MALIKA MALIK CHAPTER 1 BY JANAFTY

MALIKA MALIK CHAPTER 1 BY JANAFTY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

KATSINA_

     “””Da misalin karfe 11:20pm na daren Ranar jumma”a Akan Titin dake tsakanin Dutsenmah da katsina wacce take gabda shiga katsina.

Adaidai kan Titin akwai yan Sanda wadanda suke patrole awajen,Suna tsatsaye ne Gefe kuma ga motocinsu guda biyu akallah yan sanda zasu kai su Biyar kowannesu, sanye da uniform dinsu bakake,da ganin kayan jikinsu basai ka tambayesu ba,zaka gane dukansu inspector ne,domin basu da kowani Rank ajikin kakin nasu,dukkansu fuskarsu sanye da Hula p-cap,da bakaken safan hannu sai manya manyan Tociloli masu bala”in haske kamar ta yan fashi,wanda in aka dallareka dasu, sai ka dakata saboda bala”in haskenta,Duk motar da tazo wucewa sai sun tsaidata sunyi bincikenta saboda tsaro  dakuma bincike, wanda daga sama suka sameshi saboda masu shiga da fita da mugayen makamai wanda ake Shigo dasu daga  bodar katsinar aboye.

   Motocine jere guda goma sha biyu dukkansu 11 din iri daya ne Corollahx sai babban ciki wacce tafita dabam itace Range cover baka ce gabadaya motar Tinted ne gaba da bayanta kowacce mota bayan motan an saka musu Nomba mai dauke da Tambarin *MALIKA MALIK1* har zuwa na 12,gudu suke ta shararawa bisa Titin Dutsenma zuwa katsina,Tundaga nesa Yan sandan suke Dalle su da fitila Tunda sukaga yadda suke gudun ganganci bisa Titi.

     Sai da suka kawo gab kana suka fara slow,motar Farko Tana tsayawa Suma na baya suka tsaya,Wani inspector ne ya karisa kusa da motar yana kwankwansa glass din motar,sai da aka bata lokaci kana aka zuke glass din motar.

Wani Inyamuri ne zaune a mazaunin Direba sanye da wasu kaya brown colour Riga da wando da alamu dai kamar Uniform ne,Kallonsa yayi daga sama har kasa kamar yadda Dan Sanda ke karemasa kallo,Cikin gadara ya furta”Lafiya mallam.?.”Dan Sandan yayi mamakin jin Hausa abakinshi don akallon Farko bai yi kama da wanda yakejin Hausa ba.

  Gyara tsayuwa yayi yana fadin”Zamu bincika duka motocinku ne,daga ina kuke da tsohon daren nan? kuma kuke gudu ba bisa ka”ida ba..?.”Yafada yana leka motocin dake bayansa Dan ware ido Direban yayi yana fadin”kai kana ko da hankali kasan motocin waye ka tsare kuwa? dariya Dan Sandan yayi yana fadin”Wannan bashi ne Abun da na Tambayeka ba,tambayanka nake daga ina kuke,? bai mai mgana ba kawai sai ya kada kai yana fadin”Zaka shiga mtsala matukar *MADAM* Ta fahimci meke Faruwa..”Yafada kai tsaye.

  Tana kishingide abayan motan Tana Karanta jaridar Dailytruth bata ma Fahimci meke Faruwa ba,sai zuwa chan Ta fahimci motar da suke ciki ta tsaya cak,cikin mamaki ta dago da kanta bayan Ta kauda jaridar lokaci daya take fadin”Joy Har mun iso gidane..?daga gaban motan ya amsa mata da fadin””A”a madam yan Sanda ne suka tsaidamu wai zasu binciki motocinmu…”Wani zabura tayi tana fadin”What…? wani banzan Dan sanda ne ya tsaidamin motoci,i swear sai na koya masa hankali sai ya gane ba”a yima *MALIKA MALIK* wargi..”

Tafada cikin Fushi kafin ta balle murfin motan ta fice,Doguwa ce  sosai kirarta irin kirar Cocacola ce,Tana sanye da Riga da wando blank and white,tayi Stoking ta ciki ta Kama gashin kanta da band daga tsakiyar kanta bayan ta saki jelan Ta baya,Kafanta sanye da wani takalmi sawu ciki mai tsini sosai blak colur ne,shima Doguwar Fuska gareta wanda kusan Rabinta yake rufe dawani bakin glass,mai kyau da tsari,yadda ta fito cikin Fushi ya sanya duka bodygourd dinta suka Firfito,suna take mata baya cikin Fushi Tanufi wajen Dan Sandan da suke Rigima da Direnba Tun Farko.

Ganin yadda suka nufosu ne yasa yan sandan dasuke gefe suka kariso daidai lokacin data kariso Gabansu ta tsaya suma Bodygourd din nata,sukaci burki abayanta Gilashin idonta ta cire tana fadin”Waya sakaku ku tsare ma mutane motoci,?kuma don Rashin kunya harda motocina,cikin shashancin ku,Uban waya sakaku,waye shugabanku C.P ko IGP  gayamin Shiyace ku tsare motocin *MALIKA MALIK..*? tafada cikin Tsawa Tana binsu da wani matsiyacin kallo.

Jin sunan da tafada ne yasasu mamaki dama sun dade suna jin lbrinta da irin Rashin mutumcinta gashi yau sun gamu da ita,saboda kwarjinta da haibanta dukkansu sun kasa maida mata da martani balle wani cikinsu yayi magana.

  Yana cikin motar yan sand’an Ta patrole video call yake Shida *YAYA MARWAN..* Hira suke sha suna dariya,ta madubin motan yake hango Abunda ke faruwa,saurin yima Marwan sallama yayi Shiko yana tsokanarshi da *INSPECTOR..* Cikin hanzari ya katse wayar lokaci daya yana bude murfin motan ya fito,dogon Namiji ne,sanye da bakaken kaya Riga da wando harda wata rigar sanyi wacce takaimai har zuwa gwiwansa,ba”a iya ganin Fuskarsa saboda ya sanya p_cap ne kuma ya sauko da ita ta Rufemai rabin Fuska,cikin takun isa ya nufi wajensu ammh duka hannuwansa suna,coge a aljihun wandonsa ne.

Tana ganin ya Fito daga motan Ta nufeshi tana fadin”AU shine wannan yabaku umarnin ku Tsaremin motoci ko,toh yau zan koyamasa Hankali in yana neman na goro ne,ko na Sigari bazai kara yunkuri sawa Atsareni ba…”Tafada Tana karisawa garesa Tana zuwa batayi wata wata kawai ta kifesa da mari jikake Kau…!Saboda zafin marin saida ya fito da duka hannuwansa daga aljihu har wayarsa ta fito ta fadi bai sani ba,Hannu biyu ya sanya ya dafe Fuskarsa yana binta da kallon mamaki,miyau ta tsirtamai kafin tace”U Stupid kai ne kasa wadan nan kananun karnukan naka su tsaremin motoci ko,Dama ku yan sanda ba mutane bane,all of u,are Monkey and bakusan komai ba sai tsaida motoci kuna karban na goro dana Sigari Tunda daman ba Abunda kuka iya sai shaye shaye da yima mata Fyade ko,?Toh as From Today bazaku kara tare wata mota ba, joy bring d box Now…”

Tafada ciikin Tsawa Da hanzari wanda aka kira ya nufi mota ya dauko wata yar karamar akwati yazo gabanta wani abu kawai ya danna sai Ga kudi suka bayyana dollars ne Shimfide batai wata wata ba ta dumbuza ta watsamai Afuska tana fadin”Take d money ayi na goro dana Sigari banzaye Yan”iskan kan hanya kawai,wlh i hate aikin yan sanda hardama Uniform dinsu all of dem basu da wani amfani a akasarmu sai lalacewa,Next time ka sake sakawa Atsare motocin *MALIKA MALIK..*Kagani wlh sai na saka an batar dakai Rubbish…”Tafada tana juyawa kamar walkiya Sukuma suka take mata baya.

   Tunda ta kifamai mari da wadandan mugayen maganganun datake fada suka daskaran dashi gabadaya Tunaninsa da zuciyarsa ta tsaya lokaci guda,wani bakin ciki da takaichi tare da wani Fushi suka lullubeshi,kowacce kalma in ta fada sai yaji kamar saukan aradu,tacima kakin yansanda mutumci tayi jam”i gabadaya ta hada kenan harda mahaifinsa mafi soyuwa garesa,wanda yabada komai nasa domin Taimakon kasarsa,yan sanda da basa barci domin kare dukiyan al”ummah da lafiyansu sune take kira basu iya komai ba sai shaye shaye dayima mata fyade,kakin dayake burin yaga ya sanya ajikinsa Shitake kira Rubbishi…Ina!Da sake Tuni wani Bakin ciki  mai hade da wani Tarnakin hawaye suka kwaranyomishi tana gabda da Shiga mota ya daga murya cikin Fushi da amo mai Sauti yace”” *MALIKA MALIK…!SAI NA RAMA…* …”yafada cikin wani irin amo,waigowa tayi kafin tayi danyi dariya tace”Ok start d game young police man..”Tafada kan Tafada mota,dukkansu kowa yakoma motarshi Suka tadasu suka wuce da gudun bala”i kamar zasu bankesu.

  Suna Wucewa ya nufi mota yana fadin” Inspector Saleh take me to home now…”Yafada muryansa ya fara rawa  saboda bacin rai lokaci daya ya bude gaban motan ya shiga,da hanzari Inspector saleh yayi mgana da sauran yan Sandan kafin shi ya nufi motar ya shiga mazaunin direba yaja sukahau kan titin da Sauri,Suma din dai cikin katsinar suka nufa adaren.

____________________

Anguwan *LAYOUT* suka nufa daya daga cikin anguwannin masu hali dake cikin katsina ta dikko Dakin kara,kofar wani makeken gida motar patrole ta yan Sandan tayi parking Tunkafin motar tagama tsayawa ya bude murfin motan, ya Fita da Sauri yarda yake tafiya kadai zaka gane yana cikin Fushi ne da Fusata.

Inspector Sale ya kalleshi yana kada kai,bai Fito daga motar ba, yamata kwana ya juya lokacin agogon dake hannunsa yake nuna karfe 1:00am na dare,shiko yana zuwa jikin get dinsu yasaka hannu ya shiga bugawa da karfi kamar zai tashi sama,megadi dake zaune gefe gyangyadi yafara dibamshi kamar amafarki yaji bugun get,da hanzari ya mike sanye da yake da uniform irin na yan mopal,koda yaji bugun bai razana ba,Nufar get din yayi yana Fadin”Who iz dis..? 

Tsaki yaja kafin yace *AM SALEEM FREEKING KABIR KUMO..* Yafada ransa na kuna,da hanzari jikinsa na rawa da bari yabudemai karamar kofar yana Fadin”Am sorry sir did know….”Baigama Rufe baki ba ya wucesa Fuu kamar iska baki ya rike yana binsa da kallo,domin a iya saninsa Saleem baida dabi’ar shariya.

Maida kofar yayi ya Rufe yana Fatan Allah yasa koma miye ya Faru mai dadi yadda yake alfahari da wanda zai gaji Yallabai.

Babbar kofar da zata sadaka da babban falon gidan Abude take,sakamakon ansan komai dare zai dawo yana Shigowa Falon babu kowa yadda yake tafiyane zai ankarar da mai kallonsa kamar agauce yake.

  *CP KABIR KUMO* dake tsaye kofar dakinsa ya kuramai ido yana kallonsa yana neman Shiga dakinsa ne yasa yayi kiransa..”Saleem….”Yafada cikin datattako,Waigowa yayi da sauri yana kallon Abbin nasa,saurin sadda kai yayi saboda kada Abbin nasa ya fahimci halin dayake ciki kakalo mirmishi yayi yana Fadin”Na dawo Abbi…”

Gyada kai yayi yana Fadin”Ai na ganka,ammh why naganga kamar azafafe..? Saurin Washe hakora yayi yana Fadin”la babu komai Abbi,barci nakeji dat why na dawo da Wuri..”Yafada yana Jin takaichin karyan dayayi,kallonsa kawai Abbi yayi kafin yace “Ok sai da safe..”Yafada yana kuresa da ido,da hanzari yace”Sai da safe Abbi…”Yafada yana tura kofar dakinsa ya Shige da sauri,Yana sauke ajiyar zuciya.

Yana Shiga yayi tsaye yana karema dakin nasa kallo,hannu ya dungula ya daki bangon dakin,bayan kunnuwansa suna jiyomai amom muryanta,fuskarsa tana jin zafin karan Tafinta kana idanuwansa suna kallon sanda ta Tofamai miyau,ta watsamai kudi,kana kunnuwansa na jiyomai sanda tace yan sanda basu da wani amfani,sai yima mata fyade da shaye shaye? kenan harda Abbinsa tayi jam”i ? yazama dole ya binciko ko wacece wannan yarinyar domin yayi Saurin ankarar da ita kuskurenta.

Kan gado yafada yana dukan katifan kota ko”ina Yana fadi da karfi..* WLH SAI NA RAMA…”!* yake Fada yana jin wani tukuki daga kasan ransa,har sai da wasu hawaye suka zubomai,yasaka hannu ya sharbe kafin yace”No saleem kuka bana ka bane,juz stand up kayi karatu tukuri domin ka zama DAN SANDA,ka nuna mata cewa ita bata karfin kowa ba,ammh duk hakan bazasu samu ba sai yafara gano ko  *WACECE ITA*…”

  _*Tirkashi….Salon na dabam ne,haka Jimarin na mussaman ne,wannan karon Abun zai taba zukata,wannan karon Abun zai taba kowa ne,Kada Abun ya daure muku kai Abu daya zaku nemo Wacece MALIKA MALIK.!? kuma waye wannan Dan MATASHIN SAURAYIN? miye alakarshi da Aikin yan Sandan? Duk ku biyoni Zan warware muku Zare da Abawa*_

_Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *MALIKA MALIK* Akan Naira 200 kachal?,ta wannan account Nombar, *0552179550* JAMILA UMAR GT BANK,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *09069067488* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *09069067488* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

_NIGERIAN POLICE FORCE-BIRNIN RUWA ZAMFARA STATE_ 

  “””Wata babban Headquater ce mai dauke da haraba mai girma da Fadi,da ban sha”awa,ginin wajen gini mai kyau da tsari domin da Duste aka gina wajen.

Daga haraban Compound din Motocin Police sunfi guda goma Fake,awajen kana ga wasu yan sanda nan na shawagi awajen daga Inspectors sai su sargent suke yawo aharaban wajen Fuskarsu kwata kwata babu Annuri.

Daga cikin Babban ginin, akwai tarin Afisoci kafin kayi gaba karatsa wani dogon lungu ka isa kofar Office din Shugaban Headquater wanda Sunansa yake makale jikin wani dan Anini daga saman kofar Office din, *ACP SALEEM KABIR KUMO* naga an Rubuta da manya baki,ban tsinke da al”amarin ba,sai da kofar Office din ta wangale kanta,Cak na tsaya ina bin kayatattacen office din da kallo azahirin batu an tsara wannan office din,daga yammah wasu kujeru ne guda uku ga wani karamin center table mai kyau da tsari atsakiyar wajen,kana daga gefe ga wani karamin frigde,mai kyau da tsari,daga kudu,kuma kofar wani daki,wanda yake akulle,daga gabas,kuma wani katon Tebur ne mai dauke da Takardu da kuma Laptop,sai wasu kananun hotuna wanda suke sanye cikin Frame,sai daga chan sama kuma Hotuna ne,Farko na Shugaban kasa ne,sai daya na gwannar Jahar Zamfara,sai guda daya na Shugaban Yan sandan NIGARIA,IGP NA POLICE GABADAYA wato *IGP KABIR KUMO*..”

Ashe duk wannan Abun kalle kallen danikeyi ma mallakin office din na zaune akan kujeransa irin mai juyawan ne,ta juya dashi yabama kofar Shigowa baya,juyo da kujeran yayi Idanunsa duka suna Rufe ne,kuma dukka hannuwansa suna kan kirjinsa ne,da alamun yayi Zurfi cikin Tunanin dayakeyi,baki na sake ina karemai kallo cike da mamaki da al”ajabi.

Shiba fari bane Bakin mutum ne,ammh Ganin farko zakamai ka zata cewa Fatarshi batayi kama da yan Nageria ba,sai dai tafi chanchanta na yan kasar maroco,saboda yadda tahade tabada wani choculate,na kyau da tsari,doguwar Fuska gareshi sai dai tana  da dan Fadi kadan,Hancinsa dogo ne,wanda ya hade da bakinsa karami mai dauke da bakin Sajensa,wanda yakara ma Fuskarsa kyau lebensa Pick ne,yana Fitar da maiko kamar yasanya Man baki,giransa tana cike da gargarsa wanda taso ta hade da yar”uwanta haka gashin idonsa,Bude idanunsa dayayi ne yasa nayi baya ganin yadda Fararen idanunsa suka bayyana awaje,farare kal dasu gasu basu da girma na azo agani ammh suna cike da wani Sirri,mikewa yayi cikin azama yana goya duka hannuwansa abaya yafara zagaya office din yana cije baki,Ashe dogo ne sosai ammh yana da murjewa ta wadanda sukaji dadi da hutu sosai Wadanda ake kira giant,matashin Saurayi dan kimanin Shekaru 28 Aduniya,wanda akallo daya in kayimai zakayi mamakin yadda Yaro matashi mai kananan shekaru kamar sa zai iya taka wannan mtsayin,yana sanye da Uniform dinsa bakin wando da Rigarsa mai launin Ruwan Bula ammh light dinshi,daga hagu dan aninsa ne,mai dauke da Sunansa ajikin bayan gefen duka kafadunsa suna sanye da duka rank dinsa ma”ana amtsayin dayake kai ayanzu.

  Komawa yayi yazauna yana Dora kafansa daya kan Daya,wayarsa ya zaro wata faskekiyan wayar Kirar Samsumg,yana latsawa kafin hotonta ya bayyana,tana sanye da Riga da wando black and white,kayan sun dameta bayan sun Fitar da duka Surarinta waje,kanta babu kallabi,illah dogon gashinta wanda ta daure atsakiya da band,ta saki jelan yayi kasa,fuskarta sanye da wani bakin glasa,yacikamata rabin Fuska,kafarta kuma wani takalmi ne,mai tsini wanda har ya Wuce misali lokaci da aka dauki Hoton tana saukowane daga matattakalan benen Jirgi,wasu Exscorts suna biye da ita su biyu kowanne sanye da Court sun saka wasu galasai Abun sai wanda ya gani,daya yana dauke da Brief case,sai daya yana dauke da wata karamar jaka na mata,kunnanta yana sagale da waya tana mgana sanda aka dauketa hoton da alamun ma bata da masaniyar sanda akayi hoton.

  “”Kuramata ido yayi zuciyarsa na bugawa,Tuni hoton Abunda yafaru Shekaru biyar baya ya Shiga dawomai daki daki,har saida ya dafe kuncinsa ba dama inda ta shararamai mari,,har sai da ya Runtse ido,kamar alokacin take marin nashi,matse bakinshi yayi yana Shafawa,daidai inda ta tofamai miyau,idanunsa ya Runtse yana Sauke ajiyar zuciya yana tuni sanda ta watsamai kudi ajikinshi tana kiran aikin yan sanda da Rubish,Saurin bude ido yayi yana wani Zare ido,tsoro naji saboda ganin yadda gabadaya jijiyoyin kansa suka Fito radau,ga idanuwansa sunyi jajir kamar barkoni bayan gabadaya muscle din hannuwansa sun bayyana suna wani motsi daga cikin Abun tsoro wlh..?

Wayar ya kifar akan teburin kafin ya mike azuciye kamar tana gabanshi yasaka hannu ya daki gaban Teburin yana huci yake fadin”, *MALIKA MALIK..Sai na rama..”Nayi alqawarin sai na wulakanta rayuwarki sai na nuna miki ke ba kowan kowa bace,sai na miki matsayi tare da zati,jarumta da sadaukanta yafi komai muhimmaci,wlh tallahi sai na nuna miki mtsayin kakin yan Sanda yafi uwarki yafi ubanki da duka danginku da dukiyar dakuke takama…!!!!”Yafada yana Fitar da huci Shikadai kafin yakoma yazauna jagab yana Ajiyar zuciya.

Duk tsawon wannan Shekarun daidai da Rana daya baitaba barin Abun yafita daga Ranshi ba,barci yake,cin abinci,wanka yakeyi karatu yake,driving yakeyi,komai in yana yi sai Abun ya fadomai,zuciyarsa taki barinsa sukuni daya Runtse ido ita yake gani tana tsaye gabansa tana aibatanshi tare da wulakanta martaban mahaifinsa bayan ta hada ta shararamai mari,kamar wani sa”anta yarayu cikin wadannan shekarun cike da zumar da zati na Ramuwar gayyah ga malika malik,duk iya tsawon wannan Shekarun daya kwashe baitaba yarda yabar bibiyar Rayuwar Malika ba,duk wasu bayananta da hallayanta da komai nata yana dashi kuma ko”ina zata yana da ido kanta,bai ta bari koda ta minti daya yarasa wani Abu game da ita ba,saboda ita ya chanza burinsa na zama *ENGNEARING*,saboda ita ayau yake zaune awannan mtsayin domin ya nunamata Wutsiyar Giwa tayi nesa dana Rakumi,kuma tsakanin shi da ita kamar tazaran sama da kasa ne.

Da hanzari ya mike yafara tararra kayansa,Wayarsa ya maida aljihun kafin ya maida laptop dinsa ama”ajiyarsa key din motarsa kawai ya dauka ya Fice da hanzari,yana Fitowa suka dinga kamemai suna Fadin”Sir..”ko kallonsu baiyi ba iilah jefama wani daya daga cikinsu key yayi yana fadin”Close d office,..Kai kuma Sargent musa follow me,Abuja zamu yanzu..”Gabadayansu suka amsa da ok sir Safe landed..”Har yafara taku ya waigo yana kallon Sargent musa yana Fadin”Bring d key back to me sargent musa,i will drive my self juz take care, komai kenan zamu waya sai Monday,zan dawo ok..”Da kai suka amsa kafin sargent musa ya mikamasa key din motar,da sassarfa ya fice suka mara mai baya,sai da suka rakasa har wajen motarsa 320 kirar Toyota,Sargent musa ya budemai gidan gaba ya Shiga,sai da ya daura belt kafin ya bama motar Wuta rufemai kofar motar sukayi suna dagamai hannu,mirmishi yayi musu yana kara jadaddamusu su kula sosai,ribas yayi yana danna hon da hanzari megadi yazo ya wangalemai babban get din waje ya sulala zuwa waje da gudu,sanin dayayi akwai Tafiya agabanshi yasanya yasakarma mota Wuta,duk da yasan ko atsarin doka hakan ya haramta,ammh bashi da zabi dole ce tasashi yin haka domin yana bukatar isa Abuja kafin duhu ya shiga,sanda yake duba Rantsatsen agogon Fatan dake hannunsa Hudu saura kwata,jinjina kai yayi bai Fita daga garin zamfara ba,sai da ya tsaya awani masallaci yayi sallar La”asar kafin ya dauki hanyar Abuja.

   ________________

_GARKI ABUJA_…

  Karfe 8:30pm na dare yasaka Hancin motarsa Cikin Rantsatsiyar anguwan nasu tamasu hali,wato GARKI,wani tamkamen gida naga yana ta zuba hon,inda megadin gidan yazo da hanzari ya wangalemai get,Koda ya sulala ciki,parking space ya nufa inda ga motocin nan birjit,afake akaton haraban gidan,gidan gabadaya dauke yake da Security yan mopal,sukai su goma suna zagaye gidan,megadin da kanshi yazo ya budemai yana Fadin”Barka da zuwa yallabai..”Amsawa yayi yana Shafa kanshi Motar Ummi dake fake a haraban gidan ya kallah ajiyar zuciya ya sauke,Thank god Tunda Ummi tana gida yafada aransa,Wayar dake aljihunsa yafito dashi daidai lokacin da kiran *YA MARWAN* yafito daga wayarsa da hanzari ya daga yana Fadin”

“Wai nikan Yaya marwan,bazaka iya kwana bane, batare da kaji muryata bane..? yafada yana dagama Mopal din dasuka sarama hannu,,hanyar dazai sadashi da Falon gidan,ya nufa yana dariya jin Abunda Ya marwan ke fada”Kai kai..lallenema yaron nan,daga ina kula da Amanan Abbi,sai na murdema kunni in nadawo malalacin Acp kawai”Dariya ya kece dashi daidai yana Shiga falon,tsaye yayi yana Fadin”Kai ya marwan,kullum haka kake cewa,ammh kaki dawowa u know  we all miss u ko.? yafada yana kokarin zama a daya daga cikin Royal chair din dasukayima Falon Kwanya,kawai yaji kikam ta fadomai tana Fadin

“Oyoyo Ya saleem….”Take Fada Tana ihu,saboda yadda ta fadomai harsai da wayar hannunsa ta subuce tafada kan kujeran da yake kokarin zama,dagowa yayi yana riketa dakyau kunnanta ya murde yana Fadin”Yarinyar bakijin mgana ko? Baki ta bare da karfi tana Fadin”wayyo Allah kunnena Abbi,Ummi ku fito ya saleem zai karyamin kunni na, yarage min sadaki..”Take Fada tana kware baki harda buga kafa,shiko da gangan yakara murdemata kunni yana Fadin”Har yaushe ne,zan ce kidaina fadomin ajiki kai tsaye,ke bakisan kin girma bane..”? yafada yana dalle mata baki da dayan hannunsa,yana dariya yace”Dallah yima mutane shuru,ai babu mai zuwan cetonki…”Gum…!Yaji an makamai Filon kujera a keyarsa lokaci daya da Fadin”Sakarta don mai garinku kumo..”Tafada tana tsaye tana hararansa,dafe keyarsa yayi bayan ya saki *SALEEMA* wacce takoma gefe tana Fadin”Yauwa hajiya,ramamin..? tafada tana murza kunnanta saboda zafin dataji bana wasa ba.

Da Kallo yabi *HAJIYA BABBA* wacce ke tsaye da Filon kujera tana Fadin”Ai Tunda naji ihunta nasan Azzalumi ya dawo,wlh duk kakoma dukanta sai naci kaniyarka acikin gidan nan,yarinya tazama budurwa ko yanzu aka kaita daki zata zauna,ammh kana jibgarta kamar kasamu jaka..? Tafada tana Hararansa again,Bata Fuska yayi yana kallon Saleema wacce hajiya ta karisawa wajenta tana fadin”Muga Fuskar da kunnan,wlh indai naga Shaidan yatsu sai yabiyamu,kowani yatsa dubu daya ne,dubu biyar dinmu ahannu,kaji da wai kuma Uwarka ce zata bimana hakki tunda lauya ce..”

Tafada tana duba Fuskarta itako Saleema tana kara Narkewa tana fadin”Hajiya dubamin kunnan nan,Allah banaji sosai..”Tafada tana matso kwallah,Tsaki Saleem yaja yana Fadin”Allah yasa kidaijin gabadaya naga karshen iyayi da rashin kunya..”Hajiya ce tayo kanshi da gudu tana fadin”Ja’irin yaro kawai..”Take Fada tana binsa da gudu suka fara zagaye falon Saleema dake gefe tana dariya tayi wajen wayar Saleem nan ta iske haryanzu Ya marwan na bisa layi,dariya kawai yake ci diramar hajiya da Saleem shiya hanashi kashewa domin duk duniya babu wanda yakeso da kauna kamar family dinsa,da ihun murna Saleema tace.

“Ya marwan I miss u..”Miss u too our little kiddo,ya sch..? Amswa tayi da lafiya kalau kafin tace”Ya marwan yaushe zaka dawo…? Kwalla ya Share saboda kewan Gida yace”Very Soon Little,naji Hajiya ita da megidanta suna kwamawa,ina ta dariya”Dariya tasaka tana kallon yadda Saleem yake gajiyar da hajiya da gudu itako taki daina binsa shiko da gangan yake zagaye falon yana mata gwalo,dariya saleema ta saka Tana Fadin”Wlh ya saleem zai gajiyar ma Da hajiya kashinta kaga yadda yake sakata gudu..? Da sauri Ya marwan yace”Little bari na kiraki Vid cll,juz ki haskamin nga wannan diramar kinji..”Da hanzari tace”Yanzu kuwa ya marwa mai jirgi,..”Tafada tana dariya yanke kiran yayi da hanzari ya Shiga wattsop,dayake tasan wayar Ya Saleem baya sanyamata password da hanzari ta shiga chairt dinshi tana bude data sai ga kiran ya marwan ta dauka tana Fadin”Ya marwan wacth dis comedy plz..”Take Fada tana haskomai Saleem wanda ya dage yana zagaye kujera hajiya na binshi da Filon kujera tana Fadin”Allah sa na kamaka ka gani maketancin yaro kawai..”Kan kujera Saleema ta haye tana Fadin”Yauwa hajiya ki kamasa,kin kusa,yauwa kamasa ….”

Take Fada tana dariya Ya marwan saboda dariya sai da ya duka cikin dariya yake Fadin”Dan sanda yabada training na rage kitsen jikin hajiya fa..”

‘””Kai Saleem ungo naka nan,don mai garinku Uwartawa kake son kashemin…”

Sukaji anfada daga  saman saukowa step Din benen dakin Abbi,dukkansu suka waiga suna kallon wani Dan Dattijo wanda akallah zai bama Shekaru 58 baya aduniya,ammh akallon Farko bazakace haka,saboda yadda yake dogo,kadan kadan Farin gashi yake akansa da gemunsa,Sanye yake da bakar jallabiya sai wani karamin gilashi mai karamai karfin gani,Jarida ce ahannunsa yana kokarin saukowa yake kara cewa”Saleem wlh kafita daga idona,so kake ka kashemin uwa da shanshancinka ko?

Hajiya na jin haka ta zube kasa tana Share gumi ga hawaye suna zubomata tana Nurfafashi kamar mai Asthma,Saleema tayi saurin yanke wayarsu da Yaya marwan ta nufi Hajiya tana Fadin”Hajiya hajiya sannu bari na kawo miki Ruwa..”Tafada tana kunshe dariyarta,Saleem dake gefe ya tafi ga Abbi yafadamai yana Fadin”I miss u Abbi…”Turesa yayi yana Fadin”banyi kewarka ba,tunda daga dawowa zaka saka hajiya adamuwa..”Yafada yana karisa saukowa gaban hajiya ya durkusa yana Fadin”Don Allah hajiya kidaina biyema Saleem,wahalar dake kawai yakeso ya dinga yi..”Dagowa tayi tana share kwallah tace”Kabiru ka barni da yaron nan,Allah sai na mai rashin mutumci,kalli yadda yasani Gudu yanzu gabadaya jikina ciwo yake,Numfashina na Fita da Sauri Sauri,kilama na samu ciwon na Iska me ma sunanshi Saleema..”Da hanzari Saleema tace”Hajiya Asthma..”Da hanzari tace”Eh Asma,kalli kagani..”Take fada tana share zufa.

Saleem dake gefe  ya kyalkyace Da dariya Haryana rike ciki yace”Bawanni Fa Asthma,Abbi kawai nasata gudu ne ta jijjiga jini,kullum tana zaune agida,kitse yazauna mata waje daya..”Yake Fada yana ta kwasa dariya ji yayi an Damkemai kunni ta baya ana Fadin”Saleem wai kunnenka na kashi ne? kwata kwata bakajin mgana,kullum kana girma ne,kana cin kasa ko..”Hannunta yariko yana Fadin”Ummi na…”Yake fada yana zagayowa ta gabanta kallonta yayi kafin kawai ya Rumgumeta yana Fadin”Nayi kewar Lauya mamata..”Yafada yana wani narkemata bayansa ta shafa tana Fadin”Nima haka my Son,ya aikin..?Tafada tana dagosa daga jikinta Yamutsa Fuska yayi yana Fadin”Ba dadi Ummi,wlh wahala tayi yawa baki ga sai Rama nake ba..”Dariya suka sakamai kafin saleema tace,”Bawani kaida wlh lalacinka yayi yawa Ya saleem…”

Daure Fuska yayi yana Fadib”Waye malalacin..? Makewa tayi bayan Abbi tana Fadin”Acp Saleem kabir kumo mana..”da gudu ya bita bayan Abbi,Ummi na Fadin”Saleem kabari meye haka,zaku fara ko..? ina ko jinta bayayi zungurota yake daga bayan Abbi yana Fadin”Ki fito kigani wlh sai na Barki kwance yau zaki gane waye malalaci tsakanin ni da wanchan dan kauyen Saurayinnaki..”Abbi ne ya harde hannu akirji yana Fadin”To daketa mara kunya,ai ko mutuwa najin kunya mahaifi mallam..”Bata Fuska yayi yana Fadin”Haba Abbi yanzu don Allah sai na bar karamar yarinya nacemin malalaci in kyaleta..”Hajiya dake zaune tace”To karya tayi,ai ni inaga aikin yan Sandan ma,babanka yayi munamuna aka baka,ammh bawai don ka chanchanta ba,jarumi dayane agidan nan Marwanuna shine kadai Namijin gaske..”Tafada tana hararansa,wani Abu yazomai wuya ya juya yana kallon Hajiya rai bace”Karki kara walh…”Abbi yace”in kuma takara fa..? Yafada yana kallonsa Waigowa yayi yana wani hade rai yace”Ta kwana acell..”!,Yafada kasa kasa yadda bamai jinsa,kallonsa Ummi tayi tana dariya tace'”Mekace..? Hanyar Dakinsa yayi yana Fadin”Bance komai ba..”Dariya suka sakamai Abbi ya girgiza kai yana Fadin”Ke kuma Fito daga bayana,sau nawa zan fadamiki kifita harkan Saleem ehe…?Tura baki tayi tana Fadin”Abbi shifa ke shiga harkata..”Hajiya ta karbe tana Fadin”kaji ka dawani zence,wannan Ja”irin Da’n naka,ko ba’a shiga harkansa sai ya Shiga na mutum,ni wlh addu”a,nake Allah yabashi wata mata masifaffa,yadda zataci mana ubanshi dakyau..”Gabadaya suka kece dariya Ummi na dariya ta Wuce kichen tana Fadin”Little ni zo ki tayani kwaso abincin nan zuwa Dinner area,don rigimarku bata karewa keda Saleem da hajiya..”

Jin haka yasa ta Fito daga bayan Abbi zata bi Bayan Ummi kamar walkiya taga Mutum agabanta yana fadin”Wa na kama..”Ai da gudu ta juya ta nufi sama tana tana fadin”Wayyo Ummi,kinganshi ko..? Shima agujen ya marata baya yana Fadin”Ummi ta aikeki kiman Rashin kunya,..”Taka taka sukayi sama aguje,Girgiza kai Abbi yayi yana zama kan kujera yana Fadin”Saleem,da saleema bansan yaushe zasu girma ba..”

Hajiya data cicciba tatashi dakyar tace”Sai Ranar da kuka gama akidarku ta boko kuka aurar dasu,banda lalacewa yara sun balaga sun balage agida,ammh ba wanda yayi aure,shi wanchan babban kwabo,yana chan yana yawo asama,shiko wannan banda lalaci bai iya komai,sun zauna suna ta sakarci da saleema acikin gida,Allah dai ya ganar dakai kabiru..”Tafada Fuska ba Annuri kafin ta dingisa ta Shige wani korido tana ta mita ita kadai,da kallo ya bita kafin yabi Ummi da kallo,wacce ta kwaso kololi,yana kallonta ta kalleshi ta kauda kai,tana cije baki,kamar zatayi dariya,dan mirmishi yayi yana maida hankalinsa kan jaridan dayake karantawa,domin indai wannan mganar ne,Hajiya kullum sai tayimai gori,kamar shi yahanasu yin Auren,batasan komai lokaci bane.

*Hohoho Fans,yanzu fa aka Fara wasan akwai kitimulmula?tare da chakwakiya awannan KAFCHAN?Wlh Duk wacce bata karanta Malika malik ba,taga salon Soyayyah cikin daukan Fansa ba,am srry to say ansha da ita,domin Abun zaifi daukan hankali Fiye da Amanar da HAFIZ ABDALLAH RUMA Yabama HAFSAT ATTIHIRU ATTA,Kuma zai bambamta da irin Sakacin da SAKINA KABIR KANKIA,tayi ga mijinta DR SAFWAN SALE SAFANA,Kuma soyayyar ba irin wacce NAZIR ADAM GALADANCHI ,Yanuna ma NUSIBA ABUBAKAR BUNZA,bane,Kana ba irin kaunace wacce MU”AZZAM MUHD MODU,Yanunama ZAHIRA ABUBAKAR BHAGANA,bane Kuma ba irin Shakuwa da Kauna bane irin wanda SARKI ALIYU ABDULNASEER,yanuna ma Masoyiyarsa AZEEMA LAWAL BATURE,bane✌,wannan salon zai Bambamta dako wanne,wannan zuwan Salon na ACP SALEEM KABIR KUMO NE,Dakuma MALIKA ABDULMALEEK DAN KASUWA,Kada kibari ayi baki*

_Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *MALIKA MALIK* Akan Naira 200 kachal?,ta wannan account Nombar, *0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *09069067488* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *09069067488* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu KISHIN MATA,na HAFNAN,300 ne kachal?shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*…

About AIS

Check Also

MALIKA MALIK CHAPTER 17 BY JANAFTY

MALIKA MALIK CHAPTER 17 BY JANAFTY Www.bankinhausanovels.com.ng  ……………….”””Rayuwar Farinciki tare da Wata Soyayyah mai tsayawa azuciyar …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *