MISBAH CHAPTER 6 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH CHAPTER 6 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Deeni ,abba na yamana maganar aure yau,kariga da kasan hakain abba,muna gama secondry sch yake aurar damu,kuma kasan tsattsauran raayi irin nasa,ba mai canja masa,wannan akidar gidanmi ne ,ni ban isa incanja ba . Kuma deeni kasan kaine rayuwata,baza iya ko tunanin rayiwa da wani da namiji ba ,inba deeni ba . Abba yace katuro,in baba yaki fa ?

     ” bazai ki ba farida ,saboda baba naso na,kuma zan nuna masa idan bayason rasa kai na to ya auramun farida “

     Tuni muryarshi ta canja ,”Farida kimun alkawari duk runtsi bazaki rabu dani ba ki auri wani ba. Farida bansan ya zan rayu bake ba .” 

  ” Deeni nima ba zan iya rayuwa dawani ba in ba kai ba ,,nutsuwata da lafiata sai in ina tare da kai deeni” 

Cikin muryar damuwa yace ,farida muna tare duk rintsi bazamu rabu ba ,zan fadawa abba zai zo nema mun aurenki gurin abbanki”

     ” kayimun alkawari deeni?? Nayi miki alkawari farida ” ya bata amsa. 

  Nan sukaita bawa juna kwarin gwiwa tare da kaunar juna,,sannan sukayi sallama.

     Wannnan tsoron dashi deeni yake kwana yake tashi ,wato tsoron rasa farida. Yana firgitashi sosai,sabida sanin halin mahaifinshi dana farida,dukkansu suna tafia ne akan ra’ayinsu da tsarinsu,ba wanda ya isa ya canja musu ,,sai dai yakan danji sanyi idan ya tuna irin soyayyar da mahaifinsa ke masa,zai iya aura masa farida don farin cikin sa.sannan a tunaninsa daga shi har farida basu da wani dogo buri,,dakinshi zai ishesu rayuwa kafin su kai ga inda zasu.

Suna gama waya bai bata lokaci ba ya nufi dakin mahaifiyar sa,kai tsaye ya labarta mata abinda ake ciki. Kansa sunkuye gaban ta yana sauraron amsar ta,yayin da ita kuma tayi jugum tana juya maganar a ranta.

 Tabbas tasaan abu ne me wuyar gaske,sai dai kuma tasan irin tarin soyayyar farida da deenikarfin soyayyarsu ya wuce a rabasu,,ya wuce tsattsauran ra’ayi da akida irinta iyayensu ,dole ne daya zai sakko ko mahaifinsa ko nata,raba deeni da farida sai Allah .

      “”Mama””deeni ya katse mata tunani.

Ya kalketa,tunanin me kike ? Ko akwai matsala ne ? 

Tayi masa murmushi tarw da girgiza Kai , ta ce .

  “”” Bawani matsala insha Allah ,anjima idan ya shigo zanyk masa maganar ,karka damu “

 Ya sake kallonta cikin fuskar damuwa ya ce ;;

” mama ba ‘ a samj matsala ba ko ?

 Tayi masa daria ,deeni kenan ,baza’a samu ba insha Allah ,komai zai tafi dai dai .ba kai kadai keson farida ba,nima ina sonta “

   Murmushi yayi ya sunkuyar da kai,, ya fiya zuciyarahi cike da murna.

 Tun fitarsa mama tashiga cikin damuwa da maganar zuci,tasan dole akwai rigima tsakanin deeni da mahaifinsa. Nan tacigaba da addua Allah ya kawo abun cikin sauki.

 Daga deeni har mahaifiyarsa sun kasance cikin zulumi da tunanin me zai faru ? 

Jin dawowar mahaifin nasa yasa yaji bugun zuciyar sa ya karu ,ya dunga safa da marwa a tsakar dakinsa. Baiyi yunkurin fita ba ,yana jira har sai an bukaci yaje.

    Yadda deeni yake cikin tunani da fargaba haka farida ma ta kasance ,tana sauraron wayar deeni .

  Bayan Ahj umar wato mahaifin deeni ya gama duk wani abu daya saba na al’adar sa in ya dawo,yana zaune a falonsa haj A’i ta same shi da maganar deeni . 

“Alhaji magana zamuyi” ta fada tana kallon sa ,hakan yasa ya juyo ya maida kallonsa gare ta tare da tattaro hankalin sa akanta yace “””  wace irin magana kuwa “? Ta gyara zama tacw ,,nu kabata sanin soyayyar deeni da farida kuwa,,”??

Ya kalleta ban gane ba ,deeni da farida?

 “”.  Ta girgiza kai ” kwarai……

Nan ta bashi labarin soyayyarsu,da shakuwarsu, takara da cewa .

“Yanzu lokaci yayi da mahaifin farida yakeson ya aurar da ita tarw da yan uwanta,kamar yadda kasani shi mahaifinsu yaranshi na gama secondry sch yake aurar dasu ,farida kuwa bata da wani saurayain da yawuce deeni ,,dan haka tayi masa magana ya fito,ya tura iyayensa a san da maganar neman aurenta ,shi ne ya min magana ya ce in fada maka””

Alhaji ya kallwra cike da mamaki ,ya ce .

Haba hajia ,ya kikemun irin wannan maganar kamar wata karanar  yarinya ? Insu yara ne kema sai ki zama yarinyae ki biye musu ? Yaron da karatu ma ba inda yaje ? Yaron da baisan ciwon kanshi ba shine zaa nemar masa aure? Dan uwansa ma yaushe akayi maganar airen sa wanda ya girme da komai balle shi ? Da maganar shamsu ma kika min sai na saurareki amma DEENI ?ai ko ina da yarinya bazan aurawa kamar deeni ba ,yaron da yaki karatu,ya kasa nai da hankali akan rayuwar sa, yasan me yakeyi,ahekarun deeni nawa wai kike maganar auren sa? Shekarunsa ishirin da daya,yaro ne dabai san ciwon kansa ba balle har a dora masa na wata .

” baba addini ya hana dan shekara ishirin da daya aure ????

Muryar deeni sukaji tsaya daga kofa……………….

 Muryar deeni sukaji tsaye daga kofa.

  Ya karaso cikin falon hankalinsa a tashe. In akwai abinda take dagawa deeni hankali be wuce ace zai rasa farida ba ,ya durkusa a gaban mahaifinsa idanunsa jawur ,hanakalinsa baya jikinsa,,ya ce ,

“Baba addini be hanani aure ba ,hasali ma ya halattamun yin aure a wannan lokacin. Baba addini bece dan bakaci jarabawar makarantar duniya ta boko karkayi aure ba ,,addini bece dole sai kanada gida da mota da abun duniya sannan kayi aure ba . Baba ka fadamun hujja da addini ba da abin duniya ba . 

   ” ina zaka ajiye matar?

“Dame zaka ciyar da matar?:

   Mahaifinsa ya jefa masa tambaya fuskarsa a daure,saboda koda wasa bai shirya yiwa deeni aure a yanzu ba .

Baba inada mahaifina wanda yake da arzikin da zai iya rikeni nida mata ta,har zuwa lokacin da zan gina kaina incigaba da rike kaina da matata har da iyayena da kuma sauran ‘yan uwana. Baba ba zama zanyi kaita ciyar dani kana rike ni ba ,zan tashi in nema ,zanyi karatu,komai zanyi dan in kafa kaina . Baba ka taimaka mun matsayinka na mahaifina ka dafa mun .

 Baba ni dan gatan ka ne ,na roke ka don Allah kayimun wannan gatan ka auramun farida, baba idan na rasa farida na rasa komai,baba farida macece ta gari,yarinya ce kamila ,ga nutsuwa da addini,macece danake yiwa yayana kwadayin samun uwa kamar ta.

 Na jima ina gina soyayyata da rayuwata da zanyi da farida,baba banj da wata rayuwa in har ka rusa min wannan rayuwar na rasa ta…………

      Tausayinsa ya kama hajia don haka itama tasa baki tana taya deeni rokonsa. 

     Alhaji yaji ransa na baci ,,sai dai deeni yayi abinda zai yi ,amma bai isa yace zaiyi aure yanzu ba ,hasali ma ya dauki abin nasa a yarinta ,dan haka ya mike yabar musu falon ransa a bace batare da yace musu kala ba . Sai dai hakan ya tabbatar musu dacewa bai yiwa deeni abinda yakeso ba ,lokuta da dama daga yanayinsa suke gane eh ko a’a dinsa.

Hakan ya kara rikita deeni ,yabishi yana rokinsa.

  Ransa na matukar kaunar deeni ,,komai zai iya masa amma fa banda maganar aure yana dan karaminsa. Bashida wani dalilin da zai sa yaki aurawa deeni farida,sai don kawai ba yanzu bane lokacin da yakamata  deeni yayi aure ba . Don haka ya dauka kai garesu yayi tafiarsa.

       Bangarensa ya nufa batare da damuwa da halin da deeni yake ciki ba,dan yasan yarinta ce ke damunsa,rashin sanin ciwon kansa ne yasa yake cewa zaiyi aure yanzu.

   Deeni yakasancwe cikin halin dimuwa da tashin hankali,lokaci guda yaji duniyar tana juye mishi sama da kasa ,rayuwa ba farida wani abune da bai taba tunani ba ,don haka da sake .

Ganinsa cikin tashin hankali yasa mama itama hamkalinta ya matukar tashi,ta hau lallashi da bashi baki cewa zata cigaba da lallaba mahaifinsa har ya amince. Da kyar tasamu ya saurareta ,sabida idonsa ya rufe ,bai san ma me yake fadi ba .

Yace ,, ba wanda ya isa ya hanani auren farida ,ko mahaifinsa bai yadda ba shi zai aureta a haka”. 

A wannan dare deeni yayi kwanan tashin hankali da bakin ciki tare da tsoron rasa farida a rayuwar sa,a duk lokacin da yatuna zai iya rasa farida idan har nahaifinsa bai amince masa ba sai yaji ya tsinci kansa cikin gigita da dimauta. Haka ya kwana abin a ransa,ya kuma tashi dashi ,yayin da hajia ta kwana magana daya da mahaifinsa tana nuna masa  tsakanin deeni da farida in an raba su ba karamin illata rayuwar su za’ayi ba.amma fir Alhaji ya kafe ba wanda ya isa ya canja mishi ra’ayi.

 Washe gari a haka suka tashi gidan cikin rashin kwanciyar hankali ……

About AIS

Check Also

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  iya ganin damuwarta ko …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *