UMM ADIYYAH CHAPTER 70 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 70 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

***********
Zaid ya san yakin da yake gabansa a wannan
lokacin ba na wasa bane, don haka,
bai dauki damuwar Adda Sadiya a matsayin
wata damuwar da za ta daga masa
hankali ba.
Ai ko ya tarar da yaki a ka.
“Oho, to, to, to. Wace Ummun kenan?” Baffa
ya tambaya lokacin da ya sanar da shi,
sun daidaita da Ummu, yana so kuma a ja masa
gaba ayi magana. Tunda duka
yaran gidan idan an tashi aure, wurinsa ake
zuwa tambaya ko kuma shi ya je ya yi.
Tun daga lokacin ya san tasa ta same shi.
“Baffa, Umm Adiyya dai ta gidan nan,
gidanmu. Mun zauna mun yi magana, na
fadawa su Baffan Legas da Baffa Mai
Kano, to amma kai ma na ga ya dace na zo na
fada maka saboda ayi min jagora.”
Sarai Baffan yake sane da cewa dan nasa ya bi
kan ‘yan-uwansa, shiru ya yi yana
so ya ga iya gudun ruwansa. Kallonsa yake yi
kamar ya kwada masa mari lafiyayyu.
Amma ya daure bai yi hakan ba, “Mun maka
kama da shashashu ne?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Wani gumi ne ya karyowa Zaid, nan take ya
gwammaci dalilin da ya sa ya yi tunanin
saka gare da hula a yau din, yana tunanin
sanyin da ya buso ne a safiyar ranar a


garin Gombe, amma a halin yanzu ko na April
a Sakkwato ya fi shi jin dadi.
“Baffa, ayi hakuri, na san abubuwa da dama
sun faru, wanda ba dadin tunowa da su
bare yinsu ma a karon farko. Amma mun samu
fahimtar juna da ita, kuma ina so na
maidata dakinta.”
Jaridarsa ya daga ya budo shafin da yake
karantawa, kafin Zaid din ya shigo, ba
tare da ya ce da shi ci kanka ba. Ganin shirun
ya mika ne, ya sa ya hakura da
batun, ya mike ya fita jiki ba kwari.
****k *********
Washegari Sai wuraren karfe sha daya ya gama
kimtsawa ya yi shirin kwanciya,
amma ba zai hutawa ransa ba, har sai ya ji
daga Twinkle dinsa, wunin ranar kaf!
Tana ransa, amma ba su yi magana ba, tun
gaisuwar safe. Wannan ya sa ya zauna
a bakin gadon, ya danna lambarta.
Sallamarta ce ta fara ratsa shi, yana amsa mata
ya ce, “Yau dai ko ayi cikiyata, Www.bankinhausanovels.com.ng
bayan ba aji na ce komai ba.”
“Yi hakuri, na so kira, amma da yake na ji ka
ce kai da su Yaya Saadik da Yaya
Nazeef za ku je Nafada ne, ya sa ban damu ba,
na san abubuwa ne su kayi makuu
yawa.”
“Yanzu kam ma na kara tabbatar da batun.”
Me fa?”
Okay, na ce miki zan yi tafiya, amma shi ne ko
ma ki dan kira ki ji isa ta.”
“Yau na ga ta kaina, ka yi hakuri, ban same ka
bane, amma ai na turo maka sako.”
“Eh, kin turo “Yaya hanya? A huce gajiya. Al-
lah ya kiyaye hanya.’ Wa take tura irin
wannan sakon wa mijinta?”
“To ba addu’a na yi ba? Kuma yaushe ka zama
mijin nawa?”
Murmushi ya yi kawai hade da yin kwafa.
“Don Allah ka yi hakuri, to idan mun gama
Magana, zan turo maka d0000gon
message.”
“Ba kin daina so na ba? Har da kallon idanuna
dai kin yi Twinkle, ki ka ce ki na jin
so-na yana fita a ranki, har ma hira kin yi, da
bazawarinki a gabana.”
Dariya ta yi sosai, jin har cikin ransa ya fadi
maganar da ya fada. “Don Allah Yaya
Zaid, ka daina cewa bazawarina, kalmar ba
dadin ji kamar wata…”
“Wata me? Me zance to? Ba duk ke ki ka jawo
mana ba?” Ya fada hade da
jinginuwa da filon da ke kan gadon, ya mike
dafafunsa a sama.
“Kar dai ayi ta tone-tone. Sai da safe zan
kwanta.”
“Ai ba ki isa ba, ki hana ni barci, ke ki yi naki
har ma da minshari?”
Umm Adiyya ta yi dariya kasa-kasa tana jin
zuciyarta na bada wani balli-balli, ina,
yau ne ta san tana jinta a seti.
“Adiyyata! Don Allah kar ki sake nisantar
kanki daga gareni. Ba zan taba iya jurewa
ba. Allah kadai ya san mutuwar tsaye nawa na
yi da na rasa ki.”
“Hmmm!”
“Wai sayan bakinki zan yi ne, kan ki min mag-
ana ko me? Kar ki sa gobe na zo da su
Baffa Mai-Kano a daura auren.”
“Lala lala, ni din kuma sai aka ce na zamo ‘yar
tsana?”
“Da din ke mece ce? My babydoll. Ki zauna
cikin shirinki, ban yi tsammanin za ki iya
kai sati a gidan Abba ba,”
Dariya ta yi cikin nishadi ta ce, “Yaya Zaid
don Allah ka bar zancen wasa, ka ga
haka wancan karon ma.. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Na taba miki zancen wasa?” Nan da nan ta
hadiyi wani abu makogwaron wuyanta,
jin canjin sautin muryarsa. Ta san a hakikan ce
ya yi magana, kuma tana wasa, sai
dai ta ji an daura auren.
“Ka bi duk matakan da suka dace wajen neman
yardata, wata kila na duba
sha’aninka. Date me.” Ta samu kanta da fadin
haka.
Idanu ya bude ya kada harshe, sannan ya
lumshe idanunsa tamkar tana kallonsa,
“Twinkle, darajarki da kimarki da kuma mu-
tumcinki sun wuce wurin, zan mai da ke
matata, na mika miki martabar da ta dace da
ke. Daga nan zan ba ki as many dates
as our busy lives can let us have and more.”
“Shi kenan, Noorie.”
“Sake fada, na ji?”
Shiru ne ya dan ratsa tsakaninsu, ba ka jin ko-
mai sai fitar numfashinsu a sannu a
hankali, “Noorie,” Ta sake fada a tausashe.
“Na amince zan kara zama matarka, iya
rayuwata. Allah ya ba mu sa’a cikin
tafiyarmu, ya kawar da dukkan wani sharri.
Sannan don Allah idan ka ga na fara
baudewa ka dan maren, ko zan shiga taitayina,
amma kar ka sake biye min ka rabu
da ni.”
“Ina so ki sake maimaita min wadannan kala-
man ranar da na dauke ki daga gidan
Abba.”
“Ka na nufin dai ranar da aka kai ni gidanka?”
“Uhm uhm! Da kaina zan dauke ki, domin ak-
wai abu daya da na ke son na fadawa
Abba.”
“Hmm! Allah ya nuna mana, amma dai ka san
mun yi alkawarin ba kai kara.”
“Sai na sauke wannan karar, alkawarin zai fara
aiki.”
“Ah, Yaya Zaid gaskiya wannan cuwa-cuwwa
ne.” Ta fada a shagwabe,
Ya Ilahi! Abinda muryarta ke haddasa masa.
Allah kadai ya sani, “Hankali kar ki sa a
daren nan na fita kai sadaki.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsam ta yi tana raba idanuwa, “Me na yi?”
“Kin san tasirin da ki ke da shi kuwa a kaina
Twinkle? Ba za ki taba ganewa ba,
amma zan tabbatar da na kwatanta miki shi, ki
samu misali.”
“Good night.”
“Kar ki yarda ki kashe min waya.”
“A’a wai, na ji dai kamar ka dan fara jin barci
ne.” Ta fada, amma a hakikanin
gaskiya kwalla ne suka taru a idanunta, na
tsananin jin dadi.
Da wata irin murya mai sanyi, da nauyi, da
zurfi da shiga zucci ya ce mata, “A’a, ban
gaji da jinki ba, bani labarin komai.”
Haka ya rinjayeta da hira, har sai da ya ji, duk
abinda ya fada mata, sai ta yi hamma,
kan ta amsa, ya ce, “Zan mana addu’a, ki shafa
ki yi barci. Yanzu kam na san na
gajiyar da ke. Ki huta gajiya.”
Shiru ya ji a daya bangare, “Hello, Twinkle?”
Bai sake jin muryarta ba, sai murmushi
kawai ya yi, ya kada kansa, ya yi addu’a hade
da seta alarm dinsa, don ya san yau
kam sai da alarm zai iya tashin asuba.
**********x*
Haka aka dauki kwanaki biyu ana abu guda.
Baffa bai ce komai ba. Zaid bai fasa
roko da magiya ba. Don haka ya badawa ida-
nunsa toka ya tari aradu da ka, ya
wuce gidan Modibbo, kai tsaye dakin Hajja
Ku ya nufa, ya sameta a babban falonta,
da masu aikinta biyu. Suna aiki suna hirarsu.
“A’a ni ma dai na ce na ji, kamar muryar
Malam, ashe dai kai ne. Sannunka da zuwa.
Mutanen birni.”
“Hajja ke ma dai ya kamata a dauke ki daga
nan ki je ki dandana birmin, ki ji yadda
dadewa a cikin sa yake.” Lokacin ne masu
taya ta zama suka gaisa da Zaid. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ahaf, koma dai menene, yanzu kam ka yi
kwantai ai, mutum ya zauna sama da
shekara ba mata, ina abin arziki a nan?”
Murmushi ya yi, kullum ya zo sai tayi masa
gorin rashin mata, tun baya tankawa har
ya taba ce mata ita
ma ta taimaka a wajen
kwacen.
“Hajja Ku, to ai ba zan fasa gode miki ba, idan
ki ka min kyautar matar ma, bare abu
naki, ai ke ki ke da iko.”
“Kai din wai? Wa zai sake daukar ‘yarsa ya ba
ka? Idan ka bushi iska, ka korata wa
iyayenta. Wanda aka yin dai Allah shi am-
fana.”
“Haba Hajja ke da zan daukeki mu je neman
sulhu?”
“Hala ka fara zukan wani abin ne Zaidu, oh ni
Ummu na ga abin da ya isheni.” Ba
zai tanka ba. Koma meye ta kira shi idan ta ga
dama. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Wai yanzu nan don rashin kunya tayi maka
yawa, har za ka zo dama ka dawo da
matar taka shine ka rabu da ita, ka ki a
daidaitaku tun lokacin a gaban kowa ka yi
fafur. Ka ce ba ka san zancen ba. Ai na dauka
ka na da fadin kanka ne, ya sa ka
yanke wancan hukuncin. To bari ka ji, na fada
maka ko iyayenka za su amince, ni ba
zan yarda ka koma zaluntar yarinyar nan ba,
akai gaba.”
Take fa ya ji hankalinsa ya kara tashi, ya ma

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE               …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *