ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 6 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 6 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

              Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

sun kara shakuwa sosai, domin ta gama gane
Haaya mutuniyar kirki ce har ta ji tana daina
kishinta saboda kyawun halinta ta ji tana jin za ta
iya taimaka mata ta so Ya Abbanta, ba don wai ba
ta son shi ba sai ganin kamar za ta iya ba shi farin
ciki saboda ta karanci kyawun tarbiyyarta kamar ba
wacce ta yi girman Turai ba, ko kadan cikin
halayenta ba ta ga mara kyau ba, donhaka take jin
idan Allah ya yi auran za su iya zaman lafiya, haka
ta dinga jin kamar za ta iya bar mata shi.
Da wannan ne ma ta fara jin gwara ta tsaya su
kawar da matsalarsu ita da Mr. Sameer duba da

zuciyarta ta kara jin za ta iya bar wa Haaya Ya
Abba saboda son da take mata da kuma shakuwar
da suka yi.
Karfe biyar jirginsa ya yi landing Fu’ad da
Al’amin da Kabir su ne suka je dauko shi a airport.
Ya ji dadin ganin ‘yan uwansa haka suka taho suna
hira har suka zo gida, nan fa ‘yan uwansa suka fito
yara da manya kowa sai wani nuna farin cikinsa
yake.
Haana na can gefe tsaye ta harde hannayenta
biyu sai wani kayataccen murmushi take yi da jin
dadin ganin yadda zuri’a dinsu kowa ke nuna
kaunar
Junansu nan ta godewa Allah da
daidaituwarsu guri guda, take ta ji Mr. Sameer ya
fado mata a rai, domin zuwansa rayuwarta ya kawo
mata abubuwa da dama na farin ciki a take ta ji yau


ta daina jin duk wani zafinsa, domin shi ne ya yi
mata sanadin wannan farin cikin da take yi a
yanzu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin wannan lokacin shi ma Malam M.J ya
fado mata wanda har yanzu yana can kasan
zuciyarta ta kasa fitar da shi ta manta da shi gaba
daya, ko ba komai shi ma addu’arsa ta yi tasiri
Cikin rayuwarta, saboda Allah ya amsa tunda ga shi
ya kawO mata mataimaki cikin rayuwarta har ta kai
ga cimma burinta.
Can Ya Abba ya hango ta ya ce, “My Swcet
SISTER ya ki ka tsaya guri guda ko ba kya murnar
dawowar tawa’?


Wani irin abu Haana ta ji yana taso mata a
Rantan zuciyarta kishi ne ko murna ita dai ta kasa
rabewa kawai sai ta ce, Shike nan Haaya bari na
koma sai na ji ki. Suka rabu a wayar.
Ya Abba yana lura da irin sanyin da jikin ta ya
Yi nan da nan ya ce  wai ya akai haka
na ga kin canza akwai damuwa ne?
Murmushi ta kirkiro ta ce, Babu komai Ya
Abba na bari na zo na yi sarbing dinka na ga su
Rauda sun kasa yi maka komai sun wani cika ka da
Surutu.
Dariya aka yi ya ce,Ban yarda ba kina dai
boye min wani abu ga shi nan fuskar ki ta nuna.
Oh! Ya Abba trust me mana. Ta fada cikin
gajiyawa da kuma kalar fuskar shagwaba.
Gaba daya gurin dariya aka yi, Rauda ta ce To
fa ai Ya Abba ya dawo yanzu za a dawo mana da
shagwaba dama kwana biyu an rabu da yi mana.
Nan Ya Abba ya yo caa kan Rauda nan fa aka
samu abin yi, haka kowa ya ci aka watse. Haana ba
ta yi wa Ya Abba maganar Haaya ba haka shi ma
bai mata ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan sallar Isha I ne suna zaune a karamin
falo suna hira shi da ita, ta tashi ta je ta dawo, tana
barin gurin sai ga sallamar Haaya ta ji falon tsit ta
Shiga mamaki yadda gidan nan yake da jama a yau
Ta ji shi shiru, sai ta fara tunanin cewa ko sun fita
ne saboda zuwan Ya Abba.Haana kawai sai taji kamar ba ta kyauta mata
ba, kawai sai ta yanke shawarar zuwa ta ganta ta ce
mata ta amince da Ya Abbanta ba ta ji wani shayın
zuwa ba, tunda ba ta san shi ba, bai san ta ba ko
sun hadu a hanya ba zai gane ta ba, tunda babu
wanda ya san juna.
Da wannan tunanin ta zo don hakajin gidan tsit
yasa ta fara tunanin komawa gida, ta kira tata wayar ta fada mata ta zo ba ta same ta ba.
Sallamar da ya jiyo ya sa ya baro falon don ya
ga mai sallamar, daidai lokacin da ita kuma ta bada
baya don juyawa ta fice, yana zuwa ya ga
gilmawarta ta baya ya ce, “Wa alaikumus salam wa
ki ke nema, Bismillah.
Da sauri ta juyo domin muryar da ta ji ta doki
dodon kunnenta, tsananin BUGUN ZUCIYA mai
hade da tsananin mamaki shi ne ya bayyana a
dukkan fuskoki biyun tare da shiga wani irin
rudani da damuwa na Zuciyoyinsu.
Mustapha!”
Haaya!
A tare suka ambaci sunayen junansu cike da
mamakin ganin haduwar da suka yi.
Da sauri ya karaso gurinta ya ce, “Haaya yaa
kai ki ka gane gidanmu, yaushe ki ka zo Nigeria
din?
Cikin kaduwa da tsananin harbawar da
zuciyarta take ta ce, ‘Mustapha dama kai ne Ya
Abba da ake min magana a kansa?
Eh, Haaya nine ya a kai ki ka san address dina
ki bani amsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wasu hawaye ne suka wanke mata fuska masu
cike da KUNAR ZUCI (Littafi na mai zuwa
kwanan nan idan Allah ya nufa). Ta ce, “nnalillahi
wa inna ilaihir raji ‘un! Na shiga uku!” Tana fadin
haka sai kuka ya ci karfinta, doleta juya da gudu ta
kasa tsayawa a gurin.
Shi ma wani irin rudani ya shiga cike da
mamakin faruwar wannan al’amari, nan take
zuciyarsa da tunaninsa duk suka yamutse ya kasa
yadda zai yi ya sarrafa tunaninsa wai yau ga Haaya
a cikn rayuwarsa ta dawo kuma bai tashi ganinta
ba sai a gidansu.
Ba dai ita ce Haaya din da su Abba suka hada
auranmu da ita ba’? Idan haka ne Haaya tana cikin
zuri’ a dinmu kenan ikon Allah Mai gima Shi ke
tsara yadda ya ga dama, ashe son da Haaya take
masa ba a banza ba ne, ke nan jininta take so.
A cikin wannan halin Haana ta zo ta same shi
ta ce, Ya Abba ina kuma za ka na gan ka a nan?
Da sauri ya juyo ya yi kokarın boye tashin
hankalinsa don kada ta gane cewa ya shiga rudani,
sai kawai ya soma in-ina da kame-kame daidai
lokacin da Granny ita ma ta kawo kanta falon ita da
Aziza Little ((Karama).
Da yake namijn gaske ne nan ya yi kokarin
danne duk kan damuwar da yake ciki ya koma suka
zauna suna cikin hirar su Abba ya kira shi a hankali
Haana take hira da shi kamar akwai wani abu da
yake damunsa yake kuma kokarin boye mata ta san
dai ba zai wuce a kan hadinsa da Haaya ba ne, don
haka tunda shi bai mata maganar ba, ita za ta rufe
Ido ta fara yi masa taji mai zai ce domin ta gama
yabawa da halinta gudun ta daya kada ya ce ba ta
yi masa ba.
Al amarin Haaya kuwa tana kOmawa gida ta yi
Saurin komawa dakinta ta shiga ta rufe ban da kuka
babu abin da take yi duniya ta yi mata zafi ta rasa
yadda za ta yi da ranta ta dinga jin kamar ba ta da
kowa da komai a duniyar ma bakı daya.
Yau ta kara sawa a ranta cewa ta kara rasa
Mustapha a rayuwarta da duniyarta ga baki daya, ta
san ma ba zai taba sonta ba, tunda da can bai so ta
ba Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba ta taba tunanin cewa Mustapha shi ne Ya
Abba da aka hada su da shi ba, ashe dan uwanta ne
na jini wanda suke ZURI’ A DAYA, shi yasa nake
tsananin sOn sa da kaunarsa.
Dole ne yau ta hakura da irin son da take masa
tunda ta gano waye shi wa kuma yake so, tana son
Haana ba ta jin za ta iya hada miji da ita, saboda
tuni ta gama sanin cewa a duniyar nan babu macen
da Mustapha yake so sama da ita, don ko ta yarda
Ta aure shi ba za ta taba samun abin da takeso a
gurinsa ba, don haka dole ta janye ta bar shi ya auri
wacce yake so. Za ta fito ta fadawa Daddy cewa ta
hakura da Mustapha dinta ba ta son Ya Abba su ba
ta duk wanda suka ga dama.
Haka ta wanzu cikn kullawa da sakawa a
Zuciyarta babu wanda ya san halin da take ciki
daga ita sai zuciyarta.
Haana kuwa kai komo take cikin falo tana jiran
Saukowar Ya Abba daga kiran da Abbansu ya yi
masa ta kasa Sakin r’anta tun ganinsa sauyin da ta
gani a fuskarsa ga shi kuma tana so ta yi masa
maganar Haaya.
Zaune ya hange ta cikinfalon ita kadai ta yi
tagumi da sauri ya karaso gurinta Sister Haana ya
dai na gan ki a nan ke kadai me ki ke jira ba ki je
kin kwanta ba?
Murmushi ta kirkiro ta ce, ‘Ya Abbana nake
jira domin ina son magana da shi.
Shi ma murmushin ya yi wanda daga gani ka
san da alama anyi shi ne don dole.
To gani ya aka yi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya Abba idan na fuskance ka kamar kana
cikin damuwa, kuma kana son boye min bayan na
ga komaiya bayyana a fuskarka. Please ya Abba
kada ka boye min damuwarka kamar yadda ba na
iya boye maka tawa.
Idan damuwar ka Haaya ka saki ranka na gani
halinta ba ta da matsala yarinyar kwarai ce ina mai
maka albishir ka yi sa’ar mata za ka yi farin ciki da
ita saboda na san irin taste din Ya Abbana tunda na
ganta na gane za ka so ta.
Haana ya akai ki ka san ina da damuwar da
nake son boye miki?
Murmushi ta yi ta je ta janyo hannunsa ta ce,
Ya Abba zauna mu yi magana.
Bai mata musu ba ya bi ta ya zauna inda ta kai
shi
Ya Abba kar ka manta tun ba yau ba muka
gama sanin kanmu da karantar duk abin da
waninmu yake so ko yake ki, tun ina karama ka
koyar da ni h aka, abin da yake Cikin Zuciyarmu
duk abin da
muna iya yin tunaninsa a tare sai mun bayyana shi
Sai mu yi mamakin ya a kai haka ta faru, tsananin
shakuwarmu da KAUNARMU ya sa muke tunani
Iri daya har ta kai mu da gano irin halin farin ciki
ko na damuwa da waninmu zai shiga, don haka
kada ka yi mamaki don na gano haka Jikina da
Zuciyata ne suka ba ni haka da kuma taimamkon
fuskarka da ta nuna min haka.
Ya Abba ka taimaka min ka so Haaya domin ita
ma tana cikin rashin wanda take so rana tsaka ta ji
an ce an hada ta da kai ba ta taba ganin ka ba, babu
yadda ban yi da ita ta gan ka a hoto ta ki, domin
tana jin zafin hadin da aka yi mata.
Haaya is a good girl Ya Abba za ka ji dadin
zama d aita, ni kaina yanzu wanda aka hadani da
shi ba son shi nake ba wanda nake so ya yi min
nisa don haka na hakura zan yi auren ne kawai.
Tana gama fadin haka hawaye suka wanke mata
fuska.
Zuciyar Ya Abba ta shiga kuna da wani rin
radadi na damuwa ganin hawaye a kan fuskar
Haana ya ji kamar ya je ya janyo ta ya hada da
jikinsa domin yadda yake jin zafin zubar
hawayenta Www.bankinhausanovels.com.ng
Da sauri ya kai hannu ya goge mata hawayen
ya ce. “Calm down Haana ban so kina zubar da
hawaye i promise you idan har za ki yi farin ciki da
na auri Haaya tunda ta yi miki nima ta yi min,
sannan ba na SO ki kuma cewa ba kya so Sameer
idan kina fadin haka zan yi fushi da ke tunda da
can kina son shi yanzu ma dole ki so shi.
SO shi,
Ya Abba ko ka san abin da yake mini?
Girgiza kai ya yi ya ce, Bana son jin abin da
Yake fada miki, 1dan ya fada miki yanzu wata rana
zai dauna, Haaya kuma ina sonta zan kuma SO ta
zan ba ta dukkan farin cikin da ki ke s0 na ba ta
matukar yin haka zai saki farin ciki ni kuma Ya
Abba zanyi miki shi.
Har cikin ranta sai da ta ji BUGUN ZUCIY ARTA ya karu jin cewa yana sonta, ina ma
a ce ita ya ce yana so da ta yi farin ciki, amma
tunda haka Allah ya kaddara mata rasa duk abin da
take so dole ta hakura ta karbi kaddara. A bayyane
ta ce.
Ya Abba me yasa ka fiye san farin cikina da
naka? Me yasa ba ka son abin da ka ke so sai
wanda nake so? Me yasa ka fi so na yi farin ciki
fiye da kai kan ka? Me yasa ka fiye ba ni dukkan
kulawa fiye da kanka? Duk abin da na ce ina so ko
ya yi maka ko bai yi maka ba sai ka ce kai ma kana
SO, to ban yarda ba Ya Abba daga yau na daina
yarda kana bin ra ayina, kawai yau dole naka zan
bi.Na san ka yi wa Abba biyayya ne kana da
wacce ka ke so ka hakura kabi zabinsu daga yau
Babu mai dane maka abin da ka ke so, ka fada
min nda budurwarka take ni da kaina zan je na
fada mata na kuma fadawa su Abba ga wadda ka
ke so, daga nan ni da kai mu tashi mu je mu taya
Haaya neman inda Mustapha dinta yake a kyale ku
kowa ya auri abin da yake so.
Ya Abba na san a takure ka ke ba son auran nan
ka ke ba, dole su Abba suka yi maka kana da
wacce ka ke so. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wa ya fada miki dole suka yi min, ni da kaina
na bawa Abba damar ya zaba min matar da ya ga ta
dace da ni, don haka yanzu sun zaba min na yi
na am da ita. Sannan idan na zabi farin cikin ki a
kan nawa ba laifi ba ne saboda irin hakan ne zai
sani farin ciki. Ki cire komai a ranki ki saka cewa
Haaya zabina ce ba zabin su Abba ba, ba dole suka
yi min ba. Saboda haka mu ajiye wannan maganar
ki je ki kwanta insha Allahu gobe zanje mu gana
da Haaya idan kina free sai mu je tare. Happy?
Ta dan murmusa, sannan ta daga masa kai shi
ma murmushin ya yi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sam daren yau ya nemi barci a idanunsa ya rasa
ya rasa me yasa ya ji ya kasa fadawa Haana
gaskiyarsa na cewa ya Jima da sanin Haaya tun a
baya hakan da ya yi duk sai ya ji kamar ya jefa
kansa cikin wani takunkumi. Me Haana za ta dauke
shi idan ta gano cewa dama can sun san juna? Bai
wani jefa kansa cikin wani dogon tunani ba, domin
ya ajiye wa ransa cewa gobe ne zai je su ga juna
kai tsaye da Haaya, yau ya kara sakawa ransa cewa
har abada shi da samun Haana a matsayin matarsa

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  gurina. Oya, …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *