JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 4 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI

JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 4 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

cikin wani faffadan waje daya kilace ya kuma karamin
kogi a gidansa yana kiwon kadoji.
Wannan birnin na arnan daji ya kasance
yana da kyau da kuma tsari anyi gidajen daga duwatsu
suna mulki a karkashin sarkin su Jamhas wanda ya
kasance gawurtacen jarumi mai juriya da kuma bajinta
a fagen fama.
Matsala daya take damun sarki jamhas shi
ne rashin samun haihuwa, ya yi maganin ya kuma bi
bokaye da ‘yan tsubu ya yi tsatsuba amman haihuwar
bata samu ba hakan ya saka ya hakura ya saka
sha’anin sarautarsa a gaba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka suka ci gaba bauta ga wannan gunki
suna yi masa hadaya da jinin duk wani bako da suka
kamo,kuma hasalin yiwa gunki hadaya ya samo asali
ne daga gabar da suke yi da jama’ ar Birnin
Hindu wanda gunki ne yake basu sa’a a duk lokacin da
suka tashi yin artabu da dakarun birnin Hindu.
Ana kawo sham gaban sarki jamhas ya tashi
yana dubansa cikin nutsuwa ya daga kai yana kallon
dakarunsa yace musu.
Ya naganshi a cikin wannan halin na


Ya
galabaita kuma ga ciwo a jikinsa? Anya kuwa abin
bautar mu zai amshi wannan a matsayin hadayar da za
mu yi masa? Ya ci gaba da kallon sham sannan ya
tashi yana zagaya shi.
*”Wane irin ciwO ne ya samu wannan har ya
kasance a kwance kamar matacce?” cikin sauri ya
shiga wani dakin da yake kusa da fadar wanda anan
kayan tsatsubarsa yake. Ya dauko madubin sihiri ya
soma bincike akansa nan yaga artabun da ya yi da
jama’ar kasar Hindu da yanda suka shigo cikin dajin
tare da macen sirri. Amman abinda ya bashi mamaki
ya kuma daure masa kai yadda madubinsa ya kasa
nuna masa macen sirrin.
Ya yi iya yinsa domin ganin ya samu bayani
akan macen sirri da kuma nemo daga wane jinsi ta fito
ganin haka ya saka hankalin sarki jamhas ya tashi,
cikin zafin nama ya ajiye madubin tsafin ya dauko
kayan tsatsuba ya bude kwatarniyar tsafí ya baza wuri
ya soma duba bisa tafarkin tsafi.
A lokacin da yake wannan binciken game
da wacce ce macen sirri ita kuma a lokacin ta shigo
cikin birnin arnan daji cikin fushi da fusatar zuciya.
Macen sirrin kai tsaye ta shiga cikin fada
ai kuwa dakarun fada suna ganinta suka yo kanta cikin
halin fushi suna daka mata tsawa.
“Ke yarinya wane ya baki izinin shigowa Www.bankinhausanovels.com.ng
cikin garin nan babu shakka halaka ce ta kawo ki
Macen sirri ta daga kai tana dubansa kafin tayi wani
murmushi mai dauke da fushi tana kallon yadda suke
kusanto kawunan su zuwa ga halaka tabbas yaro
baisan wuta ba sai ya takata.
“Kana kallona kasan ban yi kama da
yarinya ba, domin yarinta tana bayan mahaifiyarta
ahir! Dinka da kuma gangancin kuma fadar wannan
Kalmar, maza ku miko min abokin tafiyata cikin
ruwan sanyi idan ba haka ba fushina ya sauka akan ku
Nan wani ma gigiwa
ya yo kanta cikin fusata
musamman domin ganin mace ce bata da wani
jarumtaka.
Rashin sani yafi dare duhu. Yana zuwa kusa
da ita yakai hannu da zumar zungure mata hanci
amman ga mamakınsa sai ya j1 hannunsa ya soma
lakwashewa yana komawa zuwa cikin hancinsa, nan
yaga lamarin bana wasa bane, ya soma kokarin hana
faruwar hakan amman ya kasa take ya soma kwaranya
ihu take jini ya soma fita daga cikin hancinsa ta sake shi ya fadi yana burgima a kasa.
Ganin wannan abin mamakin daya faru ya
saka sauran dakarun suka sha jinin jikinsu, tabbas
wanan macen tana takama da sirrin tsafi idan kuma
haka ne gidan shi ta zo, haka ya saka suka ja da baya
wasu dakaru da aka horesu da tsafi suka dawo gaba
nan suka soma tsatsubaa sai kaga badakare ya zama
zaki yayo kanta da gudu, kafin ya karaso wajenta sai
dai kaga ta kalle shi da ido sai kaga wata iska ta sure
shi tayi watsi da shi can gefe guda.
Sai kaga wasu a cikinsu sun zama wuta
kafin su zo wajen sai wani ruwa ya baiyana ya hadiye
su. Ai ko da ganin sirrinta yafi na su sai suka yi dauki
kanta da takobi a zare, masu kibiya suka soma yi mata
ruwan kibiya amman abin mamaki duk kibiyar data je
jikinta sai kaga ta narke ta zama ruwa ta zube a kasa.
Hakan bai hana su dauki kanta,ba abin kallo Www.bankinhausanovels.com.ng
ya samu nan suka gauraya ta zare takobin sarki samzan
data amsa nan fa kasuwar yaki ta soma ci, mutuwa ta
soma shawagi a tsakaninsu kawunan sadaukai na
birnin arnan daji ya soma zuba a kasa kamar ana
sassabe.
Babu abinda zaka gani sai gilmawar
makamin macen sirri yana ratsa tsakanin mazaje yana
fasa kirjinsu zuciya tana fadowa kasa jini yana zuba
shaaa! Kamar gulbin ruwa. Kalar jan jinin dakarun
birnin Arnan daji su kansu suka san cewar yau wata
shaidaniya ta sauka a kasar su yau kam sun tsokano
tsuliyar dodo.
Suna cikin wannan dauki ba dadi suka ji an
kwatsama musu wata tsawa cikin sauri suka ja da baya
suka tsaya carko-carko kamar zakaru suna kallon
junansu a lokacin sarki jamhas ya fito daga cikin dakin
tsatsubar shi cikin fushi ya dubi ginin fadar yaga yadda
ya rine da jinin jama’ arsa ya dubi kasa yaga yanda
kawuna suka wadata a zube.babu jikuna take ya tsorata
da shu’umanci macen sirri babu shakka yanzu ya
gamsu ita ce.
Ya yi saurin dakawa jama’arsa tsawa da
cewar. Maza ku zubar da makamanku kuma ku zube
gabanta domin nemn afuwa akan zunubin da kuka
aikata mata Ai kuwa da jin wannan kalaman na sarki
sai mamaki ya kama su suka zube a gaban macen sirri
suna neman tuba.
Sarki jamhas ya karasa gabanta ya kalleta
cikin girmamawa yace mata.
Muna neman afuwa bisa laifin da muka
aikata cikin rashin sani. Tun sanda naga abokin
tafiyarki na shiga cikin dakin bokancina domin gano
wane shi, a bincikena ne komai na ki ya bayyana a
gare ni don haka muna neman afuwa a gareki bisa
wannan lamarin da muka aikata miki Jin kalaminsa
ya saka macen sirri ta maida makaminta ba tare data ce
komai ba ta nufi wajen da sham yake tana zuwa ta
sunkuya ta dauke shi cak kamar ta dauki karmami ta
nufi wajen da karagar sarki jamhas take ta kwantar da
shi ta tsaya tana kallonsa har lokacin numfashinsa yana
fita. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sarki jamhas ya yo wajenta cikin sauri ya
zo kanta yana kallon sham zuwa wani lokaci ya nisa
yace mata.
Takobin sarki mazwan ce tana dauke da
wani dafi, kuma wannan dafin yana halaka mutum.
Badon sham yana da nisan kwana ba da tuni ya halaka.
Don haka mu jama’ar daji za mu karya wanna sirrin da
yake jikin takobin Take ya buda gefen duga-diginsa
ya dauko wata yar buta ya dauko wani guntun dan
itace ya karyo shi ya saka a baki ya taunashi ya soma
marmasa masa a wajen daya ji ciwon.
Ai kuwa mintina goma da yin haka sai
ciwon ya soma wata irin kumfa wajen yana tafasa
kamar an saka abu a cikin wuta, kafin wani lokaci
wajen ya gama zabalbala a hankali ya soma kamewa
Yana komawa kamar babu abinda ya faru a wajen a
lokacin sham ya bude idonsa suka hada ido da macen
sirri suka yi murmushi.
Ya mike yana duban jama’ ar Arnan daji
sannan ya maida hankalinsa zuwa ga sarki jamhas.
Ina godiya bisa kubutar da ni da ka yi, kuma ina yi
maka jajen rashin jama’ar ka da ka yi wanda macen
sirri ta yi maka, nasan idan za ku shekara kuna
fafatawa ba zata taba saduda ba. Ita da kuke ganinta
hatta ni tsoron fushinta nake saboda bata san ayi hakuri
ba. Kune alkarya da kuka bata mata rai bata karar da
ku ba” Macen sirri ta yi murmushi jin abinda ya fada
ta dubi sarki jamhas tace masa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kar ka damu nima zan saka maka da alheri
kamar yadda ka taimake ni, zan baka maganin
matsalarka ta rashin samun haihuwa, matarka zata
haifa maka ya mace wacce zata zama jaruma mai
bajinta, kuma zan kawo karshen wannan bakar gabar da take
tsakaninka da sarki mazwan wanda hakan zai bunkasa
tattalin ar in ku” Tayi shiru tana dubanin birnin
arnan daji ta kuma kallon sarki jamhas wannan karon
babu walwala akan fuskarta.
“Ina bakin cikin sanar da kai nan gaba za a
haifi wani yaro da zai kawo karshen wannan zaman

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 1 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI

JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 1 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI Www.bankinhausanovels.com.ng  JARUMI DAN BAIWAYaro ne …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *