KASAR WAJE CHAPTER 1 BY MARYAM DATTI

KASAR WAJE CHAPTER 1 BY MARYAM DATTI

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 
No.1 hausa novels, site all over the world with more than 5000 books uploaded, the site was found on 2014 by A/I/S
All our books are free, we do not charge for uploading , we upload novels, daily and over 400+ chapters montly.Kawo Kaduna!+

Tana zaune 3sitter d’in falonta tanata kallace-kallacen hotuna a Istagram inda ta ga hotonan wasu abokai matasa su biyu sun bala’en had’uwa musamman d’ayan
d’an tsayuwa tayi tanata kallon hotunan inda tana kallon hotonan wani tunani take na burin da suka dad’e suna yi a rayuwarsu

Shiga accnt d’in mai hoton tayi sosai sunansa ta kalla Yasir Mai tumbi

Tunani ta d’an tsaya tana yi a ina take jin sunan tabbas a nan Kaduna ne
Fita daga ista tayi ta shiga Facebk inda ta shigar da sunan ta fara dubawa ay kuwa ta gani ta fara shiga sosai har hotunan da ta gani a ista inda taga hotunan tare da sunan sauran da ke kan hoton

Bibiya ta k’ara yi tana so ta gane wanda hankalinta ya kai kansa shi meye sunansa

Don haka ta k’ara jefa sunan farko dake saman hoton “Yusuf Suleiman”

Ay kuwa shima ta ga nasa accont ta shiga
Tsayuwa tayi ta karanta komai na information d’insa dake accnt saidai babu wani information sosai sai sunansa da origin d’insa da garin da yake yanzu wato “Toronto Canada”

Ajiyar zuciya tayi gaskiya wannan shine perfect miji da suka dad’e suna yiwa HAYFA buri dukda ita hayfar na soyayya da Kamal amma ga wannan da gani d’an wani k’usa ne gashi babu laifi yanada kyaw da kwarjini

Nan dai Aunty ammah ta turawa yusuf friend request inda tayi sa’a tana shirin sauka jin an kira asar shi kuma Yusuf na hawa yana gani haka kawai shima bai saba saurin ansa request ba hasalima shi abokansa basuda yawa sabida baya ansa request
Ganin har ya ansa ammah ta tura masa da gaisuwa

Yusuf bai iya ansa mata ba ya share ya sauka!

d’an shiru tayi na takaici yaga msg d’inta bai ansa ba
Saidai d’an tsaki tayi tace haka suke shegu yaran masu kud’i girman kai amma wlh kaine abinda muka dad’e muna nema ni da goggo da Adda suwaiba kuma IA burinmu zai cika

Kashe data tayi ta mik’e taje tayi sallah kafin su hayfa su dawo tanason yin d’an bacci

MALAM HALADU

Ba barbarene d’an asalin garin maiduguri yawon cirani ya kawoshi kaduna yake gyaran agogo a badarawa
A nan Kaduna ya auri matarsa y’ar garin ancau Hausa-fulani ce dake kaduna, sunanta Aljanna saidai suna kiranta goggo alje da fillanci
sunyi aurensu sunada yara 2 duka mata Suwaiba itace babba sai Amina ana kiranta Ammah kasancewar sunan kakarsu mahaifiyar babansu take ci

Tun bayan haihuwarsu Suwaiba da ammah goggo alje bata k’ara haihuwa ba ana haka wani mak’ocin malam haladu buzu y’an gudun hijiraatarsa ta rasu sai y’arsa d’aya shima baya lafiya sosai ya rok’i malam haladu ya auri y’ar mai suna safiyya

Bayan auren malam haladu da safiyya da kwana tara babanta ya rasu
Itama safiyya shekara d’aya da aure tazo haihuwa ta haifi y’arta mace ta rasu wacce aka sawa suna Hadiza sunan kakarta ta gun uwa saidai ana kiranta HAYFA

STORY CONTINUES BELOW
Inda goggo alje ta rik’e hayfa kamar su suwaiba da amina saidai har zuwa yanzu lokacin Mahaifinsu babu wani ci gaba a rayuwarsa da k’yar ake samun na dafawa kullum da haka da k’yar ammah da suwaiba suka samu gama secondary suka yi aure saidai suma duk talakawa suka aura babu wani ci gaba sosai da k’yar aunty ammah ta lallab’a tayi degree d’inta a Kasu ta samu aiki a wani govmen school, ita kuwa suwaiba ta samu ta saya friza biyu manya tana kunun aya da zobo da jinja
Yaran aunty ammah uku na suwaiba biyar

Ganin har hayfa ta gama primary babansu saima babu da ta k’aru suwaiba da amma suka yanke hukuncin ammah ta d’auki hayfa sabida iyayensu su samu sauk’I sannan su maida hankali hayfa tayi karatu mai zurfi  su samo mata miji attajiri ko d’an wani babban attajiri sabida su wanke talaucin da suka taso har yanzu suke rayiwa ciki ganin ita hayfa ta fisu kyaw

Hadiza Haladu Aka Hayfa!

Shekarun hayfa yanzu sha bakwai suna gab da zana jarabarsu a makartarsu Zamani college Kaduna

Da bashi da yaudarar samari haka ammah ke biyawa hayfa school domin school fees d’inta a shekara yakai 411k
inda itama tabi ra’ayin yayyunta sam bata son wahala itadai taji dad’i tayi kud’i ta sayawa iyayenta da yayyunta komai na masu kud’i da gida da motoci

Doguwa ce da dogon fuska mai dogon hanci kamar na India tsawonta ya kai 160m tanada shafewar mara sosai sannan tanada cikar gashi ba wai mai mugun tsawo ba dukda tanada jinin buzaye batada mugun fari fatarta kusan kalar na babnta ba bak’a bace amma ba fara bace sosai tanada manyan idanu masu haske da cikar k’irji da baya mai kyaw
Sosai aunty ammah ta koyawa hayfa jiji da kai domin kuwa sam bata kula samari sai taga mutum da yakai da mota kuma ba tsohuwar mota ba domin har k’irorin mota hayfa duk ta sani ta  haddace

A gefe guda tana d’an soyayya da wani d’an yayar k’awar Aunty ammah kamal yana aiki first bank dake yakubu gawan way dukda Aunty ammah ba wani so take ba domin burinsu akan hayfa yafi k’arfin auren kamal amma ta k’yaleta da kamal ganin baya gajiya da kashewa hayfa kud’i sosai da bata waya dukda ita ba damuwa tayi da wayar ba saidai in ya bata baifin wata uku su sayar Aunty ammah ta k’ara mata atamfofi da takalma tayi mata d’inkuna su ce masa wayar ta b’ata ya sake bada wani haka dai suke wahal dashi mamansa ma tazo bata so amma ganin yadda kamal ya nace ta k’yaleshi

Kwatakwata albashin ammah 70k ne amma da cutar masoyan hayfa ta gyara gidanta kujerunta masu tsada kusan 200k da dinning kai ammah ta gyara gidanta kamar na y’an gayun kd komai akwai sabida a falonta hayfa ke zance da duk wani hamshak’i da zasu yaudara su tatseshi tas su koreshi

Hayfa kuwa yadda kasan wata y’ar attajiri haka ammah ke kashe kanta wajen kashewa hayfa kud’i don a ganinta ta hakan ne zasu samu d’an mai kud’i ko wani k’usa da zai auri hayfa su maida fiye da abinda suke kashewa a kanta

Tuntuni baban kamal ke cewa zasu zo saka ranar hayfa da kamal Aunty ammah da suwaiba su k’ak’alo k’arya su ce a jirasu basu shirya ba har dai a k’arshe suka ce sai bayan hayfa ta zana jamb taci sai a saka ranar wanda shima wannan wani salo ne na yaudara domin amma da suwaiba sun shirya in har zuwa lokacin hayfa bata samu wani babban d’an attajiri ko d’an wani k’usan gomnati ba to zasu ce bata samu jamb ba inta samu sai ta samu za’a saka ranar. Haka iyayen kamal suka gaji da rainin hankalin yayyun hayfa suka zuba musu idanu ganin har gida kamal na dashi a halliru d’an toro road u/rimi amma sai juyashi hayfa da yayyunta keyi.

da wannan burin da mugun jiji da kai irin na yaran zamani college hayfa ko y’an mata a unguwarsu Kawo ba kowa ce budurwa take kulawa ba dama kuma batada magana sai abin ya had’u mata in bata school tana gida domin ta kusa saukarta a islamiyyarsu ta Al-mannar kabala shima tsada ne dashi haka ammah ke biyawa hayfa ita ko super bata sakawa saidai k’ananan atamfofi burinsu kaf akan duk randa hayfa ta samu irin mijin da suke ta mata hidima domin samunsa toh a lokacin ne su kuma zasu fara cin tasu duniyar.

*******

*Yusuf Suleiman*

iyayensa fulanin sokoto ne wani gari waishi dogon-daji

Babansa yayi aikin gomnati a Nepa gidansu na unguwar kotu-road farin masallaci kano, sunan matarsa lauratu garinsu daya da matarsa yaransu biyar Yusuf, Ahmad, Qassim, Layla sai Rafiya

Yusuf kyakyawa ne babu laifi idanunsa kamar mai jin bacci hanci masha Allah dogo ne fari ne gaskiya saidai ba irin farin nn na turawa ko indiya ko Latino ba ah ah fari namu na Africa

Yusuf na d’an kamanni da sani danja saidai yafi sani danja tsawo sosai da tsawon hanci domin hancinsa kamar na turawa yake

Bayan babnsu yayi ritaya d’an kud’in da aka bashi gomanti ya sayi k’aramin gidansa dake kotu-road bayan shekara hud’u da ritaya ya rasu dalilin ciwon sugar inda bai bar komai ba sai gidansa da suke ciki
A lokacin Yusuf ya gama secondary yayi jamb sau biyar bai samu ba babu kud’i da k’yar dama yake daure yin jamb d’in domin babu kud’in yana ma ta tunani in ya samu jamb d’in yaya zaiyi ya yayi karatu ga nauyinsa ga na k’anninsa da innarsa

Ganin danginsu a dogon-daji suma ba wani k’arfi ke garesu ba duk talakawa ne dama babnsu Yusuf d’in ke taimaka musu da yana raye dukda shima ba wai kud’in ne dashi ba

Sunada babban abokin babansu na k’uriciya a Kaduna mai kud’i alhaji Sammani mai kobo gidansa na Aliyu turaki road unguwar rimi

Alhaji sammani matarsa ta shanye shi sosai ko y’an uwansa baya musu ihsani sai rabo ya rantse shi kuma Yusuf bama ya tab’a tanbayarsa komai saidai in ya shiga Kaduna yana gaisheshi kamar yadda babansa ya bar masa wasiyya

Ganin rayuwar ta musu k’arfi ga nauyi Allah ma ya taimakesu basu haya gashi shi ba karatu yayi mai zurfi ba ya rasa yadda zaiyi ya samu abinda zai rik’a d’aukar nauyin kansa da gidansu.

Yana zuwa kasuwar Kantin kwari yayi leburanci  abinda yake samu baifi suyi girki ba su cinye da k’yar yake iya biyawa k’aninsa karatu don ma innarsa na y’an sana’un mata na gida tana taimaka masa da wasu hidindimun gida

Ana haka Yusuf ya saba da yaron maigidansa inda yake dako yaron kuma akwai son harkar fita k’asar waje

Sosai suka saba da Yusuf dukda Yusuf baya da yawan magana haka Aliy ke jansa suyi ta fira har yake bashi labari da zai fita waje da shekara uku zai zama milloniya

Kallonsa Yusuf yayi yace da gaske?

Aliy yace k’warai acan fa kud’i sosai kamar banza kana aiki kana ka koma karatu ba nan ba ka wuni dako da yamma a baka #800 ko #100

d’an shiru Yusuf yayi kafin yace “toh ni ina naga kud’in fita wajen”?

Aliy ne yace kaci bashi mana…

Yusuf yace bashin 5k ma ta zama fitina mutum yayi wata yana nema bai samu ba bare kud’in zuwa waje

Shiru shima Aliy yayi yace ka bari zanyi tunanin mafita gobe mu had’u sai na fad’a maka

Haka suka yi sallama Yusuf cike da tunanin maganarsu da Aliy gaskiya maganar ta samu gurbi sosai a zuciyarsa

Haka koda ya dawo gida innarsu da suke kira da Inna Fulani ta masa tayin abinci yace ah ah ya wuce d’akinsa cike da tunanin maganarsa da Aliy haka ya kwana

da safe ma bai karya ba ya wuce kasuwa dukda yasan shi aliy sai ya tashi FCE yake zuwa kasuwa
Haka ranar yake ta dako babu kuzari yana so aliy ya iso yaji ina suka kwana
Koda Aliy ya iso kasuwa suka had’u da Yusuf yace masa “abokina ka sayar da gidanku mana”!

Zaro idanu Yusuf yayi yace “ay bazai yiwu ba inkai mamana da k’annina ina”?+

Aliy yace ka kama musu haya kana zuwa waje shekara zaka tara kud’in da zaka saya musu gida a sharada ma ko rijiyar zaki

Shiru Yusuf yayi yace to kasan wani wanda zaimin hanya?

Eh aliy yace akwai abokin abbamu aikinsa kenan nima abbamu bayaso ne wai sai bayan degree kuma nayi aure tukuna zan fita

Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace shikenan ka bari zanyi tunani sai na fad’a maka

Suka yi sallama!..

Yau kwana goma da maganar Yusuf da maganar yake kwana yake tashi inda a k’arshe ya yanke hukuncin bayar da gidansu jingina ya samu kud’in fita k’asar waje

Kuma bazai fad’awa innarsu wannan gangancin ba gara yayi komai a sirri har buk’atarsa ta biya
Da haka ya nemi aliy saidai bai gaya masa ainihin hukuncinsa saida sukaje gurin alhaji shamsu yusuf ya masa bayani inda aliy yasa baki yayita rok’on alhaji ya karb’a jinginar takardun

Alhaji shamsu ya amince aka kira dillalai suka duba information d’in gida darajarsa million 4 inda alhaji ya tanbayi Yusuf k’asar da yake son zuwa2
Yusuf yace Toronto Canada yana yawan ganin k’asar a labarai sabida yawan da musulmai suka yi a k’asar

Kallonsa alhaji yayi yace Toronto zaka kashe kusan millions5 komai da komai da visa 2yrs da masauki da d’an kud’in da dole mutum ke shiga k’asar waje dashi
Shiru Yusuf yayi alhaji ya kalleshi yace in haka ne babu damuwa zan maka komai kaidai ka nutsu ka biyani kud’ina in kaje bana fata mu rabu babu dad’i
Yusuf yace IA bazan baka kunya ba

Alhaji yace Allah yasa.

Amin suka ce shi da Aliy

Yusuf ya k’ara godiya nan alhaji yace kaje gobe zamu je mu fara shiri
Toh yace yayi godiya sosai suka yiwa alhaji sallama aliy nata taya Yusuf murna da mamakin irin kwarjinin da Yusuf yayiwa alhaji har ya amince taimakonsa babu sharad’i ko ribau

Koda Yusuf ya isa gida yayiwa innarsa bayani da cewa aiki ya samu daga ogansa zai turashi
Tayi murna sosai tasa masa albarka

Aka gama komai cikin 2wks cikin kud’in Yusuf ya rok’i alhaji 100k yayiwa innarsa cefane buhun shinkafa wake carton taliya couscous macaroni semovita manja man gyada maggi sannan ya bata saura kusan 35k a hannunta
K’anninsa da innarsa sunsha kuka domin tun bayan rasuwar babnsu haka suke ganin yusuf kamar babansu haka Yusuf ya wuce sai Canada!

A Canada Yusuf da k’yar ya samu aiki a wani swimming-pool  da nisa shima duk rashin maganarsa haka ya daure ya rok’i wani mok’ocinsa bak’in fata ya samo masa aikin da visarsa kasancewar alhaji yayi masa komai a matsayin driver wani kanti da alhaji ya sansu a Toronto don shiga k’asar yayi masa sauk’i.

sai train da yake biya da cefane da biyan gaz da electric da ruwa bills dai biyar yake biya banda gida.  
Ana biyansa babu laifi saidai k’alu bale na farko da ya fara ganewa shine kud’in yadda kake samunsu a gurin yawanci haka suke wucewa a gurin sai mutum ya jure sosai kafin ya tara

STORY CONTINUES BELOW
domin ogansa na pool ya fad’a masa dole ya rik’a shiga mai kyaw kada customers suganshi da k’azanta su gudu

A pool d’in ya had’u da wani matashi kamarsa d’an Kaduna Yasir inda Yasir sosai halin y’an fafan Kaduna gareshi sai ya fake da tsaftar da akace su rik’a yi yana wanka na fitina yayi ta hotuna a pool in oganninsu basu nan yana lodawa a istagram inda y’an mata y’an kwad’ayin kasar waje suna tsammani duk saurayin da ke zaune turai mai kud’i ne ko d’an mai kud’i su yita rububin binsa suna zaton mugun watayawa a keyi a wajen

Sannan ya saya waya da sim yana kiran innarsa da aliy inda Yasir ya nuna masa ya bud’e Facebook zaifi masa sauk’in kashe kud’in kiran gida sai ya rik’a wpp da Facebook da haka Yusuf ya amince Yasir ne ma ya bud’e masa accnt d’in

A haka ne rannan
ana wani party na wasu turawa su Yusuf da Yasir suna jira a gama suyi gyaran gurin bayan an ragu sosai Yasir ya rik’a musu selfi da Yusuf sunyi kyaw sosai barin yusuf da ya zama kamar wani half-cast sosai ya canza kamar ba shiba duk kuwa da bawai hutawa yake a wajen ba weather ce ta karb’eshi inda Yasir nan ya watsa social media har Aunty ammah ta gani ta zauce.  Bayan tayi asar ta d’an mik’e a gado cike da tunanin gaskiya yaron da ganinsa d’an wani hamshaki ne ko k’usan gomnati jiba yadda fatarsa a jik’e fresh fari ga kyaw da gani yana hutawa

Tab ina ay da wannan mugun jiji da kai na hayfa gara ni na gama shigar masa da ita a zimmar itace sai ya fad’a sosai tukuna na had’asu musha biki ga wajen nan ance kud’i kamar banza tab muma mu fara tara daloli
Murmushi tayi bari na duba k’arfe nawa ne a k’asar da yake yanzu
Nan ta duba ta gani hawa kusan hud’u tsakani ta haddace komai ta koma ta kwanta kafin larai mai aikinta tazo girkin dare sabida tsabar iskancin da ta koyawa hayfa bata aikin komai sai zuwa boko da islamiyya bokon ma  hayfa yafi na yaranta tsada haka islamiyya domin su ubansu ke biya ita kuwa hayfa aunty ammah da suwaiba ke mata komai barin ma ammah

Koda Yusuf ya kashe data tunani ya fad’a yau watansa16 a Toronto amma 800k kawai ya turawa alhaji shamsu sabida hidimar kansa domin har ciwon sanjin ruwa saida yayi baida insurance dole ya kashe kud’i sosai kwanansa biyar a asibiti
Sosai yake tunani tare da fatan Allah yasa kafin kud’in d’an gidan da yake zaune ya k’are ya biya alhaji koda 3M ne
Gidan ciki d’aya ne tak k’arami sosai sai room k’arami gado 6/4 k’arami d’an kanta ce zagaye a falon akayi masa kiching sai k’aramin toilet

Fata yake sosai kada Allah yasa kud’in gidan su k’are bai biya alhaji koda 3m ba in ba haka ba baisan ya zaiyi ba nauyin zai masa yawa ga visa ga cin yau da gobe ga gidansu tunda yazo sabida biyan alhaji sau 4 kawai ya tab’a daurewa ya tura musu d’an abu ya sani innarsa ko zasu mutu da yunwa ba zata tab’a tanbayarsa ba domin in suka yi waya cewa take lafiya
Wayarsa ya d’auka ya kunna data ko aliy ya hau suyi hira ya rage masa tunani

Mai aiki tazo amma ta tashi ta bata kud’i ta siyo nama da ogun ta musu tuwon shinkafa bayan tafiyarta amma ta bud’e data
Ga mamakin ta taga Yusuf online ta k’ara yi masa sallama
A dole ya ansa saidai baice komai ba
Tace ni sunana Hayfa ina kaduna
“OK” yace!..

Tace kai d’an kano ne ko?

Yusuf a tak’aice yace “eh”

Tsaki tayi tace iskanci yaran manyanan basu da mutunci jiba yadda yake magana kamar in yayi yayi asara
A haka dai aunty ammah tayi ta jan yusuf da fira
Saida ma ya kusa sauka aliy ya hau suka d’anyi fira ya sauka

Kamar da wasa yau aunty ammah da Yusuf 3wks ana chart sosai ammah ke shigar da kanta a zimmar hayfa

shima tun yana shareta har ya d’an saki jiki suna chart
inda yau suna chart yake tanbayarta
Zan iya ganin hotonki?

ganin hoton wasu yarane a dipin
Ammah tace yaran yayata ne! da sauri amma ta d’auko wayar hayfa dake gefenta ta kunna datar hayfa ta turo duk wasu hotunan hayfa wayara kafin ta turawa Yusuf duka

Wani irin harbawa zuciyar Yusuf tayi kallon farko da yayiwa hoton hayfa babu komai fuskarta sanye da uniform d’in islamiyyarsu ta almannar a k’ofar almannar d’in

Nan dai ya shagala kallon hotunan hayfa kusan 10mnts Aunty ammah jin shiru hankalinta ya tashi cewa shareta yayi ya saba ganin y’an mata fiye da hayfa a kasar waje

Cikin fargaba tace kaga pics?

“Eh” yace a tak’aice
domin har kokacin idanunsa na kan hotunan hayfa wasu a school wasu a islamiyya tayi kyaw har ta gaji sabida a d’akinta ammah har AC  ta saka mata

da k’yar suka k’arasa chart ya sauka inda hankalin ammah baya kwance domin a tsammanin ta Yusuf bai k’yasa hayfa ba
Tab tace ay kuwa kome zanyi wannan abin ya tabbata yaushe zanga samu na ga rashi irin wannan mazan basu da yawa a duniya

A Toronto Yusuf bayan sunyi sallama da ammah da yake tsammanin hayfa ce ya dad’e yana kallon hotunant a sosai zuciyarsa ke harbawa

Kamar da wasa yau 2wks sosai Yusuf ya kamu da mugun son hayfa da baisan bada ita yake chart ba

Saidai sanin matsayin sa da nauyin da ke kansa yasa yake kamewa domin yasan baya da kud’in aure a yanzu.

Yau 5wks sosai Yusuf ya fara sukurkucewa da son hayfa domin ya kan raba dare kallon hotunanta yana ayyana da zai ganta gabansa a zahiri

Wani irin so ne ya kamu dashi na ta mara iyaka wanda har abokin aikinsa Yasir ya gane yanada damuwa ya tanvayeshi

Ya fad’awa Yusuf amma a tak’aice kawai cewa ya had’u da wata yarinya ya kamu da sonta

Dariya Yasir yayi yace kai mai yayi maka zafi da soyayya yanzu?
Ya kamata ka sani sai kayi 8yrs baka je ko ina ba kana cikin kasarna kafin ka samu takardar zama d’an k’asarnan sannan yaushe ka shigo albashinka nawa ne?

Ka rufawa kanka asiri ka cireta a ranka domin yanzu za kaji ance ka fito ayi aure wai ma y’ar ina ce?

Yusuf a kasalance yace Kaduna!

Yasir yace tab ka gani kasan hidimar aure zuwa kawota k’asarnan saika kashe millions kana dasu a yanzu?

Yaci gaba nasan k’ila kaima kurb’a-kurb’a kayi kamar ni ka shigo k’asarnan ko?
Ka shigo k’asar nan don haka ka manta da ita ka maida hankalinka akan abinda ya kawo ka.+

Ay ni nan da ka ganni mata ba yanzu ba saidai 4fun amma babu ruwana da serious relationship!

Yasir ya kalli Yusuf yace muga pics d’in gimbiyar da ta tafi da imanin abokina cikin kwanaki kawai
nan Yusuf ya bud’e gallery ya mik’awa Yasir…

Zaro idanu Yasir yayi yace “Wow” gaskiya ta had’u kuma daga gani y’ar manya ce!

Yusuf ya kalleshi yace mai yasa kace haka?

Yasir yace ka manta ni d’an kaduna ne? Gidanmu na badarawa kwaru majalisa.

babu wani school d’in yaran masu kud’i da ban sani ba wannan uniform d’in nata na wani shegen school ne ana kiransa “Zamani college” yaran k’usoshin Kaduna ke zuwa haka wannan islamiyyar sunansa almannar shima sai yaran manya gaskiya yarinyar da gani y’ar wani isashen mai kud’i ne ko k’usan gomnati

Shiru Yusuf yayi yana tunani tab lallai aiki yake son saka kansa ina zai iya shi d’an waye
Dafa shi Yasir yayi yace wallahi ka rabu da ita yaran talakawa ma a Kaduna burinsu yafi k’arfin mutum bare yaran manya irin wannan yarinyar

da sharwawarin yasir da ganin shima nauyin da ke kansa Yusuf yayiwa kansa nasiha ya k’udiri aniyar yakice hayfa a zuciyarsa dukda yasan hakan abu ne mai wahala
Haka tun daga ranar in Aunty ammah ta masa magana baya cika ansawa wani lokacin ma ya sauka onlyn saidai a zuciyarsa kullum son hayfa k’aruwa yake
Ta b’angaren ammah ganin sabon salon Yusuf ta k’ara shiga damuwa cewa wato ya raina level d’in hayfa shiasa amma dole kuwa susan yadda za suyi ayi wannan auren da wannan tunani ta mik’e ta d’auko wayarta ta kira suwaiba suka yanke hukuncin kai Yusuf gurin malamai a tunzurashi ya auri hayfa.

Ta b’agaren hayfa sun gama zana waec da jamb inda suka sha party a school kamal ya kashe mata naira sosai d’inkuna takalma da sauransu ya mata alk’awarin in ta samu jamb da admission zai saya mata motar zuwa school dukda yasan burin hayfa shine tayi university d’inta a k’asar waje!1

Sosai tayi farin ciki kamar ta rungumeshi sannnan ya sanja mata waya zuwa Iphone11 yace ta had’a da techno k7  d’inta na zaman gida da Infinix d’in da ta d’auka office d’insa

Iskancin hayfa dayawa wai harda wayar zaman gida

Inda wani saurayinta da suka raina sosai ita da yayyunta driver ne na motar kamfanin NNPC shima ya bata iPhone7 da 20k  wai ta saya chocolate tukwicin gama waec d’inta
Inda ammah da suwaiba suka saida iPhone d’aya suka bazama malamai neman kan Yusuf ko ta halin k’ak’a

tsafi gaskiyar mai shi suka yi sa’ar samun wani malami da yayi musu aiki akan Yusuf zai amince aure kafin ma a masa magana
sannan ba zai farga ba sai bayan anyi auren an gama ranar da ya fara saduwa da matarsa maganin zai warware
Su ammah suka ce sun yadda suka biya aiki 100k akayi musu aiki suka taho gida cike da fatan samun nasara a aikin.

A Toronto Yusuf yau watansa18 inda ya biya alhaji 1.400!

Yau yana aiki a pool yaji kansa ya wani sara sosai ya ajiye rariyar tace d’aud’ar ta pool yaje ya zauna gefen kujerar shak’atawar gurin ya kama kansa da duka hannayensa, Shiru yayi idanunsa a lumshe kansa naci gaba da sara masa sannan zuciyarsa ta fara tuno masa hayfa sosai ga sonta da yaji ya k’aru masa kamar zuciyarsa zata b’allo k’irjinsa ta fito

STORY CONTINUES BELOW
Sosai ya dad’e a zaune kafin da k’yar ya mik’e ya k’arasa can baya wajen pool d’in yara ya rok’i Yasir ya k’arasa masa aikinsa zai koma gida baya jin dad’i
Yasir yace toh suka yi sallama ya hau train ya wuto gida

Sosai ya shagala a d’akinsa babu wani abu da yake tunani illa ya mallaki hayfa kuma ko mainene zai yi domin ta zama matarsa
Wayarsa ya d’auka ya jefa layin Alhaji shamsu

Bayan sun gaisa cikin dakiya ta namijin da yasan abind ya ke so Yusuf ya fara yiwa alhaji shamsu bayanin yana son yayi aure kuma alhaji shamsu ya k’ara masa wani bashin wajen d’aukar nauyin zuwan matarsa Toronto
Sosai alhaji shamsu ya girgiza da al’amarin saidai zuwa yanzu akwai fahimta sosai tsakaninsa da Yusuf sabida ya gano yaron jarumine kuma mai kishin kansa wata k’ila sha’awa ta fara damunsa ne kuma gara yayi auren da yaje ya fara neman mata a turai a k’arshe ya kwasowa kansa fitina
Ajiyar zuciya alhaji shamsu yayi yace babu komai Yusuf zan mata komai tazo ta same ka dake ma kunada gun zama nata bazai d’auki kudi kamar naka ba

Alhaji yace to ya za kayi ka samu kud’in hidimar aure?

Yusuf yace shima inaso a yimin komai na lefe a k’ara cikin lissafi wallahi alhaji zan biyaka daga farko har k’arshe.

Alhaji yayi shiru na mintoci a k’arshe yace shikenan Yusuf Allah yasa haka shine alkairi ya baku zaman lafiya!

“Amin” Yusuf yace su kayi sallama.

Bayan sun gama waya da alhaji shamsu ya jefa layin k’aninsa ya kaiwa innarsu nan itama ya mata bayanin buk’atarsa sam bata hanashi ba sabida babansa bai kai shekarunsa ba lokacin da suka yi aure
tace Allah yasa haka shine alkairi kuma tunda kace Kaduna iyayenta suke ka nema abokin abbanku yayi komai kaga danginmu sunyi nisa in muka shi go dasu cikin lamarin abin zai maka yawa kaga ga k’anninka kwanan kasan suka gama jarabawa suna jiran sakamako a zo a fara hidimar jami’a In Allah yasa sun samu

Toh Yusuf yace, inna kice Qassim ya turomin number Alhajin yanzu!

“Toh” tace  suka yi sallama.

Baifi minti biyar ba k’aninsa ya tura masa number alhaji sammani
yana ganin msg din ya bud’e ya jefa layin alhaji sammanin

Alhaji sammani mai kobo yayi mamaki da yaga number kasar waje duk da yana da abokan harka a waje amma wannan bak’on number ne da haka dai ya ansa.  Sallama Yusuf ya masa ya ansa cike da mamaki

Yusuf ya gaisheshi sannan yake fad’a masa ay 19mths kenan da ya shiga Canada alhaji sammani yayi mamaki sosai ina yaron ya samu kudin fita waje?

ko da yake matasan zamani babu abinda ba suyi idan zarar sunyi niyyar fita a ganinsu babu arziki a k’asarsu sai sun fita waje

Alhaji sammani na tunani yaji muryar Yusuf na masa bayanin buk’atarsa na son ya wakilci aurensa  kamar mahaifinsa

alhaji sammani yace masha Allah babu damuwa sai ka turo lambar iyayenta

Yusuf yace toh yayi masa godiya suka yi sallama!

Suna gama magana ya fad’a tunani bashida number hayfa ko ince Aunty ammah don haka dole ya kunna data ya gani ko tana online
Cikin sa’a itama ammah lokacin ta kunna sabida ba taje aiki ba

Nan ta gaishe shi kamar yadda ta saba
tace kwana dayawa!
yace ayyuka ne suka  yi yawa!

Murmushi tayi…

abin mamaki shine tun ranar da Aunty ammah taga pic d’in Yusuf har suka zama friend zuwa yau bata tab’a tanbayarsa shi waye ba ko d’an waye kawai information d’in da ta gani da Yasir ya saka masa na d’an kano yana zaune Toronto da hotunansa a pool shikenan abinda ta sani ta kuma hak’ik’ance d’an wani babban mai kud’i ne so no need ta tanbayeshi kar yaga kamar ta fiya kwad’ayi dama gashi ta lura yana da wulak’anci
STORY CONTINUES BELOW
Tsaki tayi duk yanzu in gama jure naka iskancin inzo in fara jure na hayfa da kamal ya gama hutsubeta da kananun kyawtutuka nasan saina had’a musu da farrak’u kafin su rabu dukda ba wai mugun son kamal d’in take ba

Gani tayi Yusuf yace ki bani number ki na kiraki yanzu

Mugun bugawa k’irjin ammah yayi ganin hayfa bata nan don haka tace masa yanzu ina tsakanin mutane amma ga number na ka kirani anjuma

Toh yace ta tura masa number hayfa
Ya sake ce mata na shirya inaso muyi aure k’arshen watan nan
Wani wawan tsalle ammah tayi don farin-ciki
Dake ammah duka shekarunta itama 33yrs tanada wayewa sosai ga boko haihuwa kuma girman Kaduna

Yusuf na jiran jin mai zata ce yaji shiru….

Yace ko yayi sauri?

“Ah “ah tace na Allah ya tabbatar mana da alakairi zan fad’awa mominmu anjuma
Amin yace kafin suka ci gaba da chart

Sunyi kusan 40mnts suna chart da hayfa ko ince aunty ammah kafin suka yi sallma ya sauka shima cike da farin-cikin zai mallaki macen farko da ta shanye masa zuciya

A b’angaren ammah suna gama chart da Yusuf ta zari hijabi tayi gidan yayarta suwaiba dake badarawa
Acan ta bawa suwaiba labarin aikin malam yaci Yusuf ya amince da aure
Nan suka fara shirin yadda zasu nema bashi suyi hidimar biki na kece raini ba zasu rik’a yawan tanbayan ango ba kada ya gano su tun da wuri

A gefe suka yanke hukuncin baza ma su yiwa hayfa magana ta rabu da kamal ba zasu koma gun malaminsu ya mantar da ita kamal

Daga gidan suwaiba suka wuce gidan malaminsu dake unguwar dosa layin baba marte suka fad’a masa yace babu damuwa saidai matsala d’aya
Suka kalleshi suka ce ta me?

Yace ko na mantar da ita da zarar mijin da zata aura ya sadu da ita ko wani asiri zai warware daga nasa har nata saidai mu k’ara yin wani
Shiru suka yi kafin suwaiba tace babu komai malam sai mu sake yi daga baya ay lokacin ta fara turo mana daloli
Murmushi ammah tayi tace haka ne Yaya! malam ayi kawai.

Nan malam yayiwa kamal da hayfa farrak’u suka taho cike da murnar mafarkinsu na shekara da shekaru na gab da zama gaskiya

A haka suka k’arasa gidansu suka labartawa goggonsu komai itama tayi murna sosai inda suka yanke hukuncin sayar da su friza da kujerun ammah da su shoglass d’inta da a lot kayanta na gida sannan suma suka bada jinginar takardun gidansu da babnsu ya shafe 25yrs yana adashin biyan gidan sabida gidan ne su kansu basu samu yin karatu mai zurfi ba
Nan suka duba kayan babansu da taimakon goggonsu suka ga takardun gidan da kud’in gidan yakai million biyu da rabi suka kai bankin da ammah ke ansar albashi na ja’iz bank suka nema rancen kud’i 2M suka samu sabida hidimar kayan garar hayfa so suke su mata komai biyar na kayan abinci tunda ba garar furniture za suyi mata ba

da yamma tare suka wuce gidan ammah yara sun dawo hayfa na dinning tana cin couscous da miyar vegetables da kayan ciki

Tana ganinsu ta d’an kalli aunty ammah cikin maganarta ta yanayin kamar bata son yi tace

Mominmu kun dawo? Murmushi suka yi mata duka suka ce eh kici abinci kizo d’aki muna jiranki ki tura su ayman waje suyi wasa

“Toh” tace suka wuce d’akin ammah

A Toronto Yusuf bai fad’awa Yasir maganar aurensa ba sabida baya son ya hanashi ko ya kashe masa gwiwa in matar tazo kawai ya ganta
Duk da shi kansa yana yawan tunanin yadda zai zauna da mata a wannan gidan nasa kamar rai gashi albashinsa bazai rik’a isarsu su biyu ba shi d’in ma ya ya k’are ga bashi daya k’aru masa kusan 10M ga ga ga haka yake ta tunanin matsaloninsa saidai abin mamaki inda shine yadda dukda matsalolin baya jin zai tab’a fasa yin auren komai zai faru kuwa

Bayan hayfa ta gama cin abinci sanye take da wata riga iya gwiwa dark pink ta kama gashinta tsakiyar kanta ta wuce d’aki inda yayyunta ke jiranta

Suwaiba ce ta kalleta tace hayfa kinsan yadda muka dage tun kina k’arama muke k’ok’ari kada ki shiga rayuwa kamar ta mu ko?

Girgiza kai kawai tayi….

suwaiba taci gaba akan idonki muke hana kanmu da yaranmu sabida mu miki gini mai kyaw da gobe zamu girba to Allah ya kawo mu lokacin

Yanzu haka yanzu Allah ya cika mana burinmu mominku ta samo miki irin mijin da mu ka dad’e muna fata kuma ya amince yana son aurenki a k’arshen watan nan ma

d’agowa hayfa tayi tana kallonsu da idanunta masu rikitarwa da alamar tsoron abinda suka fad’a

Suwaiba taci gaba kinga dama burinki kiyi university waje to kin samu sannan ki maida hankali munci bashi da ganganci dayawa sabida cikar burinmu da naki akan auren nan ki maida hankali da kin isa kiyi ta kwaso kud’i kina turowa mu biya basusuka mu sanjawa su abba gida itama mominku ta maida kayan d’akinta nan dai suka k’ara warwarewa hayfa zare da abawar hud’ubar da suka raine ta akai  na yadda aurenta zai kasance da Yusuf kamar kasuwanci zata ba aure ba

No.1 hausa novels, site all over the world with more than 5000 books uploaded, the site was found on 2014 by A/I/S
All our books are free, we do not charge for uploading , we upload novels, daily and over 400+ chapters montly.

About AIS

Check Also

KASAR WAJE CHAPTER 15 BY MARYAM DATTI

KASAR WAJE CHAPTER 15 BY MARYAM DATTI Www.bankinhausanovels.com.ng  Tana saka d’an k’aramin d’an kunnenta mai …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *