K’ADDARA CE CHAPTER 8 BY MAMAN NUSAIBA

K’ADDARA CE CHAPTER 8 BY MAMAN NUSAIBA

Www.bankinhausanovels.com.ng 

 Inda  su Iman suke Imam ya soma k’okarin  nufa, Sultan  ne Ya ankara  da barin Imam  gurin da sauri  ya janyo shi da karfi  yana  fad’in. Kai Malam! Ina zakaje ne haka? Naga kuma kana  nufar  cen  inda Y’an Mata suka taru, ko  kasan  wata a cikin  suke? 

Imam  cikin  jin  haushi  ya tsaya  Ya ce.” To ina ruwan ka ! Ai nace  maka saina rama  abun  da waccen  marassa  tarbiyar  tayi min, shine Yanzu  na ganta zanje na rama ka  hanani.

Sultan Ya ce.” Wai kai Imam  meye  yake damun  kanka ne? Ayi Mutum  sai bak’ar  zuciya haba da Allah! To Wallahi  inma kaje  ka taro  Aljannun wacce  Yarinyar  ni dai babu  ruwana, kana gani  dai ranar  yadda  ta maka  saida  wani  yazo  ya kwace ka, shine dan b’atan basira  kake  neman komawa ko? To kazo ma Yanzun nan Daddy ya kira  Ya ce.” Mu koma Gida  tinda  mun daura kayan  da mukazo siya,   kuma kaga Alhaji Aliyu  mai atamfa  d’in  ma baizo  ba! Dama au Sallama  ce mukazo yi  masa  to tinda baya  nan mu koma muje mu  had’a  kayan  mu mutafi  Gida kana jina dai ko! 

Imam  ko  k’ala  baice  ba ya juya suka koma ,motar  su suka  hau  suka koma hôtel d’in  da suka kama,  babu  b’ata  lokaci  suka had’a  komai  nasu  suka  fito  zuwa Airport,  basufi minti  goma ba jirgin  _TEEGO_ ya sauka , Sultan shiya shiga musu da kayan su ciki saboda  Imam  ya had’e  girar sama data  k’asa , shi  ala dole fushi yakewa  Sultan  daya hana shi yaci  mutumcin  Iman yaga waye Uban ta a cikin  garin  Kwatano, shiyasa  da sukazo yaki  kulashi yana ta had’e rai…..

Sultan  Ya dawo  inda yake  Ya ce.” Malam  saika tashi mutafi  ko  in kuma anan  zaka  zauna saika fad’a min naji!  Idan kuma har Yanzu  fushin ne kake yi to koma cen kasuwar  ka yi duk Abun da kakeso , Mutum sai shegen  wulak’anta  Talaka  dan kawai  ka fishi  arziki,  to kayi  duk Abun kaga ya dace rayuwa ce nidai  iya bakin k’okari  na ina yi  a kanka Allah ya gani,  dan Allah  Aboki kake sawa zuciyar ka ruwan  sanyi! Yanzu  kai ba abun kunya  bane kake  fad’a  da Mace? Kuma Macen ma Yarinya Y’ar k’arama wadda  bata  fi shekara  15 zuws 16! To ka tashi  mutafi nace in kuma ba haka ba in kira Daddy na fad’a mishi komai shashasha kawai  mai banzar zuciya. Sultan  Ya k’arasa maganar yana  k’okarin  fiddo  wayar shi ya kira Daddy…..

Wani  Tuk’uK’in bakin  ciki ne ya rufe Imam  jin  Yace” mishi  mai banzar  zuciya , kallon  shi Yayi  Ya ce.” Ni kake cewa  mai banzar zuciya Sultan? Akan Y’ar Talakawa mai talla a titi marar  tarbiya! Shine ka Zab’e ta a kaina ko? To Wallahi  nayi alk’awari koba Yanzu  ba duk ranar  dana sake haduwa da ita saina kakkarya ta, saina mata rashin mutumcin dako  wani akace ta zaga bazata  tsaya a wajan ba, badai  na gane fuskar su ba har ita dayar  tinda a dalilin ta sobar ta taci Mutumci na , dukkan su saina  nuna musu  ruwa ba sa’an kwando bane Wallahi!  Saina wulak’anta su naga waye  Uban su dame suke tak’ama ne da har suka min  haka! Yana  fad’in  haka ya tashi  fuuu ya bar wajan  ya shiga cikin  jirgin…..

Sultan  girgiza kai kawai  Yayi, yana mamakin  Zuciya  irin  ta Imam  Ya ce.” Allah  ya shirye ka Imam  Allah yasa  ka gane Annabi  ( S.A.W) ya faku, kai inba hauka bama  meye  da wani b’ata rai a wannan  Abun? Naga dai marin mata Y’ar Uwa  kayi ta rama mata,  to meye à ciki? Insha Allah  wata  rana  sai wannan  Yaran daka  ke son wulak’anta wa sun taimake ka.. Wayar shi ya maida aljihu ya shiga ciki  shima, babu  jimawa jirgin su ya d’aga zuwa  K’asa _TEEGO_……

A ban garan  su Iman kuwa tinda  ta shak’i wata  Budurwa  suka kama  dambe, da k’yar  aka  rabu su shima sai da wannan  Tsohon  ya mata magana  tukun ta saki  ta. Kallon ta Iman Tayi  Ta ce.”   Wallahi kinci darajar  Baba  Tsoho  da sai  na koya miki  hankali  a Kasuwar  nan! Kuma ki  fita harka ta inba haka ba zakiga yadda  zanyi wajijin  kura  dake  a kasuwar nan! Ni bana shiga harkar  Mutum  amma  inka shiga gonata  to saina keta maka rigar  Mutumci, Jaka aladiya  jahila kawai wandda bata san mahimmancin kanta ba bare  Addinin  ta .. Iman  sai huci  take tana  idon  ta Yayi jajur saboda  masifa nacin  ranta, dama  neman  soban yi take sai ga shi wannan  Budurwar  ta shiga gonar ta.. …..

 Sultana  kamar  zatayi kuka  saboda wannan  karan  ma a dalilin  tane Iman  take  hawa kamar  fulawa  Ta ce.” Haba Iman kike hak’uri  da Mutune mana! Ki  k’yale  ta  kawai  aiko Yanzu  jikin  ta ya gaya mata keba sobar yinta bace kinji! Bana so kina fad’an nan a kasuwa Wallahi…..

Iman  Ta  wugawa Sultana  Harara  Ta juya ta kalli  sobar fad’an  nata Ta ce.” Ke! Daga rana irin  ta yau inna sake ganin ki a wajan  mu saina tsone wannan  idon  naki da kika zubamin su! To Wallahi  ahir  d’inki  nafi karfin ki  koda wasa kika kuskura  naji labarin kin zauna anan  zakiga mai zan miki! Marar  kunya gyara  a koma makaranta , wannan  kan naki  ya d’auki  Hadisi da K’awa’idi  da Alkur’ani,  sauran  littatafan  Addini  dan na kula baki da ilimin su……..

Iman  Ta kuma cewa  kallini da kyau ta juya ta zagata ta tukun taci gaba da cewa. Dan kin ganmu  muna talla  bashi ke nuni  da cewa mu  bamu da kamun kai ba, ko bamu da Ilimin Addini kamar ke ba, to wannan  kan da kike ganin shi  da bakin  nan, Iman  Ta nuna kanta da hannu da bakin Ta ce.” Cike yake da Hadisai  da Surorin  Alkur’ani mai girma dan Uban  Babarki ! To ki fice mana anan ko na karya  miki  hannu. Tana fad’in haka ta nufeta……

Da sauri  Sultana  Ta janyo ta ta rumgume  ta tana fashewa  da kuka Ta ce.” Yanzu ke Iman  ban isa na fad’a miki magana kiji ba? Nace ki k’yale ta amma kin ki  sai masifa kike meye haka? 

Hankalin Iman ne ya tashi  ganin  Sultana  na kuka, itama  rumgume ta Tayi  tana fad’in.  Kiyi Hak’uri  Sultana!   Bazan iya jure naga ana cin miki  Mutumci nayi shuru ba , Shikenan ki dena kukan na dena Wallahi  bana son ganin kukan ki Y’ar Uwa ta! 

Baba Tsoho ne yake Kallon su cike da burgewa Ya ce.” Kai iko  sai mai duka  wannan  shak’uwa  taku ko  ciki  d’aya kuka fito ai sai haka. Da hannu Yayi  Sultana alama da suzo, kama  hanun  Iman  Ta yi  suka k’araso wajan  Baba Tsoho. …..

Kallon su Yayi  Ya ce.” Wai to meye ma ya gama ku da Indo ne?

Sultana ce ta soma magana kamar haka: 

Baba  Indo ce tazo  inda muke zaune muna jin wa’azin  da Malaman Sunnah sukayi  kamayya wanda akayi shi a garin  Kaduna,  Wani  Malami Yace.” Ace kana Musulmi  amma  baka iya karanta  Fatiha a dai-dai  ba ai kaci  baya, ko  kuma kana Musulmi  kake tsallake Salla kamar  kayi Azuhar  bazayi La’asar ba zakayi  Isha’i amma  baza kayi Salla Asuba ba, ko kuma kake aikata aikin  sab’on Allah  kana sane amma  ka kasa tuba, ko  kake aikata zina  alhalin kasan  haramun ne kuma kaki  yin  taubatan nasuha, ko kuma son zuciya ya maka yawa, duk masu irin  wannan  halayen  indai basu tuba ba suka cikin  masifa da bala’i musamman  ma wanda basa Salla ko basa cika Salla, Duk wannan  lefukan  dana zanau  idan ka tuba Allah  zai yafe maka amma  fa indai Allah kana Musulmi baka  Salla to kana cikin  tashin  hankali  saima ka shiga k’abarin ka…

Sai muka kunna d’ayan  wa’azin  sai Malamin yake magana  akan  tarbiya kamar haka:

Ya ce.” Indai ka kuskura ka auri Mace  marar  tarbiya to kana cikin  jarabawa, ko ka kake mu’amala da wanda bashi da tarbiya  to in baka yi sanadin shiriyar ba to shi zai lalata maka taka  tarbiyar, Y’an mata  masu  zuwa Makaranta, ko masu  talla ko masu  zuwa aiki office aiki, ku kula da tarbiyar  da Iyayen ku suka baku  ,kada  son  kudi ya kaiku ya baro,  yanzu Duniya ta lalace Yanzu saita biya Saurayi  ya lalata mata rayuwa  saboda taki  maida hankali tayi  karatu sai jarabawa  tazo taje Tace” ya mata shi kuma ya nemi saiyayi  zina da ita tukun zai mata , ita kuma dake mahaukaciya ce saita yarda, ko  Y’an Mata masu  talla  Mutum zaike miki  juye  ke kuma kina jin dad’i, idan yaga kina yarda ki zauna kusa dashi zai soma nuna miki  kud’i idan ke mai son kud’i ce saiki  yarda  shi kuma Yayi zina dake ya lalata miki  tarbiya,  sai kuma daga baya kizo kina cewa sharrin  shedan ne, to dan haka  kuke rike mutumcin ku , da Mazan da Matan…….

Sultana Ta ce.” Baba  wannan  shine fa da mika gama ji sai nace , mu dama muna ta kame kanmu  Insha Allah  baza mu  bawa iyayen mu kunya ba,  Allah ma ya raba da zuwa d’akin  Saurayi ko masu yin juye, shine kafin na k’arasa maganar Indo ta soma cewa.

Ai muna ce mata  tana zuwa d’akin Saurayin ta da yake mata juye, nidai bance mata komai ba lokacin Iman tazo kawo maka Abinci  ta dawo ne t’a soma zagina  tana cewa ai dama da ita muke , shiyasa  muka kunna  Wa’azin dan muci mata mutumci  ne ai , shine fa Iman  ranta ya b’aci ganin ban rama  ba tana  zagina da fad’a min magana, sai ta tashi  taci kwalar ta suka kama fad’a  wannan shine fa ya had’a su fad’a, kuma  da gasken  zuwa take d’akin  Saurayin  ta, sau nawa ana kamasu, Sallar ma bata cikawa , idan munci muje muyi Salla sai tace wai  ai ba kab’ari d’aya  za’a binne muba, ita in taje Gida  da had’a suka sai tayi gobe…..

Baba Tsoho yaja numfashi  Ya ce.” Kuyi hak’uri! ku rabu da ita , indai rayuwa ce Duniya zata koya mata Hankali,  Yanzu kuje ku tafi Gida tinda kun siyar  Abincin……

Iman  Ta  mike tana  sauke ajiyar zuciya akai-akai Tace.” Baba  ka fad’a mata karta sake shiga harkar mu nida Y’ar Uwa ta, inba haka ba zan bata mamaki! 

Murmishi  Baba Tsoho Yayi  Ya ce.” Insha Allah  zab gargad’e ta kuje Gida sai gobe kuma in muna da rabon ganin ta. To sukace nan suka koma wajan  kayansu, t’attrape komai sukayi  suka fita a kasuwar zuwa bakin hanyar neman Abun haka.

Suna nan tsaye  Abdul Malik  yazo  ya tsaya  Ya ce.” Kuzo n’a kaiku  Gida  Sultana.

Hararar shi Iman  tayi  tana cuno baki  kama  sai wani  bud’e kofar hanci take. Dariya  Yayi  Ya ce.” To duk ni akewa haka My heart  ? 

Sultana itama murmishi Tayi  ganin yadda  Iman  tayi  zatayi magana  Iman taja ya ki ta tura ta motar  wanda ta tsaida, kallon Direban  Tayi  Ta ce.” Malam  kama muje. To kawai yace” mata yaja suka bar Abdul Malik  maki a sake yana mamakin  hali irin  na Iman, motar ya juya ya bisu a baya ……

Idan kin karanta ki daure kiyi comment sister ??

_Taku har kullin Maman Nusaiba ce_

About AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *