ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 5 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 5 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

ya yi min auran dole.”
Da sauri ta zo ta rike ta ta ce, “Eh, My little Sis,
Daddy ya ba ni dama ki taya ni murna.
Duk suka saka dariya a gurin suna jinjina irin yar
surutu da wayon Afra yar kimanin shekaru shida
zuwa bakwai.
Cikin sanyin jiki ta shigo gidan, Mamah Me ta
gani a falo tana kallo ita da yara, gaisawa suka yi ta
ce, “Mamah Me ina Raudana.
Tana daki tun jiya ta zabawa kanta rayuwar
zama a daki sam ba ta san rabar jama’ a na yi mata
magana ta ki ji ba sai ta je ta yi ta yi ba, ita ta ga za
ta iya aure kuwa babu fashi tunda duk mu ma haka
aka yi mana kuma ga shi mun rayu babu abin da ya
faru da mu, gara ki je ki ba ta shawarar ta yi wa
mahaifinta biyayya tun kafin ya yi fushi da ita.
“Haba Mamah Me ke ya kamata ki kwantar
mata da hankali ba ki yi mata fada ba, kin ga sam
abin babu dadi.”

“To shi ke nan Ammina je ki ki wakilce ni kin idan kin gama ni kuma sai na dora a inda ki ka tsaya.
Ba haka ta so ji daga gare ta ba, don kada ta
tsaya su yi ta canjin magana ta juya ta tafi.
Kuka take tana ganin Haana ta yi saurin boye
damuwarta, don kada ta yi kukan ta gani, ta shiga
Rauda na ba zan hana ki kuka ba, ki yi
amsa mata sallamar ta.
kukanki ba zan hana ki ba, saboda damuwa aka
saki sai dai da za ki gane da sai na ce kin fi ni
cabawa saboda na yaba da halin Yaya Fu’ad yana
da kirki na tabbata zai saki farin ciki, ni kuwa da na
zaba da kaina yanzu haka da na sani nake wallahi.
Rauda yanzu ba na son Mr. Sameer na rasa me
yasa ko da yake dama ba cancan nake son shi ba.
Rauda son Ya Abba nake yi sosai a raina a Www.bankinhausanovels.com.ng
duniya yanzu ba wacce nake jin kishinta irin Haaya
tunda na ji an ce min wai ita aka zabawa Ya Abba
na tabbata Ya Abba ba zai so ta ba da su Abba sun
sani dama da ni suka hada ba da ita ba, idan ya so
sai su bawa Mr. Sameer.


Wallahi ba don kada na zo Ya Abba ya tsane ni
ba da na je na ce musu shi nake so tunda na rasa
Malam M.J nake ji a raina shi kadai zan iya rayuwa
da shi.
Rauda ko kadan yanzu ba na son Mr. Sameer
saboda kullum sai mun yi rigima da shi a kan Ya
Abba,
Abba, wanda hakan yasa ma ya dawo min da
Sonsa, ba na son kuma na bude ido na ga Haaya
kusa da ni domin jin hada auransu da wanda nake
So.
Rauda ba ta ce komai ba, har sai da ta tsaya da
maganarta cikin ranta ta ce, ‘Sister ba ki san halin
da zuciyata take ciki ba, a kan wanda ki ke cewa ba
Kya so da kin san kukan son shi nake da ba ki zo
min da Wannan maganar ba, sai dai kuma har abada
ba zan taba fallasa miki damuwar da nake ciki ba.
Rauda ta bude baki da niyar za ta ba wa Haana
amsa, sai ga wayar ta cika dakin da kara da sauri
Haana ta duba don ganin mai kiran wayar tsaki ta
yi ta yi cilli da ita gefe.
Rauda ta ce, Sister me ye haka kuma wa yake
kiran ki ba za ki daga ba, ai babu dadi.
Bata rai ta yi tana wani harare-harare ta ce,
Wannan yarinyar ce ko uban me za ta fada min.
Wacce ke nan? Www.bankinhausanovels.com.ng
Haaya mana ba ta san haushinta nake ji ba.
Duk da irin damuwar da Rauda take ciki sai da
ta yi dariya ta ce, “Sister kishi kumallon mata, to ai
ita ba ta da laifi please ki daga wayarta ga ta nan ta
sake kira, ki ka san abin da take tafe da shi.
Za ta yi gardama ta hana ta a dole ta daga ta
kiranta, don kafin ta daga har ta katse. Bugu daya ta
daga ta ce, Hello Sister dina ya ki ke.”
Yadda ta ji muryar tata sai ta ji kamar cikin
nishadi take wato dama so take, ta ji wani
wani haushinta.
Lafiya!” Ta fada a takaice.
Kin ji abin da su Daddy suka yi min ko wai
yayanki zan aura, please yar uwata zan zo mu yi
magana da ke don wallahi bana son shi ina da
wanda nake so na ji Daddy wai sai yabonsa yake
yana da kirki, ni ina ruwana da kirkin sa ni dai
please ki fada masa ya ce shi ma ba ya sona, don ni
ko waya ba zan masa ba, wallahi iya gaskiya nake
fada miki abin da yake raina ba zan iya auran
wanda bana so ba.
Ki jira ni anjima zan zo gidan ki ba ni shawarar
yadda zan yi na kuma fada miki yadda muka yi da
Daddy ke kadai ce wadda za ta iya taimaka min.
Kar ki damu sai kin zo din zan taimaka miki,
kamar yadda ki ka nema idan har zan iya.
Za ki iya ma saboda kina da kirki.
“To. Ta fada.
Suka yi salalma da juna.
Suka hada ido da Rauda da yake handstree ta
saka ta duk ta ji abin da ta ce.
Rauda ta ce, Haana iyayen mu sun jefa mu
cikin matsala garin gyara za su janyo matsalol─▒
idan ban da ke da Fadeela ba wanda nake gani yana
cikin farin ciki, domin ku ne kadai za ku auri abin
da ku ke so mu kuwa sai dai mu y1 biyayya.
Ki kwantar da hankalin ki ina miki hope a kan
Yaya Fu’ad za ki ji dadin auransa insha Allah,
yana da kirki ba na ji kin ce min ya kira ki ba ya ce
Allah ya ba mu ikon yin biyayya ba?
Haka ya ce, Www.bankinhausanovels.com.ng
“To kin gani wallahi Rauda za ki yi farin ciki
da auransa insha Allah, ni kuma zan Jira yarinyar
nan ta ZO zan ba ta duk wata gurguwar shawara don
kawai kada, ta samu Ya Abba saboda ban so ta
Zamo masa matsala ko ban aure shi ba zan so shi ya
samu wacce yake so yadda zai yi rayuwar farin
Ciki, amma tunda yarinyar nan ta fara da haka ina
gudun kada abin ya tabbata ta zo tana ba shi
matsala.”
Rauda ta ce, “A’a Haana kada ki cuce ta, ita ma
fa yar uwarki ce ba ki ji abin da ta ce da ke ba da
ba ta yarda da ke ba ai ba za ta fada miki abin da
ke ranta ba, just ki dauke ta kamar yadda ta dauke
ki wannan shi ne adalCi.
Shi ke nan kin kashe min jiki zan yi abin da ki
ka ce, amma wallahi 1dan na fuskanC1 tana Son shi
zan tsane ta ne kawai.
Dariya Rauda ta yi ta ce, “Hohoho! Sis ni ban
san ina za ki kai wannan dan banzan kishin naki ba
na son maso wani.
Rauda ba za ki gane ba ne ke dai kawai mubar zancen.
Kamar yadda Haaya ta ce za ta zo ba ta zo ba
sai bayan sallar Magriba, sun kule a dakin Haana
ta gama gaya mata duk yadda suka yi da Daddy
dinta ta kara da cewa.
Sister
“Sister Haana am Sorry to say bana son
Son
Yayanki, don Allah kada ki ji baushina ba laifina
ba ne laifin zuciyata ne, na san za ki fahimce ni ne
shi yasa na fada miki Fadcela ce ta gama fada min
komai a kan yadda ku ke ke da shi.
Hakan yasa na zo na same ki don na san ke
kadai ce za ki iya taimaka min. Sister ina so ki taya
ni ne nawa saurayin daga gobe nake so mu fara.
Zaro idanu Haana ta yi ta ce, Haaya kina da
hankali kuwa ta ina za mu fita nemansa ko kina
zaton Kano karamin gari ne?
Girgiza kai ta yi ta ce, “Na sani Daddy shi ma
haka ya ce min, amma ina da nawa tunanin na
gurinda nake zaton idan ina Zuwa zan iya ganinsa
saboda zuwa ire-iren gurin Hobbies dinsa ne.
Kin gane shi mutum ne mai mutukar son gurin
da yake da ni ima, yana son Zuwa gurin hutawa
mutukar gurin ya kawatu yana son ya samu gurin
da zai tsaya yana kallon raintall ire-iren wajajen
nan kan sa shi nishadi. Sannan yana son joint-joInt
ba don komai ba sai don kawai ya dinga samun
nishadi a zuciyarsa, haka zalika yana son zuwa
Malls kala-kala da dai sauransu.
Sister idan har za mu Juri zuwa ire-iren nan
gurin ina mai tabbatar miki za mu iya haduwa da
shi cikin sauki, plecase ki kai ni irin wajajan nan a
nan nake tunanin samunsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kan uba! Haaya kin zo da jan aiki, sam wasu
daga cikin ire-iren guraren nan ba gurin zuwana ba
ne, amma babu komai zan duba, amma don Allah
Jna son tambayar ki me Yayana ya yi miki da ba
kya son shi, kin kuwa ga haduwarsa? Bari na nuna
miki shi a hoto.
Cikim sauri ta ce, Sister kar ki damu ba sai na
gan shi ba, wallahi ni ba abin da ya yi mini, kidai
taimaka min da abin da na ce miki.
Babu yadda Haana ta iya dole ta amsa mata
abin da take so ba dan ta so ba, haka ta ji kishin da
take mata yana raguwa.
Kwanaki uku suna fita haka za su je su dawo ba
tare da kowa ya sani ba, domin rokon Haana ta yi a
kan don Allah kada ta fadawa kowa fitar ma tasu
Cikin satar jiki suke yi, duk fitar da suka yi idan sun
dawo babu nasara, haka Haaya za ta yi ta yi mata
kuka ita ke ba ta hakuri.
Haka Haana ta ji tana tausaya mata, ta ji tana
kara sonta, saboda wata irin shakuwa suke kara yi
duk abin da take fada mata iya gaskiyarta take fada
mata, don haka Haana ta ajiye abin da ta kudurta a
ranta ta zage za ta taimaka mata bil-hakki.
Haka dai kullum suke, domin dai Haana ta
kowanne bangare mai taimakon ‘yan uwanta ne ga
matsalar Fadeela da Yaya Muhammad ga ta Rauda
da Yaya Fu’ad, ta ki ta yarda ta ba shi zuciyarta.
Haka kuma ita Fadeela kullum zullumin ta
dawowar Yaya Muhammad tana jin tsoron kada ya
ce shi bai yarda ba, domin har yanzu ba ta ji ya kira
ta a waya ba, kuma ita idan ta kira shi baya nuna
mata cewa akwai wani abu da ya sani sai ya ce shi
ma yana nan daf da zuwa.
Abinciken da ta yi gurin Haaya ta fada mata
cewa Daddy ne ya ce kada kowa ya fada masu duk
yadda aka yi abu daya idan ta tuna yake sata
nishadi shi ne furucin da ya taba mata cewa idan
har Daddy ya yarda da auransu ba shi da matsala
da hakan wannan shi ne kawai yake kurar mata da
fargabar da take ji. Www.bankinhausanovels.com.ng
Don haka ta ki komawa Abuja ta ce ita ta zo ke
nan haka Mama Bara ta tafi ta bar ta tana zaune
gurin Hajiya Babba a cewarta ta fi son Yaya
Muhammad ya zo tana nan haka suke kowa ya
samu damuwa ko neman shawara a cikin su Haana
yake zuwa ma da ita, haka duk ta samu connection
da kowa ta san duk abin da suke so ta kuma ce
tunda sun ba ta wannan damar kowa za ta taimaka
masa da abin da ta ga za ta iya gwargwadon
Iyawarta.
Duk da kuwa ita ma tana da tata matsalar da
damuwar amma tana daukan tata da sauki saboda
cikin zuciyarta tana da dakiya sai dai ita ma da Mr.
Sameer babu wani sauki tun lokacin da akai abin
ya shiga hura hanci da nuna mata cewa yanzu ba
shi da wata matsala da ita, tunda kam dangi sun san
ta zama tashi don haka yasa ya ji karfin gwiwar
tafiyarsa South Africa, domin wasan Polo da za su
Je su ashirin aka zaba a Nigeria, da yake dama shi
ba aikin gwamnati yake ba, yana hadawa da
da
kasuwanci dinsa ne a Kasuwa Online.
Don haka ta tattara ta watsar da shi shi ne ta
Samu nutsuwar talalfawa ‘yan uwanta, tunda baya
nan bare ya hana ta sakat, sai dai haka zai neme ta
a waya suna ta musayar yawu duk yadda ya kai ya
lada mata magana mai dadi sai ta baude masa, da
ya fuskanci duk wayar da suke yi ba ta da hira sai
ta Ya Abba ya san tana yi ne don ta kona masa rai,
Sai ya fuskanci hakan sai ya mayar da babu wanda
yake so su yi hirarsa sai shi, tunda ta fuskanci ya
daina jin haushi ta hakan sai ta daina ma
Sauraronsa, idan ya bugo hirar ba ta wani armashi
haka zai rabu da ita, ba don ya so ba.
***
Yau Lahadi wanda a ranar ne Ya Abba ya yi
wata daya da sati guda da tafiyar da ya yi bayan
zuwansa LagoS, Sun wuce Abuja daga nan ne suka
nufi China ya samu tarin kyaututtuka (Awards) a
guraren da ya je wanda ya wakilci Abba ya dora
shi ne a kai domin yana son ya gama gane
makamar aikin tunda kusan komai zai danka masa
a hannunsa na manyan kamfanoninsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yau ne ake shirin dawowarsa shi kuma Mr.
Samcer lokacin satinsa biyu kenan shi ma suna
shirin dawowa. Gidan su Haana ya rude sai shirin
taryar zuwan Ya Abba ake yi kusan duk yawancin
yan matan family din duk suna gidan Haana ta
gayyace su su taya ta yi masa kayan kwalam da
makulashe, haka gidan ya zamo kamar wani
karamin biki su Fadeela duk an wani dage sai aikin
kayan fulawa ake tukuru
Rauda, Haaya, Yusra, Kubra, Nabiha karama,
kai ga su nan dai abin dai gwanin
sha’awa, family din dai dole ya burge ka
yadda suke abin su so da kaunar juna haka Granny
ta zo Cikinsu sai taya su hira take. Ammi duk
Jimawa sai ta leko ta yI wa ‘yan matan nasu sannu
Cikin jin dadi haka sauran suke saka Haaya a gaba
Suna ta tsokanarta wai ana sO ana kaiwa kasuwa,
nan ta kule ta bar aikin ta samu guri ta zauna.
Haana ce ta je ta shiga ba ta baki a kan ta share
Su ta zo ta yi aiki, babu yadda ba ta yi da ita ba da
Kyar ta shawo kanta, ta ce ‘Sister da kin bar ni ma
nake jn
na tafi gida wallahi na rasa me yasa nake jin
gabana yana faduwa na kasa samun nutsuwa, ga
shi kuma su Fadeela da Yusra sun sani gaba ni kam
ba na jin zan tsaya.
A’a Haaya na kada ki yi min haka ki rabu da
su ai ba Ya Abba ki ke wa aiki ba ni din ki ke wa
don ko ya zo ma ba zan taba nuna da hannunki
cikin aikin nan ba.”
Sister don ke zan yi babu komai mu je mu ci
gaba, amma dai ni faduwar gaban ya fi damuna.
Ki dinga addu’ana san kina tunanin
haduwarku da Ya Abbana ne kar ki damu nothing
can happen sai alheri, tashi mu je Ta karasa fada
tana dariya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tare suka jero zuwa wajen su Rauda su Fadeela
ba su fasa tsokanarta ba, ta yi banza da su kamar
yadda Haana ta fada mata, wani abin ma idan sun
yi Haana din ce ke tare mata.
A iya zaman nan da suka yi Haana da Haaya
sun kara shakuwa sosai, domin ta gama gane
Haaya mutuniyar kirki ce har ta ji tana daina
kishinta saboda kyawun halinta ta ji tana jin za ta
iya taimaka mata ta so Ya Abbanta, ba don wai ba
ta son shi ba sai ganin kamar za ta iya ba shi farin
ciki saboda ta karanci kyawun tarbiyyarta kamar ba
wacce ta yi girman Turai ba, ko kadan cikin
halayenta ba ta ga mara kyau ba, donhaka take jin
idan Allah ya yi auran za su iya zaman lafiya, haka
ta dinga jin kamar za ta iya bar mata shi.
Da wannan ne ma ta fara jin gwara ta tsaya su
kawar da matsalarsu ita da Mr. Sameer duba da

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  gurina. Oya, …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *