ZAFIN RABO CHAPTER 4 BY SAKIEYY

ZAFIN RABO CHAPTER 4 BY SAKIEYY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Sakeena bata koma gida ba sai kusan 9 na dare, yanzu hankalinta ya kwanta tun bayan maganar da hamida tayi mata, ita kuwa ba abunda zata ce ma da k’awartata sai dai Allah ya biya ta, da bata da hamida a duniya bata san yarda zatayi ba. Tana shiga d’akin ta taji wayar ta na ringing wacce ta bari a kan gado tayi gidan hamida, saurin k’arasawa wurin ta tayi kanta katse, tana isa ta d’auka sai ga sunan shaheeda a kan screen d’in, ji tayi gabanta yayi mumunar fad’uwa, a hankali ta latsa kan green button d’in tare da saka wayar a kunnanta, sallama tayi bayan ta samu wuri akan gadon ta ta zauna,

+

“Da aka cemun kina nema na a waya har da cewa in nemi ki in wayata ta dawo abun ba k’aramin mamaki ya bani ba”

Abunda shaheeda ta fara ce mata kenan ko sallamar da tayi bata amsa ba, Sakeena wata harara ta saki sai kace shaheedar na gabanta,

“Ke bakya amsa sallama ne?”

Shaheeda dariya ta saki, “daman shirin da muke har ya kai mu amsa sallamar juna?”

Tsiyar ta da shaheeda akwai wawta da shahanci, shi ya saka bata tab’a biye mata in tana irin wannan abun dan sai ta zama irin ta, share tayi ta fara cewa,

“Wani abu daman nake son na tambaye ki”

Ko da tayi maganar sai da gabanta ya k’ara fad’uwa, anya ta shirya jin labarin Kamil, amma kuma rabi da kwanta zuciyar ta na mutuk’ar san jin labarin tsohon saurayin ta, muryar shaheeda ce ta katse ta daga tunanin da take,

“Mene abun da kike son tambaya ta?”

Shiru tayi ta kasa bud’e bakin ta ta bata amsa, ga zuciyar ta ba abunda take sai faman bugawa, sai can da kyar da iya furta,

“Labarin Kamil”

Tsit daga d’ayan b’angaran, ta tabbata itama shaheeda mamaki abun ya bata, Sakeena kuwa ji ta hannunta ya jik’e da gumi ita kanta bata san me ya saka duk tabi ta rud’e ba haka kawai, da taga kamar shaheeda bata da niyar magana ta dake ta k’ara cewa,

“Kada kice mun biki sani ba, nasan kin san komi kin san shi wane”

Ji tayi ta k’ara sakin dariya, “me yasa kike san sanin labarin shi?, duk zama na dake baki tab’a tambaya ta ba, ko shekaru takwas da suka wuce bayan abun ya faru dashi ko da wasa baki tab’a tambaya ta ba, me ya saka sai yanzu”

Ita kanta bata san me ya saka take son sani ba, maybe ta gaji da zama cikin duhu, maybe tana san sanin me tak’amaimai Kamil ya b’oye mata game dashi, ji tayi shaheeda tace,

“Ki saurare ni da kyau dan bazan k’ara mai mai ta miki labarin nan ba”

Gabanta ne ya k’ara fad’uwa, amma a haka ta kasa kunnnta dan jin labarin shi.

LABARIN

Mahaifinsa UMAR ADAMU DATTI haifaffan d’an garin yola ne, bafulatani ne gaban shi da bayan shi, shi kad’ai iyayen shi suka haifa, ya tashi a garin yola har ya kai shekara goma, iyayen mahaifin shi wato kakanun shi basu da wani k’arfi dan kakan shi me suna ADAMU DATTI manomi ne, kakan shi yana da wani babban aboki ALHJ JAMILU wanda yayi zaman yola a daa daga baya ya sami arziki sakwamakon kasuwan cin da ya fara a garin kano, bayan babban abokin kakan shi yayi arziki yaje gun kakanshi dan neman alfarma ya bashi mahaifin shi su koma kano ya saka shi a makaranta dan a lokacin shine kawai gatan da za’a mai, kakan shi ya so ya hana saboda shi kad’ai ne tilon d’anshi a cewar shi zai dunk’a taimaka mishi, amma da saka bakin matar shi kakar su Kamil kenan me suna HABIBA har ya barshi suka koma kano tare.

Bayan sun koma kano ALHJ JAMILU ya saka shi a makaranta har ya samu ya gama secondary school, a lokacin Allah yayi ma baban shi ADAMU DATTI rasuwa, abun ba k’aramin girgiza su yayi ba, kakan shi na da wata d’aya da rasuwa Allah yayi ma kakar shi rasuwa, HAJ HABIBA, daga lokacin ya koma gaba d’aya wurin ALHJ JAMILU dan bashu da kowa a yola, bayan ya kamala karatun shi na jami’a, Alhj jamilu ya saka shi a hanyar kasuwan ci, a haka shima har ya fara samun arziki, yana da shekaru 28, ya had’u da Haj rahima, wace take balarabiyar egypt, haj rahima wacce tazo nigeria tun tana y’ar shekara uku tana zama wurin yayar ta wace take auran d’an kano, sakwamakon rashin iyayen su, soyyaya mai k’arfi ta shiga tsakanin su basu dad’e ba sukayi aure.

STORY CONTINUES BELOW

Auren su baiyi shekara d’aya ba ta haifo y’an biyu kyawawa maza identical twins, wanda ranar suna aka saka ma Hassan KAMAL, Husaini Kuma KAMIL, sun tashi cike da so da kulawa amma sai dai they’re polar opposite, Kamal baya san jama’a, baya san surutu da hayaniya, shikuwa Kamil na mutuk’ar san jama’a, dukda halin su yasha babban bai hana shak’uwa mai k’arfi ta shiga tsakanin y’an biyun ba, suna mutuk’ar san juna su, in ka tab’a d’aya kamar ka tab’a d’aya ne, suna da shekara takwas a duniya haj rahima ta k’ara haifo santaleliyar mace, wace take a matsayin gambon su aka saka mata suna Kamila, a lokacin kud’i masu yawa sun zauna ma Alhj umar datti yayi mugun arziki kuma sunana shi yayi fuce a nigeria saboda harkar kasuwan cin sa, kuma a lokacin yayi sha’awar shiga siyasa, bayan gwagwar mayar siyasa ya samu ya hau reps anan yola, shekara biyu da samun muk’amin nan, lokacin kamila nada shekara shida, Kamal da Kamil nada shekar sha hud’u, aka haifi auta Kausar, sun tashi dukan su suna matsayin san junan su, ga Allah yayi musu wani azabbabn kyau, ga sun had’a ruwa biyu, bayan Alhj Umar datti ya sauka a reps suka tattara suka koma abuja da zama ya bar harka kasuwancin shi gurun wani babban yaran shi da ya yarda dashi.

Kamal da Kamil basu tab’a kasancewa wuri d’aya ba, dan ko makaranta ba d’aya sukayi ba, abokanan su daban ne sai dai guda d’aya me suna Imran wanda yake d’an babbar k’awar haj rahima, Kamal akwai miskilanci, akwai kuma taurin kai, shi kuwa Kamil akwai san wasa da dariya, sakwamakon rashin san jama’an Kamal shi ya saka ba wanda yasan shi, ko abokan Kamil sai sun saba dashi sosai suke sanin shi y’an biyu ne, lokacin da suke da shekara sha bakwai a lokacin baban su ya hau gwamnan Adamawa wato yola kenan, Kamil ko da wasa bai tab’a nunawa baban shi gwamna bane in har ba full sunan shi kaji ba, zai shiga cikin na k’asa dashi ya saje dasu, zai kuma shiga cikin talakawa suma ya saje dasu, ya iya zama da ko wane irin mutum, ya d’auki wannan dab’iar ne dan ya tantance masu sanshi tsakani da Allah da masu sanshi dan kud’in babanshi, shi ya saka ma ya zab’i yayi university d’inshi a k’asar da ba nigeria ba, baban shi yayi shekara takwas yana governor a adamawa, yanzu ne ya zama minister of agriculture.

———

Sakeena da tayi shiru duk jiki yayi sanyi ta k’ara jin shaheeda tace,

“Lokacin da kika had’u dashi lokacin ya gama degree d’inshi a dubai ya fara masters d’inshi a makaran tar ku”

Ta kasa cewa komi kawai tana zaune tana wasa da rigar da take jikinta, labarin ya girgiza ta saboda bata tab’a sani baban shi nada mugun arziki ba, ji shaheeda ta yi ta k’ara cewa,

“Ina ji abunda ya saka Kamil bai tab’a gaya miki shi wane ba saboda yana jin tsoro in har kinsan wane baban shi zaki canza mishi”

D’aga kanta tayi saboda ta yarda da maganar shaheeda, a makaranta bai tab’a nuna mata iyayen shi nada kud’i ba, kuma baban shi gwamna ne, dan sau da yawa ita take siya misu abinci, har kayan sawa ma wani sa’in ita take siya mishi saboda sai ya saka kaya d’aya sau uku a jere, dukda bai tab’a amsar su ba komin mitar da zatai, ran 18th birthday d’inta dab ta zai koma nigeria da ya bata wani agogo mai mugun tsada birthday gift sai da abun ya bata tsoro, ta dunk’a tambayar shi inda ya samu kud’in sai dai kawai ce mata yayi da kud’in part time jobs d’inshi dan ba guda d’aya bane ya tara ya siya mata, bata tab’a doubting abunda ya fad’a mata ba a lokacin saboda tayi mutuk’ar yarda dashi,

“Kamil mutumin kirki ne, ban tab’a ganin mutum irin shi ba a rayuwa ta, duk wanda na san ya sanshi yaban shi yake” shaheeda ta fad’a a hankali,

Kwalla ce ta cika idanunta, jikinta ya k’ara yin sanyi, duk da shaheeda ta gaya mata abunda take son ji amma baza ta tab’a iya manta abunda tayi mata ba, har yanzu tana jin zafin abun saboda shaheeda jinin ta tace ba bare ba,

“Yaushe zaki bani hak’urin abunda kikayi mun?”

Sakeena ta fad’a muryarta na rawa kamar kuka nasan kub’oce mata, dukda hakur’in da zata bata bazai saka ta manta ta rad’adi da ciwon da zuciyar ta tayi mata ba lokacin da tasan suna tare, lokacin da tasan y’ar uwar ta jini taci amanar ta,

“Kinyi snatching d’inshi daga wuri na yana taka kaf’ar shi a nigeria, saboda kina kishi dani? Ko kuma saboda kinsan baban shi nada arziki ba d’an k’arami ba? Ko kuma saboda kina jin haushin na samu me sona tsakani da Allah?”

Dukda ranta a b’ace yake a hankali tayi mata magnar, har lokacin in ta tuna abunda ya faru sai ranta yayi mugun b’aci, kwana da kwanakin da tayi tana kuka tare da neman Kamil a waya kamar tab’arbiya, anya zata yafe ma shaheeda abunda tayi mata,

“Sau nawa zan gaya miki ba laifi na bane shi ya fara cewa yan…”

Saurin dakatar da ita sakeena tayi, dan ko sau nawa zata gaya mata Kamil ne ya fara cewa yana santa baza ta tab’a yarda ba, duk da shekara d’aya da rabi kawai sukayi tare zata iya cewa tasan halin shi, tasan abunda zai iya aikatawa da abunda bazai iya aikatawa ba,

“Ya isa haka, naji duk abunda zaki ce, na gaji yanzu bani da lokacin sauraron shirman da zaki gaya mun, sai anjima”

Tana fad’ar haka ta kashe wayar, shiru ta zauna a d’akin ta, sai hawayen da suke zubowa a fuskar ta, zata iya yafe ma Kamil koda ace laifin daga wurin shi yake, amma baza ta tab’a iya yafe wa shaheeda ba sai in har tazo da k’afunta ta nemi gafarar ta, haka ta zaune tana ta zubar da hawaye masu zafi sai can daga baya ta mik’e ta fad’a bathroom danyin alwala takai kukanta ga mai duka, danshi ne kad’ai zai saka ta sami nutsuwa.

Shirye shiryen bikin Kamal akeyi gadan gadan saboda ba wani isashen lokaci, kowa yayi busy, shi kuwa ba yarda baiyi ba yai convincing d’insu ayi kawai d’aurin aure akai ta amma sam sam mami tak’i yarda, ba k’aramar drama sukayi ba da yace mata ba a abuja zai zauna ba a kano zai zauna, da ga baya ta bari da ya samu aiki a CBN, kuma branch d’in kano, ya gama plan d’inshi na tarwatsa rayuwa Sakeena, kuma insha Allah ba wanda zaiyi mishi cikas, zai kaita inda bata da kowa ya dai zaiji dad’in yi mata duk abinda ya ga dama.
+
Yana kwance akan 3seater d’in parlor d’inshi, remote a hannun shi yana ta canza channel, k’afa d’aya kan d’aya, yaji an banko k’ofa da wani mugun k’arfi, kai idanunshi wurin yayi yaga imran a tsaye a bakin k’ofa, yana ta huci, Kamal saurin mik’ewa yayi daga kwanciyar da yayi a lokacin imran ya shigo har inda yake, zai bud’e baki yayi mishi magana kawai yaga imran ya cillo mishi wani abu, sannan ya nuna abun da d’an yatsan hannun shi,
“Yi mun bayani me nake gani a katin nan, Kamal wa kake shirin aura?”
Da mugun ihu yayi maganar har sai da ya saka Kamal lumshe idanun shi da saka hannun shi a kunnen shi, sai can ya bud’e su ya sauke akan imran, daman yana jiran lokacin nan, lokacin da imran zai san wace zata zama matar shi,
“Gashi kana ganin sunanta b’aro b’aro a jiki, me kuma ya saka kake san in k’ara maka bayani”
Kamal ya fad’a tare da gyra zaman shi hannun shi ruk’e da katin bikin shi, duk yarda yake da imran bai isa ya ruguza mishi shirin shi ba, yana gani abokin nashi ya saka hannun shi a k’ugu tare da ciza leb’anshi,
“hanklin ka d’aya kuwa? kasan wace ita ka kuma fi kowa sanin matsayin ta a wurin Kamil amma har kake shirin ka aure ta?”
Yanzu kuma da aka ambaci sunan Kamil ya had’e fuska kama bai tab’a dariya ba, tashi yayi dan ya bar wurin saboda imran ya fara shirin b’ata mishi rai, kan ya fara taku abokin nashi ya fisgi kwalar rigar shi, wani irin mugun kallo Kamal ya sauke mishi, kana gani kasan ranshi yanzu ya b’aci,
“Daman maganar ta da kazo yi mun a gida last week abunda kake shirin yi kenan?”
Kamal sa hannun shi yayi ya fisgi rigar shi, sannan yabi imran da kallo, kallon harara yake mishi dan bala’in haushin shi yake ji a lokacin,
“Bazan matsa daga wurin nan ba sai har ka bani amsar dalilin auran ta da zakai, dan nasan ba santa kake ba”
Yarda imran yake maganar shima ranshi a mugun b’ace yake, amma duk zafin shi bai kai Kamal ba, kowa yasan yarda yake in har ranshi ya b’aci, amma dole ya a jiye duk abunda yake ji gefe ya tsara abokin nashi dan yanzu zai iya yi mishi aikin aika aika yaje ya gaya ma mami, kallon abokin shi yayi da wannan manyan idanun nashi, da sunyi jaa ja wur yanzu saboda b’acin rai,
“Sonta nake”
Imran hangame baki yayi ya bishi da kallo tsabar yarda abun yayi mutuk’ar bashi mamaki, shi kuwa Kamal in ka ganshi baza ka tab’a zata k’arya yake yi ba, idanunshi sunyi narai narai da su kamar har cikin zuciyar shi yana son sakeena, kallon juna suke shi da abokin shi yasan imran so yake ya gano in har k’arya yake mishi, abunda shi kuwa bazai tab’a bari ba,
“Tun ran da na fara ganinta, shine sanadiyar zuwa wurin ka da nayi”
Imran shiru yayi kamar yana nazarin wani abu, Kamal da yaga kamar abokin nashi ya fara yarda dashi yayi saurin samun wuri ya zauna akan kujera tare da ma abokin nashi nuni na shima ya zauna, sai da imran ya zauna sannan ya fara ba shi labari, k’arya ya shirga mishi tare da tsara shi yadda ya tabbata imran ba zai yi zargin shi ba, yarda abokin nashi ke kallan shi ya nuna mishi ya yarda, wani dad’i ne ya kama Kamal da farin ciki har tsalle yayi acikin zuciyar shi,
“Still, i dont think its right” imran ya fad’i a sanyaye,
“Kai a ganin ka wa yafi cancanta ya aure ta duk fad’in duniyar nan?, tunda baza ta tab’a kasancewa tare da Kamil ba na tabbata zai so ace ni na aure ta”
STORY CONTINUES BELOW
Abokin nashi bai san lokacin da ya d’aga kai ba alamun ya yarda, tabbas abun haka yake Kamil zaifi kuwa so Kamal ya auri Sakeena saboda shi da twin d’in nashi kamar hanta da jini suke, kuma shi kanshi yasan Kamal zai kula da ita kuma zai ruk’eta hannu biyu saboda duk abinda Kamil ke so shi Kamal ke so, mai da kallon shi kan abokin nashi yayi sannan ya fara bashi hak’uri, Kamal murmushi yayi tare da ce mishi ba komi, nan suka saka hirar kamar ba wani abu da ya tab’a faruwa a tsakanin su, shi kuwa kamal ba abunda yake in ba farin ciki ba.
——–
Zaune take da towel a jikinta, gashin nan nata me yawa a cikin ribbon, ga masu gyaran jiki su biyu da suka saka ta a tsakiya suna ta faman aiki, kana ganinta a wurin kasan zaman dole take dan kawai bata ta yadda za tayi, duk lokacin da ta tuna saura kwana uku a d’aura mata aure sai hankalin ta yayi mugun tashi, gashi har lokacin bata san wane zata aura ba, ko tsoho ne, ko makaho ne, ko kuma kurma ne duk bata sani ba, abunda kawai ta sani tasan yana da mugun kud’i tunda jiya da aka kawa lefanta akwati 36 aka ajiye mata, kuma komai na ciki mai mutuk’ar tsada ne, sukan su akwatinan abun kallo ne, mommy ce ta saka ta a gaba sai da taga lefan duk da bata so, zuciyar ta kullum sai ta gaya mata da taje da tambaye mommy ko sunan shi ne amma baza ta tab’a iya wa ba, tana zaune tana wannan tunanin taji an bud’e k’ofa, dukan su su uku da suke cikin d’akin sai da suka juya suka mai da hankalin su kan k’ofar, shaheeda ce ta k’arasa cikin d’akin ba sallama, sakeena wata harara ta daka mata, yanzu shaheeda ta iso gidan daga lagos amma har zasu fara fad’a,
“Me ya saka baki iya sallama ba ko kin zata d’akin kafirai kika shigo”
Itama shaheeda harara ta daka bata,
“Aka ce miki zama nazo nayi”
Bata jira sakeena ta maida mata da magana ba ta ajiye mata katin bikin ta a k’asa a kusa da ita,
“Na kawo miki kiga katin bikin ki”
Tana fad’a ta saki murmushin mugunta ga daman ta had’e hannunta biyu akan k’irjinta, k’ara cewa tayi,
“Na tabbata kika ga abunda ke ciki sai kinyi k’aramin hauka yau a cikin gidan nan”
Bata jira amsar ta ba tayi gaba abinta tare da rufo mata k’ofa, Sakeena tabi k’ofar da harara bayan ta fita tare da fad’in Allah ya shirya, banza tayi da katin duk da tana bala’in so da bud’e taga mene a ciki, sai da aka kusa kai k’arshen gyaran jikin ta taga baza ta tab’a iya hakura ba ta dakatar da masu gyaran jikin tare da jawo katin kusa da ita, a hankali ta d’auke shi daga k’asan da yake, binshi tayi da kallo kamar tana yanke shawarar ta bud’e ko kawai ta barshi, can dai ta dake ta bud’e shi a sanyaye kamar wacce bata da laka.
Wani irin mummunar fad’uwa gabanta yayi zuciyarta ta fara mahaukacin bugawa saboda sunan da take gani a jikin katin,
“KAMAL UMAR DATTI”
Haka ta furta sunanshi a fili, ji tayi hannunta ya fara rawa bayan wani irin sama da numfashin ta yayi, wani ciwon kai ne ya zo mata ta farar d’aya, me ya saka take ganin sunan twin brother d’in Kamil a jikin katin, girgiza kanta ta fara anya ba mafarki take ba, cizar lebanta tayi har sai da taji zafi shi ya tabbatar mata da ba mafarki take ba, zumbur tayi ta mik’e daga zaman da take ta fita daga d’akin da gudu tayi wurin mommy daga ita sai wannan towel d’in a jikinta, ga gida ya fara cika da bak’in da suka zo biki.
Mommy da take zaune da k’annanta a bedroom d’inta suma sunzo suna hira da shaheeda a gefanta tana cin chewing gum da faman danna waya suka ji an bugo k’ofa, sakeena da ke ma mutane fad’an sallama yau ba ta tsaya tayi ba saboda kwata kwata bata hayyacin ta, su kansu da suka ga yana yinta sunsan ba lafiya ba fuskar ta d’auke da kurkur ga jikin ta da raguwar dilka da halawa,
Shaheeda na ganinta ta k’ara sakar wani murmushi, gani Sakeena a haka yana mutuk’ar yi mata dad’i, tsugunna wa tayi a gaban mommy tare da ruk’e cinyoyin ta a lokacin idanunta sun cika taf da kwalla, kan mommy ta tambaya lafiya sakeena ta ganta haka ta riga ta,
“mommy ki cece ni, Dan Allah kada ku aura mun shi, dan girman Allah ku raba ni dashi, wallahi bana sanshi mommy in har kuka bari na aure shi zan iya zare wa ko ma in mutu saboda bak’in ciki, dan darajar Allah mommy ke cece ni kada ki bari daddy ya d’aura auran nan, wallahi na yarda ku bani kowa in aura amma banda shi dan Allah mommy kiji tausayi na”
Yanzu hawaye ya jik’a mata fuska, bayan kuka wiwi da take ga jikinta da bai bar rawa ba, kowa na wurin yayi shiru ita ma mommy jikinta yayi mugun sanyi, tana mutuk’ar san Sakeena kamar y’ar cikin ta, ita kanta sai da tama daddy d’in maganar ya janya auran amma yak’i sauraron ta, ya zatayi da y’ar marainiyar nan, ji tayi itama idanunta sun cika da kwalla, jawo sakeena tayi da take faman kuka kamar ranta zai fita ta rungumo ta jikin ta, ta fara juya ta a hankali alamun rarrashi,
“Ki yi hak’uri y’a ta kinji, ki yafe mana”
Abunda mommy ta iya fad’a kenan saboda tasan mijin nata bazai tab’a canza ra’ayin shi ba duk abunda zatayi, wani irin masifafan taurin kai ne dashi, ita kuwa sakeena da ta k’ara sakin wani kuka me d’auke da abun tausayi,
“Bazan iya auran shi ba ballan tana har na zauna dashi, mommy bazan iya ba”
Cikin shashek’ar kuka tayi magana bayan rawar da muryar ta take, mommy lumshe idanunta tayi da taga kwalla na shirin zuba, har sauran k’annenta sai da suka sauko daga kan kujera sukayi kan sakeena suna rarrashi, ita kuwa shaheeda ta d’ora k’afa d’aya kan d’aya sai faman kwai take da chewing gum d’in bakin ta, abun nayi mata masifar dad’i.
Mommy da taga Sakeena na shirun rikece musu tak’i yin shiru ga jikin ya d’auki wani irin zafi, ta kama fuskar ta ta fara magana a hankali,
“Ki kwantar da hankalin ki, zan wa kawun ki magana kinji, ki daina kuka kada kiyi ciwo, insha Allah zan shawo kanshi”
Sakeena k’ara sakin kuka tayi amma wannan karan kukan dad’i ne, dukda tasan abu ne me wuya ya canza ra’ayin shi amma yarda mommy tace za tayi kokarin shawo kanshi abun yayi mata dad’i, da kyar ta iya daina kukan, har sai da monmy da kira hamida tace tazo yanzun nan, sai da hamida ta iso, mommy da ita suka zauna suka ci gaba da bata hak’uri sannan suka sanu tayi shiru.

About AIS

Check Also

ZAFIN RABO CHAPTER 7 BY SAKIEYY

ZAFIN RABO CHAPTER 7 BY SAKIEYY                Www.bankinhausanovels.com.ng  Tana …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *