ZUMA CHAPTER 12 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 12 BY SHATUUU

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Security din mu da kanshi ya leko ya sanar dani zuwan Yusuf, se lokacin na tuna na bar wayata a daki tana chaji ni kuma na fito parlor Muna assignment dasu, lubna nace tazo muje Zan karba sako, Nawwara na fadin

” Nidai kwana biyunnan you acting strange”

Hararta nayi muka saka hijab muka fita, yana tsaye jikin motar Daddy Dan dama nace masa ya shigo dashi ciki, gurin akwai yalwatuwar haske hakan ya bamu damar yiwa juna kallon kallo, sure Ina ganin shi na fahimci daga inda yake, a lokacin tabbas naga kamar su da Abban su amma da Zama yayi Zama se naga kawai jini ne, jikina yayi sanyi saboda zuwan shi ya fara tabbatar min da zargin da nake akan baban shi, kada fa so na yake? To idan so na yake ta Yaya Zan Kai kaina gidan shi na zauna da matar data haife ni matsayin kishiya? …..

” Babbar Anty barka da fitowa, Ina wuni?”

Ya fada yana durkusawa har kasa, innanlillahi na furta gaba daya kunya kamar zata saka na nutse,  lubna Kam da a baya na take Amma ta fito fili dan ganin drama.

“Dan Allah ka tashi”

Na fada a hankali Ina rufe fuskata, yayi murmushi me sauti yace

” Se kin amsa tukunna”

Dole seda na amsa sannan ya tashi , Suka gaisa da lubna sannan ya bani Yar karamar jakar hannun shi yace

” Abbah yace na kawo Miki, ni Zan koma”

Naki karba se ya mikawa lubna ta mishi godiya sannan ya juya zai tafi se ya dawo yace yana son karbar contact din lubna, ta bashi ya juya ya tafi, jikina a sanyaye muka shiga ciki, suna zaune kamar yadda na barsu tunda ba dadewa mukai ba, Zama nayi lubna tace

” Ni Yaya Nanah ban gane ba, shi din waye? Waye kuma ya aiko shi?”

Se naji idanuna sun ciko da kwalla, nace

” Nima bansan me ke faruwa ba, I’m confused gaba daya,bansan me yasa rayuwata take leading dina haka ba”

Se kawai na fara kuka, suka sukai shiru suna kallona da tausayin maganar da nayi, daki na tafi na dinga kuka Wanda bansan kukan me nake ba, kawai dai nasan zuciyata a cunkushe take,kuma tsoro nake ji kuma bansan tsoron menene ba. Da naga na kasa daina kukan kawai na janyo wayata Ina ayyana abinda zanyi a Raina,gwara ayi ta ta Kare kawai, wannan fear din da fargabar da nake ciki gwara ta Zama resolved kawai, banyi tunanin komai ba nayi dialing number da nayi saving da Abban Yasir,bugu daya ya katse Kiran ya kirani,

” My dear! How are you?”

Se naji zuciyata ta narke na kasa magana se sheshekar kukan da nake,

” Nanah kuka kikeyi?”

Se na tuna Aliyu ranar da muka hadu Ina kuka da daddare, a lokacin gani nake na gama dariya, gani nake dawamma zanyi Ina kuka,amma it took me only a few months na ware na manta da abinda ya faru, gashi yanzun I’m trapped again,

” Me ya faru? Tell me kinji”

A hankali kamar me tsoron abinda Zan fada nace

” Me yasa kake min hakan…”

Se ya katse ni

” Me nayi Miki? Wani abu Yusuf yace Miki?”

Na girgiza kaina kamar yana ganina nace

” Bai ce komai, he’s just been nice, kaima you’re too kind and ni tsoro nakeji”

Zan rantse naji yadda ya sauke numfashi in relief, yayi murmushi yace

STORY CONTINUES BELOW

” Nanah shekarar ki nawa?”

Na bude idanuna a hankali Ina jin gudun da hawayen suke da ya ragu, nayi pouting baki na nace

“23 ne!”

Yayi dariya yace

” My baby no wonder, kina jin tsoron menene to?”

Na danyi shiru Ina tunanin me zance se yace min

” Kar nace Ina son ki?”

Nace

“Eh!”

Se ya sauke numfashi yace

” I’m sorry Nanah da gaske ne tunanin da kike, Ina son ki kuma idan Zaki iya Zama da tsoho kamar ni ina son kimin alfarma ki aureni, I can’t go following your tail, I’m too old for that, Amma ki sani I’ve cleared all the spaces for you, ke kadai nake jira kiyi occupying….”

Kashe wayar nayi Ina panting tareda jin kamar iskar dake kadawa tayi min kadan,hannuna nasa Ina fifita kaina Ina sauke numfashi tareda runtse idanuna, can kuma na girgiza Kai na na toshe kunnena Ina fadin

” No! Bashi ya fada ba, hallucinations ne kawai!”

Gadon na kwanta Ina jin jikina ya mutu, idan na tuna

“…ina son ki kuma idan Zaki iya Zama da tsoho kamar ni ina son kimin alfarma ki aureni…”

Se na toshe kunnena ko kuma na saki Yar karamar Kara, a hakan na Jima a dakin ban fito ba sune suka shigo ganina haka sukai tunanin bacci nake, amma a lokacin bana bukatar wani yayi min magana, kunya nakeji gaba daya!

A bangaren shi cire wayar yayi yana murmushi, da alama bazai Sha wahala ta bangaren Nanah ba, aje wayar yayi ya kwanta yana tunanin yadda zai fara tunkarar maganar, mummy ce ta shigo ta dube shi, thinking yayi bacci yasa ta wuce toilet tayi wanka tazo ta kwanta gefen shi. Washegari Early morning bayan ya dawo a masallaci yaje strolling din daya saba zuwa ya dauki wayar shi ya tura min daddan text, not like kalmar soyayya ya fada aa they were only plain words,sede behind those words nasan Wanda ya turo truly cares. Banyi replying ba saboda har lokacin I was confused, bansan ta Ina Zan fara ba,nidai Ina ganin hakuri Zan bashi Amma yayi min girma da yawa, wannan shi ne abinda nayi believing na daura kaina a Kai amma a kasan Raina, I want the thing to happen Amma tsoron da nake Daddy, siblings Dina ya zasu karbe shi?

Kamar yadda ya yiwa Hanoon alkawarin tare zasu fita ya sauketa makaranta haka yayi, daga shi se ita a motar dan kowa ya fice zuwa gurin aikin shi, suna tafe ya dubi Hanoon da take kallon hanya yace

” Hanoon Zan Kara aure”

Da sauri ta kalleshi da mamaki tace

” Aure kuma Abbah?”

Ya gyada kan shi yana maida hankalin shi kan tukin da yake yace

” As you heard aure zanyi,ba kyaso?”

Da sauri ta girgiza Kai fuskar ta na nuna rashin jin dadi tace

” A’ a Abbah kasan you’ll always have my support, Allah ya Sanya alkhairi. Will mummy be ok with it?”

Dan murmushi yayi yace

” Allah yayi Miki albarka, I’ll take care of mummy kinji? Karki fada mata komai”

Ta gyada kanta tana jin tausayin maman tata, shekarar ta Sha tara kuma Bata da exposure sosae Amma tasan a kasar hausa most abinda Maya Suka tsana shi ne kishiya, balle mummy da ta gama sakin jiki da cewar Abbah bazai Yi aure ba, Tasha taji kawayen mummy nace mata taji dadi ita daya a gidan ta da yayanta, Allah sarki rayuwa!

” Karfe nawa Zaki tashi?”

Tace

” By 2pm Zan gama”

STORY CONTINUES BELOW

Yace

” Ki jira Zan aiko a kaiki unguwa”

Ta amsa masa da to Amma gaba daya Bata jin dadi, she need to support her father amma tausayin maman ta take, wannan yinin ranar haka Hanoon tayi shi Babu dadi.

Misalin biyu na rana, na gama shiri  na tsaf na fito aiki, da nazo banje ko Ina ba na wuce department din mu, nayi taking over na shirya komai sannan na dakko lab coat din na zura saman grey abayar dake jikina,rolling dina na gyara na zauna tareda fara saurar mutanen dake sayan magani, wayata dake gefe na ta fara ringing, sunan shi Dana gani yasa gabana faduwa, naki dauka har ya Kira sau biyu se yayi min text

Har yanzun kunya kike ji? Ki fushi kikeyi? Don’t mind me kinji. Hanoon zata zo gurin ki anjima, she’s our last daughter for now!  Calm shift

Na maimaita na Kara kanatawa, nayi saurin ajewa Dan naji message din na kokarin huda wani sashe na zuciyata, murmushi nayi kawai na cigaba da aikina. Wajen 3pm se gata ta karaso, da tazo a kofar ta tsaya tace min

” Anty Nanah nake nema dan Allah?”

Na Kara kallon ta sannan nace Maya

” Ni ce Nanah, how may I help you?”

Se tayi murmushi Wanda kamar faking tayi tace

” I’m Hanoon!”

Ni kuma se na Bata genuine murmushi nace

” Shigo Mana”

Ta shigo a hankali na Bata kujera ta zauna tana karewa pharmacy kallo, na zauna bayan na aje mata drink da ruwa dana bada a siyo mata, nace

” Ina fata warin magungunan Basu damunki ko?”

Ta girgiza Kai da sauri kawai, she’s feeling awkward, na bude mata ruwan nace

“Kisha kin gaji”

Se tayi murmushi ta karba Tasha sannan ta min godiya,mukai shiru dukka kowa deep in his own thoughts, ni ce ma nake attending ma customers lokaci zuwa lokaci. Zama ta gyara ta min tambayar da ban taba expecting ba

” Kina son Abban kuma?”

Kallon ta nayi na Dan lokaci ita kuma ta dauke kanta avoiding my eyes. Na sauke nannauyen numfashi nace

” Ko daya Hanoon”

Se ta kalleni da sauri tace

“Me yasa Anty? Shi yana son ki, kuma ban taba ganin babana is desperate akan Abu ba irin akanki, da na ganki se naji you worth it. Dazun ya fada min banji dadi ba,bayan ya fada min naji I hate whosoever is destroying my family, Amma da na ganki se naji Ina son ki, Dan Allah Anty Nanah ki yadda ki aure shi”

Se nayi dariya nace

” Hanoon, I’ve family bansan ko zasu karbe shi ba”

” Me zai Hana muyi addua?”

” Hakan ma yayi Allah ya zaba Mafi alkhairi”

Shikenan se ta ware tana ta bani labarin mostly akan Abban ta, se naji we have something In common son da muke yiwa baban mu, Nima Ina Bata labarin sisters dina tace

” Kai Anty Nanah I’m jealous, kina da Yan uwa, nikam mu hudu mummy ta Haifa fa”

A Raina nace idan nazo Zan Kara Miki kanne, se nayi dariya a Raina Naga na zake, har nayi accepting din sa be da nake tunanin Haifa Masa Yara. Anan tace min tana jin Yunwa, na aika wani sabon restaurant aka mata order aka kawo ta dage sede muci tare wai fuskana ya nuna Ina jin Yunwa. Bayan laasar sega kira a wayarta, ta dauka tana fadin

” Mummy ….. Aa naje gurin Aiken da Abbah yayi min…. it’s a secret ni dashi nace bazan fadawa kowa ba….se anjima zan dawo….ok I love you mummy”

STORY CONTINUES BELOW

Ta aje wayar tace min

” Mummy na ce, tana da hakuri nasan ba zaku samu matsala ba”

Na gyada kaina bance komai ba ta cigaba da fada min good sides na maman ta, se naji indai haka ne Zan iya Zama da ita, se bayan maghrib Yusuf yazo Suka tafi na Rakata har mota,nace tazo gida da weekend Ina off, tace min da sassafe zata zo. Na dawo inajin kewar ta cikin Raina, wayata na dauka na turawa Amina text akan Ina son muyi magana da ita.

Bamu samu munyi magana da Amina ba se ranar Dana gama evening, washegari Saturday se gata tazo, tana zuwa Ina bacci ban tashi ba, baa Jima ba se ga Hanoon wadda ta gaji da Kirana, mahaifin ta na Taya ta dukda yasan bazan dauka nashi ba, tsananin mu message ne tun ranar da yayi proposal, nikam wayar na silent shi yasa banji ba, duk Suka kalleta tace musu gurina tazo, Amina tace

” Ummu taso Yaya Nanah”

Babu musu ta tafi dakina ta taso ni, na tashi nayi brush na canja Kaya Dan da asuba nayi wanka Wanda alada ta ce hakan, dukda Bata cemin Hanoon tazo ba tace min Amina ce tazo, a parlor na same su zaune sun kammalla hada breakfast dan Daddy ya fita hadejia tun sassafe, zama nayi a lokacin na lura da Hanoon,nayi dariya na zauna gefenta nace

” Kinzo, sannu da zuwa. Ina Yaya Yusuf.”

Tayi dariya sosae yace

” Anty Nanah shi Yaya Yusuf din kike cewa Yaya Babu ruwana kuda Abbah”

Lubna tace

” Yaya Nanah at least introduce her Mana”

Na dalla mata harara, Amina tace

” Gaskiya ta fada meye na hararta”

Hanoon tace

“Laaa! Bata fada muku ba? Ni Yar ta ce, sunana Hanoon Abbana yake son ya aureta”

Gaba daya Suka kalleta in disbelief, Nawwara tace

” Yayanki ko?”

Se tayi dariya tace

” My father ko baza ku bamu ba?”

Se sukai shiru kamar yadda nayi tsumu tsumu Ina jin kaifin daggers din da Amina me wullo min,

” Mu ci abinci se muyi maganar”

Hakan mukai breakfast, Hanoon ta ware ta samu Amal daidai shekarun ta, Suka dinga hira, daki muka shiga da Amina na kwashe komai na fada mata, tayi wani ihu tace

” Da gaske Yaya Nanah! OMG alhamdulillah! Dama jinkiri haka yake”

Seda ta gama murnar ta sannan nace

” Bana son shi fa”

Da mamaki tace

” Me yasa? Bai Miki ba”

Na girgiza kaina nace

” Kunya nake ji wallahi, kuma….”

Ta girgiza Kai tace

” Kin to istikhara?”

Nace

” Aa banyi ba”

” Idan kikai se muyi magana, Amma Dan Allah kada ki watsawa yarannan kasa a Ido da suke ta bibiyar ki, suna nuna Miki sun karbe ki”

Nayi shiru muka Kara tattauna maganar akan Zan fadawa Anty sumayya sannan muka fito na tarar dasu suna kallo Hanoon na gyangyadi, dakina na rakata ta kwanta, nayi musu bayani Amma kowa ya dinga fadin ai yayi musamman Nawwara data ganshi da idonta.

Da daddare yazo ya dauki Hanoon daidai Salem yazo tafiya da Amina Suka gaisa tareda exchanging contact da Salem, har ya tafi yana tsokana ta, a Daren na fadawa Anty sumayya komai, yadda nake tunanin zasu ki amincewa se akai akasin haka, Dan conference call sukai Suka tattauna akan indai Ina son shi, matar shi Bata da matsala to su dai sun bada blessings dinsu.

Misalin biyu na dare, yana zaune a saman praying mat,ya idar da sallah yana lazumi, yaji motsi a bayan shi, kallon gadon yayi mummy ce a zaune tana kallon shi, casbahar hannun shi ya aje ya maida hankalin shi kanta yace

” Me yasa Kika tashi?”

Sakkowa tayi ta zauna gefen shi tace

” Ina son muyi magana ne”

Seda gaban shi ya Fadi yace

” At this time kuma? Akwai gobe fa inshallah”

” Bazan iya jira ba shiyasa”

Se ya gyada kanshi yace

” Ina jinki”

” Me yake damun ka?”

Da mamaki ya kalleta yace

” Me Kika gani?”

Zaman ta ta Kara gyarawa tace

” You act strange these days kaida yaran ka, ka fitar dani daga cikin abinda kuke kullawa, yau se naji Hanoon na magana da Yusuf a waya, na fahimci Ashe aure zaka Kara Yi…”

Hannunta ya Kama zaiyi magana ta girgiza Masa Kai tace

” Me yasa ni ba zaka fada min ba, sede yaran nan, kana sasu suna ganin kamar I’m a monster Zan hanaka abinda kake so,…”

” Ba haka bane gimbiya, I met her once kiyi hakuri Ina fada Miki wannan, naji Ina sonta kuma I want to keep her by my side, nasan Abu ne da baki taba kawowa ba, Nima ban taba kawowa ba a rayuwata, shiyasa nake using yaran muyi forming team da zamu lallashe ki dashi. I can count on you bazaki bani matsala ba”

A hankali ta banbare hannun ta daga nashi,tace

” Who’s she”

” A young girl older than Hanoon, younger than Yasir!”

” Maganar yayi nisa ne?”

Ta Kara tambayar shi, kanshi ya girgiza yace

” Aa am planning”

” Tsoro kakeji? Haba dai ta Yaya zaka dinga kula yarinya for more than two months iyayenta basu sani ba, come to think of Hanoon”

Hannunta ya Kara kamawa yace

” Gobe inshallah nake son samun mahaifin ta, kiyi min addua!”

Tace

” Allah ya zaba Mafi alkhairi!”Na yarda da mutane da ke cewa komai lokaci ne, a rayuwata na fahimci komai yana tafiya yadda Allah ya tsara shi, duk yadda ka Kai da son Abu indai Allah Bai yarda ba to hakan bazai kasance ba.+

Washegari Sunday Babu inda kowa zai je har Daddy wannan aladar gidan ce, tun asuba nasa Amal hada abincin Daddy so naje na kwanta na dinga bacci abuna, kwana biyu na koyi bacci na Babu gaira Babu dalili. A bangaren su Hanoon Basu San yadda ta kasance ba tsakanin iyayen su biyu, da safe Abbah ya tashi garau dashi Babu wani damuwa a tare dashi, kana kallon shi kasan he’s extremely happy. Mummy ta fito daga kitchen bayan an gama breakfast, ta Jima a tsaye tana kallon Abbah da ya maida hankalin shi akan wayar shi yana ta murmushi, wani Abu me zafi taji ya taso mata yana kokarin danne mata tunani, cikin sauri tayi auziyya sannan ta karaso cikin parlon tana fadin

” Abbah, karfe nawa zaka fita?”

Ya dago da sauri tareda sakar mata murmushi yace

” After breakfast!”

Ta gyada Kai ta nufi dakunan yaran ta taso su, duk sun ma tashi se kowa ya fito sukai breakfast sannan ya nufi daki mummy na biye dashi, wayar shi ya aje ya dubeta bayan ta zauna gefen shi

” You look disturbed, I’m sorry to cause you all this”

Ta girgiza kanta tace

” I’ll be ok inshallah! Ka tashi ka shirya”

Babu musu ya shirya cikin manyan Kaya,ya kafa hula wadda tayi Masa kyau, ya daura agogo sannan ya dauka key da wayoyin shi da kudi ya mata sallama. Ta biyo bayan shi tana fada masa zata fita da Adnan da Hanoon, yayi musu addua nasara tareda bata kudi ko zasu nema wani abu, bayan ya tafi ta koma daki ta kulle ta dinga kuka tana jin kamar zuciyar ta konata akeyi.

Shikam yana fita ya wuce gidan Registrar Wanda abokin shi ne sosae kuma shi zai Masa iso wajen Daddy, Suka dauka dayan suka tafi gidan mu. Tun kafin su karasa Registrar ya Kira Daddy ya sanar dashi zai zo gidan da baki, so tun daga gate security ya raka su har cikin gida part din Daddy, a zaune suka same shi ya gama breakfast Nawwara tana kwashe kwanuka, ta gaishe su sannan ta fita, Bata Jima ba ta dawo da katon flask din tea hade mugs da sauran su Madara dasu nescafe, ta aje can ta kawo Kwan da Suka soya, Daddy suka gaisa ya dubi sauran yace

” Registrar jiya mun hadu baka cemin zaka zo ba”

Ya shafa kan shi yace

” Yallabai ai na kawo maka bako ne”

Daddy ya Kara duban su tareda musu sannu da zuwa a Karo na biyu, Prof. Nura ya fara yiwa Daddy bayanin abinda ya kawo su,seda ya gama sannan Daddy yace

” Duka yarana mata ne, banida namiji ko daya,wacce a ciki kuke nufi?”

Se lokacin Abbah yayi magana yace

” Fadima ce”

Daddy yayi shiru yana jinjina maganar, Nanah dai Nanah tashi. Ya dubi Abbah yace

” Yata Nanah ita ce ‘yar da nafi so a zuciyata duk cikin yarana, duk yayana ita tafi kowa Shan wahala, Nanah tasan uwa ta haifeta Amma Bata taba ganin ta ba, Nanah wata Bari ce ta jikina da rayuwata, yata ce wadda idan nace ta hakura da Abu zata hakura, duk cikin yayana Ina mata adduar samun Abu mafi daraja da kuma kwanciyar hankali. Na karba kudin auren Nanah na mayar saboda mutumin yana da mata kuma tazo har gida tayi min warning akan zata lahanta min yata,it might be an empty threat, Amma saboda rayuwar Nanah ake magana shiyasa Dole na bar maganar auren. Bawai Zan ki ka ba, Aa Nima nayi aure a kusan shekarun ka,na aura yarinya wadda Bata Kai Nanah ba, in fact ni past dina bashi da kyau akan aure so ba Zan ki auren ku ba, matsawar Nanah ta amince da kai haka matar ka nayi bincike batada matsala to Zan baka auren Nanah, I was in your shoes then!”

STORY CONTINUES BELOW

Abbah ya sauke ajiyar zuciya yana jin wani farin ciki marar misaltuwa yana shigar shi, yasan baida damuwa da Barira sun riga sun wuce wannan gurin, Nanah ce ta rage. Daddy ya dauka waya ya Kira lubna tunda yasan ta tashi yace ta turon yanzun nan. Ina bacci lubna tazo ta tashe ni wai Daddy na Kirana, tashi nayi na wanke fuskata da bakina na saka dogon hijab na fito, duk tunanina abinci ne baa Kai mishi ba, so Ina fitowa tsakar gida nace

“Yanzun Daddy ma abincin shi bazaku Kai ba”

Nawwara tace

” Aa na Kai fa tun dazun, Kiran wani abun may be yake Miki”

Daddy na jin mu yace

” Kun ki ko? All her life she served me and supported me”

Ban lura da takalma ba, kawai shigowa nayi cikin dakin bakina da sallama Ina fadin

” Daddy baa kawo maka abincin bane?”

Kallona yayi with so much love yace

” Zauna magana nake son muyi dake”

Lokacin dana zauna na lura dasu, na gaishe su lokacin na tabbatar Abbah ne a gurin a zaune, gabana ya Fadi na dube shi briefly, murmushi yayi min nayi saurin sauke kaina kasa Ina wasa da hannuna, kamar nayi ihu naji Daddy yace

” Nanah kin gane shi?”

Ya fada yana nuna Abbah, na dubi Abbah Wanda yake min wani kallo kasa kasa ba lallae wani ya gani ba, cikin sauri na sunkuyar da kaina Ina jin yadda butterfly ke yawo cikin cikina, it making my heart melting, kaina na gyada bayan Daddy ya Kara maimaitawa,

” Tashi kije kinji”

Jikina a sanyaye na Mike na fita, Daddy yace Masa zai nemeshi soon. Ina komawa daki naji kamar zazzabi nakeji, Shima yana fita ya kirani wannan Karan banki picking Dan I badly wants to talk to him

” Armor!”

Na lumshe idanuna nace

” Mhmm!”

” How are you?”

“Baka ganni ba, ni lafiya nake”

Yayi murmushi jin yadda na shagwabe murya ,yace

” Naga kin yimin magana kikai, kina ta sunkuyar da Kai”

Hararar wayar nayi Kai kace  yana kallona nace

” Shi ne kazo baka fada min ba”

” Ba wani Abu nazo Yi ba, nazo nayi introducing kaina ne kawai, ai baki fara Sona ba, Zan jira se kin fara se muyi aure”

Unconsciously nace mishi

” Waye yace maka bana sonka…”

How I wish you can take back what you’ve said nidai Dana maida maganata ciki,yayi dariya yace

” Armor ba Wanda ya fada min,Amma tunda kinyi denying kina so na kenan”

Na kashe wayar tareda bubbuga kafata Ina turo baki, se naji karar message

Thank you darling!

Nayi murmushi na kwanta Ina kankame jikina, tareda ayyana da gaske ina son shi kamar yadda na fada, Kai na girgiza nayi pouting baki na nace bana son shi gaskiya, bansani ba ko deceiving kaina nake. Daddy Bai Kara maganar ba Nima haka Ashe bincike yake bayan ya samu goyon baya daga gurin manyan yayan shi.

Bangaren su Adnan sun fita tare da mummy,ita kanta ba wani guri take son zuwa ba, kawai gidan yayi Mata zafi ne yasa Dole ta fita Dan taji Iska, Adnan ya tambayeta inda zai kaita tace

“I just need fresh air, idan kuna son zuwa wani gurin to?”

Hanoon ta dubi mamanta kamar zatayi magana se ta basar kawai, hakan Suka dinga yawo cikin gari, daga wannan street su fada wancan, a hakan ta samu ta warware taji abinda ya tokare Mata kirji yana dan raguwa, gida tace su koma bawai Dan ta gaji ba se dan Kiran ta da Hajiya lubabtu tayi akan tazo gidan Babu kowa, tace ta jirata ba nisa tayi ba. Adnan ya juya kan motar Suka nufi gida, a parking lot suka samu motar Hajiya lubabtu tayi parking ta fito tana jiran su, da murmushi Suka tarbi juna sannan Hanoon ta gaishe ta, haka kawai Bata son matar, ta kalleta tace

” Hanoon ‘Yata, Ina samarin har yanzun baa kawo min daya daga ciki ba”

Hanoon ta bata rai ta cigaba da Danna wayar, mummy tayi murmushi tace

” Kema dai Hajiya da wata magana, nawa Hanoon din take”

Suka nufi parlor mummy, Hajiya na fadin

” Ki bar yaran yanzu”

Suka Dan taba hira, dukda mostly Hajiya ce karfin zancen, mummy mostly tana tafiya tunani Wanda Bata San dalili ba, Hajiya lubabtu tunda mummy ta shigo ta lura da canjawar yanayin ta, tace

” Hajiya Barira kamar kina cikin damuwa?”

Mummy ta danyi yake tace

” Rayuwar ce hakan”

Tace

” To Allah ya saukaka Mana, Ina fata ba yaran bane”

Da da farko Bata son fadawa kowa maganar har se ta kankama Amma kuma yanzun ta canja shawara tana ganin idan ta samu ta fadawa wani kamar zata samu sauki a ranta.

” Yallabai ne zaiyi aure”

Idanu a warwaje ta rike hannunta a kirji tace

” Ki Bari Dan Allah wanne irin aure ana zaune lafiya?”

Tayi dariya tace

” Da gaske nake, jiya ya fada min, zancen da nake Miki yau yaje gurin mahaifin ta ya tambaya”

Da wani irin yanayi ta kalla mummy tace

” Se ke kuma Kika Yi me? Se kika nade hannu Kika zuba mishi idanu kenan?”

Mummy ta kalleta da mamaki tace

” Me zanyi to?”

” Kije ki samu yarinyar kici ubanta, kije gidan su kiyi hauka, make a fuss and empty threat kiga idan baa fasa ba!”

Mummy ta girgiza Kai tace

” Dana San shawarar da Zaki bani kenan da ban fada Miki ba, kuma ni da girmana Zan zauna Ina fada da yarinyar cikina, bazan iya ba na riga na Basu blessings Dina saboda ko me zanyi tunda yayi niyya se yayi, plus bana jin akan kishiya Zan barwa yarana abin Fadi!”

Kamar Hajiya lubabatu zata daki mummy ganin taki yadda da daya daga cikin abinda ta fada mata, se tace

” Kin bani kunya, na aza munyi alkawarin ba zamu zauna da kishiya ba”.

” Yaushe? Ba dai ni ba gaskiya, a barshi na fada Allah ya yafe min Amma ni banfi karfi ba, to wai dama a addini ance se na yarda zai Kara aure, abune da Allah ya hallata Masa, kyautatawar sa ita ce sanar dani, Dan hakan ki manta kawai”

Ran lubabatu a bace ta bar gidan ta bar mummy da tagumi.

Da daddare Ina kwance a parlor bayan munyi dinner, Abbah ya Kira ya gama zolayata munyi sallama Sega wani Kiran ya shigo wayata,ban tsaya duba number ba kawai na Kara a kunnena. Idanuna na bude jin wata kalma Dana Jima banji an kirani da ita ba!

” Sahiba!”

Babu tantama Aliyu ne, shi kadai ya taba Kirana da wannan sunan, Babu wani mahaluki daya taba Koda arar sunan…..Kullum ka wayi gari a Rana akwai lesson din da rayuwa ke koya maka sede idan Kaine baka maida hankali ka fahimci it’s a lesson ba. A lokacin da bakida saurayi, kina zaune ke daya babu wani mahaluki da zai zo yana son ki Amma daga lokacin da Kika samu tsayayye tamkar kiranye zakiga kowa yayi Miki caaa akan ki, da wasu crush dinki, side love, tsoffin samarinki da sauran su wannan nasan duk wata mace can testify on this. Abinda na fahimta a nawa tunanin, dukka jarabtar Allah ce, na farko Allah na fada maka kayi hakuri ka jure yana sane da kai, kuma idan lokaci yayi zaka samu babban rabo, nifa Nasha na tsaya na kalla madubi Dan ganin meye makusa ta da samarin Basu rushing akaina, I remembered wata antyn mu a hadejia tana ce Mana wai mu dinga fitowa da wani sashe na jikin mu ko ma samu miji, idan ta fada se muyi dariya Dan na fahimci haka duniyar take,you expose your body and get followed by people like you! Na biyu kuma Allah na nuna maka turn to him, ka nemi zabin shi, a ganina most Mata anan suke Making mistake, lokacin da Maza suke rushing kanmu lokacin muke bude sabon iskanci da zabe zaben, wani lokacin har mu saki na hannun mu thinking wancan Zama zasui,da kin sake shi to wancan kamar vapour zasu bi Iska!1

” Sahiba!”

Ya Kara maimaitawa, wani mugun tsaki naja na kashe wayar tareda mikewa na zauna, Ina jin wani mugun bacin rai yana ziyarta ta, wayata na dauka nayi dialing abinda nasan zai saka ni farin ciki bana ma son nayi tunanin wani Aliyu balle har Raina ya baci a banza, Bai picking ba like always ya katse ya kirani

” Abbah!”

Na fada a hankali

” Armour ya akai? You sound upset, waye ya taba min ke?”

Nace

” Babu komai, I’m missing you ne!”

” Da gaske, naji dadi sosae. Nasan Daddy zai yanke decision soon, I promise you baza ki Dana sanin Zama Dani ba!”

Hararar wayar nayi nace

” To nace Zan aure ka ne?”

Dariya yayi yace

” I’m sorry! Shikenan”

Na gyada Kai, se yace

” Armour Ina ta son na tambayeki, like naji Daddy yace baki taba haduwa da Mom dinki ba? Da gaske ne?”

Se naji idanuna sun ciko da kwalla,nace

” Mhmmm, bansan se yaushe ba”

” Zan kaiki da kaina, I promise you da ita zaayi bikin ki”

May be da Ace a gefena yake Zan iya rungume shi, shi ne mutum na farko daya fara min alkawarin mafi dadi a duniya, nayi dariya nace

” Thank you so much Abbah”

” Ni bana son Abbah fa!”

Se nayi dariya nace

” To me zance maka,bayan ko sunan ka ban sani ba”

” Haba dai, Wasa kikeyi”

” Allah da gaske nake, ka taba fada min ne?”

” Sunana Idrith, ni Dan asalin Taura ne, mahaifina shi ne dagacin garin, tun Kano tana hade da jigawa, da muka rabu se ya Zama hakimi. Saboda Muna da sarauta shiyasa nayi karatu,back then yawanci traditional rulers ke saka yayan su a farko saboda sauran Yan gari suyi koyi. Nayi primary dina anan sannan secondary nayi a kiru dake Kano, na gama secondary na fara karatu a ABU Zaria, na karanta business administration, nayi masters dina a UDUS, nayi aiki da gwamnatin tarayya, daga baya na samu na tafi UK nayi PhD dina akan Banking and finance dama akan shi nayi Msc sannan na dawo nayi commissioner of finance a jigawa, nayi chairman na FIRS, yanzun Ina matsayin governor of CBN jigawa state branch. Matata daya Barira, yaran mu hudu, Yusuf, Adnan, Yasir da Hanoon. Munyi aure inada shekaru masu karanci, ita maman su ma gidana ta gama secondary anan tayi nursing school tayi har Bsc yanzun tana aiki a shekoni. Kamar haka yayi?”

STORY CONTINUES BELOW

Na gyada kaina nace

” Kaga yanzun nasan sunanka , but I can’t call the name, Zan cigaba da ce maka Abbah!”

“Aa bana so”

Da wannan nayi ta tsokanar shi yana cemin baya so har dare yayi na fara gyangyadi se mukai sallama, Dana kashe na manta da wani Aliyu ya kirani balle har Raina ma ya baci. Cikin kwanakin Aliyu ya dage tun karfin shi da Kirana,bana picking hakan bana karanta messages din da yake turo min, a ganina ni dashi bamuda wani sauran Abu da ya rage, ni da ya Kira da mayaudariya me zai ce min kuma.

Seda aka Kara kwana wajen uku sannan Daddy ya kirani parlon shi, gabana nata faduwa Ina adduar Allah dai yasa alkhairi ne Kiran, yana zaune kamar ko yaushe na zauna Ina kallon yadda girma ya Kara Kama shi, jiya ba yau ba.

” Nanah Aliyu ya kiraki?”

Da sauri na kalleshi tareda mamakin tambayar shi, kaina na gyada nace

” Ya kirani Amma banyi picking ba!”

Kai ya jinjina yace

” Wasu lokutan yana da kyau mu dinga saurarar abinda mutane zasu fada mana, da kin dauka kinji me zai ce Miki”

Se nace

” Daddy ai bashi da amfani hakan”

Ya gyara zaman shi yace

” Not really! Ya Kira ni shekaran jiya munyi magana dashi sosae, nayi bincike akan Professor, zanji dadi idan ya kasance kin aure shi, Amma Ina son kiyi tunani, nan da jibi ki kawo min sakamako kowa Kika zaba tsakanin su ni me Goya Miki baya ne…”

Cikin rashin fahimta nace

” Daddy tsakanin wa da wa kenan?”

” Kije ki saurara Aliyu,kiji me zai ce Miki idan yaso se ki zaba ko shi ko Prof din!”

Daga haka yayi shiru nasan ya sallame ni kenan se na tashi na fita zuwa dakina,Ina jina in a dilemma . Me Aliyu ya fadawa Daddy da har yasa yayi changing mind din shi akan maganar nan. Wayata na dauka for the first time in eight months na Kira Aliyu, tana ringing kamar jira yake ya dauka

” Sahiba…”

” Ban kiraka kace min sahiba ko kace min wani dadin baki ba, na kiraka bisa umarnin Daddy Amma bacin haka kaima kasan kayi tsalala, ruwan randa ya fika kauri”

Seda na gama sannan yace

” Ni nasan nayi deserving duk abinda Zaki ce, so nake kawai ki saurare ni, Fatima yau kwanan ta Tara da rasuwa…”

” Maman munib? Innanlillahi wa inna ilaihil rajiun! Ya Rabbi!”

Haka na give saboda yadda sakon ya dake ni, se naji duk wani fushin da nake ya tafi, se jimami da tausayin shi daya Kama ni

” Ta rasu Fadima, ta fita mota ta buge ta bayan kwana biyu on admission deeply unconscious ta rasu!”

Kaina na jijjiga Ina jin kamar bana duniyar, wani zufa ke karyo min, nayi shiru Ina tunanin yadda rayuwa take, ta tafi ta barwa Mata Aliyu duk fadan ta da balain ta, ta tafi lahira ta bar Aliyu da Mata a duniya, to kishin na meye, tashin hankalin da masifar na meye, bayan lokacin da muke dashi a duniya kankani ne, ya ilahi ya rabbul alamin. Da kyar na Masa gaisuwa ya amsa with a heavy heart!

” Daddy ya Hana ni auren ki saboda threat din Fatima akan ki, yanzun Fatima ta rasu ki bani chance na dawo Mana da alkawarrurrukan da muka dauka, mu zauna tare har abada!”

Dukda tausayin shi da nake ji Bai Hana nace Masa

” Ka manta kalaman da ka fada min, ka manta no mayaudariya ce, ai banyi tunanin kana da kunyar tunkarata da maganar nan ba.”

Yace

” Na dauka laifi na, nasan text dinnan was too harsh, sahiba nayi tunanin abinda zai raba mu cikin sauki Babu, kullum Rana we’re getting closer, ni kuma duk kokarin na rabu da Kai na kasa, shiyasa na tura Miki text din to provoke you, yadda Zan sawa rainaunyi fada mun rabu, but wallahi I never meant any of those words”

Hankalina naji ya kwanta saboda ya karba kaifin shi, se naji wani mugun tausayin shi ya rufe ni, bashi da Mata, kada na manta alkawarin mu na Zama tareda juna har abada, ganin abinda zuciyata ke Shirin yi ga uban magiya da yake min,hade da kashe min zuciyata da abinda nafi kauna, se nace Masa zanyi tunani. Tunda na kashe wayar na runtse idanuna Ina adduar Neman saukin lamura da kuma zabin Allah mafi dacewa!

Wanann Daren bacci dai se barawo ya sace ni. Tunani me zurfi kawai nake in hango wannan mutumin da mukai shekaru har hudu tare sannan in tuna Wanda na hadu dashi baifi wata uku ba, Amma kowa nashi ya amince dani, na tuna each and every bit of our conversatio, tunda na sake jiki da Abbah Bai barin bacin rai na, Aliyu Fatima ce damuwata kuma ta mutu! Na rasa ya zanyi bani na samu nayi bacci cikin dadin Rai ba se bayan asuba.

Da Rana, na Kira hibba Dan Ina jin ya kamata nayi shawara da wani,idan na sake zanyi abin kunya. Bayan min gaisa nayi updating dinta akan latest development, tayi wani ihu kunsan hibba is lousy

” Ayya Allah ya jikan ta! Da ana tafiya da miji da ta tafi dashi na tabbatar! To ke meye damuwarki?”

Se na fahimci bata gane abinda nake nufi ba kwatakwata,

” Daddy gave me an option akan na zaba tsakanin su….”

” Don’t tell me Zaki bar Prof for Aliyu?! How can you even think of doing that?”

Na marairaice nace

” Hibba na kasa tunani, na rasa yadda zanyi wallahi, duk kaina ya kulle, I’m thinking of wa zan zaba?”

Zagina ne kawai batayi ba, tace

” You’re confused kenan? Why should you? Kina nufin Aliyu Zaki komawa mutumin da bazai tsare gidan shi ba? Mutumin da matar shi tafi karfin shi, akwai HIKMA a raba ku da turo Miki Abbah Prof. Don’t break his heart, his children’s heart da suke kaunar ki suna tarbar ki, Dan Allah ki bi abinda zuciyar ki ke so kada kibi whispers din shaidan”

Haka ta dinga min, ta dinga kokarin convincing dina Amma Ina zuciyata tayi nisa, nasa a raina komai zanyi deciding to Allah ne yayi guiding Dina saboda daren jiya nayi sallah nayi ibada kamar ba gobe so nasan zaiyi wuya abinda na yanke ba shi ne daidai ba. Na dauki wayata na Nemo number Abban Yasir nayi deleting bayan na sending mishi message

I’m sorry,2

Yana Zama delivered na dauki hijab na nufi parlon Daddy.

About AIS

Check Also

ZUMA CHAPTER 10 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 10 BY SHATUUU Www.bankinhausanovels.com.ng  Kamar yadda Daddy yayiwa Hibba alkawari personally akan ranar …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *