ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 9 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 9 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Sakar masa key din ta yi ta koma cikin gida da
gudu, bin ta ya yi da kallo fuskarsa cike da
damuwa yana mamakin abin da ta yi masa ya zai yi
ya bi ta, domin bai san kowa ya san da Wannan
matsalar tsakaninsu yake so su sulhunta hakan sai
ga shi Haana tana so ta fallasa kowa ya sani.
Misalin karfe biyar da rabi na yamma mota ta
yi parking a cikin    Dan fillo estate kofar gidan
Alhaji Jafar wanda muke yau ranar Litinin mota ce

taxi ta arport ta kawo Muhammad Jalar Nasir da
Kaninsa Abdurrahim ya fito daga cikin motar
yana mai mika hade da yi wa Allah godiya da ya
kawo su lafiya cikin zuri’arsu murmushi ya saki,
yammacin ya yi masa dadi haka kawai yake jin
wani irin nishadı yana ratsa masa zuciyarsa.
Cikin ransa ya ce, ‘Raihanatu gani nan na dawo
cikin rayuwarki nazo miki da wani irin big
surprise wanda za ki jima ba ki daina tunawa ba,
yau za ki ga Malam M.J dinki a matsayin baban
yayanki dan uwanki na jini, what is wounderful
surprise Raihana da zan ba ki a rayuwa zan so ni na
gan ki a haka ba ke ce za ki gan ni ba.
Abdul ya kai duba ga Yayansa ya ce, ‘Barrister
ya dai na gan ka sai wani nishadı ka ke ne me ka ke
dubawa ne? Www.bankinhausanovels.com.ng
Murmushin ya yi masa ya ce, “Ka share Abdul
yau jina nake so much happy kamar ba ni ba na ji
duk gajiya da damuwar suna barin jikina.
Gaskiya ne to mu karasa mana estate din
namu kamar ba kowa so silent and boring.”
Sun sallami mai taxi ya juya zai fara tafiya
kamar jira ake ya tafi sai suka ga jama a na fitowa
yara, mazza da mata.
Kannansu suka fara gani da sauri suka zo suka
rungume su duk daga cikin gidan nasu suka fito.
Mamaki ne ya kanma M.J da Abdul ganin tarin
Jama’a kamar wanda dama suke labe, nan fa suka
fara karbar gaisuwar kannansu da iyayensu da suke


tafe da Daddy dinsu a wannan lokacin suna sa kai
cikn gidan daidai lokacin da Haana ta cillo kan
motarta cikin Danillo Estate ta hangi tarin jama’a
da har gabanta ya ladi sai data karaso ne ta hangi
Jameel kanin Fu’ad ta tambaye shi me ke faruwa
nan ya fada mata cewar Yaya Muhammad ne suka
z0 da Yaya Abdurraheem.
Buga kanta tayi ta yi dariya ta ce, “This is
serious, Haana kin manta Fadeela ta fada miki
ne?
Yadda ta yi sai abin ya bawa Jameel darıya ya
ce, “Aunty you funny.
Dariya ta yi ta ce, “Ni din ce Jamel ya je abin
ka nima bari na karasa gida am so tired.
Haka ta tafi ta bar shi yana dariya sh dai haka
kawai yake son halin yayarsa kullum ka ganta cikin
nishadi ba ta da wata damuwa ga ta da yawan abin
dariya. Da wannan tunanin ya wanzu.
Lokacin da ta dawo gida ta iske Ya Abba ba ta
sakar masa fuska ba don ya gane har yanzu da
fushinsa a tare da ita. Cikin rashin sakin fuska ta
gaida shi ta ce, “Sannu da gida.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Duk da damuwar da ke fuskarsa sai da ya
danne ya yi murmushi ganin yadda ta turo bakinta
gaba ya ce, “Yauwa da fatan kin huce dai ko tunda
Granny ta sa baki?
“Ni ban huce ba. Ta fada tana kara tura baki
gaba.
Sai yaushe?
Bata rai ta yi ta ce, Please Ya Abba ka bar ni
na gaji.
To jeki huta ki raka ni gurin Haaya yau ko me
za ta yi sai ta fito mun hadu zuwana na uku ba na
ganinta Rauda ma ta je taki saurarenta, plcase
Sister ki taimaka min i nccd your help.”
Ganin damuwarsa duk sai taji babu dadi domin
ba ta jure son ganinsa cikin damuwa ba, sai ta ce,
Zan yi maka, amma nima sai ka yi min abin da
nake so anjima mu hadu tukunna.”
Tana gama fadin haka ba ta jira cewarsa ba ta
wuce abin ta.
Mintuna fiye da talatin da dawowarta kamar
yadda suka ce za su hadu sai ga ta nan har side
dinsa ta je baranda dinsa suka hadu.
Fuskarta ba a’ wani sake ba bayan ta gaida shi ta
ce Dama na zo ne mu yi magana kafin mu je gurin
Haaya din ina son ka fara yi min abin da nake so.”
“Fadi mu ji me ki ke so a gare ni?
“Ina son ka je ka samu Mr. Sameer ka ce ba
zan aure shi ba idan har da gaske yana so na to ya
auri ‘yar uwarta Rauda, domin ita ce take son shi
ba ni ba, ni kuma na yi maka alkawarin mantar da
Haaya neman Mustapha din ta za ta yarda ta aure
ka. Www.bankinhausanovels.com.ng
Dam! Ya ji gabansa ya fadi, amma sai ya cije
ya ce, Haana yaushe raini ya soma giftawa
tsakaninmu da ke ni za ki aika gurin saurayinki da
wannan maganar, are you nad?
Ta so ta dan tsorata ganin yadda ya daure fuska
sai kawai ta dake ta ce, “Ya Abba wallahi ba zan
auri Mr Samcer ba, matukar Rauda na raye duk da
tarin laifin da ta yi min dazu maganar Granny tasa
na sauko na yafe mata da har ta iya boye min abin
da take so idan har na yarda na aure shi ba zan iya
yafewa kaina ba wallahi idan ba ka fada ba zan
fadawa Abba ko da za a kashe ni ba zan yarda na
auri wanda ‘yar uwa takeso ba.”
“Dole ki aure shi Sister a da ke nan nake son
shi, amma ba yanzu ba na gama nazari da nutsuwa
babu wanda zan aura a yanzu sai Yaya Fu’ad
zuciyata ta gama nutsuwa da shi tun bayan
rabuwarmu shekaran jiya.
Gaba daya suka juyo jin muryar Rauda tana
fadi tana kuka., da sauri ta zo ta rike hannun Haana
ta ce, “Plcase ‘yar uwa ki yafe min I know ban
kyauta miki ba da ban fada miki abin da yake raina
ba, na yi haka ne ganin Ya Sameer hankalinsa ya fi
tafiya gare ki ban da wannan ban taba boye miki
komai na rayuwarmu da ke ba.”
Hankalinta ne ya tashi ta yi saurin saka hannu
ta goge hawayen da ke zubo mata ta ce, “Wallahi
ba zan aure shi ba tunda zuciyarki ta taba son shi
gwara ki hakura ki yarda ki aure shi.”
“Ni ma wallahi ba zan aure shi ba, ki tuna cewa
ke ma da bakin ki kin fada min kin gamu da son
shi lokaci guda, be sincere sister mu ajiye wannan
maganar ta wuce.
Ba ta wuce ba lokacinta ne kuma dole ne mu
yi ta kin rantse na rantse dole a cikinmu a ga wacce
za ta yi kaffara, don haka ki tafi babu ruwana da
ke.”
“Dole ki yi abin da na ce tunda ya za ki yi da
alkawarin da ki ka yi da Yaya Fu’ad ranar na zo
gurin ki aka ce min kuna baya ke da shi na z0 sai
na ji kuna magana na buya na ji duk abin da ku
ke cewa, kar ki manta kinyi masa alkawarin duk
abin da na ce za ki fada masa.
To na amince da shi shi zan aura babu fahi ke
kuma ya rage naki kin dai san girma da nauyin
alkawari, ni babu ruwana Yaya Sameer bai ce yana
sona ba, ni ce na ke son shi na boye a zuciyata ban
kuma san ya a kai ya san ina son shi ba, har yanzu
ina yi a kaina wannan tambayar na kasa samo
amsarta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Idan za ki hakura ki aure shi tunda na fada miki
Iya gaskiyata to ya rage naki idan kuma kin ki to ni
dai har ga Allah na gama abin da zan yi ki je ke da
Yaya Fu’ad ki fada masa abin da nace.
Tana gama fadin haka ta juya za ta fice, Ya
Abba ya dakatar da ita ya ce, ‘Ki tsaya ki gama
wayar mata da kai mun yi mata haka ne don farin
cikinta ba don mu hade mata kai ba, muna son ta
muna kuma son abin da take so babu cuta ko
ZURT’A
wariya a tsakaninmu dukkannin
DAYA NE babu bambanci sadaukar da farin
cikinmu shi ne makasudin zumuncinmu ba komai
ba.
