MISBAH CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

MISBAH CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kamar yadda kace baka da damuwa da MISBAH sai brains dinsa ,to nima bani da damuwa dashi,damuiwata shine deeni,in kuwa labaransa na dauke hankalin deeni a kai na ,to inada matsala da hakan ,don haka inada matsala da brain dinsa,da intellegent dinsa,i have a problem wit his stories”

     Ya dan fadada murmushinsa tare da fadin “” anyi an gama ,daga yau bani ba karanta littafin MISBAH ;nayi alkawari””

   Tayi daria har da tsallen farin ciki ta ce ” shiyasa nake son deeni na ,he care for me yana jin maganata ya damu da farin ciki na ,,my deeni is d best””” 

 Dariya yake mata shima yace my farida is d best”ki tsaya a gabana in ta kallonki ina jin dadi . Haka kawai kin hanani jin dadi da sukuni ,kwana uku ban ganki ba ,meyasa kika ki zuwa ki ganni ? Kinsan baba kulle yakemun inmun fara jarrabawa ya hadani da wannan manya manyan takardun ina karantawa, bana ganewa,daga na bude littafin sai inga furkar farida tanamun murmushi,bana iya komai sai kallon fuskarki a littafin “tayi murmushi tace meyasa baka dirko ta window ba ? Www.bankinhausanovels.com.ng 

 Yace ” so kike in karye a ce mijinki gurgu?

Tayi daria tace “to ina ruwansu ,inma gurgun ne ba mijina bane ? Deeni na ne ni daya ” 

    Yace haka farida na ni daya “”

  Farida ta dubeshi tace deeni yaushe zamuyi aure ? Ya kalleta ya ce ko yau Abbanki ya shirya aura minke zan aure ki ” Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ta masa hararar wasa ta ce ina zaka ajiyeni baka da gida baka da aiki ? Ya ce,shine damuwarki ? Kalli girman dakin nan bazai ishemu ba ? Ya jawota ,”zo kiga yawan abincin da mama take samun kullum so uku so hudu a rana ,ko ke rumbu ce zaki koshi. Awani lokaci mama nasamun abinci fiye da kala hudu a rana ,wani lokaci ma bana ci ake fita dashi .

 Bari in fada miki ni mrs deeni NURADDEN dan gatan mama da baba ne auren gata zatamun dakina ya ishemu,abincina ya ishe mu ,balle ma inkin zo mama zata kara kara. Kayan sawa zan sai miki ko wanne ,inada kudi enough a account dina ,kullum baba samun yake bana kashesu . Zan iya kula da lafiyarki ,babban shine zan kula da farin cikin ki,kullum zan dunga saki daria ,har funny faces zan dunga miki in kina so .

   Zan so ki sosai my farida ,ki rayu a dakina ,gado na,wardrop dina,toilet dina ,komai na baki . Ni zan rayu a jikin ki” yana magana yana lumshe ido.

Murmushi tayi ,kunya tasa ta sunkuyar da kai. 

Ya kira sunanta yana mata murmushi,wannan tunanin da halayyar tasa yake kara haukata zuciyarta cikin soyayyarsa, itama murmshin take masa,ganin yana matsowa gareta yasa ta fara ja da baya ,tayi hanyar fita tana kallonsa,bataki tai ta kallon sa a haka ba. Sai dai ya zama dole tayi gidan dan an fara kiran sallar magriba,za’a nemeta a gida in anji shuru bata dawo ba . Haka tana tsoro kar mama ta leko su .     Bata ankara ba kuwa taji tayi karo da abu,da sauri ta juyo tare da daga kai. Yaya SHAMSU ne yayan deeni ,ya kalleta .   Haba farida yi a hankali maba,bakya gani ne?” 

 “Yi hakuri yaya ai duk laifin deeni ne ” ya zaro ido ,sharri zaki mun ? Yaya laifinta ne” girgiza kai ya yi tare da murmushi ,ya ce “Deeni da Farida sai Allah ,ba’a gane muku kuma ba’a shiga tsakaninku . Ni kan nayi masallaci ,maza kaima kayi harama ,kema ki shige ciki ayi sallah,in yaso kuyi soyayyar daga baya “

 Kunya tasa ta rufe fuska ,ta fita da gudu ko sallama da mama batayi ba, deeni yabita da kallo yana murmushi ,sonta na bin jikinsa . Ya Shamsu ya kalleshi yace wai wani irin so kake wa farida ne ?

“Yaya nima ban sani ba ,ni kaina na rasa wane irin so nake mata da yawansa “

 Girgiza kai shamsu ya yi ya wuce ya barshi a wurin … Www.bankinhausanovels.com.ng 

Nuradden da farida sun kasance makwabtan juna,gidajen su na kallan na juna ,haka nan akwai mutunci da zumunci me karfi a tsakanin gidajen,akwai abota a tsakanin iyayen deeni da na farida,,haka iyayensu mata wanda zaman unguwa daya ne kawai ya hada su,duk da yanayin rayuwarsu da dukiyarsu ya ban bamta,,wannan be hanasu abota da zumunci da juna ba.
         
     Mahaifin deeni mutum ne dan kasuwa ,mai dukiya. Rayuwar gidansa kuwa zamu iya cewa rayuwace ta yan bariki tsantsa,dayawa sukan masa lakabi da bakin bature ,saboda yanayin rayuwar sa .
      Matar sa daya hajia A’i da yaransu maza uku rak. Shamsudden shine babba, sai Nuruddeni da kaninshi lukmanudden wadan nan sune yaran hajia A’i .su biyar dinnan su ke rayuwa a gidansu,sai ma’aikatansu,sai dai lokaci lokaci yan uwa na kawo musu ziyara..
 Alh Umar mahaifin deeni duk da turancinsa da bokon sa bashi da wani mugun hali, ko wani mugunta . Mutum ne me kirki da alkairi ga mutane,jamaar unguwa sunajin dadin zama dashi da mu’amalar sa da su . Shi dai kawai baya so a shigar masa rayuwa,ko wani shisshigi ta fannin gidansa ko iyalinsa. Haka mutum ne me yanke shawara akan abinda ya ma sa ta harkar gidansa ko iyalinsa,mutum ne me ra’ayi da akidar tsiya.. bai shiga harkar rayuwar wasu haka nan beso a shiga nashi. Mutum ne da in ya yanke abu ba wanda ya isa ya canja mishi ra’ayi..
      Duk wani abun jin dadin rayuwa ya mallakawa iyalinshi,,matarsa da yaransa,,haka sauran dangi da iyayensa ya wadata su da duk wani abu da zasu bukata. Sai dai fa yaransa da matarsa shi ne me yanke musu hukunci,duk wani abu dazasuyi kamar ta fannin karatunsu,me zasu karanta ,a ina zasuyi karatun ,da sauran su…
   Shamsu babban danshi yasa shi ya karanta fannin kasuwanci domin taimaka masa wurin business dinsa,yana da shekara ashirin da bakwai a duniya ya kammala masters dinsa,yana aiki tare da mahaifinsa a kamfaninsu.
    Suna zaune cikin garin kaduna ,sai dai mutanen gombe ne ,,gaba dayan zuriarsu suna can gombe.
  Shamsu yayi karatunsa a waje ,sai nurudden da mahaifinsa ya ce medicine zaiyi duk da kuwa baya so,sai dai bai masa musu ba saboda sanin hali irin na mahaifinsa.
   Tun suna yan yara shine me yanke hukunci ,ko da abincin da zasuci ne ,hatta suturar da zasu sa shike yanke musu hukunci . Sai dai wannan shekararsa ta biyu ,amma abin ya gagara ,duk nacin sa ya kasa,har yanzu yana aji daya ,duk yan ajin su da suka tare sun wuce sun barshi.
    Mahaifinsa yaso turashi waje kamar yadda yayiwa shamsu ,sai dai ranshi nason deeni da yawa da bazai iya nisa dashi ba. Cikin yan uwansa yafi kaunarsa,ba mahaifinshi kadai ba duk wanda ya zauna dashi sai yaji  ya shiga ransa,yana kaunar sa.haka nan Allah yamasa wannan baiwar. Halayyarsa da dabiunsa abin so ne da shaawa ga kowa,dan haka yasa duk tsananin Alh umar amma yana dagawa deeni kafa.. 
       Wannan karan deeni zai sake jarrabawa ta shiga aji biyu a ABU zaria,yayin da babanshi ya mishi alkawarin yi mishi duk abinda yakeso matukwar yaci jarrabawarsa. Haka nan deeni ya dage domin a zahiri ba abinda deeni yakeso kamar farida,,zai yi dukkan iyawarsa dan mahaifinshi ya bashi farida ,ya aura masa ita . Www.bankinhausanovels.com.ng 
 Soyayyar farida da deeni da shakuwarsu ya samo asali,tun suna yara ,tare suka tashi suna girma,saboda zumuncin da iyayensu mata sukeyi…. Deeni ya girmewa farida da shekara hudu ,tun suna wasan yara har takai ga suka fara girma da abota,har ta juye soyayya da shakuwa me tsanani,,wanda mutum bazai gane wayafi son wani ba a cikinsu. Iyaye da yan uwansu duka ba wanda baisan maganar soyayyarsu ba . Mahaifiyar deeni na matukar son farida sabida kaunar  da sukewa juna,da kuma irin tarbiyyarya da nutsuwarta . Ta fita daban da yan uwanta.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

About AIS

Check Also

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  iya ganin damuwarta ko …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *