MISBAH CHAPTER 9 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH CHAPTER 9 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wani irin farin ciki taji ya lullubeta ,bata san lokacin da tasaki dariya ba tana fadin.

     ” Nagode Abba “

    Kafin ma yace wani abu tayi ciki da gudu tana tsananin murna.

   Binta yayi da kallo yana murmushi tare da karkada kai.

       Tana shiga daki ,ta fada kan gado ta zari wayarta tana kiran deeni,amma layinsa yaki shiga ,ta kira har ta gaji hakan ya tabbatar mata wayar sa na kashe. Amma duk da haka bata hakura ba ,haka ta dinga danna wayar har bacci ya dauke ta. 

    Deeni kuwa a wannan dare kwana yayi yana safa da marwa,kansa ya dauki zafi,yana tunanin yadda bappansa zai kaya da babansa,in yaji zai daura masa aure. To amma duk da haka Bappansu ya tabbatar musu da in har baba yaki yarda shi zai shige masa gaba a al’amarin aurensa. Saboda Bappan sa mutum ne me addini da sanin ilimin sanin yakamata,duk zafin mahaifinsa ba zai hana shi fadar gaskia ba da yin abinda ya kamata.

    ” farida insha Allah sai na mallake ki matsayin mata,sai kin zama abokiyar rayuwata,uwar ‘ya’yana ,soyayyar da sukeyiwa juna ba zai tafi a banza ba ,burinmu da mafarkin mu zai rushe ba “b

       Da wannan tunanin a ransa da zuciyarsa har asuba .

   Bayan dawowarsa daga masallaci ne ya dauko wayarsa , anan ya lura ashe ma tana kashe ne. Nan yayi saurin kunnata ,don yana son jin muryar farida kafin kowa,muryarta na bashi nutsuwa da duk wani kwarin gwiwa. Dan haka ya danna sunanta,shiga daya kuwa yaji ta dauka da sauri tana haki,tamkar wacce tayu gudu. 

    “” farida lafia kuwa ? Ya fada a firgice.

   “” haba deeni “” 

Ta fada cikin muryar haki da sauke ajiyar zuciya, ta cigaba.

  ,”” me yasa ka boye min gaskia baka fada mun ba tsawon dare ,ka sa na kwana cikin tunani da dokin wayewar gari ?

     Farida me kike fadi?  Me na boye miki ?

 Ban fahimta ba “

   ‘ deeni ashe baba da Abba sun amince su daura mana aure ?”

      “WHAT ” ya fada da karfi .

” me kike nufi ? Wa ya fada miki ? Ina kikaji ? 

   A jere ya mata wadannan tambayoyin .

 “Hey deeni relax,kana nufin baka sani ba ? 

  ” Ni ban san komai ba ,ba wanda ya fadamun .

    Farida tace ,to nidai jiya da daddare abba ya kirani ya fadamun ,yace jiya babanku yazo sunyi magana,kuma sun yanke hukuncin daura mana aure ” ALHAMDULILLAH ” 

Ya fada da karfi tare da ajiyar zuciya ,ya ce .

   _” farida wannan albishir din naki wani irin tukuici kike so na baki ? Da yardar ubangiji farida zata zamo mallaki na,uwar ‘ya’yana ?

 Ban san ma wacce irin murna da farin cikin zan nunawa abba ba,ya gama min komai a duniya farida ina zuwa ……..”

  

     Nan ya kashe wayar ya nufi falon babansa da gudun sa ,zuciyarsa cike da tsananin farin ciki da jin dadi mara misaltuwa. Ya same shi zaune a terrance na falon sa,hannunsa rike da jarida yana karantawa yana shan tea. Da Murnar sa ya iso yana daria tare da  fadin .

   “”Baba ina kwana ? Baba dama na san kana so na ,ba zaka so gani na cikin damuwa ba ,you re d best father in d world nagode baba ,Allah ya kara girma da daukaka. Baba na maka alkawari  i”ll  do my best to prove myself,,zan yi karatu ,in tsaya da kafafuna ,zanyi duk wani abinda kakeso ,daga yau bani da wani buri ko mafarki sai na faranta maka ya babana.

     Na gode da wannan gata da ka min na aura min abinda nakeso ,ka tsareni daga fadawa sharri iri iri,kamin babban gata ,ka min abinda kowani uba mai hali zai yiwa dansa. Allah ya. Kara arziki ,Allah ya barni da kai ya babana,nagode”.

     Kawai sai ya rungumeshi ,abin da bai taba masa ba da girmansa.

 Wani irin sanyi da farin ciki yaji a zuciyar sa,tabbas yana matukar kaunar dansa Deeni fiye da komai ,ganinsa haka a jikinsa tamkar yadda yake masa tun yana dan karaminsa yawanci da yake yaro in ya masa wani abu da yake so,irin wannan rungumar yake masa,yana nuna masa yaji dadi soaai da abinda ya masa.

     Tuni shauki ya dibesa ,har yaji hawaye sun cika masa ido. Shima ya dada rungumar sa tare da sa hannu yana shafa bayansa,ya ce.

   ‘Naji dadin ganinka haka Deeni,wannan farin cikin da jin dadin da na jima inason ganinsa a fuskar ka ban ganshi ba sai yanzu ,nayi missing din wancan deenin nawa da wannan moment din a kokarina na gyara ka in sa ka a hanyar da naga ya dace da kai, kazama mutum mai daraja da kima anan muka samu sabani ,muka yi nesa da juna ,muka zama tamkar bakin juna,”” 

    Ya dada manna shi a jikinsa tare da fadin . 

   “” Bari inyi enjoying wannan moment din don ban san yaushe zan sake samun wannnan kauna da kulawa daga gareka ba haka deeni “”” 

    A zuciyar sa yake wannnan maganar ,sai  dai a zahiri lumshe ido kawai ya yi yana jin kaunar dan nasa cikin farin ciki.

    Muryar deeni ya jawo hankalin mama da ya shamsu da lukman zuwa inda suke ,suka tsaya suna kallon su. Mama ce ta ga abin ba na karewa bane tace . 

    ” Deeni lafia ko ? 

  Nan ya saki baban da sauri ya nufe ta, ” Mama “

 Ya kalli ya shamsu ,ya kamo hannunsa yace ,,

  ” kaji baba ya amince zai aura min farida ,mama ku tayani godia wurin baba,ban san irin godiar da zan masa ba sai addu’a”” 

  Dukkansu murna suke suna dariar ganinsa cikin farin ciki.

 “” Deeni abinda zai sa shi farin ciki ba wani abu mai wuya bane ,dan shi bai dau duniyar da zafi ba,,,”” mama ta fada a ranta .

“” Dama nasan mahaifinka zai gane cewa abinda yake hanga maka da rayuwar da yake son maka ba shi ne a gabanka ba,farin cikinka yana ga abubuwa masu sauki,rayuwa mai sauki.Allah ya tabbatar da wannan farin cikin a rayuwarka “;;

    Ya koma gaban mahaifin nasa tare da zama a daya kujerar dake gefen sa,ya jawo hannunsa ya hada da nasa ya manna,ya ce ,,

    ” Baba me kakeso in maka a rayuwa ??

 Mahaifin ya kalle shi ya yi murmushi , ya ce.

     “. Karatu nakeso kayi Deeni ,zaka iya barin kasar nan karatu,ba zaka dawo ba sai ka gama ????????????

About AIS

Check Also

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  iya ganin damuwarta ko …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *