JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 5 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI

JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 5 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

lafiyan da zan samar a tsakaninka da sarki mazwan. ka,
Yaron zai zo birnin ku yana neman taimakon ka,
saboda sarki mazwan yana son halaka yaron kai kuma
ya zamar maka dole ka taimake shi ka kubutar da shi,
zan mallaka maka wasu dawakai guda biyu baki da
fari kuma zan yi wata tsatsuba a bayan gidanka tanan
zaka fitar da yaron kuma dole ka hadasu da ‘yarka shi
ka bashi farin doki ita kuma ka bata baki ka aika da su
zuwa birnin sin anan za a koya musu horo na yaki Ta
dan saurara kadan taci gaba.
Ka sani yakai jamhas duk wanda bai Www.bankinhausanovels.com.ng
taimaki wannan yaron ba babu shakka nan gaba zai
kasance cikin kaskanci saboda jarumi ne dan baiwa.
Yana da abin al’ajabi mai tarin yawa shi ne kuma zai
kawo karshen bakin zallunci sarki mazwan zai kawo
zaman lafiya da kwanciyar hankali, ka sani duk duniya
babu wani wanda ya isa yın nasara akan sarki mazwan
face wannan yaron, tabbas ya bayyana gare ni sai ya
zo wannan birnin naku, kuma tsakanin kai da sarki
kasar Nur daya daga cikinku wani zai mallaki takobin
sarki mazwan wacce ita ce sirrin mulkinsa.
Amman abinda sarki mazwan da bokansa
basu sani ba wannan takobin ba komai bace a tarihin


mulkinsa, wannan lamarin ya boyewa boka marmasi a
cikin sha’anin bokancinsa kuma ba zai taba gano
gano
hakan ba sai lokacin da yaro dan baiwa ya bayyana, za
su fahimci sun aikata kuskure wanda ba za su taba
gyara shi ba kasan shi zalinci baya taba dorewa
Yanzu menene abinyi inji sarki jamhaz
“Ka taimaka masa ka tura shi zuwa birnin
sin Cikin kadu yace mata.
“Birnin sin fa kika ce birnin da zuwan sa
yafi komai tashin hankali da hatsari na tsafafiyar
yafi birina da kuma mashahuran yan fashi ga balai kala-
kala a hanyar zuwa kasar ta sin, haka idan mutum ya
isa birnin bai tsira ba saboda acan cibiyar mashahuran
bokaye ta duniya take kuma a can ake saye da sayarwa
na tsafi akan hanya a ko ina zaka koyi sihiri na tsafi
acan idan baka zama matsafi ba tabbas ba zaka iya
zaman kasar ba” Jin wannan kalamin ya saka macen
sirri ta yi murmushi har sai da hakoranta suka
bayyana. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wannan duk abinda kake gani lamari ne na
sihiri domin a rika wahalar da jama’a, wannan birinyar
da take tsare fatake tana kashe su wani boka ne ya
samar da ita domin ta adabi jama’ar da suke kai kawo
a wannan dajin zuwa birnin sin. Anyi haka ne domin
hana jama’ar da suke tureniyar zuwa birnin sin.domin
koyon tsatsuba da kuma kai bayi.
Nasan baka da sanin kasar shamawa ta
kasance babbar daula data shahara wajen sayen bayi da
kuma sayar da su zuwa ga manya dauloli wannan
damar ya saka ta kula yarjejeniya da kasashe masu
a hankali yace mata.
Ina jinki kina bayani game da samuwar
birinyar tsafi wacce ta adabi aljanu da mutanen da
suke ilahirin dajin Macen sirri tayi murmushi a
hankali tace masa.
“Ku ‘yan adam kuna son jin labarai, bari kaji labarin na su a takaice, duk dana san tarihin duk
duniya
babu mai halaka tsafafiyar birinya sai jarumi dan
baiwa Ta saurara tana kallonsa sannan ta ci gaba.
Bayan wani dogon zamani sarakuna sun
gabata a wani karni aka yi babbar daula ta kasar sin,
ita kuma kasar shamara tana can gefe da kasar judan
karamar kasa ce da take cikin tsuburi da sai ka ratsa
kwazazzabai da dajujjuka sannan zaka karasa zuwa
kasar sin.
A wannan lokacin babu abinda yake ci sama
da tsafi duk wanda ya iya tsafi shi ne mai dukiya mai
kuma iko da kowa a garin. Wannan dalilin yasa jama’a
da dama suka rika bazama cikin duniya domin koyyo
tsafi.
Kasar shamara suna bin tafarkin duk wanda yafi
wani karfin tsafi shi ne zai zama sarkin daular wannan
dalilin ya saka sarakunan da suke kasar basa jimawa akan
mulki, saboda duk lokacin da wanda ya fi ka karfi ya zo zai
kashe ka ya haye kan karagar.
Jama’ar kasar da kuma wani shashashan dan sarki wanda
duniya bata dame shi ba, a iya tarihin kasar ba a taba yin
sokon dan sarki kamarsa ba.
Mulkin babansa bai dame shi ba zaka same shi Www.bankinhausanovels.com.ng
ko wane lokaci a karkashin bishiyar mangwaro yana
kallon iskar dake kada ruwan wani tabki da yake gaba kadan
da gidan sarki, wannan dabi’ar tasa tana damun mahaifinsa
ganin cewar tsufa ya kama shi kuma gashi dansa ba zai gaje
shi ba saboda bai san tsafi ba ko na sisin kwabo.
Hakan ya saka ya kasance cikin fargaba da
faduwar gaba, wannan dalilin ya saka sha’anin mulki ya
soma tangarda yana samun koma baya. Saboda yasan
tabbas idan ya fadi ya mutu abokin gabanshi đan boka
dukum ne zai gaji sarautar. Kuma yasan halin jamru ba shi
da tausayi bai ki idan aka zo fitar da gwani na magajin
sarauta ba ya kashe dansa kamzu, saboda yana bukatar
daukar fansar abinda sarki ya yi wa kakansu ya amshe
mulki a hannunsa.
Yasan babu makawa sai jamru ya yi amfani da
tsatsuba kala-kala saboda ganin bayan kamzu, hakan yana
nuna za a yi haihuwar guzuma da kwance uwa kwance zai
zama mutuwarsa data dansa takin sa’a ne.
Tunda ana gudanar da gasar zama sabon sarki
ne sa a uku bayan mutuwar tsohon sarki duk mai sha’awar
shiga zai zama ya iya tsatsuba gwani kuma wajen iya
bokanci.
A safiyar yau ne sarki lakamu ya kirawo dansa
cikin turakarsa yana kishingide suka zauna yana kallonsa
cikin nutsuwa fuskarsa sam babu walwala yace masa “Me
Ban tanadi komai ba, tunda kaga ni ba jarumi
bane kuma ban iya tsafi ba. Haka kuma ban maida
hankali domin koyon ko daya ba Jin wannan maganar ba
Raramin konawa sarki rai ta yi ba.
Kai tafi can soko sulutun banza gwara
haihuwar mace da kai… kana zaton akwai wanda zai gaji
sarauta cikin sauki,  ka tashi tsaye domin
neman kariya idan ba haka ba tabbas jamru ba zai sassauta
maka ba. Ni kuma da kake gani kaga dai tsufa ya riske ni
babu wani taimako da zan iya baka sai dai wanda ba a rasa
ba, saboda duk wanda zan baka zuwa yanzu jamru yasan
shi, saboda ya zama gagarabadau a fagen sihirin tsafi
Wadannan kalaman sun dagawa kanzu hankali, shi a
ra’ ayinsa sam babu ruwansa da sarauta saboda baya fatan
gadon mahaifinsa saboda ganin yadda ake fama da tsatsuba
da amfani da jinin mutane ana yin bokanci.
Wannan abun yana damunsa yasan zalunci ne Www.bankinhausanovels.com.ng
da kuma neman duniya. Yana gani wani lokacin za a yanka
jarirai a yi sihiri dashi ko kuma a bine mutum da ranshi a
kasa sai ya yi kwana goma sanan a tono sassan jikinsa a yi
sihiri da shi, ganin wannan zallunci ne yana daga masa
hankali yasa baya kaunar mulkin na mahaifinsa.
Amman wannan kalamin na mahaifinsa sun
tsuma masa zuciya, ya soma tunanin kalamin da zai fadawa
mahaifinsa domin kwantar masa da hankali. “Kayi hakuri
ya mahaifina tabbas baya taba yiyuwa barewa tayi gudu
danta ya yi rarafe, kai ka zama madaukaki shi yasa kowa
yake tsoronka amma ni kuma ban dauki ko daya daga cikin
wannan ranar ta zo, zan so wannan ranar ta zo min a
lokacin kana numfashi tabbas da sai ka yi alfahari da ni
domin zan zama mashahuri, kuma zan kauda tsafi daga
doron duniya domin ni sam ban bada imani da su ba
Wannan maganar ba karamin dagawa mahaifinsa hankali ta
yi ba.
“Kar ka zo min da irin wannan salon na
maganar bana jin wanan maganar zata zama mai tasiri a
gare ni, don haka na umarce ka daka tashi tsaye domin
neman tsatsuba da sirrin tsafi domin kare kanka Ya jinjina
kai.
Zan nemi mafita wacce zata kare ni” Yana
gama fadin haka ya tashi ya fita ya nufi can wajen daya
saba zuwa yana zama, shi kam yasan jarumtaka ba zata kai
shi tudun muntsira ba domin jamru ya kasance gawurtacen
jarumi haka kuma mashahuri a fagen tsafi idan haka ne ta
yaya rago kamarsa zai samu nasara akansa har ya dare kan
karagar sarautar mahaifinsa? Sanin hakan ba mai yiwuwa
bane shi yasa ya cire ransa daga kan lamarin yasan kuma
duk lokacin da jamru ya zama sarkin kasar sai dai shi da
iyayensa su idan kuma ba haka ba sai ya kashe su ko kuma
ya rika gana musu azaba har zuwa lokacin da za su halaka
don haka ya zamar masa dole ya nemo mafita.
Kanzu ya ji duk abin duniya ya yi masa yawa
ya rasa ina zai saka kansa, yana zaune a wajen da yake har
zuwa gefen faduwar rana sai ya ji wani sanyi yana sirarowa
sanyi da sai daya saka jikin kanzu ya soma karkarwa yana
makyarkyatar sanyi. Zuwa wani lokaci sai iskar ta tsaya
wata mace doguwa mai kyawun diri ta bayyana tunda yake
yake cikin tsananin tsoro ya mike da zumar zurawa da gudu
amman sai ya ji kafafunsa sun saki sun koma kamar
jikaken lagwani yana wajen har farar macen ta karaso
wajensa zuwa wani dan takin lokaci tace masa.
Ko kasan ni wacece? Ya gyada kai.
A’a amman alamu sun nuna ke sarauniyar
aljanu ce Tayi murmushi.
Ka saki jikinka ka daina jin tsorona domin da
ina da nufin cutar da kai a duk lokacin daka zo bakin kogin
nan ka zauna. Ka sa ni na kasance sarauniyar aljanun cikin
ruwa kuma bani da wajen zama face wannan kogın na
kasance ina bin addinin musulunci, babu cutarwa a cikinsa
yana kuma hani da aikata zallunci da mugunta da hani da
aiwatar da kafirci” Ta saurara tana kallonsa sannan ta ci
gaba da magana. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ka yi sani cewar na zo ne domin na taimake
ka, saboda da zu ina jin yadda kuka yi da mahaifinka kumna
gaskiya. ya fada maka saboda idan jamru ya zama sarki za
ku kasance cikin kaskanci, haka kuma jama’ar kasar za su
kasance cikin kaskanci da tagayyara wanda babu ranar fita
daga ciki. A wannan zamanin babu jarumi kamar Jamru
haka kuma a fanin tsafi, don haka ina kiranka daka zamo
ma’abocin-musulunci addinin da bai aminta da tsafi ba” Ai
koda ya ji wannan maganar cikin sauri ya saukar da
numfashi yace mata.
“Ni kamar mahaukaci ne da yake jin yunwa
komai na samu ci zanyi haka kuma kamar wanda ruwa ne
ya ci yo shi, don haka zan amshi wanna addinin da kika zo
saka sarauniyar aljanun Cikin aljanu tayi murmushi.
Babu shakka zaka kubuta daga sharinsa yanzu
abinda nake so dakai shi ne ka shiga cikin kasuwar bayi
zaka samu an kawo wata bakar baiwa ka siyeta tana bin
addinin musulunci, sai ka bata aminci da salama ka kuma
nemi ta sanar da kai komai daya shafi addinin tsira hakan
zai kubutar dakai daga duk wani sharrin jamru Tana kawo
wanan sai ya ji iskar da take kadawa ta dauke ta koma
daidai kamar bata taba faruwa ba.
Ganin haka yasa ya sauke ajiyar zuciya ya tashi
cikin sauri da azama ya nufi cikin kasuwar bayi da zumar
ya sayi wannan bakar baiwar yana shiga cikin kasuwar ya
Soma dube-dube yana waige-waige ko zai ga bakar baiwa
amma ko kadan bai samu damar hakan ba. Haka ya yi ta
yawo duk wajen daya gifta sai jama’a su zube suna yin
gaisuwa a gare shi wasu suna cewa gaisuwa ga sarki mai
Jiran gado, amman shi bata su yake ba abinda ya kawo shi
kawai yake yi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan ya gaji da nema har zuwa yamma rana ta
tafi faduwa a lokacin ya gaji tikis da nema ya fita da ran
samun wannan bakar baiwa ya zo fita daga cikin kasuwar
bayin ya ci karo da wani ayari na fatake sun shigo cikin
kasuwar ga alama zuwansu kenan a cikin bayin daya gani
suna cikin sarka hard a wata kyakkyawar bakar fata baiwa
tana cikin sarka hannu da kafa kanzu ya zuba mata idanu
yana kallonta babu shakka ita ya zo nema.
Cikin sauri ya sha gaban shugaban ayarin
shugaban su yana ganinsa ya yi saurin zubewa a gabansa

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 1 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI

JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 1 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI Www.bankinhausanovels.com.ng  JARUMI DAN BAIWAYaro ne …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *