UMM ADIYYAH CHAPTER 71 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 71 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

har za ka zo dama ka dawo da
matar taka shine ka rabu da ita, ka ki a
daidaitaku tun lokacin a gaban kowa ka yi
fafur. Ka ce ba ka san zancen ba. Ai na dauka
ka na da fadin kanka ne, ya sa ka
yanke wancan hukuncin. To bari ka ji, na fada
maka ko iyayenka za su amince, ni ba
zan yarda ka koma zaluntar yarinyar nan ba,
akai gaba.”
Take fa ya ji hankalinsa ya kara tashi, ya ma

rasa ta inda zai fara taro tsohuwar nan,

wannan ya sa ya ce, “Idan tokenki tana so ta

koma fa?”

Wani

kallo tayi masa ta ce, “Kai, Malam tashi

ka bacen da gani, na ga alama sakin

fuska ya janyo ka na min kallon wacce ba ta

san me take yi ba.”

Shi kam yau nasa ya same shi.

**x**********

BABI NA ARBA ‘IN DA HUDU

Dama Hajja Kubitto yaya, bare ka tabo To-

kenta? Dabara daya ta fado masa. Baffan

Legas ya kira a waya ya yi masa bayanin ko-

mai akan yadda Hajjan ta ciji birki, kuma

Baffa ma ya ki motsawa kan batunsa. Da yake

kowa ya san yadda Hajjan take da

autantan, duk abinda ya ce, to zai yi wuya ta ki

yi. Don haka ya bullo mata ta can.

Amma cikin ikon Allah wannan karon cewa ta

yi.

“Kai Rilwaanu, idan ka damu da ka ga toke, ta

yi aure. Ka samo mata wani mijin, ba

dai wannan mai shegen mugun hali da kafiyar
ba. Lokacin da ake tausan sa da
lafuzza. Duk da mun san dole abu ya yi mata ta
nemi sakin nan dai, ai bai nemi a
sasanta ba, sai da ya je duniya ta garo shi. Zai
ce zai dawo mata? Na yarda ‘yarku
ce, amma ni kam dai ba hannuna a auren nan
da Malam yake son rikitowa, ya sa a
tursasa yarinya, kwana biyu ya ga wani aibun
nata ya korata.”
“Hajja hakuri za mu yi ta yi da su, kin san
yaran ne yanzu sai ana yi ana masu
lallami da addu’a. Amma idan muka ce za mu
biye ta tasu, to zumuncin ma yanzu
kam ba za ayi shi ba. Tunda dai har duka sun
sauko din, ina ga a bar su su koma
din a bi su da addu’a Allah ya sanya alkhairi,
da kaina zan zaunar da su, na yi masu
jan kunne, za mu taho da su Firdausi ma cikin
satin nan, sai mu yi maganar sosai.”
“Hmm! Dan nan da ka yi zamanka, kar ka yi
asarar kudin jirginka.” Www.bankinhausanovels.com.ng 
A gaban Zaid aka yi wayar da Baffan Legas.
Ya san yanzu kanm sai dai ya sawa
sarautar Allah idanu kan lamarin Hajja Ku.
Kafin ta sauko za a sha fama.
Hajja Kubitto dai ba ta sauka ba, don haka ya
juya wurin Modibbonta, don shi kadai
ne ya ki sa kansa kan batun shari’ar auren nasu,
lokacin da aka yi. Wata kila shi zai
fahimta. Shi ma ya sake maimaita masa
bayanai, ya kuma nemi albarkarsa.
Modibbo ne ya ce, “Ka ga wancan karon ban
ce komai ba a kan batun ku ko? To ba
wai don ba ni da abin cewa bane, amma yanzu
da ban ce ba, ina fata ka dauki
darasi a cikin shiruna? Abinda ya faru shi nee
jarabawarku. Kun yi kokari kun cinye,
duk da ya dauki lokaci kan ku fahimci hakan,
idan ku ka bari aka sake jin kanku, ya
tashi a kuskure ya dawo wauta, don haka na ke
maku fata Allah Ya tsame ku daga
cikin wawaye.”
Zaid ya dade da sanin Modibbo, mutum ne
mai karancin kalamai, wannan ya sa duk
abinda ya kan fada masu yake natsuwa da
kyau ya saurara, domin ma’abocin
hikimar zance ne.
“Mun gode sosai, kuma za a kiyaye Inshaa Al-
lah.”
“Yawwa yanzu na ji dama-dama. Allah ya yi
albarka.”
“Modibbo, Hajja ce yanzu ita ta kafe kai da
fata ba ta san zancen auren. Kuma Baffa
ma yana nan fafur ya ki ma zancen, kuma ta
kirasu ta ce kar wanda ya sa baki a
batun auren.”
Modibbo ne ya yi murmushi, sannan ya gyara
kishingidansa, “Ka san me za ka yi?”
Da sauri Zaid ya girgiza kansa. “A’a.”
“Ka koma Abujan.”
Ya koma Abuja kuma? Ai shi kam ba shi ba
komawa, sai ya samu amincewarsu kaf.
Amma gudun kar ya yi gardama, aga ka-
sawarsa ya sa ya amince zai daure ya koma
ko ma menene sai ya gani.
**********
Justice Khadija ta yi shiru tana sauraren ‘yarta,
amma da alama babu cikakken
abinda zai fito daga bakinta.
“Ummu idan ba ki shirya fadin abinda yake
ranki ba, ki bari sai kin shirya kin sani a
gaba tun dazu sai in ina ki ke min.”
Nan da nan ta kai hannu bayan wuyanta tana
yan soshe soshe, “Dama Maami,
ehm… Yaya Zaid ne ya ce min yana so mu ko-
ma…” A hankali ta dago idanunta tana
kallon fuskar Maami, ta ga ko me za ta gani a
fayyace a kai.
Amma babu komai, sai shiru ko murmushi ko
tsumewa duka babu komai. Haka aka
dauki tsawon minti biyu, daga baya ta mike za
ta bar falon. Maami ta ce, “Ummu,
dawo ki zauna.” Www.bankinhausanovels.com.ng 
Wani kullallen yawu ta hadiya.
“Yaya za ki fara magana ba ki karasa ba, ki
kama hanyarki za ki tafi?”
“Maami kawai dai na ga kamar ranki ya baci
ne, amma babu komai, shi kenan
daman zan je na kwanta ne.” Tana magana
hawaye na bin fuskarta, dama ta sani
dole Maami da Abba su ki karban zancen nan
da hannu bibbiyu, bayan irin wautar
da ta tafka tana ta fade-fade, yanzu ga irinta
nan, da wani idanu za ta kallesu, ta ce
ta dawo ta fasa cewa za ta mutu, idan an bar ta
a gidan Yaya Zaid.
“To shi wannan hawayen naki, idan akwai na
sayarwa, ina ga zai fi kyautuwa ki
sayar, don za ki yi arziki.”
“Maami, fa…” Bayan hannunta ta saka tana
mutsuke idanun, kamar daga sanma ta ji
Maamin ta ce, “Ke me ki ka ce masa?”
“Na’am?”
Kallonta kawai Maami ta yi ta ce, “Uhm!
Dama cewa na yi bari na fada miki tukuna
dai.”
Wani murmushi ne ya ziyarci fuskar Maami,
ka ji yarinya wai su za su rainawa wayo,
ko sun zaci da makafi suke zaune, tun kwanci-
yar Zaid a asibiti, oho. Ko kumna
soyayyar ce aka ce masu ba su iya ba, idan an
debe randa ta zo ta samu an sha
hidima a gidan, da ta tambayi Faruk ko baki
suka yi a gidan, sai ce mata ya yi Yaya
Zaid ya zo, kuma har dawowarta yana gidan
bai tafi ba. Ta san dai ruwa baya tsami
banza, bare ma da ba sa iya ko kallon juna
musamman bayan rabuwarsu, yanzu
kuma sun dinke ko ta ina. Sai sintiri take yi a
kansa.
“Ke me ki ke so? Ki na so ki koma?”
Kanta a sadde kasa, ta dan gyada shi da
Maami ba ta kallonta da kyau ba za ma ta
kula da cewa ta motsa ba.
“Kun san dai aiki ne ja a gabanku, amma ko?
Kin san ba karamin fushi Baffanku ya
yi ba kan batun rabuwarku?”
Kai ta gyadawa Maami, sai lokacin kuma ta
tuna maganarsu da Zaid ya ki fada mata
komai ya ce sai ya iso.
“To ina so ki shirya fuskantar dukkan wani
kalubalen da ku ka san za ku samu, ba
zance daga ina ba, amma fatana shi ne Allah ya
tabbatar maku da abinda ya fi
alkhairi.”
“Ameen.”
“Sai ku yi ta sawa a addu’a.”
“Maami?”
“Na’am?”
Ki na ga idan na amince ba damuwa?” Maami
ta yi wani murmushi na manya, wato
ita nan wayo take mata, tana so ta san ko tana
goyon bayan abin ko kuwa akasin
haka.
“Ummu, mu farin-cikinki shi ne abinda muke
so, tashin hankali bayi da dadi. Idan har
muddin kun dauki darasi kan abinda ya faru a
baya, ku ka kiyaye, to ni ba ni da wata
matsala.”
****k ***** ***
Zaid yana dawowa ofis ya wuce kai tsaye, saboda
ya kwana biyu baya nan. Sai da
ya sha kan ayyukan da ya samu jingim, nan mma
Femi yana nan amma abubuwa sun
yi yawa kasancewar yanzu wani sabon sakatare
gare shi, don Stella ta fara hutun haihuwa.
Yana kammalawa ya fada mota, sannan ya
daga waya ya nemi Salisu. Www.bankinhausanovels.com.ng 
“Dan group ka na office ko gida?”
“Haba sai ka ce wani kai, kalli agogo mana
karfe tara kam, ai duk wani mai iyali, ya
san inda dare ya yi masa.”
“Ban son shegantaka, yi min gorin iyali na san
ka na da mata.”
“Waye ya so hakan, idan ba kai ba? Yanzu dai
koma meye ne, sai da safe ni na
shiga.”
“Za ma ka fito ai don gani a kofar gidanka.”
“Kai Wallahi ba ka da mutumci watarana, ka
faye naci kamar da ya so fitowa a ciki.”
Salisu ya mike ya dau makulli ya saka
takalmansa, sannan ya nufi kofar gidan ya
bude.
Suna hada idanu ya ce, “Me ya same ka haka?”
“Ka tambayeni me bai sameni ba. Ina
Mashkura?”
“Tana ciki, me ya faru?”
“Meye shirye-shiryenka na gobe?”
Salisu yanzu kam kallonsa yake yi wani iri.
Yana sanye da soci mai gajeren hannu
da wando jins mai ruwan bula da agogonsa a
hannunsa, ya tsaya hannayensa duka
biyu a kan kugunsa. Www.bankinhausanovels.com.ng 
“Daga ina ka ke?”
“Daga office, ina son kayi min wata alfarma
ne. Ka shiga ka shirya da safe za mu tafi
Gombe.”
“Kai fa wataran ka na wasu abubuwa kamar
wani tababbe, me zai kai ka gida bayan
yau ka dawo?”
“Akwai matsala, Hajja ta kafe kai da fata ba
zancen na maida Ummu, idan ta ga na
je da mutane za ta san da gaske na ke yi.”
Dariya Salisu ya saka ya dade yana yi. Zaid ya
hura hanci yana harararsa, “Wane
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

About AIS

Check Also

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE               …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *