MISBAH CHAPTER 10 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH CHAPTER 10 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Shuru yayi na tsawon lokaci,yana kallon sa ,sannan ya ce.

     ” Baba ban fahimta ba “”

 Ya yi murmushi ya ce ,” zan fahimtar da kai ,ba dai farida kakeso ba ?? 

Ya girgiza masa kai da ,Ehh ” 

“” kanason farida ,inaso kayi karatu,tunda kuwa na sama maka farida kai kuma zaka cika min burina na ganka a cikakken likita ko ? Ya girgiza masa kai alamar eh . Yace ” to nayi magana da mahaifin farida ya amince zai bar farida ta jiraka,kaje kayi karatunka ka dawo tunda har nasa baki yasan da gaske nake. Sai dai duk da haka zabi biyu na bashi ; ko ya amince sai ka dawo ,ko kuma a daura auren karshen wata baka nan sai kadawo ta tare,da kanshi ya yanke shawarar se ka dawo din,saboda ba yadda za’ayi ka tafi da ita wata kasa kana karatau ita kuma tana zaune haka a kasar da bata san kowa ba ,haka karatunka nason nutsuwa da mai da hankali,ba gadda za’ayi ka raba hankalinka ya zama baka bata lokaci ba,haka baka bawa karatun ka lokaci ba,kaga za’ayi biyu babu.Don haka ya amince mana na tsawon shekara biyar din nan ,dan mutunci na da kuma zumuncin da ke tsakaninmu da kuma soyayyar da ke tsakaninka da faridan. Amma yace idan ya wuce shekara biyar din nan bazai kara maka ko kwana daya akai ba ,don haka ya rage naka kayi kokari kagama karayunka na likita a cikin wadannan shekarun ka dawo ka aureta ,ko ka tsaya wasa kayi ta komawa baya wannan damar ta kubuce maka..” Www.bankinhausanovels.com.ng 

     Ya kalli mahaifin nasa ya ce ,,”Abba na.maka alkawarin zan yi dukkan iya kokarina da iyawata ,ba zan yi wasa ba ,zan dage inyi karatuna in gama a cikin shekarun nan insha Allah . Ina fatan in cin ma manufata; in cika burinka da nawa ,ba zanyi wasa da damar da Abban farida da kai ku ka bani ba ,fatan zaku taya ni da addu’a kusa min albarka ,Allah ya taimake ni “””Zamuyi maka Deeni insha Allah ,Allah ya saka maka da mafificin alkhairi ,Allah ya baka abinda ya fi maka alkairi albarkacin wannan biyayya da kai min “” 

    “”Ameen baba “”

     Ya amsa yana godiya ,sannan ya kalli mahaifiyarsa yace ,,,

“Mama ina bukatar addu’arki,ya shamsu kaima kasani a addua. Sannan mama na baku amanar farida ,da kula da ita kafin in dawo””

     Tayi murmushi,” zan maka addua deeni,,sannan farida “yata ce,zamu kula da ita insha Allah “”

     Nagode mama

  Ya fada yana murmushi,ya fita jikinsa a mace sabida tafiyar ya bar farida ba abu ne me sauki ba ,sai dai zai dage ya yi abinda zai sa ya samu farida ,ya mallaketa na har abada.

       Wata guda da maganar Alh umar ya yi ta shige da fitar samawa deeni addmission gurbin karatun likita a America,ya taki sa’a suna daukan sabbin dalibai,dan haka ya shiga ya fita sai da yaga ya samawa deeni gurbin karatu a florida medical collage .

   A wannan lokacin kafin tafiar deeni kullum suna tare da farida,,baiyi wasa da wadannan kwanakin ba gurin kasancewa da farida,ko a gidansu ko a gidansu faridan,don kuwa haka suke shiga gidajen juna kai tsaya kamar nasu,haka irin so da kauna da tarairaya da mahaifiyar Deeni ke nunawa farida ko mahaifiyarta sai haka,son da mahaifiyar deeni kee masa ya shafi farida,haka mahaifan farida keji da Deeni sosai.

  Ranar da deeni zai tafi tun sassafe farida taje gidansu ta tayashi shirya kayan sa,duk inda deeni yayi idanun farida na kansa,ya lura da hakan amma sai yai kokarin kau da kai saboda kar tayi kuka ,,amma daga karshe sai tayi abinda bai so din,ya matso gabanya yana mirmushi tare da ciro wayar sa ya ce ,, Www.bankinhausanovels.com.ng 

      “” saki fuska ki daina daure shi in dauke ki hoto in dinga kallonki ina tuna ranar da na tafi na bar farida “” 

       Kara kumburo kumatu tayi saura dis tasa kuka,haka ya dunga daukarta hoto , ya ce .

   “” To na kumburarrun fuska da kumatun sun ishe ni haka,ayi min murmushi kuma in gani. Ki tuna duk randa kika sake ganin deeni to ranar zai zama angonki ,me gidanki,,wannann kadai be isheki murmushi ba ;;? 

    Nan da nan tasaki murmushi ,bai bata lokacin daukar ta hoto ba . Ya yi saurin matsowa kusa da ita ya dauke su tare suna yiwa juna murmushi,wanda daga karshe mirmushin ya koma kuka.

        Farida tasa kuka da karfinta,,”” yanzu deeni bazan sake ganinka ba se bayan shekara biyar? Ya zan rayu na tsawan wannan lokacin ? Deeni bazan iya jure rashinka na tsawon wannan lokacin ba ,,ni dai karka tafi ka barni,ka tsaya a daura mana aure ka tafi dani,”

     Kuka take sosai wanda kukanta da yanayinta ya mugun karyawa Deeni zuciya,yaji kamar ya zubar mata da hawaye,tausayinta da tsananin soyayyarta ya dinga ratsa shi . Ranar ta farko kenan dayaji yason ya rumgumeta a jikinsa domin ya lallasheta. 

     Son ta mai karfi da wani irin shaukinta yaji yana fisgarsa,ya yi nufin rungumar ta din ,amma sai ya dinga jin zuciyar sa na bugawa da karfi,ta hana shi ,tsananin tsoron yin hakan ya shige shi,tsoron Allah ya shige shi. Shin in ya taba ta suka kai ga aikata abinda bai kamata ba fa ?

    “A’uzubillahi minasshaidanirrajim ” 

  Abinda ya dunga maimaitawa kenan.

Gaba daya ya rude ,ya rasa abin yi ,ga sonta ,da tausayinta,ga tunanin tafia ya barta. Dabara ce ta fado masa,ya jawo hijabinta da take sake dashi,ya fisgeta har dakin mama,ya kaita gaban mama ya ce . To mama kinganta zata hana danki tafia ko ? Ta sani a gaba tanamun kuka ,fada mata manyan ‘yan mata da suka isa aure ba sa kuka kamar na ‘yan yara”….

Ai kuwa kamar ya ce ta kara kukan ta kara fashewa da kuka.

     Ta ce ” To wata baturiya ma zan samo can in aura”

    Nan ta dalla masa harara hawaye na zuba ta ce ,,

   Mama kin ganshi ko ? Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mama ta jayota jikinta,”Rabu da shi kinji,duk baturiyar da zai je ya samo bazata kai rabin farida ba ,zai yi ya gama ne ya dawo ya nemeki,duk randa ya dawo ki masa yanga son ranki,ki kyale shi ki sami wani mijin .

   Duk da wasa mama take amma sai da yanayinsa ya canja,ya canja fuska duk da yana kokarin murmushi,juyawa yayi ya nufi ciki.

   Farida tasan halin kayanta,don haka ta bi bayansa ta ce .

  ‘” Ai duk duniya ba wanda ya kai deeni na a wurina,indai ba deeni ba sai dai in hakura da aure”

  Jin hakan yasa ya tsaya tare da juyowa ya kalleta tare da sakar mata murmushi,yace.

   ” shi yasa nake sonki farida na,kin san yadda zaki kawo murmushi fuskata,kin san yadda zaki kula dani. Ina da yakinin in na aureki zan kasance ciikin farin ciki tare da ke. Farida inasonki,ina kaunarki ke daya,ki saka wannan a ranki daga ke ba wata.”

      Tayi masa murmushi itama,ta ce,” Deeni na ka rike wannan a ranka ,daga kai bawani a zuciyar farida ,na ma alkawarin kaina da ajiyar kaina da zuciyata,zan tsare maka amanar kaina.”

Nan suka zubawa juna ido suna yiwa juna murmushi na tsawon lokaci,sannan deeeni ya yi ciki,ita kuma ta wuce gida da niyyar sai yazo tafia tazo su kaishi airport.

    Sai dai deeni bai bari hakan ya faru ba,wannan sallamar da sukayi shine ban kwanan da yayi mata,saboda yasan inta rakashi airport bazasu iya jure rabuwa da juna ba .

        Jirgin deeni karfe biyu ne,amma sai yace mata karfe shida ne ,saboda baiso ta rakashi.

     Lokacin tafiyar su ,har gidan su ya shiga ya yiwa iyayen farida sallama,sai dai basu san lokacin zai tafi ba . Nan suka masa addu’a tare da fatan alkhairi da kuma Allah ya kiyaye masa hanya. Lokacin nan farida na ciki tana ta kokarin faman neman kayan da zata sa ta yiwa deeni gayu ya yanga lokacin da zata rakashi,a wannan lokacin ma har deeni sun kama hanyar airport har da mahaifin faridan.

   Tunda suka dau hanya yake basu amanar farida,tare da kara jaddada musu irin son da yake mata,da kuma irin dagewar da zaiyi ya yi karatu. Nan mahaifinsa ya kara masa tuni da ko hutu bazai zo ba ,shi da nigeria sai ya gama karatu.

       Ya kalli mahaifin nasa yace,” nasani baba,ba zan dawo ba sai na cimma manufata da burinka da yardar Allah.,” 

       Mama da shamsudden tare da kaninsa. Lukman da mahaifin farida suka masa rakiya wanda mahaifin sa kuma tare zasu tafi sai ya kaishi sannan ya dawo .

    Bayan sun isa zasu shiga jirgi kafin ya kalli mama yace,

” in farida taji na tafi zatayi kuka,ki lallasheta sosai kinji mama ?

  ” To deeni ,zan lallasheta,sai dai kai kuma wa zai lallashe ka?

    Idanunsa suka kada sukayi ja ,ya yi saurin kai da kai ya ce,ba komai zan lallashi kaina” Www.bankinhausanovels.com.ng 

     Shamsuddeen yayi saurin rungumarsa yana lallashi har da lukman a masu bashi hakuri,dakyar ya iya danne zuciyarsa ya juya ya tafi. Har ya bar ganinsu yana kara maimaita musu ,mama,shamsu,lukman ku kula min da farida ,na baku amanar farida.Mama tayi karfin hali kamar zatayi kuka tace .

   Mun rike amana deeni,Allah ya kai ka lafia,ya kare ka”

     Ameen” ya amsa,sannan ya shige suka tafi. 

     Su mama basu bar filin jirgin ba har sai da suka ga tashin jirginsu sannan suka kama hanyar gida,dukkan su jikinsu a mace,zuciyar su cike da kewar deeni.

    Suna isowa kofar gida kuwa sukaci karo da farida ta hada kai da gwiwa tana ta zabga kuka,,tun daga wannan lokacin mama tasoma aikinta na lallashi. Ta ja hannunta suka shiga ciki,ta dinga lallashinta tare da kalamai masu dadi da kwantar da rai,ta nuna mata deeni ya yi haka ne saboda kada ya ganta ya karaya ya kasa tafiya. Www.bankinhausanovels.com.ng 

 “”  farida kiyi masa addua tare da kara masa karfin gwiwa har ya samu nasarar yin abinda ya kai shi ya dawo lafiya kuyi aurenku kinji ko ?

   Ta girgiza mata kai ,. Naji mama ,na gode,zan jure in Allah ya yarda.

Yawwa farida ,shiyasa nake sonki,akwai biyayya da jin maganar na gaba da ke. Allah ga miki albarka.

    Ameen mama” . Ta fada murya a sanyaye. Ta mike tayiwa mama sallama ta nufi gida zuciyarta cike da tsananin son deeni,da kuma kewar sa. Ita dai bataki ta dawo gidan da zama ba tayi ta zama a dakin deeni tana kallon inda yake rayuwar sa tana jin dadi ,sai dai ba halin yin hakan sai dai ta dinga zuwa,ya zama dole tayi hakuri da rashin Deeni……

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

About AIS

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *