K’ADDARA CE CHAPTER 6 BY MAMAN NUSAIBA

K’ADDARA CE CHAPTER 6 BY MAMAN NUSAIBA 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Iman  na shiga  ciki  kafin ta k’arasa  ta tsaya a bakin  k’ofar Gidan ta fashe  da  kuka, Cikin  kuka ta soma magana kamar haka: Kayi hak’uri Abdul Malik bazan  iya  Auren  mai kud’i ba, gashi  ka dasa  min Soyayyar ka a raina , ni kuma bani da ra’ayin auren irin ku. Saina taci kuka mai isar ta tukun  ta shiga ciki, babu  wanda tawa magana ta shige  d’aki.  Sultana  ce ta bita  ciki  ganin  yadda  hawaye ya jik’a mata fuska…

A Zau ne ta sameta  tana  kallon gefe  d’aya , zama Tayi a kusan ta Ta ce.” Iman  banji  dad’in  Abun da kika fad’awa  Abdul ba  gaskiya! Kina tunanin  Abdul Malik zai cutar  dakene? Ko kina tunanin  zai ke wulak’anta kine? Da ace  zaiyi  haka da bazai ce yana son  Y’ar Talakawa ba, sai kuma gashi  Yace” yana sonki da aure,  Iman wai wannan  wani irin  ra’ayi ne gareki? Ko  kanki  ya soma kuncewa ne? 

Kallon ta Iman  Tayi  Ta ce.” Ki  fad’i duk Abun dake ranki, amma ni bazan  auri  mai kud’i ba,  kema kinsan tin muna Yara  nake da wannan  ra’ayin,  ke kanki  kisan  masu kud’i in suka auri  D’iyan  Talakawa  sai suke wulak’anta su, ni kuma kinsan  bana daukar  reni….

Sultana Ta ce.” To shikenan  ai amma  baki yiwa masu kud’i adalci ba Iman, tinda har kika musu kud’in goro, ai ba duka aka taru aka zama daya ba, akwai  na gari a cikin su, dan Allah  ki  daure ki amshi  Soyayyar shi! Idan  kika mishi  haka  kin  zama  marar adalci, kuma kinga Abdul Malik da gaskiya yake sonki ba da wata  manufa ba! Amma kiyi tunani akan  magana ta ni zan koma Gida, Abincin mu ma shiya  siyawa Y’an tsaron  shagon  Daddyn shi…..

Ita dai Iman  shuru  Tayi  bata k’ala ba, sai  bin Sultana da ido  take ganin  tana  had’e rai, tana ganin fitar ta ta koma gado ta kwanta  , sosai  take jin  zuciyar ta na mata wani  irin  rad’adi  da zafi, taya  zata iya rabuwa da Abdul Malik  a lokaci d’aya? Alhalin  zuciyar ta Ta dad’e ta kamuwa da k’aunar shi. Haka  tayi  ta tunani ban katai  har bacci Yayi gaba  da ita….

**************************

B’an garan su  Sultan,  tinda  suka  bar Kasuwar  ran  Imam  a matuk’ar  b’ace  har  suka nufi  Masaukin  su, _Royal Hotel_ nan naga sun nufa ,sun packing  ko  motar  Sultan bai kashe ba Imam  ya futo  fuuu…..

Shi dai  Sultan da kallo ya bishi  san nan  Yayi  dariya,  fitowa  Yayi  ya  nufi  ciki,  da mai lamba 25 suka shiga,  a kan gado  Imam  ya zauna sai cin  magani  yake yana huci kamar  wani  kumurcin maciji.. Sultan Ya ce.” Haba  Imam  wai duk saboda  da wannan  Yarinyar ne kake wannan  hawan kamar  an fulawar  yin banke? To kayi hak’uri!  Bakaga  Yarinyar  ma bata da lafiya,  kai da gani  wannan  mai irin  sunan  naka  Aljannu gareta…

Kamar  Imam  bazai yi magana  sai cen yaja  numfashi  tukun  ya motsa d’an k’aramin  bakin shi  Ya ce.” Haba  Sultan taya  zakace  wai karna  damu! Ka duba fa wannan  k’azamar  Y’ar Talakawa  kucaka  marar  tarbiya mai gantali  da Kasuwa, ta had’a jikin  ta da nawa taya  zaka ce ba wani  abu bane? Kaima kasan  ai  wannan  renin hankali ne. Imam  ya k’arashe maganar yana  cire rigar shi……

Sultan  baiyi  mamakin  jin haka daga  Abokin  nashi  ba, saboda ya riga daya  san yadda  Imam ya tsani  Talaka  baya  son had’a  guri  da Talaka, zaiyi  magana  yaga  Imam  ya shige  toilet  yana kwarara  amai.  Zama  Yayi ya dafe kanshi  Ya ce.” Ya Allah! Ina rok’on ka da Sunayen  ka tsarkaka Allah  ka  shirya  min Abokina,  Allah ka jarabceshi  da son  Y’ar Talakawa ita kuma Tace” duk Duniya va wanda ta tsana  kamar shi, dauke hannun  shi Yayi  yana fad’in. Wallahi  Imam  sai kaga yadda  rayuwa zatayi  dakai! Ni bansan  wani  irin  bak’ar  zuciya ne dakai  ba! Wai kake cewa  baka son Talaka ko? To Insha Allah  Y’ar  Talakawa  ce Matar ka, kuma itama  sai yi  kamar  kayi  hauka  akan  son ta tukun  ta aure ka, banza  kawai  shashasha,  Wallahi  da ana  cenja  zuciyar Mutum  ba tare  da sanin  mai zuciyar ba dana  canja  taka!  Zakaga yadda  ake wulak’anta  Talaka,  saika nemi  taimakon  Talaka a rayuwar ka.. Sultan  iya  matuk’ar  b’acin rai yau  Imam  ya k’ure shi, saboda  yadda  yake fad’awa  Imam  bak’ar  magana……

Fitowa  Imam  Yayi  yana  wani  done hanci  sai  shinshina  jikin  shi yake yana yin  kamar  zaiyi  amai , Ya ce.” Oho  dai koma meye  kai kasan  har abada  bazan  taba  neman taimakon  talaka ba, kuma  ko a mafarki  bazan taba had’a gurin  zama  da Y’ar Talakawa ba bare har na zauna inuwa  d’aya  da ita a matsayin Matar aure na ta Sunna, kai meye  had’in ka  da wannan  banzayen  Yaran  da har kake fad’a min magana  a kansu?

Sultan  Ya ce.” Y’an Uwana ne tinda suma mutane  ne kuma Musulmai  , k’ila ma sun fika matsayi da daraja a wajan  Ubangiji,  Wallahi  Imam  kabi  Duniya a hankali! Nifa gaskiya  nake fad’a  maka , duk Abun  da kaga ina maka son ina k’aunar  kane tsakani da Allah,  sai fa Masoyin ka yake fad’a maka  gaskiya  duk d’acinta! Ka sani  ita fa rayuwar  ba wata mai tsayi  bace, Imam  ka zauna  da kowa lafiya saboda  baka san  nan gaba waye zai taimake kaba! Yanzu  su Yaran  da kake  fad’a  musu  bak’ar magana kana tunani  wata  rana bazasu  taimake  kaba? To ka canja  halin ka tin kafin Duniya da Mutanen  cikin ta su canja maka! Idan  kaga dama ka dauka,idan baka ga dama ba karka dauka ruwanka ne. Sultan na gama  maganar shi ya janyo  wayar shi ya danna kira……

Imam  kuwa ko  a jikin shi babu  wata magana data shigeshi saima mita daya soma yana fad’in. Ba dama Mutum yayi  abu sai an mishi sa ido  to ni bazan iya irin wannan  banzan halin  naka ba, kai kowa ma ka gani saika ce zaka kula shi , kuam Allah  ya kiyaye  ma wannan  marassa  tarbiyar Yaran  su taimakeni,  ko  mafarki  nayi sun taimake  ne inna tashi  sai nayi  Addu’ar neman tsari dasu…..

Sultan  na jin shi  amma  ya maida shi gefe yaci gaba  da maganar  da yake a waya, Ya ce.” Y’an Mata  ya jikin  naki? Kiyi Hak’uri kinga banzo na duba kiba Wallahi  mun  zo K’asar Kwatano  ne bama Gida, amma  inna koma zanzo yaga ya jikin naki yake….

Daga cikin wayar  Yarinyar ta soma magana ,dayake ya bud’e  volume d’in ne duk dan ya cusawa  Imam  haushi,  Ta ce.” Uncle yau she zaka  dawo? Inaso na ganka  kuma Mama  ta nuk’o  gari zata maka tuwon  gero  da miyan  kuka, to da baka zoba sai ta shanya ya bushe Tace” wai sai kazo  sai ta maka, Uncle  ka siyo min Teddy mai kyau  inaso kaji! 

Y’ar dariya Yayi Ya ce” to shikenan  zan kuwa siyo  miki, kice wa Mama  na kusa zuwa Gida  tayimin  tuwon dama na jima banci tuwo ba.. To Yarinyar  Tace” mishi tukun sukayi Sallama….

Done hanci  Imam  Yayi  Ya ce.” Wai kai har  Yanzu  kana tare  da wannan  Y’ar Yarinyar? Har da wani  a maka tuwon  gero da miyan kuka, wai Allah  kamar  nayi amai  nakeji,  ai ko  ciwon  mutuwa nake bazan ci tuwon  gero ba…..

Sultan Ya ce.” To ina ruwan ka? Ni  da nakeso ai zanci  d’an renin hankali,  kaje kayi duk Abun da kaga dama.. Yana fad’in haka  ya kwanta ya juya mishi  baya. Shima Imam  kaya ya saka  marar nauyi  ya kwanta a gefe d’aya  yana cin alwashin  duk ranar  daya  gamu  da Iman ko  Sultana saiya musu  rashin mutumci,  tinda a kansu  ne har  Sultan  yake mishi muguwar  Addu’a, saiya wulak’anta su fiye  da yadda  basa  tunani  tinda su basu da tarbiya. Haka dai yake karatun  jaki  har  bacci  Yayi  gaba dashi………

**************************

Hanan ce ta fito  jiki a sanyaye  ta saka  hijabin ta, komai a sanyaye take inta tuna wai  ita ce zatayi  auren  cin  amana? Hakan na sakata damuwa, su Saudat  ta raka  school  tukun  ta nufi  Gidan  Maman Islam.  Da Sallama  ta shiga tana   kallon  ko ina kamar  wata  B’akuwa a Gidan. 

Ilham ce ta fito  tana  saka  mayafi  kafad’ar ta dauke da Y’ar k’aramar  jakar ta, cikin  fara’a  Ta ce .”A q Hanan  kece dama jiran ki nake yi sai gaki  kinzo….

Cike da fargaba  Hanan  ta dafe  kirji  Ta ce.” Ni  kuma Anty! Allah  yasa  ba wani  abu  nayi ba…

Ilham  dariya Tayi ganin  yadda ta tsorata  Ta ce”. Babu  Abun  da kikayi   Hanan  girki  zaki mana  duka daku zanje Unguwa ne, kafin na dawo k’ila  kin gama ko  kin kusa…

Hanan Ta ce.” To Anty  amma in kika jima zan tafi Gida.

Ilham Ta ce” to bazan jima ba na tafi saina dawo. Tana fad’in bata ko tsaya jin  Abun da Hanan  zata fad’a ba ta wuce …..

Ajiyar  zuciya  Hanan  ta sauke  tukun  ta shiga kitchen d’in,  Abinci mai sauk’i  Ta dafa, komai a gaggauce take yi  saboda  bata so Yaya Faris yazo  ya sameta a Gidan, tana  gamawa  ta jere  kulolin  Abincin a kan  dirning…

Duk  Abun da take  Yana zaune yana kallon ta shi dariya ma ta bashi  ganin  yadda  take sauri,  baiyi  magana saboda yanaso ya more da kallon ta…

Hanan ta fito  falon,  dan kwalin  ta ta cire  tana zama a kan kujera Ta ce.” Wash Allah  gaskiya  na gaj… Ai bata k’arasa maganar  ba  tayi  ido  hud’u  da Faris  har tana  gogar  kafad’ar shi.  Da sauri ta yunkura  zata  mike Yayi  saurin  janyota  ta fad’o jikin shi ya rufe mata baki…….

Zaro  ido  Tayi  jin ta a jikin shi, sosai  taji yadda  zuciyar shi take  bugawa da sauri da sauri, jin ya k’ara  rumgume ta sai Abun  ya tsorata matuk’a  gaban ta na dukan  uku- uku jin yadda  ya matse ta kamar  zai maida ta cikin shi…….

_Wannan Littafin na kud’i ne ki biya naki kud’in Sister domin ayi tafiyar nan dake_

_Nomal N 300 ne_

_Vip  N500 ne_

TAKU HAR KULLIN MAMAN NUSAIBA CE ✍? ALK’ALAMI YAFI TAKOBI ?️?

About AIS

Check Also

K’ADDARA CE CHAPTER 2 BY MAMAN NUSAIBA

K’ADDARA CE CHAPTER 2 BY MAMAN NUSAIBA  Www.bankinhausanovels.com.ng  Marubuciyar  *AMEER DA AMEERA* *ALJANAR JARUMAI* *HAFSAT* …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *