[Advertisements⬇️]

DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 3 BY ZAHRA'U BABA YAKASAI - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 3 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

Mal. Bala ya ce, “Ya kike zancen shari’a ne? Sun kawo takardar sammaci ne?” “A’a, na san ko ba jima ko ba dade sai sun kai”.
Ta dubi Mubarak, “Mubarak, ka nemo min Mustapha, ya yi fushi damu”.
Ta ce, “Ka nemo shi, mu muka yi masa laifi, dole mu lallashe shi”. Ta fada cike da jin zafi.
Gidan cin abinci ne na Five Ster inda

majalisar su take, nan Mubarak ya yanke ya je ya ga Mustapha.
Misalin karfe tara na dare ya isa wajen, haske tarwai kamar rana, gefe ga manyan motoci na alfarma an aje su, shi ma ya zo ya faka Lifan dinsa. Sanye yake da kananan kaya, ta haska sosai, sai rama da yayi.
Ya karaso gurin ya mika musu hannu duk suka yi musabaha, ya samu gefe ya zauna yana baza ido yaga ta inda Mustapha zai billo. Ko minti biyar bai yi da zuwa ba Alpha ya zo ya faka motar sa, sanye da manyan kaya. Sai da ya fito suna iya hango shi, ya cire babbar riga da hular sa ya jefa bayan motar, sannan ya rufe ta, ya kira Faisal, ya ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Mutumina, ince ko da Boss aka fita?” Ya ce, “Wallahi daga Karaye muke, can
dangin Boss, duk ansa nayi shigar manyan kaya sai kace wani tsoho”.
Suka bushe da dariya, Naseer ya ce.
“Ai su iyaye akwai takurawa, dole sai ka sa manyan kaya, mu fa ‘yan gidanmu ko Alhaji za ka gaisarwa sai ka sa hula”.
Suka bushe da dariya, Mubarak ya ce

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


“Ai sanya hula kamala ce, haka
Hausawa sanya manyan kaya yana saka kwarjini da kamala, kuma shi ne zai nuna kai din Bahaushe ne.
Alpha ya ce, “Au, Mubarak ko kasa kayan Hausa ko baka sa ba ai kai din ka san kai Bahaushe ne. Wallahi yau gaba daya ni a takure na yini, kai nifa yau ko dariya nayi kamar kuka nake yi, saboda yake ce. Ni kam yau da na san dani Alhaji zai yi tafiyar nan da tuni na gudu”.
Mubarak ya ce, “Lallai kam da ka yiwa kanka mugunta, kaga yau tarin ladan zumuncin da ka samu? Ka san zumunci na sa tsawon rai”.
Alpha ya ce, “Ban yarda ba, kaga Mahfuz
yayana mutum ne mai masifar son zumunta, ga
kyauta, amma gashi ya mutu a hanyar sa ta zuwa
Karaye, ko yau hirar sa ake”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Mubarak ya ce, “Yauwa, to ai kaga tsawon ran nasa, ma’ana za a dade ba a manta dashi ba. Ba wai ana nufin ba zai mutu da wuri ba, duk lokaci zuwa lokaci za’a yi ta zancen sa. In ko bashi da zumuntar ya mutu, tunda ba haihuwa yayi ba tuni za a zmania dashi”.
Faisal ya ce, “Wallahi na kuma yarda da batun ka, Allah Yasa muyi ta zumunta da ‘yan uwanmu. Shi yasa Mustapha yake burge ni, yana da matukar son ‘yan uwansa ko da shi daya ne. Jifa duk Juma’a yayi da kafar sa, da aljihun sa”. Mubarak an soso masa inda yake masa kaikayi.
“Oh, kwana biyu banga Mustapha ba, na kira wayar sa shiru, ko lafiya?”Alpha ya ce, “Kada kace baka san ya tafi Turkey ba?”
Ya ce, “Ban sani ba, yaushe ya wuce?” “Ina ji ya koma can da zama fa, kasan shi
yawancin rayuwar sa a can yayi”. Ya gyada kai, Faisal ya ce.
Alpha, naji ance Mami wai aurenta ya mutu, gaskiyas ne? Wai ance matsala ya samu da Momi ya koma can, kuma wa…”.
Alpha ya mike, “Haba da Allah, ka ringa
kyauta zaton alheri, dan uwanmu ne, abokin mu ne, komai ya faru da shi in da mutunci ai ya same mu. Ni fa bana son tsurku”. “Haba Alpha, daga magana sai kace tsurku?
Kai ka fiya zulama”.Oho dai, in ta faru tayi wari ma ji, don me shegen wari ne in batun ya bayyana”. A fusace Alpha ya mike, “Duk mutumin da
za ka rayu da shi ka so shi don Allah ba don wani dalili ba, a shirye nake in tallafi rayuwar Mustapha, komai ya same shi in da mutunci ai ya same mu ko?”
Suka yi tsit babu wanda ya kara magana, yasa Alpha ya mike, yace. “Mu kwana lafiya”.
Sai da ya shiga motar sa yana shirin ja, Mubarak ya karaso, ya ce. “Gashi ina son mu tattauna’.
Ya ce, “Yanzu bani da nutsuwa, mu hadu gobe”.Ya ce, “A ina?”
Ya ce, “Ka zo gidanmu”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “Ba zan iya zuwa gidan ku ba”.Why?”
Ya ce, “Akwai dalili, unguwar kuma na daina shigar ta”.
“Babu Mustapha ko?” Ya ce, “No, ba haka bane, akwai dai dalili”.
“To ni zan zo gidan ku (around 8:00pm)”.
Ya ce, “Okey, ina jian ka”.
Ya ja motar sa, shi kuma ya dauki lifan dinsa ya wuce gida.
Haj. Saratu ta zama tamkar zautacciya,  idanunta kullum da hawaye, tunaninta ina za ta sake ganin Mubarak? Zuciyar ta tayi sanyi.
Haj. Lami ta ce, “Saratu ki ji tsoron Allah, tunda ki ka haifi Mustapha ni hankalina bai kwanta ba, naki bai kwanta ba, na mijin ki bai kwanta ba. Tunda yaron nan yayi hankali ya gano ba ki sonsa, haka ake rayuwa? Ki ji tsoron Allah, ‘ya’ya amana ce da Allaj (S.W.T) Ya bamu”.
Ta ce, “Hajiya, ina da hankali, na san abinda nake. Ko ku yarda ko kada ku yarda da da uba sai
Allah, na rantse dana ne”. Ta ce cikin fushi, “Tunda danki ne sai kije ki karɓe shi”.
Kamar jira take, ta ce, “Zan dawo da wurina ko zan rasa zanin daurawa”.yarona
“A’a baza ma ki rasa ba, kije duk inda za ki, Allah bada sa’a, jiki magayi. Kuma ki sani, duk abinda ya faru ni babu ruwa na, ba zan sake shiga salgarku ba tunda abinda ki ka ga shi ne abu mafi soyuwa a gare ki kenan”.
Fita tayi ta je ta samu wani lauya mai zaman kansa, Barr. Sunusi Baba Yakasai, dama shi ne lauyanta, ta sanar da shi komai.
Ya ce, “Ikon Allah, to ke meye shaidar ki a jikin sa na zamantowar shi dane a gare ki?”Ta ce, “Kai zaka yi bincike, ni dai dana ne”.
Ya ce shi kenan, ko ma dai ya aka yi za su
shigar da kara kotun Musulunci. Ta ce, “Na gode Barrister”.
Ya yi mata alkawarin zai tsaya mata har yaron ta ya dawo hannun ta, sannan ya ce ta je ta shigar da kara, ko ma dai me ake ciki ta sanar masa.
Kai tsaye ta je tayi komai, cikin kwanaki biyu har kotu ta aika masu  da sammaci. Misalin karfe sha daya da rabi na safe Mah
tana zaune cikin zaure ita daya, ta rasa abin da
yake damun ta, yaro ya shigo ya ce.
“Wai ana kiran Baba”. Ta ce, “Ba ya nan”.
Yaron ya dawo dauke da takarda, ya ce. “Wani mutum ya bani takarda ya ce in kawo miki ki ajiye masa, kuma wai kiyi (signning) anan”.Ta ce, “Mene ne haka?”
Yaron ya ce, “Ki sa hannu”.Ta ce, “To ba sai na iya ba?”
Ya je ya gayawa mutumin, ya dawo da (ink)ya ce ta dangwala ta sa. Hakan kuwa tayi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Takardar meye?”Ya ce, “In ya karanta zai gani”.
Ta ce, “To Allah Ya jishe mu alkhairi”.Ya juya ya fita.
Mubarak ne ya fara dawowa, ya yi wanka ya ci abinci, ya same ta a zaune, ya ce.Mah, lafiya kike?”
Ta ce, “Oho, wallahi kawai na ji bani da nutsuwa, kuma abun yana damu na sosai a rai na”. Sai kuma ta soma hawaye, “Mubarak bansan me ke damuna ba”.
Ya kai kololuwar tashin hankali wanda tunda yake a rayuwar sa yau ce rana ta uku da yaji yayi muguwar kidima, ta farko ran da Hajiya Hadiza maman Suhaila ta wulakanta Mah, ta biyu ran da Maman Musty ta ce shi danta ne, sai kuma yau da Mah dinsa ke tsiyayar da hawaye.
Hakika ba ya son ɓacin ran Mah, da ranta
ya ɓaci gara ran kowa ya baci. Wa ya taba masa
ita? Ya ce, “Mah, bana son kukan ki, don ba zan iya jure kukan ki ba, domin zubar hawayen ki jidali ne a gare ni”.
Ta ce, “Rabu dani su zuba Mubarak, zubar su zuciya ta na yin sanyi”.
A haka Malam Bala ya shigo faram-faramda babbar rigar sa, ya zauna ya ce. “Um-um, anya lafiya ku ke?”
Ta dago ido ta kalle shi tana son tayi masa sannu da zuwa, ya ce.
“Halima, lafiyar ku kuwa?”
Ta ce, “Lafiyar kenan”. Ya juya ya ga Mubarak, ya ce.Me ke faruwa?”
Ya ce, “Haka na same ta, wai itama bata san
me ke damunta ba”.”ki dinga Istigfari kina Hailala, kina Salatin Annabi, duk suna yaye kuncin zuciya”. Ta mike don ta kawo masa abinci, ya ce.”Ki barshi kawai, kawo min ruwa ma ya isa,
anjima na ci abincin”. Ta kawo masa ruwa mai sanyi na randa a
sabon kwanon sha, ta tsuguna ta bashi, ya karba. Ya kalli Mubarak ya ce, “Kayi ciwo ne?”
Ya ce, “Me ka gani Baba?” Ya ce, “Duk ka kade”.
Ya ce, “Wallahi ba na iya bacci, ni kaina ban san me ke damu na ba”. Ta mike ta dauko takarda ta mikawa Malam Bala.
“Dazu aka kawo maka, amma ba su same ka ba, na karba na dangwala hannu”. Ya bude ya kalla, ya mikawa Mubarak ya
duba. Sai suka ga ya hade rai, ya zauna turus.
Malam Bala ya ce, “Ta meye Mubarak? Ni ba haya nake ba bare ince takardar (notice) ce, kuma ni ban yi tashin hankali da wani ba bare ince kuliya ke nema na. Dana fada min takardar meye?”
Idanun Mubarak suka yi ja kamar gauta, a hankali sai hawaye ya ringa biyo fuskar sa. “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan minha. Allah da Kai muka dogara, mun gode Maka, kuma muna neman taimakon Ka, kuma Www.bankinhausanovels.com.ng
muna neman mafitar Ka. Hakika Kai Ka so
rayuwar mu ta tafi a haka, Allah Ka zo mana da
agaji, domin mu din gajiyayyu ne, bamu da wani
karfi sai naka, Ya Allah”.
Mah ta ce, “Ka fada mana gaskiya”.
Ya ce, “Wannan bakar takarda ce, domin kirane daga kotun Musulunci, Hajiya Saratu tana karar Mah akan cewa danta Mubarak danta ne”.
Mah ta fashe da kuka, “Wai me yasa masu kudi suke da son zuciya da zarmewar zuciya? Wallahi ba ta isa ba, ko ina zamu sai munje, nima ba zan bar mata dana kwal guda daya, yaron da na sha wuya da rainon sa, yaro mai tausayi, yaushe ne za ta rabani da shi? Nima ko kashe ni za a yi ban bar mata yarona, sai dai in su kashe ni sannan
su dauke shi. Wayyo Allah na”. Ganin halin da take ciki duk yasa suka nutsu, kowa ya jure.
Malam Bala ya ce, “Kada ka damu, in su suna da kudi mu muna da Allah, Shi Ya yi mu Ya yi su, Shi ne kuma Zai shige mana gaba”.
Mah hankalin ta ya tashi, ta ga wa zata fadawa taji dadi? Ita ba uwa ba ba kuma uba ba, sai ‘yan uwan iyayenta, sai yayar ta Haj. Hadiza. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Bari in asubancin zuwa garin mu in sanar da dangina da duk wanda na san zai zamar min shaida, kuma su sa ni a cikin addu’a, domin abin ya fi karfin mu sai dai mu zubawa Sarautar Allah idanu”.
Da ta sanar da malam Bala ya ce, “Haka ne, kinyi tunani mai kyau. Ni zan je can garin namu, amma ki zauna ki samu nutsuwa”.
Ta ce, “Zan je gidan Haj. Hadiza, domin
dan uwa shi ne mai jin tausayin ka, ko magana mai
dadi ta fada min zan ji sanyi”.
Ya ce, “Shi kenan, a dawo lafiya”.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]