TSINTACCIYA CHAPTER 3 BY NIMCY LUV

TSINTACCIYA CHAPTER 3 BY NIMCY LUV

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Jiyayi Numfashinsa na wata iriyar fusga lokacin daya sauke idanunsa a saman ƙirjinta, cikin sauri ya zame idanunsa yana shafa fuskarsa.

Bai taɓa ganin halittar da yaji yana mutuwar so, irin son nan mai zautar da mutane irin Akeela, at least zai iya good 35yrs ko sama da haka, kusan jiƙarsa ma take ba ƴar ba, ko zai haɗata da yaransa sai dai suyi age mate da  Aleema.

Malam ne yay gyaran murya kafin yace “zauna mana Bukar” zama yay still idanunsa akan fuskar Akeela kamar zai haɗiye ta,  saboda wani mugun kyau da tayi masa a fuska, ga ƙirjin nan dam, so Ma sha Allah, But even her lips are looking luscious succulent and irresitable every tensed man.

Shafa fuska ya sake yi kafin yace.

“Baffa badai Akeela tayi wannan girman ba?” Murmushi Baffa yay yace “Wallahi Bukar” “Allah sarki, the last time dana ganta tana primary 2 ne” cewar Abbu ya faɗa murya a shaƙe.

A sanyaye Baffa yace.

“Kayi hqr Bukar garin ceto ƴar dana haifa ɗan cikin ka yay asara nasa rayuwar” kamar Baffa zai kuka saboda damuwa cikin damuwar shima Abbu yace “haba Baffa, da abinda ka haifa da nawa ai duk ɗaya ne ko? Blood is thinker than water, koni i can do anything for this innocent gril, she deserved it” Murmushi Baffa yay zuciyarsa na masa zafi sosai Kafin yace.

“Ban san mene yasa Akeela tayi hakan ba, tana da hankali amma lalurar da Ubangiji ya jarabce ta dashi na neman zautar da tunaninta” da Mamaki Abbu yace “lalura?” “Eh! Tana da Amosa nin jini (SIKILA), wanda ke sonta tunda yaji labarin ciwonta yace ya fasa, bazai iya zama da mai ciwon SIKILA ba, haka nan taje ta shafa masa, shiyasa na yanke shawarar bawa wani auranta mai suna Malam Buba, yana da mata uku yara goma tsoho ne domin ya girme min, yace yaji ya gani zai zauna da ita a hakan, tun lokacin Akeela ta daina walwala na san bata son shi, to idan bata Aure sa ba wane zata aura? Eh? Kasan yadda ciwon SIKILA yake kamar Annoba a wannan lokacin musamman a wannan lokacin damuna da muke ciki, wannan dalilin yasa ta nemi kashe kanta ta wuta da bala’i”

Shiru Abbu yay Mamaki duk ya kamasa, yarinya like Akeela da ciwon SIKILA? Allah Al-hakkamu kenan  bowayi gagara Misali.

Gyara zama Abbu yay cikin serious tone voice yace.

“Cutar sikila ko amosanin jini na ɗaya daga cikin cututtukan da za’a iya cewa na neman zama ruwan dare, saboda yadda ake yawan samun yin aure tsakanin masu rukunin jini AS da AS ko SS da AS, amma Abu mafi muhimmanci Shine babu yadda za’ai ba tare da gamayyar ƙwayayen haihu ba mutum ya samu SIKILA, babban jahilci ne ma gamai cewa za’a shafa masa, ai ba tari bane, ko H.i.v SIKILA zan iya haɗata da Asthma, amma Baffa batun zaka aura wa Akeela wani can banza bai taso ba, kai mata aure inda ake sonta kuma za’a kula da ita, na tabbatar he loves her just of her beauty and..”

Shiru dan baya jin iya cewa wani abun.

A hankali Baffa yace “To Bukar yay zan? Wayewar inda kuke da nan akwai bambanci sosai” idanunsa akan Akeela yace “Allow me to go with her, ka bani ita, zan haɗa ta da miji na gari wanda zai kula da ita, tai cikakken ilimi inda zakai farin ciki zan haɗa ta da yarana” ya faɗi maganar ba tare daya shirya ba, domin ji yake ko mintina goma bazai iya ba tare daya kalli Akeela ba, yay hakan ne saboda ya samu very close to her ya dasa mata masifafan son sa a Zuciyarta wanda Turawa suke cewa _ETERNAL LOVE_ yasan kuma soyayyarsa da ita ba zata taɓa zama _FORBIDDEN LOVE_ ba.

Jin muryar Sarkin ruwa a bakin ƙofa na sallama yasa Baffa Miƙewa cikin sauri yay waje.

Yana fita Abbu ya miƙe, cikin tafiyar nan wacce ya kejin kansa ontop, a hankali ya ƙarasa inda Akeela ke shimfiɗe kamar ma matacciya,

Ƙirjinta dake sama da ƙasa ya kalla ganin hakan yasa ya tabbatar she still alive.

Tsaye yay a kanta yana sauke numfashi tare da lumshe idanunsa slowly kuma ya ƙara buɗe idanunsa, kamar zai juya sai kuma ya sunkuya dai-dai kanta yana Kallon Zallar kyan fuskarta.

Hannunsa ya sanya ya ɗan ƙara zame zanin kanta nan take sumar kanta ta bayyana irin sosai ɗin nan gata rabi baƙa rabi jaa.

Wani cute smile yay yana yin ƙasa da bakinsa zuwa saman fuskarta bakinsa ya manna a goshinta tare da bata wani special kiss wanda ya kejinsa best kiss in his whole life.

Baffa ne ya kalli Sarkin Ruwan kafin yace “fatan an samu Adnanu ɗin?” Girgiza kai Sarkin Ruwan yay yace “gaskiya babu wani labari, amma dai ga abinda muka samu” ya faɗa yana miƙawa Baffa rigar jikin Md Adnan karɓa Baffa yay yace “to mungode ƙwarai shi kuma Allah ya bayyana mana shi, idan yana raye ya kai sa hannu na gari” da Ameen Sarkin Ruwan ya amsa.

Har Baffa zai juya sai kuma ya nufi motar Akeem yana zaune zuwa lokaci ya zame rigar jikinsa daga shi sai singlet murɗaɗɗan ƙirjinsa ya bayyana, ga sumar nan har lokacin na zubda ruwa, banda sauke numfashi babu abinda yake.

“Mai sunan kawo” Baffa ya kira Akeem, gently ya ɗaga kansa tare da sauke ganinsa akan Baffa kallo guda yay masa ya ɗauke kansa yana taune leɓansa tare da lumshe gajiyayyun Maraitattun idanunsa.

“Nasan kana jin haushin na ne ko? Kana ganin kamar da gangan nai hakan ko, to wallahi tsananin son da nakewa yarinya ta yasa nai haka amma nama fika baƙin ciki a yanzu haka”

Shiru Akeem yana danna system ɗinsa ba zaka taɓa cewa dashi Baffa yake Magana ba, fuskarsa looking okay Babu wani sauyi.

Sanin halin Akeem yasa Baffa juyawa.

A tsaye Baffa ya samu Abbu yana kallon Akeela kafin yace “to ko dai kwana za kuyi ne?” Girgiza kai Abbu yay yace “A’a yanzu zamu tafi in sha Allah” da sauri Baffa yace “to bari na kwaso kayanta ko” kallon Baffa Abbu yay kafin yace “haba Baffa no need, Akeela is like my daughter zan mata komai” murmushi Baffa yay hawaye na saukar masa domin gani yake ƙanin nasa kawai daurewa yake rashin Md Adnan ba ƙaramin babban giɓi bane a rayuwarsa.

Baba Rabi ce ta shigo idanunta yay jaa sosai irin taci kuka ta ƙoshi, kafin ta kalli Abbu tace “Mungode sosai Alhaji Bukar Allah ya bayyana mana Adnanu cikin aminci” “Ameen” kawai Abbu yace domin sosai zuciyarsa ke masa zafi kuka ne kawai da bazai ba, amma ganin fuskar Akeela na yaye masa wani ƙuncin.

Baffa ya nufi wajan Akeela zai ɗauke ta da sauri Abbu yace “A’a Baffa, Ni da zamu tafi tare bari na ɗauke ta”

Hannu yasa ya ɗauke ta sassanyar Ajjiyar zuciya Abbu ya sauke yana jin zuciyarsa na sanyi sosai, wani mayataccen Murmushi Abbu yay tare da fakar idanun Baffa yay wani tura ƙasa tsakiyar wuyanta…

Bayan sallar magrib motocin su suka fara shigowa cikin haɗaɗɗan titin _Railway quarters Nasarawa, Kano_
A gida mai number 112 suka fara shigar da motocin bayan gatekeeper ya buɗe masu ƙaton gate ɗin.
Motar Abbu ce a farko shida Bala driver sai Akeela dake kwance a baya.
Mota ta biyu kuma P.a a ciki shi ɗaya yana janta motar ƙarshe kuma Oga Dr Abdul-hakeem Bukar Bello ne zaune ya ɗura hannunsa guda ɗaya a saman string motar ɗaya hannunsa kuma ya tsakiyar kansa yana hargitsa sumar kansa, a hankali kuma yake sauke ajjiyar zuciya ajajjere.
Zafi da raɗaɗi da zuciyarsa ke masa na tawowa da Akeela da Abbu yay yafi komai baƙanta masa, cos she’s the reason behind anything daya samu Md Adnan.
Bama ya so ya buɗe ido yaga yarinyar shiyasa yau zamansa cikin motar tare da lumshe idanunsa yana so Abbu ya shige da ita domin ta riga data zame masa mujiya.
A hankali Abbu ya buɗe back seat tare da zura kansa cikin motar, dim! dim!! dim!! Haka zuciyarsa ke bugawa aduk sanda ya kalli ƙyakkyawar fuskarta wata nutsuwa ta saukar masa.
Zama yay cikin motar tare da miƙa hannunsa gaba ɗaya biyun ya jawota sosai very close to him, hannunsa dake rawa yasa tare da yin baya da gashin ta wanda ya sauke wai wist ɗinta,
Lumshe idanunsa yay cikin ƙasa da Murya yace “Uhm baby na mai kyau, nine ko?” Ya faɗa yana shafa kanta sai kuma ya cireta sama tare da fito da ita daga cikin motar, dai-dai kunnanta kamar wacce ta kejin sa yace.
“I’m your dad, your boyfriend uhm baby kina cin abinci kuwa? You are so light Baby” ya faɗa yana tafiya da ita kamar wani mai sabon jini bayan yay jika da ita.
P.a dake tsaye ya ɗauke idanunsa a hankali kuma yabi bayan Abbu da some things na Md Adnan.
Tsayawa Abbu yay tare da danna wani ma danni a hankali ƙofar ya fara ja baya tare da buɗewa ciki ya shiga babban Parlo ne daga cikin ƙofar, iya haɗuwa ya haɗu komai na Parlo Ash ne daga kujeru zuwa Flowers da labulaye anything dai.
Ga ƙatuwar cineme kusan rabin bango sai deep frizer mai gida wajan uku,ga senter table a tsakiyar mai ɗauke da wata ƙatuwar flower jikin bangon parlon duk Album ɗin ayatul kursiyu ne, da fatha e.t.c
Daga can bayansa yaji ana faɗin.
“Ya..yah kamar dai ƴan gudun hijira kuka faɗo mana gida babu ko Sallama? A’a babu ruwana kuda Allah tun dai duk musulmai ne a gidan da haka nan kamar ƴaƴan arna zaku faɗu mana gida, ai ko ƴan dama ne ku kwayi sallama musan da zuwanku kuma musan abinda zamu baku”
Kallon Didi Abbu yay kafin yace.
“Afuwa Didi”
Taɓe baki tayi kafin tace “A’a astagafirullah mene kuma afuwa fisabilillahi kamar dai nace akan Bukari siya min tsire? A’a ni rayuwar duniya mai sauƙi na ɗauke ta, Wacece wannan kuma Aljanu take ko shan Inna ce ta kamata”
Ta faɗa Idanunta akan Akeela wacce take jikin Abbu.
P.a Murmushi Yay domin yana son dramer tsohuwar kafin yace.
“Barka da dare Didi”
Washe baki Didi tayi tace “A’a ƙasimu ince dai ka samu matar aure? Yooo ba Gwamma kai ba ko babu komai zan baka shawara mai kyau kabi, kaga dai babu dangi iya babu na baba jinƙai da tausayi irin nawa nasa aka baka aiki gashi kuma yanzu nace kaje wajan yarinyar idan ubanta har yanzu yaƙi yadda ta Aure ka kawai kayi mata ciki kaga ko babu komai dole a baka ita ka aura ni wallahi yarinyar ba tayi min ba” shi dai Shiru kawai yay yana Murmushi ita a dole shawara ta bashi idan kuwa haka ake bada shawara da an shiga uku.
Kwantar da Akeela Abbu yay a hankali kuma fara faɗin.
“Ummi!! Mami!!”
Mami ce ta fara fitowa idanunta ya kumbura sosai saboda kuka, baƙa kana ganinta kaga mahaifiyarsa Md Adnan zatai shekaru wajan 42 tana sanye cikin wani haɗaɗɗan lace, Zama tayi a kujerar dake farcing Abbu ba tare da tace komai ba.
Not too long Ummi ta fito daga part ɗinta hannunta riƙe da wata ƙyakkyawar Yarinyar zatai shekaru 4 haka fara ce sosai kamanin Akeem zane raɗau a saman fuskarta Amani kenan jika a wajan Alhj Bukar Bello ƴar kuma wajan Dr Abdul-hakeem Bukar Bello.
Zama Ummi tayi kusa da Mami tana sanye cikin wata orange ɗin lafaya tai mata kyau sosai zatai shekara 45 haka amma jikinta a murje yake sosai har tafi Mami gogewa da kuma wayewa.
“Barka da dare ya hanya” Ummi ta faɗa murya ƙasa.
Kallon su duk yay kafin fuska a ɗan haɗe domin bai fiya sakin fuska ba idan ba keɓewa yay da matansa ba yace.
“Kunga abinda ya faru da Adnan ko? Jikina yana bani yana raye kuma komai jimawa zai dawo gare mu, i believe cewa komai sai Ubangiji ya tsara mu ɗauki hakan a wata sabuwar ƙaddara daga Allah wacce ya jarabce mu domin gwada imanin mu, ko yarda na yarda cewa hakan ya faru ne dalilin shigarsa ruwan, amma ruwan ne dai kawai ya zama sanadi amma tuntuni Ubangijin AL-ARSHI ya tsara faruwar hakan a Lauhil Mahfouz…”
Da sauri Didi tace.
“Sadaƙallahul Azeem,amma dai Bukari ka cuce mu da baka zama malami ba ka rasa mai zakai sai siyasa, ai yasin naji daɗi daka sauka daga kujerar mulkin baki ɗaya, ai da wallahi har govmet hausi ɗin zani nace bada yawo na ni Uwarka idan suka zaɓe maka, haka kurum na fita waje a dinga shunani da baki ana gata can ɗan ta yana handime kuɗin jama’a”
Ta faɗa tana cuna baki gaba, shi dai Abbu bai ce komai ba domin yasan rikicin tsofa ne.
“To! Ubangiji ya dubi idanun mu ya sanya Adnan yana raye ya kuma dawo gare mu, Allah ka dubi halin da muke ciki”
A sanyaye Mami tace “Ameen” idanunta na ƙara kawo ruwa ajjiyar zuciya Abbu ya sauke kafin ya kalli Akeela yace.
“Ɗiyar Baffa ce da Baba Rabi dalilinta Adnan ya faɗa ruwan kuma Thank God Dr ya ciro ta…”
A nan ya kwashe labarin kakaf abinda ya faru ya basu.
Ihu da kuuu Didi tasa zani na faɗuwa tace.
“Kun kashe min Adnanu wallahi hisba zan kaiku”
Tana faɗin hakan ta nufi waje a hanya taci karo da Akeem dake shigowa fuska ya haɗe sosai ko alamun annuri babu.
Ganin haka yasa Didi washe baki tace.
“Yooo yanzu naji bayani ai cewa nayi bari na leƙa naji mai gidan Shiru fa”
Bai ƙara kallon ta ya matsa can gefe sallama ma ciki yay kai tsaye upstairs ya nufa wajan part ɗinsa.
Ganin haka yasa Abbu faɗin “Dr kazo ka duba Akeela” jin sunanta yasa Akeem yaji kansa ya sara Mami kam Miƙewa tayi domin tunda taji a kanta Adnan ya faɗa ruwa taji wata muguwar tsanarta ya cika Zuciyarta.
Da ɗan sauri Akeem ya ƙarasa haurawa saman ko takan Abbu bai bi ba ganin hakan yasa Ummi faɗin.
“Bari na duba ta”
Ɗaukan ta Abbu yay zuwa part ɗin yaransa mata, ɗakin duhu alamar duk sunyi bacci On yay na wutar bedroom ɗin Aleema,Afaf  duk suna kwance wajan Ameera da take zuwa hutu ya kwantar da ita, lokacin tuni Ummi ta ɗauko kayan aiki, cikin sauri ta fara duba ta ganin har yanzu da ruwa a cikinta yasa ta danna cikin da sauri sai ga ruwa na fita.
Tana ƙara dannawa Akeela tai hau yin tari.
Wata Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya Abbu ya sauke tana gama tarin kuma bacci ya ɗauke ta, sai da Ummi tayi mata injection  kana ta ɗaura mata drip Abbu yi yayi kamar bazai fita ba ganin kallon da Ummi ke masa yasa ya ɗan shafa kansa yace.
“Miss You dear, let’s go”
Gaba yay ta bisa a baya  kana ta jawo masu ƙofa,
Daman p.a tuni yay masu sallama ya tafi gida.
A hankali bakinsa ke motsawa yana tasbihi can ƙasa zuciyarsa, saboda zafin da zuciyarsa ke masa, cikin haɗaɗɗan parlonsa ya shiga komai na Parlon white ne.
Ya haɗu sosai har ba’a magana, kai tsaye wata corridor ya bi hadle ɗin ƙofar ya buɗe, wani irin lumshe idanunsa yay tare da sauke wani maraitaccen numfashi yaja tare da saukewa, saboda wani sassanyan ƙamshi daya daki hancinsa ya sashi lumshe idanun da bai niyya ba.
Tura kansa cikin bedroom yay bakinsa ɗauke da wata kamilalliyar sallama yana maida ƙofar ya rufe.
Derect bathroom ya nufa yana mai zare kayan jikinsa, a saman hanger ya saƙale tare da sakarwa kansa shower, a hankali yake sauke ajjiyar zuciya yana jin yadda ruwan yake dukan saman fresh skin ɗinsa.
Bayan yay wankan ya ɗaura alwala kana ta ɗauki wani long white towel ya dauraia wist ɗinsa, ko kansa bai tsane ba ya fito ruwa na sauka daga sumar kansa zuwa ƙwantaccen gashin ƙirjinsa.
Wani irin ɗaci bakinsa yake masa rabon da yaci abinci har ya manta wajan fridge ya nufa ya ɗauki Apple da cake ya fara ci bai wani ci da yawa ba ya ajjiye.
Wasu haɗaɗɗun nightwear slik Pajamas milk colour, a hankali ya miƙe tare da goya hannunsa a bayansa ya ɗan fara tafiya yana mai karanta addu’a yana bin duk kusurwa ɗakin da tofi bayan ya gama ya kwanta saman bed ɗin tare da jan duvet ya rufe jikinsa, gaba ɗaya ya ƙasa bacci tunda matarsa ta rasu wajan haihuwar Amani baya iya cikakken bacci ya saba da jikin mace sosai duk da auran kamar na dole ne bai so amma ya saba da jikin matarsa ainun.
A haka bacci ya ɗauke sa.
Misalin 4 na dare ta shiga buɗe idanunta wanda sukai mata nauyi kanta na sarawa sosai, hannunta mai ɗauke da carnoner ta kala ɗan marai-raice fuska tayi kamar wata ƴar baby Wanda ya sanya manyan dimples ɗinsa bala’in lomawa.
A hankali kuma ta shiga bin bedroom ɗin da kallo sosai gabanta ya faɗi ganin bata dan ɗakin ba, jiki babu ƙauri ta miƙe tsaye tana Miƙewa gashinta ta sauka har wajan manyan ass ɗinta.
Da Mamaki tabi jikinta da kallo ganin wata Robe Nightgown silver wacce ta sauka iya laps ɗinta gaba ɗaya manyan gwayen ƙafafuwanta suna waje ga wani gashi da yay kwance lub a saman fatar ta.
Shanyayyun idanunta wanda kullum suke a Lumshe ta ƙara buɗe, jikinta babu ƙwari ta nufi ƙofar data gani, tana tafe ko’ina na jikinta moving yake kamar tarwaɗa.
A hankali ta buɗe ƙofar ta fita ita bama ta san dare bane sai da ta fito parlon daga duhu ga wani masifafan sanyi na Kaɗawa, da sauri ta matse jikinta waje guda ta shiga taune bakinta kamar wata ƴar turawa haka ta zama cikin nutsuwa take tafiya harta isa tsakiyar Parlo tana zuwa zata shige taji an sanya mata ƙafa baya tayi tare da hantsilawa zata faɗi wata kuma ƙyakkyawar Ajjiyar zuciya ta sauke jin ta faɗa saman ƙirjin mutum…

About AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *