan su. Suna (parking) suka samu su Alpha a zaune a wani kebaɓɓen waje da suka saba zama,
Mustapha ya fito ya yi ciki, Mubarak ne ya yi
wajen su.
Alpha ya ce, “Lafiya kuwa Musty?”
Ya ce, “Eh to, lafiyar kenan”.
Gaba daya suka wuce dakin sa, abin mamaki suna shiga suka ganshi ya shige cikin bargo yana rawar dari.
“Lafiya?” Suka hada baki suna tambayar sa, ya ce.
“Sanyi nake ji, zazzabi ya kama ni. Zuciya ta tayi kunci, ina ji a jikina rayuwata ta shiga hadari, ina ji a jikina wani abu zai faru dani. To mene ne? Shi ne abinda ban sani ba”.
Duk sun yi kasake babu wanda ya iya cewa komai, jikinsa ya ci gaba da bari. Mubarak ya zuba masa ido, ya ja kafafu ya zauna daf da shi, ya ce.
“Abokina, kada ka sa kanka a wahala, kada ka damu da mace har ka yiwa rayuwar ka illah. Yaushe ne za ka damu da mace wacce bata da tabbas? Duk yadda za ka so mace ka kyautata mata ita fa ba ta gani. Ni ka ganni nan, mace ba ta dagacikin abinda zan sanya ta a raina ta dame ni, don ni
gaba daya tausayi rayuwar ‘ya mace take bani”. Mustapha ya daga masa hannu, ya ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Kada ka rugurguza min kwanya da maganganun ka masu zafi da ciwo, mace aba ce mai daraja, domin ina girmama soyayya. Ya za ka dinga magana kamar wanda ba ka fada tarkon so ba?
Don Allah ka kyale ni inji da abinda ya dame ni, domin mace abar asota ce, abar a kula da ita, abar aso ne, abar ayi mata komai, a bata kulawa da dukkan gata.
Ka tuna mace ita ce, ita ke bamu dukkan kulawa, ita ke daukar ciki cikin laulayi da wahala, ba ta bacci cikakke, ba ta iya ci. Sannan ta haife, ta dauki dukkan so da kauna ta danka wa danta, ta hana cikinta ta bawa danta. Kan mace zan kwana in yini ina baka,,,,, na ‘ya mace, kuma ban gama ba.
Me irin wannan halin ya zaka ce kada a sata a rai? Mubarak ka so kanka da yawa, ban zaci haka daga gare ka ba”.
Alpha ya ce, “To anji an yarda, ka kwanta
ka huta. Bari in kawo maka magani”.Ya kudundune jikinsa, sai karkarwa yake.
Wani matsanancin tausayi ya kama Barek, ya kasa tunani, take ya mike kai tsaye gidansu ‘Yar kurma ya wuce. Yana tsaye yana neman yaro amma bai samu ba, can yaga wata dattijuwa za ta shiga gidan, ya yi sauri ya ce. “Hajiya”.
Ta juyo, ya kwashi gaisuwa, ya ce.
“Na jima tun dazu ban samu yaro ba, don Allah in kin shiga ki turo min Surayya”.
Ta ce, “To”. Ta shiga ciki, minti uku kacal sai gata, tana ganinsa ta ce.
“A’a, dawowa kayi? Ina abokin naka?”
Ya ce, “Zuwa nayi mu kawowa kanmu masalaha, wallahi Mustapha ya kamu, rashi Izzat zai iya salwantar da rayuwar sa. Yanzu haka yana cikin wani hali, ki fada min gaskiya, shin kina ganin ba zata so shi ba? Ina tsoron rayuwar sa ta samu nakasu, ki bani amsa”.
Ta kalle shi ta ce, “Mubarak, ta ya zan baka amsar da ban sani ba? Saboda ni ba ni ce zuciyar Izzat ba, ban san me ke ranta ba. Hakika ada na san ta so Mustapha so ba dan kadan ba,domin babu abinda ya fi mata dadi tamkar ta zauna tana hirar sa, tana siffanta shi. To amma kuma ta tsani Mustapha, saboda ya wulakanta ta, ta jima kafin ta fidda abinda yayi mata. Amma me zai hana mu barwa Allan ikon sa, ma’ana mu zuba mata ido?”
Mubarak ya ce, “Mustapha yana sonta, yanzu ma yana cikin wani hali, ni kawai ina so ki kira min ita”.
Ta ce, “Kayi hakuri, tana cikin kuka, har yanzu rarrashinta Umma take”. Ya wana hannun sa, ya dunkule su, ya girgiza kansa, ya ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Shi kenan, zanyi duk iya yi na don ganin na ceci abokina daga fadawa tarkon so, ko ince Koshin wahala. Hakika rayuwar sa na cikin hadari, zan roki Allah Ya cire masa son Izzat, ya yi masa sauyin alheri, kila sonta ba alheri bane a tare da shi, shi yasa hakan ta faru”.
Ya juya a fusace, don zuwan nasa bashi da amfani. Surayya ta tsaya tana kallon sa cike da
takaici, ta juya.
Umman su ta ce, “Waye ya zo?” Ta ce, “Mubarak din Mustapha ne”,”Lafiya?”
Ta ce, “Eh to, wai Mustapha ya shiga mummunan yanayi, shine ya zo ya ji ya za a yi? Ni kuma na ce suyi hakuri su nemi wata”.
Umma ta ce, “Saboda me?”
Ta ce, “Saboda Izzat ba ta sonsa”.
Umma ta ce, “Karya ne, kin san Izzat na son Mustapha, don ta ce ba zata iya rabuwa da shi ba, ya zaki ce ya hakura?”
Ta ce, “A’a, Umma mutum ne yayi maka ya baka hakuri ka ki, to ya zai yi? Ki kyale Ashe duk Izzat na kula da bakin su, tana laifi ta”.
fahimtar me suke cewa, ta ce.
“Surayya, ya za ki ce ya rabu dani? Kin san girman son sa a zuciya ta? Kin san yadda nake jin kaunar sa? Dole in nuna masa girman laifin sa a gurina, ina ji nima in na rasa Mustapha hakika zan iya rasa rayuwa ta”.
Surayya ta ce, “Oho miki, ni kam na ce ya rabu dake. Ai kinga yadda ‘yan mata ke sonsa yana share su”.Zazzafan zazzabi ne ya rufe Musty, Momie tana tsaye akan sa tana kallon yanda idanun sa suka yi jajir, hatta bargon sa yayi zafi sosai.
Daddyn sa ya ce, “Sannu”.
Ya duba agogo sha biyu da minti biyar na dare, ya yiwa Dr. Shuriem waya ya sanar masa.  Ya ce, “Gashi kuma ina shirin shiga tiyata,
amma zan turo Dr. Yaseen ya zo ya ganshi”. Alhaji Albadulmajid ya ce, “Bari kawai in kawo shi, don jikin nasa ya dan yi zafi”.
“Ok shi kenan Alhaji, sai kun iso”. Nusshu Clinic & Maternity shi ne asibitin Dr. Shuriem, shi ne kuma (family Doctor) dinsu. Asibitin nasu yana da kyau, ga manyan likitoci, duk wani babban likita dake Kanon Dabo to yana da ranar da yake ganin (patients) a can. –
Da isowar su aka karbe su akayi ciki da su, cikin kwarewa da aikin su Dr. Yaseen ya kula da shi. Cikin lokaci kankani ya gano damuwa ce tayi masa yawa, don gashi har jininsa ya hau, sannan bugawar zuciyar sa ya sauya.Nan da nan ya dura wasu allurai cikin ruwa, ya sanya masa, sannan ya yiwa Alhaji bayani.Mamaki ya kama shi, yac”To me ya
damu Mustapha?”
Zahra’u Baba Yakasal Nan da nan ya dura wasu allurai cikin ruwa, ya sanya masa, sannan ya yiwa Alhaji bayani.
Bai koma gida ba a gurinsa ya kwana, ko da gari ya waye bai bar asibitin ba sai wajen tara. Yana isa gida a zuciya ya isa dakinta, yace
“Wai ke wacce irin mace ce? Danki mu tafi da shi cikin tsananin ciwo amma ki kira ni a waya ki tambayi jikin sa kin gaza? Haka ake dan fari? Wallahi indai haka za kiyi lallai ‘ya’yan ki ba za su soki ba, wannan wanne irin shashanci ne?”
Ta tabe baki, “Haba Alhaji, ba gaka a gurin ba? To meye zanyi masa? Zan ba shi lafiya ne?”
Ya yi kwafa yace “Hakika yanda kike
nuna rashin kaunar, ki ga Mustapha wani cewa
zai yi ba danki bane”. Ya yi kwafa ya shige.
Ko a jikinta, don ita irin mutanen nan ne da ba su sanya da cikin zuciyar su. Ita babu abinda ya dame ta, tun abin na damun Mustapha har ya hakura. Shi yasa ya fi son baban sa, don ya fi kulawa da shi, ya fi bashi soyayyar iyaye. Bayan ya fito yana staye a farfajiyar
gidan, Alpha ya shigo. Alhaji yace “Ba ka tafi aiki ba? Yadda Mustapha yafi ku kula da aiki”.
Alpha ya ce, “Na je dawowa nayi, na kira Mustapha a waya (switch off) jiya na abrshi bashi da lafiya, shi yasa na kasa hakuri na dawo”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “Yana asibiti, jiya acan na kwana,
yanzu ma can zan wuce”.
Ya ce, “Amma Daddy ba a sanar min ba?”
“Abu ne cikin dare”. Ya ce, “Shiga ka karbo abincin sa”.
Ya shiga ya fito da kwandon abinci da wasu hadaddun kuloli a ciki, ya sanya a bayan mota, ya ce.
“Ma hadu Daddy, bari in dauko mota ta”. Ya ce, “Okey”. Ya ja ya tafi.
Maigadi ya bude masa yana cewa.
“A gai da mai jiki, ayi masa sannu.
Ubangiji Yasa kaffara ce”.Alhj Yace, “Amin”.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]