Gaskiya ne Ya Abba.” Cewar Rauda.
Idan ku ka yi min haka kamar kun yi min dole
ne tunda na kira Mr. Sameer na fada masa ba zan
aure sh ba da kaina, to ba zan aure shi ba, da zan
aure shi ba zan kira shi na fada masa haka ba,
tunda ta nan ku ka biyo ni ce mai auran za ku gani,
yadda za mu yi da shi
Ya Abba an jima da kaina zanje nayi maka
abin da ka ke so gurin Haaya ba sai mun je tare ba
gobe ka je idan na shawo maka kanta maganar Mr
Sameer kuwa mun rufe ta da ku babu wanda zan
sake yi wa maganar ku jira ku ga yadda za mu yi.
Ficewa ta yi abin ta Rauda ta bi bayanta, suka
bar Ya Abba a gurin tsaye yana mamakin taurin
kan Haana da ta koya kwanan nan, bai so ta hana
shi su je tare ba, amma tunda tace haka dole ya bar
Ta gudun tashin balli.
Sai bayan ta yi sallar Isha lokacın ne ta fito don
zuwa gurin Haaya ta taci saa saboda tana shiga
gidan ita ta fara ganı, suna hada ido Haaya ta sakar
mata murmushi da ka ganta ka san tana farin ciki
ne da zuwan Yayanta. Haana ta wani karkace ta
harare ta ta ce, “Wa ki ke wa murmushi?’
“Ke mana ‘yar uwata, hala ke ma kin z0 gaida
su Ya: Muhammad suna sama gurin Daddy nima
abu na zo dauka tun dazu na ga kowa ban ganki ba
na fara tunanin meya hana kı zuwa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Daure fuska ta yi ta ce, “To sannunsu da zuwa
ni ba gurinsu na zo ba gurin ki na zo mu yi magana
Idan mun gama sai na je a gaida manyan yayana
da ban san su ba.
Oya mu je dakinki ban san kowa ya san na zo
baresu katse mu da abin da na zo miki da shi.
Za ta yi magana ta ja hannunuta suka yi
dakinta. dogon bayani da banbaki da tausarsa ta
fara yi a kan ta daure ta saurari Ya Abba bai
kamata tana wulakanta mata yaya ba, ba ta jin
dadin abin da take masa gaskiya.
Tun da ta fara maganar ba ta ce komai ba har
sai da ta gama, sannan tace, “Kin san kuwa mai ki
ke fada ‘yar uwa, idan sadaukar da farin cikinki za
ki yi a kaina to ki bari tuni ni na yi miki saboda
kokarin da ki ka yi min, kirkinki da kaunar da ki ka
nuna min yasa na janye kudurina.
Haana ko kin san Ya Abba shi ne Mustapha
dina da muka bazama nemansa ashe yana cikinmu
ba mu sani ba’?
Zuciyar Haana ta buga ta wani kankance idanu
ta ce, ‘Haaya dama ke ce Haaya din da Ya Abba
wadda naci karo da mail din ki kwanki?
Daga mata kai ta yi alamar haka ne.
“Ya Salam! Ta fada sai kuma ta dan yi
murmushi ta ce, ‘Ai faduwa ta zo daidai da zama,
kaya sun tsinke a bakiin kaba.”
Da sauri tace “Ba wani tsinkewa da suka yi
suna nan daure abin su kin tuno ni ko ya ba ki
labarina ko?”
Eh, ya fada mini na tausaya miki Haaya to ya
a kai ki ka gan shi bayan ba ku hadu ba?
“Au! Bai fada miki mun hadu ba, ai ba zai fada
miki ba tunda baya son bacin ran ki a kanki mun
sha fada da shi a school. Don haka ina mai muku
fatan alheri da samun farin ciki a cikin rayuwar
auranku na bar miki shi ki je ki aure shi.
Tsawa ta daka mata cikin masifa ta ce, °Haaya
me ki ke nufi da hakan a kan nace ki aure shi shi
ne za ki z0 min da wannan magana? To ki shiga
hankalinki ba na son haka.
Cikin daga murya Haaya ta ce, Dole ne na
fada miki haka saboda haka abin yake, Haana da
na tsane ki, na tsani jin sunanki gurin Mustapha
domin kece farin cikinsa ke ce kukansa, dariyarsa,
nishadinsa, ke ke ce dukkan wani feeling nasa, da
dukkan burin rayuwarsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Mustapha yana matukar son ki tiye da kansa
Zan iya fada mikı cewa bai san irin tarin son da
yake mikı ba, tsananin son da yake mıki ne yasa na
ji na tsane ki ganin babu sauyi yasa na zo masa da
cewa na amince ya fara auranki sannan ya aure ni.
Babu abin da Haaya ba ta fito ta fada mata ba
na iya rayuwar da suka yi har kawo wannan
haduwar da suka yi yasa ta boye kanta ta ki bari su
hadu ta kara da cewa.
Sister tun ranar da na gano cewa Ya Abba shi
ne Mustapha na yi kokarin cire shi daga raina
domin ya fada min ba zai taba aurena ba. idan ba
ke ya aura ba, amna ke duk da tarin yawan wannan
son da yake miki ki ka dage wai sai dai na auri
Yayanki. Plcase sister ki je ki auri Ya Abba domin
ke ce burinsa don ki ba shi tarin farin cikin da yake
nema gurinki tunda nake a rayuwa.
Ban taba ganin nutumin da yake son ki ba
kamar Ya Abba ba, hakan yasa na daina nuna
kishinki a gabansa, ganin nima ina son ki ya saki
ransa har na samu matsayi a gurinsa don haka ni
ma yanzu zan yi kokarin ganin ya same ki saboda
na samu labarin komai da kansa yace ya bar wa Ya
Sameer ke a gaban iyayenmu.
Tun da Haaya take maganar Haana ta rude ta
shiga tashin hankali ta kasa cewa komai tana
sauraron duk abin da take fada mata, jin batun
maganar Mr Samcer sai hankalinta ya kara mugun
Tashi.
Cikin rudani hade da wasu hawaye ta ce,
Haaya da gaske ki ke fada min wadannan
maganganun da nake ji?”
Gaskiya nake fada miki ‘yar uwa pleasc ki
daure ki koma cikin rayuwar Ya Abba yana sonki
ni kadai ce wadda zan iya fada miki  tarin son
da yake miki, na hakura da shi.”
Tana gama fadin haka wasu hawaye masu
dumi suka wanke mata fuska.
Dora hannu ta yi a kai ta yi kasa cikin kuka ta
ce, “Na shiga uku! Haaya me hakan yake faruwa
da ni? Wallahi ban san Ya Abba na sona ba.”
Kasa Haya tayi ita ma tana share mata hawaye
Tace, Calm down, “yar uwa kada ki daga
hankalinki shi kansa ya fada min a wancan lokacin
bai fada miki ba, mun rabu da shi idan ya dawo zai
fada miki na sha mamaki bayan na gano waye Ya
Abba naji kuma cewa shi da kansa ya ce ya bar wa
Yaya Sameer ke duba da irin mahaukacin son da
yake miki.
Amma na san tunda ki ka ga ya yi haka ya na
da dalilinsa na haka.”
Cikin wani irin rudani da masifa ta mike
hawaye na zubo mata ta ce, “Haaya yau za a yi ta
bari na koma gida at now ba ni da abin da zan iya
cewa da ke sai dai na ce na gode da ki ka fada min
gaskiyar abin da ban sani ba, ,na gode.”
Tana gama fadin haka ta fice a gaggauce ko ta
kan ta ba ta bi ba. Fitar ta ke da wuya Mal. M.J ya
Zo gurin ganin kanwarsa cikin damuwa da sauri ya
Zo gurin yana tambayarta meke faruwa don ya
ganta zaune kuma kamar tana kuka.
Da sauri ta goge hawayenta ta shiga kokarin
korar damuwar da ke fuskarta ta ce, Ya
Muhammad bugewa na yi da wannan kujerar gurin
yake min zafi shi ne nake kuka.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Dariya ya saka ya ce, “Hohoho! Haaya ban san
lokacin da za ki daina abu kamar su Amal ba to
tashi ki mu je ki dauko min abin da na aike ki ki zo
mu zanta da ke ina son jin abubuwa alot a cikin
family din mu tun zuwanku har kawo yau don
yanzu ke ce ‘yar gida yanzu na san kina da labarin
komai da kowa na family dinmu.
Murmushi ta yi kamar ba ta da wata damuwa ta
ce, “Za ka ji komai kuwa Yayana.
Shi ma dariyar ya yi ya kama hannaycmenta ya
langwabe har da wani cewa. “Wash!

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  gurina. Oya, …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *