MALIKA MALIK CHAPTER 2 BY JANAFTY

MALIKA MALIK CHAPTER 2 BY JANAFTY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

KANO*

_MALLAM AMINU INTERNATIONAL AIRPORT KANO_

“””Jirgin karfe 12:00pm shine ya sauke mutanen daya dauko daga birin London

Acikin jerin mutane na 8 masu Fitowa *MALIKA* tana daya daga ciki bayanta kuma Amintattun Excorts dinta ne joy and peter,sanye cikin bakaken court kowanne ya toshe bakar Fuskarsa da wani makeken bakin gilas,Joy shike rike da Brief case dinta,wanda manyan bayanai game da document na kamfafonin mahaifinta ke ciki,ma”ana kowani Kundin bayanai,Shiko peter dama kullum dan Rike jaka ne da wayoyi dama aikinsa kenan.

Yau din ma tana sanye ne cikin shigarta,buh na yau Suit tasaka na mata riga da sikat,Ash and white,wanda sikat din,da kadan ya wucemata gwiwa,Fararen kafafunta kal,duk suna waje bayan ta kawata kafarta da wani Ash din cover,wanda yake da dan Dudu,Yau anci sa”a bayan ta dane gashinta atsakiyar kanta ta Makaleshi da band,tasaki jelan ta baya,sai ta dora wani ash din vail,ta yaneshi daga tsakiyar kan,Fuskarta sanye da wani glass,mai duhu wanda ko kwayan idonta baka iya hangowa.

Farace Tar sosai,irin Farin ne bamai launin jaja ba,Doguwa ce ammh ba sosai ba,Allah yabata wani Abu waishi tsarin hip,ga kuma madaran shanu suma babu laifi,daga tsayenta tana da Shape din,cocacola ne,Hancinta ba dogo bane sosai,ammh yadace da Doguwar Fuskarta,mai dauke da karamin bakinta,wanda yake Fari tas,shima Gashin idonta zarazara ne kamar yadda idanuwan nata keda girma,Gashin giranta ko baki silif,yana ta Sheke,.

kallo daya zakamata Kazata wannan bata hada komai da Hausa Fulani ba,kai infact ma, zaka zata irin bakin nan,ne dake Shigowa Nageria harkan kasuwanci ,daga yanayin dresssing dinta da yanayin yadda take mgana zaka  Shaida tabbas wannan ko Aturawan takai makura.

*MALIKA MALIK..”* Kenan Y’a kwaya daya Tak,ga *ALHAJI ABDULMALIK DAN KASUWA* Wanda saboda kudinsa da tarin kaddarorinsa da kamfafononi,tundaga gida Nageria har zuwa kashashen ketare,yasa ya zamanto cikin jerin masu kudi na hudu A kasarmu ta Nageria.

Tana Saukowa daga kan Step din jirgin Tuni dama motocinta tare da Sauran Excort dinta sun zo daukanta,Duka motocin wannan karan 4matic ne,kuma 12 ne,kowane akwai tambarin *MALIKA MALIK*1 har zuwa 12 akallah excorts dinta masu tsaronta zasu kai su ashirin,kuma babu dan musulmi ko daya kuma babu jinsi mace,duka mazane kuma wasu gardawa konace samudawa,Tunkafin ta kariso suka bude mata Daya daga cikin motocin,ta Fada cikin isa da takama,nan da nan kowa yakoma motarsa suka bata Wuta sukabar Aiport din aguje,babu wanda ya damu domin indai malika malik ne kaf Nageria,yaro da babba babu wanda baisanta a Talabejin ba,in ma Mutum baita ganinta ba,to babu Shakka yasan lbrin sangarta tare da lalacewa ta malik malik,da sunan wayewa ko kuma nace GATA.

*******************

_KATSINA_

*GRA*..

Cikin Gra ne Tamkamemen gidan mahaifinta yake,mai kama da yanki Guda saboda girmansa da kuma Fadinsa,inda za”ayi Estete,tsab za”a iya yin guda 40 kuma kowanne da girmansa,Hon suka zuba masu gadin dake sanye da Uniform sukazo suka budemata don sunsan hali,minti daya suka kara korace Awajenta.

lokacin da motocin suka Fara sulalawa parking space,kowani Excort ya fito daga motarshi yana bin motarta da gudu bata tsaya ba,sai A babbar kofar da zata sadata da cikin babban Falonsu,Budemata sukayi jikinsu na Rawa masu,gadin kuwa fadi suke”Wlcm back madam…”cikin isa ta zuro kafarta waje kafin ta bayyana waje Fuskarta babu Fara”a  ko kadan bata kallesu ba,kawai tafara Tafiya joy da peter suka take mata baya,ajiyar zuciya sauran suka saukesu,suna Fatan yasa anrabu lafiya kenan.

Tana Shiga Falon wanda ya kawatu dawasu royal chairs hadaddu masu kyau da tsari sai wani tamkamemen plasma,daya kusa cinye rabin bangon dakin,ko sallama batayi kamar ba,don ba dabi”arta bace, *HAJIYA BINTA* ,Dake zaune tana kallon Atashar Arewa24 ta dago tana kallon Malika wacce ko kallonta batayi ba,saima zuwa datayi ta gabanta zata Wuce,tasa Tudun takalminta ta murje mata kafa,Azaban da Hajiya binta taji ne yasa ta saka ihu,wanda ya Fito da Alhaji maleek da hanzari wanda ke kayatattacen Falonsa na sama yana hutawa,Dattijone don zai iya kai shekara 67 aduniya Abun mamaki baki ne silif,ammh kuma yana da kyau  da hanci,Fuskarsa tacika da Farin gemu ammh kana kallonsa zaka Fahimci Farin gemun na halitta ne ba wai na Tsufa bane,domin duk inda jin dadi da Hutu yake toh Alhaji Malek na tare dashi,don Shida iyalansa basayin wata Daya A nageria sai Sun Fita waje sun Huta.

Ihun Hajiyane yafito dashi yaga ko lafiya,ammh sai ya ci karo da Malika tana kokarin karisowa gareshi da hanzari ya tafi gareta yana Fadin”Wlcm back my Sweetbbby….”Yake Fada yana Rumgumeta matseshi tayi tana Fadin”Dddylove i really miss u…”Kiss yayimata agoshi yana Fadin”Miss u more Sweetbby,yanzu mrs Suzan takirani tace komai yayi daidai..”

Wani mirmishi tayimai Tana Fadin”U know me Daddy,bazan taba baka kunya.”Wata Dariya yasa yana Fadin”Hhhh..Datz my Sweetbby,maza ki wuce daki kiyi wanka ki Shirya ki sauko muyi lunch..”Tabe baki tayi kafin ta cire glass din idonta tana Fadin”No not now, Daddy naci abinci a cikin jirgi,but now zan Shiga in huta sai na Fito we tok later..”Shafa kanta yayi yana Fadin”ok maza my Sweetbby ahuta lafiya karki sake kitashi sai around 6 haka kinji..?”Kai tadagamai tana bashi kiss a kumatu tace”Daz why i love u,my Daddylove much wlh..”dariya yayi kafin Shima ya maidamata da kiss din,da hanzari Ta nufi wani Daki dake kusa da Inda Abbanta ya Fito tana Shiga dakin su peter suka rufamata baya.

 Alhaji Malik ya kalli Hajiya binta yana Fadin”Lafiyanki kuwa naji ihunki daga sama…? dagowa tayi daga murza kafarta, datakeyi Yar matashiyar matace wacce ashekaru bazata gaza 36 aduniya ba,farace tas,ammh tana dan jiki,idonta cike da kwallah tace.

  “Haba Alhaji,malika ce fa tashigo babu ko sallama kamar ba yar musulma ba,kuma don rashin kunya tabiyo tagabana zata wuce hakan bai isheta ba,sai da ta takani da Katon takalminta mai Tsini..”Tafada cikin takaichi.

 Tsaki Yaja yana Fadin”Gaskiya Binta fitinarki da tseguminki yafara isata fa,Haba kin sakama yarinyarnan ido,ita da gidan Ubanta in bataji dadi anan ba,waje kikeso taje taji dadi ehe..”?Yafada yana tsareta da ido.

 Kallonsa tayi baki bude tana Fadin”Ammh tsakani ga Allah Alhaji Abunda Malika tayi yanzu ya kyautu..?”Hannu ya dagamata yana Fadin”Kinga Binta kifita daga idona indai akan Malika ne,banda Abunki nawa malika take,haryanzu fa yarinyace wani Abun sai ana nusar da ita,kuma kibar wannan mganar kada ki kuskura ki tankamata,yanzu nan sai takama Fushi,kuma kinfi kowa sanin yadda Fushin malika yake awajena Atoh.”Yafada irin Abun ya isheshi haka,ya sa kai yakoma cikin kayatattacen Falonsa bayan ya saki Siririn tsaki.

 Hajiya Binta ta bishi da kallo tana kada kai,idonta ya ciko da hawayen takaichi da kuma haushin iyayenta da suka biyema Rudin Duniya da kuma tarin Dukiya suka kawota inda ba”a san mutumcinta ba,daga Uban har yar duk basu da mutumci babu wanda ke ragamata.

Dauke hawayenta tayi tana mirmishin karfin hali,Tuna duk mutuwa ce taja mata wannan Tonon Sililin,da”ace Abban *JODA* na raye ta tabbata da bata auri Alhaji Malik ba,balle har tazama Abun wulakantawa awajensu.

  Mikewa tayi rike da wayarta tashige wani korido tana kwalama Atika mai aikinsu kira,domin ta umarceta ta shirya lunch bisa Dinning area.

Katon Falo ne,wanda yaji kayan alfarma,Tunda tashiga tafara yadda kayanta,Tacire vail ta Wurga ta cire band din kanta,ta warware gashin kanta bayan ta Fara cire botir din Rigarta gabadaya halittun kirjinta dake jikin beriziya suka bayyana,Peter ko da joy suna tsaye kyam,don madam bata basu daman Tafiya ba,Indai Tsiraicin Madam ne,Su Tuni sun dade da haddace kamminshi don bata da kunyan idon maza,Hatta Swining pool in zata wanka tare dasu take zuwa tayi Tsirara daga ita sai pant agabansu ko gefen gyalenta.

Murya ta saka tana Fadin”Merry…Dose…”Take Fada cike da Fushi sai gasu sun Bude wata kofa sun Fito da gudu agabanta suka zube suna Fadin”Srry madam…SrrrY…”Wani Wulakantattacen kallo take binsu dashi kafin ta sanya kafa ta shuri merry sai da ta kifa,lokaci daya ta gaurama Dose mari tana Fadin”U too u are Animal,..”Take Fada tana huci Baya sukayi suna kuka suna bata hakuri da hannu ta dakatar dasu kafin tace”,last chance…”Bata gama Rufe baki suka mike daya tafara kokarin ciremata takalmi daya kuma tafara kokarin karisa balle mata botir din Rigarta bayan ta ciremata Coat da hannu tayi musu peter alamu, sai kawai naga sun nufi wani kofar glass,wanda sai  da ta dauki hoton Fuskokinsu ashe Na”urace awajen kafin ta bude musu su Shiga,sun Shiga ba dadewa sai gasu,sun Fito wanda kafin Su Fito sai da Na”uran tagama cajesu tsab ta tabbatar da basu tare da komai kana ta barsu suka Fito,suna Fitowa tayi directing dinsu da hannu alamar su Fita,kai tsaye suka bude kofa suka Fita,bayan su merry sungama cire mata duka kayanta,harda bra da pant tsiraranta haihuwar uwarta suka dagata tsab,sai cikin katon bedroom dinta inda katon Tiolet dinta yake,wanda yaji kayan alfarma kyace baza”a mutu ba,cikin jazucci suka sakata bayan suncikashi da wani Ruwan kumfa,Dose ce ta Fice ita kuma merry ta fara Yimata wanka tana kwance ta lumshe ido ko agefen gyalenta..

Niko nace *KUTUMAR UBAN CHAN*?

Dose na Fitowa takoma kayattacen Falon ta kwashe duka kayanta,kafin takoma Toilet din ta watsasu cikin wani dogon kwando na tara kayan wanki,Fitowa tayi kafin ta isa wani makeken Abu wanda ke dauke da glass,ashe Na”urace Sai da Ta tantance Fuskar Dose kafin wata yar kofa ta bude,Kayane jere cikin tsari iya kallonka mallam,dogayen Riguna,riga da wando ne,suit ne mini sikat da mini wando,Duk sagale cikin hanger,kai kace ka shiga bouitque ne,Wata yaloliyar Doguwar Riga ta daukomata wacce marabanta da Tsirara kadan ne,saboda tasan yanzu barci zatayi kuma iyakarta gwiwa,ta Fito mata dashi kafin kuma wajen ya Rufe kansa,Sun dauki tsawon minti talatin atiolet din kafin Dose ta kuma suka daukota wacce suka nannade da wani katon Towel,suka zo suka ijyeta kan wani dogon Stool,ban gama mamaki ba,sai da naga tana ta Shafemata da mayuka masu tsada itako tana zaune idonta na lumshe,har tagama ta fesheta da body sray,Dose ta matso kusa tana gyaramata zaman gashinta wanda yadan jike kadan da Ruwa,tana kokarin kunna Hand drayer,ta dakatar da ita,da hanzari ta dauko yar Rigar data dauko ta ziramata wacce ta Fito mata asalin tsarin kirjinta,tunda babu bra babu pant,Dose ita kadai ta dagata bata sauketa ako”ina ba sai akan wani gado,mai kama da alkaki saboda yadda yake amulmule,wani karamin Filo fari dake gefe ta Rumgume tana lumshe ido,Katon blanket ta dauka ta Rufamata shi har zuwa Kanta

Gefe suka koma ko motsi basuyi suma dana kallesu suna sanye da Riga fara,sai bakar biri da wando,sai Hula akansu kace wasu ma”aikatan hotel,sai da tasha iska kafin tadaga  musu hannu,da hanzari suka kada kai suka Fice suka jawomata kofar,nan kowaccensu ta maida hannuwanta abaya,domin akidar madam in tana barci babu mai tashinta sai ta tashi da kanta,kuma zata iya bukatan wani Abu,kuma in tamaka kira daya baka zo ba,korace sudinma tana daga musu kafa ne don tana jin dadin zama dasu.

   _________________

*ABUJA*

“”Duka iyalan gidan sun hallara bisa babban Dinning area,mai kama da Fili guda,ajiyane da daddare suka kara samun Zuwan wani dan gidan,bayan Saleem,wato Ya marwan wanda yake aiki alagos,Zaune suke dukkansu suna breakfasrt suna dariyan hajiya wacce ta sanya kujeranta kusa data saleem,Ummi na kokarin saving dinta,tayi Saurin Tsoma hannu a filet din gaban Saleem,wanda yake cike da Soyayyan dankali da kwai,bata Fuska yayi kamar yayi kuka,itako hajiya ta cika baki hartana maida Saura a Farantin,Ummi tana Dariya tace”Hajiya ki barmishi kayanshi bari na zuba miki naki..”..

Hajiya ta gyara zama tana Tsungulin Saleem tace”Barni Aisha yau tare da Ja”irin nan zan karya..”Tafada tana kara saka hannu ta cika baki,har miyau dana baki suna biyowa,Kauda Fuska Saleem yayi yana Fadin”Na Shiga uku Ummi,kalli harda miyan bakinta take sakamin..”Dunguremai kai tayi tana Fadin”An saka din,don kaniyarka,Wlh in kaja tsiya zan maka kaki yanzu nan,kuma wlh na matseka saika hadiye,..”Tashi yayi da Sauri yana kakaro amai,tako damke hannunsa gam,taki sakinsa,Ya marwan dashi da Saleema suna ta tsintsiran dariya Abbi na zaune yana kallonsu,don yasan koyayima Hajiya mgana baji zatayi ba,Ummi ko bata saka baki ba,sanin halin hajiya in Tafara Abu bata iya bari,Saleem din ne kadai mganinta.

Gani yayi tasaka karfinta tana Rikeshi tana neman ta maidashi inda yatashi,Ganin haka yasa ya rike mata hannu yana Fadin”Sakarni kiji wata mgana..”Hararansa tayi tana gyara daurin dankwalinta tace”Anki din,ni zakama wayau,ai wlh yau in har ba lbrin kasamu matar aure zakamin ba,ko ubanka kabiru bai isa ya kwaceka ba,sai kasha majina na..”Tafada tana kebe Fuska,Ummi ce ta rike baki tana bin Fuska Saleem da kallo…

Shuru yayi yana bin Hajiya da kallo kafin yace”Really,,? kina son nayi aure kenan hajiyata..,?”Jin haka yasa ta washe baki cike da goro tace”Sosaima Haba Salihu,kunfa girma kungama balagewa asannin haihuwarku a kumo harda masu mata biyu,bama daya ba..”Rausayar dakai yayi yana Fadi cikin Ransa” Dis iz d right Time….”Yafada kafin yakalli hajiya yana Fadin'”,kamar ko kinsani Hajiya mganar auren ce tadawo dani wannan weeked din..”

Kowa dake wajen yadauka yanamata wasa ne don ta sakeshi,shiyasa harda Ummi amasu dariyan,kura masa ido tayi kafin tace”Da gaske kake Salihu..? Gyada mata kai yayi kafin yace”Eh da gaske nake Hajiya ina son kisa baki Abban yaje nema min auren yarinyar danike so..”

Jin yadda yayi mganar babu alamun wasa yasa kowa yadaina dariyan dayakeyi hatta Abbi dake ta cin abinsa sai da yadago yana kallon Saleem,wanda ya kurama waje daya ido,Jansa kan kujeran daya tashi Hajiya tayi bakinta yaki Rufuwa tana Fadin”Alhamdulillah Allah yakarbi Addu”a ta,to maza ga kabirun nan,sanar dashi wata yarinyace,Allah sa dai yar gidan Mutumci ne..?Bai wani Damu ba kai tsaye yace””Ba wata bace illah Diyar shahararran Dan kasuwan nan wato *ALHAJI ABDULMALEEK DANKASUWA*…”

Gabadayansu suka razana da jin zencensa saleema data tura chips abaki sai da ta Furzoshi waje,Shiko Ya marwan,yakafa kai yana kurban coffoe,sai da ya kware yafara Tari sama sama,Ummi dake zaune sai da ta mike hannunta dafe da kirji shiko Abbi kasake yayi yana Bin Saleem da kallo,wanda yayi saurin boye razanar daya ga sunyi Afuskarsa.

Saleema ce cikin Rudani tace”Ya saleem Wai wakake Nufi..? Kai tsaye yace mata..” *MALIKA MALIK..”*…Da ita da Ya marwan sai gasu tsaye suna zaro ido atare suka Furta..”,Bura uban chan…”

Suka Fada suna kallon Saleem kamar wani tababbe,Hajiya datake nazartansu tace”Kai wai miye haka daga Fadar suna,kun shiga Rudi lafiya meyake Faruwa ne..? Ya marwan ne yace”Komai ma yafaru Hajiya bakiji sunan daya Fada bane..?Tabe baki Hajiya tayi tana Fadin”Wannan bai dameni ba,indai yar gidan mutumci ne,Amemasa aurenta Tunda yana Sonta..”

Wani kallo Ya marwan,ya ke Wurgama Saleem,wanda yaki bada damar Ya kalleshi balle ya Fahimci wani Abu,To waima yaushe Saleem yataba haduwa da Malika,yarinya da Da Namiji ma baya gabanta? Bai gama mamaki ba yaji saleem na Fadin”Nidai hajiya gashi na kawo wacce nake so don Allah ki matsawa Abbi yaje gun mahaifinta ya neman min Aurenta,kuma one anoder thing,don Allah Abbi karka sanar dasu Aikina,ka sanar dasu ina aiki da hukumar costome ne,in komai ya daidaita zan sanar da ita dakaina plz Abbi..”Yafada yana hada hannuwansa kafin ya Ture hannu Hajiya dake Rike dashi ya Nufi hanyar dakinsa da sassarfa Saleema da ya marwan suka bishi da kallo baki sake.

Hajiya ce ta kalli Abbi,wanda yacigaba da karya wasan tana Fadin”Kabiru maza ka hanzarta,Tunda daga jima kasan mahaifinta Tunda kaima babba ne agwannatin,Tunda har ya nuna yanaso to gwara agaggauta yimai kaji ni ko bakaji ni ba..?”Batare dawani Tunani ba Abbi yace”Insha Allahu hajiya zan kira mahaifinta awaya mufara mgana dashi abokina ne,tare mukayi Dan Fodiyo dashi ammh bayan mungama Zumunci yayi Rauni..”

washe baki Hajiya tayi tana Fadin”Kajima ko,to maza kabar zencen kira zuwa zakayi don wannan mganar bata waya bace..”Gyada kai yayi yana Fadin”karki damu hajiya komai zai daidaita..”Hajiya na murna tana ta sakama Abbi albarka,Ta mike tana kallon Ya marwan tace”Andai ji kunya babban banza,har kaninka yafika sanin ciwon kansa,kadai je,kayita yawo a iska haka zaka zo ka koma,wlh in ka mutu,ana sadakan uku zan saka asallami kowa,daganan kowa ya manta dakai,Tunda ba wani mgaji gareka ba,balle akalleka Atuna ka”Tafada tana Wucewa rai bace.

Ummi dake zaune takalli Abbi tace”Yallabai kako gane wata yarinya Saleem yake mgana..? Hannu yadagamata yana Fadin”mubar wannan mganar Aisha zamu tattaunata letter..”yafada hankalinsa kwance.

Ajiyar zuciya Ummi ta sauke kafin ta mike tahaye sama ranta bace,Saleema tabi bayanta aranta tana Fadin”Lallema ya saleem,ya daukoma kansa dala ba gammo,inma ta yarda zata aureshi don ita ko Qur”ani aka bata zata dafa ta karyata Cewa Ya saleem da malika malik suna soyayyah macen da bata san Darajan kanta bama balle hartasan da wani..”Saleema tace afili”kilama ta girmeshi wlh, yarinya kamar arniya wacce bataga Ruwan musulunci ba”Tafada tana bin bayan Ummi da Sauri taje tasanar da ita kamar ta wahalar da kanta bazai samu damar Auren wannan yarinyar ba,.

Shiko ya marwan bayan Saleem yabi koda yazo dakinsa sai ya tarar da ya rufe da key,jinjina kai yayi yana fadi Cikin Ransa”Ka Rufe kan ka mana,Tunda karasa wacce zaka Furta zaka aura ko wasa ne,sai wannan watsatsiyar yarinyar..”Yafada yanajan tsaki ya wuce dakinsa,yana ayyana tabbas akwai yarinya haryanzu Atare da saleem….

FLASH BACK*

   

  “”*IGP KABIR KUMO* Shine asalin sunan mahaifin Saleem,wanda ya kasance haifaffan garin gombe ne, a KUMO babbar hukumar *AKKO LOCAL GOVERMENT* Kabir ya fito daga gidan mutumci da tsatso mai kyau da Asali,family dinsu basu dawani yawa sosai,ammh suna da kudi dayake suna da manyan yan boko sosai kama daga Doctoci zuwa sama.

   Sunan mahaifinsa BASHIR,Wanda ya kasance Lacra ne,a babban jami”ar gombe kafin Allah yamai Rasuwa ya rasu yabar matarsa *HAJIYA HAFSAT* da Da’nsa kabir,wanda yake aji uku ababbar jami”ar Usmam DanFodiyo Universtiy Sokoto inda yake karantan Sciology Sanin Hallayyar dan Adam kenan.

Mutuwar mahaifinsa ta girgiza sa ammh haka ya fauwalama Allah komai ya maida hankalinsa akaratunsa,Shigansa jami”ar ne suka hadu da *ABDULMALIK SA”AD wanda shi yake karanta Business Admistration,ammh dayake hostel dinsu daya yasanya sukayi abota sosai Duk da shi Abdulmalik din dan jahar katsina ne akaramar hukumar MALUMFASHI.

  Kammallah karatunsu shiyayi sanadiyar raba zumuncinsu domin Shi kabir daganan Burinsa dama Aduniya ya ganshi yana sanye da kakin YA’N SANDA,nan da nan yasamu nasarar Tafiya *POLICE STAFF COLLAGE JOS PLEATUE* makarantace dake horar da manyan ya”n sanda mussaman wadanda aka dauka daga matakin Degree,shekara daya yayi ya Fito amtsayin *ASP*

  lokacin ne,kuma yayi Aure da yar”uwansa AISHA,Wacce ta kasance diyar wan babanshi ne uwa daya uba daya aka hadasu zumunci lokacin itakuma tayi candy,sai ya taho da ita nan ZARIA inda akayi posting dinshi,har yayimata cuku cuku ya sanyata a ABU Kongo,tana karantar Sharia Low,Shekaranta biyu tagama lokacin kabir yasamu chanji wajen aiki,zuwa kano suka tararra suka koma inda tadora daga Karatunta a low sch kano,Shekararta ta Farko Allah ya azurtata da ciki,inda ta Haifi danta na Fari  Wato *MARWAN* Shekaran Marwan biyar Aduniya ta sake haihuwan Danta na Biyu Wato *SALEEM* Lokacin kuma Kabir yana matsayin *DEPUTY COMMISSIONER OF POLICE* Na jahar katsina.

Sai da Saleem ya shekara Hudu Aduniya kana aka haifi *SALEEMA* wanda daga ita Allah bai kara bata haihuwa ba,kuma bawai don ta tsayar ba,Allah ne ya tsaidamata,Tunda daga ita har kabiru,suna bukatar ya”ya sosai atare dasu lokacin ta kamallah karatunta na low school ta Fito da sakamako mai kyau sai Kabir ya nema mata aiki ababban kotun jaha dake katsina nan da nan tafara aikinta amtsayin Lauyan gwannati.

Tun Marwan na dan karami yake da sha”awan Zama matukin jirgin sama wato pilot,shiyasa yana gama secondry sch dinsa Iyayansa suka Turasa Kasar Russia,domin karantan Abunda yashafi Tukin jirgin sama,wanda zai dauki kimanin shekaru biyar achan,lokacin Saleem da Saleema,duk suna Nagerian Turkish Acadamy Abuja,Saleem na jss2 ne,Saleema na primary 4,ko lokacin tafiya Marwan Hajiya hafsat mahaifiyar Kabir taso ta nuna gaddama ammh iyayan suka lallasheta suka nuna,kamar yadda suka gini da boko to suna Fatan suma iyalansu sun san ilimin Addini hade dana boko,wanda malami na mussaman garesu,mai koyar dasu karatun Addini,Saleem dai ya sauke alqur”ani Tuni,Sauran littafai yake bita yayinda Marwan yasa wasa har kaninshi yazo yawucesa.

Tun bayan haihuwan Saleem da tasowarshi mutum ne mai kulafuncin iyayansa,mussaman ma Abbansa,wanda suke kira Abbi,duk inda zashi yana makale dashi shiyasa dayawan abokan mahaifinsu sunfi sanin Saleem akan Marwan saboda shi nanike yake da mahaifinsa,shiyasa ko affice zashi dashi yake zuwa tun yana karami saleem yake jinjinama masu sanya kaki kowani iri,lura da ganin yadda mahafinsa ke kokari da fadi tashin kare hakkin al”ummah,Tun Abun na bashi sha”awa haryazo yana burgesa,ammh baitaba jin zai iya zama kamar mahaifinsa ba,shi arayinsa yafison zama *ENGINEARING*

Lokacin dayayi Candy lokacin ne mahafinsa yazama Commissioner of police na jahar katsina,shikuma ashekaran ne yasamu addmission a ABU ZARIA inda yake karanta Chemical engenearing,Ammh duk sanda suka samu hutu yana dawowa gida ko kuma ya Wuce kauye kumo wajen Kakarsa wacce suke kira da Hajiya babba,ko yaje da niyyar yin sati,to dakyar zaiyi kwana biyu,ya wuce katsina saboda yadda basa shan inuwa daya da Hajiya babban,saboda sa idonta,shikuma tsokana da neman Fada itakuma ba hakuri sai suyita bugawa har sai ta gaji ta kira mahaifinsa awaya tana kuka tana Fadin ya kira dansa yasanar dashi ya barmata gida ko wlh ta fita ta kira samari majiya karfi awatsamatashi zuwa waje,Cp kabir sai ya hau bata hakuri nan da nan sai yakira saleem ya Rufeshi da fadan Maza yatattara kayansa yakoma mkranta,haka zai tatattara ya wuce katsina in ko taga yadade baizo ba ta dinga mita kenan tana cigiyarsa wai duk yafi iyayansa son zumumci.

In yakoma katsina hutu duk inda mahafinsa zai sanya kafa,shima zai sanya,Hardai Abbansa ya bude baki ya tambayeshi koyana Sha”awar zama kamar shi ne”Girgiza kai yayi kafin yace”Ko daya Abbi,kawai kuna burgeni ne kona ce kuna bani sha”awa bama kuba,duk wasu masu kaki dake kokarin kare hakkin mutane da kuma martaba kasarsu,suna burgeni Abbi..”Tundayaji haka daga bakin dansa ya tabbatar da cewa Allah yabashi da mai hikima da kwazo,kuma yasa aranshi ko bajima ko ba dade,sai Saleem yazo yana sanar dashi ya sanyashi aikin dan sanda,saboda yadda yasan komai na mahaifinsa ya sanya ya saba da yawa daga cikin sargent da Inspectors din,wata rana ma in zasu pertrole yakan bisu,suje tare koda bazai yi  komai ba,ya zauna amota yana charting Ko Vidion call shida ya marwan,wanda yake tsokananshi sa *INSPECTOR*

Yana Final year dinshi Ajami”a Incident dinshi da *MALIKA MALIK..* yafaru,Wanda Ranar ana partrole ne atsakanin Titin shiga katsina zuwa Dutsenma,wanda ake binciken mota zuwa mota saboda masu Fitar da makamai ta bodar katsina,shine fa Saleem ya bisu lokacin yana da Shekara 24 Ne Aduniya,yazama saurayi sosai,duk da kana kallonsa zaka Fahimci alokacin yanada kurciya,Tunda ga lokacin da Abun yafaru Saleem yaji bakincikin da baita shiga ba,ya shigeshi dalilin mganganun Malika,wanda sune suka sauyasa daga yunkurin zama injiniya zuwa yunkurin zama *DA’N SANDA*

Ko barci yake Abun na Fadomai arai,saboda yadda yasanya Abun ranshi,ko abinci kirki bayaci koda yakoma mkranta ga karatu ga Damuwa,duk sai kafin su kare Final exams,dinsu sai yayi rama daya koma gida haka iyayansa suka tasashi da tambayan meke Faruwa dashi ammh yaki sanar dasu komai,Lokacin daya je yasamu Abbi da mganar Shiganshi aikin yan Sanda,yayi Farinciki ya Rumgumesa yana murna da hakan bai tafi Police staff collage ba sai da yadawo service kan lokacin kuma ya sanya wani Dan sanda mai suna inspector sale,wanda yakasance ya yarda dashi sosai shiya sanya amtsayin wanda zai binciko masa lbrin malika malik,Tunda farko har karshe bayan nan,kuma yasakashi amtsayin wanda zai dinga bibiyan duk wani motsinta.

Tafiyarsa police staff collage Jos,cike yake da jarumta da kuma buri,in akace buri toh ana nufin RAMUWA domin yayi alqawari sai yasaka malika kuka da idanuwanta,sai ya azabtar da ita,sai tayi kukan zuciya Fiye da wanda yayi sai ya nunamata cewa ba kudi bane kadai martaba Aduniya ba,Dan adam ma kanshi Abun darajawa ne,Saleem bai da aboki ko Amini,saboda shikanshi bai yarda dakowa bane,Duk duniya bayan iyayansa sai yan”uwansa bai iya zama yayi dariya dakowa ba.

yana da taka tsantsan da Duniya,miskili ne sosai mara mgana da Fara”a,ammh kuma yana da barkwaci in yaso,musasaman shida sakonsa saleema,wanda in yadawo hutu,itama tazo andinga kwamawa kenan,har hutun ya kare kowa yakoma inda ya Fito Ummi kuwa har saita gaji da raba Fada kamar mayaka,ammh bai hana anjuma ka gansu tare,Ya marwan Ya dawo Nagaria,shekara biyu kenan,yana Lagos yana aiki saboda yanayin aikinsu ashekara baifi yazo gida sau uku ba.

Shekara Biyu Saleem yayi yafito amtsayin ASP Lokacin kuma aka zana sunan mahaifinsa amtsayin *ASSISTANT INSPECTOR GENERAL OF POLICE* Shikuma Saleem akayi posting dinshi zuwa kankara dake garin katsina saboda yadda yake da kwazo baima shekara ba yasamu karin girma zuwa *DSP bai Rufe wata Shidda ba yasamu karin girma zuwa *SP* Wanda lokacin ne mahaifinsa shima yasamu karin girma zuwa * DUPUTY INSPECTOR GENERAL OF POLICE*,Suka tattara suka koma Abuja,duka iyalanshi harda Hajiya babba wanda dakyar ta yarda takoma don tace tafi sabawa da kumo.

  Yana da Shekara 28 Aduniya yasamu karin girma zuwa *ACP* akayi posting dinsa zuwa babban headquater yan sanda ta jahar ZAMFARA,wanda ko wata baiyi da samun karin girman ba,Allah yayima IGP rasuwa alokacin, nan da nan aka zama sunan mahaifinsa wato KABIR KUMO amtsayin INSPECTOR GENERAL OF POLICE* na kasa baki daya,inda suka tararra suka koma cikin katon gidansu mai kama da aljannar Duniya dake garki Abuja.

lokacin ne kuma dukkan zati da haiba ta cikakken Namiji ta bayyana ga Saleem,wanda ya girma da buri da kuma Ramuwa ga Malika,shekaru biyar din nan duk yayi su ne cikin Shirye Shiryen Ramuwa ga Malika,kuma daman yanzu Ne lokacin daya dace ya aiwatar da kudirinsa,yasanar da kudirinsa gaban kowa da kowa ne,mussaman Hajiya babba,saboda Abbi yadauki Abun da muhimmanci,duk da shi Abbi yataba sanar dashi mahaifin malika tsohon abokinshi ne,zununci ne yayi Rauni tare kuma haduwa datayi Wuya.

Ayanzu haka Saleema na aji uku a jami”ar Bayero University kano,tana karantar medicine tazama budurwa itama sosai,kuma Tana da Saurayinta *ABUBAKAR SADEEQ*Wanda ake cemai Sadiq dana ne ga wanda suke ya”ya maza da IG Kabir kumo,ammh mahaifinshi yadade da rasuwa kusan ma rikonsa Duk hajiya babba ce tayishi kuma duka wahalan karatunsa Abbi ne yayishi harzuwa yau dayake Matakin Controller,domin ma”aikacin costumer ne,yana Abia yana aiki shima bai cika zuwa gida sosai ba.

Dashi ne kadai nasan Saleem nada kayakyawan alaka,sosai domim ko Hutu yazo daki daya suke kwana,ammh koda wasa Saleem baitaba sanar dashi Abunda ke ransa ba ko damuwarsa,duk sun shaku da juna sosai,sai dama Sadeeq din ya Furta soyayyarsa ga saleema ne ma yasa yadaina shigemai saboda gudun raini,dayake kuma shi Abun shi zuwa ne,Ranar dayake jin barkwamci kaf,gidan nan sai sunji ya gunduresu musssaman ma sufara tsiyarsu Shida hajiya wanda baya mutuwa kamar cin kwan makauniya.

Tuni Sadeeq ya Fahimci Saleem nada damuwa,yayi tambayan Duniyan nan,ammh Saleem yacemai babu komai,domin yayi alqawarin babu wanda zaisan Abunda ke ransa sai ya aiwatar da Abunda ya kudirta Shekara da Shekaru,Saleem yana da zuciya sosai da kuma tsantsane ya tsani mutum wanda baisan darajan manya ba balle kuma wanda baisan darajan mutane ba,Yana da tsanani a kan ra”ayinsa in yakafe kan Abu mawuyaci ne kikaga ya dawo ga Abun nan,Kallon daya zakamai ka Fahimci ko yana cikin kunci ne,saboda baya gayyatoma kanshi Fuskar dariya ko Rahama akallon farko,sai ka zauna dashi ,yana da Kawaici da hakuri,ammh baya kaunar mutum mai cin zarafi mutum dan”uwansa,Lokaci daya Malika tasamu girbin tsana mafi girma aransa,wanda ko barci yake yana mafarkinta sai kaga ya farka yana Fadin *MALIKA MALIK..*Sai na rama..”Sai daga baya sai ya Fahimci tsabar yadda yasa ka Abun ranshi ne,kuma ya fahimci Abun bazai taba gushewa ba,sai ya nunama malika iyakarta,bai gama jin ya tsani rayuwar kudi da wayewa ba,sai da yaji duka Tarihin rayuwar malika yaji yakara tsanarta da kuma kyamatanta,da duk wasu hallayanta,kana yayi tir da Mahaifinta domin bai bi Turba mai kyau b wajen samar da ita kanta Malikn ba,,kwata kwata ba macen aure bane,ba macen mutumci bane,Aranar dayasamu lbrinta yakwana yana Tunanin mafita

Ada yaso ya Ci ubanta batare da alakar aure ta Shiga tsakaninsu ba sai ya duba da ita malika bazata damu ba,domin dama bata daraja kanta ba, balle tadamu don wani ya banzarta da darajanta,babban Abun damuwar mutumcinsa da kuma mutumcin Family dinsa,tare da tarbiyan da Abbi da Ummi suka basa,mezai ce musu in har ya aikata wani barna,wanda bai kamata ba tabbas wajen Ramuwa,shi zai kashe kansa bayan yabarma zuru”rsu abun fada na har abada,shikuma yayi watsi da mutumcinsa,don duk Duniya babu Abunda Saleem yafi darajawa kamar LOKACI DA kataba MUTUMCINSA.

shine dalilin da Yasa yayanke shawarar aurenta duk da shikanshi in ya tuna hakan sai ya tsani kansa,ammh bashi da mafita ne sai ta hanyar aure,yadda zai ci ubanta dakyau bayan ya nunamata cewa duk wanda yataba kakinsa ko yaci zarafin wani ko yataba mutumcinsa wlh tallahi bazai taba kyalesa ba.

Baya da ra”ayi zama agidajen gwannati wanda take ba ma”aikatan ta, gidanshi ya siya wani Dan daidai mai dauke da Flat biyu sai haraban farfajiya wajen adana motoci,nan bayan Headquater su ne,a anguwn Birnin ruwa.

Wannan Shine.

   ________________________

*WACCE MALIKA MALIK..*

  “””*ALHAJI ABDULMALIK DAN KASUWA* Shine asalin sunan mahaifinta wanda ya kasance bakatsine wanda ya Fito daga jahar katsina A karamar hukumar * MALUMFASHI*.

Alhaji Abdulmalik,yataso ahannun kakarsa ne ta bangaren uwa,sakamakon maraya ne,duka iyayansa sun rasu Tun yana karami,ya taso ahannun kakarsa mai suna INNARO,wacce ita silam sangarta da kuma rashin kwaba da Alhaji Abdulmalik yataso dashi tun yana yaro,sakamakon gidansu irin gidan gandun nan,kowa Abunda yaga dama Shiyakeyi,gabadaya gidan yayi suna arashin tarbiya da Sanin mutumcin manya kawunanshi ma haka sukeyi  shiyasa shima yataso awannan Turban,inda Allah ya taimakeshi innaro batayi wasa da karatunsa ba,dayake kafin mutuwar mahaifinsa dan kasuwa ne sosai yana da Abun hannunsa,to tun da aka raba gadonshi innaro take juyamai dayake itama irin yar Duniyan nan ne babu Ruwanta duk wata kasuwa dake ci ranaku duk tasansu,to dashi take mai hidima har ya kammallah sakandiri sch dinshi ya wuce jami”ar Usman DanFodiyo University inda yake karantar Business Admistration,domin tun yana karaminsa yana da burin zama gawurtattacen dan kasuwa,wanda zai tara kamfonino ya dinga harka Da turawa duniya tasanshi.

Zuwanshi mkranat ne,suka hadu da IGP KABIR KUMO,Har sukayi abota na tsawon lokacin da suka dauka suna mkarantar dayake kuma dukkansu kowa kwaro ne adepartment dinshi,shiyasa sukayi zarra,amakarantan kowa yasansu,ko alokacin Kabir yana yawan yimai Fada in yaga sun Fita ammh lokacin sallah yayi kowa yatashi yana barin jikin zuwa masallaci,ammh banda shi,toh ganin kabir nayimai Fada ne yasa yafara kokarin gyarawa ammh na ganin ido ne,indai basa tare,Abdulmalik bai damu da yin sallah akan lokaci ba,wani lokacin sai yazo barci zai hada su duka gabadaya,ga shi bashi da ilimin addini,ko kadan ko sallar ma nashi akwai gyara,shidai kawai Babu Abunda yasani sai yayi karatu yazama yawani mai kudi ,duniya tasanshi yayi gina gida mai kyau da tsari,ya kuma auri mace kyakyawa kullum burin Abdulmalik kenan 

gama karatunsu shi yaraba zumuncin dake tsakaninsu,domin tun suna gabda gamawa Kabir ya lura sam Abdulmalik yarage sakamarmai Fuska kuma yarage shigemai kamar da,saboda yana mai Fada da nasihan yabi Duniya ahankali,shiyasa da suka gama mkranta bayan Kabir yatafi police staff jos sau biyu sukayi waya da Abdulmalik inda yake sanar dashi yasamu schoolarship daga gwannatinsu,zai tafi kasar England achan zai yi master dinshi,fatan alheri Kabir yayimai,toh Tundaga lokaci babu wanda ya sake neman kowa domin Abdulmalik na zuwa kasar England ya chanza layi kuma baida contact din kabir din Shiyasanya basu kara jin juna ba.

Zuwanshi kasar England itace mafarin komai ba,domin Tunda Abdulmalik ya Shiga cikin Turawa shikenan Burinshi yakaru,yayi budewar ido sosai mussaman da mata,sai dai Abu dayane Allah ya tsareshi baya neman mata,sai dai iyakarsa ya tsaya iya Romance da Abun da ba”a rasa ba,ammh bai yarda ya zama mazinaci ba,yayi kokarin maida hankalinsa kan Abunda ya kaishi har ya kammallah master dinshi,akuma shekaran ya dora da phd dinsa duk akan harkan kasuwanci,akuma alokacin ne yafara aiki da wani kamfanin Turawa na sarrafa takalma,ko shekara baiyi ba akamfanin suka samu lambo yabo,saboda yadda ya jawo musu kasuwa da suna sosai aduniya Tuni Abdulmalik yaji kanshi yayi sama balle da kamfanin ta shiryamai taron godiya tare da wasu kyautan kudade,da kuma dorashi amtayin Md na kamfanin alokacin.

Juliyat tana daya daga cikin ma”aikatan wannan kamfanin,wanda Tunda tasaka idonta akan Abdulmalik taji duk Duniya babu wanda takeso sama dashi,ganin yaki bata fuska sai tayi ta amfani da kissa da kissina irin na mata har yafara kulata da sunan aiki,sunyi tsawon wata Shida suna Abota kafin ta rikide takoma soyayyah mai zafi,basu Rufe Shekara ba sukayi aure,wanda dalilin haka sai da yayi alqawari da iyayan Juliyat cewa bazata taba chanza addini ba,kuma ya yarda saboda shikanshi ilimin Addinin bai gameshi ba balle yagane illah dayayima rayuwarsa.

Sunyi aure tatare a gidanshi wanda kamfani ta mallakamai,watan su goma da Aure Juliyat ta haifi yarta mace,wacce tasha wahala sosai wajen haihuwarta,wanda sai da akayi mata C.S cikin ikon Allah juliyat batayi tsawon rai ba don ko Abunda ta haifa bata gani ba,Allah yayimata rasuwa,mutuwa data girgiza Abdulmalik sosai,kwanaki akayi ana shagali kafin abunne gawan Juliyat,itakuma Jaririyar data haifa sai ya mikata ga mahaifiyar Juliyat wato MADAM DORA,ta riketa kafin yadawo daga Seminar da zashi wanda kamfaninsu taturashi har kasashe uku,zai dawo nan da wani lokaci,ta karba tana kuka domin yarinyar babu inda tabaro uwarta Juliyat,ranar da zai tafi ya sakamata Suna *MALIKA*

About AIS

Check Also

MALIKA MALIK CHAPTER 17 BY JANAFTY

MALIKA MALIK CHAPTER 17 BY JANAFTY Www.bankinhausanovels.com.ng  ……………….”””Rayuwar Farinciki tare da Wata Soyayyah mai tsayawa azuciyar …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *