ZUMA CHAPTER 13 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 13 BY SHATUUU

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Na nufi wajen Daddy inata sakawa da kuncewa, Ina Kara weighing abinda na yanke, naje har kofar parlon se kuma na juya zuwa daki da sauri Ina girgiza kaina, is it a good decision I’m making? Ina Zama ummu tazo tace naje Daddy yana Kirana, hakan na Mike na fito zuwa parlon shi, gabana yana ta faduwa na wuce zuwa dakin nashi completely lost in thought. Yana tsaye yana gyara links din hannun shi, ya kalleni ya ganni kamar a birkice nake, yace

” Take it easy Mana, zauna”

Zama nayi jikina har rawa yakeyi, ya lura se ya miko min ruwan cikin tumbler yace

” Nanah meye ne matsalarki, ni nace kiyi deciding kuma ko meye decision din ki Zan saka Miki albarka”

Se naji na Dan nutsu, na gyara zaman nace

” Daddy Zan aura Abbah Prof”4

Na lumshe idanuna Ina adduar Allah yasa akan hanya nake, Allah yasa banyi zabin da zanyi da na sani ba. Wani murmushi Daddy ya sakar min yace

” Blessed you child! Ashe kina da hankali, Ina Miki fatan alkhairi a rayuwar ki,Ina fata zabin ki zai kaiki ga alkhairi. Kinyi tunani me kyau. Kije  ki ce mishi Ina son ganin shi da daddare yau dinnan!”

Se naji sanyi cikin Raina, na Mike jikina da kwari na nufi daki Ina jin farin ciki da cikar burin zuciyata. Da farko zuciyata na ingiza ni na karba Aliyu Amma ko kadan bayan nayi magana da hibba se naji mind dina duka sun canja, mindset Dina ya koma kan Abbah, bansan me yasa da nake kokarin zabar Aliyu ba, sede na kan kafa hujja da wannan na daya daga cikin hudubobin shedan lokacin da zakai abin kirki, musamman ma aure.

Ina na zaune sega kira da number dana goge dazun, hannuna nasa na dauka , kafin na gaishe shi yace min

” Why are you sorry?”

Nayi shiru Ina tunanin abinda Zan fada masa, se na tuna sakon Daddy

” Daddy yace ka sameshi da daddare”

Tabbas idan har zai dawamma da wannan farin cikin daya nuna min saboda zan zauna dashi inaga da tuni na kware shi kenan!

” Are you serious Amour? Bazaki gane irin farin cikin da nake ciki ba, Amma inshallah Zan nuna Miki shi a zahiri”

Nayi murmushi na jin dadin abinda yace, nace

” Then I’ll continue to make you happy forever!”

Nayi tunanin Yara ne kawai suke good in wordings se naga Shima ba baya ba, dukkan words din bakin shi are soothing, kalamai ne masu sanyi da sanyaya zuciya!

” Menene burin da kike son na cika Miki kafin na aureki?”

Nayi dan Jim sannan nace

“Burina naje wajen mummy kafin nayi aure sannan kuma na ganta a gurin bikina”

” Consider it done Amour!”

Da daddare wajen takwas Suka bayyana a gidan mu, Daddy yace ya bawa Abbah Prof aurena, ya yanke wata biyu kacal saboda yasan Abbah bazai so yayi ta jele gurina da girmana shi ba. Abbah ya gode ma Daddy tareda Masa alkawarin ranar monday zaa kawo kudin aurena da sadaki na. Cikin girma da mutunci aka gama komai, har zasu tafi Abbah ya dubi Daddy yace

“Daddy Ina Neman wata alfarma”

Daddy yace

” Prof menene?”

Yace

” Ina son na kai Fatima Niger idan ka yarda”

Daddy yace

STORY CONTINUES BELOW

” Why not! Babban dalilin hana Fatima zuwa gurin Aisha saboda Fatima Tasha wahala, nafi son duk ranar da zata je taje Mata complete human, nasan nayi kuskure sosae a rayuwata,da zaa dawo da lokaci Dana gyara. Nayi alkawarin se ta samu miji ta gama karatu sannan zata je. Duk lokacin daka shirya se ku wuce”

Abbah yayi mishi godiya sosae sannan Suka tafi, Babu Wanda ya fada min abinda ke faruwa, washegari Monday Abbah Suka kaso kudin nema Dana sadaki, Daddy ya kirani ya bani a hannu yace

” Na bada auren ki, Ina fata wannan zabin naki ya dawammar Miki farin ciki har karshen rayuwar ki”

Kasakasa na amsa Amin sannan na aje Zan fita,wayar Daddy ta fara ringing na Mika masa jin ya ambaci

” Tana asibiti? To zata taho yanzun! Allah ya sauketa lafiya!”

Ya aje wayar yace min

” Amina na labor, Salem yace ko Zaki je?”

Kaina na gyada Ina jin anxiety yana kamani, Kaya na dauka ban fadawa sauran ba na tafi driver Dan zasu iya cewa zasu bini, a general ya kaita Ina shiga matron din na zuwa, Dan dama tace masa duk lokacin da matar shi zata haihu ita zata karba Dan uwar dakin shi ce. Tare muka zauna bayan na shiga naga ba yadda take duk jikina yayi sanyi, wajen karfe daya na dare ta haihu, ta samu baby boy. Ni aka fara bawa bayan matron ta goge shi tas, na saka Masa Kaya na rungume shi Ina jin tsantsar kaunar shi, tamkar Salem yayi kaki ya tofar. Se asuba na fara fadawa mutane, Abbah Prof ya fara Kirana Dan tunanin shi Ina gida

” Amour voice din ki kamar baki bacci ba”

Na danyi dariya Ina jin dadin yadda yake fahimtar duk yanayin danake ciki, nace

” Tun eleven Ina asibiti Amina ce ta haihu”

” Shi ne baki fada min ba, Allah ya Raya me aka samu?”

” Ina bada hakuri, naga it’s late May be kana gida shiyasa. It’s a baby boy”

Ya mishi addua tareda ce min whenever nayi tunanin yana gida I should text him, sannan yace kafin yaje office zai leko mu. Da mukai sallah na fara Kiran Yan uwa Ina fada musu, Yaya Rahma dake a gari a asuban ta karaso muka hadu muka gama komai, Nawwara da Amal Suka tafi gidan Amina Dan kintsawa kafin mu dawo, Daddy wajen six yazo, a waje aka saka masa kujera ya zauna sannan Salem ya kawo mishi yaron ya Masa huduba, Salem yace

” Daddy kayi Masa huduba da Ibrahim”

Munji dadin karar da yayi Mana, aka rada Masa Ibrahim na saka masa Abid. Se na tuna ai baban Salem ma sunan shi Ibrahim, yaro yaci suna biyu kenan. Yan ward dinsu Wanda suke night da Wanda Suka fito morning duk sunxo. Wajen seven Abbah ya karaso, ni na taho dashi daga inda sukai parking,

” Baki ya kasa rufuwa anyi da”

Na Kara sakin murmushi nace

” Ba zaka gane ba”

Yayi dariya yana mishi addua, muka karasa ya dauki Abid ya mishi addua sannan yace

” Nanah karbe shi”

Bakina na tura gaba nace

” Ni fa mummy ce yanzun, shi ne zaka ce min Nanah”

Salem yayi dariya, shi kuma Abbah Prof yace

” To Amour tayi hakuri, me Zan dinga ce Miki?”

Ya fada yana sukuyowa daidai tsayina, tareda leka fuskata har Ina jiyo numfashin da yake fitarwa. Juyar da kaina nayi Ina fadin

” Ni ka tafi!”

Ya kalli Salem dake kallon mu yana murmushi yace

” Kaji korata take”

STORY CONTINUES BELOW

Kafata na Dan buga nace

” Ni fa kawai kaje kada ka makara”

Se ya gyada kan shi yayi gaba bayan ya Kara yiwa Salem barka, Salem ya kalleni yace

” Mom wai ba Zaki je rakiya ba?”

Se na Mika ma Salem Abid din na bi bayan Abbah na dake tafiya a hankali yana waya, suit din da yasa sun mishi kyau, ban taba ganin shi zaije office ba se yau, seda muka karasa yace

” Hanoon na gaishe ki”

Ya bani kudi na bawa babyn mukai sallama na koma, wajen nine akai discharging dinmu muka koma gidan ta bisa umarnin Daddy, muna zuwa muka tarar mahaifiyar Salem tazo, matar me kirki muka gaisa ta karbe shi tana ta Masa baa Ina Rama Masa, ni na zauna tareda su, daga baya kanwar ummanta tazo muka zauna tare. Da yamma na gama wankin babies Amal ta kawo min wayata wai ana Kirana, Ina karba nasan Aliyu ne, ni na manta dashi ma gaba daya, na manta nace Masa zanyi tunani. Bayan min gaisa na Kara Masa gaisuwa, yace

” Ina ta jiran Kiran ki ko na Daddy Amma naji shiru”

Nace

” Ni fa gaskiya I can’t do this, already ma na cewa wani ya turo, aure zanyi”

” Dama Zaki iya Zama da wani bayan ni?”

Se na Masa banza Dan tambayar ta Bata min Rai sosae, yace

” Kin manta munyi alkawarin Zama da juna…”

Da sauri na katse shi da fadin

” Dan Allah cut this, Kai hakuri Amma bazan iya aurenka ba”

” Saboda me?”

” Banida dalili”

Ganin zai Bata min Rai yasa na kashe wayar kawai na cigaba da sabgata ba tareda naji komai ba, nan na Kare tabbatar da am done with him!ya dinga Kira naki dauka se kawai na kashe wayar baki daya.

Da daddare Abbah ya koma gida bayan ya Kara biyowa gidan Amina ya ganni, wanka yayi ya shirya cikin jallabiya sannan ya kirani ganin mummy ta fita

” Kin manta na taho ne?”

Nace

” Yanzunnan nake son na kiraka fa!”

Yayi dariya yace

” You always find words to cover yourself! Zanje masallaci”

Na mishi Allah ya kiyaye sannan mukai sallama, bayan ya dawo daga sallar Isha, as usual dukka Suka zauna Dan cin abinci, seda suka kammalla tsaf, Yasir ya Mike zai tafi Abbah ya tsayar dasu. Ya Jima shiru yana tsara yadda zai fada musu maganar da yake so, words din ma sunki haduwa, se can yace

” Ina son na fada muku dukkan ki cewar nan da two months to come zanyi aure!”

Adnan da Yasir ne Basu son zancen ba hakan ya girgiza su, Adnan ya dubi Abbah yace

” Aure kamar Yaya?”

Kafin Abbah yayi magana mummy t ace

” Ungo nan! Is that how you address your father?”

” I’m sorry! Ina fatan zaku min biyayya, karku kalleta yarinya kuyi Mata abinci kuke so, I won’t take such, she’s my wife Dole ku Bata wannan girman”

Daga haka ya sallame su , shida mummy suka wuce daki, kwanciyar tayi kan cushion tana jin zafi a kirjinta, Zama yayi gefen ta, tareda birkito da ita tana facing dinshi, da sauri ya fara goge Mata hawayen da suke sauka, yace

” Kiyi hakuri! I promise you aurennan will change nothing, idan da nasan bazan iya adalci ba, bazan tarke shi ba. I know I’m a bit selfish da Zan Miki wannan maganar, Amma I’m still going to ask ki cigaba da supporting dina, I’ll not let you down inshallah!”

Daga karshe ya rungume ta, har seda kukan da take ya sassauta kafin kuma ya daura bakin shi kan nata. Washegari kamar ko da yaushe, da yamma ya dawo yasan mummy Bata nan, tana compound duty so Bata fita da safe ba, seda yayi waya da dukkan yaran Suka tabbatar Masa sun dawo har Adnan da ke fushi dashi. Tun a parking lot yasan sunyi baki, yayi parking tareda daukar backpack dinsa da kuma leda yayi ciki, kamar yadda yayi tunani Hafsa ce sister Barira, tana zaune se masifa take masu Yusuf Wanda su kuma se kallonta Suke kamar tababbiya. Yana shigowa ta Mike tareda fadin

” Da Zan tafi ganin shiru shiru baka dawo ba!”

Ya samu guri ya zauna yana duban yaran nashi with concern tareda tambayar kowa yadda ranar shi ta kasance, ya dubi Hafsa yace

” Guri na kika zo ne?”

Ta koma ta zauna tana kallon Abbah, dukda kwarjinin da take Mata,ta kudiri niyyar ita fa se ta kwatar ma yayarta yanci. Tace

” Ba gurin ta nazo ba, saboda ita Bata dauke mu Yan uwa ba. Naji zakai aure  da gaske ne?”

Ya kalleta yana mamakin halin Hafsa, ya Jima yana tausayin mijin ta, yanzun idan ba shirme ba meye ruwan ta da matsalar gidan shi

” Aure zanyi kamar yadda Kika sani to every rumor akwai traces na gaskiya”

” Wallahi baka Isa ba, kayi kadan ka tozarta min yayata, Kai ko kunya baka jiba da girmanka ka tsiri aure?”

Da mamaki yace

” Ban Isa ba? Ke wacece da Zaki fada min hakan? Mind you wannan gida nane, it’s my own territory, baki Isa kiyi questioning hukunci na ba, ki tsaya matsayin kanwar Barira Kar kisa na Bata Miki”

Daga haka ya juya zai tafi, taci darajar Barira da kuma su Hanoon dake zaune, yasan Hafsa ba tada hankali but Bai San abin yakai haka ba.

” Dama haka kuka iya, idan an taba ku kuce Sunnah, tsoho da Kai….”

” Anty Hafsa!”

Adnan ya fada cikeda tsawa Wanda yasa Abbah juyowa, yaga Adnan na tsaye yana haki, Yusuf ya bude Mata kofa Dan tare Suka Mike yace

” Anty Hafsa Dan Allah ki tafi gida, we’ve had enough, Abban mu ne Dole mu Goya mishi baya,Babu ruwan ki cikin maganar mu.”

Abbah ya girgiza Kai ya wuce parlon shi yana ayyana abubuwa da dama, irin wannan mutanen su ke saka Mata bijirewa mazajen su!Se dare mummy ta dawo, har lokacin Abbah Bai dawo a masallaci ba, yana can tunda ya tafi sallar maghrib, da aka idar yaran sun San se yayi Isha kafin ya tafi se Suka barshi, Suka dawo Isha still yana zaune a sahun farko, bayan an idar Suka ce ya taso su wuce gida yace suje zai taho, da farko sunki tafiya su lallai se ya tashi da suka gaji se Suka tafi gida suna jiran mummy ta dawo su fada Mata. Ile kuwa tana shigowa Hanoon ta fara fadin

” Mummy Anty Hafsa tazo ta zagi Abbah tas a gidannan”

Da rashin fahimta tace

” Wanne zagi kuma Hanoon? Ita Hafsar hauka ta fara da zata zagi yallabai?”

Yusuf ya zauna ya Mata bayanin komai, mummy Bata da hayaniya, tayi shiru kafin ta Ciro wayarta daga hand bag din data shigo da ita ta fara Kiran Hafsa, a ringing na biyu ta dauka

” Hafsa kin zo gidan da nake ne?”

” Nazo Yaya, hajiya lubabatu tace min mijinki zaiyi aure…”

” Kina da matsala da hakan? Ina ruwan ki! Ke zaayiwa ko ni?..”

” Amma Yaya..”

Itama ta katse ta da fadin

” Karki Kara min katsalandan cikin gida na, Babu ruwan ki, idan yayi aure meye damuwarki?”

Tana gama fadan ta Wanda yake a sanyaye Zaki dauka ba fada bane. Tana aje wayar Abbah na sallama, sauri ta tashi tana fadin

” Yallabai barka da dare”

Zama yayi gefen ta yace

” Barka dai gimbiya an tashi ko gudowa kikai?”

Yasir Suka fara dariya, mummy ta Bata rai tace

” Ni ce me gudun aikin, haba !”

Yayi ta tsokanar ta Dan ya nuna mata maganar da Hafsa tayi ta wuce, ganin hakan yasa hankalin su duka ya kwanta. Nikam har na gaji da jiran kiran shi kamar yadda ya sabar min, jin shiru yasa ni na kirashi Amma Bai dauka ba har na fara bacci. Seda ya shiga bedroom din sa sannan ya tuna rabon da muyi waya tun yana office, yayi tsaki ganin calls dina da yayi missing hade da message Ina tambayar shi ko lafiya? Bai kirani ba saboda yasan nayi bacci, mummy ta shigo ta gama Shirin ta tsaf na kwanciyar, Zama tayi tana fadin

” Ango wai me kake shiryawa ne”

Yayi murmushi tareda hararta yace

” Abin har da zolaya?”

Se tayi dariya tace

” Naga baka fara clearing gurin da zata zauna ba, ko wani gidan zaka bata daban?”

Ya Dan shafa kanshi yace

” I was thinking of that too, Amma naga gwara ta zauna nan, Dan na samu na nutsu a guri daya”

Ta gyada kanta kawai tareda kwanciya tace

” Allah ya Sanya alkhairi”

Amin ya fada yana pecking dinta a forehead, sannan yace

” Friday zamu je Bidda, Zan tafi da Yusuf saboda I can’t drive for long”

Kai ta gyada tace

” Yan Bidda ne su?”

Yace

” Her mother Amma su Yan hadejia ne”

” Allah ya kaimu”

Yace Amin ba tareda ya fada Mata cewar I’ve never met my mom ba, a ganin shi wannan magana ce tsakanina dashi, yadda bazai dakko personal maganar ta ya fada min ba. Duk yadda kuke tunanin Abbah husband material ne to ya wuce haka, Zan yiwa kowacce mace fatan samun Abbah na❤️.

STORY CONTINUES BELOW

Da asuba yayi ta Kirana naki dauka, ni a Dole nayi fushi, dana idar da sallar se na saka ta a silent na kwanta wai zanyi bacci, Amma na gagara kuma ego ya hanani na duba wayar balle na dauka ko na kira. Amina ta shigo hannunta rike da Abid daya tashi yana karamar rigimar da ya saba, Zama tayi tana fadin

” Yaya Nanah baban Abid yace wai Abbanki na kiranki”

Nace

” To naji”

Se ta Mike ta fita kawai, na Mike Nima na shiga toilet na tsiri wanka ni a Dole bandamu ba, Ina fitowa na samu Amina na jirana, kallonta nayi nace

” Meye?”

Tace

” Allah yaya Nanah bakida kirki, kije yana parlor yana jiran ki”

Na saki murmushin nasara, feeling on top Dole azo a bani hakuri, nasa kayana na fito inata Bata rai, yana zaune an aje Masa mug da coffee a ciki, se biscuits irin sugar free dinnan, tunda na karaso yake kallona har na karasa Zama nace

” Abbah!”

Salem ya bamu guri sannan yace

” Nanah me yasa baki daukar wayar ki”

Na Bata Rai Ina turo baki nace

” Bayan jiya inata kiranka baka dauka ba”

” Amma Amour kinsan hakan kurum bazan ki daukar wayar ki ba, I left the phone at home, naje masjid ban dawo da wuri ba, lokacin da na dauka wayar I’m sure kinyi bacci. I’m very sorry kinji my dear?”

” Ni nayi fushi fa”

Ya Kara gyara zaman shi yace

” Amour case! Nace fa kiyi hakuri gashi nazo rarrashin ki. Kuma kinsan me ranar Friday zamu je Bidda fa”

Se na manta ma fushi nake dashi, kunsan kadan ya rage ban fada kanshi ba fa, ya dinga min dariya yace

” Shiyasa naki fada Miki nasan Zaki ta dauki”

” Wallahi yau Zan tafi gida na hada kayana”

Yace

” Yusuf will be excorting us, se ki samu ko su lubna wani ya raka ki.”

Ya Mike bayan ya kalla wrist watch din hannun shi yace

” Amour lemme be going kada ayimin bulalar latti”

Nayi dariya tareda mikewa nabi bayan shi, amidst hallway din nace

” Baka Sha coffee din ba fa, nasan baka Sha komai a gida ba”

Ya dan yatsina fuska yace

” Bana shan coffee, I’m sorry idan naje office Zan ci wani abun”

Se na gyada kaina kawai na raka shi har bakin motar shi, bayan ya shiga yace min

” Zan je naga idan na gama dukka aikin we’ll be leaving early in the morning, idan kuma akasin haka to gobe after Jumat prayers!”

” Allah ya kaimu!’

Ina komawa ciki bayan ya tafi na fadawa Amina latest, ta dinga murna at the Same time tana jin haushin ba ita zata rakani ba, wajen nine bayan nayi wanka na koma gida na samu Daddy ya tafi office, Amal ta koma school itada Aisha, Nawwara nada lecture ta shiga school, lubna na asibiti se ummu dake secondary itama ta tafi. Ni daya na dauko madaidaicin trolley na hada kayana, dukda bansan kwana nawa ne zanyi ba Amma dai na deba wajen na one week! Na gama komai sannan na Kira hod dinmu nace yayi min afuwa tafiyar gaggawa ta Kama ni, seda ya gama min lectures din shi wai aikin asibiti ba hakan ake ba, ba yadda zaayi all of a sudden kace zakai tafiya, ganin zai Bata min lokaci yasa na fada Masa I’m meeting my mom for the second time in my life! Tuni yayimin fatan alkhairi akan zai samo wani yayi covering duty na.

Lubna Daddy yace ta rakani tunda se bayan Jumat zamu tafi, itama ta hada kayanta, na Kira sauran duka nace zanje Niger su Kai min addua tareda bada sakon gaisuwa wajen Anty Aisha, su da suka Santa kenan. Daddy ya bani kudi yace na rike Koda zamu bukaci wani abun. Misalin daya muka dauki hanya washegari, Abbah da Yusuf na gaba ni da lubna a baya, tun kafin mu bar dutse na fara bacci saboda Daren jiya doki bai bar ni nayi baccin kirki ba, na Jima Ina bacci har muka zo Zaria Shima Abbah be yace da lubna ta tashe ni min tsaya zamuyi sallah.tashi nayi ya dube ni yace

” Sleepy head!”

Murmushi kawai nayi mukai sallah, Yusuf yayi Mana take away sannan muka Kara daukar Hanya, Yunwa nake ji Amma se naji abincin ya fita daga kaina, tun lubna nace min naci har ta kyaleni, Bata San lokacin tsoro ne da fargaba sukai min dirar mikiya ba, shi Bai lura banci abincin ba, yana kuma kokarin kamewa tunda Yusuf da lubna na tare damu. Seda muka kusa Minna sannan na fara jin alamar I’m having attack, hannuna na matse Ina adduar Allah yasa kada yazo Dan attack dinnan embarrassing dina yake, Amma Ina addua ta Bata karbu a lokacin ba, lubna ta fara lura tunda ita ke kusa dani,

” Abbah”

Ta fada  tana riko hannuna, juyowa yayi ya dube mu, idanun shi a warwaje yace

” Yusuf tsayar da motar!”

Parking Yusuf yayi Abbah ya fito a kidime ya bude side din da nake, ya ruko hannuna yana fadin

” Me ya faru? Lubna!”

Lubna tace masa dama Ina yin hakan duk lokacin da na Zama anxious, Yusuf ya mike daga duken da yake yace

” Panic disorder ne”

Leda ya miko min yace na hura, tun karfina na hura se naji na fara calming, Amma har lokacin jikina na rawa kuma gumi ya jikani sharkaf! Lubna ta koma gaba , Abbah ya dawo gefena, gaba daya hankalin shi a tashe, hannuna nasa Ina share zufar dake keto min,

” Are you ok?”

Kaina na gyada nace

” I’m sorry!”

Se na fara kuka a hankali, ya zuba min idanu Yama rasa me zaice,

” Akwai inda ke Miki ciwo ne?”

Kaina na girgiza yace

” To kukan me kikeyi?”

A hankali nace

” Tsoro nake ji, kada naje na tarar ta rasu”

” Haba Amour brace yourself, I assure you inshallah lafiya kalau zamu same ta”

Ya cigaba da kwantar min da hankali har na Dan saki jiki, ya dakko wayar shi yana nuna min inda yake gyara min Zan zauna, wani nayi dariya nace yayi kyau, wani nayi squealing wani kuma na Bata Rai nace nidai se an gyara, soyayya ZUMA ce da muka Sha se muka manta dawa muke tare, Ashe Suma tasu hirar suke cikin jin dadi!

Tafiyar awa wajen bakwai da wani Abu mukai kafin muka Isa Bidda, Shima mun kusa awa daya Muna Neman gidan, seda mukai tambaya sannan aka kwatanta ma Yusuf. Jikina a sanyaye na kalli Abbah, gyada min kan shi yayi yace

” It will be ok, I got your back Amour”

Da wannan kalmar naji hankalina ya Kara kwanciya, a kofar gidan mukai parking, ana ta kokarin shiga sallar Isha, da muka fito Yusuf ya Kara tambayar gidan aka tabbatar Masa inda muke tsaye ne. Abbah ya dube ni Ina kokarin stretching hannuna yace

” Amour ku shiga ciki, zamu shiga masallaci”

Kaina na gyada tareda daukar hand bag dita muka shiga ciki, na dinga juyowa Ina kallon Abbah dake tsaye yana min murmushin Kara min karfin gwiwa, gidan babban gida ne, mansion me part da Dan dama a ciki, a gate duka security Babu ko daya hakan yasa muka shiga ba tareda ansan da shigowar tamu ba, a katon parking space din muka tsaya na dubi lubna nace

” Lub Ina zamu shiga?”

Inda yafi kusa damu nan muka nufa, knocking mukai daga ciki aka ce mu turo kofar, lubna na gaba Ina biye da ita, Muna shiga muka tarar da tsohuwa zaune akan sallayya ta idar da sallah!Bakin mu dauke da sallama muka shiga ni da lubna, looking tired and exhausted, Babu abinda nake muradi a lokacin irin naji ruwa a jikina, tafiyar awa wajen takwas ba Wasa bace, parlor ne me kyau Wanda ya kayatu da hasken bulbs da chandelier,manyan leather seat sun Kara kayata parlon, a tsakiyar parlon dattijuwar ke zaune kan sallayya da casbaha hannunta, idanunta sanye da farin medical glasses, zaune kan kujera wasu Yan Mata ne zamuyi kusan saanni dasu kowacce tana daddana wayarta, a hankali muka tako ciki jin an amsa Mana sallamar, matar tunda muka shigo take kallon mu har muka karaso ciki, tace+

” Sannnun ku da zuwa! Ku zauna”

Muka zauna lubna ta fara gaisheta sannan ta Dan matsa gefe yadda Zan bayyana dan ta kareni, na gaisheta se naga Bata amsa ba se tsura min idanu da tayi,daya daga cikin Yan matan tace

” Kai! Murya sak na Ummiey!”

Kallon sashen ta nayi muka hada Ido, ta cigaba da Danna wayar ta, dama dayar ko dagowa batayi ba. Tsohuwar tace

” Zo!”

Ta fada tana miko min hannu, a hankali na karasa na kama hannun nata inajin wani feelings me sanyi yana mamaye min zuciyata, ta rike ni gam kamar Zan gudu nace Mata

” Daga dutse muke, jigawa”

Fuskarta ta Kara haskakawa da murmushin da take tace

” Dama na fadawa Aisha Zaki zo da kanki Neman ta, gashi kuma Allah ya nuna mana wannan ranar!”

Idanuna na lumshe inajin wani Abu me tauri daya tokare min wuyana more of a lump ya sauka. Idanuna Suka cicciko da kwalla nace

” Tana Ina?”

Dagowa tayi tace

” Hasina bakuga anyi baki ba?”

Wadda aka Kira da hasina ta aje wayar tace

” Sannnun ku da zuwa”

Lubna kawai ta amsa Mata nikam bakina yayi nauyi, kallon ta nayi Ina ganin tsantsar farin cikin da take ciki, tabbas ganin wannan farin cikin daga gurin ta kawai ba daga gurin uwar data haife ni ba yasa nasan sun Jima suna jirana,

” Noor! Kaisu daki ko zasu shiga toilet!”

Noor din ta kallemu se kuwa tace

” Nanne kiga kamar face din Ummiey?”

Tsohuwar da aka Kira da Nanne ta Mata magana da yare, tayi tsalle tareda kankame ni kamar zata balla ni, dayar ma ta taso suna ihun murna. Seda Nanne ta Kara musu magana sannan Suka sakeni, na dubi Nanne nace

” Ba mu kadai bane akwai baki a waje!”

Se ta dubeni tareda mikewa tace

” Saboda wauta shi ne Kika bar su a waje, kije zaa shigo dasu”

Tare da Noor da Hasina muka nufi wani daki da ke gefe, ni na fara shiga nayi tsarki da alwala na fito, lubna ta shiga na dubi Noor da take ta kallona tana yiwa Hasina magana da wani yare, sallayyar da aka shimfida na hau nayi sallah anan lubna ta fito muka idar sannan na Ciro wayata daga jaka na Kira Daddy, na sanar Masa mun zo kuma mun samu gidan, yace ai Abbah Prof ya Kira shi tuntuni, na gaishe su zamuyi magana da safe. Wayar na kashe baki daya bayan nayi broadcasting ma sisters dina cewar mun je lafiya. Noor ta shigo da katon tray a hannun ta, aje Mana tayi tace

” Sannnun ku, tun daga jigawan kuke?”

Kaina na gyada nace

” Tun 1pm muke Hanya”

STORY CONTINUES BELOW

Tayi dariya, Hasina tace

” Akwai Anty din mu tana aure a Kano, na taba zuwa day daya ban Kara jin zanje ba”

Noor tace min

” Sister din ki ce?”

Ta fada tana nuna lubna, kaina na gyada , Hasina tace

” Smile din ku iri daya”

Lubna tayi murmushi, Noor tayi serving dinmu, Ina jin Yunwa sosae Amma yanzun hankalina ba akan abincin yake ba, burina naji inda uwata take, sannan nasan halin da Abbah yake ciki. Baifi spoon biyu nayi ba se naji abincin na shake ni, na dinga Shan ruwa se lubna ce taco sosae, Hasina tace

” Ko akwai abinda kike so, naga kamar baki son rice din”

Kaina na girgiza Amma bance komai ba, Nanne ta shigo ta zauna tana kallona tace

” Ya hanya , kunci abincin?”

Noor tayi beating Dina wajen fadin ban ci ba, Amma lubna taci. Hannuna ta Kama tace

” Muje na kaiki wajen mahaifiyar ki”

Da sauri na Mike jikina yana rawa, bayan ta na bi su lubna Suka biyo mu, parlon Babu kowa tace na zauna ta kalla Noor ta Mata magana da yare, abinda na gane Aisha ne kawai, hakan yasa gabana Kara faduwa, se kuma tone din kamar warning take Mata, ta fice Babu jimawa wani dattijo ya shigo shida wasu maza sun manyanta suma, dattijon ya zauna gefen Nanne fuskar shi tana fitar da matsanancin farin ciki, muka gaishe su ni da lubna, Suka amsa da kulawa. Dattijon yace

” Tabbas gaskiya ne da akace kowanne da zai nema uwar shi, ya sunan ki”

Na muskuta Ina feeling uneasy nace

” Nanah Fadima!”

” Amaryar gaske ce”

Sukai dariya sannan daya yace

” Nanne ga amaryar taki”

Ta tabe baki yace

” Ni Kam ai nasan tsorona take, tunda ta shafe shekara ashirin da uku a wata duniyar”

Na sunkuyar da kaina Ina murmushi, alamu sun nuna ita kakata ce shi kuma kakana, may be sauran uncles Dina ne. A hankali aka turo kofar, tun daga kofa naji murya tamkar tawa tana fadin

” Dan Allah ki barni hakan nan, kije ki karbo abinci ki daina bi na”

A hankali dukda matsanancin faduwar gaban da nake ciki Amma curiosity yasa na dago kaina, matar tana takowa kamar Kara bugun zuciyata akeyi, Ina kallonta nace tabbas wannan ita ce uwata, ban bar komai nata ba musamman fuskar ta, hatta tafiya irin tata nake, marabar mu ita kawai giant ce ni kuma komai nawa both tsayi da kiba average ne! Bata lura damu ba har ta zauna tana fadin

” Bah gani”

Hannun shi tabi har zuwa kaina, yayi Mata magana da yare yana nuna ni, ta tsira min idanu na wasu seconds, Nima na tsura Mata idanu and I felt something new, something great ya shiga zuciyata! Bah ta kalla idanun ta sun Dan fara maiko alamar hawaye sun fara taruwa tace

” Bah?!”

Ya gyada Mata Kai, se ta Mike ta nufo inda nake tareda dagoni ta rungume ni, wani dumi naji, wata soyayya, wani farin ciki, lokaci daya ya mamaye ni, hannuna nasa na zagaye bayanta dashi, se naji I’m complete, naji wannan abin da nake ji na some part of me missing naji shi daidai, ban taba jin feeling din da naji a wañnan ranar ba. Se kuma na fara kuka tareda Kara kankame ta, sassauta rikon tayi tana murmushi tace

” Kina son nayi kukan ne?”

Kaina na girgiza inata kokarin tsayar da kukan but I’m too emotional for that, Zama tayi tareda jana jikin ta ta kalla Bah tace

” Dama kunsan zata zo?”

Nanne ta girgiza Kai ta fada Mata yadda akai, ta Kara rungumata tace

” I’m sorry..”

Se ta kasa karasawa ta fara kuka itama, tana Yi Ina yi nidai nasan kukan farin ciki nake da cikar buri, ita din ce bansan kukan me takeyi ba, Amma yanayin kukan kadai zai fada maka she’s in pain.

” Banda abinki Aisha, ya Zaki saka ta gaba kina kuka kuma, ai wannan duk ya wuce tunda tazo. We welcome you dear!”

Nayi murmushi amidst tears Ina gyada Kai tareda share hawayen idanuna, Noor town crier ta sanar da few of my Aunties da cousins da suke nan, aikuwa Wanda Basu Kai ga bacci ba se da Suka zo suka ganni. Lubna na gefe tana gyangyadi na kalla mamana da taki matsawa daga gefe na nace

” Lubna na jin bacci!”

Kallon side din lubnan tayi tace

” Tare kuka zo? Sister din ki ce ko?”

Na gyada Kai,ta Dan rungume lubnan tace

” Ku muje mu kwanta.”

Dukda da mutane haka muka tashi, Nanne tace Mata ta barni nan na kwana tace aa, haka Noor ta dakko Mana bags din mu muka bar building din baki daya, a lokacin ne na tuna Abbah kuma kunya nakeji na tambaya, se na kalla lubna nace

” Lubna ki Kira Yaya Yusuf kiji ya suke?”

Cikin sauran buildings din na baya anan muka shiga wani apartment, parlon me kyau, yadda aka arranging kadai zai tabbatar maka kowacece me parlon ta zauna kasashen waje. Babu kowa cikin parlon so ko Zama bamuyi ba ta wuce damu bedroom dinta, Babu kowa nan ma yasha gyara se kanshi yake, ta kallemu tace

” Za kuyi wanka ne?”

Lubna ta Kara mikewa tace

” Aa bacci zanyi nidai”

Nace

” Eh zanyi”

Da kanta ta hada min ruwa ta Ciro min sabon towel ta Mika min da sabon sponge na shiga wanka, inajin surely I’ve missed a lot. Lokacin dana fito tana zaune tana jirana da sleeping wears, se na tuna lokacin da muka raka Amal katsina, tarairayar da mamanta tayi seda na dinga kuka Ina jin bazan taba jin wannan ba, balle kuma su lubna da maman su take yawan zuwa.

” Na kawo Miki tea?”

Na kalla agogon dake jikin bangon dakin naga already Sha daya ta wuce Dan to twelve, nayi murmushi nace

” Aa bacci zanyi”

Gefen lubna na kwanta, ta zauna gefena tana rike da hannuna Amma ni ba bacci nake ji ba, tunanin Abbah nake ko yayi bacci. Kwanciya tayi gefena tareda rike hannuna gam, bacci Babu jimawa ya dauke ta, se na Mike tareda zare hannuna na sauka, na nufi handbag Dita na Ciro wayata na kunna, na fara dialing number Abbah, bugu daya ya dauka

” Abbah na!”

‘ Mhmm Amour ba kiyi bacci ba”

” Na kasa yi, Ina ta tunanin yadda kake”

” I’m ok you know, nayi sallah nayi wanka Ina zaune Ina Miki adduar farin ciki me daurewa”

Nayi murmushi nace

“Na ganta”

” Alhamdulillah! Dama ance ai ta zo hutu. How do you feel?”

” I can’t measure the feeling, it’s immeasurable. Ina jina kamar ba a duniyar nan nake ba, Ina jina I’m a complete being. After I met you, I felt half of me is complete yanzun kuma after I met her se naji I’ve scaled!”

Mun Jima muna hira kafin yace nake nayi bacci, kashe wayar nayi inata murmushi na koma gefen ta na kwanta se naji tace

” Yanzun Zaki iya baccin?”

Idanuna na kwalalo waje se kuma na runtse idanuna Ina murmushi…

About AIS

Check Also

ZUMA CHAPTER 10 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 10 BY SHATUUU Www.bankinhausanovels.com.ng  Kamar yadda Daddy yayiwa Hibba alkawari personally akan ranar …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *