UMM ADIYYAH CHAPTER 72 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 72 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Akwai matsala, Hajja ta kafe kai da fata ba
zancen na maida Ummu, idan ta ga na
je da mutane za ta san da gaske na ke yi.”
Dariya Salisu ya saka ya dade yana yi. Zaid ya
hura hanci yana harararsa, “Wane

irin abu ne, ina maka magana ka na min dariya.

Ka ji me na ke fada maka kuwa? So

suke yi su horarmu a yanzu, a lokacin da ko-

mai ya kwance min, ba za ka tsaya a

nan ka na dariya ba. A takaice ma, da akwai

jirgi ma da dare yanzu za mu tafi.”

“Easy Malam, je ka dai da safen ka juyo.

Kuma za ka biyani daga kai har Umm

Adiyya,

“Duk abinda ka ke so,”

“Kar ka yarda ka sake batawa ‘yar mutane,

idan ka kuskura na shiga maganar nan,

don kafun Baffa ya ganka zan maka ba dadi.”

“Ka fara sani tunanin kai ke son Ummu ko ni?

Duk yadda ka ce hakan za ayi Inshaa

Allah ba za a samu akasi ba, yanzu za mu je koo

yaya?”

“Sai da safe injiniya, je ka kwanta ka na

bukatar barci.”

“No, matata na ke bukata, ka san duk zancen

da za ka tsara saboda gobe kai za ka

yi Magana, ka rarrashi tsoffinmu.”Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Me zai hana Ummun ta fada masu da kanta ta
amince, tunda don ita ake ki?”
Zaid ya yi shiru yana nazari. Eh! Tabbas Umm
Adiyya ita ce maganin Hajja Ku.
“Wataran ka na da tunani dan group, na gode.”
Janyo shi ya yi ya rungume shi,
sannan ya sake shi, yana ta fara’a. Kai ka ce an
ce masa, ana daura auren ne.
“Yikes, ka san mutane ake kiwo yanzu ko? Kar
ka sa gobe makwabtana su daina
min magana.”
“Su suka sani. Sai da safe, karfe bakwai zan
iso Inshaa Allah.”
“Me ya faru da karfe shidan kuma?”
“Ah ba ka tsammanin na tashi Madam da asus-
suba ai, kuma ka san sai ta dan
shishirya tunda ban fada mata… Subhanallah,
bari na sanar da ita batun tafiyar.”
Salisu ya kada kai yana murmushi, daga nan
Zaid ya juya. Ya koma mota, kai tsaye
gidan Abba ya isa, sai da ya danna kararrawa,
yana tsaye yana jiran a bude ne, ya
duba agogonsa, ai kuwa nan ya ga karfe goma
har da minti goma sha uku.
Ya Salaam! Me yake tunani zai kamo hanya ya
zo war haka? Har ya sa Kafa zai juya
ya ji an bude kofar. Yana daga idanu suka ci
karo da na Abba.
“Zaid?
“Na’am, Abba.” A take a lokacin sai ya rasa
abin fadi, ya hau raba idanu.
“Lafiya me ke faruwa? Shigo mana ka na tsaye
a waje?”
Karasawa ya yi, ya bi bayan Abban suka shiga
falo.
“Ehm… na zo na gaisheku ne dama ban san
dare ma ya yi haka ba.” Abba ya kura
masa idanu. “Ba komai, ba mu shiga ba tukuna
ai,”
A take ya ji wani karfin hali ya zo masa,
“Abba daman ina da wata maganar kuma.”
“Ina jinka.”
“Na je na samu Baffa ne dama batun Ummu, to
ya dai amsa, amma bai sake ce min
komai ba. Hajja kam ta ce ba ta ma san maga-
nar ba. Abba duk da na san mun yi
kuskure a baya, amma duka mun gane inda
muka kasa, yanzu mun daidaita da ita.
Ina rokon alfarmar a mayar mana da au-
renmu.”
Abba ya yi shiru yana kallon Zaid, kai a
sunkuye yana maganar da kyar.
“Akan me ya sa za ku koma? A ganina hakan
ya fi maku ba takurawa kuma kowa ya
yi abinda ya sa a gaba. Ka san me ya sa Baf-
fanka ya ki amincewa da batunka?”
Zaid ya yi saurin girgiza kai.
“Je gida da safe sai mu yi Magana. Inshaa Al-
lah.” Www.bankinhausanovels.com.ng 
Ba yadda ya iya, haka ya tashi ya tafi jiki ba
kwari, ya koma gida. Bai ma yi maganar
tafiya da Umm Adiyyar ba. Salisu ya kira ya
ce an fasa tafiyar.
Haka ya yi wunin washegari sukukuf! Duk
yadda yake son ganin Ummu ya hakura
wa ransa, ya fi son ya je mata bayan komai ya
kankama. Don haka a waya kawai
suke magana.
Da yamma ne kawai ya samu wayar Abba. “Ka
shirya gobe za mu yi tafiya idan
Allah Ya kaimu.”
Kan shi ya kulle, amma duk da haka ya amsa.
Salisun dai ya sake yiwa magana ya
fada masa abinda ake ciki.
“Ka kwantar da hankalinka, ba komai Inshaa
Allah, duk abinda ake ciki, sai ka fada
min dai.”
A safiyar Abba ke fada masa Gombe suka
nufa. Zuciyarsa a baki dai haka aka yi
wannan tafiyar. Sai da suka isa ya fahimci
dukansu ne suka taho. Maami da Umm
Adiyya jirgi suka biyo. Don haka kusan isarsu
gidan tare.
Wayar Umm Adiyya ya kira, sai da ta yi kara
kusan biyar tana katsewa ba ta dauka
ba. Daga baya ya tura mata sako.
“Ki yi hakuri, ki daga mu yi Magana.”
Sai da ya dan bada lokaci, ya tabbatar ta ga
sakonsa, sannan ya sake kirarta a
waya.
Twinkle, me ya faru ne, uhm?”
“Ban sani ba ni ma, kai zan tambaya ai.”
“Sorry, please, na san fushi ki ke yi, amma ki
yi hakuri komai zai zo karshe soon
Inshaa Allah.”
“Shi ne har ka koma ba ka nemeni ba, bare ma
ka fada min abin da ake ciki, bayan
cewa ka yi na jira, sai ka dawo.”
“Fito falo, gani a falon Maami sai mu yi mag-
ana.”
Sai da ya dauki kusan minti hudu tukun ta fito
fuskarta a daure, ta ki su ma hada idanu. Zama ta
yi a kujera a hankali ta ce, “Ina wuni?”
Hannu ya sa ya goge tsakanin idanunsa da
karar hancinsa, sannan ya zauna.
“Twinkle, don Allah ki yi hakuri kin ji? Na zo
gida ranar Abba ne ya bude kofa, kin ga
dai ba zance ya kira min ke ba ko? To mun yi
wata maganar da shi, sai ya ce na je
sai ya nemeni, wannan ya sa ban shigo na
ganki ba, ba ki san yadda na ke son
ganinki ba ni ma. Sosai, amma yanzu dole mu
bi a hankali, mu samu su amince.”
Bude idanu ta yi tana dubansa. “Dukansu sun
ki ko?”
Wata kasalalliyar murmushi ya yi mata, sannan
ya gyada mata kai, “Kar ki damu za
mu shawo kansu Inshaa Allah. Ke dai kawai ki
yi ta samu a addu’a, kin ji? Mun san
dama za mu samu wannan tangardar, dole
kuma mu shirya masa, kin san sha’ani
na iyaye dole mu lallaba su ko ba haka ba?”
Kai ta gyada masa, idanunta suka ciko da
hawaye. Tabbas yanzu take kara ganin
illar kai kara bare kuma ace ayi sulhu a ki yi,
ga shi yanzu sun zo abin yana
damunsu, ba yadda suka iya.
“Okay, yanzu ki yi murmushi, ki cire abin a
ranki. Na san zuwa anjima ko gobe wata
kila a neme mu gidan Baffa. I want you to be
strong, for us.”
“Inshaa Allah.” Har ta yi shiru ne, kuma ta ce,
“Amma idan ba mu shawo kansu ba
fa? Www.bankinhausanovels.com.ng 
Zaid shiru ya yi yana nazari, shi bai taba yarda
da bahagon tunani ba, a kullum
tunanin alkhairai ya faye yi a ransa, don haka
ya sauke ajiyar zuciya. “Za su yarda
Biizinillah.”
Idanunta sun yi narai-narai! Ta yi dan gajeren
murmushi kumatunta suka loba,
hakan ya sa shi ma ya yi mata murmushi. “Ina
sonki Adiyyata, ba abinda zai shiga
tsakaninmu In shaa Allah.”
Maami da take tsaye daga bakin kofar daki
tana hango su, sai da ta ji zuciyarta ta
matse wuri guda, “Oh Allah mai iko.” Irin
wannan abu tsakanin Umm Adiyya da Zaid
yana ba ta Mamaki, lokaci daya ana nan kamar
a hadiye juna don so, lokaci daya
kuma anyi barambaram!
Duk da hakan kuma abu daya bai gushe
tsakaninsu ba, domin sai da tura ta kai
bango Umm Adiyya ta fadi abinda ya shiga
tsakaninsu. Tabbas ta san Zaid zai rike
mata Ummunta, ya kula mata da ita. Don haka
ita kam ko kowa ba zai ba su goyon
baya ba tana tare da su, ina amfanin badi ba
rai? Tunda sun sasanta ai komai ya
wuce kuma. Kamar yadda Zaid din ya yi tu-
nani kuwa da dare Abba da Baffan suka
kira shi.
Abba ne ya fara magana, “Mun fara magana
ranar na katse ka, ina son ka san da
cewa Ummu ta gabatar da maganar wani wurin
Baffanka.”
Wata faduwar gaba ce ta riski Zaid, ya ji kamar
an sara masa gatari aka. Gyada kai
ya yi, “Eh na sani Abba.”
“Ka san hukuncin neman aure cikin nema?”
Dago idanu ya yi ya ga Baffa ya kure kunne
yana saurarensu.
“Na san ya haramta yin hakan. Abba amma shi
wancan ya fada mata cewa ya
janye.”
Abba ne ya kalli Baffa, “Haka aka yi?”
Zaid ya san suna son su saka shi a kwana ne.
Don haka bai amsa ba. Baffa ne ya
gyara zama ya ce, “Mu ba mu da labarin wan-
nan, idan wancan ya zo har nan ya
same mu ko magabatanshi suka ce an janye to.
Sai mu ji, amma ko hakan ta
kasance ba lallai bane mu saurare ku. tunda ai
ba aikinku kadai muke yi ba da za ku
yi ta mana yawo da hankali ku na samu a bakin
jama’a. Ina ce kai nan ka dauko
mana wata yarinya, ba ka nan ma abokin kan
can ka wakilta ya yi jagora aka je aka
nemi auren, ka zo ka ce mana ta fasa abin ya
warware. Www.bankinhausanovels.com.ng 
Zaginmu ku ke so ayi a gari ko meye? Ni
shiririta ce sam ba na so. Don haka duk ku
tattara ku ba ni wuri, ba na son na saurari
kowa. Idan ita Ummu an warware baikon
can a kanta, to ni da na bada auren Ummu, ba
ni da labari, kai Zubairu kai ne
mahaifinta, ban sani ba ko kai ka samu labarin
hakan?”
A take Abba ya girgiza kansa, yanzu kam ba
tantama Zaid ya san iyayen sun hade
masu baki ne.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

About AIS

Check Also

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE               …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *