K’ADDARA CE CHAPTER 7 BY MAMAN NUSAIBA

K’ADDARA CE CHAPTER 7 BY MAMAN NUSAIBA

Www.bankinhausanovels.com.ng 

_Nomal N300 ne_

_Vip N 500 ne post sau biyu kullin_

_*Domin k’arin bayani ku tintib’eni ta WhatsApp number na + 966599791573*_

??

*JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION?*

_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa}_

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

              

          *⚜️©J.A.W??️*

بسم الله الرحمن الرحيم 

Hanan  ji  tayi  kamar ta saki  zawo  saboda  tsananin tsoro  daya  cika  mata  zuciya dama  gangar jiki, jin  ya kuma had’a ta da jikin shi  sai ta saddakar  yau ai kawai  Yaya Faris  Fad’e zai mata.. Shi  kuma gogan  yana  kallon ta bako  k’iftawa so yake yaga iya gudun  ruwan ta da k’arfin ta, shi yasa ya matse ta kamar  wata  Y’ar shi, Hannun shi ya cire daga  bakin  ta daya  rufe mata…

Da  sauri  Hanan  Ta matso  hawaye Ta ce.” Yaya  Faris  please  ka cikani!  Wallahi  kila ka karya  min  kafad’a wannan  matsa  haka  kamar  ka samu soban  wasan ka! To nidai ka sakeni ko kuma Anty na zuwa nace mata  ka rumgume ni  kamar  wata  Baby  Jaririya. Ta k’arshe maganar  tana  turo mishi bakin ta…..

Murmishi  Yayi  yana binta da namujiya  , ji  yake kamar  ya maida ta  ciki  dan so da k’aunar da yake  mata, sai dai ita tsoron  shi ma takeyi,  baisan yaushe  zata  dena jin  tsoron shi ba a matsayin shi na Mijin  da zata  aura ba. Ajiyar zuciya  ya sauke  Ya ce.” To shikenan  naji  zan sakeki  amma  sai kin min  alk’awarin  bazaki  k’ara jin  tsoro na ba! Idan  kuma naga tsoron  na nan to Wallahi  gobe sai naje wajan  Baba ya daura  mana  aure in ta tsoro kuma, wai ma meye à jikina  wanda in kika ganni  kike tsoro na? Haba Hanny  bana son kina jin  tsorona  nifa Mijin  kine Insha Allah!

Kara  turo baki Tayi  tana  k’unk’unen magana Ta ce.” Kaji wani  sabon  salo  gemu  a kafad’a! Tab ikon Allah  ikon  gaske  wai kiran salla da  usir kut! Wai hadda cewa nifa Mijin  ki ne, kaji  neman guri a wajan  Yaya Faris hmm, to bazaa dena jin  tsoron  naka ba! Ni ai ba Matar ka bace  da har kake rumgume ni saika bari inka aure ni  kake  tab’a ni ai ko! To saina dena zuwa Gidan naku ma ehee….

Duk maganar  da take  bata san  tana  fitowa  fili  ba, shi kam Faris  tagumi  Yayi  yana  kallon yadda bakin  yake mutsowa  in tana  magana,  dariya sosai  yake yi ciki²  saboda  karta  gane  yaji,  saida ta gama  ne Ya ce.” Kai lalle Yarinyar  nan ni  kike fad’awa  magana ko? To kin  jawa kanki  gobe saina je wajan  Baba  an saka  bikin mu nan da wata  d’aya,  badai  kina cemin  bazata dena ba ko? 

Da sauri  ta rufe bakin  ta tana  zare ido jin  Abin da yake  fad’a  Ta ce.” Waiyo Allah  ni  Yaya  dan Allah kayi hak’uri  karka je! Nifa gaskiya  bazanyi  auren  cin  amana ba, haka kawai  ka wani  mak’ale  min, nidai  karka je kaji! 

Mik’ar da ita Yayi  ya zaunar  da ita a gefen shi,  ya  had’e rai Ya ce.” Ai baki isa  ba Yarinya tinda kika fad’i  haka dole gobe a saka  ranar  bikin  mu  nan da wata  d’aya, badai kin renani  ba to zanyi maganin wannan  bakin naki da kullin sai kin  turo min shi in muna magana! Yana  gama Fad’ar  haka  ya mike  tsaye  zai bar falon……

Da sauri  ta rike k’afar shi tana  kuka  Ta ce.” Haba  Yaya  nifa da wasa nake maka fa! Sai kace baka san wasa ba! Wallahi  naji  zan aure ka amma  karka ce wannan  shekarar  , nasan  in  kaje Baba  zai amince  tinda ya riga daya  baka ni, to meye  na gaggawa kuam? Ka bari sai sabuwar shekara kaji! Wallahi  bana son had’a  ido da Anty  gani  nake kamar zata gane ka rumgume ni…..

Danne dariyar  shi Yayi  yana  fad’in.  Tab  ban san  wannan  zancen  ba kuma zuwa sai naje gobe zan tura  Kawuna wajan  Baba,  gyarama ki  sakeni  naje na kira shi a waya  na fad’a mishi  yaje a  saka. Ranar  bikin mu gobe, dan haka kin  kusa dawowa Gidan nan na har abada…….

Hannu ta daura  akai  ta saki  wani  marayan kuka  sai Kallon  shi take, shi kuma ya daure fuska  dan kar taga ko  wasa  yake mata,  cikin kuka  Ta ce.” Wai da gaske  zuwa zakayi  Yaya? Tana  k’iftace²  kamar  wani sabon  kamu……

Hannun ta ya cire  daga rik’on  datawa k’afar shi  Yayi  saurin  barin falon ya shiga d’akin  Ilham  ya kulle duk da yasan bazata  biyoshi ba…..

Hanan  kamar  zatayi  hauka  ganin  da gaske fa Yayan  nata yake  nan da wata  d’aya  ya zama  Mijin ta,  mik’ewa  tayi  taje da d’auki Abincin  dake kula d’aya  ta saka  hijab d’in ta  ta fita daga falon. Tafiya  take tana  kuka  saboda  tsoro da fargaba daya cika mata zuciya , inta tuna  maganar  auren nan, da ta kusa isa Gida  sai ta share  hawayen ta  ta biya  wani  shago  ta siyo  musu kayan  miya da mai , tana  zuwa Gida  bata bari Baba  ya gane ba ta shige  d’aki….

Tana  nan  zaune  su  Saudat  suka shigo  suna kiran  ta, fitowa Tayi tana  musu murmishin  yak’e  Ta ce” kun dawo !  Sannunku..

A tare suka  ce eh Anty  mun dawo  kuma yunwa muke ji. Hanan ta kawo su wajan  Baba  suka zauna  ta zuba musu  Abincin  gaba daya  ta tura musu a gaba, sai da sukaci suka koshi  sukayi  saura, sai Tace” musu  suje su wanke hannun su su  kwanta su huta kafin lokacin  zuwa Islamiyya Yayi” to suka ce suna shigewa  d’akin…….

Ajiyar zuciya ta sauke ganin  Baba  ma ya koma bacci  sauran  Abincin  ta had’a  a kwano  daya  ta gyara  zaman ta ta soma ci, tana  gamawa ta dauke kwanukan  ta wanke  tukun  itama  ta dawo  d’akin  ta kwanta a kusan  su Saudat,  cike da tausayin  Yaran  ganin  za’a  rabasu………

Washe Gari  kamar yadda  Faris  Yacewa Hanan  haka kuwa ta gani,  Kawun shi ne yazo wajan  Baba  aka  saka  ranar  bikin  wata  d’aya  kamar  yadda  Faris  ya buk’ata,  ai kuwa ranar  kwana  tayi  batayi  bacci  ba tana  kuka, har kusan Asuba  kafin  bacci  Yayi  gaba  da ita…….

************************

A b’an garen Abdul Malik  yana  tafiya  Gida ya nufa jiki  a sanyaye  yake driving  duk  ya rasa  nutsuwar shi,  sai numfashi  yake sauke  wa akai-akai, Unguwar _Quartier Jacque_ ya nufa    iya  damuwa yau yana  cikin  ta, wani  Babban get  ya nufa back hon Yayi  aka  walgale  mishi  kofa ya shiga ciki, yana gama packing  ya fito  daga motar  ya nufi  ciki. 

Da  Sallama  ya shi kutsa kanshi  cikin  tafkaken  falon  , wata  Hamshak’iyar  Hajiya  n’a gani  zaune  taci ado,  kana ganin ta kasan  hutu da jin  dad’i sun zauna  mata, Doguwa ce mai jiki  dai-dai misali, wankan  tarwad’a ce gata kyakyawar  gaske  , kana ganin ta zaka san ita ce Mahaifiyar Abdul Malik,  gefen ta  wata  Budurwa ce tana kallon TV  wadda bazata  wuce shekara  17 ba da haihuwa.. 

Amsa mishi  Sallama  Tayi  Tana fad’in.  A a My  Son  lafiya na ganka jiki a sanyaye? Ko  duk gajiyar ce?

Abdul Malik  kamar  zaiyi kuka  yakeji  ganin  k’anwar shi saiya daure  ya aro jarumta ya daura  murmishin  yak’e  a kan  fuskar shi Ya ce.” sannu da hutawa Mommy  bafa komai kawai  na gaji ne. Kallon  k’awar shi Yayi  Ya ce.” Ke tashi fice mana à nan ! 

Shuru  Tayi  kamar bada ita yake ba sai da ya kuma mata wata  tsawar  tukun  ta  mik’e tana  fad’in. Kai  Yaya  kai bakaso in zaka bawa Mommy  labari  naji, to ai ba wani  zan fad’a wa ba please  kayi hak’uri  kaji  Yaya!

D’ago da idon  shi Yayi  Ya ce.” Asma ! Meyasa kika renani wai? Zaki fice ko saina make ki  nan banza  shashasha kawai…

Da gudu  tabar  falon  tana  saka  kuka  saboda  film d’in  da take  kallo yazo wajan  da takeso..

Mommy  Ta ce.” Ina jinka ya akayi? 

Sunkuyar  da kai Abdul Malik  Yayi  yana  jin  kamar  zuciyar shi zata  fasa  kirjin  shi ta fito saboda da damuwa, da k’yar  ya iya fad’in.  Mommy  Tace” wai bata sona saboda  ni  D’an  masu  kud’i ne, please Mommy  ki  taimake ni! Wallahi inban auri  Iman  ba zan iya rasa  hankali na…

Cike da tashin hankali  Mommy  Tace.”wacece  Iman  kuma? Kuma waye  Maihaifin ta da har ta dubi  idon ka Tace” bata sonka? 

Abdul Malik Ya bata labarin  Iman  da duk abubuwan  da sukayi a baya har zuwa na yau data ce bata son shi saboda suna da kud’i…..

Ajiyar zuciya ta sauke Ta ce.” Lalle Yarinyar  nan ita wani  irin  tsattsauran  ra’ayi ne gareta da har bata son mai kudi? In  banda  shirme irin  nata ina taji ana  irin  haka, to kayi hak’uri  zata yarda ta aure ka kaji! Bana son ganin ka cikin  damuwa,  ku biyu  kad’ai Allah ya bamu  banaso wani abu ya sameku,  kayi hak’uri  zatq soka kaji! 

Wani  sanyi  Yaji  saiya  matsa kusan Mommyn  nashi  ya kwanta a cinyar ta yana Jan numfashi,  ita kuma tana shafa kanshi  suka ci gaba da hira…..

************************

Hanan ce zaune ita da Ilham  tazo Gidan su ganin kwana  biyu  bata zoba, sai da tazo ta ganta kwance ba lafiya, cikin  tashin hankali  take tambayar ta mai yasa meta ne? Tace” zazzab’i ne magani ta bata tasha  tukun ta taimaka mata ta zauna  daga kwanciyar  datayi….

Ilham  Ta ce.” Hanan  dan Allah  ki  dena sakawa kanki  damuwa akan  wannan  lamarin! _K’ADDARA CE_ fa tasa  auren nan zai tabbata ! To ki  kwantar da hankalin ki kinji ko! 

Ajiyar zuciya  ta sauke  Ta ce.” To Anty  zan dena amma  Wallahi  ni kunyar ki nake ji” wannan  Abun kamar  a mafarki  nake ganin shi..

Karki  damu  K’anwata  ai komai  da kika gani a rayuwa ya sameka  yo _K’ADDARA CE_  Dan haka ki  dena tunanin komai K’anwata! To Hanan  Ta ce”  Amma  duk ranta babu  dad’i,  haka sukaci  gaba da hira har yamma tukun  Ilham  Ta mata Sallama ta tafi  Gida. …..

Washe Gari  Faris  yazo  ganin  ta, wajan  Baba ya fara zuwa  suka gaisa  tukun  Baba  Yace” mishi Hanan na d’aki,  to Yace” san nan ya nufi  d’akin  da Sallama. …

D’ago da fararen idanun ta Tayi  tana amsa  mishi  Sallamar. K’araso wa Yayi  inda take Zau ne  shima ya zauna  yana binta kallo ganin  yadda  ta  rame  sosai a hankali  Ya ce.” Hanny  ya jikin  ?

K’asa dakai  Tayi  tana wasa  Y’an yatsunta, amsa mishi  gaisuwar daga haka bata sake cewa komai ba. 

Sake matsowa  Yayi  Ita ma ta matsa  gefe tana banka mishi  harara,  dariya  Yayi  Ya ce.” Ki  tsaya  mana zanji  ya jikin  naki  ne fa koda zazzab’i ko babu..

Hanan ta  turo baki gaba  tana  murza  ido  ita ala dole tana hawaye,  Ta ce.” Wai kai Yaya  meye  yasa  dole saika taba jikina ne? Nifa bana jin dad’in  hakan  ka dena ba kyau,  ka bari  in ka aureni  komai ma sai kayi.. 

Ihmm Faris Yace” yana mata wani  shu’umin  kallon  mai narkar  da zuciyar wanda akewa,  kyale ta Yayi  danya  lura  Yarinyar  zata koma Mafad’aciyar ba arziki,  sai ya jata da hira har ta saki  jikin  ta   ta ringa bashi  labari  masu  dad’i,  shi  kuma yana  murmishi  yana bata amsa inta tambaye shi.. ….

*************************

Su Sultan ne suka shigo  Kasuwar  Imam  fuskar nan kamar  Soja zaije  filin  daga, sun nufi  wani  rumfa zasu zauna  Imam  ya juya  kamar  daga  sama  yaga  Imam ta shak’i  wata  katuwar  mata tana  surfa  ruwan  masifa, murmishin mugunta  Yayi  Yace” yar  Mitsiyata yau saina rama Abun da kika min inba n….

Idan kin karanta ki daure kiyi comment sister ??

_Taku har kullin ( Maman Nusaiba ce)_

About AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *